Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zan
fada maka, ka dauke su da muhimmanci."

Nuruddin ya wasici dansa da ya zamanto mutum
mai yawan ibada da neman gafarar Allah
madaukakin Sarki, ya kasance mai ladabi da
girmama na gaba da shi, ya zama mai rikon
alkawari da amana, ya kasance mai tausayi da
adalci. Ya yi ta yi masa nasihohi a kan neman
lahira, zaman finite da kuma sha'anin mulki.

Daga nan sai ya tuna da dan uwansa
Shamsuddin, da abin da ya faru tsakaninsu har
ya bar gida. Hankalinsa ya tashi, ya yi kewar dan
uwansa, da garinsu, ya fashe da kuka.
Bayan ya gama kuka, ya dubi dansa ya ce, "Ka
sani ya dana, ina da dan uwa mai suna
Shamsuddin, shi ne Wazirin birnin Misira,

bappanka ne. Na rabu da shi, na bar gida ba da
yardarsa ba. Ina so ka dauko takarda da tawada
in labarta maka abin da ya faru tsakaninmu
duka, ka rubuta." Hassan ya tashi ya dauko
takarda da tawada ya kawo. Waziri Nuruddin ya
kwashe duka labarinsa da dan uwansa
Shamsuddin, yadda suka tashi tun suna yara, da
yadda mahaifinsu ya mutu suka gaji sarautarsa
ta Wazirin Misira, da yadda suka rika raba
karagar Wazirtaka tsakaninsu, da niyyarsu ta
hada 'ya'yansu aure wdda ta jawo gardamar da
har Shamsuddin ya yi masa gorin Wazirtaka
wanda ya sa shi fushi ya bar garin, duk ya fada
wa Hassan, shi kuma yana rubutawa.

Sa'annan kuma ya fada masa yadda ya iso
Basara, da yadda ya auri 'yar Wazirin Basara, da
ranar da aka yi auren, ranar da ta yi daidai da
ranar da aka nada shi Wazirin Basara, da ranar
da aka haifi Hassan, duk ya fada wa Hassan,
wanda shi kuma ya rubuce komai cikin takarda.
Nuruddin ya ce da dansa, "Ka kiyaye wannan
takarda, duk tarihinka da asalinka yana cikinta,

ko bayan raina idan mutanen wannan birni sun
juya maka baya, domin ni ina jin tsoron zamani,

to ka nufi Misira ka nemi bappanka. Idan ka
gaishe shi, ka sanar da shi ko kai wanene. Ka
fada masa cewa na mutu bako a garin wasu ina
mai tsananin begensa, ya gafarta mini laifin da
na yi masa."

Hassan ya nade takarda cikin wasu tsumma
masu kyau, ya yi laya da ita, ya saka ta cikin
damarun layunsa. Ya kasance yana kuka, domin
yana ganin kamar ubansa ya kusa mutuwa ne,
shi ya sa yake yi masa irin wadannan nasihohi.

Ashe kuwa haka abin yake, Nuruddin bai gushe
ba yana yi wa dansa wasiyya, tsawon 'yan
watanni kadan, ya kwanta ciwon ajali, bayan
jiyyar kwanaki kadan, sai ya ce ga garinku nan.

Hassan da mahaifiyarsa suka yi bakin ciki mara
misaltuwa.

Ba Hassan da mahaifiyarsa kadai suka yi bakin
cikin mutuwar Nuruddin ba, hatta Sarki da
fadawansa da jama'ar birnin Misira sai da suka
yi bakin ciki mai yawa. Aka rufe shi a makabartar
da ke bayan gari, inda aka rufe surukinsa, tsohon
Waziri. Aka yi zaman makoki na kwana uku.

Tun bayan mutuwar mahaifinsa, sai ya kasance
Hassan ya daina zuwa fada. Kullum yana cikin
gida yana kuka har tsawon wata biyu. Da Sarki
ya daina ganin Hassan fada, sai ya yi fushi da
shi, ya ce a ransa, "Saboda mahaifinsa ya mutu,
shi ya sa ya daina zuwa fada? Ashe ba mu da
girman da wannan yaro zai rika zuwa yana
gaishe mu? Da ma saboda mahaifinsa ne yake
zuwa?" Nan take Sarki ya nada sabon Waziri, ya
kuma ba shi umurni ya washe dukkan dukiyar da
ke gidan Waziri Nuruddin, idan ma yana so yana
iya hadawa har da dansa Hassan, ya zama
bawansa.
***

Lokacin da wannan al'amari ke faruwa a Basara,
a Misira ma wata guguwar rikicin ce ke juyawa
tsakanin 'yar Waziri Shamsuddin da Sarkin
Misira.

Ku biyo ni gobe
hkr danifa
sabida baku ganin comment dina ko like anaku
comment. aikinne dayawa adan bani uzuri..
nagode masoya05. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Tun bayan mutuwar mahaifinsa, sai ya kasance
Hassan ya daina zuwa fada. Kullum yana cikin
http://fb.com/waziriaku gida yana kuka har
tsawon wata biyu. Da Sarki ya daina ganin
Hassan fada, sai ya yi fushi da shi, ya ce a
ransa, "Don mahaifin wannan yaro ya mutu, shi
ne ya daina zuwa http://fb.com/waziriaku fada?
Ashe ba mu da girma da mutuncin da zai rika
zuwa yana gaishe mu?" Nan take Sarki ya nada
sabon Waziri, ya kuma ba shi umurni ya washe
http://fb.com/waziriaku dukkan dukiyar da ke
gidan Waziri Nuruddin, idan ma yana so yana iya
hadawa har da dansa Hassan, ya zama
bawansa.

Nan take sabon Waziri ya aika da askar zuwa
gidan Nuruddin, su rubuto dukkan dukiyar da ya
mutu ya bari, sa'annan su dauro dansa Hassan,
su zo masa da shi. Kafin askar su isa gidan
Nuruddin, sai wani bafade, yaron Waziri
Nuruddin, ya sukwani http://fb.com/waziriaku
dokinsa a guje ya nufi gidan. Da isar bafade ya
iske Hassan a zaune, kansa na sunkuye, yana
zubar da hawaye saboda tunanin mahaifinsa.
Bafade ya ce masa, "Ya shugabana, yi hanzari ka
kama tafarkinka, Sarki ya nada sabon Waziri,
kuma ya ba shi izinin ya kwace dukkan dukiyar
mahaifinka, har kai kanka za ka zama bawansa.

Askar na nan ya turo, domin su daure ka, su tafi
da kai. Ni na ga babu adalci a cikin wannan
hukunci na Sarki, shi ya sa na zaburo domin
http://fb.com/waziriaku in sanar da kai. Yi sauri
ka fice daga wannan birni ko ka tsira da
'yancinka." Hassan ya mike tsaye da sauri, ya
ce, "Bari na shiga taska na debi wani abu domin
guzuri." Bafade ya ce, "Ya shugabana, ba ka da
lokacin da za ka dauki komai, ka yi hanzari ka
fita, kada su same ka."

Hassan ya nufi kofar gida, bai dauki komai ba
sai mayafin da ke hannunsa. Da fitarsa waje, sai
ya yi rawani da mayafin ya rufe fuskarsa, domin
gudun kada a gane shi. Ya nufi bayan gari, yana
mai bakin ciki bisa http://fb.com/waziriaku
wannan fita ta gaggawa da ya yi wa birnin
Basara, ko mahaifiyarsa bai sami yin sallama da
ita ba, bai kuma san hanyar Misira ba, inda
bappansa Shamsuddin yake Waziri, ballantana
ya nufi can.

Da fitarsa bayan gari, bayan ya tabbata ya yi
nisa da mutane, sai ya cire mayafin da ya rufe
fuskarsa da shi, sa'annan ya ce cikin ransa, bari
ya tafi makabarta, ya kai wa kabarin mahaifinsa
da na kakansa ziyara, ya yi ban kwana da
http://fb.com/waziriaku su, sa'annan ya nemi
hanyar zuwa Misira. Hassan ya nufi babbar
makabartar garin.

Yana cikin tafiya, zuciyarsa cike da tunani, bai yi
aune ba, sai ya ga mutum http://fb.com/
waziriaku a gabansa, yana jaye da rakuma,
kowane rakumi an labta masa kaya niki-niki.
Hassan ya yi niyyar ya boye wa mutumin nan,
amma ina ya makara, mutumin ya riga ya gan
shi, har ma ya gane shi. Ashe wani bayahude ne,

daya daga cikin mutanen da mahaifinsa http://
fb.com/waziriaku yake turawa zuwa fatauci, shi
ne ya dawo daga fatauci, kuma an sami riba mai
yawa.
Da ya ga Hassan sai ya ja ya tsaya, ya lura da
yanayinsa da kyau, ya ga alamun yana cikin
tashin hankali da damuwa. Ya dube shi ya ce,
"Ya shugabana, me yake damunka? Kuma ina za
ka, http://fb.com/waziriaku kai kadai cikin daji,
rana na shirin faduwa?" Hassan ya ce, "Ina cikin
bacci da rana, na yi mafarki da mahaifina, yana
zargina a kan na rabu da zuwa ziyarar
kabarinsa, shi ne na fito yanzu, hankalina a
tashe bisa http://fb.com/waziriaku wannan
zargi da mahaifina ke yi mini. Ina so in tafi
makabarta ne domin ziyartar kabarinsa tare da yi
masa addu'ar neman gafara, kafin dare ya yi in
koma gida."
Bayahude ya rike baki cikin tausayi da mamaki,

domin bai ji labarin mutuwar Maigidansa
Nuruddin ba, ya bar Basara zuwa fatauci, tun
wata biyar da suka wuce. Bayan ya yi wa
Hassan gaisuwar mutuwar mahaifinsa, sai ya ce,
"Ya shugabana, yanzu kai ne zan hannunta
http://fb.com/waziriaku wa wadannan kaya na
dukiya, duk mallakar mahaifinka ne." Hassan ya
ce, "Ba ni da bukatar dukiya yanzu, idan akwai
tsabar kudi a wurinka, na fi bukatarsu, sauran
kayan na bar maka su kyauta." Bayahude ya
zaro wata yar jaka ta kudi, ya mika wa Hassan,
ya ce, "Akwai kudi a cikin wannan jaka, dinari
dubu uku, amma ina so ka rubuta mini takarda,
shaidar ka mallaka mini wannan dukiya."

Hassan Badaruddin ya karbi kudi, bayahude ya
dauko takarda da tawada daga cikin kayansa ya
mika masa. Hassan ya rubuta takardar mallaka
wa bayahude kaya, ya mika masa. Bayahude ya
karbi takarda, ya yi wa Hassan godiya, ya juya
da http://fb.com/waziriaku rakumansa, bai ko
shiga Basara ba, ya nufi wani birnin inda ya san
zai sayar da hajarsa da daraja. Hassan kuwa ya
yi wa Allah godiya da ya sami kudin da zai yi
guzuri da su har zuwa Misira. Ya kulle jaka a
zariyar wandonsa, ya nufi makabarta, wajen
kabarin mahaifinsa.

Koda ya isa cikin makabartar yamma ta yi, ya
nufi inda kabarin ubansa yake, ya zauna yana yi
masa addu'a yana hawaye, yana tunanin juyin
zamani a kansa. Da, yana zaman dan Waziri ne,

cikin jin dadi da walwala, amma ga shi http://
fb.com/waziriaku yanzu bayan rasuwar
mahaifinsa ya zama dan gudun hijira, wannan
wane irin zamani ne? Wannan shi ake kira da
'mutuwa mai tonon asiri.' Bai gushe ba yana
zaune wurin kabarin nan, yana tunani, har barci
ya kwashe shi saboda gajiya, ya yi kwance
fuskarsa tana kallon sama.
Hassan Badaruddin ya tsunduma cikin barci mai
nauyi har dare ya yi, farin wata ya fito ya haske
fuskarsa, tana ta kyalli kamar mudubi. Allah da
ikonsa, ya nufi wata aljana, musulma, ta shiga
cikin makabartar. Ta ga Hassan kwance yana
barci, ta kura masa ido, tana kallon irin baiwar
kyau da http://fb.com/waziriaku cikar halitta
wadanda Allah ya yi masa. Ta ce, "Tsarki ya
tabbata ga Allah madaukakin Sarki, wanda ya
halicci wannan yaro da dukkan siffa ta kyau.
Hakika ko a cikin aljanu 'yan uwana, babu
tamkar wannan yaro." Bayan ta dade tana kallon
Hassan, ta tashi, ta kada zuwa ga sama, ta bar
shi nan yana barci, ta tafi tana cike da tunaninsa
a ranta.
Aljana na fita daga makabarta, sai ta hadu da
wani aljani, cikin yaran mahaifinta. Ya gaishe ta,

ta gaishe shi, sa'annan ta tambaye shi daga
inda ya fito. Ya ce mata ya fito ne daga birnin
Misira. Ta ce masa, "Zo mu je, ka ga wani
saurayi a http://fb.com/waziriaku cikin
makabartar nan, wanda babu kamarsa a kyau,
cikin wannan zamani." Ya ce da ita, "Na'am, ya
shugabata." Suka koma cikin makabarta, wurin
da Hassan yake kwance yana ta sharar barci.

Da suka isa wurinsa, suka dade suna kallon shi,

aljana ta dubi aljani, ta ce, "Duk tsawon
rayuwarka, ka taba ganin mutum mai kyawun
wannan saurayi?" Aljani ya ce, "Tsarki ya
tabbata ga mahaliccin wannan yaro, tabbas, da
farko na dauka babu wanda ya kai 'yar Wazirin
Misira kyau http://fb.com/waziriaku cikin
bil'Adam, amma yanzu na ga wanda ya kusa cim
mata da kyau, domin idan ba ta fi shi kyau ba, to
sai dai su zo daidai. Sai dai kash! Waccan
yarinyar tana cikin bakin ciki mara misaltuwa."

Aljana ta ce, "Wane irin bakin ciki take ciki?
Kuma menene sanadin bakin cikin nata?"
***
Za mu ci gaba gobe insha allahu
06. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Da aljanun nan biyu suka isa inda Hassan yake
kwance yana barci, bisa kabarin ubansa, suka
dade suna kallon shi, aljana ta dubi aljani, ta ce,

"Duk tsawon rayuwarka, ka taba ganin mutum
mai http://fb.com/waziriaku kyawun wannan
saurayi?" Aljani ya ce, "Tsarki ya tabbata ga
mahaliccin wannan yaro, tabbas, da farko na
dauka babu wanda ya kai 'yar Wazirin Misira
kyau cikin bil'Adam, amma yanzu na ga wanda
ya kusa cim mata da kyau, domin idan ba ta fi
shi kyau ba, to sai dai su zo daidai. Sai dai
kash! Waccan yarinyar tana cikin bakin ciki mara
misaltuwa." Aljana ta ce, "Wane irin bakin ciki
take ciki? Kuma menene sanadin bakin cikin
nata?"
Aljani ya ce, "Ki sani ya shugabata, tsawon
zamani a birin Misira ba a taba haihuwar yarinya
kyakkyawa ba, kamar wannan yarinya 'yar
Waziri Shamsuddin mai suna Sittul Hassanu.
Yanzu da ta girma ta kuma isa aure , Sarkin
Misira ya so ta, http://fb.com/waziriaku ya nemi
aurenta ga mahaifinta, Waziri Shamsuddin.

Amma sai Waziri ya ce da Sarki, "Ya
shugabanmu Sarkin zamani, ka karbi hanzarina,
ka share mini hawaye. Ka sani cewa ina da dan
uwa mai suna Nuruddin, ya bar gida da dadewa
ba mu san inda yake ba. Dalilin fitar sa daga
gida kuwa, ya yi fushi ne a kan wani zance da
muka taba yi da shi na hada 'ya'yanmu http://
fb.com/waziriaku aure, in har Allah ya arzutta
mu da su. Na tsaurara masa zance a wancan
lokacin wanda sanadiyyarsa ne ya yi fushi da ni.
Bayan na raka ka zuwa wata tafiya da ka taba
yi, da muka dawo sai ban iske shi gida ba. Har
yanzu kuma maganar da ake yi ke nan."
Waziri ya kwashe dukkan labarin da ya faru
tsakaninsa da dan uwansa Nuruddin, ya fadawa
Sarki. Sa'annan kuma ya ci gaba da cewa, "Ya
shugabanmu, tun ranar da na haifi 'ya mace, na
yi rantsuwa http://fb.com/waziriaku ba ni aurar
da ita ga kowa sai ga dan dan uwana Nuruddin.

Kuma Allah da ikonsa yanzu bai fi wata uku ba
da na ji labari gun fatake, cewa dan uwana yana
birnin Basara kuma har an nada shi Wazirin
Basara. Karewa da karau ma an ce, ya haifi da
namiji wanda yake kusan sa'ar 'yata ne. Ina cikin
shirye-shiryen in aika wa dan uwana da sako,
sai ga shi ka zo mini da wannan batu. Ya Sarki,
Ina rokonka da ka janye wannan bukata ta auren
'yata domin girman Allah."

Yayin da Sarki ya ji zancen Waziri, ya yi fushi,
fushi mai tsanani, ya ce, "Yaya kamar ni zan
zubar da girmana, in nemi bukata wurinka amma
ka juya mini baya, ka kawo wani dalili mara
kwari? Na rantse da raina, na fasa auren ta,

kuma domin in hukunta ka, da kai da 'yar taka,
zan http://fb.com/waziriaku aurar da ita ga
wani bawana, ma fi muni daga cikin bayina."
Daga nan Sarki ya kori Waziri daga wurinsa.
Aljani ya ci gaba da ba aljana labari, ya ce "Sarki
yana da wani bawa, wada mai kusumbi, gurgu
mai hakora zago-zago. Wannan bawa yana da
gajeren wuya, da doguwar keya, da shafaffen
goshi. Kai wannan bawa da muni yake, ya
shugabata, ban taba ganin mutum mummuna
irin shi ba. Yanzu haka dai lokacin da na fito
daga birnin Misira, Sarki ya sa an daura http://
fb.com/waziriaku wa 'yar Waziri aure da wannan
mummunan bawa. Cikin wannan dare ango zai
shiga dakin amaryarsa, wannan yarinya tana
cikin bakin ciki ita da mahaifinta, bakin ciki mai
yawa."

Aljani ya ci gaba da ce ma aljana, "Wallahi
yarinya 'yar Wazirin Misira ita ce ma fi kyawo
daga wannan saurayi. Ina ma a ce wannan
saurayi ne za a aura mata, da sun yi matukar
dacewa da juna. Wadannan yara sai ka ce 'yan
bappanni ne, ko kuma su 'yan uwan juna ne."

Aljana ta ce da shi, "Ka yi karya! Kodayake ban
ga waccan http://fb.com/waziriaku yarinyar ba,
amma na tabbata babu wanda ya kai wannan
yaro kyau a cikin wannan zamani."

Aljani ya ce,
"Ya shugabata, Wallahi ita ce ma fi kyawo daga
wannan saurayi. Ni ina tausaya mata game da
auren wannan wada, mai kusumbi."

Aljanun nan
suka ci gaba da gardama a tsakaninsu, aljani na
cewa 'yar Waziri Shamsuddin ce ta fi kyau, ita
kuma aljana tana cewa, Hassan Badaruddin ne
ya fi kyau. Shi kuwa Hassan yana ta sharbar
Barci abinsa, bai san wainar da ake toyawa ba.
Daga nan sai aljana ta ce, "Ka dauki wannan
saurayi mu tafi da shi Misira yanzun nan, mu
gwada shi da yarinyar can, mu ga wanda ya fi
wani kyau." Aljani ya ce, "Na ji, na dauka, ya
shugabata. Hakika wannan shi zai warware
mana gardama, domin an ce, gani ya kori ji." Nan
take aljani ya sungumi Hassan yana barci, suka
tashi da shi sama, http://fb.com/waziriaku
kamar kyabtawar ido sai ga su a Misira. Suka
sauka a kofar gidan da ake bukin auren 'yar
Waziri Shamsuddin, mai suna Sittul Hassana,
tare da mai kusumbi. Bayan sun sauka, sai aljani
ya zunguri Hassan da ke barci.

Hassan ya farka
firgigi, ya duba ko'ina, ya rasa gane inda yake.
Shi dai ya San yana cikin makabarta ne a gaban
kabarin mahaifinsa, wurin da in banda kukan
kwari babu abin da ake ji. To amma yanzu da
farkawarsa, sai ya gan shi cikin wani birni
tsundum, maimakon kukan kwari kuma, yanzu
babu abin da yake ji sai kade-kaden ganguna da
bushe-bushe.
Hassan fa ya rikice gaba daya, ya yi niyyar ya
kwala ihu domin ya gani shin mafarki ne yake yi
ko a farke yake. Sai aljanin nan ya yi sauri ya
rufe masa baki, sa'annan ya ce masa, "Kada ka ji
tsoro, kuma ba mafarki kake yi ba. Ni ba mutum
ba ne, aljani ne. Ni ne na zo da kai nan domin in
http://fb.com/waziriaku aikata maka wani
alheri." Aljani ya kunna fitila ya mika wa Hassan,

ya ce, "Karbi wannan fitilar, ka shiga cikin taron
jama'ar can, inda ake yin Kade-kade da bushe-
bushe. Kada ka ji tsoron kome. Idan ka tafi, ka yi
kokari ka zauna kusa da ango, har ya zama
kamar kai ne babban abokinsa. Koyaushe
mawaka da maroka suka zo wurinka, ka saka
hannunka cikin aljihu, za ka ji shi cike da kudi, ka
yi ta damka kana watsa musu. Wannan ba
dabararka ba ce ko karfinka, iko ne na Allah
madaukakin Sarki. Idan masu kawo http://
fb.com/waziriaku amarya sun kawo ta daki suka
tafi, ka tashi ka shiga dakin, kada ka ji tsoron
kome, ina tare da kai." Yayin da Hassan ya ji
jawabin aljani, sai ya ce a cikin ransa, "Kaico ni!
Wannan wane irin al'amari ne ke shirin faruwa
gare ni. Anya akwai alheri a cikinsa?" Ya dai
karbi fitila daga hannun aljani, ya tashi ya nufi
wurin da ake shagalin buki.
Yayin da ya isa cikin taron mutane, ya ga kowa
rike da fitila, irin wadda aljani ya ba shi. Makada
kuwa sun goce ganguna, 'yan mata sai rawa ake
yi. Ya ga ango mai kusumbi a can gefe daya
zaune, shi kadai kamar maye. Hassan ya kutsa
kai cikin mutane, ya nufi inda ango yake zaune.
Da mutane suka gan shi, saurayi http://fb.com/
waziriaku kyakkyawa, sanye da wata irin riga,

wadda ta sha kwalliya da ruwan zinari, da hula
bisa kansa zananniya da kumfar azurfa da
lu'ulu'u, sai suka rika ba shi hanya yana
wucewa. Su kuwa maroka da makada, suna
ganinsa sai suka dafe gangunansu suka yiwo
kansa da kida da bushe-bushe. Hassan ya sa
hannunsa cikin aljihun rigarsa, ya ji shi cike da
dinari. Ya rika damka yana watsa wa mawaka,
da 'yam matan amarya da tsofaffi. Ya cika wuri
da dinari. Mutane suka yi ta mamakin irin
kyawunsa, da kuma wannan irin kyauta tasa, sai
ka ce burgaggen famfo.

Hassan ya isa inda ango mai kusumbi yake
zaune, ya ci kwalliya http://fb.com/waziriaku
kamar wani Sarki, amma babu kowa tare da shi,

duk mutane sun tsane shi saboda muninsa, ga
shi kuma kankamo, tunda aka fara bukin bai ba
maroka ko dirhami ba. Hassan ya zauna kusa
gare shi, kamar yadda aljani ya umurce shi. Aka
ci gaba da buki, Hassan kuwa ya ci gaba da
ruwan kudi. Can zuwa wani lokaci, sai ga tsofaffi
masu kawo amarya sun iso da ita. Suka shige
da ita cikin gidan da Sarki ya tanadar musu ita
da angonta. Ango da sauran jama'a, ciki har da
Hassan, suka tashi za su shiga cikin gida.
A bakin kofar gidan akwai masu gadi, wadanda
ba su barin kowa ya shiga gidan, daga ango sai
tsofaffin mata da kawayen amarya http://
fb.com/waziriaku kawai ne za su shiga gidan.
Tsofaffin matan nan suka ce,

Allambaram su ba
za su shiga gidan amarya ba face da Hassan,
domin kuwa shi ne wanda ya raya wannan buki
da ruwan kudi. Dole masu tsaron kofa suka bari
Hassan ya wuce cikin gidan.

A cikin gidan amarya kuwa, mata sun yi sahu
biyu madaidaita, sun saki hanya a tsakanin
sahun biyu, inda amarya za ta bi. Cikinsu kuwa
daga matan Sarakuna, sai na Hakimai da
Wazirai, da manyan attajirai. http://fb.com/
waziriaku Kowace mace da fitila a hannunta mai
haske sosai. Matan nan sun ci ado,

sun kure
adaka. Da tsofaffi suka shigo tare da ango da
kuma Hassan Badaruddin, matan nan suka ga
irin kyawun Hassan, sai kowace ta rika yaye
mayafin da ya rufe fuskarta, domin ta more wa
idonta kallon kyakkyawar fuskar Hassan dan
mutanen Basara. Suna cewa, aminci ya tabbata
ga wannan saurayi. Sai kuma su rika yi wa mai
kusumbi bakar addu'a, da duk wanda ke da
hannu wajen http://fb.com/waziriaku aura masa
kyakkyawar yarinya Sittul Hassana, wadda ba ta
dace da kowa ba, face wannan saurayi.
Hassan da ango suka zauna gefe daya, maroka
suka buga tambura, tsofaffi suka fito da amarya
suka biyo da ita ta tsakanin hanyar da mata
suka yi sahu. Kai! Wannan amarya da kyawu
take, kyawun da zai iya dimautar da duk wanda
ya kalle ta. Ta ci ado da tufafi na sarauta,

wadanda aka yi wa kwalliya da zinariya, da
zane-zane masu kyau na tsuntsaye da namun
daji. Ga wani http://fb.com/waziriaku dutsen
wuya daure ga wuyanta, wanda babu irinsa duk
kasar Misira. Amarya ta zama tamkar farin wata
dan daren goma sha hudu, tsarki ya tabbata ga
mahaliccinta. Ta biyo ta tsakanin matan nan, ka
ce ita ce wata su kuma taurari, ta nufi inda
angonta yake zaune tare da Hassan.
***
Za mu ci gaba mai gobe zuwa daidai
wannan lokaci insha allahu

by YUSUF A JIBAGA07. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Hassan da ango suka zauna gefe daya, maroka
suka buga tambura, tsofaffi suka fito da amarya
suka biyo da ita ta tsakanin hanyar da mata
suka yi sahu. Kai! Wannan amarya da kyawu
take, kyawun da zai iya dimautar da duk wanda
ya http://fb.com/waziriaku kalle ta. Ta ci ado da
tufafi na sarauta, wadanda aka yi wa kwalliya da
zinariya, da zane-zane masu kyau na tsuntsaye
da namun daji. Ga wani dutsen wuya daure ga
wuyanta, wanda babu irinsa duk kasar Misira.
Amarya ta zama tamkar farin wata dan http://
fb.com/waziriaku daren goma sha hudu, tsarki
ya tabbata ga mahaliccinta. Ta biyo ta tsakanin
matan nan, ka ce ita ce wata su kuma taurari, ta
nufi inda angonta yake zaune tare da Hassan.
Da zuwanta wurinsu sai ango mai kusumbi ya
tashi tsaye ya miko wa amaryarsa hannu domin
ya zaunar da ita. Amma ina, hankalinta ba
wurinsa yake ba, hankalinta ya karkata ga kallon
Hassan, ta matsa kusa gare shi, ta durkusa ta
kura masa ido tana kallon shi, ta bar mijinta
http://fb.com/waziriaku mai kusumbi a tsaye
kamar icce. Da mata suka ga amarya ta karkata
ga Hassan, ta bar angonta, sai suka kwashe da
dariya. Hassan ya saka hannunsa cikin aljihun
rigarsa, ya damko dinari ya watsa musu. Nan
take sai wuri ya kaure da guda, mata na cewa,

"Mu, muna yi maka addu'a a kan wannan
amarya ta zama taka, tir da wannan ango
marowaci." Amarya kuwa da take durkushe
http://fb.com/waziriaku a gaban Hassan tana
kallonsa ba ko kyabtawa, ta daga hannuwanta
sama tana cewa, "Ya Allah mai girma da
daukaka, mai tsarawa da juyar da al'amurra
yadda ya so, ka juyar da wannan aure nawa, ka
sanya wannan saurayi ya zama shi ne mijina,
ina neman tsari daga wannan wada mai
kusumbi."

Lokacin da dare ya fara yi sosai, sai aka umurci
kowa ya fita daga cikin gidan. Tsofaffi suka
shiga da amarya wani daki domin su yi mata
nasiha ta karshe, kafin su kai ta ga dakinta. Duk
sauran mata suka fita daga cikin gidan, babu
wadanda suka yi saura sai ango da Hassan
Badaruddin. Da ango ya ga Hassan bai fita daga
http://fb.com/waziriaku cikin gidan ba sai ya ce
masa, "Ya shugabana, hakika ka debe mana
kewa a cikin wannan dare, ka jibince mu da
alherinka, ba domin ka ba da wannan buki ya
zama lami. Ga shi dare ya soma yi, ya kamata
ka tashi ka tafi gida haka nan, amma fa kada ka
ga kamar korar ka nake yi." Hassan Badaruddin
ya tashi ya nufi kofar fita daga gidan, yana mai
matukar bege da tausayin wannan amarya,
wadda bai taba ganin kyakkyawar mace
kamarta ba. Har ya zo bakin kofar fita, sai http://
fb.com/waziriaku aljani ya zungure shi, ya ce
masa, "Ka tsaya kada ka fita, ya Badaruddin,
idan ka ga mai kusumbi ya nufi cikin lambu, ka yi
sauri ka shige wancan dakin, inda za a kai
amarya. Idan aka kawo ta, ka ce da ita ni ne
mijinki, da ma Sarki dabara ce ya yi na cewa ya
aurar da ke ga mai kusumbi, domin kawai a
kawar da idanun mutane, kuma a yi wa mai
kusumbi dariya."

Shi kuwa ango mai kusumbi, abin duniya duk ya
dame shi, yana ta zagin Sarki a cikin ransa, ga
shi ya daura masa aure da yarinyar da ba ta son
shi, duk jama'a ma ba su son shi. Nan take ya ji
duk duniyar ta yi masa baki, ya ce a cikin ransa,
"Bari na shiga cikin lambun can ko na dan ji
sanyi a raina, kafin tsofaffi masu yi wa amarya
http://fb.com/waziriaku nasiha su gama yi mata
nasihar. Na riga na sani dai duk nasihar da za su
yi mata ba za ta yarda in kwanta kusa gare ta
ba, ballantana har in kusance ta." Ya tashi ya
nufi cikin lambu, aljani na biye da shi a baya. A
cikin lambun an rataya fitilu, ko'ina ya haskake
tamkar rana.
Yayin da Hassan ya ga mai kusumbi ya shige
cikin lambu, sai shi kuma ya yi sauri ya shiga
dakin da za a kai amarya, ya yi zaune bisa gado.

Akwai fitila a cikin dakin, tana haske tamkar
rana, an kawata bangayen dakin da zane-zane
masu kyau da ban sha'awa, an shimfide kasan
dakin da shimfidu na alfarma, masu laushi.
Hassan bai dade da zama ba, sai ga tsofaffin
nan masu kawo amarya sun iso da ita. Suka
tsaya daga bakin kofar dakin, wadda take rufe
da labule http://fb.com/waziriaku . Daya daga
cikinsu ta daga murya ta ce, "Ya Aba Shuhabi, zo
ka karbi amaryarka. Mun bar ku da Allah da
halinku. Allah ya sa ma wannan aure naku
albarka." Suka tura keyar amarya cikin dakin,
suka juya suka tafi.
Amarya ta shiga dakin ranta a bace, tana sake-
sake cikin zuciyarta, tana cewa, "Wallahi ba zai
sami hadin kaina ba, ba zai taba kusantata ba
har abada, sai dai ya kashe ni." Tana daga kanta
sai ta yi tozali da Hassan, nan take ta tsaya cik,
cikin kaduwa da mamaki. Bata san lokacin da ta
ce da shi ba, "Ya masoyina, yaya aka yi ka shigo
nan? Ina ce zan iske mijina ne, mai kusumbi."

Hassan ya ce mata, "Don me mai kusumbi zai
http://fb.com/waziriaku shigo nan, bayan an
riga an biya shi jingar aikinsa ya tafi?" Sittul
Hassana ta ce, "Shin ga wa aka aurar da ni?

Gare ka, ko gare shi?" Hassan ya ce mata, "Haba
masoyiyata, ai ko ba a gwada ba linzami ya fi
karfin bakin zakara. Da yaya kamar

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

1 Comments On HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN
avatar
rabiu-bello

1 year ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment