Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

muke
manya ba mu san mahaifinka ba. Mun dai san
cewa Sarki ya aurar da mahaifiyarka ga wani
wada mai kusumbi, ranar tarewar mahaifiyarka,
aljanu suka daure mai kusumbi a cikin lambu,
wani daga cikin aljanun ya auri mahaifiyarka har
aka sami cikinka. Duk fadin Misira babu wanda
ya san mahaifinka, babu kuma wanda ya taba
ganinsa. Lalle idan ba ka sanar da su ko wane
ne ubanka ba, ba su kara wasa da kai." Ko da
Ajibu ya ji zancen Malaminsu sai ya nufi gida
yana kuka, ranar ko karatun bai tsaya yi ba.
Ajibu ya isa gida wurin mahaifiyarsa yana kuka,

ta yi lallashin duniyar nan amma ya ki yin shiru.
Ta tambaye shi dalilin kukansa, ya kwashe
dukkan abin da ya faru tsakaninsa da yara ya
fada mata. Ya kuma fada mata abin da
Malaminsu ya fada masa, sa'annan ya dube ta
ya ce, "ya mahaifiyata, ki fada mini wanene
mahaifina?" Ta ce da shi, "Waziri shi ne
mahaifinka." Ya ce da ita, "kada ki yi mini karya,
ya mahaifiyata. Waziri mahaifinki ne, ni kuma
kakana ne. Wallahi idan ba ki fada mini ko
wanene mahaifina ba, to zan kashe kaina da
wannan dutsen!" Ya dauki wani babban dutse ya
rike ga hannunsa.

Yayin da Sittul Hassana ta ji ambaton Hassan
Badaruddin, uban Ajibu. Ta tuna da kyawunsa,
da abin da ya faru tsakaninsu a daren amrcinta.
Soyayyarsa ta motsa a cikin zuciyarta, ta waka
wadannan baitoci:

"Kun motsa mini so kwantacce cikin zuciyata.
Kun taso shi amma kuma gida ya nesanta gare
shi. Hankalina ya jirkita domin nesanta tasa
daga gare ni. Da, na hakura da rashin ganinsa
amma yanzu kun tashe ni. Kun raba ni da farin
ciki yanzu babu zama a gare ni. Hawayen idona
sun gudana domin tuna rabuwa tamu.
Hawayena sun zama tamkar kogi domin bege a
gare shi. Na yi begen in gane shi begensa yakan
dadu hakuri yakan takaita. Na misalta ganinsa a
cikin zuciyata ina bege irin na so da zumunci. Ya
wanda ambatonsa shi ne wakata ya wanda nake
jin dadi idan na tuna shi. Yaushe za ka dawo
gare ni yaushe ne wannan jinkiri zai yanke."
Da ta gama rera wannan waka, sai ta fashe da
kuka. Danta Ajibu ma ya yi kuka tare da ita.

Suna cikin wannan hali sai ga Waziri ya shigo
gidan. Yayin da ya tarar da su suna kuka, sai
ransa ya baci, zuciyarsa ta sosu, ya tambaye su
dalilin kukansu. Sittul Hassana ta labarta masa
abin da ya sami danta a makaranta duka. Waziri
ya yi shiru yana tunani, ya tuna da dan uwansa
Nuruddin, ya tuna abin da ya faru a tsakaninsu.
Ransa ya baci, zuciyarsa ta motsa, nan take ya
yi kudirin zuwa birnin Basara wurin dan uwansa
Nuruddin da kuma neman mijin 'yarsa kuma
uban Ajibu, watau Hassan Badaruddin.

Nan take Waziri ya fita daga gidansa ya nufi fada
wurin Sarki. Ya fada wa Sarki cewa ya yi niyyar
fita zuwa Basara neman dan uwansa da kuma
mijin 'yarsa. Ya nemi Sarki da ya rubuta masa
takarda zuwa ga Sarkunan da zai keta ta cikin
biranensu domin su tare shi da girmamawa idan
ya shiga biranen nasu. Sarki ya rubuta masa
takardu kamar yadda ya bukata, suka yi ban
kwana da juna. Waziri ya koma gida domin fara
shirye-shiryen tafiya.
Waziri ya hada dukkan abin da za su bukata a
wurin wannan tafiya, ya debi bayi da kuyangi,
sa'annan ya tafi tare da 'yarsa, Sittul Hassana,

da jikansa Ajibu. Suka kama hanya suka nufi
Basara. Kwanci tashi, bayan sun yi tafiyar kwana
uku, sai suka isa birnin Damashka.

Suka gan shi
birni ne ma'abocin koramu da itatuwa. Waziri ya
yi umurni da a sauka a huta kwana biyu kafin a
ci gaba da tafiya. Suka sauka a bayan gari, a
wuri mayalwaci, suka kafa tantina, suka sauke
kayansu. Waziri ya ba bayi da kuyangi dama,
duk mai so yana iya shiga cikin gari domin bude
idonsa, ko sayen wani abu da yake bukata.

Bayi suka warwatsu cikin birni domin kashe
kwarkwatar idanunsu. Wasu suka nufi dakin
baki, wasu suka nufi kasuwa, wasu suka nufi
masallacin Juma'ar Banu Umayyata, wannan
wanda babu tamkarsa a cikin duniya. Ajibu kuwa
sai ya shiga gari tare da wata kuyanga, suka yi
ta yawo cikin gari kwararo-kwararo, sako-sako,
yana rike da wata bulala ta bugun rakumi, yana
wasa da ita ga hannunsa. Yayin da mutane suka
ga Ajibu, da irin kyawun da Allah ya yi masa, da
cikar halittarsa, da daidaito, da kwarjini, da
haiba. Sai suka rika bin su a baya, suna kallon
Ajibu.

Ajibu da kuyanga suka ci gaba da zagaya gari
har kaddara ta sa suka iso wurin rumfar mai
sayar da abinci, wanda ya riki Hassan
Badaruddin a matsayin dansa. Yanzu da ya fara
tsufa, sai ya daina fitowa rumfar, ya sakarwa
Hassan ragamar tafiyar da kasuwancin abinci.

Aka kuwa yi gamo da katar, lokacin da su Ajibu
suka iso daidai wurin rumfar, lokacin kuma
Hassan ya fito daga cikin rumfar. Hassan ya dubi
Ajibu, Ajibu ma ya dubi Hassan. Nan take sai
soyayyar juna ta shige su, suka yi tsaye suna
kallon juna. Hassan ya yi al'ajabi da kyawun
Ajibu, ya fada a cikin ransa, "ya kaiton kaina! Wa
zai mallaka mini wannan yaro a matsayin dana?
Wallahi zuciyata ta so shi, raina na begen shi."

Nan take hawaye suka karyo masa ba tare da ya
sani ba. Sa'annan ya ce da Ajibu, "ya
shugabana, ina rokonka da ka faranta mini rai,
ka shiga wannan rumfa tawa ka ci daga wainar
da na toya ta kwayar ruman."

Yayin da Ajibu ya ji zancen Hassan, ya juya zuwa
ga kuyangarsa ya ce, "wannan mai sayar da
abinci, zuciyata ta so shi. Kuma ga alama yana
cikin damuwa na wani abu mai muhimmanci da
ya rasa. Mu shiga rumfarsa, mu ci abincinsa, mu
faranta masa rai, watakila sanadiyyar haka Allah
ya sa mu hadu da abin da muka fito nema."

Kuyanga ta ce, "ya shugabana, wannan abu bai
kamata ba. Kaka dan Waziri kamarka zai ci
abinci a cikin rumfar sayar da abinci, wannan ba
girmanka ba ne. Ka sani cewa an hada ni da kai
ne domin in tsare ka daga aikata abin da bai
kamata ba." Da Hassan ya ji zancen kuyanga, ya
waiwaya wurinta, idanunsa na zubar da hawaye,
ya ce mata, "zuciyata ta so shi, ku yi hakuri ku
faranta mini ciki da cin abincina." Kuyanga ta ce,

"ka bar wannan zance, domin ba mai yiwuwa ba
ne." Hassan ya yi ta rarrashin kuyanga, har ta ji
tausayinsa. Ta riki hannun Ajibu, suka shiga
cikin rumfa.

Hassan ya yi musu shimfida mai kyau, ya dauki
kwanuka ya zuba musu waina ta 'ya'yan ruman
hade da wake. Ya zuba musu mai a wani wuri
daban, ya kuma zuba zuma a wani wurin na
daban, a wani wurin kuma ya zuba musu miya
cike da nama. Hassan ya ce musu, "kada ku yi
gaggawa, ku ci a cikin nutsuwa da tsanaki.

Cewa gaggawa tana daga cikin aikin Shaidan."
Ajibu ya ce, "ai sai ka zauna mu ci tare da kai,
mai yiwuwa Allah ya hada mu da wanda muka
fito nema albarkacin wannan haduwa tamu."

Hassan ya ce masa, "ya shugabana, shin kai ma
ka hadu da bakin cikin rabuwa da masoya ne,
duk da karancin shekarunka?" Ajibu ya ce,
"na'am ya baffana. Raina na cike da bakin cikin
rabuwa da mahaifina, wanda tunda aka haife ni
ban san shi ba. Shi ne muka fito nema, ni da
kakana da mahaifiyata, har yanzu Allah bai nufe
mu da saduwa da shi ba. Ka yi mana addu'a
bisa ga wannan bukata tamu." Yana gama fadin
haka sai hawaye suka zubo daga idanunsa.
Hassan ya tausaya masa, ya yi musu addu'a
Allah ya sa su hadu da wannan mutum da suka
fito nema. Suka ci abinci tare, har ya ishe su.
Daga nan sai suka fita daga rumfar Hassan,
suka nufi bayan gari inda masukinsu yake. Ko
da suka fita daga cikin rumfar, sai Hassan ya ji
kamar ransa ne yake fita daga jikinsa. Ya ji wani
sabon bakin ciki ya lullube shi. Ya ji cewa sam
ba zai iya jimirin ganin wannann kyakkyawan
yaro ya tafi ya bar shi ba. Nan take ya rufe
rumfar abinci, ya bi bayansu, bai san cewa
wannan yaro dansa ne ba.
Ajibu da kuyanga suka nufi masaukinsu, Hassan
na biye da su a baya. Kafin su fita daga kofar
birni, sai kuyanga ta waiwaya baya ta ga
Hassan na biye da su. Suka tsaya har ya iso
wurinsu. Kuyanga ta ce, "me ya same ka, ya kai
mai waina?" Hassan ya ce, "Wallahi lokacin da
kuka fita daga cikin rumfata, sai na ji kamar
raina ne ya fita. Shi ya sa na rufe rumfar. Ina so
in tafi tare da ku bayan gari in sha iska ko na ji
sauki a cikin raina." Kuyanga ta ce, "wannan
abinci naka ya zama shu'umi, daga mun shiga
rumfarka mun ci abinci sai ka rika bin mu a
baya? Wannan ai fallasa ne, wanda zai sa duk
mutane su gane cewa mun ci abinci a rumfarka."

Ajibu ya yi fushi da Hassan, ya ce masa, "ka tafi
zuwa ga bigirenka, ka daina bin mu." Suka juya
suka tafi, suka bar Hassan nan a tsaye.
Bayan sun fita daga kofar gari, Hassan ya ci
gaba da bin su. Da Ajibu ya waiwaya ya gan shi,
sai ransa ya baci sosai. Ya duka ya dauki dutse
ya jefi Hassan da shi. Dutse ya sauka bisa
goshin Hassan, ya ji masa ciwo har jini ya fito.

Ajibu da kuyanga suka bar Hassan nan tsaye
dafe da goshi, suka tafi da sauri har suka isa
inda tantinansu. Shi kuwa Hassan ya juya ya
koma zuwa ga rumfarsa. Ya yanki kyalle daga
rawaninsa, ya daure wurin da Ajibu ya jefe shi.
Ya zargi kansa da kansa, ya ce a ransa, "ni na
zalunci kaina, yayin da na fita daga cikin rumfata
na bi su, har suka yi mini mummunan zato." Ya
zauna yana mai tunanin halin da mahaifiyarsa
take ciki a birnin Basara.

SANARWA.

Zamu dan dakata dawannan hikya zuwa ranar alhamis me zuwa saboda dalilin dan gajiya dakuma yawan aiki dayawa takuramun a wannan satin afuwan ,yan.uwa

daga naku yusuf a jibaga
This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

1 Comments On HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN
avatar
rabiu-bello

1 year ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment