Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan
bawa mummuna zai zama mijinki? Sarki ya yi
jinga da shi ne dinari goma, ya zama kamar shi
ne mijinki, domin kawar da hankulan jama'a,

kuma a yi dariya. Da ni aka daura miki aure ba
da shi ba. Tuni ma har an biya shi kudin
jingarsa, ya tafi gida."

Koda Sittul Hassana ta ji wannan zance, sai ta
lumshe idonta don farin ciki, ta ce, "Ya masoyina,
abin begena, ka taso ka kusance ni, ni taka ce,

na mallaka maka dukkan kaina. Nan take
Hassan http://fb.com/waziriaku ya tashi, ya riki
hannunta ya ja ta kan gado, ya kashe fitila, duhu
ya mamaye dakin. Suka yi kwance bisa gado
suna masu rungumar junansu. Hassan ya same
ta cikakkiyar budurwa, wadda ta tsare kanta da
mutuncinta, waninsa bai taba kusantar ta ba.

Suka kasance cikin wannan yanayi na soyayya,
har barci ya dauke su.

Shi kuwa ango mai kusumbi, yayin da ya shiga
cikin lambu domin ya ji sanyi a ransa, sai ya
sami wuri ya zauna yana tunani. Can sai ya ga
wani dan bera ya fito daga cikin rami. Sai ya ji
beran nan ya buda baki ya ce, "Zayyik!" Mai
kusumbi ya tsorata, ya ce, "Me ya kawo wannan
bera cikin lambu?" Daga nan sai bera ya kara
girma ya http://fb.com/waziriaku zama kyanwa.

Sai kuma ya kara girma ya zama kare, ya dubi
mai kusumbi ya yi masa haushi, "Uh! Uh! Uh!...."
***
Za mu ci gaba gobe insha allahu08. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Ango mai kusumbi kuwa, yayin da ya shiga cikin
lambu domin ya ji sanyi a ransa, sai ya sami wuri
ya zauna yana tunani. Can sai ya ga wani dan
http://fb.com/waziriaku bera ya fito daga cikin
rami. Sai ya ji beran nan ya buda baki ya ce,
"Zayyik!" Mai kusumbi ya tsorata, ya ce, "Me ya
kawo wannan bera cikin lambu?" Daga nan sai
bera ya kara girma ya zama kyanwa. Sai kuma
ya kara girma ya zama kare, ya dubi mai
kusumbi ya yi masa haushi, "Uh! Uh! Uh!...."
Nan take mai kusumbi ya firgice, yana cewa,

"Yau na hadu da http://fb.com/waziriaku
shu'umi." Kare ya kumbura ya kara girma, ya
zama jaki. Mai kusumbi ya fara kururuwa yana
cewa, "Ina mutanen gidan nan, ku kawo mini
agaji." Ya zabura sai sheka da gudu, sai jaki ya
juye ya zama bauna, ya tare masa hanya. Bauna
ta yi magana da harshen 'yan Adam, ta ce,

"Kaicon ka ya kai wannan wada! Don me ka auri
abar sonmu? Da sannu za mu kuntata maka, mu
mayar da kai kasa!" Mai kusumbi ya fadi bisa ga
gwiwowinsa, bakinsa na rawa, yana cewa,

"Wallahi ba ni da laifi, tilasta ni aka yi, ba cikin
son http://fb.com/waziriaku raina ba. Ni ban
san tana da masoya ba a cikin namun daji, na
tubar wa Allah, na tubar muku. Wallahi ba ni
koma kula ta, Allah ya la'anci duk wanda ya yi
sanadiyyar aura mini ita."

Daga nan sai mai kusumbi ya ji an suri duga-
dugansa, an juyar da shi, kansa a kasa
kafafunsa a sama, aka rataye shi ga reshen
bishiya. Sa'annan ya ji an ce masa, cikin wata
kakkausar murya, "Ka tsaya kamar haka, ina
nan ina gadin ka har zuwa fitowar rana. Da zarar
na ji ka furta http://fb.com/waziriaku wata
kalma guda, zan kashe ka. Idan ka ga rana ta
fito, ka sauka daga wannan bishiya, ka kama
gabanka. Kuma idan na ga ka kalli kofar dakin
amarya, yayin da za ka fita, zan yi maka azaba
mai tsanani." Aljani ya bar shi nan ya fita.

Yayin da aljani ya fito daga cikin lambu, sai ya
hadu da aljana, suka tafi tare, suka shiga dakin
da Hassan da Sittul Hassana suke kwance a ciki.

Da shigarsu, sai suka kunna fitilar dakin, suka
iske su kwance suna barci, fuskokinsu suna
http://fb.com/waziriaku kallon sama. Hassan ya
cire rigarsa da wando da hularsa, ya ajiye su can
gefen gado, daga shi sai wata riga 'yar ciki. Ita
kuwa Sittul Hassana in ban da wani dan mayafi
babu komai a jikinta. Aljanun nan suka kura
musu ido suna kallon su. Aljani ya ce, "Ya
shugabata, yanzu kin gani da idonki cewa
wannan yarinya ta fi http://fb.com/waziriaku
wannan saurayi kyau ko?" Aljana ta ce ita faufau
bata yarda ba, saurayin shi ne ya fi kyau.

Suka yi ta gardama a tsakaninsu, kowa yana
nuna wa dan uwansa abin da yake gani mai
kyau a jikin Hassan da Hassana har alfijiri ya
fara ketowa. Daga nan sai aljana ta ce,"Mu yi
sauri mu http://fb.com/waziriaku dauki wannan
saurayi mu mayar da shi inda muka dauko shi
kafin gari ya waye." Nan take aljana ta dauki
Hassan yana barci suka tashi sama da shi, suka
bar yarinya Sittul Hassana tana barci.
Aljanu suna cikin tashi da Hassan, kafin su kai
birnin Basara, sai Allah ya kaddari aka jefi aljani
da tauraro na wuta, ya kone nan take. Aljana na
ganin haka, sai ta yi http://fb.com/waziriaku
kasa ta sauke Hassan daga wajen kofar wani
birni, ta kada cikin iska ta yi tafiyarta. Wannan
birni ya kasance birnin Damashka ne, na kasar
Sham. Hassan yana nan kwance a bakin kofar
shiga birni, yana barci, har gari ya waye, rana ta
fito, aka bude kofofin birni. Mata suka fito daga
cikin birni za su tafi rafi dibar http://fb.com/
waziriaku ruwa, sai suka ga Hassan kwance a
bakin kofa yana barci.

Koda suka gan shi, suka lura da irin kyawunsa,
da kuma irin yanayin da yake ciki, na rashin
isassun tufafi a jikinsa, sai wasu daga cikinsu
suka ce, "Kai amma duk macen da wannan
kyakkyawan saurayi http://fb.com/waziriaku ya
kwana wurinta, cikin daren da ya gabata, lalle ta
more. Kaiconsa da bai tsaya sanya tufafinsa
ba." Wasu kuma suka ce, "Da ganinsa irin
'ya'yan masu mulki ne, wadanda ke aikata
http://fb.com/waziriaku yadda ransu yake so ga
talakawa. Watakila daga mashaya ya fito, giya
ta buge shi ya fadi nan har bacci ya dauke shi.
Watakila ma wajen caca ya salwantar da
tufafinsa. Amma an yi hasarar kyau wannan
wuri, tunda babu hali na gari."

Haka dai matan nan suka yi ta zancensu na son
zuciya a kan halin da suka tarar da Hassan
Badaruddin a ciki. Can sai iska ta kada, 'yar rigar
da ke jikin Hassan http://fb.com/waziriaku ta
yaye, tun daga cinyoyinsa har zuwa saman
cibiyarsa suka bayyana. Nan fa hankulan matan
nan ya tashi a kan kyawun Hassan da ya kara
bayyana. Kadawar wannan iska shi ya tayar da
Hassan daga barcin da yake yi, ya ga mata sun
kewaye shi suna kallo, kamar http://fb.com/
waziriaku masu kallon wata halitta ta daban. Ya
yi sauri ya gyara rigarsa da iska ya kwashe, ya
dube su ya ce, "Don Allah a ina nake nan? Me ya
sa kuka taru nan kuna kallo na? Shin me ya faru
gare ni?" Suka ce masa, "Mu, mun fito daga cikin
birni muka gan ka yashe a nan kana barci,
bayan wannan ba mu san kome ba game da kai.
Ina ka tafi cikin daren jiya, http://fb.com/
waziriaku har aka rufe kofa kana wajen birni?"

Hassan ya sake duba wurin da yake, da
mutanen da suka kewaye shi, ya cika da
mamaki, yana tunanin shin me yake faruwa ne?
Ya dube su ya ce, "Ku sani, ni na kwana a birnin
Misira cikin daren da ya gabata."
Koda matan
nan http://fb.com/waziriaku suka ji haka sai
suka fashe da dariya gaba daya, wata daga
cikinsu ta ce, "Ko dai ka kwana cikin ciyawa?"
Wata kuma ta ce, "A'a, a birnin Sin ya kwana fa."

Suka sake fashewa da dariya, su a ganinsu,
Hassan mahaukaci ne. Daga nan sai wata daga
http://fb.com/waziriaku cikinsu ta ce, "Ga alama
dai kai mahaukaci ne, duk da muna ganin ka
kyakkyawa. Da kaka mutum zai kwana Misira
sa'annan ya wayi gari yana Damashka, in ba
zancen hauka ba?"

Hassan ya ce, "Ni ba zan yi muku karya ba har
abada, shekaranjiya na http://fb.com/waziriaku
kwana a birnin Basara, jiya kuwa na kwana tare
da amaryata a birnin Misira." Da jin haka sai
wannan ta kalli waccan, waccan ta kalli wannan,

suna taba hannu suna rike baki, wata daga
cikinsu ta ce, "Oh, kun ji abun mamaki, ba
makawa wannan saurayi mahaukaci ne, ko kuwa
shaye-shayen da ya yi ne bai sake http://
fb.com/waziriaku shi ba har yanzu?" Wasu
kuma suka rika tausaya masa suna cewa, "Ya
hasarar kyawunsa, wallahi babu makawa ga
haukansa."

gobe zamu daura insha allahu 9pm.

bar kanku da juma,a via ajibaga09. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Da mata suka ji zancen Hassan na cewa jiya ya
kwana a Misira kuma shekaranjiya yana Basara,
sai wannan http://fb.com/waziriaku ta kalli
waccan, waccan ta kalli wannan, suna taba
hannu suna rike baki. Wata daga cikinsu ta ce,
"Oh, kun ji abin mamaki, ba makawa wannan
saurayi mahaukaci ne, ko kuwa shaye-shayen
da ya yi ne bai sake shi ba har yanzu?" Wasu
kuma suka http://fb.com/waziriaku rika tausaya
masa suna cewa, "Ya hasarar kyawunsa, wallahi
babu makawa ga haukansa." Da hassan ya ji
haka, sai ya ce, "Ni, Hassan Badaruddin wallahi
na kasance ango a daren jiya cikin birnin
Misira."

Da matan nan suka ga Hassan dai ya nace da
zancensa, kuma suka http://fb.com/waziriaku
lura da cewa ga dukkan alamu ba mahaukaci ba
ne, sai suka ce masa, "To watakila dai abin da
kake fadi cewa ka kwana Basara shekaranjiya,
jiya kuma ka kwana Misira kana ango, duk
mafarki ne." Hassan ya ce, "Wallahi ba mafarki
ba ne, idan mafarki ne ina wando na da http://
fb.com/waziriaku rigata da hulata? Ina jakar
kudin da na karba daga hannun Bayahude?
Kuma ina mai kusumbi?" Da Hassan dai ya ga
alamar har yanzu ba su yarda da shi ba, sai ya
tashi ya shiga cikin gari. Ya bi wani kwararo
yana tafiya, da yara suka gan shi haka, rabi
http://fb.com/waziriaku tsirara, sai suka dafo
masa baya, sun ga wani sabon mahaukaci.
Hassan ya ci gaba da tafiya cikin wannan
kwararo har ya iso rumfar wani namiji mai sayar
da abinci. Da yaran nan suka ga Hassan ya
tsaya wurin rumfar mai sayar da abinci sai duk
suka watse, kowa ya kama gabansa. Mai http://
fb.com/waziriaku wannan rumfa ya kasance
tsohon soja ne, duk garin manya da yara, kowa
tsoransa yake ji saboda fadansa. Bayan ya yi
ritaya daga aikin soja ne ya bude rumfar sayar
da abinci a cikin birnin Damashka. Ya kasance
babu wani abinci daga cikin rumfunan sayar da
abinci da ke birnin Damashka da ya kai na
rumfarsa gyaruwa da dadi. http://fb.com/
waziriaku
Lokacin da Hassan ya shiga cikin rumfa, mai
abinci ya dube shi, nan take kwarjininsa da
kyawonsa suka dimautar da shi, son Hassan ya
darsu a cikin zuciyarsa, ya ce, "Daga ina ka fito
ya kai wannan saurayi? Fada mini labarinka,
domin ni ban taba ganin mutumin da ya yi mini
kwarjini ba kamar ka." Hassan http://fb.com/
waziriaku ya zauna ya labarta wa mai abinci
labarinsa, tun daga farko har karshe. Mai sayar
da abinci ya yi mamaki da jin wannan labari,
matukar mamaki, sa'annan ya ce, "Ya dana,
hakika wannan labari naka abin al'ajabi ne,
zancenka bakon ji ne. Ka boye wannan labari
naka ga kowa har Allah ya biya maka bukatar
zuciyarka. Ka zauna nan tare da ni http://
fb.com/waziriaku , tunda Allah bai nufe ni da
samun haihuwa ba, zan rike ka tamkar dana,
amma fa sai idan ka yarda." Hassan ya ce da
shi, "ka aikata tamkar yadda kake so, za ka
same ni mai biyayya a gare ka."

Mai sayar da abinci ya yi farin ciki da jin haka,
nan take ya fita zuwa kasuwa. Ya sayo wa
Hassan sababbin tufafi masu kyau da tsada.

http://fb.com/waziriaku Bayan Hassan ya yi
wanka, ya saka tufafi, sai mai sayar da abinci ya
riki hannunsa suka tafi wurin alkali. Bayan ya
fada wa alkali abin da ya faru tsakaninsa da
Hassan, ya nemi da a rubuta masa takardar
shaidar cewa Hassan ya yarda da zama tamkar
dansa. Alkali ya tambayi Hassan idan ya amince
da haka, Hassan ya ce ya amince http://fb.com/
waziriaku . Alkali ya rubuta takarda ya ba mai
sayar da abinci. Tun daga ranar kowane mutum
da ke cikin birnin Damashka ya san cewa
Hassan yana zaman tamkar dan mai sayar da
abinci ne. Hassan ya zauna rumfar mai sayar da
abinci yana taimakonsa wurin karbar kudi, wani
lokaci har ma da dafa abinci.

Amma abin http://fb.com/waziriaku da ya faru
ga amarya Sittul Hassana shi ne, bayan ta farka
daga barci, lokacin da gari ya waye, ta duba ba
ta ga angonta ba, sai ta yi zaton ya shiga
makewayi ne domin yin wanka, don haka sai ta
suturta jikinta, ta zauna zuwa wani lokaci tana
jiransa. Tana nan zaune fuskarta cike da annurin
farin cikin amarcinta, sai http://fb.com/
waziriaku ga mahaifinta, Waziri Shamsuddin, ya
fado cikin gidan babu ko sallama. Yana cike da
bakin cikin abin da Sarki ya yi masa, yana cewa
a cikin ransa, "Wallahi idan har wannan yarinya
ta yarda ta ba da kanta ga wannan mummunan
bawa, mai kusumbi kuma wada,

babu makawa
sai na kashe ta." Ya iso gaban kofar http://
fb.com/waziriaku dakinta ya kwankwasa, ya ce,

"Ya Sittul Hassanu." Ta amsa masa, bayan ta
gane muryarsa. Ta tashi ta nufi kofar daki,
fuskarta cike da farin ciki.

Bayan ta bude kofa, sai ta durkusa har kasa ta
gaishe da mahaifinta, tana murmushi, fuskarta
na haske. Da Waziri ya gan ta cikin wannan hali
sai fushinsa ya karu a kan fushi, ya daka mata
tsawa yana cewa, "Kaiconki ya daddauda! Ashe
har za ki yi farin ciki http://fb.com/waziriaku
bisa ga auren wannan mai kusumbi?" Da Sittul
Hassana ta ji haka, sai ta sunkuyar da kanta
kasa ta yi murmushi, sannan ta ce, "Bayan
mutane sun gama yi mini dariya a kan auren mai
kusumbi, wanda bai ko yi tsawon yatsan hannun
mijina ba, Wallahi a cikin raina http://fb.com/
waziriaku ban kwana a wani dare mafi kyawo
daga daren da na kwana jiya ba. Kada ka ba ni
tsoro da mutumin da kuka hada ni da shi domin
a yi dariya. Ba ni so kana ambata mini wannan
mai kusumbi, ya mahaifina."

Yayin da Waziri ya ji wannan zance daga 'yarsa,
sai fushinsa ya karu, idanunsa suka kada suka yi
jawur, ya ce mata cikin tsawa, "Wannan wane irin
zance ne kike fada mini? Cewa http://fb.com/
waziriaku mai kusumbi ya kwana tare da ke shi
ne mafi kyawun dare a gare ki? Kaiconki!" Da
Sittul Hassana ta ji abin da mahaifinta ya fada,
sai ranta ya fara baci, ta ce da shi, "Don Allah ka
daina ambaton wannan mai kusumbi gare ni.

Allah ya la'ance shi! Allah ya la'anci ubansa! Ba
na so ko sunansa in ji ana http://fb.com/
waziriaku ambata a gabana. Kun dai dauko shi
haya ne domin a yi dariya, a kan kudi dinari
goma, an kuma biya shi ya kama gabansa. Ina
shiga daki na tarar da mijina ya na jira na. Shi ne
wanda ya raya buki, ya wadata mahalarta da jan
dinari. Ni na kwana a http://fb.com/waziriaku
cikin kirjin mijina, mai tattausar fata, mai fararen
idanu, mai jajayen kundukuki."

Da Waziri ya ji haka sai fuskarsa ta yi duhu,
zuciyarsa ta yi zafi tana tafarfasa, ya ji kamar ya
kashe ta. Ya ce mata, "Wai ina hankalinki ya tafi
ne? Ko kina cikin maye ne? Tun wuri ki koma
cikin hankalinki, babu wanda kika kwana da shi
sai mai kusumbi!" Sittul Hassana ta fara magana
cikin bacin rai, ta ce, "Wallahi da hankalina ras!

Ya mahaifina, ka fara ba ni tsoro, ko wani abu ne
ya same ka http://fb.com/waziriaku har ka
manta da wannan shiri da kuka yi da Sarki? Tun
da aka biya mai kusumbi ya tafi, bai komo ba.

Ka jira yanzu mijina zai fito daga makewayi, sai
ka tabbatar da abin da nake fada maka." Waziri
ya dubi 'yarsa ya ga dai da hankalinta, kuma bai
ga alamun maye tare da ita ba, kuma ya san ba
ta taba fada masa karya ba. Saboda haka sai
http://fb.com/waziriaku fushinsa ya ragu, ya
yanke shawarar ya jira har wanda 'yar tasa take
kira da mijinta ya fito, ya gan shi. Sai ya nufi
lambu domin ya jira fitowarsa daga makewayi.
Waziri na shiga cikin lambu, sai ya hangi mutum
yana reto bisa reshen bishiya,

kafafunsa a sama,
kansa a kasa. Da ya matsa kusa da mutumin
sai ya ga mai kusumbi ne. Waziri ya dimauta da
ganin haka, ya yi magana yana cewa, "Shin
wannan ba http://fb.com/waziriaku shi ne mai
kusumbin da Sarki ya aurar da 'yata gare shi
ba?" Mai kusumbi bai mayar da jawabi ba domin
yana zaton aljani na nan kusa yana kallon shi.

gobe zamu daura insha allahu10. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Lokacin da Waziri ya yi wa mai kusumbi
magana, sai http://fb.com/waziriaku mai
kusumbi ya yi kurum, bai mayar da jawabi ba,
domin yana jin tsoron watakila alajani na nan na
kallonsa. Waziri ya yi masa tsawa, ya ce, "yi
magana, idan kuwa ka ki, yanzu in yanke kanka
da wannan takobi." Mai kusumbi ya ce, "ya
shugaban aljanu, Wallahi tun da ka ajiye ni nan,
ko kaina ban motsa ba balle in yi magana.
http://fb.com/waziriaku Na roke ka don Allah ka
ji tausayina." Yayin da Waziri ya ji zancensa sai
ya ce, "Me kake fada ne? Ni ne mahaifin
amaryarka da aka daura maka aure da ita jiya.
Ni ba aljani ba ne, fada mini menene yake
faruwa? Sa'annan ka kama tafarkinka." Mai
kusumbi ya ce, "ina ba ka shawara da ka bar
wurin nan tunda wuri, kafin wanda ya ajiye ni
nan ya dawo. Ashe kun san cewa 'yarku tana da
masoya cikin aljanu kuka aurar http://fb.com/
waziriaku mini da ita? Ina rokon Allah ya la'ani
wanda ya aura mini ita."
Da Waziri ya ji zancen mai kusumbi sai mamaki
ya kara rufe shi, al'amarin duk ya daure masa
kai. Ya dubi mai kusumbi da ke reto, ya ce masa,

"sauko ka fita daga wannan wuri." Mai kusumbi
ya ce, "ni mahaukaci ne da zan bi umurninka ba
tare da wanda ya ajiye ni nan ya ce in tafi ba. Ba
zan http://fb.com/waziriaku fita daga nan ba
sai rana ta fito, kamar yadda ya ba ni umurni.
Duba mini ma ka gani shin rana ta fito? Kai ko
ma ta fito ba zan tafi ba sai na gan ta nan da
idona." Waziri ya tambaye shi, "shin wa ya kawo
ka wannan wuri?" Mai kusumbi ya ce, "ni na
shigo da kaina domin in ji sanyi a cikin raina,
daga nan sai na ga bera ya fito mini. Beran ya
girma ya zama kyanwa. Kyanwa ta girma ta
zama kare, yana yi mini haushi. Kare kuma ya
zama jaki. Jaki ya zama http://fb.com/
waziriaku bauna. Shi ne ya rataye ni a wannan
wuri, ya ce kada in fita daga nan sai rana ta fito.
Kai ma ina ba ka shawara da ka tafi kafin ya
dawo ya same ka. Allah ya la'anci wannan
amarya da wanda ya yi sanadin aura mini ita."
Waziri ya matsa kusa gare shi, ya sa hannu ya
taba shi. Mai kusumbi ya fado, kansa ya bugi
kasa. Ya tashi ya zura a guje yana waige-waige
har ya fita daga gidan, ya nufi gidan Sarki.
Yayin da Waziri ya ga mai kusumbi ya zura a
guje, ko http://fb.com/waziriaku waiwaye ba ya
yi, sai ya koma wurin 'yarsa yana madimauci
bisa wannan abu da ya gani. Waziri ya ce da ita,
"ya 'yata, na gama ki da Allah ki yaye mini
wannan bakon al'amari da na gani. Ina wannan
saurayi da kika ce kin kwana http://fb.com/
waziriaku da shi?" Sittul Hassana ta ce, "hakika
saurayin da na kwana tare da shi a cikin wannan
dare, zuciyata ta kamu da son shi, so mai
tsanani. Ka sani cewa bayan fitarka daga
wannan daki, na leka makewayi amma ban ga
wannan saurayi ba. Amma ga wandonsa, da
rigarsa, da hularsa can bisa gado, idan har ba ka
yarda da zancena ba."

Lokacin da Waziri ya ji zancen 'yarsa, sai ya
wuce cikin dakin ya nufi wurin gado inda Hassan
ya bar kayansa. Waziri ya dauki hular ya juya ta,

ya sake juya ta a hannunsa, ya dubi 'yarsa ya
ce, "wannan ai irin hular Wazirai ce." Ya sa
hannu ya dauko wandon Hassan, sai ya ji wani
http://fb.com/waziriaku abu mai dan nauyi-
nauyi kunshe a cikin wandon. Ya fitar da abin da
ke da nauyin, sai ya ga jaka ce ta kudi. Ya
zazzage kudin ya kirga, ya ga dinari dubu uku ne
cif-cif. Tare da kudin kuma ya ga takarda, ya
warware takardar sai ya ga an rubuta: Ni Hassan
Badaruddin dan Waziri Nuruddin na mallaka wa
Wannan Bayahude dukiyar mahaifina da ya tafi
fatauci da ita dukkanta, a matsayin ladar
fataucin da ya dade yana http://fb.com/
waziriaku yi wa mahaifina shekara da shekaru.
Da waziri ya karanta wannan takarda, sai ya yi
kururuwa da karfi, daga nan sai ya fadi kasa
sumamme.

Bayan Waziri Shamsuddin ya farfado daga
suman da ya yi, ya kara karanta takarda, ya yi
al'ajabi ya ce, "babu Sarki sai Allah mai iko bisa
ga kome, mai aikata yadda ya so." Sa'annan ya
dubi 'yarsa ya ce, "Shin kin kuwa san wanda ya
kwana tare http://fb.com/waziriaku da ke a
daren jiya?" Yarinya ta ce, "a'a."
Waziri ya ce,

"shi dan dan uwana ne, Nuruddin. Ke da shi 'yan
baffanni kuke. Shi ne wanda na riga na yi
alkawarin aura masa ke, amma sai Sarki ya
nuna mana karfin iko ya ba da ke ga mai
kusumbi ba tare da yardata http://fb.com/
waziriaku ba, kuma ba tare da ya bayar da
sadaki ba. Amma kin ga wannan jakar kudin, ita
ce sadakinki ta daga dan dan uwana, Allah ya
kaddara ya turo shi wurinki da ita domin halasta
saduwarku. Tsarki ya tabbata ga Allah
madaukakin Sarki. Kaiton sanina, da kaka na yi
muwafaka da wannan hukunci."

Yayin nan Waziri ya dauko ratayen layun Hassan
yana dubawa, sai ya lura da wata laya daya
wadda ta sha banban da sauran. To da ma ya
san al'adar kasarsu ta boye sako a cikin laya.
Da ganin wannan layar ta sha banban http://
fb.com/waziriaku da saura, sai ya sa hannu ya
farke ta, sai ya ga takarda nannade da tsumma.

Ya warware takarda ya karanta. A ciki ya ga
labarin da dan uwansa ya ba Hassan tun daga
haihuwarsu, da kuruciyarsu, da sanadiyyar
fitowarsa daga gida har ya isa Basara. Da yadda
ya zama Wazirin Basara, da ranar da ya yi aure
da ranar da http://fb.com/waziriaku aka haifi
Hassan, duk suna rubuce a cikin takarda. Waziri
Shamsuddin ya yi lissafi ya ga ranar da ya yi
aure ta yi daidai da ranar da dan uwansa ya auri
'yar Wazirin Basara, ranar kuma da aka nada shi
Wazirin Basara. Ya yi lissafin ranar da aka haifi
Hassan ya ga ta yi daidai da ranar da aka haifi
Sittul Hassana.

Waziri ya http://fb.com/waziriaku cika da farin
ciki, ya kwashe dukkan labari ya fada wa 'yarsa,
sa'annan ya kwashi takardu ya nufi fada, domin
ya sanar da Sarki wannan labari mai ban
al'ajabi. Da zuwansa fada, bayan ya yi gaisuwa
ga Sarki, ya duka ya fede wa Sarki biri har
wutsiya, sa'annan ya ba shi takardu ya karanta.

Sarki ya yi matukar mamaki a kan wannan
al'amari, wanda Allah ya kaddara burin
wadannan 'yan uwa http://fb.com/waziriaku a
kan 'ya'yansu ya tabbata. Ya roki Waziri gafara
bisa ikon da ya nuna masa a kan 'yarsa. Waziri
ya gafarta masa, Sarki ya sa aka rubuta wannan
labari da ruwan zinariya bisa ga takarda, aka
ajiye shi domin na baya su karanta ko za su karu
da darasin da ke ciki.

Ita kuwa 'yar Waziri, Sittul Hassana, sai ya
kasance ta dauki ciki a wannan http://fb.com/
waziriaku dare da Hassan ya kwana da ita.

Waziri da 'yarsa suka zauna zaman jiran
dawowar Hassan. Da Waziri ya ga kwanaki na ta
http://fb.com/waziriaku shudewa Hassan bai
komo ba, sai ya ce a ransa, "Wallahi sai na
aikata wani abu wanda wanina bai taba aikata
irinsa ba."

gobe zamu daura
11. HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN
UWANSA SHAMSUDDIN

Waziri Shamsuddin ya ce a ransa, Wallahi sai na
aikata wani abu, wanda wanina bai taba aikata
irinsa ba. Yayin nan ya dauko takarda da
tawada, ya rubuta dukkan yadda tsarin gidan da
Hassan ya kwana da 'yarsa Sittul Hassana yake.
Hatta rigar Hassan da hularsa da wandonsa, duk
sai da Waziri ya rubuta su yadda Hassan ya bar
su a gidan.
Ita kuwa 'yar Waziri, ta ci gaba da renon cikinta
har ya kai wata tara. Da lokacin haihuwa ya yi,
ta hai fi danta namiji, kyakkyawa mai kwarjini da
farin jini kamar ubansa. Aka yanke masa cibiya,

aka yi masa wanka, aka shafa masa kwalli ga
makyabtansa. Da ranar suna ta zagayo aka rada
masa suna Ajibu. Aka bayar da shi ga mai
shayarwa.
Tun ranaku na shudewa zuwa makonni, makonni
na komawa watanni, watanni na rikide zuwa
shekaru, a hankali har yaro ya shekara bakwai.
Lokacin da Ajibu ya shekara bakwai, sai
kakansa, Waziri Shamsuddin, ya damka shi a
hannun wani Malami, domin ya koyi karatun
Alkur'ani mai girma da kuma hukunce-hukuncen
addinin musulunci. Ajibu ya ci gaba da karatu a
hannun Malami, tsawon shekara hudu, sai dai ya
tashi a matsayin yaro mai girman kai.
Kodayaushe ya kan riki bulala yana bugun yara
'yan uwansa yana zaginsu, yana cewa, "Duk a
cikin ku, wa ya kai tamkar ni? Ni ne dan Wazirin
Misira gaba dayanta." Da yara suka ga Ajibu ya
matsa musu da bugu da zagi, sai suka kai
kararsa wurin Malaminsu.
Yayin da Malami ya ji karar yara zuwa gare shi,
sai ya ce, "bari in sanar da ku abin da za ku rika
ce masa ku yi maganinsa, ai wata magana ta fi
bugun bulala zafi. Duk lokacin da ya kara yi
muku alfahari da sarauta, kuma ya nemi ya yi
wasa tare da ku, ku ce ba za ku kara yin wasa da
kowa ba sai wanda ya fadi sunan mahaifiyarsa
da mahaifinsa." Yara suka shirya bisa ga
maganar Malaminsu.
Washe gari da yara suka hadu wurin karatu,

kafin Malaminsu ya fito, sai Ajibu ya fara zagin
su yana yi musu alfahari da cewa shi dan
Wazirin Misira ne. Daga nan wani yaro daga
cikin yaran ya ce, "idan an gama karatu yau, ba
za mu yi wasa da kowa ba, sai wanda ya fadi
sunan mahaifiyarsa da mahaifinsa." Can sai
wani yaro ya mike tsaye ya ce, "sunana Majidu,
sunan uwata Ulwiya, sunan ubana Izzuddin."

Wani ma ya tashi ya fadi sunansa da na uwarsa
da na mahaifinsa. Wani ma ya yi haka. Daga nan
sai Ajibu ya ce, "sunana Ajibu, sunan uwata Sittul
Hassana, sunan ubana Shamsuddin, Wazirin
Misira." Sai yara suka dauka gaba daya, Waziri
ba mahaifinka ba ne, shi mahaifin mahaifiyarka
ne, lalle mu ba za mu yi wasa da kai ba yau, sai
ka fada mana sunan mahaifinka. Ran Ajibu ya
baci, ya fasa kuka. Yara kuwa suka yi ta yi masa
dariya da shegantaka, suna cewa, "eho! wani bai
san ubansa ba sai kakansa."

Suna cikin wannan hayaniya sai ga Malaminsu
ya shigo. Ajibu ya kai karar yara gaban
Malaminsu, ya kwashe duk yadda aka yi ya
shaida wa Malam. Malamin ya ce masa,
"gaskiya ne, ka sani cewa ko mu da

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

1 Comments On HIKAYAR WAZIRI NURUDDIN DA DAN UWANSA SHAMSUDDIN
avatar
rabiu-bello

1 year ago

Reply

Nice one

Please Login or Register in order to submit comment