Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yadda ta yi masa aure har zuwa lokacin da
ta saya masa jaki ya rik'a bin masu saran
itace. Sannan ya ba ta labarin yadda saukar
ruwa ya tilasta musu shiga kogo domin su fake,
a nan kuma ya rik'a buga gatarinsa har ya ci
karo da rijiyar zuma. Da yadda 'yan uwansa
suka tafi suka bar shi da yadda kunama ta
fad'o masa ya gane wurin da ta fito har ya yi
babban rami ya fita zuwa inda ya ga k'ofa ya
shiga zuwa wannan fadar. Har zuwa inda ya
gamu da sarauniyar macizai. Daga nan ya ce
mata, "wannan shi ne labarina daga farko har
zuwa yanzun nan da nake magana da ke, Allah
shi ne kuma ya san abin da zai faru da ni nan
gaba."
Sarauniyar macizai ta ce, "kwantar da
hankalinka, babu abin da zai same ka sai
alheri."

ZAMUCI GABA03 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

bayan Hasib ya gama ba wa
sarauniyar macizai labarinsa sai ta ce da shi,
"babu abin da zai same ka sai alheri, amma ina
so ya zauna nan na ba ka tarihina gami da
labarai masu ban al'ajabi wad'anda suka faru
da ni." Hasib ya ce, "na ji na amince."
Sarauniyar macizai ta soma ba shi labari kamar
haka:
LABARIN BULUKIYA
Ka sani ya Hasib akwai wani Sarki a birnin
Misra cikin Bani Isra'ila, ya kasance malami ne
mai tsoron Allah da gudun duniya wanda ya
karanta littattafai ma su yawa, yana d'a namiji
ana kiransa Bulukiya. Yayin da tsufa ya zo
masa ya raunana, jikinsa ya mik'a wuya zuwa
ga mutuwa sai ya tattara manyan fadarsa gaba
d'aya, suka gaishe shi alhali yana kan gado
yana jinya. Ya ce da su, "babu wata wasiyyar
da zan muku face a kan d'ana Bulukiya, ku kula
da shi bayan na mutu. " Daga nan ya yi kalmar
shahada ya mutu. Allah ya ji k'an sa da rahma.
Bayan mutuwarsa aka yi ta koke - koken al'ada
sannan aka shirya shi aka bisne. Daga nan aka
zab'i Bulukiya ya zama magajinsa. Ya rik'a
mulkin mutane da adalci da mutuntawa ya
zamana kowa yana son sa.
Wata rana sai ya shiga taskar mahaifinsa domin
ya ga abin da ta k'unsa ya ci karo da wata
k'aramar k'ofa ya shiga sai ya ga wani d'an
d'aki ya bud'e sai ya ga ashe k'aramar taska ce
da ginshik'i a cikin na farin ruhham. A k'asa
kuma akwai wani akwati na zinariya. Bulukiya
ya d'auko akwatin ya bud'e shi sai ya tarar da
takardu a ciki masu yawa tamkar girman littafi.
Ya bud'e su ya shiga karantawa, ya ga a ciki an
yi bayani siffofi da halaye da d'abi'un Annabi
Muhammadu mai tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi. Ya ga an rubuta cewa za a
aiko shi a k'arshen zamani, amma shi ne
shugaban farko da na k'arshe ga dukkan
annabawa da manzanni.
Yayin da Bulukiya ya k'are karatun takardun, ya
fahimci siffofin Annabinmu Muhammadu mai
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, sai
ya ji k'aunarsa ta shiga ransa, ya tara manyan
fadarsa da sauran masu fad'a a ji cikin Bani
Isra'ila da malamansu da Ruhubaniyawa da
bokayensu duka ya nuna musu wannan littafi,
ya bayyana musu abin da ya k'unsa. Ya
karanto musu wani b'angare daga cikinsa
sannan ya ce, "ya ku jama'ata, ni ina nufin zan
fito da ubana daga kabari na k'one gawarsa."
Suka ce, "don me za ka aikata haka?" Ya ce,
"saboda ya samu wannan littafi da jimawa
amma ya b'oye mana shi bai bayyana mana
ba. Ya samo shi daga littattafan da aka saukar
wa Annabi Ibrahima da wasu bayanan daga
Attaura, amma ya saka shi cikin taska ya b'oye
bai nunawa kowa ba." Suka ce, "ya Sarki, ka
sani mahaifinka ya riga ya bar duniya, gawarsa
na cikin rami kuma da sannu za ta zama k'ura
lamarinsa na wurin Ubangijinsa. Kada ka fito da
shi daga kabarinsa." Da ya ji haka sai ya k'yale
maganar fito da gawar mahaifinsa ya tafi wurin
mahaifiyarsa ya ce, "uwata kin ga abin da na
samu a taskar mahaifina, littafin da ke bayani
kan siffofi da halayyar Annabi Muhammadu mai
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi,
wanda zai zo a k'arshen zamani, na ji zuciyata
ta tafi ga begensa. Na k'udurce a raina zan tafi
yawo a doron k'asa ko Allah zai sa na sadu da
shi, idan ba haka ba kuwa zan iya mutuwa
saboda k'aunarsa da nake yi." Ya cire tufafin
sarautarsa ya saka rigar fatar akuya da
takalman fata ya ce da mahaifiyarsa, "ya uwata
kada ki manta da ni a addu'oinki." Ta yi kuka
mai yawa ta ce da shi, "me zai same mu bayan
baka nan?" Bulukiya ya ce, "ba zan iya hak'uri
ba sai na tafi, na mik'a al'amarina da naku ga
Allah mad'aukakin Sarki."
Daga nan ya fita a k'asa zuwa yankin Sham ba
tare da sanin mutanensa ba. Ya tafi har zuwa
gab'ar kogi ya shiga suka tafi zuwa wani tsibiri
suka sauka gaba d'ayansu domin su huta.
Bulukiya ya tafi k'ark'ashin wata bishiya ya d'an
kishingid'a, babu jimawa barci ya kwashe shi
saboda gajiya da ya yi. Yayin da ya farka ya
tashi zuwa inda jirgin yake sai bai ga komai ba,
jirgin ya tafi. Yana tsaye yana jimamin abin da
ya same shi sai ya rik'a ganin macizai manya -
manya, wasu girmansu kamar na rak'umi wasu
suna da tsawo kamar bishiyar dabino, ya yi ta
maimaita ambaton sunayen Allah yana neman
tsari. Sai ya ji su ma suna hailala da tasbihi
gami da salati ga fiyayyen halitta Annabi
Muhamamdu mai tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi. Ya ji suna ambaton sunayen
Allah mad'aukakin Sarki. Bulukiya ya cika da
mamaki bisa ga wannan.
Yayin da suka
gan shi sai suka kewaye shi suka ce da shi,
"kai wanene? Daga ina kake, kuma ina za ka
je?" Ya ce musu, "ni sunana Bulukiya daga Bani
Isra'ila nake, na fito domin k'aunar saduwa da
fiyayyen halitta Annabi Muhammadu mai tsira
da amincin Allah su tabbata gare shi. Amma ku
su waye, ya kuka kasance halitta mai ban
mamaki haka?" Suka ce, "muna daga halitttun
cikin wutar jahannama, Allah ya halicce mu
domin mu rik'a d'and'anawa kafirai azaba."
"Ta yaya kuka zo wannan wuri?"
Suka ce, "ka sani ya Bulukiya cewa wuta ta
tafarfasa, tafasa mai yawa, saboda tsananin
zafin da ta yi sai ta rok'i Allah da samun
sassauci. Allah ya nufe ta da yin numfashi sau
biyu a shekara. Takan shak'i iska a lokacin
hunturu ta fesar a lokacin bazara, wannan
dalilin ne ya sa ake samun hunturu yake da
sanyi, bazara kuma zafi. To duk lokacin da ta
saki numfashinta sai ta watso irinmu waje.
Yayin da ta natsu kuma za ta shak'i iska sai ta
ja mu zuwa cikinta." Bulukiya ya ce da su, "shin
akwai macizan da suke fi ku girma kuwa a
jahannama kuwa?" Suka ce, "ka sani mu ba ta
fito da mu nan ba face saboda k'ank'antar mu,
akwai a cikinta macijiyar da idan babbar mu a
nan za ta yi tafiya ta kafar hancinta ba za ta
sani ba." Bulukiya ya ce da su, "na ji kuna
ambaton Allah tare da ambaton sunan Annabi
Muhammadu mai tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi. Ta yaya kuka samu
labarinsa?"
Suka ce, "ka sani ya Bulukiya, cewa wannan
suna an rubuta shi a k'ofofin aljanna. Allah bai
halicci duniya ba wala wuta, wala aljanna sai
domin darajarsa. Haka nan sama da k'asa da
abin da ke tsakaninsu duka domin alfarmarsa
aka samar da su. Sannan Allah ya had'a
sunansa da nasa a wurare da dama, don haka
muke son Muhammadu mai tsira da amincin
Allah su tabbata a gare shi."
Da Bulukiya ya ji sai begensa ga Annabi
Muhammadu ya k'aru, ransa ya ratayu ga son
saduwa da shi. Daga nan ya yi bankwana da
wad'annan macizai ya tafi zuwa gab'ar kogi ya
samu jirgi ya shiga. Suka yi ta tafiya har suka
isa wani tsibiri suka sauka suka shiga ciki. A
nan suka ga macizai manya da k'anana, babu
wanda ya san adadin yawansu sai Allah. Daga
cikinsu akwai wata macijiya fara mai hasken jiki
fiye da buluri, tana zaune a kan wani faifan
zinariya wanda yake bayan wani maciji babba
kamar giwa. To ita wannan macijiyar ya Hasib
ita ce sarauniyar macizai watau ni da nake
magana da kai a yanzu." Hasib ya ce, "fad'a
min yaya kuka yi da Bulukiya." Sarauniyar
macizai ta ce, "ka sani ya Hasib, yayin da na
gan shi sai na yi masa sallama ya amsa min,
na ce da shi, "fad'a min wanene kai, me ya
kawo ka nan wurin kuma ina ka nufa?" Ya ce,
"sunana Bulukiya, ina daga Bani Isra'ila kuma
na fito domin mararin saduwa da Annabi
Muhammadu wanda aka siffanta kamanninsa a
littattafai, shi na fito ina nema. Ke kuma
wacece, me wad'annan macizan suke miki?" Na
ce, "ya Bulukiya ni ce sarauniyar macizai , idan
ka sadu da Annabi Muhammadu ka isar min da
gaisuwa gare shi." Daga nan Bulukiya ya yi min
bankwana ya tafi har ya isa ga birnin Baital
Muk'addis. To a cikin birnin nan akwai wani
masani wanda ya karanta littattafai da yawa,
yana da d'imbin sani na daga lissafi da magani
da sauran fannoni na daga ilmin taurari da hirji.
Haka nan ya karanta attaura da zabura da
littattafan da aka saukar wa Annabi Ibrahim.
Ana kiransa Affanu. A cikin karance -
karancensa ya karanta a wani littafi cewa duk
wanda ya sanya zoben Annabi Sulaimanu, to
dukkan mutane da aljanu da tsuntsaye da
dabbobin gida da na daji da dukkan abin halitta
za su yi masa biyayya. Haka nan ya gano cewa
an binne Sulaimanu a cikin wani akwati wanda
aka d'auke shi zuwa wani gida a can bayan
koguna bakwai aka binne a can. Zoben kuma
na hannunsa babu mai ikon cire shi daga gare
shi, walau mutum ko aljani, domin kuma jirgin
da zai iya ratsa koguna bakwai shi kad'ai ko
gayya ne.
Affanu ya karanta a
littattatafai cewa mutum ko aljan babu mai ikon
cire zoben nan daga hannun Sulaimanu,
sannan babu jirgin da zai iya ratsa kogunan
nan ya je wurin da aka binne shi. Haka kuma ya
karanta cewa akwai wata itaciya daga itatuwa
idan mutum ya samu wani abu daga jikinta ya
nannaga ya matse ruwan sannan ya matsi man
da ke jikinta ya gama ya shafa a k'afafunsa, to
zai iya ratsa dukkan kogunan da Allah ya halitta
a duniya tamkar yadda yake tafiya a k'asa ba
tare da ya jik'e ba. Sai dai ita wannan bishiyar
ba a iya sanin ta sai mutum na tare da
sarauniyar macizai. Yayin da Bulukiya ya isa
Baitil Muk'addis ya samu wani waje ya zauna
yana ibada. Sai Affan ya zo gare shi ya yi masa
sallama suka gaisa. Affanu ya ga Bulukiya yana
karanta wani abu daga Attaura yana addu'a sai
ya ce masa, "ka fad'a min kai daga ina kake
kuma ina za ka? Ya ce, 'Ni sunana Bulukiya,
kuma na fito daga Misra za ni neman
Muhammadu mai tsira da abincin Allah su
tabbata a gare shi." Affan ya ce, "ka zo mu je
gidana domin na sauke ka ka zama bak'ona."
Bulukiya ya ce, "na ji na amince." Suka tafi
zuwa gidansa suka ci abinci sannan suka shiga
tattaunawa. Affanu ya ce, "ka ba ni labarin inda
ka samu labarin Ma'aikin Allah Muhammadu
mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi." Bulukiya ya kwashe labarinsa kaf daga
farko har karshe har gamuwarsa macizai duk ya
fad'a masa. Affan ya ji kamar hankalinsa ya fita
daga jikinsa don murna da ganin wanda ya san
inda sarauniyar macizai take. Ya ce da shi ka
kai ni inda sarauniyar macizai take ni kuwa na
yi maka yadda za ka sadu da Muhammadu
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ka
sani bayyanarsa lokaci ne mai nisa daga yanzu.
Amma idan muka yi sa'ar kama sarauniyar
macizai muka sa ta a tarko za mu zagaya da
ita tsakanin itatuwan da suke cikin duwatsu. To
matuk'ar tana tare da mu duk bishiyar da muka
wuce ta gabanta za ta fad'a mana irin amfanin
da ake yi da ita na daga magani cikin ikon
Allah. Idan muka samu bishiyar da ke da
wannan amfani sai mu matse ruwan jijiyar ta
mu shafa a k'afafunmu za mu iya tafiya bisa
doron kogunan da Allah ya halitta ba tare da
mun jik'e ba. Idan mun samu bishiyar sai mu
dawo da ita inda muka d'auke ta, mu kuma mu
shafa ruwan a k'afafunmu mu ratsa koguna
bakwai har mu isa inda aka binne shugabanmu
Sulaimanu d'an Dawuda. Daga nan sai mu cire
zoben daga hannunsa mu mallaki duniya gaba
d'aya kamar yadda Sulaimanu ya yi, mu samu
cimma burinmu. Bayan haka sai mu ratsa kogin
duhu mu sha ruwan rayuwa, ka ga sai mu yi
tsawon rai har zuwa bayyanar Annabi
Muhammadu mai tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi."
Da Bulukiya ya ji haka sai ya ce, "ya Affanu zan
kai ka inda sarauniyar macizai take." Affanu ya
shirya tarkon bak'in k'arfe ya sa kasake biyu a
ciki. D'aya ya cika shi da madara d'ayan kuma
ya cika shi da giya, suka d'auka suka tafi
kwana da kwanaki, ranaku da darare har suka
zo tsibirin da Sarauniyar macizai take ciki suka
ajiye tarkon bakinsa a bud'e ya saka abin rud'i
na daga madara da na giya, suka b'uya. Bayan
wani lokaci sai ga sarauniyar macizai ta ji
k'amshin madara, sai ta sauko daga kan
faifanta ta shiga ta sha madara ta ishe ta,
sannan ta juya giya ita ma ta sha ta k'oshi.
Daga nan sai kanta ya juye ta kwanta barci a
nan. Su Affan na ganin haka suka yi hanzari
suka d'auke ta. Yayin da ta farka sai ta ganta a
cikin d'akin bak'in k'arfe bisa kan wani mutum,
gefensa kuma Bulukiya ne suna tafiya. Ta ce da
Bulukiya, "yanzu wannan shi ne sakamakon
wanda ba ya cutar da bil adama?"

ZAMUCI GABA GOBE INSHA ALLAH04 HIKAYAR SARAUNIYA MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI
Bulukiya ya ce, "ka da ki ji tsoron komai daga
gare mu, mun d'auko ki ne domin mu wuce da
ke ta gaban itatuwa za su rik'a fad'in amfaninsu
da kansu. Muna son sanin bishiyar da ake
shafa ruwanta a k'afafu a shiga kogi a yi tafiya
ba tare an jik'e ba. Idan mun samu wannan za
mu dawo da ke wurinki ba tare da cutarwa ba."
Affanu da Bulukiya suka hau bisa duwatsu suka
yi ta ratsa tsakanin itatuwa suna yin magana
suna furta irin amfaninsu cikin ikon Allah. Bayan
sun wuce itatuwa da yawa suna ta fad'in
amfaninsu a hagu da dama can sai wata itaciya
ta ce, "ni ce itaciyar da duk wanda ya rik'e ni ya
dandak'a ya matse ruwan ya shafa a
k'afafunsa, to zai tsallake duk wani kogi da
Allah ya halitta ba tare da ya jik'e ba." Da
Affanu ya ji haka sai ya sauke sarauniyar
macizai ya rik'i abin da zai ishe su daga itaciyar
ya nannaga ya d'ebe ruwan cikin battoci biyu
saboda gaba. Daga nan suka juyo suka mayar
da sarauniyar macizai inda suka d'auke ta.
Bayan ta samu kanta sai ta ce da su, "me za ku
yi da wannan ruwan haka?" Suka fad'a mata
aniyar su. Da ta ji daga bakinsu sai ta ce, "ni
sarauniyar macizai ina sanar da ku cewa ba za
ku tab'a samun cire zoben nan ba har abada!"
Suka ce, "don me kika ce haka?" Ta ce, "Allah
mad'aukakin Sarki ya ba wa Annabi Sulaimanu
zoben nan bisa baiwar da ya yi masa
albarkacin addu'ar da ya yi cewa 'Ubangijina,
ka ba ni mulki da sarauta wadda ba kamar ta
ga wani bayan ni. Hak'ik'a kai ne mai baiwa.'
Don haka wannan zoben ya fi k'arfinku, ba naku
ba ne." Sannan ta k'ara da cewa, "ina ma a ce
ku biyun nan itaciyar da idan aka ci ta ba a
mutuwa kuka ci ai da ba haka ba. Idan mutum
ya ci itaciyar to ba zai mutu ba har san an busa
k'ahon farko. Kuma ita wannan itaciyar tana
nan wurin da kuka je." Da suka ji haka sai suka
yi bak'in ciki da nadama mai yawa. Daga nan
babu yadda za su yi suka wuce zuwa aiwatar
da aikinsu.
yayin da Affanu da Bulukiya
suka ji zancen sarauniyar macizai, sai suka yi
bak'in ciki da nadama mai yawa. Daga nan
babu yadda za su yi suka wuce zuwa aiwatar
da aikinsu. Wannan kenan game da lamarinsu.
Ni kuwa da na samu kaina sai na tafi wajen
mutanena, na same su sun raunana suna halin
jimami da firgici. Masu k'arfinsu sun zama
raunana, raunanansu sun mutu, wasu sun
jikkata, sun kasa motsi. Yayin da suka gan ni
sai suka taso gaba d'aya suka yo kaina cikin
farin ciki suka ce da ni, "me ya same ki?" Na
fad'a musu abin da ya faru, daga nan na had'a
kan rundunata na jagorance su zuwa dutsen
kaf inda nake zama a lokacin d'ari, da bazara
kuma ina hutawa a wannan wurin da ka gan ni.
Ta dube shi ta ce da to Hasib Karimuddini
wannan shi ne labarina da abin da ya auku gare
ni." Hasib ya cika da mamaki mai yawa sannan
ya ce da ita, "ni dai ina rok'on alfarmarki da ki
sa d'aya daga hadimanki ya fitar da ni zuwa
doron k'asa domin na koma wajen mutanena."
Ta ce, "ya Hasib ba za ka bar mu ba sai lokacin
d'ari za mu tafi da kai zuwa dutsen Kaf ka yi
kallo a can ka shak'i iska mai dad'i, ka ga
tuddai da rairayi da itatuwa da tsuntsaye
manya - manya suna tsarkake sunan Allah mai
girma. Kuma ka ga Maridai da Ifritai da Aljannu
wad'anda babu wanda ya san adadin yawansu
sai Allah."
Yayin da Hasib ya ji haka sai ya fashe da kuka
mai tsanani. Bayan ya natsu ya ce da ita, "fad'a
min game da Affan da Bulukiya yayin da suka
bar ki suka tafi, yalla sun samu tsallake koguna
bakwan, sun isa inda suke son zuwa, sun yi
nasarar d'auko zoben?"
Ta ce, "yayin da suka bar ni, suka shafe
k'afafunsu da ruwan nan suka shiga kogi suna
tafiya da k'afafunsu kuma ba su nutse ba, ba
su jik'e ba. Abin gwanin ban sha'awa da
mamaki. Suna ta kallon ikon Allah na game da
girman kogunan da zurfinsu har suka kai kogi
na bakwai sai suka hangi wani tsauni mai girma
wanda ya tokare sararin sama, duwatsunsa na
zubarjadi ne, k'asar wurin ta miski ce, daga
k'ark'ashinsa ruwa ne ke gudana. Yayin da
suka ga wurin sai suka cika da farin ciki suna
cewa, "mun samu cikar burinmu." Suka kama
hawan tsauni har suka ga wani kwararo a ciki
suka shiga cikin tsaunin suka yi ta tafiya har
suka ga wani haske na fitowa daga wata
k'ubba. Suka shiga cikin k'ubbar a nan suka ga
wani gadon zinariya an yi masa ado daga
dukkan nau'in jauhari, a gaba gare ta kuma
kujeri ne reras bilahaddin. Suka ga Annabi
Sulaimanu kwance a bisa gadon tamkar yana
barci. Yana sanye da riga ta d'anyen alharini,
an yi masa zane da zinariya sannan an daje shi
da zab'ab'b'en lu'ulu'u da jauhari. Ya d'ora
hannunsa na dama akan k'irjinsa, zoben na
cikin yatsansa. Hasken zoben ya rinjayi dukkan
hasken abubuwan da ke wajen.
Affanu ya koya wa Bulukiya wasu addu'o'i da
d'alamisai ya ce ya yi ta karantawa kada ya
daina har sai ya d'auko zoben. Bulukiya ya yi ta
maimaita kalmomin yayin da Affanu ya matsa
kusa da gadon yana karanta addu'oi. Ya taka
matakala kenan sai wata babbar macijiya ta
bayyana gabansa, ta yi gunji gami da kururuwa
har sai da wajen ya rik'a raurawa. Tartsatsin
wuta ya rik'a fita daga bakinta ta ce, "koma da
baya ko ka mutu!" Bai saurare ta ba ya ci gaba
da karance - karancensa yana matsawa zuwa
ga zoben. Ta huro masa wata dunk'ulalliyar
wuta gabansa ta ce, "kaitonka! Koma da baya
ko na k'one ka!" Da Bulukiya ya ji haka sai ya
razana ya fita daga wajen, shi kuwa Affanu ya ci
gaba da matsawa gaba yana addu'a. Ya matsa
kusa da shugaba Sulaimanu ya sa hannunsa
kan zoben, sai dabbar da ke kusa da gadon ta
yi kuka, macijiyar nan ta feso masa wuta ta
k'one shi nan take ya zama toka. Wannan
kenan game da Affanu. Amma Bulukiya kuwa
da ya ga haka sai ya gigice ya fad'i k'asa
sumamme.

ZAMU CI GABA05 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

sarauniyar macizai ta ci
gaba da ba wa Hasib labari, "yayin da Bulukiya
ya ga wutar da ta k'one Affa
nu ya zama toka sai ya gigice ya fad'i k'asa
sumamme. Macijiyar kuma ta haw
o zuwa inda yake domin shi ma ta gama da shi.
Allah ya aiko wani mala'ika y
a d'auke shi, ya kub'utar da shi sannan ya
tashe shi ya yi masa sallama ya
ce, "ta yaya ka zo wannan wurin?" Bulukiya
wanda a tsammaninsa da d'an Adam
yake magana ya ba shi labarinsa, sannan ya
k'ara da cewa, "na zo nan a bur
ina na saduwa da Annabi Muhammadu mai
tsira da amincin Allah su tabbata gar
e shi, Affanu ya shaida min cewa sai a k'arshen
duniya zai bayyana don haka
muka zo da nufin samun yadda za mu sha
ruwan rayuwa ta zoben shugaba Sulai
manu, hakan zai sa mu tabbata a k'arshen
zamani lokacin da zai bayyana." Ya
ci gaba da cewa, "ga shi yanzu mun zo wajen
shi kuma Affanu ya rasa ransa.
Ni kam yanzu burina shi ne ka fad'a min ta
yaya zan sadu da manzon tsira M
uhammadu?" Mala'ikan ya ce masa, "ka
dangana ka koma gida, cewa ba zai bayy
ana ba sai a k'arshen zamani." Daga nan ya
bar shi ya koma zuwa sama.
Bulukiya ya zauna yana kuka mai tsanani yana
tuba bisa ga zunubansa yana na
dama. Daga nan ya tuna gargad'in da na yi
musu na cewa d'an Adam bai isa ma
llakar zoben nan ba har abada. Ya gangaro da
tsaunin cikin damuwa ya tafa g
ab'ar kogi ya kwanta yana ta mamakin
tsaunuka da tsibirin da ke kewaye da s
hi. Da gari ya waye ya shafa ruwan bishiyar nan
ya shiga cikin kogin yana t
a tafiya dare da rana har ya zo wani tsibiri mai
cike da 'ya'yan itatuwa ta
mkar aljanna domin kyawo. Ya sauka a cikinta
ya ga tana k'unshe da abubuwan
al'ajabi da yawa. K'asar wajen ta yak'utu ce,
duwatsun na zubarjadi sannan
akwai wad'anda suke dangin murjani da ambar,
rairayinta na k'amshin yasimi
, ganyayenta na haske da k'amshi, bishiyoyinta
na turaren wuta ne sandal ma
i haske. 'Ya'yan bishiyun gwanin zak'i
kowannen su tamkar ya fi d'an uwansa
zak'ak'awa. Akwai furanni bilahaddin masu
mabambamtan launi da k'amshi.. Is
kar wajen na bugawa gwanin sanyi mai
sanyaya zuciya. A tak'aice dai wannan
tsibiri ya had'a dukkan abin da ake buk'ata na
kyawo da ban sha'awa. Ga kum
a tsuntsaye suna wak'ok'i da murya gwanin
dad'i wadda za ta sa mutum ya dul
miya duniyar bege da nishad'i. Gefe d'aya kuma
bareyi na tsalle - tsalle su
na kiwo, ga dabbobin daji dangin su b'auna da
gada suna kai wa da komowa a
sararinta. Bishiyoyinta dogaye ne, daga can
jikin wani tsauni kuma ruwa ne
ke gangarowa zuwa wata k'orama mai haske da
dad'in sha da dad'in gani. Bulu
kiya ya tsaya yana mamakin wannan tsibiri da
bai ga tamkarsa ba tun da ya f
ito. A nan ya fahimci ya kuskure hanyar da
suka biyo shi da Affanu. Ya zaga
ya cikin tsibirin ya yi kallo ya kashe kwarkwatar
idanunsa har zuwa dare sa
nnan ya hau wata bishiya ya kwanta barci. Tun
barcin bai yi nisa ba ya ji w
ata k'ara mai ban firgici da wani irin motsi daga
cikin kogin. Can jimawa s
ai wata babbar halitta ta fito daga ciki tana
gurnani da huci. Bulukiya ya
tsorata da ganin ta har ya kusa fad'owa daga
kan bishiyar. Ya rik'a mamaki
n irin girmanta.
Babu jimawa sai ga wasu halittun suna fitowa
daga cikin ruwan, kowanne na d
'auke da jauhari yana haske, har sai da tsibirin
ya haskake saboda yawan ja
uharin. Bayan haka sai ga dabbobin daji suna
tattaruwa a wajen, sun had'a d
a dukkan namun daji na daga zaki da damisa
da kura da giwaye babu wanda ya
sa adadinsu sai Allah. Suka yi ta hira da
junansu har zuwa asuba sannan kow
anne ya kama hanya zuwa ga halin tafarkinsa.
Da Bulukiya ya ga haka sai ya
tsorata ya shafawa k'afarsa ruwan nan ya shiga
kogi na biyu. Ya yi ta tafi
ya dare da rana har ya isa k'arshen kogin zuwa
wani tsibiri inda ya shiga y
a sadu da wani dutse mai girma da wani kwari
a cikin dutsen wanda ba shi da
iyaka duka duwatsunsa maganisu ne kuma
dabbobinsa duka zakoki ne da zomaye
da damisu. Bulukiya ya hau bisa ga wannan
dutsen ya yi ta tafiya har zuwa
maraice ya zauna k'ark'ashin wani kogon dutse
a gefen kogi ya rik'a tsintar
busassun kifaye da ruwa ya turo gefe yana ci.
Yana cikin wannan halin ya w
aiwaya kenan sai ya ga wata babbar damisa
mai girman gaske tana sand'a domi
n ta taushe shi. Ya firgita da ganin haka, cikin
hanzari ya shafawa k'afars
a ruwa ya fad'a kogi na uku ya tafi cikin dare.
Daren kuwa ya kasance mai d
uhu iska na kad'awa, igiyar ruwa na murd'awa.
A haka har ya isa wani tsibir
in ya sauka ya ga 'ya'yan itace na daga kayan
marmari d'anyu da nunannu da
busassu. Ya d'ebi daidai gwargwadon da yake
buk'ata ya ci ya k'oshi ya gode
wa Allah. Ya zagaya cikin ta yana yawo, ya yi ta
zagayawa har dare ya yi.
Bulukiya ya yi ta yawo cikin tsibirin nan har dare ya yi sannan
ya samu wuri ya kwanta.. Da
gari ya waye ya ci gaba da zagaya tsibirin yana
kallo idan ya gaji ya zaun
a ya huta har kwanaki goma. Daga nan ya
shafa ruwa a k'afarsa ya shiga kogi
na hud'u. Yayi ta tafiya a cikinsa dare da rana
har ya iso wani tsibirin,
ya ga k'asar wurin tattausa ce fara, babu komai
a cikinta na daga itace ba
llantana shuka ko tsuntsaye. Ya huta a cikinta
sa'a guda sannan ya tashi y
a shiga kogi na biyar ya yi ta tafiya ba dare ba
rana har ya isa wani tsibi
rin mai k'unshe da duwatsu masu haske kamar
k'ank'ara.
Daga duwatsun akwai irin wad'anda ake samun
zinariya a ciki da wad'anda ake
gyara su a yi zinariya da su. Ya ga a ciki wasu
irin itatuwa masu ban mam
aki wad'anda bai tab'a ganin tamkarsu ba a
baya, furensu tamkar zinariya, '
ya'yansu tamkar lu'ulu'u. Ya shiga cikin tsibirin
ya zagaya yawo har lokaci
n da dare ya yi, sai ya ga furannin nan na
haskakawa kamar taurari. Ganin h
aka ya yi mamaki sosai ya ce a ransa, 'ko
furannin nan suna daga wad'anda k
e fad'owa daga rana zuwa duniya sai iska ta
kad'a su zuwa

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment