Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zaune tsakanin
wasu kaburbura guda biyu, yana kuka yana
gunji. Bulukiya ya yi masa sallama, saurayi ya
dakata da kuka ya mayar masa da sallama.
Bulukiya ya tambaye shi, "wanene kai?
Wadannan kaburburan fa? Su waye a cikinsu?"
Saurayi ya dube shi ya kara fashewa da kuka.
Ya yi kuka har sai da hawaye suka jike masa
gaban riga. Sa'annan ya ce, "ka sani ya kai dan
uwana, labarina abin mamaki ne da ban
tausayi. Amma ba zan gaya maka shi ba har
sai ka zauna tare da ni ka gaya mini labarinka
da kuma inda ka nufa."
Bulukiya ya sami wuri kusa ga saurayi ya
zauna. Ya kwashe labarinsa duka, tun daga
mutuwar mahaifinsa da yadda ya fito gida da
dalilin fitowarsa da abubuwan mamaki da ya
gamu da su, ya gaya wa saurayi. Ya kara da
cewa, "yanzu Allah kadai ya san abin da zai
faru gare ni bayan wannan."
Saurayi ya yi ajiyar zuciya, bayan ya ji labarin
Bulukiya. Ya ce, "ya dan uwana, Wallahi ba ka
ga kome na mamaki ba a kan abin da na gani.
Ka sani ya kai Bulukiya, ni na gamu da wakilan
Shugabanmu Annabi Sulaimanu wato wadanda
ya dora kan wakilci tun a lokacin rayuwarsa. Na
gamu da abubuwan mamaki barkatai. Hakika
labarina bako ne, ina so ka zauna nan wurina
har in gaya maka dukkan labarina. Za ka ji
sababin zamana a wannan wuri, da labarin
wadannan kaburbura da kake gani."
Lokacin da Sarauniyar Macizai ta kawo nan da
labarinta sai Hasibu ya katse ta ya ce, "Allah ya
ba ki nasara ya Sarauniya, ki bar ni in tafi gida.
Ki hada ni da bayinki su fitar da ni daga wannan
rami su kai ni bisa ga bayan kasa. Na rantse
miki da Allah idan na koma gida ba zan kara yin
wanka a gidan wanka ba sai a gidana duk
tsawon rayuwata."
Ta ce, "ba zan bari ka fita daga wannan rami
ba, domin ban yarda da rantsuwarka ba." Da ya
ji haka sai ya fashe da kuka, macizai suka yi
kuka don tausayinsa. Suka shiga ba Sarauniya
hakuri suna cewa, "muna rokonki ki hada shi da
daya daga cikinmu ya fitar da shi daga wannan
rami. Ya ranste miki ba zai kara shiga gidan
wanka ba tsawon rayuwarsa."
Yayin da Sauraniyar Macizai, mai suna
Yamlaika, ta ji macizai sun matsa mata da roko,
sai ta juya wurin Hasib ta sa ya rantse har cikin
zuciyarsa cewa bayan ya fita daga wurinta ba
zai kara shiga gidan wanka ba. Bayan ya
rantse sai ta umurci wani katon maciji, wanda
ya fi jaki girma, ya dauke shi ya fitar da shi
waje. Maciji ya duka zai dauke shi, sai ya juya
wurin Sarauniya Yamlaika ya ce, "ba zan tafi ba
sai na ji labarin saurayin nan da Bulukiya ya
iske yana kuka a cikin tsibiri da kaburbura a
gabansa."

ZANCI GABA INSHA ALLAH09 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

bayan Bulukiya ya gama
labarinsa, sai saurayi ya ce, "ya dan uwana, me
ka gani na mamaki? Ai ba ka ga kome ba a kan
abin da na gani. Ni na ga Shugaba Sulaimanu a
lokacin rayuwarsa. Na hadu da abubuwan
mamaki iri-iri wadanda wani na bai taba gani
ba. Sai ya fara labarinsa kamar haka:
LABARIN JANSHAHU DAN SARKIN KABILA
Ka sani cewa ya kai Bulukiya, mahaifina Sarki
ne, sunansa Daigamusu. Yana mulkin daular
Kabila (Kabul) da ta Banu Shahalan. A
karkashin mulkinsa akwai daulolin sarakuna
dubu goma, kowane sarki yana mulki da birane
dari, kowane birni yana da kauyuka dari a
karkashinsa. A cikin kowane kauye akwai akalla
gidaje dari. Duka wadannan dauloli sukan kawo
masa haraji a kowace shekara. Saboda haka a
tsaya kwatanta yawan arzikinsa da yawan
askarawansa bata lokaci ne kawai. Ya kasance
Sarki mai adalci, yana kuma mulkin jama'arsa
da gaskiya. Sai dai duk da wannan ni'ima da
yake ciki, Allah bai nufe shi da samun da ba,
wanda zai gaje shi bayan ransa.
Kullum da wannan tunani mahaifina ke kwana,
da shi yake tashi. Rannan dai sai ya sa aka tara
masa dukan Malaman kasar, da masu bugun
taurari da masu hisabi. Ya ce musu, "ina so ku
duba mini taurari ku gani, shin zan sami dan da
zai gaje ni kafin mutuwata?"
Kowanen su ya dukufa ga aikinsa. Masu bugun
taurari suka shiga zane bisa kasa suna
sharewa, masu hisabi suka shiga lissafi,
Malamai suka dauko takardu suka shiga nazari.
Zuwa can suka ce masa, "ya Sarki, hakika Allah
zai arzuta ka da haihuwar da namiji. Amma ba
za ka sami wannan da ba sai tare da 'yar
Sarkin Hurassana."
Sarki ya yi farin ciki da wannan albishir na
Malamai. Ya yi musu kyauta mai tarin yawa, ya
sallame su. Ya kira babban Wazirinsa mai suna
Ainazari, shi kuma wani shahararren jarumi ne
wanda shi kadai yakan fatattaki rundunar
mutum dubu. Duk fadin daular Kabila da
kewayenta sun san shi, sun san tsananin
jaruntaka tasa. Da ya zo Sarki ya gaya masa
abin da Malamai suka gani a cikin taurari. Ya
kara da cewa, "yanzu sai ka shirya maza ka tafi
zuwa Hurassana, ka nemo mini auren 'yar Sarki
Baharwanu."
Waziri Ainazari ya tafi ya hada tawagar da zai
tafi da ita, suka kafa tantuna bayan gari suna
jira Sarki ya sallame su. Sarki Daigamusu ya
kawo dukiya mai yawa ciki har da kyankyandi
na alharini alfan da dari biyar da zinariya da
azurfa da yakutu da sauran duwatsu masu
daraja, ya ce a kai wa Sarki Baharwanu. Ya
kuma kawo kaya irin wadanda amarya za ta
bukata wajen yin ado ya bayar. Aka labta wa
rakuma da alfadarai kaya. Kafin su tafi Sarki ya
dauko takarda da alkalami ya rubuta wa Sarki
Baharwanu wasika. A cikin takardar ya rubuta:
Bayan gaisuwa da fatar alheri, daga Sarki
Daigamusu zuwa ga Sarki Baharwanu. Ka sani
cewa mun tara masana ilimin taurari da hisabi
sun gaya mana cewa za mu samu haihuwar da
namiji, amma wannan da ba zai samu ba face
tare da 'yarka. Saboda haka ne na turo
Wazirina Ainazari tare da gaisuwa zuwa gare ka
da kuma dukiyar neman aure. Na umurce shi,
idan ka yarda, ya zama wakilina a wurin auren
da duk wata hidima da za a yi. Idan an
kammala kome ya zo mini da amarya. Kamar
yadda na san ka mutum mai saukin kai da
saurin fahimtar al'amurra na san ba za ka juya
wa wannan muhimmiyar bukata tawa baya ba.
Kada ka manta ya Sarki Baharwanu, ni ke mulki
da daular Kabila da ta Banu Shahalan, a
karkashina ina da dauloli masu karfi. Idan na
auri 'yarka za mu yi tarayya a cikin mulkin
wadannan dauloli, na kuma yi alkawari zan rika
turo maka da wani yanki na harajin da nake
karba duk shekara. Ko ba kome ma, ai dan da
za mu haifa shi zai gaje ni, kuma jikanka ne.
Wannan ita ce bukatata zuwa gare ka.
Sarki ya like bakin takarda, ya manna mata
wata alama shaidar daga gare shi take, ya ba
Wazirinsa. Waziri ya tafi tare da tawagarsa
zuwa birnin Hurassana. Kwanci tashi har suka
isa bayan birni, suka kafa tantunansu. Yayin da
labarin zuwan su ya iske Sarki Baharwanu sai
ya tada manyan fadawansa domin su tarye su.
Aka aza wa dabbobi abinci da abin sha da
kuma harawa saboda dabbobi, suka nufi wurin
tawagar Waziri Ainazari da ke bayan gari. Da
suka isa suka sauka daga kan dabbobinsu,
suka gaggaisa da juna, aka shirya abinci da
abin sha. Suka zauna suka ci suka sha har
suka tumbatsa, daga nan sai suka shiga hira.
Haka suka kasance a bayan gari tsawon
kwana goma, sa'annan suka shirya kayansu
duka, suka hau dabbobi suka dunguma sai
cikin gari.
Sarki Baharwanu ya taryi Waziri Ainazari a
bakin fadarsa cikin murna da farin ciki, suka
rungumi juna, Sarki ya ja shi zuwa cikin fadarsa.
Ainazari ya kawo dukan dukiyar da ya zo da ita
daga Sarki Daigamusu ya ba Sarki Baharwanu,
ya zaro wasika ya ba shi. Bayan Sarki ya
karanta wasika ya fahimci sakon da ke cikinta,
sai murna ta kashe shi. Ya juya wurin Waziri
fuskarsa cike da fara'a ya ce, "ka yi murna ya
kai Waziri, wallahi da Sarki Daigamusu zai
bukaci rayuwata da sai in ba shi balle 'yata." Ya
tashi ya shiga cikin gida, ya tarar da diyarsa da
mahaifiyarta, ya kwashe labarin abin da ke tafe
da Wazirin Sarki Daigamusu ya shaida musu.
Ya tambayi ra'ayinsu, suka ce ya yi abin da
duka ya ga ya dace. Ya kuma tara fadawansa
ya gaya musu dalilin zuwan Ainazari, ya nemi
shawararsu. Su ma suka ce masa ya yi abin da
duk ya ga ya dace.
Sai ya tafi wurin Waziri Ainazari ya shaida masa cewa ya amince da bukatar Sarki
Daigamusu ta auren 'yarsa. Waziri ya zauna a
wannan birni tsawon wata biyu, daga nan sai
ya ce wa Sarki, ya kamata a yi haramar daurin
aure domin yana so ya koma kasarsu. Sarki ya
ce, wannan shi ne zancen hankali.
Aka shirya dukkan abin da ake bukata na
daurin aure. Sarki ya tara waziransa da hakimai
da fadawa da malamai, kai har da talakawan
gari sai da aka gayyato. Aka taru tinjim a kofar
fada. Sarki ya umurci malamai su daura auren
Sarki Daigamusu da 'yarsa karkashin wakilcin
Waziri Ainazari. Bayan an daura aure, Sarki ya
sa aka kawata birni da kwalliya, aka shimfide
dukkan hanyoyi da shimfidu na alfarma. Aka
shirya amarya da kayan ado iri-iri ta fito kamar
'yar tsana.

ZANCI GABA INSHA ALLAH
matsalar dayace gaskiya comment da like suna kasawa dole mutum yaji sanyin jiki wannan fa anayi ne kawai dan sha'awa bawai kudiba' anma in zaku karanta kuwuce shuru to tayaya zangane cewa bani daya nake rawa na ina kida ba.

WhatsApp only 08032767547

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment