Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

k'ark'ashin duwat
su idan an fasa dutsen a fito da su ana aikata
zinariya da su?'

ZANCI GABA INSHA ALLAH

06 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

Ya yi barci a nan har zuwa wayewar gari
sannan ya shafa ruwa a k'afarsa ya shiga kogi
na shida, ya yi ta tafiya dare da rana har ya isa
wani tsibiri. Ya sauka a ciki yana tafiya kimanin
sa'a guda sai ya ga wasu duwatsu manya guda
biyu itatuwa sun mamaye su wad'anda
'ya'yansu tamkar fuskar mutum suke, akwai
gashi da hanci da ido da baki da kunne a
jikinsu. Wasu kuma 'ya'yansu tamkar tsuntsaye
suke suna mak'ale da k'afafunsu a jikin
bishiyar. Wata bishiyar kuma 'ya'yanta tamkar
k'wai da nama suke suna fad'owa. Ta kasance
tana cin wuta a bisanta duk wanda ya je kusa
da ita zai iya k'onewa. Wasu kuma 'ya'yan
itaciyar tamkar mutane na dariya, wasu kamar
suna kuka. Ya ga dai abubuwan al'ajabi da
yawa a wannan tsibirin. Da gari ya waye ya tafi
gab'ar kogi sai ya ga wata doguwar bishiya ya
zauna k'ark'ashinta har lokacin da dare ya yi
sannan ya hau kan ta ya yi barci. Ya zamana
yana tunanin ayyuka da hikimomin ubangiji
mad'aukakin Sarki, yana wannan tunanin sai ya
ga ruwa ya yi k'asa, 'ya'yan ruwa suka fito
daga ciki kowanne na d'auke da jauhari yana
haske. Suka tattaru a k'ark'ashin bishiyar nan
da yake kai suna wasanni suna rawa, suna
wak'a, shi kuwa yana daga sama yana kallon
su yana nishad'i, yana mamakin haka. Ba su
gushe ba suna haka har gari ya waye sannan
suka koma cikin ruwa suka b'ace. Ya sauko
k'asa ya shiga kogi na bakwai bayan ya shafe
k'afarsa da ruwan nan. Yayi ta tafiya ba dare
ba rana bai ga wani tsibiri ba ko gab'a ko itace
ko fili ko kwari har wata biyu cikakku sannan ya
kawo k'arshen sa. Ya wahala sosai saboda
yunwa har sai da ya kai yana farautar kifi da
hannunsa kuma yana cinsa haka d'anye
saboda yunwa. Ya sauka daidai lokacin walaha
cikin wani tsibiri mai yawan itatuwa dogaye. Ya
rik'a dubawa dama da hagu yana tafiya ciki har
ya ga itaciya tuffaha mai 'ya'ya a jikinta, ya sa
hannu zai tsinko, sai ya ji an daka masa tsawa
daga saman bishiyar ana cewa, "kul ka kuskura
ka matso kusa da wannan bishiyar, zan raba
jikinka biyu!" Ya d'aga kai cikin firgici ya ga
wani jiki ya kai zira'i arba'in na mutanen
wannan zamani. Tsoronsa ya k'aru ya yi
hanzarin barin wannan bishiyar. Sannan ya ce
da jikin, "me ya sa ka hana ni ci daga wannan
bishiyar?" Jikin ya ce, "saboda kai d'an Adam
ne ubanka Adamu ya manta da alk'awarin Allah
ya ci daga bishiyar da aka hana shi ya aikata
zunubi.
"To kai menene, kuma wannan tsibirin na
wanene, kuma yaya sunanka?" Bulukiya ya
tambayi jikin.
"Ni sunana Sharahiyu kuma tsibirin nan
mallakin sarki Saharu ne, ni bawansa ne wanda
ke kula da nan." Daga nan ya ce da Bulukiya,
"kai kuma wanene, ta yaya ka zo nan?" Ya
fad'a masa labarinsa kaf, daga nan ya ce,
"kada ka ji tsoro, babu abin da zai same ka." Ya
kawo masa abin da zai ci na daga abinci, ya ci
har ya ishe shi sannan ya yi sallama da jikin
nan ya tafi. Yayi ta tafiya tsakanin duwatsu da
hamada da rairayi har kwana goma. Daga nan
ya tsinkayi k'ura na murtukewa daga nesa
kamar rumfa. Da ya sake matsawa sai ya ji ana
kururuwa da nishi da tankiya. Ya ga jama'a
bisa dawaki suna ta yak'i da junansu jini na
zuba har ya zama tamkar k'orama na gudana.
Muryoyinsu na rugugi tamkar aradu, suna rik'e
da takubba da masu da gatura da majaujawa
da kibiya da sulke da buke da duk wasu nau'in
kayan fad'a abin k'erawa da bak'in k'arfe. Da
ya ga haka sai ya firgita tsoro mai tsanani ya
kama shi. yayin da Bulukiya ya ga irin
wannan yak'i sai ya firgita ya razana da tsoro
mai tsanani. Yayin nan ya toge bai iya
k'arasawa gare su ba, can sai suka hange shi,
suka rirrik'e hannayen junansu suka bar yak'in
suka taho zuwa gare shi. Suka kewaye shi suna
mamakinsa, d'aya daga cikinsu ya ce, "wanene
kai, ta yaya ka zo nan kuma ina za ka je,
sannan wanene ya nuna maka wannan gari
namu?" Ya ce musu, "ni d'an Adam ne daga
cikin Bani Isra'ila, na fito cikin begen saduwa da
annabin k'arshen zamani Muhammadu mai
tsira da aminci su tabbata a gare shi, amma na
b'ace hanya ne na biyo nan." Mahayin dokin ya
ce, "ba mu tab'a ganin d'an Adama ya zo nan
ba sai kai a yau d'in nan." Suka yi ta
mamakinsa da iya maganarsa. Ya ce musu, "ku
wace irin halitta ce?" Suka ce "muna daga
k'abilun aljanu ne."
"Menene musabbabin wannan yak'in naku,
yaya sunan wannan bigire kuma daga ina
kuke?" Suka ce, "daga farar k'asa muke, duk
shekara Allah kan umarce mu da mu zo wannan
wuri mu yak'i kafiran aljannu." Bulukiya ya ce,
"ina farar k'asa take?"
"Can ne bayan dutsen K'af daga nan tafiyar
shekara saba'in da biyar ne, nan kuma tana
cikin k'asashen Shaddadu d'an Adu, mu
aikinmu kenan yak'i da kuma tasbihi da hailala
ga Ubangiji. Kuma muna da sarki sunansa
Saharu, babu komai a kan ka za mu je tare da
kai wajensa domin ya gan ka ya ji dad'i." Suka
tafi tare da shi har suka isa masaukinsu inda ya
ga wasu manya - manya shigifu na koren
alharini babu wanda ya san adadinsu sai Allah
mad'aukakin Sarki. Daga tsakiyarsu kuma wani
d’aki ne ma fi girma an yi masa ado da jan
alharini fad'insa ya kai murabba'in zira'i dubu,
gefensa an d'aura shudin alharini, sannan
itatuwan da aka kafa shi an d'ad'd'aura
zinariya da azurfa. Bulukiya ya yi mamaki mai
yawa da ganin wannan wuri ya tafi tare da su
zuwa babban d’akin, wanda shi ne na sarkinsu.
Suka shigar da shi gaban sarki Saharu wanda
ke zaune akan k'asaitacciyar kujera ta azurfa
kansa na d'auke da kambi na jan zinariya, an
mata ado da lu'ulu'u. Daga damansa
sarakunan aljanu ne hagunsa kuma malamai
da mahukunta da sauran ma'abuta daula da
wasun su. Da sarki ya gan shi sai ya buk'aci a
shigo da shi gabansa. Bulukiya ya sunkuya ya
sumbaci k'asa a gaban sarki. Sarki Sahara ya
ce, "matso nan kusa da ni ya kai namiji." Ya
matsa kusa da shi, Sarki ya yi umarnin a kafa
masa kujera ya zauna sannan ya ce masa, "kai
wace halitta ce? Bulukiya ya ce, "ni bil adam ne
daga cikin Bani Isra'ila."
"Fad'a min labarinka da yadda ka zo wannan
wurin namu." Bulukiya ya kwashe labarinsa ya
fad'a wa sarki Saharu. Sarki ya cika da mamaki
da jin wannan labari.

Zanci gaba insha Allah07 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

bayan Bulukiya ya k'are bai
wa Sarki labarinsa, Sarki ya yi ta mamaki da
haka. Sannan ya yi umarnin a shigo da abinci,
suka kafa manyan shimfid'u aka shigo da
kabuka guda dubu d'aya da d'ari na jan
zinariya da azurfa da tagulla, wasu kabuka na
d'auke da dafaffun rak'uma ashirin, wasu
hamsin, wasu kuma na d'auke da tumaki
hamsin wasu d'ari. Bulukiya ya cika da mamaki
mai yawa. Suka wanke hannu gaba d'aya fada
aka shiga cin abinci har da Bulukiya. Suka ci
suka tumbatsa sannan aka kawar da kabuka
aka shigo da kayan marmari da ruwan sha.
Suka ci suka sha suka gode wa Allah
mad'aukakin Sarki sannan suka shiga zikiri da
salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu
mai tsira da amincin Allah su tabbata a gare
shi. Da Bulukiya ya ji suna ambaton sunan
Annabi Muhammadu sai ya yi mamaki mai
yawa ya ce da Sarki, "ina so na yi maka wata
'yar tambaya." Sarki ya ce, "yi tambayar ka ko
wace iri ce."
"Ya sarki, ku wacce irin halitta ce, menene
asalinku, ta yaya kuka san sunan Annabi
Muhammadu har kuke k'aunar sa?" Sarki
Saharu ya ce, "ka sani ya Bulukiya, Allah halicci
wuta bisa rufi bakwai, tsakanin kowane rufi da
wani rufin nisan tafiyar shekara dubu ce. Ya
ambaci rufi na farko da Jahannama domin
hukunta musulmi masu sab'o da suka mutu ba
su tuba ba. Rufi na biyu ya ambace shi da
Laza, an tanade ta domin kafirai. Rufi na uku
mai suna Jahimu domin a jefa Yajuju da Majuju
ne. Rufi na hud'u kuwa sunansa Sa'ir domin
Iblis da rundunarsa. Na biyar kuwa sunansa
Sak'ara an tanadi wannan domin masu wasa
da sallah. Na shida sunansa Hud'ama domin
yahudu da nasara, sai na bakwai kuwa Hawiya
an tanade shi domin munafukai. Wad'annan su
ne rufin da aka yi wa wuta." Bulukiya ya ce,
"kenan Jahannama ta fi kowacce sauk'in azaba
kasancewar ta a rufi na farko." Sarki Saharu ya
ce, "na'am domin ita ce mafi sauk'in azaba
duka, amma duk da haka a cikinta akwai
duwatsu dubu na wuta a ciki, a bisa kowanne
dutse akwai jeji dubu saba'in, a kowanne jeji
akwai birane dubu saba'in na azaba a cikin
kowanne birni akwai gidaje dubu saba'in na
azaba, a kowanne gida akwai, d'akuna dubu
saba'in, a kowanne d'aki akwai gado dubu
saba'in na wuta. A kowanne gado akwai dangin
azaba dubu saba'in. Amma ragowar rufin wutar
kuwa babu wanda ya san k'iyasin tsananin
azabar da ke ciki sai Allah." Yayin da Bulukiya
ya ji haka sai ya fad'i sumamme saboda tsoro,
yayin da ya farfad'o ya yi kuka mai yawa
sannan ya ce, "ya Sarki yaya halinmu zai
kasance?" Sarki ya ce, "kada ka ji tsoro, na sani
cewa duk wanda ke k'aunar Annabi
Muhammadu mai tsira da amincin Allah su
tabbata a gare shi to wuta ba za ta shafe shi
ba. Domin kuwa duk wanda ya kasance bisa
tafarkinsa to wuta gudunsa take. Game da mu
kuwa Allah ya halicce mu daga wuta, farkon
abin da Allah ya halitta da jahannama su ne
wasu jiki guda biyu ana kiransu Halitu da
Malitu. Shi Halitu an yi masa fasali kamar zaki,
wutsiyarsa kamar ta kunama. Tsawonsa ya kai
tafiyar shekara ashirin, an yi masa azzakari irin
na namiji. Malitu kuwa an yi masa siffar kura,
yana da wutsiya irin ta maciji, gabansa kamar
farjin mace. Sai Allah ya nufi wad'annan
wutsiyoyin su had'u su yi aure inda suka
hayayyafa daga macizai da kunamun cikin
wuta wad'anda Allah zai azabtar da wad'anda
aka jefa a ciki. A kullum suna k'ara yawa suna
rub'anya yawan su. Daga nan Allah ya umarci
wutsiyoyin Halitu da Malitu su sake aure a karo
na biyu, suka haifi 'ya'ya goma sha hud'u,
bakwai maza, bakwai mata. Su kuma suka yi
aure a junan su suka. Dukkansu suna biyayya
ga iyayensu sai guda d'aya da ya fand'are sai
ya zama tsutsa wadda ita ce asalin Iblis,
la'ananne. Iblis ya kasance daga makusantan
Allah yana bauta gare shi har ya zama an
d'auke masa sama ya zama cikin mala'iku
yana bauta tare da su. Iblis ya ci gaba da bautawa
Allah cikin mala'iku har ya zuwa lokacin da
Allah ya halicci Adamu, amincin Allah ya
tabbata a gare shi, sai ya yi umarnin mala'iku
su yi masa sujjada, Iblis ya k'i bin umarnin. Don
haka Allah ya kore shi daga sama Allah ya
la'ance shi. Shi Iblis yana da zuri'a wad'anda
su ne shaid'anu, amma ragowar mazaje shidan
nan da ba su fand'are su ne rundunar aljanu
nagari. Mu kuma muna daga zuri'arsu. To ka ji
Bulukiya wannan shi ne asalinmu." Bulukiya ya
yi mamaki mai yawa dangane da wannan
labari. Daga nan ya ce da Sarki, "ina rok'on ka
sa wani hadiminka ya d'auke ni zuwa garinmu."
Sarki ya ce, "mu ba mu da ikon aikata komi dai
da iznin Allah, amma idan kana da muradin
tafiya daga gare mu, to zan d'ora ka bisa wata
god'iyata na sa ta kai ka can iyakar mulkin
k'asata inda za ka sadu da wani Sarki mai suna
Barahiya. Idan ya ga god'iyar zai shaida ta, ya
karb'e ka sannan ya dawo mana da ita.
Wannan ne iyakar abin da za mu iya maka,
babu k'ari." Da Bulukiya ya ji haka sai ya yi
kuka sannan ya ce, "aikata hakan gare ni ya
Sarki."
Daga nan sarki Saharu ya d'ibiya shi akan
god'iya ya ce masa, "ka yi hankali kada ka
zungure ta ko ka yi mata kururuwa za ta kashe
ka. Kai dai ka zauna kurum a bayanta cikin
natsuwa za ta kai ka inda aka umarce ta."
Bulukiya ya ce, "na ji na d'auka." Ya hau ya
zauna, god'iya ta soma tafiya ta wuce da shi ta
gaban d’akuna zuwa inda ake girki da dafe -
dafe. A nan ya ga manyan tukwane an hura
wuta k'ark'ashinsu, kowace tukunya akwai
rak'uma hamsin a cikinta. Wasu rak'uman
kuma an rataye su wuta na ci a k'asan su suna
gasuwa a haka. A nan ya tsaya yana kallo cike
da mamaki har Sarki Saharu ya yi tsammanin
yunwa yake ji. Ya yi umarnin a k'unsa masa
rak'umi biyu gasassu. Aka sassara masa
naman aka cusa a kwacciyar god'iya sannan
ya yi bankwana da su ya yi gaba.
God'iya ta yi ta tafiya da shi har zuwa k'arshen
iyakar ikon sarki Saharu sai ta tsaya cif, shi
kuma ya sauka ya shiga karkad'e k'urar da ta
mak'ale a tufafinsa. Yana cikin haka sai ga
wasu jama'a sun zo gare su, suka shaida
god'iyar suka tafi da ita tare da shi zuwa ga
sarki Barahiya. Bulukiya ya gaishe da shi yana
mai yi masa sallama. Sarki ya amsa gaisuwar
da sallama, sannan ya zaunar da shi a kujerar
alfarma a kusa da shi kewaye da rundunar
jarumawansa da zab'ab'b'unsa da sarakunan
aljannu sun jeru hagu da dama. Bayan sun d'an
tattauana aka shigo da abinci suka ci suka
k'oshi suka tumbatsa suka gode wa Allah.
Sannan aka hallaro da kayan marmari suka
sha. Sarki Barahiya wanda fadarsa take tamkar
ta sarki Saharu ya ce da Bulukiya, "yaushe ka
baro sarki Saharu?" Bulukiya ya ce, "kwana biyu
da suka wuce." Sarki Barahiya ya ce, "ka kuwa
san nisan tafiyar da ka yi a wad'annan kwana
biyun?" Ya ce, "A'a."
"Ka sani kai ka yi tafiyar shekara biyar da wata
goma ne a wannan tsakanin."
Barahiya ya ce da Bulukiya,
"tafiyar nan da kake gani tamkar ta kwana biyu,
to tafiyar shekara biyar da wata goma ce ka yi.
Don ma god'iyar da ta d'auko ka ta razana da
kai ne, domin ta ga kai d'an Adama ne ta yi
nufin ta jefar da kai ka halaka, to amma nauyin
rak'uman nan biyu da aka d'aura mata ya sa ta
ji nauyi ba ta iya jefar da kai d'in ba." Bulukiya
ya gode wa Allah da ya tserar da shi sannan
Sarki ya ce da shi, "fad'a min labarinka da
sanadin zuwanka k'asashenmu." Bulukiya ya
zanta masa labarinsa gaba d'aya da yadda ya
zo har nan wurinsa. Sarki ya yi mamaki da jin
wannan labarin, ya zaunar da shi a wajensa har
wata biyu." A nan sarauniyar macizai ta tsahirta
da bai wa Hasib labarin Bulukiya. Hasib ya yi
mamaki mai yawa, sannan ya ce da ita. "Ni dai
ina rok'o cikin alfarmar ki da kyautatawarki ki
umarci wani daga sarakunanki ya kai ni bayan
k'asa na sadu da mutanena."
Ta ce, "kai Hasib Karimuddini idan ka fita wajen
iyalinka za ka shiga gidan wanka, idan ka k'are
wankan ni kuma hakan zai yi sanadin mutuwa
ta." Hasib ya shiga rantsuwar cewa ba zai sake
shiga gidan wanka ba har abada. Ya k'ara da
cewa, "idan wanka ya kama ni zan rik'a yi a
gidana." Sarauniya ta ce, "ai fa da za ka rantse
min sau d'ari ba zan yarda da kai ba, ku 'yan
Adam ba ku d'auki alk'awari a bakin komai ba.
Hatta babanku Adamu da ya yi alk'awari da
Allah wanda ya halicce shi daga tab'o ya rik'a
cud'a yumb'unsa safiya arba'in sannan ya
umarci mala'iku su yi masa sujjada, amma
daga k'arshe sai da ya manta ya sab'a umarnin
da Allah ya yi masa."
Da ya ji haka sai ya yi shiru, ya yi ta kuka, bai
daina kuka ba har kwana goma sannan ya
dangana. Ya ce da sarauniyar macizai, "to ba ni
labarin k'arashen hik'ayar Bulukiya." Sarauniya
ta ce, "ka sani ya Hasib bayan Bulukiya ya
kwashe watan biyu a wajen sarki Barahiya sai
ya yi masa bankwana ya tafi cikin daji dare da
rana har ya sadu da wani babban tsauni mai
girma. Ya kama ya hau. A nan ya samu wani
mutum zaune a saman yana tasbihi da hailala
da salati ga Annabi Muhammadu tsira da
amincin Allah su tabbata a gare shi. Ya yi masa
sallama ya amsa masa, sannan ya tambaye shi
daga inda ya fito da inda ya nufa. Bulukiya ya
fad'a masa sannan ya ba shi labarinsa daga
farko har k'arshe. Mutumin ya yi mamaki mai
yawa, sannan ya yi addu'a da fatar alheri suka
yi bankwana.
Ya ci gaba da tafiya ba dare ba rana har ya
sadu da wani kwari mai girma, ya gangara zuwa
cikinsa inda ya ga k'orammu bakwai masu
girma da bishiyoyi gewaye da wajen. Ya tsaya
yana kallon kyawon wajen yana k'ayatar da shi.
Daga wata kusurwa kuma ya hangi wata
babbar bishiya k'ark'ashinta wasu halittu ne
guda hud'u. Ya sake matsawa kusa domin ya
k'are musu kallo, ya ga na farko yana kama da
mutane, na biyu yana kama da dabbobi na uku
yana kama da tsuntsaye na hud'u kuma yana
kama da bajimi. Ya ji suna tasbihi suna
tsarkake sunan Allah Mad'aukakin Sarki suna
salati ga fiyayyen halitta. Bulukiya ya yi mamaki
sannan ya yi gaba yana tafiya har ya sadu wani
babban dutse a samansa wani mutum na ta
sallah. Ya isa gare shi ya yi masa sallama.
Mutumin ya amsa masa sannan ya nemi sanin
daga inda yake da inda ya nufa, ya fad'a masa.
Sannan Bulukiya ya tambaye shi sunan wurin
da abin da yake yi a nan. Ya amsa masa ya ce,
"wannan shi ne Jabala K'af babban dutsen da
ya kewaye duniya duka. Ni kuma Allah ya
sallad'a min dukkan duniya da abin da ke
cikinta a tafin hannuna. Idan Allah ya so wuri
da azaba na daga girgizar k'asa ko yunwa ko
fari ko yak'i ko ni'ima yakan umarce ni da na
aiwatar gwargwadon yadda ya so ba tare da na
bar wurin nan da nake ba.

ZANCI GABA INSHA ALLAH08 HIKAYAR SARAUNIYAR MACIZAI DA HASIB KARIMUDDINI

waliyin nan ya fad'a wa
Bulukiya game da zaman da yake a dutsen Kaf.
Bulukiya ya ce, "yalla bayan dutsen nan akwai
wani abu da Allah ya halitta?"
"Allah ya halicci wata duniya wadda take fara
tamkar azurfa, babu wanda ya san girmanta sai
shi. Tana cike da mala'iku wad'anda abincinsu
da abinshansu zikiri da tasbihi gare shi. Duk
daren Juma'a suna tattaruwa a kan dutsen nan
suna bauta wa Allah. Idan gari ya waye sai su
nemi gafara ga al'ummar fiyayyen halitta mai
tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da
kuma dukkan mai wankan Juma'a. Aikinsu
kenan har ya zuwa ranar alk'iyama."
Bulukiya ya ce, "yalla bayan wannan dutse
akwai wani babban dutsen a gabansa?" Waliyi
ya amsa ya ce, "kimanin tafiyar shekara d'ari
biyar akwai wani dutse na rab'a da k'ank'ara
ne. Shi yake hana zafin jahannama shigo wa
duniya, ba domin shi ba da ta k'one duniya
duka. Sannan a bayan wannan dutse akwai
duniyoyi guda arba'in kowace duniya ta ninka
duniyarmu sau arba'in. A cikinsu gaba d'aya
mala'iku ne ke tasbihi. Su kuwa sun kasance
kowace da irin launinta, wata ta zinariya, wata
ta azurfa, wata ta tagulla da yak'utu. Mala'ikun
da ke ciki babu wanda ya san adadinsu sai
Allah, ba su san Hauwa'u ba ballantana Adamu,
ba su san dare, balle rana. Aikinsu kawai tasbihi
da tahmidi. Ka sani ya Bulukiya yadda sama
take bakwai haka k'asa take bakwai. Allah ya
halicci wani mala'ika mai girman halitta, babu
wanda ya san girmansa sai wanda ya halicce
shi. To shi yake d'auke da dukkan k'assan. A
k'asa da shi kuma wani babban dutse ne, a
k'asan dutsen bajimin sa ne ke d'auke da shi. A
k'asan sa d'in kuma wani babban kifi ne, a
k'asan kifin wani makeken teku ne. Allah
mad'aukakin sarki ya tab'a fad'a wa Annabi
Isa, amincin Allah ya tabbata a gare shi game
da wannan kifi. Sai Annabi Isa ya ce, "ya
ubangiji ka nuna min wannan kifin na gan shi.
Sai Allah ya umarci mala'ika da ya kai Isa zuwa
inda kifin ya ke. Ya ce da shi, "duba izuwa ga
kifin ya Isa." Isa ya duba bai ga komai ba sai
wani haske da ya wuce ta gabansa tamkar
walk'iya. Ganin hasken sai Isa ya fad'i
sumamme. Yayin da ya farfad'o sai Ubangiji ya
ce masa, "ya Isa ka ga kifin?" Isa ya ce, "da
girman buwayarka da d'aukakar ni ban ga kifin
ba, amma na ga wani haske ya wuce ta gabana
gwargwadon nisan tafiyar kwana uku." Ubangiji
ya ce, "wannan hasken da ka gani gwargwadon
tafiyar kwana uku kan kifin ne ya wuce ta
gabanka. Ka sani a kullum ina halittar kamar
wannan guda arba'in."
Bulukiya ya yi mamaki gaya da jin wannan
labarin, sannan ya ce, "yalla ko a bayan tekun
nan da kifin ke ciki akwai wani abu da Allah ya
halitta?"
"A bayan tekun Allah ya halicci iska mai yawa, a
k'asan iskar akwai wuta, a k'asan wutar wata
macijiya ce mai girman halitta ana kiranta
Falaki, ita ta kasance ba domin tsoron Allah ba
za ta iya lank'wame duniya da abin da ke
cikinta da dukkan abubuwan da ke bisanta na
daga mala'ika da sa da kifi da ruwa da wuta
duka, cikin abin da bai fi k'iftawar ido ba.
, Waliyyi ya ci gaba da ba
Bulukiya labari ya ce, "ba don da wannan
macijiya take jin tsoron Ubangiji Mai Girma da
d’aukaka ba, da tuni ta had’iye dukan abin da
ke bayanta na iska da wuta da Mala'ikan da ke
tare da su. Ba tare da ta ji kome ba a cikin
cikinta. Lokacin da Allah ya halicci wannan
macijiya sai ya umurce ta da kudurarsa, "bude
bakinki zan yi ajiya a cikinsa." Macijiya ta
amsa, "na ji na yarda, ya Ubangijina." Sai ta
bude bakinta. Allah Madaukin Sarki ya saka
wuta a cikin bakin macijiyar ya ce, "ajiye mini
wannan har zuwa ranar tashin kiyama."
Idan ranar ta zo, Allah zai aika Mala'iku da
sarkoki, ya umurce su su kawo masa wutar a
daure. Sai su zo da ita a gabansa daure cikin
sarkoki tana toroko, tana tirjiya, tana neman
abin da za ta lasa. Idan aka tara mutane sai
Allah ya umurci wuta da ta bude kofofinta. Idan
kofofin sun bude za su rika fitar da wadansu irin
tartsatsi na wuta, girman kowane tartsatsi ya fi
duk wani babban tsauni da ke cikin duniya."
Yayin da Bulukiya ya ji zancen Waliyyi sai ya
fashe da kuka don tsananin tsoro. Ya yi kuka
kuka mai tsananin, ya wuce gaba yana zubar
da hawaye ya nufi Yamma. Bayan ya yi tafiya
mai tsawo sai ya hangi wadansu halittu guda
biyu, manya-manya kowanensu ya fi giwa
girma, suna zaune a gaban wata kofa da take
rufe, suna tsaron ta. Yayin da ya yi kusa ga
wadannan halittu sai ya ga daya na da siffar
zaki, daya kuma siffarsa irin ta bajimin sa ce.
Ya yi sallama gare su, suka mayar masa da
sallama. Suka tambayi labarinsa da inda yake
nufin zuwa.
Bulukiya ya ce, "Ni dan Adamu ne, na fito
yawon neman shugabanmu Annabi
Muhammadu, mai tsira da amincin Allah, hanya
ta biyo da ni ta wannan tsibiri." Sa'annan ya
tambaye su labarinsu da kuma dalilin zaman su
a gindin wannan kofa kublalliya.
Suka amsa masa, "mun kasance masu tsaron
wannan kofa tun lokacin da aka halicce ta.
Bayan wannan kuma ba mu da wani aiki sai na
zikirin Allah da yi wa Annabi Muhammadu
salati. A haka za mu dawwama har zuwa ranar
tashin kiyama."
Bulukiya ya yi mamaki, ya tambaye su menene
a cikin kofar? Suka amsa masa da cewa, "ba
mu san abin da ke cikin ta ba."
Ya ce, "na gama ku da Allah ku bude mini ita in
shiga domin ganin abin da ke ciki."
Suka ce, "ba mu da ikon bude maka ita. Duk
duniya babu mai iya bude ta sai fa Ubangijin da
ya halicce ta."
Da Bulukiya ya ji haka sai ya daga hannayensa
sama yana addu'a, "ya Ubangiji, ka bude mini
wannan kofa in ga abin da ke cikinta." Allah
kuwa ya karbi rokonsa, ya umurci kofa ta bude,
nan take sai ta bude a gabansa. Bulukiya ya
shiga cikinta, ta koma ta rufe kamar yadda take
da farko.
Bulukiya ya yi duba a gabansa sai ya ga wani
babban teku yana gudana, rabin ruwansa na
gishiri rabi kuma mai dadi. A kowane gefe na
tekun a kawai manyan duwatsu na jan yakutu.
Ga kuma wasu irin halittu ko'ina suna ta
ambaton sunan Ubangiji tare da yi wa Annabi
Muhammadu salati. Bulukiya ya tafi gare su ya
yi musu sallama. Bayan sun amsa masa
sallamarsa, ya tambaye su labarin wannan teku
da duwatsunsa.
Suka ce masa, "wannan teku da kake gani ya
kasance asalin dukkan ruwan da ke bayan
kasa. Ruwan gishiri ya tafi zuwa ga tekunan da
ke bayan kasa. Ruwa mai dadi kuma ya tafi ga
gulabe da koramu da tafukka. Haka wannan
teku za ta dawwama cikin kudurar Ubangiji,
buwayi gagara misali, har zuwa ranar tashin
kiyama. Duwatsun nan suke tare ruwan idan ya
yi yawa." Su kuma suka tambaye shi labarinsa
da inda ya nufa.
Ya kwashe labarinsa duka ya gaya musu, ya
tambaye su tafarkin da zai bi, suka ce masa ya
ketare tekun da ke gabansa. Ya shafa ruwan
ciyawar nan da ke tare da shi ga tafin
kafafunsa, ya yi sallama da su, ya taka ruwan
teku ya ci gaba da tafiya. Bayan ya yi tafiyar
kwanaki da yawa a bisa teku rannan sai ya
hadu da wani kyakkyawan saurayi yana taka
ruwa yana tafiya, kamar yadda shi ma yake
takawa. Da suka hadu da juna suka gaisa,
amma babu wanda ya tsaya jin labarin dan
uwansa sai kowa ya kama gabansa.
Bayan Bulukiya ya rabu da saurayin nan sai ya
hangi wasu halittu guda hudu manya-manya,
kowane daya ya fi giwa girma, daga nesa, sun
tinkaro inda yake suna tafiya kamar walkiya. Da
suka zo kusa gare shi sai suka tsaya. Ya yi
gaisuwa gare su, sa'annan ya ce, "ina gama ku
da Allah Mai Girma da daukaka, ku gaya mini
labarinku, ina kuka nufa cikin hanzari haka?
Suka ce masa mu bayin Ubangiji ne, Allah ya
umurce mu da mu tafi zuwa ga Gabas domin
kamo wani babban maciji wanda ya rushe
birane ya darkake mutanen da ke cikinsu. Allah
ya umurce mu da mu kashe wannan majici
domin mutane su huta da zaluncinsa." Bulukiya
ya yi mamaki da irin girman siffarsu, ya ci gaba
da tafiya ba dare ba rana har ya iso ga wani
tsibiri. Ya shiga tsibirin yana yawo a cikinsa.
Bulukiya ya shiga cikin tsibiri yana yawo, sai ya tarar da wani saurayi
kyakkyawa, fuskarsa tana sheki, hawaye na
tarara daga idanunsa. Yana

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment