Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

rawa sai ya ji
zuciyarsa ta yi fari, wani lokacin ma har yi musu tafi
yake. Da zarar ya yi tafin sau daya sai ka ji gaba dayan
jama'ar da ke fadar ma sun yi koyi da shi.
Ana cikin wannan nishadinc aka ga wani. Bardc
daga cikin Dakarun da ke gadin gidan sarauta ya ratso
ta tsakiyar 'yan matan da ke rawa da sauri ya iso gaban
Sarki Ishmar.
Da zuwansa sai ya zubc a kasa ya kwashi
gaisuwa sannan ya budi bakı da nufin ya yi bayani, sai
Sarki Ishmar ya yi masa nuni da cewa ya yi shiru.
Cikin farin ciki ya mike tsaye sannan ya dubi
wannan Barde da ke tsugune a gabansa, ya ce masa,
"Ma za ka kona can bakin kofar gidan nan ka shaidawa masu gadi cewa su budewa bakona Yarima
Huraisu kofa ya shigo da sauri. Kuma ka yi musu
albishir da cewa ina sane da zuwansa, ina yi masa
barka da zuwa."
Koda jin wannan umarni sai Barden ya mike
zumbur! Ya juya ya fice daga fadar. A sannán ne 'yar
matan da ke rawa suka cigaba da rawarsu, sauran
fadawa da jana'ar gari kuwa sai suka cika da tsananin
mamaki bisa jin cewar Sarki yana marhabin da dan
Sarki Salmar babban makiyinsa a rayuwa.
Maimakon Sarki Ishmar ya koma kan karagar
mulkinsa ya zauna, sai ya daga hannunsa na đama
sama, ta ke masu kida suka daina, masu rawa suka
kame, fadar tayi tsit! Tamkar babu nmai rai a cikinta
Sarki Ishmar ya kada tafin hannunsa, kawai sai
Makadan nan da 'yan rawar nan suka juya suka fice
daga cikin fadar.
Sarki Ishmar ya sake tafa hannunsa, sai ga
wadansu kuyangi su tamanin sun fito daga can cikin
gidan sarautar sun caba ado na gani na fada. Kuma
kowacce daga cikinsu tana dauke da karamin Kwando
wanda aka cika da fure mai ruwan dorawaa. Arba'in
daga cikin kuyangun sun jeru a layi tun daga bakin
kofar shigowa fadar har izuwa daf da karagar Sarkin
hannun dama. ragowar arba'in din su ma suka jeru
6angaren hannun hagu.
Tsakiyar fadar ta zama wajen babu kowa kuma
ba a hango kowa face Sarki shi kadai tak! da karagar ta mulki ya tsaya cak! Yana kallon kofar shigowa,
yana ta murmushi.
A dai dai wannan lokacin ne aka ga Yarima
Huraisu tarc da yaransa bivu Busara da Sadauki
Rauhaz sun shigo cikin fadar.
Huraisu ne akan gaba. Busara da Rauhaz na take
masa baya, dukkanninsu a cikin gagarumar shigar yaki
suke.
Koda suka sawo kafafunsu cikin fadar, suka fara
tafiya, sai wadannan kuyangi suka rinka debo wannan
fure suna watsa musu a jikinsu yana ta zubewa kasa.
Ya yin da kamshin furen ya doki hancin su
Huraisu sai suka cika da farin ciki, domin alamace ta
cewar ana nurna da zuwansu.
Koda Sarki Ishmar ya hango tahowar Yarima
Huraisu sai ya kasa jiran karasowarsa inda yake ya
taho gareshi da sauri fuskarsa cike da annuri kamar
wanda ya ga dan uwansa na jini wanda suka dade ba
su hadu ba.
Sarki Ishmar ya bude hannayensa biyu ya tari
Huraisu shima sai ya bude nasa hannayen, ai kuwa
suna haduwa suka rungume juna. Saboda murna har
sai da Sarki Ishmar ya sumbaci gosbhin Huraisu ya ce,
"Lale marhaban da haske mai yaye duhun bakin cikin
Zuciya,"
Huraisu ya janye jikinsa daga cikin na Sarki
Ishmar suka fuskanci juna ya ce,"Ya ya aka yi na
zamo haske mai yaye duhun bakin cikin zuciya?
Sarki Ishmar ya ce, "Ba komai bane ya sa na yi
maka kirari da wannan suna ba face kaine mutumin da
zai cika mini burin zuciyata burin da ya addabi
iyaycna da kakannina."
Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya kama
hannun Huraisu ya ja shi suka nausa cikin gidansa
sarautar. Har Busaru da sadauki Rauhaz sun yunkura
za su bisu a baya, sai Dakarun Sarki Ishmar suka sha
gabansu wani daga cikinsu ya ce, "Ai ku iyakarku ke
nan."
Kamar Sarki Ishmar ya
bayansa sai ya waigo ya dubi
Busaru ya ce da shi, "Akai su
san abinda ke faruwa a
Badakaren da ya tare su
Busaru na su masaukin".
Nan take Badakaren ya yiwa su Busaru jagora
suka shige cikin wata kofa mai zurfi. Sarki Ishmar da
Huraisu ma suka shiga cikin wata kofar dabam suka
kulle. Faruwar hakan ke da wuya sai fadar ta fara
watsewa, kafin a jima ta zama wayam kowa ya kama
gabansa.
Lokacin da Sarki Ishmar ya kama hannun Yarima
Huraisu ya ja shi izuwa cikin gidan sarautar sai suka yi
ta tafiya tamkar gidan bashi da karshe, duk inda suka
wuce sai dai ka ga Dakarun tsaro suna rabc musu suna
basu hanya. Abinda ya daurcwa Huraisu kai shi. ne
yadda Sarki Ishmar ya saki jiki da shi kuma suke ta
hira a ya yin da suke tafiyar tamkar dama can,sun saba
da juna.
Cikin wani katon falo suka tsaya. Da shigarg
Huraisu ya ga babu komai a ciki facc wani katon
zagayayyen tebur wanda a kansa an jcra farantan
abinci iri-iri sama da kala dubu kuma a gaban
kowannc faranti akwai Kuyanga guda daya wacce ita
ce za ta zubawa mutum kalar wannan abinci idan yana
da bukata.
Madakin Gini
Duk da cewa Huraisu dan Sarki ne sai da ya
rinka hadiyar miyau domin kamshin abincin ma kawai
ya addabi hancinsa, so yake kawai su zauna su fara cin
abincin in ban da ma yana jin kansa da tun kafin ayi
masa tayi zai fara gusar da yunwarsa.
Kamar Sarki Ishmar ya san abinda ke ran
Huraisu, suna zama ya dubi kuyangin gaba daya su
dubu ya ce, "Kowacce ta zubo kalar a cikin falle biyu
ta kawo. Aka tara kalolin abinci a gaban su. Sarki
Lshmar ya dubi Yarima Huraisu ya ce, "Ya kai babban
bakona ai sai kayi sauri ka ci abincin nan domin mua
da aiyuka da yawa a gabanmu."
"Ko da jin wannan batu sai mamaki ya kama
Huraisu. domin shi a ganinsa bai ga wasu aiyuka da za
su yi ba facc tattauna maganganu.
Nan dai suka dukufa wajen cin abincin. Da farko
sai Huraisu ya tsaya yana ruwan ido, domin va rasa
kalar abincin da ya kamata ya ci. Duk wanda va kalla
sai ya ga cewa dole ne ya yi dadi. Kawai sai ya rinka
yin loma daya a cikin kowanne tamka yana
dandanawa ne.
Kafin ya ankara tuni ya koshi, kuma bai đancfana
koda kala arba'in ba. Bisa dole ya hakura ya sha nuwan
inibi sannan ya dauki tulun giya ya fara sha.
Koda Sarki Ishmar ya ga Huraisu na neman shan
giyar da yawa, sai yai sauri ya fisge kofin giyar da ke
hannunsa ya ajiye a gefe daya ya dubeshi ya kyal kyale
da dariya, ya ce, "Ya kai wannan dar Sarki, ina mai
shawartarka da ka rage shan giya, in ba haka ba kuwa,
wata rana za ta sa ka aikata abin da za ka yi ta
nadamarsa har izuwa karshen rayuwarka. Yanzu haka
fa kafin ku iso nan Kasata ka shanye ganga biya: ta
giya a cikin kwana ashirin da daya. Kuma a can
gidanka na dajin Hirzul, a kullum sai ka sanye tulu
uku na giya."
Sa'adda Sarki Ishmar yazo nan a zancensa, sai
Yarima Hraisu ya yi gyatsa, sarnan ya ce, "Ya kai
wannan Sarki mai daraja, ka y1 sani cewa giya tana
kankare damuwa da bakin cikin zuciya, shi ya sa ba
zan iya rage shanta ba a lokaci guda, sai dai a sannu.
Bakin cikin da ya addabi zuciyata kuwa.
komai ba ne face tsananin kiyayyar da ke tsak tia da
mahaifina da kama đan uwana, na rasa hvar da zan
bi na kar6o mulkin birnin Lairis daga hannunsu ya
Zamana cewa na shafe Su a doron kasa."
Lokacin da Yarima Haraisu yazo nan a Zncensa,
sai Sarki Ishmar ya bushe da mahaukaciyar dariya har
ia fadowa Rasa daga kan kujerar da ya ke zaune.

Nima saboda jin wannan dariya haka yasa zan dakata anan saikuma lokaci na gaba
Insha Allah

Fatan AlkhairiMungyarA Matsalar

ßµŠÅ Ä MµTµ
Littafi Na Daya (1)
Part C

Marubucin Littafin
Abdulaziz Sani M/Gini

Likes and comments
Domin Mu cigaba

Al amarin da va matukar baiwa Huraisu mamaki
ke nan. Ya mike da sauri ya taho gareshi da nufin ya
tashe shi tsaye, kawai sai ya ganshi tsulum! A kan
kujerarsa tamkar iska ce ta daukoshi ta mai da shi kan
kujerar. Shi kansa Haraisu ya san cewa wannan abu
aikin tsafi ne.
Nan take Sarki Ishmar ya murtuke fuskarsa ya
daina dariyar, sannan ya dubi Huraisu cikin tsananin
damuwa tamkar zai fashe da kuka, ya ce, "Ya kai
Huraisu, ka yi sani cewa lokaci ya yi da burinka zai
cika, amma anan gaba bayan wadansu shekaru da za
su z0, ni da kai zamu shiga cikin tsananin tashin
hankali wanda idan tun yanzu ba mu yi wa tufkar
hanci ba sai mun tozarta.
Ina son ka saurarcni da kyau da kunnen fahimta,
kuma ka kiyaye dukkan abubuwan da zan zaiyana
maka domin idan ka yi kuskure daya sai nun shiga
cikin fargabar da bana son mu shiga.
Da farko dai, na san ka sani cewa a halin yanzu
mahaifinka ya kwanta ciwo, kullum sai dai a kwantar a
tayar, baya iya yiwa kansa komai. Bisa bincike da na
yi na gano cewa abu nc mawuyaci nan gaba ya yi
shekara guda a duniya ba tare da ya mutu ba.
Tabbas wannan wata dama ce muka samu da
zamu iya tara mayaka masu tsananin yawan da zamu
iya cin birnin Lairis da yaki a cikin watannin kađan.
Ka sani cewa, a halin yanzu ma yawan mayakana
ne yasa Sarki Salmar da jama'arsa suka kasa
samun
nasarar yaRi a kaina. Koda yake, yakin da makayi a
shekarun baya ne sa'adda kai da yayanka Muraisu kuna
yara kanana bare kuma ayi yakin da ku, amma nayi
imani cewa ko a yanzu ne za ayi yakin da ku ba za ku
sami nasara ba akan jama'ata ba, musamman saboda na
san cewa kai ba za ka yake ni ba.
To yanzu fa Sarki Salmar ba zai iya yin yaki ba
sai dai Yarima Muraisu ya wakilceshi. Na sani cewa,
Sarki Salmar yafi Muraisu juriya, na ci, kwarewa da
sanin tuggun yaki kuma koda ya koyar da Muraisu duk
wadannan abubuwan Muraisu ba zai iya yin abin da ya
yi ba, domin kama da wane bata wane. Shima Salmar
ba zai yi irin jamurtakar da Kakanka ya yi ba.
Bisa wannan dalili ne na ke son daga yau ka fara
tanadin mayaka a can gidanka da ke daji, ya zamana
cewa kullum muna basu horon yaki har tsawon kamar
wata biyar, sannan sai mu yi gagarumin shirin yaki mu
tasamma bimin Lairis.
Tabbas idan har mu ka yi haka sai mun sami
nasarar kama birnin. Matakin farko da zamu lura da
shi, shi ne, dole ne mu hada karfi ni da kai mu yaki
đan uwanka Maraisu a lokaci guda. Wannan ita ce,
kadai hanyar da za abi a kai shi kas. Idan muka
kuskura dayan mu ya tareshi har aka fafata sama da
tsawon rabin sa'a sai ya sami nasara a kansa, Ina
tabbatar maka da cewa, ni da kai zamu iya kai Muraisu
kas idan har mun hada karfi. Da zarar mun kaishi kas kuwa, ni da kaina zan
tsaga kirjinsa na dauko sirrin da za'a iya shiga dajin
Kirzufa da shi. Ina so ka sani cewa duk fadin duniyar
nan babu wata wuka da za ta iya bude kirjin Huraisu
face wacce ake kira "Hirzul Subura".
Ita dai wannan wuka ta Hirzul Subura, a yanzu
haka tana nan acan birnin Darul Wasus, birnin da duk
duniya babu kamarsa a fagen sarrafa karafa iri-iri,
kuma 'anan ne makera na duniya kaf suka gama kure
basirarsu ta kera makaman yaki da sauran kayan alatu
na rayuwar yau da kullum.
Fiye da shekaru dubu kawo i yanzu ba a taba
kera Wuka mai kaifi ba tamkar Wukar Hirzul Subura,
babu abin da bata yankawa, walau karfe ko dutse,
kuma komai taurin abu ko kwarinsa, bayan ta yanka
shi ba za aga ta dakushe ba, kuma kaifinta ba zai ragu
ba. Idan akai yanka da ita sannan ne ma kaifinta ya ke
karuwa.
Wukar Hirzul Subura an bata mugun tsoro na
gaban kwatance domin an ajiye ta ne a tsakiyar fadar
birnin Darul Wasus, kuma an sakaleta a sama jikin
rufin gini. Ba mna mutum ba, komai hatsabibancin
aljani bai isa ya rabi inda takobin take ba, saboda
karfin sibirin tsafin a ke jikinta duk abinda ya yi
yunkurin taba wannan wuka take yake zama gawa.
Bays ga haka, a kullum Dakaru dubu dari tara ne
suke gadin wannan wuka dare da rana, kuma an kasa
Dakarun gida biyu masu aikin rana dabam, haka ma
masu aikin dare. Bisa binciken da na yi, mutum uku ne
kacal a cikin fadin duniyar nan za su iya zuwa birnin
Darul Wasus su iya dauko wannan wuka. Daga
mabaifinka sai fan uwanka Muraisu sai kusna kai
kanka."
Koda jin wannan batu sai Huraisu ya dubi Sarki
İshmar, cikin tsananin mamaki to mene ne dalilin da
yasa Sai mu uku kacal za mu 1ya dauko wannan
wuka?"
Sarki Ishmar yai ajiyar zuciya sannan ya ce,
"Ainihin wukar Hirzul Sabura wani mashahurin
mayakine ya kerata wanda ya kasance Rasurgumin
matsafi kuma shi ne, tushen zuri'ar dangin mahaifinku.
A yadda ya kera muku wukar babu wanda ya isa ya yi
amfani da ita face ya kasance jinin zuri'arku. Wani
abin mamaki shi ne, gaba dayan zuriar tasa ta kare
babu irinta a doron kasa face ku ukun nan kacal."
Yarima Huraisu ya yi shiru yana nazarin
al'amarina cikin zuciyarsa har izuwa wani dan lokaci
sannan ya dago kai ya dubı Sarki Ishmar ya ce, "Na ji
ka ce an baiwa wukar Hirzul Subura mugun tsarc ta
ya ya zan iya kavar da tsaron har na daukate?"h,
Ishinar ya yi munushi ya ce, "Ta hanyar hada karfi
da ni gami da kiyaye dokokin da zan shimfida mana.
Duk za ka san wadannan al'amura anan gaba kəfin
ranar zuwanmu birninku ta zo. Mataki Da farko da za
mu oi don cimma nasara b:sa wannan gagarimin aiki
da ke gabanmu shi ne, doic mu baiwa juna horon yaki
[ni da kai domin kowanncnmu ya
kowa domin na koyar da kai abinda baka sani ba,
kaima ka koyar da ni abinda ban sani ba. Ta haka ne
san iyakar jarumtakar
kadai zamu
larwatsa Dakarun da ke tsaron wu kar Hirzul Subura
Kuma mu sami nasarar a yakin da zamu je mu yi a
Rasarku.
iya hada karfi biyu wanda
Mataki na biyu shi ne, dole ne mu ci gaba da tara
nayaka wadanda ba za su gaza miliyan daya da rabi
ba, kuma mu basu horon yaki irin wanda
A kalla sai wadannan mayaka sun shafe
Suna karbar wannan horo sannan za su kware ainun su
Zama GUGUWAR ANNOBA mai shafe birni komai
girmansa da karfin tsaronsa. Mataki na uku wanda shi
ne na karshe kuma shi ne mafi hadari, dole ne mu
kama Yarima Muraisu da hannunmu ya yin da muke
yaki da su sannan mu kaishi kas mu tsaga kirjinsa mu
ciro wannan gashin sihiri da ke jikinsa sannan ne
burinka zai gama cika idan na sanya wannan gashin
sihirin a cikin kirjinka yadda za ka iya zuwa dajin
Kirzufa ka yi farauta a cikinsa kamar yadda
mahaifinka ya yi har ya sami daukaka a duniya fiye da
kowannc Sarki."
nuke da shi.
wata bakwai
Sa'adda Sarki Ishmar yazo nan a zancensa sai
hankalin Yarima Muraisu ya dugun
Muraisu ya. dugunzuma saboda
tunanin wasu al'amura guda biyar da suka fado masa a
rai. Abu na farko shi ne, yanzu mece ce ribar Sarki
Ishmar idan har ya taimaka mani na ci kasarmu da
yaki, kuma na sarni damat shiga dajin Kirzuts? A
bayaninsa bashi da wani buri wanda ya fi ya mallaki
dajin Kirzufa, Babu yadda za ayi ya iya nallakat đajin
Kirzufa face ya mallakí yashin sihirin mahaifina.
Waninan yana nufin ke nan ba lallai bane idan ya ciro
gashin sihirin a kirjin dan uwana ya mallaka mini ba.
Ashe kuwa akwai alamun cewa Sarkí ya
yaudarata, wato ya yí amfaní da ní don kawai ya biya
bukatarsa, idan kuwa haka ne dole ne ya dauki
tsattsauran matakí akan hakan,"
Huraisu na cikin wannan tunanin zuci ne shmar
ya dafa kafadarsa ya ce, "Wai shin tunanin ne kakec yi
ne haka ina ta nagana armma hankalínka ya tafi wani
wurí? Huraisu ya yí firgigit kamar wanda ya farka
daga barci sannan ya dubi Ishmar ya ce, "Ka yafarceni
ya kai wannan Sarki, ka yi sani cewa hankalina ne ya
dugunzuma bisa jin wadannan tsauraran matakai uku
da zamu bi don ganin mun címma burinmu, ni kam
guiwata ta fara yin sanyí, dornin ganí nake karmar ba
zai yiwu ba,"
Koda jin wannan batu saí Sarkí Ishmar ya bushe
da dariya sannan ya ce, "Ai idan har mun bi wadannan
matakai daí-daí tabbas bukata za ta biya. Yanzu sai ka
tashi mu tafi na kaika izuwa masaukinka domin ka
samí barci da isasshen hutu saboda gobe da sassafe zan
turo a tashcka domín mu je filin motsa jini mu jarraba
jarumtakar juna ni da kai".
Koda jin wannan batu sai Yarima Huraisu
dubi Sarki Ishmar ya yi masa murmushin mugunta
sannan ya ce a ransa, "Ya
zai hada jarumtakata da tasa kasance sa'an
mahaifina. Lallai kuwa Zan nuna masa cewa sabon
kashi da sabon jini ba dai-dai take da tsohon kashi ba
ma za ayi wannan dattijon
Ganin murmushin da Huraisu ya yi ne ya sa Sarki
Ishmar ya yi zargin irin abinda Huraisu ya aiyana a
ransa don haka sai shima va maida masa da mnartanin
murmushin kuma ya ce a ransà, "Lallai yaro, yaro ne,
domin bai san wuta ba sai va tabata da hannunsa.
Tabbas sai na nunawa Huraisu cewar ko Zaki ya mutu
gawarsa ta fi gaban wargi."
Gama aiyana hakan ke da wuya sai Sarki Ishmar
ya mike tsaye shima Huraisu sai ya mike tsayc suka
kama harnun juna suka ice dana cikin dakin cin
abincin, a sannan ne wadannan kuyangi guda dubu
suka kwashe farantan abincin da ke kan tebur din suka
fice a su zuciyoyinsu cike da takaicin an sa su sun dafa
abincin da mutum dubu za su iya ci su koshi, amma
gashi mutum biyu ne kacal suka taba dan kadan sai dai
su je su ci iya Cinsu ragowar kuwa su zuba a shara.
Kullum haka suke faman wannan aiki darc da rana,
sbaoda wadatar da tayi musu yawa a gidan Sarautar.
Lokacin da Sarki Ishmar da Yarima Huraisu suka
baro cikin dakin cin abincin suka ci gaba da tafiya a
cikin harabar gidan sai kwatsam! Suka hango wata: santaleliyar halitta abar kwatance daga necsa adan da
ta nufo yaresu, fuskarta cike da annuri tana
murmushi, wanda yasa tsigar jikin Yarima Huraisu ta
tashi gaba daya ya tsaya cak a waje daya kuma ya
Rame kamar gunki.
Tunda Yarima Huraisu yazo duniya bai taba
ganin tsaleliyar byaklyvwar budurwa ha
ha kamar
wannan. Kai ko a tarihi ko labaran duniya bai taba jin
labarin mace mai kyau kamar na ta ba.
Mace ce doguwa mai matsakaicin kaurin jiki,
Kirjinta a cike yake, cikinta a shafe, kuma
kugu mai fadi da matukar tudu daga Laya, grshin
kanta baki ne sidik yana ta kyalkyali da shcki kuma ya
zuba har kasan kwankwasonta. Idan tana tafiya sai ka
ga kanuar dukkan gabban jikiría karyewa za su yi,
domin ko ina motsawa yake. Fatar ¡ikinta fara ce sol
irin farin nan mai kyau wanda babu ratsin komai,
kuma tana sheki da taushi tamkar idan aka latse jini
zai fito.
Tun daga nesa kyakkyawar budurwa bude
hannayenta biyu ta rugo izuwa ga rkr ishmar ta rungumeshi cikin farin ciki. Sarki Ishtaar ya janye
jikinsa daga cikin na ta ya dubcta cikin damuwa ya ce,
"Mene ne ya hanaki zuwA dakin cin abinci yau? Tun
dazu ina tare da bakona a can har mun kammala cin
abincin mun fito".
Budurwar tayi murmushi ha kyawawan fararen
hakorarta suka baiyana a fili ta ce, "Ka gafarceni ya: kai dana uwana, ka yi sani cewa jiya da daddarc na
muka yi da kai wacce ta sa idanuna suka bushe, shi ya
sa na yi ta barci har na makara ban fito da wuri ba".
Sarki Ishmar "Ya ke
ya yi murmushi ya ce,
Husnaila rabin jikina, kin san cewa ba kya laifi a
wajena koda kuwa kin karva dukkan dokokin da na
kafe a garin nan, saboda haka ban ga dalilin da zai sa
ki nemi gafarata ba. Yanzu zan raka bakona izuwa
masaukinsa don haka ki je turakata ki zauna ki jirani
Zan dawo mu tattauna
muhimmanci."
wani al'amari mai
Cikin murna Husnaila ta juya ta nufi inda
bangarcn turakar Sarki Ishmar take, ko kallon Yarima
Huraisu ba ta yi ba, bare ma ta yi masa magana,
tamkar ma ba ta san da shi ba a tsaye a wajen.
Shi kuwa Huraisu tun sa'adda idanunsa suka yı
arba da ita ya rude, ya kidime kuma ya dimauce ainun
domin ji ya yi kamar an zare masa ransa gaba daya
don haka sai ya kame kamar gunki kuma ya kura ma ta
idanu ko kiftawa ba ya yi, har moa ya tafi duniyar
tunani inda ya tsinci kansa a cikin wani kcrarren gida
kuma akan wani luntsumemen gado shi da Gimbiya
Husnaila suna morewa Soyayya.
Yana cikin wannan tunani ne Sarki Ishmar ya
girgiza kafadunsa ya dawo cikin haiyacin sa, sannan ya
daka masa tsawa ya ce, "Koda wasa kada ka taba
tunanin za ka kusanci wannan yar uwa tawa, domin ba: irin sauran 'yan matan da kake yiwa fyade bane a can
Kasarku. Wannan kanwata ce uwa daya uba daya,
kuma ita ce kadai ta rage mini a duniya. Ina sonta fiye
da yadda nake son kaina, kuma na rantse da darajar
iyaycnmu zan iya karar da dukkan mutanen wannan
nahiyar tamu idan har aka taba lafiyarta ko
mutuncinta. Duk wata alaka da ke tsakanina da kai za
ta iya rushewa idan ka kuskura ka kusanceta. Abinda
nake so da kai shi nc, ka dauka cewa a mafarki kuka
hadu, mafarkin da har abada ba zai taba zama gaskiya
ba.
A karshe ina mai sanar da kai cewa kariwata
Gimbiya Husnaila ba za ta yi aure ba kuma har ta bar
duniya babu wani da namiji da ya isa ya santa 'ya
mace koda kuwa bana numfashi a doron kasa, domin
na cire ma ta sha'awar da namiji, kuma na tsareta da
dukkan karfin sihirina na tsafi. Kai in takaice maka
zan ce ko mutuwa tayi namijin kuda ma bai isa ya taba
jikinta ba bare bil'adama ko aljan".
Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya wuc
gaba ya ci gaba da tafiya abinsa ya bar Yarima Huraisu
a tsaye cikin tsananin mamakin wannan jawabi da ya
yi masa. A sannan ne ya gano dalilin da ya sa Gimbiya
Husnaila ta shareshi ya zamana cewa ko kallonsa bata
yi ba a sa'adda suka hadu.
Nan dai Sarki Ishmar ya kai Yarima Huraisu har
masaukinsa inda suka yi sallama ya juya ya tafi ya
barshi. Huraisu ya kunna kai izuwa cikin tafkeken: falon wanda Sarki Ishmar ya yi masa nuni a matsayin
masaukinsa.
Falo ne babba mai fadi da tsawo wanda ke
shimfide da koren kilishi mai taushi, ga kujeru manya
da kanana suma duka koraye. Kai hatta labulayen da
aka sa a jikin tagogi da kokofi duk koraye ne, abin dai
gwanin ban sha'awa.
Da shigar Yarima Huraisu cikin wannan falo sai
ya tsaya ya yi turus! Ba komai ne ya haddasa hakan ba
face ganin abokan, wato manyan yaransa guda biyu
Busaru da sadauki Rauhaz a kwance bisa wannan
kilishi ga abinci nan a gabansu iri-iri birjik da 'ya'yan
itatuwa sun ci sun bari. Sannan sai ya ga wadansu
kuyangi guda shida a tare da su suna yi masu tausa.
A can gcfe daya kuma wadansu kyawawan
kuyangi ne guda goma a zaune waje daya suna jiransa
domin su tayashi kwana. Kallo daya Yarima Huraisu
ya yiwa kuyangin ya ji ko kadan baya bukatar su
kusanceshi.
Cikin hanzari Busaru da Rauhaz suka mike tsaye
zumbur! Suka risina suka yi gaisuwa ga Yarima
Rubaisu suna wadannan kuyangi gaba dayansu sai
suka zube suka gaisheshi. Busaru ya yi gyaran murya
ya cc, "Ya shugabana ga kuyangi nan masn tayaka
barci suna jira, kuna akwai giya ganga-ganga guda a
cikin dakinka an tanada
Kafin Busaru ya gama rufe bakinsa sai Yarima
Huraisu ya tari numfashinsa ya ce, Bana bukatar
komai yanzu, zan shiga dakina na kwanta, kada kowa
ya dameni
Koda gama fadin haka sai Huraisu ya bude daki
ya shiga ya kwanta akan wrani kasaitaccen gado wanda
ke dauke da shimfida mai tudu da taushin gaske ya
kwanta. Kwanciyarsa ke da wuya sai ya daga kansa
sama ya kurawa rufin cakin ido. Nan take fuskar
Gimbiya Husnaila ta baiyana akan rufin dakin, yaji
wani farin ciki ya lullubeshi. Kawai kuma sai ya ga
hoton fuskar ta ta ya Bace. A dimauce ya mike zaune
daga kan gadon ya kama kalle-kalle a cikin dakin ko
zai sakc ganin fuskar Husnaila a jikin bango ko a kasa,

Nima kuma a dimauce Na tashi Na tuna cewa zanfita kasuwa sbd haka sai Anjima

Likes and comments
Zai bamu zummar cigabaaßµŠÅ Ä MµTµ
Littafi Na Daya (1)
Part D

Marubucin Littafin
Abdulaziz Sani M/Gini

Likes and comments
Domin Mu cigaba

Amma bai gani ba. Nan take ya gano cewa tsananin
begenta nc ya sa ya ga kamar tana yi masa gizo.
Al'amarin da ya matukar girgiza hankalinsa ke nan
domin shi a rayuwarsa bai taba yin soyayya ba kumna
bai laba jin yana son wata 'ya mace ba face da lalata,
amma sai gashi wannan karon yaji yana son ya mallaki
Gimbiya Husnailaa matsayin matar da zai aura".
Koda Huraisu ya luno da kashedin da Sarki
Ishmar ya yi masa akan Husnaila da irin maganganun
da ya shai ia masa sai hankalinsa ya dugunzuma ya
rasa abinda ke masa dadi. Shi kam yanzu ya san cewa
ba zai iya cire son Husnaila a zuciyarsa ba, kuma ba
karamin tashin yankali ne ya ce zai nemi soyayyarta
tunda ita ba ta ma san meye so ba, kuma ba ta taba yin
soyayya ba.
Huraisu ya ci pgaba da tunani cikin matukar
damuwa har izuwa lokaci mai tsawo, daga bisani sai
ya yanke hukuncin cewa ya yi hakuri har izuwa
lokacin da zai zama Sarkin birnin Lairus, tabbas a
sannan ne zai iya mallakar Gimbiya Husnaila ko da
tsiya-tsiya tunda a sannan ma ya mallaki gashin sihirin
da ke kirjin mahaifinsu, in kuwa ya mallaki wannan
gashin sihirin ya san cewa babubwani tsafi da zai yi
tasiri a kansa. Idan kuwa tsafi ba zai yi tasiri ba a
jikinsa lallai ya fi karfin Sarki Ishmar.
Koda Huraisu ya zo nan a tunaninsa sai ya cika
da farin ciki ya ji kamar ma ya mallaki Gimbiya
Husnaila ne.
Kashe gari da sassafe bayan su Yarima Huraisu
sun yi buda baki sai aka turo wani hadini ya yi

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

2 Comments On BUSA A MUTU Book 1
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

Aha

avatar
bilkisu-adam-yusuf

11 months ago

Reply

Littafin yayai dadi

Please Login or Register in order to submit comment