Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sai ta wucc kai tsayc izuwa
turakar Sarki Salmar. Da shigarta sai ta iske an
gyarawa Sarki kwanciya, wannan karon an sanya
bayansa bisa matashin kai an jinginashi da jikin gadon
shi ba a kwance ba kuma shi ba a zaunc ba.
A wannan lokaci akwai hadimai hudu a cikin
turakar, biyu maza, biyu ma ta.
Koda Sarki ya ga shigowar Kuyanga Sabirat sai
ya ce da wadannan hadimai su fita su basu wuri. Nan
take kuwa Hadiman suka fice suka turo kofar dakin ya
zamana cewa saura su biyu kacala cikin fakin.
Sarki Salmar ya daga hannunsa da kyar ya yafito
Sabirat yana mai yi ma ta nuni da ta zo ta zauna daf da
shi. Cikin hanzari taje ta zauna a gefen gadon da yake
kwance suka kuawa juna ido, sannan ya ce, "Ya ke
Sabirat bani labarin abinda ya faru tsakaninki da dana
iyakar gaskiya".
Ba tare da ta boye komai ba Sabirat ta zaiyane
masa komai. K.oda gama jin hakan sai Sarki
ajiyar zZuciya sannan ya dubi Sabirat cikin alamun
tausayawa ya ce, "Yarinya buki da rabo, inda ace baki
zuba masa banjua cikin vannan abincin ba, sai a cikin
ruwan inibi da sa'adda kica rungumeshi din nan ku ka
fadi kasa kika rinka shafar gashin kansa da tabbas sai
ya tara da ke, duk macen da dana ya fara tarawa da ita
sai ta sami juna biyu da shi. ldan kuwa haka ta faru sai
na 'yantaki kin aureshi, kn ga ke nan da tafiyar da zai
yi gobe an fasa yin ta, kin ga ke nan abin da za ki haifa
shi ne anan gaba zai gaji sarautar garin na. Tashi ki
tafi, amma ki sani cewa gobe kina daga cikin mutum
uku wadande za su yiwa Yarima rakiya izuwa taftya
Deman matar da zai aure.
Maganata ta karshe a gareki ita ce, idan kin rayu
nan gaba, ki zamo bai kula da ikana da za a haifa, ni
kuma ladan da zan biyaki da shi mai tsoka ne, amma
ba zai zo hannunki ba sai bayan jikana ya dawo nan
birnin ya karbi kujerarsa ta mulki".
Sa'adda Sarki Sainar ya zo nan a zancensa sai
Kuyanga Sabirat ta cika. da mamaki kuma ta kasa
fahimtar abinda ya ke nuii, ta ce a ranta, "To mene ne
zai sa jikan naka ya tafi wani wuri sannan kumna ya
sake dawowa ya karbi karagar tasa?"
Nan dai Sabirat ta mike tsam! Ta fice daga cikin
turakar Sarki zuciyarta cike da tsananin bakin ciki bisa
damar da ta subuce ma ta ta zama matar Yarirna
Muraisu.
Kashe gari da sassafe Yarima Muraisu ya yi
wanka ya kintsa. Yanafitowa daga wanka ya iske
abincin kalacinsa a aiive inda aka saba ajiye masa,
amma bai ga mai kawo abincin ba, wato Kuyanga
Sabirat. Har ya yi nufin ya kwala ma ta kira ta zo
domin ya tambayeta yadda aka yi ya yi barci a jiya da
daddare nan da nan cikin dakiku kadan, sai kuma ya
fasa.
Nan dai ya zauna ya ci abincinsa, da ya kammala
sai ya dauko damararsa ta yaki ya daura, ya kwashi
dukkan kayan farautarsa sannan ya fita domin yaje
turakar Sarki su yi sallama.
Lokacin da Yarima Muraisu ya shiga cikin
turakar Sarki sai ya iske boka Rufyan, Kuyanga
Sabirat da wani barde wai shi Kurzal zaune a gefe
daya. Al'amarin da ya matukar ba shi mamaki ke nan,
domin bai ga abinda suke yi ba a turakar Sarki a
wannan lokaci.
Shi dai Kurzal, wani kwararren masanin hanya
ne da daji, ko kunnensa ya kara bisa kasa yana iya
gane abinda ya wuce a kanta sama da tsawon sa'a
guda. Duk irin sawun da ya gani a kan kas, walau na
mutum, aljan ko dabba yana iya shaidashi ya yi bayani
a kansa. Idan ya kallo hanya yana iya fadin inda za ta
kai mutum, walau wajen da za a riski ruwa, tsauni ko
bishiyoyi ko duhuwa.
A zamanin da Sarki Salmar ke fita farauta daji
duk sa'adda zai fita tare da Kurzal yake fita. Idan kuwa
Kurzal bashi da lafiya sai dai shima ya fasa fita
farautar.

Kai tsaye Yarima Muraisu ya nufi gadon da Sarki
ke kwance. Da zuwa sai ya sumbaci goshin Sarki, a
lokacin ne yaji jikin Sarki ya dume da zafin zazza6i
gaba daya. Al'amarin da ya matukar daga hankalinsa
ke nan, ya zauna daf da shi ya rike hannunsa a lokacin
da suka kurawa juna ido, kowannensu sai kwalla ta
cika masa idanu.
Sarki Salmar ya budi baki ya ce, "Ya kai dana
kayi sani cewa yau ne babbar rana ta bakin ciki a
gareni, saboda abu ne mawuyaci mu sake jin muryar
Juna daga yau. Haka kuma, yau ne babbar rana ta farin
ciki a gareni, domin kana daf da taka babban matsayi
irin wanda na taka a rayuwata.
Wadannan mutane uku da ka gani yanzu tare da
mu su ne za su yi maka rakiya a cikin wannan tafiya da
za ka yi, wacce nake son ka je ka dawo a cikin
kwanaki arba'in cif-cif.
Hakika duk Su ukun Suna da matukar
muhimmanci da amfani, amma ba za ka san hakan ba
sai kun yi tafiyar."
Sarki ya juyo da fuskarsa ya dubi Boka Rufyan,
zal ya ce, "Ku yi mini
a dana bisa amana".
Je, "Mun yi alkawari za
Kuyanga Sabirat da Barde
alkawari cewa za ku
Cikin hadin baki su ukun.
mu yi iya kokarinmu wajen kare rayuwar Yarima daga
dukkan abin ki".
Koda jin haka sai Sarki ya yi guntun murmushi
sannan ya ce, "Shi ke nan, ku fita ku bani wuri zan
gana da dana, kuma ina son ku rufe marna kofa da
dukkan tagogin turakar ran".
Ba tare da gardamar komai be su Boka Ruf'an
suka cika wannan umarni. A sannan ne Sarki ya dubi
Muraisu ya ce, "Bude bakinka ya kai dana".
Ta ke Muraisu ya bi umami ya bude bakinsa,
shima Sarki Salmar sai ye bude nasa bakin, kawai sai
wani silin gashi guda daya tamkar na wuyan doki ya
fito daga cikin bakin Sarki ya shiga cikin bakin
Muraisu.
Faruwar hakan ke da wuya sai Muraisu vaji wanı
Iin gagarumin karfi ya shigeshi irin wanda bai taba jin
kamar sa ba a rayuwarsa. A sannan ne Sarki Salmar ya
turnuke da matsanaicin tari A dimauce Yarima
Muraisu ya yi saurin zuba ruwa a kofin zinarc ya
baiwa Sarki ya sha, sannan farin da yakc yi ya lafa.
Tsawon 'yan dakiku suka ci gaba da kallon juna
sannan Sarki Salmar ya yi ajiyar nunfa shi kamar
wanda ya farfado daga dogon suma, ya ce, "Ya kai
dana kayi sani cewa daga yanzu habu wani sihirin tsafi
da zai yi tasiri a jikinka, kuma babu wani daji wanda
ba za ka iya shigarsa ba. Babu wala jarumt:aka da ba za
ka iya yinta ba. Amma idan makiyanka guda biyu suka
hada karfi za su iya kaika kas su rabaka da wannan
sihiri da na baka a yanzu. A sannan ne za a ci birninmu
da yaki ayi masa ado da jini da gawarwaki.
Abinda za ka yi kawai kafin makiya su kai ka kas
shi ne, ka tabibalar da cewa ka tscrara da rayuwar matarka da wadansu daga cikin jama armu domin kada a shafemu a doron kasa mu zama Tarihii...

Nima Zan dakata anan
Sai kuma wani lokaci insha Allah
ßµŠÅ Ä MµTµ
Littafi Na Daya (1)
Part F.
Karshen Littafi Na (1)

Marubucin Littafin
Abdulaziz Sani M/Gini

matarka da wadansu daga cikin jama'armu domin kada
a shafemu a doron kasa inu zama tarihi.
Wannan shi ne kalamina na karshe a garcka.
Sauran bayani za ka įi a ɔakin Boka Rufyan. Ina mai yi
maka fatan sa'a da nasata bisa abinda za ka fita nema.
ldan ka dawo gida ka islc na mutu ka ziyarci kabarina
tare da matarka, itama ta sumbaci kabarin nawa ta
shatashi da hannunta, wannan shi ne kadai bukatata a
garcka"
Koda Sarki Salmar ya zo nan a jawabinsa sai
hawaye ya zub0 masa.. Nan take zuciyar Yarima
Muraisu ta karaya ya dora kansa akan kirjin Sarki ya
fashe da matsanaicin kuka. Sai da suka jima
kankamc da juna duk suna kuka sannan Sarki ya janye
jikinsa daga cikin na Muraisu, ya ce, "Tafi abinka ya
kai dana, daga yau kada ka sake yin kuka komai bakin
ciki ko wuya, sai dai zubar da hawaye. Idan za ka fita
yanzu daga cikin turakar nan kada ka waigo mu sake
ganin fuskar juna".
Koda gama fadin haka sai Sarki ya lumshe
idanunsa a lokacin da hawaye ke shatata bisa
kurmatunsa. Cikin matukar sanyin jiki Yarima Muraisu
ya mike tsaye ya taka sawayen sa ya nufi kofar fita
daga turakar. Kafin ya isa bakin kofar sai ya tsaya sau
uku ya yi kamar ya juyo ya yiwa Sarki kallon karshe,
amma sai ya kasa saboda biyayya ga furucin Sarki.
Tun Yarima Muraisu na yaro karami bai taba
ketare maganar Sarki ba, kuma ko a cikin wuta ya ce
ya shiga sai ya shiga.
A wannan lokaci ne Yarima Muraisu ya rinka
tunowa da duk abubuwan da suka faru tsakanin sa da
Sarki a baya tun sa'adda ya fara wayo kawo izuwa
girmansa. Kawai sai yaji ya kasa daurewa, bai san
sa'adda ya fashe da matsanaicin kuka ba ya yi sauri ya
fice daga cikin turakar.
Yana fita sai shima Sarki ya fashe da matsanaicin
kuka, domin ya san cewa shi ke nan har abada ba za su
sake ganin juna ba, domin Boka Rufyan ya gaya masa
cewa duk ranar da ya rabu da wannan gashin sihirin da
ke jikinsa ba zai Rara kwana arba'in ba a duniya, kuma
gashi wannan tafiya da Yarima Muraisu zai yi ba zai
dawo ba sai bayan kwana arba'in din.
Da fitowar Yarima Muraisu kofar turakar Sarki,
sai ya iske Boka Rufyan, Kuyanga Sabirat da Barde
Kurzal tsaye a jere suna jiransa.
Ko kallonsu bai yi ba sai ya wuce gaba ya mufi
can bakin kofar fada. Cikin sauri suka bishi a baya. Da
zuwansu kofar fadar sai suka iske an tanadar musu
dawakai guda uku, gami da guzuri. Nan take suka
kama dawakan suka hau, Muraisu ne a kan gaba,
sannan Kuyanga Sabirat a tsakiya, sai Boka Rufyan da
Barde Kurzal a baya.
Haka dai suka ci gaba da tafiya har suka fice
daga cikin birnin Lairus suka nausa cikin daji. Ba su
gushe ba suna wannan tafiyar har sai da rana ta take, a
sannan ne dawakansu suka fara sassarfa, kai da gani ka
san cewa suna bukatar su sha ruwa, kuma su huta.
Koda ganin haka sai Boka Rufyan ya dubi barde
Kurzal ya ce, "Wane irin nisa ne a gabanmu kafin mu
riski Rorama ko kogi?"
Koda jin wannan tambaya sai Kurzal ya yi
murmushi ya ce, "Ya kai abin dogaronmu ai bamu yi
nisa ba da barin gida ba fa, ca nake kowa a cikinmu
nan ya san a inda muke. Nan da tafiyar zango daya tal
zamu riski koramar Salzas".
Koda jin wannan batu sai kowa ya cika da murna,
saboda sanin cewa koramar Salzas wani wuri ne mai
ni'ima inda ruwa ke zubowa kasa daga saman wani
dogon dutsc, kuma akwai tarin 'ya'yan itatuwa
wadanda suka yi tsuro a wajen.
Shi dai wannan wuri ya yi kaurin suna domin ya
zama tamkar sansanin Fatake, inda sukan yada zango
su huta kafin su shiga birnin Lairus.
Wani lokacin ma sai Fatake sun kwana sun yini a
wajen suna gyara kayan kolinsu sanann su Rarasá cikin
birnin Lairus.
Kamar yadda masanin ya Kurzal ya yi bayani,
haka al'armari ya kasance, walo sai da suka kara tafiyar
Zango guda sannan suka iso daf da koramar Salzas.
Tun daga nesa kadan Kurzal ya daga hannu sama
yana mai yi musu nuni da su tsaya.
Nan take duk su ukun suka yi turjiya da
dawakansu suka tsaya cak.
Kurzal ya sauko daga kan dokinsa da sauri ya
dubi hanyar, sai ya ga sawaycn dawakai, kawai sai a
tsugunna ya dora kunnensa akan kasa, har iZuwa
tsawon dakiku goma sannan ya mike tsaye ya rike
kugu yai ajiyar zuciva ya dubi Yarima Muraisu ya ce,
"Ya shugabana wadansu mutane masu yawa sun zo
bakin koramar nan sun yada zango, kuma eun huta har
tsawon kamar sa'a guda, sannan suka tashi Suka ci
gaba da tafiya, kuma maimakon su bi hanyar da za ta
kaisu birninmu sai suka bi wata hanyar dabam wacce
babu inda za ta kaisu face cižkin muggan dazuzzuka
masu matukar hadari".
Koda jin wannan batu sai Yarima Muraisu ya
dubi Boka Rufyan ya ce, "Duba mana mu ga ko su
waye, kuma mu san daga ina suke da inda suka dosa"
Boka Rufyan ya ce, "An gama ya shugabana.
Amma zai fi kyau mu karasa bakin koramar tukunna
mu sauka mu sami nutsuwa".
Ba tare da gardamar kormai ba kuwa Yarima
Muraisu ya amince da wannan shawara suka karasa
bakin koramar suka yada zango.
Sai bayan dawakansu sun sha ruwa, suma sun
sha, kuma aka ci abinci sannan Boka Rufyan ya share
kasa ya rintsa idanunsa ya karanta wadansu dalasimai
na tsafi sannan ya tofa akan kasar, sai ga hoton cikin
birnin Hutaira ya baiyana akai, aka nuno cikin gidan
sarautar Sarki Ishmar. Sarkin yana tsaye tare da 'yar
uwarsa Gimbiya Husneila suna sallama zai yi tafiya,
duk su biyun suna kwalla.
Husnaila ta dubi Sarki Ishmar cikin matukar
damuwa ta ce, "Ya kai dan uwana kayi sani ccwa
bamu taba rabuwa ba facc idan za ka tafi yaki, kuma
ko yaki ka tafi baka wce sati biyu zuwa uku baka
dawo ba, amma yau gasni ka ce dani zamu rabu har
tsawon wata bakwai, ta ya va kake tsammanin cewa
zan iya jure kewar rashinlka a tare dani?"
Sarki lshmar yaji wannan tambaya sai hawayc ya
Zubo masa ya ce, "Ya ke 'yar uwata ki sani cewa bisa
dolc zan tafi na barki ba don ina so ba, kuma wannan
tafiya zan yi ta ne don cika babban burin rayuwata
wanda idan ya tabbata sai mun sami daula, đaukaka da
arziki irin wanda bamu taba samu ba. Na sani cewa za
ki cikin kewata matuka, amma akwai abinda zai kawar
miki da wannan damuwa. Na sani cewa rayuwarki
babu abinda kike so sama da yin rangadi a cikin daji
kina kallon kyawawan tsuatsaye da kyawawan namun
daji, saboda haka na shirya miki wannan rangadi. A
duk bayan wata guda za ki fita tare da Dakaru dubu
dari uku wadanda za su baki tsaro, amma duk sa'adda
kuka fita kada ku sake ku haura kwana goma baku
dawo gida ba.
Abu na biyu, akwai dajin Kirzufa wanda ba a
shigarsa, lallai ku nisanceshi. Abu na uku wanda shi ne
na karshc, kada ku kuskura ku bi hanyar da za ta kaiku
birnin Lairuf. Koda kun bi hanvar kuwa ya kasance
iyakarku ita ce koramar Salzas, daga nan sai ku juyo
ku bi wata hanyar dabam".
Sa'adda Sarki Ishmar ya zo nan a zancensa sau
Gimbiya Husnaila tayi ajiyar zuciya ta ce, "Ya kai dan
uwana shin yanzu kana ganin ccwa wadannan Dakaru
da za su yi mini rakiya ya yin da zan fita rangadi za su
iya karcni daga dukkan mugun al'amari?"
Sarki Ishmar ya yi murmushi sannan ya ce, "A1
koda ba za su iya kareki ba babu wani tsautsayi da zai
iya hawa kanki saboda na karc lafiyarki da dukkan
karfin sihirina"
Da jin haka sai murna ta kama Gimbiya Husnaila
ta rungume Sarki Ishmar ta sumbaci goshinsa, sannan
ta ce, "Ya kai dan uwana hakika yanzu hankalina ya
kwanta kuma na san cewa har watanni bakwai su cika
ba zan shiga tsananin damuwa ba tunda zan dinga fita
wannan rangadi. Amma abinda nake so da kai shi ne,
da zarar watanni bakwan sun cika ka gama shirinka to
kafin ka tafi yakin ka dawo gida ka daukeni mu tafi
tare".
Sarki Ishmar ya ce, "Ai wannan mai sauki ne, na
yi miki alkawari cewar lallai haka za a yi".
Nan takc Sarki Ishmar ya rungume Husnaila suka
yi bankwana sannan ya juya ya tafi.
A dai-dai nan ne Boka Rufyan ya goge kasar da
ke gabansa, hoton komai ya bace. Yana dago kai sai
ya ga ashe Yarima Muraisu, Barde Kurzal da Kuyanga
Sabirat sun kame kamar gumaka.
Ba komai ne ya haddasa musu hakan ba face
tsananin rudewa da dimaucewa da suka yi sakamakon
ganin kyawun Gimbiya Husnaila.
Ita kanta Kuyanga Sabirat da take mace sai da ta
rude matuka, domin tun da tazo duniya ba ta taba
ganin mace mai kyanta ba.
Ya yin da Boka Rufyan ya ga su Yarima sun
dimauce sai ya takarkare ya bushe da mahaukaciyar
dariya.
Al'amarin da ya janyo suka dawo cikin
haiyacinsu ke nan. Yarima Muraisu ya dubi boka Boka
Rufyan ya ce, "Yanzu dama akwai mace mai irin
wannan kyau a duniya? Ni kam yanzu na ga matar
aure".
Koda jin haka sai Boka Rufyan ya sake bushewa
da dariya a karo na biyu, sannan ya murtuke fuska
kamar an aiko masa da sakon mutuwa.
Ita kuwa Kuyanga Sabirat sai taji kishi ya
turnuketa kamar ta fashe da kuka.
Boka Rufyan ya duk arima Muraisu cikin
matukar damuwa ya ce," gabana kayi sani cewa
mallakar Gimbiya Husnailaercka ba karamin aiki ba
ne. Zan iya cewa dai-dai yake da tafiya neman Jaki
mai kaho, ko kuma ace SIYAN AJALI, tun gabannin
ajali ya zo.
Za ka iya mallakarta, amira za ka iya rasa
rayuwarka a ko karin maliakarta, sabod tsananin
Rarfin sihirin da ke iikinta wanda xi kaina ban san
makarinsa ba.
Da farko dai ina so ka sani ccwa Gimbiya
Husnaila bata ta6a vin sovavya ba, domin babu ni
da namiji da zai burgeta kornai
kyansa ko
jarumtakarsa.
Abu na biyu, an circ mata sha'awa irin wacce
ke tsakanin mace da namiii barc tayi sha'awar yin
aurc.
Duk wadannan abubuwa Sun faru
sakamakon sihirin da dan uwanta ya sanya ma ta a
Jikinta. In har kana son ka karya wannan sihiri da ke
jikinta dole nc sai ka je ka vaki Dakarun da ke tsaron
lafiyarta a yanzu su dubu dari uku. Ko ka tarwatsasu
ko kuma ka kashesu gaba dayansu sannan ka
daukcta ka shigar da ita cikin dajin Kirzufa ku yi
rayuwa ta tsawon kwana uku a cikin dajin, kuna ci
kuna sha daga dabbobin dajin da 'ya'yan itatuwansa.
To fa a sannan ne sihirin tsafin da ke jikinta zai
karyc, sai kuma ka san hanyar da za ka bi ka sami
soyayyarta har ta amince ta biyoka izuwa birnin
Lairus domin ayi bikin aurcnku.
Babban abu mai hadari a cikin wannan al'amari
guda biyu ne Abu na farko shi nc, yaki da
wadannan Dakarn guda dubu dari uku masu tsaron
lafiyar Gimbiya Husnaira ba karamin bala'i bane,
domin Dakaru ne na musamman wadanda aka siyesu
daga can birnin Romaniya.
A duniya kaf, babu wadansu mutane masu
girma da karfi kamarsu, sannan an tsumasu a cikin
tsafin da' babu wani kaifi ko tsini da zai yi tasiri a
jikinsu, kuma basa gajiya da yaki koda za a kwana
uku ana yakin da su. Duk wuya, duk gumu basa
gudu a filin daga.
Abu na biyu shi ne, tunda dajin Kirzufa ya
wanzu ba a taba samun tnahalukin da ya taba kwana
a cikinsa ba. Shi kansa mahaifinka da ya shiga dajin
sa'a uku kawai ya yi a cikinsa ya fito saboda bala'i
da masifar dabbobin da Ke cikin dajin. Shi kansa ya
lura cewa idan ya ce zai kwana a cikin dajin yana
farauta to zai iya shiga mugun hali ko kuma gaba
daya ma ya rasa rayuwarsa, shi yasa ya hakura ya yi
sa'o'i kadan a ciki ya fito.
Idan har ka iya yin wannan kwana uku a cikin
dajin Kirzufa tarc da Girabiya Husnaila kuma har ka
sami soyayyarta ku ka yi aure, tabbas sai kun haifi
da wanda ba a taba yin jarumi kamarsa ba a duniya
wajen tsananin Karfi da jarumtaka. Amma kuma
rayuwarsa a doron kasa za ta zama annoba ga
dukkan manyan Sarakunan duniya, matsafa da
manyan attajirai, domin za su rinka rasa 'ya'yayensu
akan kari, saboda haka za su bazama wajen farautar
rayuwarsa.
Dalilin da zai sa su rinka farautar rayuwarsa shi
nc, akwai wani narkekcn kahon tsafi a cikin dajin
Kirzufa wanda ake viwa lakabi da suna BUSA A
MUTU. Kullum sai wannan da da ku ka haifa ya
daga kahon ya dubi kudu ya busa shi sau uku.
Da zarar ya busashi kuwa 'ya'yan manyan
mutanc uku za su mutu a kasashc uku.
Shi dai wannan kaho idan ya busashi sai an ji
sautinsa a ko ina a cikin duniya.
Ba wani abu bane zai sa ya inka busa wannan
kaho ba sai domin yana son ya ta fita daga cikin
dajin Kirzùra ya koma can birnin Lairus domin ya
dauki fansar kisan gillar da aka yiwa jama'armu,
kuma ya karbi karagar mulki daga hannun dan
uwanka azzalumi Yarima Huraisu.
Ba zai sami damar fita daga dajin ba, inda anan
nc ya girma har sai ya busa kahon sau adadin yawan
dabbobin da ke cikin dajin Kirzufa. Har yau, har
gobe babu wani matsafi da ya iya gano yawan
dabbobin.
Amma dai bincike ya nuna cewa yawansu kaf
bai kai dubu daya ba.!"

Topah Aikin Aikineh

*SHIN YARIMA MURAISU ZAI IYA
TARWA TSA DAKARUN DA KE TSARON
GIMBIYA HUSNAIRA DOMIN YA DAUKETA YA SHIGA DAJIN KIRZUFA DA TTA DOMINv SIHIRIN
TSAFIN DA KE JIKINTA YA KARYE HAR TA
AMINCE DA SOYAYYARSA?

WANNE HALI SARKI SHMAR DA
YARIMA HURASU SUKE CIKI?

YAUSHE NE ZA SU GAMA DUKKAN
SHIRYE-SHIRYENSU DON SU IE BIRNIN
LAIRUS SU YẤKESHI HAR SU SAMI NASARAR
MALLAKAR GASHIN SIHIRINV DA KE JIKIN
YARIMA MURAISU?

*WADANNE IRIN HADARURRUKA SU
YARIMA MURAISU ZA SU RISKA A YA YIN
WANNAN TAFIYA TASU?

YAUSHE NE ZA SU HADU DA SU
GIMBIYA HUSNAILA DA DARUN U HAR A
FAFATA AZABABBEN GUMURZU?

YAUSHE ZAA HAIFI JARIRIN DA ZAI
ZAMO GUGUWAR ANNOBA GA AL'UMMAR
DUNIYA, WANDA ZAI RINKA BUSA KAHON
BUSA A MUTU?

Mu hadu a kashi na biyu, don jin ci gaban
wannan kayataccen, kasaitaccen labari.
Daga mai debe muku kewa a kullum da ko
yaushe.
ABDUL'AZIZ SANI M/GINI.
(King of Adventures Story)
.
Dafatan labari ya kayatar
Kowa ya ajiye mana hasashenshi...

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

2 Comments On BUSA A MUTU Book 1
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

Aha

avatar
bilkisu-adam-yusuf

11 months ago

Reply

Littafin yayai dadi

Please Login or Register in order to submit comment