Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu
jagora izuwa can filin motsa jiki.
Wani katon fili ne mai tsawo da fadin gaske
wanda aka kewayeshi da shingen karfe gaba dayansa,
kasan filin an zuba ya shi mai taushi.
Da isowar su Yarima Huraisu wannan fili sai
suka iske Sarki Ishmar shi kadai a tsakiyar filin a tsaye
ya yi gagarumar shigar yaki ta bakin sulke kuma ya
rataya zabgegiyar takobi a bayansa. Sarki Ishmar ya
dubi Yarima Huraisu ya ce, "Yau ne ranar da zamu
fara bin matakin farko don samun nasara bisa bukatar
da ke gabanmu. Ya kai Huraisu yanzu sai ka shigo
Cikin wannan fli domin mu jarraba jarumtakar
junanmu". Koda jin haka sai Huraisu ya yi murmushi ba tare
da ya ce komai
ba. Nan take ya cire alkyabbar da ke
ikinsa ya zama daga shi sai doguwar riga da wando,
sai kuma danarar da ya yi a kugun sa. Maimakon ya
hude kofar shiga cikin filin ya shiga sai kawai ya daka
wawan tsalle sama tamkar an cillashi, daga cikin baka
ya dira a cikin filin nesa kadan da inda Sarki Ishmar ke
tsaye. Nan fa suka fara kewaye juna suna kallon-kallo.
Busara da sadauki Rauhaz suka gyara tsayuwarsu daga
bayan filin domin su baiwa idanunsu abinci.
Bayan Huraisu da Ishmar sun zagaya jauna
kamar sau uku sai suka rugo da gudu izuwa kan juna.
Sai da ya rage bai fi taku uku ba su hadu, sai
kowannensu ya zare takobi, ai kuwa suna haduwa suka
kacame da azababben yaki.
Sai da suka shafe sa'a guda cur suna kaiwa
junansu sara da suka amma dayansu bai sami nasarar
koda yakusar jikin daya ba, kuma cikin tsananin zafin
nama, juriya da bajinta suke yakin.
Hakika sadaukantaka ta hadu da sadaukantaka,
haka ma naci ya hau da naci. Da kansu suka rabu
suka ja da baya, kowannesu ya kama haki kamar
zakaru.
Busara da sadauki Rauhaz kuwa basu san sa'adda
suka kama yi mnusu tafi ba, domin su kansu sun san an
yi jarumtakar da ta wuce saninsu.
Bayan yan dakiku kadan sai Sarki Ishmar va
dubi Yarima Huraisu ya yi murmushi ya ce, "Tabbas ka cika jarumi juriya. Yanzu
kuma zan sauya salon fada domin na nuna maka cewa
ni tsohon hannu ne kuma na fi ka kwarewa da Sanin
makamna tunda na kara da mabaifinka ma bai sami
nasara akaina ba. Duk sa'adda muka hadu sai dai mu yi
jarumi ma'abocin jarumtaka da
KARE JINI, BIRI JINI."
Koda jin haka sai shima Huraisu ya yi murmushi
sannan ya ce, "Tabbas na yarda ka fimi kwarevwa kuma
na yarda cewa jarumtakarka tafi tawa tunda har
kwanan gobe ni ban isa na kara da mahaifina ba, duk
da cewa tsufa ya kamashi, amma zan nuna mmaka ccwa
dole ne mahaifina ya fika iarumtaka da juriya, lallai
sa'adda kuke haduwa in dai za ku yi gaba da gaba har
tsawon sa'a
guda
Sa'adda Sarki Ishmar yaji wannan batu sai ransa ya
sai ya hallakaka. "
baci zuciyarsa ta kufulo, ya kasa cewa komai domin ya
san cewa abinda Huraisu ya fadi gaskiya ne. Kawai sai
ya sake rugawa izuwa kan Huraisu ya rufeshi da
SARA DA SUKA cikin sabon salon yaki.
Wannan karon dai tsalie-tsalle Ishmar ya kama yi
yana shawagi a saman Huraisu tamkar tsuntsu mai
fuka-fuki. Nan da nan kuwa Ishmar ya rikita Huraisu
ya zamana cewa baya iya inai da martani sai dai kare
hari.
Koda Ishmar ya ga ya sami wannan nasara sai ya
kara ZAGE DANTSE ya dada kuntatashi har ma ya
sami nasarar yankarsa akan kirji. Duk da cewa yankan
bai yi zurfi ba, amma sai da jini yai feshi. Koda Huraisu ya shafa kirjinsa ya ga jini kuma
cewa rigarsa ta yage sai ransa ya baci, zuciyarsa
kufulo, kawai sai ya ja d baya ya kama rigar tasa ya
ketata gida biyu ya yi wurgi da ita. Kawai sai ya ruke
takobinsa da hannu biyu sannan ya fuskanci Sarki
Ishmar ya yi masa inkiya da ya sake kawo masa hari.
Ai kuwa sai Ishmar ya ka bi tayin nasa ya rugo gareshi
da gudu. Maimakon ya tsaya jiransa sai shima ya ruga
kansa da gudu. Koda ya rage bai fi taku uku ba su
hadu sai kowannensu ya daka tsallc suka hadu a sarma.
Ishmar ya kaiwa Huraisu wawan sara a kafada ya goce
cikin zafin nana amma duk da haka sai da takobin ta
shafi jikinsa aka yi sa'a bata yankeshi ba, amma ta
sarce gasin kirjinsa tamkar zabira aka sa aka askeshi.
Shi kuwa Huraisu a cinya ya kaiwa Ishmar sara,
maimakon takobin ta nutse a cikin cinyar sai ta shafci
kadan daga cikin tsokar naman, jini yai tsartuwa. Tun
a sarnan Sarki Ishmar ya kwalla ihu sakanakon
tsananin zafi da zogin da yaji, amma yana durowa kasa
sai yai sauri ya cire rawaninsa ya dauure raunin don
tsaida jinin sannan ya sake afkawa Huraisu da dukkan
karfinsa da zafin namansa kai ka ce da mutum dubu
yake fada shi kadai.
Sai da suka shafe sa'a daya da rabi suna gumurzu
a wannan karon, gumurzu na tashin hankali wanda ya
firgita 'yan kallon nasu domin gani suke yi cewa lallai
a ko yaushe dayansu zai iya rasa rayuwarsa donin
dukkaninsu neman hallaka juna suke

Kamar hadin baki sai duk su biyun suka ja da
baya suka tsaya cak! ga barin yakar juna sannan kuma
sai suka bushe da dariya a lokaci guda, suka rungume
juna.
Sarki Ishmar ne ya fara janye jikinsa daga cikin
na Huraisu ya dubeshi ya ce, "Hakika yanzu na gamsu
cewa kai abokin tafiya nc, kuma albasa tayi halin
uwa, domin ka gado wani abu daga cikin jarumtakar
mahaifinka. Yanzu bani da wata fargaba akan
matakinmu na farko domin nà san cewa idan muka
hada KARFI DA KARFE ni da kai zamu iya kai
Yarima Muraisu kas. Abu na biyu da zamu yi yanzu
shi ne, mu tafi izuwa can gidanka domin mnu fara hada
rundunar mayakan da zamu tafi da su yaki can
kasarku.
A kalla wannan aiki zai daukemu tsawon wata
shida kafin mu kammalashi, domin ba zamu tafi
wannan yaki ba da Dakaru kasa da miliyan biyu, kuma
dole ne mu basu horon yaki na musamman irin wanda
zai sa zuciyarsu ta kekashe ga barin tsoron komai.
Tuni na aika da wasikar gayyata izuwa ga wadansu
manyan sarakuna a wannan nahiya tamu wadanda
suka kasance abokaina kuma aminaina na neman
gudunmawar Dakarun yaki a wajensu kuma sun
tabbatar min da cewa za su bani hadin kai dari bisa
dari. Yanzu gobe da sassafe zan sake aikawa da
wasiku ga wadannan Sarakuna na sanar da su cewa su
turo mini Dakarun izuwa can gidanka
mu samesu a can ko kuma su su samemu a can "
Sa'adda Sarki shmar ya zo nan a zancensa sai
Yarima Huraisu ya yi ajiyar zuciya ya ce, "To yanzu
vaushe ne kuma za mu je mu dauko wukar Hirzul
Subura."
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Ishmnar ya
bushe da dariya sannan ya ce, "Ni kuwa dadina da kai
ke nan ka cika hanzari a cikin al'amuranka. Kada ka
damu kafin mu gama baiwa Dakarunmu horon yaki za
mu je mu dauko wukar Hirzul Subura".
Koda gama fadin haka sai Sarki Ishmar ya yi
nuni da hannunsa na hagu izuwa ga raunin da ke
cinyarsa wanda bai taba wanzuwa ba. Al'amarin da ya
matukar baiwa Huraisu mamaki ke nan domin ya san
cewa aikin tsafi ne kawai wannan".
Koda Sarki Ishmar ya fahimci cewa Huraisu ya
yi mamakin abinda ya faru sai ya bushe da dariya
sannan ya sake nuna raunin da ke jikin Huraisu. Take
shima na sa raunin ya warke sumul. Kawai sai ya
kama hannunsa ya jashi suka fice daga cikin fillin
motsa jinin suka nufi cikin gidan sarautar. Busara da
sadauki Rauhaz suka take musu baya.
Wannan shi ne abinda va faru a birnin Hutaira
bayan Yarima Huraisu yaje ncmi hadin kan Sarki
Ishnar domin ya biya bukatarsa ta ganin ya mallaki
birnin Lairus.

A CAN birnin Lain:s kuwa, lokacin da Sarki
Salmar ya kamu da cutar ajali va kwanta
ciwo sai hankalin Yarima IHuraisu ya dugunzuma
ainun ya rasa abinda ke masa dadi a duniya har ta kai
cewa bashi da sukuni dare da rana, kuma baya iya cin
abinci sosai baya saraun isasshen barci, al'amarin da ya
janyo ya dinga ramewa ke nan tankar shima bashi da
lafiya.
Ba komai ne ya jefashi a cikin wannan mugun
hali ba face ganin yadda ciwo nai zai ya kama
mahaifin nasa a kankanin lokaci har ta kai cewa
bakinsa ya kulle baya iya yin magana. Idanunsa sun
rufe baya ganin komai ku.ma baya iya yin komai da
kansa sai dai ayi masa. Bara Yarima Muraisu ba,
gaba dayan jama'ar kasar Iarus birni da kauye sai da
hankalinsu ya dugunzumna ainun bisa jin halin da
Sarkinsu ya shiga saboda sun san cewa shi nc babban
katangarsu wacce ta hana makiya yi musu dirar
mikiya.
Tabbas duk. ranar da aka ce babu Sarki Salmar to
fa babu cikakkn tsaro a birnin duk da cewa an san
akwai halifansa, wato Yarima Muraisu saboda kowa
ya yarda da jarumtakar Sarki Saimar wacce tafi gaban
tunani kuma kowa ya san kwarewarsa a yaki da kuma
tsabar sa'arsa ta tsawon shckara da shekaru.
Kullum Yarima Muraisu na zaune a gaban gadon
Sarki Salmar yana kallonsa yana zub da hawaye domin a duniya babu mnutumin da ake shakka sama da Sarki
Salmar tunda kusan shire ya renesu tun suna yara shi
da Huaisu kamar yadda uwa ke rainon danta. Sabo da
tsananin Raunar da Sark Salmar ke yiwa Muraisu da
Huraisu hatta wanka da tsarkin kashi shi yake yi musu
da kansa tun suna jarirai har suka rirma suka iya yin
komai da kansu bai taba bari kuyangi da barori sun yi
musu ba.
Sai da Sarki Salmar ya kwana talatin da tara a
kan gado yana jinya ba. A daren
kwana na talatin da taran ne, Huraisu na zaune akan
kujera dab da gadon Sarki ya fara gyan-gyadin dole
bai sani ba sakamakon bashin barci da ya dauka na
tsawon kwana biyu, kawai sai yaji an dafa cinyarsa. A
firgice Muraisu ya farka daga barcin, sai ya ga ashe
Sarki ne ya dafashi har ma ya kura masa ido hawaye
na shatata bisa kumatunsa.
Saboda tsananin murna da mamaki sai Muraisu
ya yunkura da nufin ya rungume Sarki, armma sai Sarki
Salmar yz daga masa hannu yana mai yi masa nuni da
ya dakata.
Muraisu ya koma kan kujerarsa ya zauna ya ci
gaba da kallon Sarki a cikin nutsuwa domin ya ji
abinda zai fito daga bakinsa.
Sarki Salmar ya budi baki da kyr ya ce, "Ya kai
dana, kayi sani cewa wannan sauki da na samu ba
sauki bane na samun lafiya, tabbas sauki ne yazo mini
dormin mu yi bankwanan karshe. Tabbas tawa ta kare domin zan iya mutuwa a cikin kowacce sa'a ko dakika
mai zuwa nan gaba ko kuma a cikin yini ko kwana ko
wata. Wata kila ma shekara, bani da tabbaci dai.
Kafin na ce da kai komai yanzu ina son ka tashi
ka garzaya gidan boka Rafyan yanzu-yanzu ka ce da
shi ya zo ina son ganinsa."
Cikin tsananin damuwa Yarima Muraisu ya mike
tsaye jikinsa a sanyaye kamar zai fashe da kuka domin
gani yake kamar idan ya tafi gidan bo ka Rafyan kafin
ya dawo Sarki ya mutu.
Haka dai ya daure ya tafi. Cikin gudu Muraisu ya
isa gidan Boka Rufyan ya isar da sako. Nan da nan
kuwa suka juyo suka dawo gidan sarauta suka shiga
cikin turakar Sarki.
Koda Sarki Salmar ya yi arba da boka Rufyan sai
ya yunkura da kyar ya juyo da fuskarsa sosai ya
fuskancesu, su kuma sai suka yi sauri suka zauna a
gabansa suka fuskanceshi. Sarki Salmar ya kama
hannun boka Rufyan ya rikeshi gam a cikin nasa
sannan ya ce, "Ya kai amintaccen bokana gaya mini
iyakar gaskiya kamnar yadda ka shaida mini a baya
kimanin shekaru ashirin da biyar da suka gabata. Mene
ne zai faru bayan mutuwata anan birnin Lairus?"
Koda jin wannan umarni sai boka Rafyan yai
tsuru-tsuru yai shiru bai ce komai ba, ya dinga raba
idanu tsakanin Sarki da Yarima.
Koda ganin haka sai Yarima Muraisu ya dakawa
boka Rufyan tsawa ya ce"Saboda me za ka tsaya kana
Jinkiri bisa bin umarnin mahaifina, ko kuwa don ka ga
vana kwance nea cikin wannan hali?"
Sa'adda boka Rufyan yaji wannan tambaya sai
hawaye ya zubo masa sannan ya dubi Sarki cikin
matukar damuwa ya risina ya ce, "Ya shugabana shin
ka mantane cewa mun yi alkawarin cewa ko ni ko kai
dayanmu ba zai tona wannan sirri ba, saboda mc yanzu
ka sauya shawara?".
Koda jin wannar tambaya sai hawaye ya sake
zubowa Sarki Salmar ya cc, "Ai dole ne na sauya
shawara tunda bakin al kalami ya bushe ko mun
baiyana ko bamu baiyana ba sai wannan al'amari ya
faru, kuma ka sani cewa idan ba mu yiwa Y arima
bayani ba tun yanzu to fa asarar da za ayi ta rayuka da
dukiya sai ta wuce yadda duk ake zato. Na umarceka
da ka hanzarta yi masa bayanin komai tun kafin an
koma cikin mugun halin da na kasance n rashin' gani
da kasa yin magana".
Koda jin wannan batu sai boka Rufyan yai shiru
isawon 'yan dakiku bai ce komai ba. Dega can kuma
sai ya dubi Yarima Muraisu cikin nutsuwa ya ce, "Ya
kai gwarzon jarumi magajin ubansa, ka yi sani cewa
bayan rasuwar mahaifinka mummunan yaki zai 6arke
anan kasar wanda babu mai iya kare rayukan jama'a da
dukiyarmu. Tabbas sai an cimu da yaki, kuma ba wani
bane zai kawo wannan yakin ba face dan uwanka
Yarima Huraisu. A yanzu iaka Yarima Huraisu ya bar
nan kasar gaba daya, ya jevcan ya hada kai da
makiyanmu suna hada rundunar mayakaa ta mutane
masu yawan gaske wadanda
Za su yakemu.
Tabbas nan da wani lokaci burinsu zai cíka burinmu".
Koda boka Rufyan ya zo nan a zancensa sai
Yarima Muraisu
Ya tari nun:fashinsa ya cc,Tunda dai
Yanzu an san da haka me zai hana sarki yayi mini izini na debi dakaru masu yawa mu tafi har can sansanin su huraisu mu yakesu shida wadanda suka hada kai mu kawar da su?",

Caraf! sai Sarki Salmar ya ce, "Shin ka manta ne
cewa wannan abu da zai samcmu kaddara ce kuma
bamu isa mu kaucewa kadiara ba? Babu makawa sai
an cimu da yaki, lallai babu abin da za mu iya yi face
kawai mu yi kokari mu rage asarar da za ta samemu.
Ya kai Rufyan yanzu mcne re abin yi?"
Boka Rufyan yai shiru yana mai sunkui da kansa
kas tamkar mai daukar karatu ashe tunani da bincike
yake yi a cikin hallarar tsafir.sa. Tsawon lokaci bai ce
komai ba, can kuma sai ya dago kai ya dubi Sarki
Salmar ya ce, "a shugabana idan har muna son mu
rage asarar rayuka da ta dukiya da za ta biyo baya dole
ne Yarima Muraisu ya gaggauta yin aure a cikin
watannin da basu wuce biyu zuwa uku ba, kuma dole
ne matar da zai aura ta zamo daga cikin zuri'ar abokan
gabarmu. Lallai idan ya yi wannan aure zai sami
haihuwa da ita kafin zuwan ranar da warnan yaki zai
Zo kuma Allbarkacin dan da za su haifa ne ita da
dubunnan daruruwan mutane za su iya yin ayari guda
su yi gudun hijira su bar winnan kasa tamu. Suma ba
Zai yiyu ba dukkaninsu su tsira da rayuwarsu da
dukiyoyinsu ba face sun isa dajin Kirzufa."

Sa'adda Boka Rafyan yazo nan a zancensa Sal
Yarima Muraisu ya cika da tsananin mamaki ya
dubeshi cikin tsananin damuwa ya ce, "Yanzu ta yaya
zan auri 'yar abokan gabar mu a cikin wannan yanayi
da mahaifina ke ciki? A ina ma zan ga 'yar abokan
Gabar tamu har na aureta alhalin bani da lokacin da zan
tafi ko ina?"
Boka Rufyan ya tari numfashin Muraisu ya ce,
"Ai kuwa zema bai samcka ba dole ne ka mike ka yi
shiri ka bazama neman matar da za ka aura. Kuma
bincike ya nuna cewa ta hanyar farauta za ka hadu da
sirikarmu wacce za ta zamo uwar dan da zai gaji
sarautar kasar nan a nan gaba, wanda shi kadai ne zai
iya karbar mulkin da za a kwace daga hannunmu da
karfin tsiya.
Bincike ya dada tabbatar da cewa baka da
sasshen lokaci na zama a gida, ya zama wajibi ka
gaggauta shirin fita farauta a daji idan har muna son wannan bukata tamu ta biya

Sa'adda Boka Rufyan yazo nan a jawabinsa sai
hankalin Yarima Muraisu ya dugunzuma ainun fiye da
ko yaushe, saboda jin cewa dole ne ya yi shiru ya fita
farauta a wannan
wannan lokaci da Sarki ke tsakanin
MUTUWA DA RAYUWA. Nan take hawaye ya subutowa Muraisu ya
durkusa a gaban Sarki ya đora kansa akan cinyarsa.
Sarki Salmar ya đaga hannunsa na dama da kyar ya
dora akan Muraisu yana wasa da gashin kansa a
lokacin ne shima hawaye ya kubuce masa domin yana
Ji yana gani zai rabu da babban masoyinsa a duniya.
Hakika ko a mafarki Sarki Salmar bai taba
Tunanian cewa wannan rana za ta zo masa ba a rayuwa.
Shi kansa boka Rufyan saadda ya ga Sarki da dansa
suna zubar da hawaye sakamakon wannan rabuwa ta
dole da za su yi sai da ya kamu da tsananin tausayinsu,
domin ya san irin shakuwar da ke tsakaninsu ta fi
gaban kwatance.
Boka Rufyan ya mike tsaye sannan ya ce, "Ya
kai Yarima Muraisu, ka tashi ka je ka fara shirye
shiryen wannan tafiya da za ka yi gobe, kuma ka
tabbatar da cewa ka dawo gida a cikin kwanakin da
basu haura arba'in ba tare da matar da za ka aura."
Da jin haka sai Muraisu ya mike zumbur! ya dubi
boka Rufyan cikin rashin fahimta da damuwa ya ce,
"To wai shin yanzu wane daji zan je na yi farautar har
na hadu da wannan mace wadda zan aura, kuma ya za
a yi na san ita ce wadda zan aura din? Wai shin ma ta
ya ya za ta amince da ni har ta biyoni nan birnin mu zo
a daura mana aure?"
Koda jin wadannan tambayoyi sai boka Rufyan
ya ce, "Amsar wadannan
wannan tafiya da za ka yi. Amma a yanzu duk duniya babu wani boka da ya isa ya baka amsar komai bincikensa da matsayin a hallarar tsafi........

To NimA dai Bari Naje FarautAr Yarinyar da Zan aura Daga India Ko zata Amince Ta Biyoni Gida Nigeria hhhhhhh

Anan Zan Dakata Saikuma Wani lokaci
Insha AllahßµŠÅ Ä MµTµ
Littafi Na Daya (1)
Part E.

Marubucin Littafin
Abdulaziz Sani M/Gini

babu wani boka da ya isa ya baka amsar komai
binciken sa da matsayin sa a hallarar tsafi".
Koda gama fadin haka sai boka Rufyan ya juyo
sosai ya risina ga Sarki ya cc, "Na barka lafiya ya
shugabana. "
Nan take ya juya ya fice. Har Muraisu ya yi
yunkurin ya sake zama a gaban Sarki sai ya yi masa
nuni da cewar ya tashí yajc ya fara shiryc-shiryen
tafīya.
Cikin sanyin jiki Yarima Muraisu ya juya ya nufi
kofar fita. Har ya sa kafarsa guda wajen kofar sai ya
kira sunansa ya waigo suka dubi juna. Sarki ya yi masa
wani dan guntun murmushi, ya ce, "Kafin ka tafi a
goben ka zo mu yi sallama domin na baka
gudunmawata ta kariya, domin ba lallai bane ka dawo
ba ka riskeni a rayc".
Koda jin wannan batu sai zuciyar Muraisu ta
karaya, nan da nan idanunsa suka ciko da kwalla
amma sai ya daure ya juya ya fice daga cikin urakar
zuciyarsa cike da sake-sake yana mai cewa a ransa,
"To wai shin wacce irin kariya Sarki zai bashi alhalin
ya yarda da kansa kuma ya san zai iya kare kansa daga
kowacce irin masifa?".
Tun da Yarima Muraisu ya bar turakar Sarki ya
koma tasa sai ya kasa zaune ko tsaye, tunani da
fargaba suka cika masa zuciya. A haka dai ya samu ya
Byara kayau yakinsa kuma ya kimtsa kayayyakinsa
Wadanda zai yi wannan afiya da su. A sannan ne ya
zauna ya yi tagumi ya shiga sabon tunani. Abinda y
fara fada masaa rai shi nc wai shin waccc irin sabuwar
rayuwa ce ne ta zo masa haka? Ya ya shu da bai taba
yin soyayya ba, bai ta6a magana da budurwa ba ta
tsawon dakiku za a cc da shi ya tafi neman wadda zai
aura a lokaci guda haka?"
Muraisu ya sake zurfafawa a tunaninsa sai ya
fahimci cewa akwai alamun cewa wannan sabon
yanayin rayuwa da ya tsinci kansa a ciki yana da
matukar rikitarwa da tashin hankali domin ya fahimci
cewaa lokacin da zai rasa komai da kowa nasa ne ya
zo tunda an cc lallai za a ci su da yaki. To abin
tambaya anan shi ne shi yana ina har za a zo a cisu da
yaki? Abinda ya yi imani da shi shi ne, idan har za
cisu da yaki, tabbas baya nunfashia doron kasa.
Muraisu na cikin wannan hali
hali ne wata
Kuyangarsa mai kula da abincinsa ta shigo cikin
turakar ta ajiye masa abinci da ruwan inibi a cikin
tambulan da kofi a gabansa. Maimakon ta juya ta fita
sai ta zauna a gefe daya ta zuba masa ido kawai.
Al'amarin da ya matukar bashi mamaki ke nan domin
sama da shekara bakwai kenan wannan Kuyanga tana
yi masa wannan bauta amma duk sa'adda ta kawo
masa abinci ajiyewa take ta fita. Hasali ma basu ta6a
yin magana ba da juna a tsawon shckarun zamansa da
ita.
Ita dai wannan Kuyanga kyakkyawa ce sosai
kuma launin fatar jikinta ruwan kasa ne mai ban sha'awa, sannan akwai kuruciya a tare da ita, domin
sa'adda ma ta fara yiwa Muraisu bauta ba ta fi shekara
goma ba a duniya, don haka yanzu tana da shckara
goma sha bakwai ne kacal, kuma ana kiranta da suna
Sabirat.
Lokacin da Yarima Muraisu ya ga Sabirat ta
zauna kuma ta Kura jnasa idanu sai ya daka ma ta
tsawa ya ce, "Ke kuma fa, lafiya, akan wane dalili za
ki zauna mini a cikin turakata?".
"Ka
Cikin firgici Sabirat ta mike tsaye zumbur!
sannan ta durkusa bisa gwiwoyinta ta ce,
gafarceni ya shugaban a, Sarki ne ya ce lallai yau idan
na kawo maka abinci kada na fita sai na tabbatar ka ci
ka sha tukunna sannan na korna na bashi labari".
Koda jin wannarı batu sai Yarima Muraisu yaji
wari irin dadi ya shigeshi, bai san sa'adda ya sakia
murmushi ba ga Sabirat.
Wannan shi ne karo na farko da ta taba ganin ya
yi ma ta murmushi a iya tsawon rayuwarta da shi.
Shi dai Yarima Muraisu ko kadan mace bata
dameshi ba, domin ba a taba ganian ranar da ya bukaci
wata baiwa ba ko Kuyanga, kai har ma wasu suna
zargin ko bashi da cikakkiyar lafiya. Babu abinda ya sa
a gabansa kullum dare da rana face horar da kansa
yaki da kuma yin ladabi da biyayya ga Sarki yana
gudanar da duk aikin da aka umarceshi da yi.
Lokacin da Kuyanga Sabirat ta ga Yarima
Muraisu ya dubeta har ya yi ma ta murmushi sai
hankalinta ya kwanta ta mikc tsam daf da shi ta zauna
yadda har suna iya jin num fashin juna ta ce, "Shin ka
yi mani izini na civar da kai da hannuna?
Maimakon ya ba ta amsa sai ya dubcta kawai ya
sake yin murmushi. Nan take Sabirat ta dinga đebo
abincin tana bashi a baki. Fara hakan ke da wuya sai ta
ga hawaye ya zubo masa, al'amarin da ya matukar
girgiza ma ta hankali ke nan ta firgita ainun ta ce, "Ya
shugabana ka yafeni, idan wannan abu da na yi maka
ya bata ma ka rai?"
Da jin haka sai Muraisu ya yi mnurmushi sannan
ya dubeta ya ce, "Mene ne sunanki?" Cikin matukar
mamaki ta ce, "Sunana Sabirat."
Ba komai ne ya sa Sabirat tayi mamakin jin
wannan tambaya ba face sanin cewa bata da matsayin
da zai tambayi sunan na ta kuma ta san lallai bai sani
ba, tunda a shi da wani amfani a wajensa.
Muraisu ya sake yin murmushi a karo na biyu a
gareta, sannan ya sa hannu ya share hawayen da ke
zuba a idonsa ya ce, Ya ke Sabirat kiyi sani cewa a
iya sanina ke ce mutumn na biyu a duniya wanda ya
taba ciyar da ni a hannunsa. Mahaifina shi ne mutum
na farko. ba wani abu bane ya sa ni kika ga ina zubar
da wannan hawaye ba face na tuna cewa a rayuwata
ban san dadin uwa ba, tun ina jariri ta mutu ta barni.
Mahaifina ne ya ci gaba da renona har na girma, yau
gashi shima mutuwa za ta rabamu a ko yaushe daga
yanzu.

Yanzu an umarceni da na fita neman matar da
zan aura gobe, kuma zan tafi na bar mahaifina a cikin
wannan hali na matsanaiciyar rashin lafiya. Bani da
tabbacin zan dawo na sameshi a rave. bani da tabbacin
zan zamo abinda zan tafi nema, Shin mene ne karshen
rayuwata? Ga dukkan alamu zan rasa komai da kowa
ke nan tunda dan uwana ma guda daya da ya rage mini
ya zama abokin gabata, kuma ya gujeni. Ashe haka
rayuwa take da rashin dadi idan mutum ya rasa
masoyi?"
Sa'adad Yarima Muraisu yazo nan a zancensa, Sal
Kuyanga Sabirat taji ta kamu da tsananin tausayinsa,
bata san sa'adda ta rungumeshi ba, suka fadi kasa,
kawai sai ta shiga shafar gashin kansa.
Ashe abinda ta bashi ya ci akwai banju a ciki.
Nan take kuwa barci ya kusanceshi, cikin tsananin
farin ciki ta mike tsaye ta kura masa idanu. Nan take
taji ta kamu da tsananin kaunarsa, domin shi ne da
namiji da ta taba runguma a rayuwarta a lokacin da
balaga ta zo ma ta. Kasancewar babu inda tayi bauta
face a wajensa, kuma musaranan Sarki Salmar yasa
aka siya ma sa ita domin ta rinka debe masa kewa,
kuma ya yi saboda ita tunda tun tana karama aka
siyota, shima a lokacin bai fi shekara ashirin ba a
duniya, amma sai gashi bai yi sabon da ita ba, kai ko
sunanta ma bai taba sani ba sai a yau din nan.
Lokacin da Kuyanga Sabirat ta kurawa Yarima
Muraisu idanu sai ta ce a cikin ranta, "Hakika duk
macen da ta auri Yarima ta garma morewa, dormin duK
abinda mace take so akwai a tarcd a shi. Ga kywawan
halaye, kuma gashi dan Sarki. Ina ma dai a ce ni ce
matar aurcn da zai tafi ncma a gobc. hakika da na
Zama tauraruwa a cikin matan wannan zamani.
Koda gama fadin haka sai Sabirat ta tafi da baya
da baya ta fice daga cikin turakar tana kallon Yarima
kamar za ta fasa fitar ta koma ta zauna a gabansa.
Fitarta ke da wuya

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

2 Comments On BUSA A MUTU Book 1
avatar
shuraihu-usman-1

1 year ago

Reply

Aha

avatar
bilkisu-adam-yusuf

1 year ago

Reply

Littafin yayai dadi

Please Login or Register in order to submit comment