Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*Y͟͟A͟͟N͟͟C͟͟I͟͟N͟͟ B͟͟A͟͟Y͟͟I͟͟*
{Historical fiction}



*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻


*SURAYYERH B.ADUL*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation



*SANARWA*

*Dafarko littafinnan na siyarwa ne amma saboda murnar shiga sabuwar shekara yasa namaidashi free*


Dz book completely goes to *HASSAN 80k & HUSSAIN 90k*



*Special gift to my besty*

*UMAMATU UMAR ADAM*


*APPIE NEW YEAR 2020*


*PAGE 1*



Bismillahirrahmanirraheem.




Kallo daya zakayiwa gidan ka fahimci cewa talauci yayiwa ahalin gidan katutu sosai a gindinsu,duk da kasancewar gabadaya gine ginen garin na jar kasa ne kuma gajeran gini,amma Wannan gdn daban yake a cknsu don ko arzikin gini da laka ma bai samu ba,ginin langa langa ne itama ta lalace sosai don duk ta bubbule tayi tsatsa,,gajeran ginin bandakin gidan ne kawai na laka amma hatta dakunan ckn gidan na kara ne dama kuma guda 1 ne.


Wata matashiyar budurwa ce wadda batafi 18 year's ba tafito daga gidan ckn sauri kafarta na sanye da wani kodadden silifas wanda aka kulle da leda saboda tsinkewar da yayi,kana kallonshi zaka hango tarin dinkunan da akai masa, tana sanye da bluen yadi dinkin riga da zani single, kallo daya zakayiwa kayan kabashi sunan uniform, batada hijab sai dankwalin da ke daure a kanta wanda bai hana dogon kashin kanta da ke kitse da manyan kitso fitowa ba,dogowa ce siririya chocolate colour,tanada tsananin kyau na fada a ko'ina me ban mamaki,idanuwanta manya wanda idon ka kalleta zakayi tunanin tanajin bacci ne,,hancinta dogo ne me tsananin kyaun fasali,,bakinta girmansa dai² gwargwado abin sha'awa,gaban goshinta wani kwantaccen gashi ne baki sidik wanda yai bala'in kara mata kyau kana kallonta zaka fahimci tanada sanyin hali.

Ckn sauri take kokarin barin kofar gdn nasu tajiyo muryar mahaifiyarta sama² tana kiran *MUWADDAH! MUWADDAH!!*,murmushi tayi tareda girgiza kai tana buga kafa irin na shagwababbun yara,,da gudu takoma ckn gidan tashiga dakin karansu wanda akaiwa labule da wani yamushasshen buhu,mahaifiyarta na xaune da Kofi a gabanta ta zubawa kofa ido da alamun tana jiran shigowar muwaddan.

Tana shiga ta kyabe fuska kamar zatayi kuka, ckn shagwaba tace "Don Allah iyata ki banni nayi tahiyata kada ayi babu niya,,takarasa tana turo baki gaba.


Murmushi mahaifiyartata tayi ckn kulawa tace " muwaddatu na ki rage wanga zumudi kyajiya??,,kizo kisha kunun nan ko kadanne banson ganinki da yunwa koda nikuwa zan dawwama cknta,, takarashe ckn raunin murya.

Shiru muwadda tayi ckn matsanancin tausayin mahaifiyar tata,Abubuwa da dama ne suka shiga dawo mata tamkar ynz suke faruwa,lokaci guda idonta yakawo kwalla alamun zatayi kuka,kallonta takai kan kafafuwan mahaifiyarta da ke kunbure suntum rabinta a rarake an barbada magani amma hakan bai hana hango kashin kafar ba, wani gigitaccen kuka ne ya kwace mata,durkushewa tayi a gurin tanajin zuciyarta tana mata matsananciyar suya, ckn kuka take cewa "Allah yai miki sakayya iyata!!!Allah yaiwa Babana sakayya!!! Wlh natsenesu!!banida makiyan da suka hisu,,Tabbas bantabba ganin mugaye Azzalumai wadanda kansu kawai suka sani ba tamkar *MASARAUTAR ZINARI*,,,natsanesu iyata!!Wlh bana kaunar ganinsu!!!Takarashe dasakin wani gigitaccen kuka.


Cikin dauriyar gaske mahaifiyarta ta janyota jikinta tareda goge mata hawayen fuskarta tana bubbuga mata baya,,tasani tabbas ya cancanta muwadda tayi kuka,amma baxata nunamata hakaba dole ta tausashi zuciyar yar tata saboda shine abinda yafi komai cancanta da tayi ko da kuwa bataso,,cigaba da buga bayan muwaddan tayi har saida tayi shiru sai sheshshekar kuka da takeyi,daukar kofin da ke gefenta tayi tanufi bakin muwadda,,,kauda kai tayi alamun baxata sha ba,Ajiye kofin iya tayi a gefenta tareda kawar da kanta gefe,,dasauri muwadda ta taso tarike hannun mahaifiyarta tareda goge hawayen fuskarta tace " Kiyi hkr kyajiya iyata??To zansha.

Ba musu iya tadauko kofin kunun da baifi rabi ba ta mikawa mata,,karba tayi ta kurba sau uku ta ajiye tareda mikewa tace "iyata ni zantahi,ki tayani da addu'a Allah yasa ina daga ckn bayin da sarki zai y'anta yau,,badon kamai ba don nasamu damar kula da ke.

Ckn kulawa iya tace " Karki damu diyata nayi miki dama,,maxa ki tahi kar ki makara.

Ckn sanyin jiki ta fito daga gidan nasu,,tana tafiya tana sauri tare da sharar hawaye,tayi tafiya mai nisa kafin taxo kofar wani dankamemen gida me tsananin kyawun gaske,,duk iya kulewarka a kallo baxaka hango karshen gidan ba,,gine ne tamkar a kasar turai,bazaka taba tunanin a ckn garin yakeba,,kallo daya zakayiwa gidan ka tabbatar gidan sarauta ne,,A can saman katuwar kofar gidan aka rubuta *MASARAUTAR ZINARI*.

Ckn sauri ta wuce masu gadin gidan ta shige ciki,,bayi ne birjik kowa da abinda yakeyi,,dukansu mazansu da matansu suna sanye da yadi blue irin na jikinta amma maza wando ne,mafi yawansu fuskarsu dauke da annuri suke aiwatar da al-amuransu.


Kai tsaye wata doguwar hanya tabi,batayi tafiya mai nisa sosai ba sai gata a wani bangare me tsananin kyau,,bayi maza guda biyu suna kofar shiga wajen a tsaye sunyi kekam ko cikakken motsi basayi,,yayinda wasu mata bayi suke shawagi a wajen.

Batareda fargabar komaiba tashiga wajen,,hadadden parlour ne mai tsananin kyawun gaske wanda aka kayata da kayan Adon sarauta,,wasu bayi yammata guda 4 suna tsaye a dakin babu wadda takewa yar uwarta mgn,,haka tabi sahunsu ta tsaya a inda suke,,a kalla sunshafe awa 2 tsaye a wajen amma kaf cknsu babu wadda zaka kalla kace tagaji da tsayuwar,don da alama sungama sabawa.


Cikin tsananin takun kasaita da kololuwar ji da kai take tafiya tamkar bata kaunar taka kasa,,bayanta wasu bayi ne a kalla sunkai 8 suke take mata baya,, yayinda daga cknsu ke rike da hadaddiyar Alkyabbarta wadda tagaji da haduwa.

Suna hangota gabadayansu ckn rawar jiki suka zube suna jero mata kirari,,batare da ta kalli ko dayansu ba taxauna akan hadaddiyar kujerar sarauta,,cigaba da jero mata kirarin sukai ba kakkautawa,a kalla saida suka shafe 20mints suna Abu daya kafin daya daga ckn bayin da ke tsaye tace *GIMBIYA JALILA* ta amsa gaisuwarku yayan talakawa.


Sai a sannan suka mike daga tsugunnan da sukayi.

Ckn matukar kyama gami da tsananin wulakanci da kaskanci gimbiya jalila ke binsu da kallo,,saukar da kai kasa muwadda tayi don ko kadan bata kaunar kallon fuskar gimbiya jalila saboda tsananin tsanarta da tayi.

Wulakantaccen kallon da gimbiya jalila ke aikawa muwadda na musamman ne,,batasan me yasaba yarinyar ba abinda tai mata amma tana tsananin tsanarta fiye da kowa,kuma baxata ce ko saboda kyawun muwaddan bane don itama kyakykyawa ce amma tabbas tsanarta me tsanani ce a ranta.


Daga ckn masarautar suke jiyo muryar wani bafade yana sanar da cewa sarki yabada umarnin kowa ya hadu a fada ynz saboda gabatar da yantaccun bayi na Wannan shekarar,,dadi ne yarufe dayawa daga ckn bayin banda muwadda wadda ta tsinci kanta da tsananin bugawar kirji da tsoro dukda cewa tayar darwa zuciyarta tana daga ckn bayin da yakama ace suna sahun farko a wadanda za'a yanta,,ita abinda yasa take kaunar a yantata saboda tasami damar kula da mahaifiyarta yadda yakamata.

Gimbiya jalila batayi mgn ba sai baiwar da tayi mgn dazu ce tabasu umarnin yafiya,,said da suka yi gdy sannan suka fita.


Suna fita ubaida taja hannun muwadda fuskarta dauke da fara'a tace "muwadda nasan kina ckn bayin da zasu sami yanci yau,,na tayaki murna".

Girgiza kai muwadda tayi ckn sanyin jiki tace " Allah yasa ubaidah".

Ameen amma nikam nasan ma hadda ke,,saboda kaf gdnnan babu wanda baisanki wajen aiki ba.

Shiru muwadda tayi har suka karasa katuwar fadar masarautar inda suka tadda bayi dankam wasu suna farin ciki wasu suna fargaba.


Lkc guda wajen yayi tsit tamkar babu wani Abu me rai a wajen sakamakon shigowar *SARKI ALIYU* da ahalinsa.

Zubewa sukayi gabadayansu ckn girmamawa suka kwashi gaisu*Y͟'A͟N͟C͟I͟N͟ B͟A͟Y͟I͟*
{Historical fiction}


*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻



*SURAYYERH B.ABDUL*




Dz book completely goes to *HASSAN 90k & HUSSAIN 80k*


*Special gift to my besty*

*UMAMATU UMAR ADAM*

___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


___________________________________






*PAGE 2*



Bismillahirrahmanirraheem.


Sunjima sosai a tsugunne kafin abada umarnin mikewa.


Sarki Aliyu da iyalansa suna zaune akan wasu hadaddun kujeru masu tsananin kyawu gefensu bayi nayi musu fiffita sai kuma wasu a bayansu wasu a zaune a gabansu,waziri ne yamike tsaye tareda yin bayani kamar haka:
"Sanin kanku ne cewa a kowace shekara a masautar nan ana dibar bayi guda 50 a yanta su,,To ynz ma Allah yakawomu lkcn saboda haka ynz ba bata lkc za'a gabatar dasu,ihu mutane sukasa ckn farin ciki tareda jerowa masarautar kirari,,,tunda waziri yafara mgn kirjin muwadda yake bugawa tanajin ance ynz za'a fara kiran sunan wadanda za'a yanta kafafuwanta yayi mugun sanyi kamar zata zube amma ba dama,don babban laifi ne a masarautar sarki yana zaune ka zauna kaima.


Wani bafade ne yamike da zungureriyar takarda a hannunsa yafara kiran sunan wadanda aka yanta,,wajen yayi tsit kowa kirjinsa yana bugu saboda fargaba,,tuni muwadda tagama sarewa ganin an kirawo mutane 46 amma ba sunanta,wasu hawaye ne masu matukar zafin gaske suka shiga tsere a kuncinta,sosai zuciyarta take suya da radadi,bata kara tsinkewa da lamarin ba sai da taga ankira mutum ta 50 ubaidah,ihu suka dauka ckn farin ciki,,tuni wajen yakaure da kide² na farin ciki.


Zamewa tayi tafice daga wajen,ko gabanta bata gani dakyau saboda tashin hnkl,,can gefe da fadar tasamu wani dan dandamali ta zauna tareda hada kai da gwuiwa tasaki wani azababben kuka mai cin rai,,Babu abinda yafi damunta sama da kula da mahaifiyarta,inda akwai yanda zatayi jitake dauke mahaifiyarta zatayi su gudu daga Wannan bakar kasar,ynz haka zata kare rayuwarta a bauta??,,kuka take sosai harda sheshsheka tanajin wata muguwar kiyayyar masarautar zinari.



Tundaga nesa yarima yusufu yahangota kuma ya ganeta,,da kai yayiwa bayin da ke biye dashi alamar su koma,ba musu suka juya,,tsayawa yayi akanta yanajin yanda take garsheken kuka,runtse idonsa yayi saboda kukan yana taba ransa,zama yayi kusa da ita ckn daddarar muryarsa me sanyi yace *MUWADDAAAT*,,dasauri ta dago tareda ja da baya tana kalle²,,Ajiyar zcy tayi ganin ba kowa a wajen,,ckn sanyin murya me cike da tsoro da rauni tace "Don Allah yarima ka taimakamin ka tahi kar nashiga matsala",,, murmushi yayi ckn tsokana yace " Kinhiya tsoro muwaddatt to sai me don anganmu???ynz dai fadamin me kikewa kuka???,,,,mikewa tayi tsaye idonta har yaciko da kwalla,ckn raunin murya tace "Bakomai", tana kokarin barin wajen,,dasauri yasha gabanta tareda kallonta ido ckn ido yace " Baxan iya yafewa zuciya ta ba indai har naganki ckn damuwa kuma nabakki a cknta,saboda haka ki fadamin abinda akai miki ko kuma kiyi murmushi nagani,,babu yanda ta iya dole tayi murmushin da ke kara mata kyau tana mamakin karamci irin na yarima yusufu bakamar sauran yan gdnba,shima murmushin tareda fadin "ko kefa,ni ynz zamuje kilisa ne ina tunanin kafin badawo kin tahi ne??daga mai kai tayi alamun eh,tanayi tana waige² don Allah Allah take yatafi kar wani yagansu,,sallama yai mata yatafi,Ajiyar zuciya tayi don ita har ga Allah batason yarima yana rabarta don babban tashin hnkl ne a wajenta.

Ubaidah ce ta hangota dasauri takaraso wajenta tareda rikota ckn tausayi tace " kiyi hkr kinji muwadda??Allah yasa haka shiyafi alkhairee,,, Hawayen fuskarta ta share ckn rawar murya tace "Ubaida ynz a haka rayuwar iyata zata kare babu cikakken me kula da ita???karki manta ni kadai fa gareka,,Wlh bantaba tsanar wasu mutane ba sama da ba masarauta....dasauri ubaida tarufe mata tareda juyawa tana kalle² da addu'ar Allah yasa ba wanda yagansu,,ckn sanyin murya tace " kidaina irin magannan muwadda,Allah yana sane da iya kuma..... Shiru tayi sakamakon jin sanarwa da akeyi daga ckn masarauta na ana neman kowa da kowa ynz a fada,Ajiyar zuciya muwadda tayi tanajin gabanta na faduwa,Jan hannunta ubaida tayi suka nufi ckn fadar data cika tayi dankam,,Sarki Aliyu yakame akan kujerarsa fuskarsa a hade ynz sabanin dazu da akwai dan annuri,lkc guda jikinsu yayi sanyi kowa yana tsoron abinda yafaru,,waziri ne yamike shima fuskarsa a hade yace ina *KUYANGA MUWADDA??*,,,wani irin masifaffen bugawa kirjin muwadda yayi tamkar zai fado kasa,,karfin hali tayi ta fara tafiya don zuwa gaban fada,,da kallon tausayi ubaida tabita tareda goge hawayen da ta zubo mata na tausayin rayuwar kawar tata kullum cikin matsala,,duk inda muwadda ta gifta sai an bita da kallo har takarasa gaban fada ckn girmamawa ta tsugunna ta sunkuyar da kanta,,wani bafade ne ya taso hannunsa dauke da wata zabgegiyar bulala tanata kyalli,tuni tausayin muwadda yakama daya daga cknsu,,ckn fuskar rashin imani Wannan bafadan yacewa muwadda "Keee baiwa yar gdn matsiyata kinsan mene ne laifinki ????.

Ckn dakiya muwadda ta girgiza kai.


Wani bafade ne yamike dauke da takarda a hannunsa ya karanta kamar haka:" Kuyanga muwadda ta karya doka ta takwas a gidannan karo na farko,an kamata da laifin tsayuwa da yarima yusufu har tana yimasa murmushi saboda haka zata karbi hukuncinta ynz".

Zaro ido mutane sukayi ckn tsananin tausayin muwadda don sunsan babban laifi ne sosai Wannan a masarautar nan.


Tunda bafaden nan yafara bayani har yagama muwadda bata dago kanta ba,banda tsananin suya ba abinda zuciyarta takeyi tuni idanunta suka kame babu alamun hawaye,,Wannan bafaden ne yacigaba da bayani "Kuyanga muwadda zata karbi bulala 20 ynz take,sannan zatayi zaman kurkuku na mako daya.


Sai a lkcn hawaye ya zubowa muwadda saboda tsananin tashin hankalin wane ne zai kula da iyarta???,Dayan bafaden nan me dauke da bulala ne yashiga laftar muwadda babu tausayi sai da yaimata bulala 20 cifff amma ko motsawa batayi ba,, haka akasa wasu bayi mata sukajata a kasa suka nufi kurkuku da ita,,babban daki ne me tsananin duhu ga tarin sauraye da cinnakai,,suna tafiya muwadda tasaki wani gigitaccen kuka tareda zubewa a kasa tana birgima tareda fadin " Nashiga uku!!ya Allah ja kawomin agaji,,iyata bata iya mikewa komai ni nake mata,,wane zai samo mata abinci??wane zai kaita bayi??wazai debe mata kewa??Ya Allah ka taimakamin ka taimaki iyata,kabata juriyar rashina na kwanakin da zanyi a wajen nan,,,haka tadinga kuka tamkar ranta zai fita babu abinda yake kara tasar mata da hankali sama da yanda rayuwar mahaifiyarta zata kasance babu ita.


***************

Tafiya take ckn sassarfa har takaraso kofar shiga part din,da hannu taiwa bayinta alamun su tsaya,kai tsaye tashiga ckn parlourn,wata dattijuwar mata ce fara me matsakaicin kyau zaune akan wata hadaddiyar kujera tanashan fruit din da ke gabanta,kana kallonta kasan tana tsananin ji da mulki da isa,ita kanta matar da tashigo ynz saida ta russuna mata dukda cewa kana kallon shigarta kasan itama jinin sarauta ce,matar ce tayiwa bayin umarnin fita,zama tayi kusa da dayar matar race "Me babban daki akwai babban labari fa".

Ajiye tufar hannunta tayi tareda facing matar tace " Fadamin labarin me??".


Nan da kwana 8 *YARIMA SAMEER* zai dawo kasar nan.


Tuni fuskar matar nan ta fadada da murmushi sosai wanda kana kallonshi zaka tabbatar na tsantsar mugunta ne.wa.*Y͟A͟N͟C͟I͟N͟ B͟A͟Y͟I͟*
{Historical fiction}


*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻



*SURAYYERH B.ABDUL*


Dz book completely goes to *HASSAN 90k &HUSSAIN 80k*

___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________








*PAGE 3*






Bismillahirrahmanirraheem.




Gyada kai me babban daki tashigayi still fuskarta shimfide da murmushi,maimakon tayi mgn saita janyo wayarta tadanna wata numb tareda karawa a kunnenta,,harta tsinke ba'ai picking ba,ajiye wayar tayi tareda kallon dayar matar tace "Fulani tabbas kinzomin da babban labari mai dadi,saboda yarima sameer yadawo a lkcn da nake bukata ,tabbas bazan taba bari ya....ringing din wayarta ne yakatseta daga abinda take fada,,Picking tayi ckn murmushi tace " Da na na kaina,maman taka ma sai kayi mata Jan aji???".

Yarima sameer dake zaune a wani hadadden parlour kan kujera three sitter ya mike kyawawan fararen kafafunsa jin abinda maman tafada yasa ckn shagwaba yace "wane ni nayi wa mama na jan aji,ban kusa da wayar ne fa".

Tabe baki me babban daki tayi ckn tsananin tsanar yarima sameer,dannewa tayi ckn kissa tace " Ai ni fushi nake ma da kai yarona,ynz ace xaka dawo amma baxaka sanarmin ba".

Murmushi yayi tareda fadin "Afwan mama na,aimin hakuri,mai martaba kawai ma nafadawa amma ko princess bata saniba.

Ckn jin haushi tace " Ohhhh kana nufin princess taka ta fini ko??".

Dasauri yace "No mamana ai matsayinki da nata daban,amma dukanku mutane ne masu matukar daraja da matsayi tareda kima a ido na,mama u are my mother nd jalila is my beloved wife,so kinga dukanku ai kunada matukar muhimmanci gareni ko??.

Hakane amma yakamata kasanarmin ai.

Rintse ido yayi tareda fadin " Sorry mama na zan kiyaye".

Yawwa ko kaifa da na,anjima zan kiraka ynz inada baki ne,ka kula da kanka kaji??.


Ckn jin dadin yanda me babban daki ke kula dashi yace "Tnx mama na takaina.

Katse wayar tayi tareda fadin " Sakaran banza,xakasan koni wace,sai na tarwatsa rayuwarka".


Ckn karin munafurci da zuga fulani tace "Wlh me babban daki gara kiyi gaggawar aiwatar da nufinki idan ba haka ba kinaji kina gani yaronnan zai hau mulki ya juya kasar nan sannan yasauka dansa yahau,naki yayan ko oho.


Dariya me babban daki tayi sannan tace " Amma dai kema fulani kamar sakarya haka kike,anfada miki da haka na zauna ne???surutunki ne yasa bana sanar da ke komai idan nayi amma tsawon shekarunnan ni nahana yarima sameer haihuwa,kuma wallahi bazan taba bari ba indai ina numfashi haka gantalallen yaron nan zai kare rayuwarsa babu da,,ke ko mufeedah da take sonshi inason ya aureta amma ko ita bazan taba bari ta haihu ba da yarima.


Zaro ido fulani tayi ckn mamaki tace "Mufeeda yar yayarki fa???".

Murmushi me babban daki tayi tareda fadin " Mufeeda ko yar wace kuwa,nifa kisani banida burin daya wuce naga yarima yusufu akan karagar mulki kuma tabbas indai ina nimfashi sai na cika burina.


Shine yadace me babban daki don tabbas indai yarima sameer yahau mulkinnan mu kammu munzama abin tausayi.

Bude baki tayi da niyyar mgn yarima yusufu yashigo a fusace,ckn bacin rai yace "Haba mama! Haba mama!!Wlh Sam Wannan ba adalci bane ko kadan,,,Mikewa me babban daki tayi tareda karasawa wajen yarima yusufu ta dafa kafadarshi ckn mamaki tace " me kuma yafaru shalele??",,janye hannunta yayi daga kafadarshi yace "Haba mama akanme za'a saka kuyanga muwadda a kurkuku saboda kawai tayimin murmushi,indai adalci za'ayi kamata yayi ace hadda ni za'a kulle saboda nima nayi murmushin,wlh Sam ba adalci ba n.....Tassssss me babban daki ta daukeshi da mari,ckn takaicin halin dannata tace " yarima mai martaba ne baiyi adalci ba kenan???Tabbas bantaba ganin shashashan yarima kamarka ba,kai ko kishin yarima sameer bakayi kayi koyi dashi??yarima sameer a tsawon rayuwata dashi zan iya lissafa maka dariyarsa,kana kallonshi kaga yaro me tsantsar ji da mulki ba kamarka ba sakarai ,shi ko kallon bayi yanayi ne balle yashiga harkarsu???Amma kai akan kaskantarciyar baiwa irin kuyanga muwadda kake tada jijiyoyin wuya saboda bakasan ciwon kanka ba,,to idan barci kake ka farka ka tuna wane ne kai ".

Murmushin takaici yayi tareda fadin " Ko zakisaka kaina gabas ki yanka mama baxan fasa fada ba me martaba bai yanke hukunci ckn adalci ba saboda bai hada da niba,kuma mgnr yarima sameer Wannan rayuwarsa daban tawa daban,saboda haka nima a yanzu zanje na rufe kaina a kuskuku har zuwa lkcn da mai martaba ya dibawa muwadda,,yakarasa yana kokarin fita,,A fusace me babban daki ta fuzgoshi idonta har yasauya saboda bacin rai,,ckn masifa da takaici tace "Yarima yusufu kana ckn hayyacinka kuwa???,,kasani Wannan shine mafi girman kaskanci da zakayiwa kanka a masarautar nan, wace ce kuyanga muwadda da zaka damu saboda an rufeta,to inaso kasani indai ka aikata abinda kafada wlh saina wulakanta kuyanga muwadda a garinnan,sai na maidata abin kyama a wajen kowa idan kayi musu jeka ka aikata.


Murmushin takaici yayi tareda matsowa daf da ita yace " Narantse da Allah mama abinnan da kika lissafo indai ya tabbata akan kuyanga muwadda to tabbas zai tabbata akan danki yusufu,don zan koma kaskantacce mara yanci ko kadan,,A fusace ta fuzgosa ckn matsanancin Bacin rai tace "Me kake nufi???.

Babu abinda nake nufi face abinda nafada ynz,yana gama fadin haka yafice daga dakin a fusace.


Sharaf ta zube akan kujera ckn matsanancin bacin rai,kallonta takai kan fulani wadda tasaki baki da hanci tana kallon ikon Allah,ckn bacin rai me babban daki tace " Tabbas fulani yazama dole nadauki tsatstsauran mataki mafi muni akan kuyanga muwadda".

Girgiza kai fulani tayi tareda fadin "Karkiyi haka me babban daki, wlh abinda yarima yusufi yafada har zuciyarshi ne,saboda haka ko wani Abu zaki aikata kibari daga baya amma ba ynz ba,,shawarar da zanbaki ynz kije gurin me martaba ki rokeshi a fito da kuyanga muwadda ko dan rayuwar danki.

Ajiyar zuciya me babban daki tayi tace " Anya kuwa fulani me martaba zai fito da kuyanga muwadda???kinsan halinsa idan ya yanke hukunci kaifi daya ne.


Hakane amma kije ynz ki jarraba.


Mikewa tayi ckn sanyin jiki tace "To bari naje,,Tana gab da fita sukayi karo da mufeedah zata shigo,,ckn iyayi mufeeda tace " Yawwa mama gurinki fa nazo,Wai yaushe yarima na zai dawo ne??Wlh na kagu yadawo kimasa mgn ta.

Ckn kosawa da mgnr mufeeda tace "Nan da kwana takwas",,,Wani mugun tsalle mufeeda tayi ckn matsanancin farin ciki tayi hugging me babban daki tareda fadin " Wayyo dadi yarima na zai dawo".

Ckn takaici me babban daki ta yakiceta daga jikinta tafita don abinda ke damunta ma ya isheta.

Mufeeda ko kulawa batayi ba ckn murna tadinga kissima gata a faffadan kirjin yarima anyi aurensu suna soyewa,A fili tace "Gimbiya jalila kinkusa wulakanta".


Yarima yusufu yana fita kurkuku ya nufa ,yana zuwa yacewa ma'aikatan wajen su bude yashiga su rufeshi,ckn mamaki da tsoron abinda zai biyo baya sukace " Ranka ya dade a rufeka fa kace??".

A fusace yace "Ehh ko bazaku bude bane??.

Russuna sukai tareda cewa " Allah ya huci ran yarima ai mana aikin gafara",,daya daga cknsu ne yadauko mukulli ya bude katuwar kofar kurkukun,,cire alkyabba yarima yusufu yayi yabasu sannan yashiga wajen".

Sudai gabadaya a tsorace suke,don tashin hankali ne aga yarima a kurkuku, amma ba yanda suka iya tunda umarnin yariman ne.



Saboda tsabar kuka idanun muwadda har sun kankance sosai,gawani yaji

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

1 Comments On YANCIN BAYI 1
avatar
fatima-abdullahi-5

11 months ago

Reply

Please how can i get the complete book

Please Login or Register in order to submit comment