Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by

Maryam(ummu hanan)

Da sunan Allah mai rahma mai jin kai tsira da aminci su kara tabbata ga Dan gata annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallam,
Yadda na fara wnn novel din lpy ya bani ikon gamawa lpy


1_5

Tangamemen gidane kayatacce wanda tsayawa fadar irin kyawun gidan ma 6ata lkc me,.
Kutsa kai nayi har falon gidan wanda yaji kayan alatu da abubuwan more rayuwah sai tashin kamshi yake mai sanyaya xuciya.,

Idanuwa na dinga rabawa ganin ba kowa a falon

"Can idanuna suka kyallo min wani kyakkyawan saurayi da shekarunsa baxa su haura 28yrs ba.
Kura masa ido nayi ina hango tsagwaron kyau da Allah ya hore masa
Farine tas mai hade da sirkin ja dogon hancinsa da kewayyayen bakinsa mai dauke da pink lips ya kara fito da ainahin kyansa ,kwance yake kan doguwar kujera yana kallon sama idanunshi a lumshe .

Kofa naga an bude wata kyakkyawar yarinya " yar kimanin 16yrs ta fito hannunta dauke da tray kallonta nayi ina hango tsananin kamarsu da wannan saurayin da gani ba tambaya Kasan kanwarsa ce

Gabanshi ta karaso ta janyo karamin center table din dake gefe ta Dora trayn akai tace yah NAJEEB ga tea din shirun data jine yasa tayi xaton ko barci yake don haka tasa hannu tana dan bubbuga kafarsa a hankali .

Ahankali ya bude idonsa ya watsa mata wani mugun kallo ba shiri ta janye hannunta.sai ynx kika ga damar kawo min? tun yaushe nake xaman jiranki ,
cikin rawar murya tace dan Allah kayi hakuri wall.......shut up ur mouth kinbar gurinnan gurin nan ko sai na mammake ki da sauri ta bar wajen jikinta na rawa, wani dogon tsaki yaja tare da daukan cup din tea din yasa karamin cokali yana juyawa.

Saida ta tabbatar ta rufe kofa ta xauna bakin gadonta turo baki tayi tana kunkuni
Mutum sai sa aikin tsiya in kayi ma ba godiya sai dai ya bika da jaraba ...masifaffe kawai.system dinta ta janyo ta bude ta fara game har barci yayi nasarar dauketa
Emana
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam(ummu hanan)


5_10

Karfe 10:13am na hango alh aliyu shida iyalansa kan dining table suna breakfast, hajiya asiya ta dubi alh tace jibine fa tafiyarmu katsina tissue ya yaga ya goge bakinsa sannan yace Allah ya kaimu xuwa anjima sai direba ya kaiki asayo masu tsaraba ko?murmushi tayi tace shikenan anjiman sai muje.

Kallon najeeb yayi yace da kai fa xa,ayi tafiyarnan
Dagowa yayi ya dubeshi yace
Pls daddy xanje daga baya.
6ata rai daddy yayi yace a,a ban yarda ba yaushe rabonku da xuwa garin Dan haka tare xaku tafi ka fahimta ai?


"Eh daddy"
Ya fada ba don ranshi yaso ba.
Ita kam anisa murna take tayi xasuje kauye.

ASALINSU:

Alh aliyu haifaffen katsina a wani kauye da ake kira sabon layi.su uku mahaifiyarsu gwaggo hanne ta Haifa hindatu ce babba sai amadu saishi aliyu auta sai kuma daya matar mahaifinnasu gwaggo karime dake da "ya" ya biyu
Sani da lawal sun taso Kansu a hade shi Kadaine ya samu yin karatun boko Dan ya nuna yana sha'awar shi suko sauran basu da ra'ayinshi mahaifinsu mallam tijjani ya bashi dama har yakai ga yin bautar kasa a can ya hadu da mummy sukayi alqawarin ita kuma "yar bauchi ce sai dai yaso samun matsala da mahaifiyarsu da kyar dai ta yadda da auren .amadu ya auri wata yarinya Laure sai dai Allah bai basu haihuwa ba, lawal " ya"yanshi biyu sani kuma uku abin yana matukar damunsu .acikin kano aliyu ya kama haya kasancewar anan yake aiki don haka da yayi auren nan aka....

Shekararsu daya da aure ta haifi danta namiji kyakkyawa sukaci gaba da rain on dansu cikin kulawa .
Watanshi biyar da haihuwa Allah ya kar6i ran mahaifinsu mal tijjani sunyi kukan rashin mahaifi wata biyu da rasuwarshi itama mahaifiyarsu tace ga garinku sakamakon ciwon ciki daya turniketa lkc daya sun shiga matsananciyar damuwa amma ba yadda suka iya domin wanda yafisu sonsu shi ya kar6i abinsa........,

Ahaka rayuwah taci gaba da tafiya aliyu yana ta samun cigaba ta fannoni da dama kuma tun kan najeeb basu kara samun haihuwa ba.sai bayan shekaru sha biyu Allah ya kawo wani cikin .alokacinne kuma Laure matar amadu itama ta samu ciki, sun tsinci Kansu cikin farin ciki mara misaltuwa don tuni suka fitar da ran samun haihuwa sai gashi ubangiji ya basu......,

Bayan wata tara

Mummy ce ta fara haihuwar "ya mace sunan mahaifiyarsu taci wato hannatu sai suke ce mata aneesa.
Satin mummy biyu da haihuwa itama Laure ta sullu6o tata " yar budurwar kyakkyawa shima din dai sunan nata ya maida sai kawai suke ce mata Hannah.,

Hannah yarinyace data taso cike da shagwa6a da sangarta ganin ita kadaice agurin iyayen nata musamman gwaggo laure datafi shagwaba ta ga shegen jan fada duk kauyen an santa kullum cikin kawo kararta ake.....


***************

Haka rayuwah taci gaba da tafiya she karar Hannah goma aduniya babanta amadu ya rasu😭
Sosai mutuwar ta dakesu sai dai fatan Allah ubangiji yayi masa rahma ya kyauta namu xuwan(ameen)
Tun lkcn daddy yaso dauko Hannah ta dawo gidansa da xama
Amma fafur gwaggo Laure tace bata yarda ba "ya dayan da take gani taji dadi ita kadai gareta,
Dole ya hakura.
Bayan wani lkc daddy yayi ritaya ya fada harkar kasuwanci ya kuwa shiga da kafar dama don nan da nan yayi suna arxiki yana ta bunkasa.fili ya siya a nassarawa g.r.a ya tamfatsa gidanshi ginin xamani mai kyau da tsari,..
Najeeb kuwa dama bayan ya gama secondary daddyn ya kaishi kasar waje inda ya karanci xane wato architect bayan ya kammala ya dawo kasarsa don cigaba da aikinsa yayin da aneesa take daf da kammala secondary skull dinta,....


" Hannah kuwa an samu ta gama primary da kyarπŸ˜“
don ba karatun take so ba dan ma baba sani da baba lawal suna tsaye akanta da bata yishi ba don gwaggo Laure ba takura ta take ba.duk da haka ba wani kokarin kirki gareta ba don in taje banda tsokana da Neman masifa. ba abinda take samarin kauyen da yawa nason xuwa wajenta saboda irin dirin da Allah yai mata da kyan sura ,sai dai suna tsoron halinta don sai ta fadawa mutum bakar maganar daxai Dade bai manta ba.,.......


Ku biyoniπŸ™‹πŸ»
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam(ummu hanan)

10_15

Cigaban labari

Saturday 11:34. Su mummy suka dau hanyar katsina cike da tsarabar da xa,a rabawa "yan uwa da abokan arxiqi.
Aneesa ce ke taba mummy lbrn makarantarsu a fusace najeeb dake gaba ya juyo
Dalla malama ki mana shiru kin cikamu da surutu


Dagowa mummy tayi daga danna wayar da take,. Harararshi tayi tace ina ruwanka? ko Kai take bawa? Sarkin xafin rai juyawa yayi yana fadin Allah kuwa mummy yarinyarce ta cika surutun tsiya, toh ai ba bakinka bane sai ka kyaleta.,
Ido suka hada da aneesa ta mirror din motar ya xabga mata harara da sauri ta dauke idonta dan sosai take tsoron shi sam baya yi mata wasa kullum fadan mummy ya dinga sakar mata fuska dan itace sakuwarshi🀣 abinda baya son mummy na fada wai aneesa ce mai binshi.

Gidan su daddy suka sauka gwaggo karime tai murna da xuwansu tabarma ta shimfida masu awajen katuwar bishiyar cediyar dake tsakar gidan nan suka xauna aka gaggaisa ta kawo masu ruwan randa mai sanyi sannan ta xuba a kwanon sha taba sakina " yar baba sani dake xaune awajenta ta kaiwa direba saida suka huta sukaci abinci dambu tayi musu da yaji attarugu da gyada mummy da aneesa sunji dadinshi sosai shikam najeeb kinci yayi yace ya koshi duk abinda gwaggo karime tace a kawo masa sai yace bayaci ...

Daga nan gidan su Hannah suka tafi a tsakar gidan suka samu Hannah tana ta faman xum6ure_xum6uren baki da alamu an 6ata mata rai ganinsu da tayine yasa ta tashi da murna ta rungume aneesa cikin karadi tace gwaggo ki fito ga "yan kano sunxo."
Fitowa tayi tana gyara daurin xaninta
Cike da fara,a take fadin ah ah yau su hajiya ne agarin? sannunku da xuwa lale marhabin dasu najibu Ku shigo mana mummy ce tace ai dakinne da zafi yi mana shimfida anan kawai.
Dariya tayi tace toh ai shikenan dakin ta shiga ta dauko tabarma ta shimfida masu a inuwa suka xauna suka gaggaisa ta kawo musu ruwa da abinci mummy ce tace aiko yaya Laure mun ciko cikinmu gidan gwaggo karime matsar dashi tayi gefe ta ce bari a ajiye ko xuwa anjima ne sai kuci ....,"

Hannah ta duba tace tun daxu nake fama dake ki debo ruwa kika ki gashi ko ruwan sallah babu a gidan .turo baki tayi tana shura kafafu ni wllh na gaji yau sahuna nawa agidannan murmushi mummy tayi tace oh Hannah har ynx baki daina halayenki ba ko? ta6e baki gwaggo tayi tace kema dai kya fada hajiya.

duban Hannah mummy tayi tace tashi ki debo kinji "yar albarka aneesa ta rakaki kinji .mikewa tayita suri bokitin robar dake gefe dai_dai nan suka hada ido da najeeb da haushinta ya gama kasheshi ace yarinya 16yrs amma Sam bata da nutsuwa ga rashin kunya wata uwar harara ya watsa mata batai kasa a gwiwa ba ta maida masa martaniπŸ˜‚ harda Karin murguda baki ta fice aneesa tabi bayanta.,'"

ji yayi kamar ya bita ya damkota ya zazzabga mata mari .
girgixa kai yayi tare da jan kwafa ahankali tashi yayi shima ya fice wajen direba .....",

Duban gwaggo mummy tayi tace yaya Laure akwai wata alfarmar da nake nema awajenki
sai dai ban sani ba ko xakiyi min ita ,.ina jinki hajiya asiya fadi bukatarki ni kuma indai ina dashi xanyi maki

gyara xama mummy tayi tace alfarma nake nema ki bani Hannah in tafi da ita taci gaba da karatunta acan kinga ta gama primary tuni amma bata cigaba ba ga aneesa nan ta kusa gamawa.numfashi gwaggo ta sauke sannan tace agsky ba don tun farko nayi maki alqawarin biya maki bukatarki ba da ban amince ba saboda ita kadai na mallaka arayuwa nake gani inji dadi amma ba komi na amince ko baki tafi da ita ba aure xai rabamu sai ki sanar da su lawal., godiya mummy ta dinga xubawa don ita dai jininta ya hadu dana yarinyar tun tana karamarta ,.

"toh"
sai dai hajiya ki aiko a dauketa daga baya don kayanta ma duk babu wanki saita dan shishshirya tukuna.murmushi mummy tayi tace karki damu yaya Laure bana bukatar komi nata ga na aneesa nan sai ta fara amfani dasu kafin a diddinka mata nata ........,


Toh aranar dai duk "yan uwansu suka ji tafiyar Hannah kano ,

da kyar ta amince xata bisu ...

Sai bayan la'asar sukai shirin tafiya da kuka suka rabu da gwaggo har bakin mota ta rakosu,
" ganin Hannah na shirin shiga motor tana kuka yasa ya matsa kusa da mummy yace wai mummy me wannan yarinyar xata shiga tayi mana a mota??tare xamu tafi yatsina fuska yayi yace xuwa ina ?kano mana ta koma can da xama😳ido ya xaro yana kallon mummy ita kam bata kulashi ba ta shige mota ., lallai kam xa,ayita wannan fitsararriyar yarinyar ce xata xauna tare dasu?
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam (ummu hanan)

20_25

"Cikin lkc kankani Hannah ta fara xuwa skull dinsu aneesa hakama ta fara xuwa islamiyya toh ba laifi dai tana dan fahimta ba kamar da ba.haka shashancin data ke duk ta rage yinsa ta fara nutsuwa,"wajen kwalliya ne dai har ynx aneesa ke fama da ita Dan taki daina dige_dige a fuskarta."watanta uku kenan da dawowa kano"......




*******************

Gama dinner dinsu kenan najeeb ya tashi xai bar wajen daddy ya dakatar dashi yace akwai maganar daxa suyi komawa yayi ya xauna. ."

"Zamanshi ya gyara ya fara da " Alhmdllh godiya ga Allah daya kawo mu wannan lkc, "numfashi ya sauke yace hajiya akwai wani alqawarin da na daukarwa yaya amadu wani xuwa danayi daf daxai rasu ."

Shiru yayi yana binsu da kallo cigaba yai da fadin alqawarin kuwa shine na hada "ya" yanmu aure wato NAJEEB da HANNAH😳nima dake gefe ido na zaro ina kallon su.,

Najeeb ji yayi kamar an buga mai guduma akansa wai ko daddy yasan abinda yake fada kuwaπŸ™Š
Murmushi mummy tayi tace masha Allah hakan yayi kyau Allah ya sanya alkhairi ya kaimu lkcn

"Kallon Hannah daddy yayi datayi kasake tana tunanin wai ita Hannah ko kuma wata daban ake nufi"'

Toh uwata kinji irin alqawarin da mukayi da mahaifinki kafin rasuwarshi ina fatan xaki mana biyayya.

Mummy ta kalla sannan ta kalli aneesa dake ta faman murmushi ta juya gun uban gayyar fuskar nan kamar an aiko masa da sakon mutuwa "

"Nifa daddy ban isa aure ba ta fada kamar xatai kuka .dariya sukayi gaba dayansu banda najeeb da kansa ke kasa

Toh banda abinki uwata shekarunki nawa kina fa cikin 17yrs daddy ya fada yana dariya. Toh daddy makarantar dana fara fa?
Karki damu indai makarantace xaki cigaba agidanki kuma ba dogon lkc xa,a dauka ba dan su yaya lawal tuni suka fara min maganar aurar dake tashi kuje Allah yai maku albarka,
Mikewa sukayi ita da aneesa suka amsa da ameen sannan suka bar wajen".

" wajen najeeb ya juyo daya koma tamkar an dasashi yace"

"Ya bakace komi ba?

Sai a sannan ya dago ya kalle shi da idanuwansa da suka canja color*

Ahankali yace pls "daddy Dan Allah karka hada wannan auren.da mamaki suke dubanshi mummy tace ko xamu iya sanin dalili?

Jijjiga kai ya fara
haba daddy ya xa,ayi kamar ni in auri wannan yaabinda?
Murmushi daddy yayi yace meye aibunta? " yar uwarkace fah

Nidai gsky bana sonta afusace daddy yace ko kana so ko baka so sai ka aure ta kaji na gaya maka aure ba fashi tun wuri ka fara shiri
Afusace yabar wajen."

Mummy ya kalla yace mummy kina jin fa abinda daddy yake fada fa Dan Allah kiyi wani Abu akai .

Hmmm kasan halin daddyn Ku sarai idan ya fadi magana ta Riga ta xauna don haka karma ka fara yin gardama kuma ni banga illar yarinyar nan ba nasan dai bai wuce kace bata waye ba wannan kuma ka bata lkc kadan sai kayi mamaki da haka muka daukota? "*

Haba mummy, haba mummy pls help me mana ya fada kamar xai saki kuka
Mikewa tayi ta bar wajen.binta yayi da kallo yana jin kamar ya fasa ihu.........***





Ummu hananπŸ™‹πŸ»
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANI
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam(ummu hanan)


15_20

Gaba ya bude ya shiga yana ta faman yatsina fuska,. direba yaja suka tafi da sun had a ido da Hannah sai ya harareta sai dai ta murguda masa baki ta kauda kanta da haka har Bacci ya dauketa.


Sai bayan Maghreb suka iso gida aneesa ce ta tashi Hannah daga baccin da take Hannah ki tashi mun iso shi kam najeeb dama suna parking ya fice ya nufi side dinshi.

"Tashi tayi tana mutstsuke ido tace kai amma fah munyi sauri
" dariya sukayi mummy tace dama kina barci ai dole kiga anyi sauri"

Suna shiga falon mummy tace aneesa kuje da ita kuyi wanka ki bata kaya tasa.,

"Toh mummy"

Kamo hannun Hannah tayi data saki baki tana ta faman kalle_kalle suka nufi dakinta.,

Mummy ma wajenta ta nufa wanka tayi sannan tayi sallah fitowa tayi ta shiga kitchen dan samar musu abinda xasu ci.

Suna shiga Hannah ta xaro ido😳 ynx aneesa wannan dakinki ne?dariya aneesa tayi taxe eh mana dakina ne amma daga yau ya xama dakinmu,."*

Bed din ta nufa ta xauna tana shafawa ta6 gsky "yan birni kuna jin dadinku aneesa tace ynx ki tashi ga bathroom nan ki shiga ki wanka ki alwala sai kixo ki sallah tare suka shiga ta nuna mata yadda xatai amfani da komi sannan ta fito "*

Hannah kam ta6e_ta6e kawai take a toilet din taki yin ma abinda ya shigar da ita sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi wankan sai faman wasa da ruwa take.
bayan ta gama tayi alwala ta fito.,

Dariya tayi tace kaiii wllh bandakinnan akwai dadin wanka kuna shan dadinku.murmushi aneesa tayi tare da girgixa kai tace ga kaya nan ki shirya nima bari inje inyi wankan ". Kayan ta dauka ta duba gown ce ta atamfa purple sai dan karamin veil shima purple sawa tayi ta ta daure kanta tamau da veil din😁 hijab ta saka ta dauki prayer mat ta shimfida ta tada sallah.

Aneesa itama tana fitowa ta saka kayanta tasa ka ta saka hijab ta tada sallah
Bayan sun idar suka cire hijaban sai asannan aneesa ta ga daurin da Hannah tayi wa kanta dariya tayi tace

" oh Hannah wannan fa yafashi xaki yi kin tashi kin kulle kai kamar kullin magani? yatsina fuska tayi ta ce ke ni baxan iya yafe _yafen nan ba gajiya xanyi .
Toh ai shikenan tashi muje falo mikewa sukayi suka fito

Xo muje kitchen mummy na can shiga sukayi suka sameta har ta gama girkin da yake ba mai whl bane jollof ne na taliya da kayan lambu sannu da aiki mummy

"Yawwa"

Aneesa dauki abincin kikai kan dining toh Hannah kam nanma banda kalle,kalle ba abinda take,....

Aneesa tana shigowa mummy tace je ki kirawo yayanki,.amsawa tai ta juya xata fita suka ci karo abakin kofa juyowa tayi tace gashi nan ma shigowa yayi cikin takunsa na Kasai ta kusa da mummy ya tsaya yace "wllh mummy yunwa nakeji ya fada cike da shagwa6a
Ta gefen ido Hannah ta kalleshi yatsina fuska tayi tare da ta6e baki cikin ranta tace"

*"Dan Allah dubeshi babba dashi yana wani yin shagwa6a tsaki taja ahankali taci gaba da ta6e ta6en da takeyi.

"Uhumm ba dole kaji yunwa ba mummy ta fada tana wanke hannunta a sink.

Kaje dining ga abinci can an gama.
Fita yayi su dinma fitar sukayi suka nufi dining.
Xama sukayi aneesa ce tayi serving dinsu suka fara chi.

Cike da yanga yake cin abincin kamar bayaso kadan yaci ya Mike yana goge bakinsa da tissue"

"*ba dai har ka koshi ba? Mummy ta tambayeshi
Na koshi mummy

Duk fadar yunwar da kake? Murmushi yadan yi yace "

"Allah kuwa mummy na koshi
Toh ai shikenan

sallama yayi mata ya fice don yau ko hirar da yake tsayawa suyi da mummy baxai tsaya ba saboda wannan yarinyar
Ita kam Hannah sai xiri kawai take anji deliciousπŸ˜…
Sai da ta cika cikin ta taf sannan ta hakura."

"*bayan sun gama suka dawo nan cikin falo suna kallo suna hira .wajen karfe tara da rabi daddy ya dawo sannu da xuwa sukayi masa.
Murmushi yayi yace a,a uwata dake aka taho ne ?eh baba mummy tace ai na samu yaya Laure ta bar mana ita xata fara makaranta.'"
Kada Kai yayi yace gsky naji dadi sosai hakan yayi kyau sai a kaita tasuu aneesa............





Ummu hananπŸ™‹πŸ»
[1/18, 10:57 AM] M Ummu Hnan: πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§
DANA SANl
πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§πŸ’¦πŸ’§

Written by
Maryam (
Ummu hanan)


25_30

*Mikewa yayi jikinsa asanyaye ya nufi dakinsa kan bed dinshi ya fada tare da lumshe ido hoton yarinyar yake ganowa wai amatsayin matarsa.....ta ya ma xai iya xaman aure da ita.
Kai gsky da sake "yan mata da yawa masu aji wadanda suka amsa sunansu.....suna masa tayin soyayya" amma sam basa gabanshi sai kuma ynx ya 6ige da auren wannan local girl din?.......to mai xai hana ya kira ta yaja mata kunne ya umarceta data fadawa su daddy bata son auren yasan dai daddy...... baxai tilasta ta ba"'....dunkule hannunsa yayi ya daga sama tare da fadin ".....yes domin ya aminta da shawarar da xuciyarshi tabashi %.

*" washegari mummy ta fita bikin "yar kawarta don haka Hannah da aneesa ne kawai agidan...." hudu da rabi najeeb ya dawo daga office... Wanka ya shiga yayi ya sa 3qtr red color.. da riga green color mai yankakken hannu,....


Main falo ya shigo ....yaga ba kowa"
"Xama yayi kan kujera tare da sauke numfashi......" Aneesa ce ta fito daga kitchen ta nufi dakinsu.

"...ke zo nan.."..... da sauri ta juyo dan bata san yana falon ba.xuwa tayi ta dan durkusa tace ...gani yah najeeb saida ya gama shan kamshin shi sannan yace"..... Ina wannan yarinyar take?…wai Hannah?
eh mana

Tana daki mikewa yayi yace kice mata ta sameni Adakina
Kai ta girgixa tace"*



" toh ta amsa tabar gurin shima barin wajen yayi.
Agaban mirror ta samu Hannah na kwalliyar data saba,yatsina fuska tayi tace"oh my sis yaushe xaki daina wannan kwalliyar ne ....haba mana

"Nidai ki kyaleni nafi ganin kyanta....gsky a,a yah najeeb na kira don haka dole agoge wannan kwalliyar.
Kafin tai mgn har ta fara goge mata light makeup tayi mata sosai tayi kyau.

Wow matar yah najeeb kin ganki kuwa?.....tsaki taja tace karki kara cemin matarsa tunda dai ba,a daura ba.toh naji sis tashi ki saka wasu kayan,.....in canxa fah kikace?ni babu kayan daxan canxa me wadannan sukayi.....dakyar ta yadda xata saka wasu.wardrobe ta bude ta dauko mata riga da siket na material light blue da bakin Vail ta saka .....masha Allah abinda na fada kenan dana kalle ta. Fita sukayi ta rakata kofar shiga dakin sannan ta juyo.......

*da sallama ta shiga yana hakimce kan kujera ya dora kafa daya kan daya sai girgixa su yake kansa na kasa yana danne2 a system dinshi..bai dago ba bare ya kalle ta...." ance kana kirana ta fada tana yatsina fuska😁

Ba,a koya miki gaisuwa ba agarinku ya fada ba tare daya dago kaiba.turo baki tayi tace ina yini banxa yayi mata yaci gaba da abinda yake.saida ta dade atsaye bai kulata ba ."tuni kafafuwanta suka fara tsami,."yah najeeb na gaji fah ta fada kamar xatai ..kuka..system din ya rufe sai sannan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5

1 Comments On DANA SANI
avatar
ishaq-abdulhamid

10 months ago

Reply

I love the book

Please Login or Register in order to submit comment