Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tunda akai rasuwar nan wannan yarinyar banga tanuna damuwarta sosai akai bah,Anya kuwa jannat"

"Mama kenan ya za,ai tadamu sosai tunda ba ubanta bane, ai tazata damuba"
Cewar Zainab,

"Murmushi tayi tace sai nadawo tafice don idan tace magana daza tsaya yi masu, zasu b'ata Mata lokaci"

Taxi tashiga tagaya Mai inda zai kaita,
Sunyi tafiya Mai nisa kafin su isa wajen,
Tabiyashi ta k'arasa wajen waje tasamu ta zauna,
Wayarta taciro tafara kiransa,
Taji ance basai kinkiraba mun iso tare,

Murmushi tayi maikyau,
"Na d'auka ko madam tarik'eka ai"

Zama yayi yace"Ah haba dai ai tasan abunda zanzo nayi Mai muhimmancine dole tasako ni"

Mekike buk'ata akawo maki,
"Wallahi nagode koruwa bazan shaba,"

Shikenan tunda bazaki kici komiba yayi magana akan abashi lemo da Chip's,
Aka kawo mashi"inajin ka malam jabeer"

Zama yagyara yace"am jannat kinsan dai wannan case d'in, sannan kinga irin abubuwan dasuka faru akotu, and kinga hukuncin da kotu tayanke akan d'an uwana kuma aminina"

"Agaskiya jannat bazan iya jure ganin Adam cikin halin dayake cikiba,don nikad'ai garai inason ganin yacigaba da rayuwarsa Mai kyau kamar yanda nakeyi,
Don haka ina fatan zansamu gogon baya dakuma taimakon ki akan wannan case"

"Ajiyar zuciya tayi tace jabeer,zanyi wannan aikin badan komai ba saidon bayyanar gaskiyar cewar bashine yayi bah,wad'anda Sukai sunyi ne don wani cikar burin su,bazanyi don Adam ba, zanyi don Allah don haka insha Allah daga yau zancigaba da bincikena kaikuma abunda zakai, shine kafara fitar da jaridar d'aukaka k'ara atleast zuwa gobe da yamma jaridar tafito tagama kewaye gari,
Sannan kawuce Abuja don Isar da k'arar zasuba takardar sammaci kazo gidanmu kabasu,"

"Sannan dole zangana da shi Abokin naka, Kama sanar dashi babu batun boye b'oye,idan har yace zaiyi haiding wasu sirrika dasuka shafi wannan case d'in to gaskiya bana tunanin zamuyi nasara akai,"

"Haka ne jannat mungode Allah yasaka da alkairi,
Kamar nawa kike ganin zamu biyaki"

"Murmushi tayi tad'an kawar dakai tace sai angama sharia, sannan"

"Shikenan Allah yabamu Sa,a yanzu bari nawuce gidan radio d'in sai munyi waya,
Yawwa zuwa yaushe zaki gana da shi Adam d'in"

"Tace sai antsayar da lokacin shiga kotun sannna"

"OK yayi, muje nasaukeki idan babu damuwa"

"To nagode"
Tare suka jera suka fita har mota shiya bud'e Mata gaba tashiga kafin yazagaya yatada subar wajen.

Har kofar get di'n gidan yasauke ta,
Tayi mashi godiya sannan tawuce cikin gidan lokacin angama sallar mangaruba,

Babu kowa falon shiyasa tawuce d'akinta salin alin,
Tayi sallarta tare da rok'on Allah yabata Sa,a akan niyyarta,

Tunani tashiga yi akan binciken ta agidan,
Tatab'a jin wata hayaniya tsakanin mama da dady tun yana raye,
Idan bazata manta bah taji mama nacewa,

_Alhaji inajin tsoro fah Allura nashirin tono galma, gaskiya nagaji, nagaji fah kullum cikin zullumi nake kwana nake tashi, idan wannan asirin yatonu yakakeson muyi,dawane ido zamu kalli mutane,bama wannan bah yazamuyi da jannat yau saura sati biyu bikinta..........._

"Mai yasa basu idasa ba naji, Anya mama batanada masaniya da mutuwar sagir bah,idan bahaka ba meyasa take fad'an saura sati biyu bikina mezasu fad'aman.......... Tabbas sunada saka hannu wajen sace sagir da kuma mutuwarsa,

Innalillahi wa inna ilaihir raju'un......
Dole zanyi binciken abunda yake faruwa cikin gidan nan, akwai wani Abu dole akwai wani sirrin da mama kad'ai tasanshi.

Kamar an tsikareta tatashi tafito daga d'akin tafito falo,
Mama ce da mubee ta na cin abinci,
"Mama sannu da gida"
Wani kallon wulakanci tayi Mata kafin tace"ke nafa gaji da ganinki cikin gidan nan, kizo kikoma k'auyenku haka nan tunda bakida gadon Alh"

Murmushi tayi tace"nasani mama kiyi hakuri kid'an bani lokaci zankoma insha Allah"

"Dadai yafi maki, don naga kamar Neman gyara zama kike acikin gidan"

Batasake cewa komiba tazauna ta na kallo alhalin ba kallon ne takeba tunanin yanda zatayi tashiga d'akin mama tayi binciken da take sonyi,

Zainab tafito tana cewa"mama wallahi d'akin ki yakoma na k'azamai yafi wata ba,a yi mashi kwalema bah,kinga yanda k'ura ta b'ata kasan gadon dak'er nasamu na ga inda kikai aji.............
Shiru tayi ganin jannat,

Itakuwa kar take karkard'e kunnenta taji komai,
Saitayi kamar batajiba tamaida hankalinta wajen TV
Basarwa tayi tanemi waje tazauna.

Hirar suka canza har mubee tagama tatashi takai plet d'in kitchen,
Tadawo tace"mama nifa ina tunanin ciki garan"

Wata fad'uwar gaba ce tasamu mamar, tadafe kirji"nashiga uku na ni gaje,karya kike mubee neman hanyar dazaki kusanta kanki da wancan d'an fashin kike ko, to wallahi baki isaba, karya kike wallahi koshine zubar dashege zanyi"

"Fashewa tayi da kuka wallahi babu Wanda zai zubar man da ciki inason kayana,"

"Zainab tace mama karewar karya gobe muyi sabko mukaita asibiti, idan ma shine ayi duk yanda za,ai azubar da shege"

Wani sanyi dad'i jannat taji don zata samu damar yin binciken ta yanda take so,

Mama tace haka za,ai Zainab don bazan had'a zuria da d'an fashi bah,

Haka sukaita maganganunsu tana masu kuka ita babu wanda zai rabata da cikinta,
Anrabata da masoyinta tak'arfi da yaji yanzu kuma d'an nnashi ma rabasu za,ai to wallahi bata yarda,

Nan jannat ta sake gasgata cewar babu makawa Adam bashine yayi kisan ba,
Sunsan Wanda yayi ko ita mubee d'in batasani bah,

Murmushi tayi cikin ranta tace komi zanbayya na insha Allah.

Tatafi kitchen don zuba abinci.


*MUHADU PAGE NAGABA*

TAKUCE MAMAN MUHSEN.

~*(MAGAJIYAR KAINUWA)*~✍🏻✍🏻
[1/10, 11:55 AM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: 🎀🎀🎀🎀
*AKWAI BANBAM CI*
🎀🎀🎀🎀



*_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*
_*(MRS BB)*_

_*{MAGAJIYAR KAINUWA}*_


*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


~BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM~.

11&12.

Karfe takwas suka yi sabko sukanufi asibiti da mubeee,
Don hankalin mamar Yatashi batason zargin cikin yatabbata,

Hakan yabawa jannat dama tashiga d'akin Dady,
Don tasan anan zata fara samun duk wata hujjar ta datake so,
Duk wata durowa dake d'akin saida ta bincikata taduba nan taduba nan,
Amman Allah baisa taga wata Takarda Mai muhimmancin abunda takeso bah,
Cikin wadrop din kayansa takoma,
Nan ma tacigaba da bincikawa tanayi tana gyarawa,

Can karshen kayansa yaga wani akwati,
Bakowa zai iya ganinsaba saboda anyi ma shi kyakkyawar ajiya,
Amma fah kulle yake gam da alamun saida makulli za,a iya bud'eshi.

Duk tayi zufa tsoro take kar sudawo tashiga neman makullin,
Amma batasamu ba ganin lokaci na niyyar kure Mata yasaka ta d'auko shi tatafi d'akinta tayi mashi boyon da babu Wanda zai iya tunanin Sa awajen,

D'akin mama tashiga babu inda tayiwa tsinke sai kasan gadonta,
Tabbas yayi daud'a amman haka jannat ta d'age katifar sama,
Wata bakar ledace viva tabincikata envelop ce babba aciki,
Acikin emvlop din taladdune aciki bata tsaya dubawa bah,
Tamaida katifar,
Tagyara gadon kamar ba,atab'ata ba,

Aguje takoma d'akinta tayi Mata wani mahaukacin boyo zuciyarta ta na bugawa,
Tabbas dole tazo tabar gidan tun kafin sunemi kayansu suzargeta,
Ajiyarsu nan wajenta had'arine dole tanemi jabeer tabashi su ajiya,
To yanzu ina zansamu makullin wannan akwatin,
Dole saida makullinsa zai bud'u.

Wayarta tad'auko takira jabeer,
Kamar yanajira yad'auka bata jira sungaisaba tace"jabeer inason ganinka yanzu ina zamu had'u,
Emergency ne don Allah"

"Nima dama kiranki Zan ingaya maki, ansamu buga jaridar,anfara fitar da ita yanzu haka,
Zuwa anjima zanbi jirgi zuwa abuja"

"Jabeer kana ina yanzu"

"Ina gidana yanzu haka idan babu damuwa kisaman agidan,"

"Kituroman adress d'in yanzu ganinan"

Takashe wayar, jikkarta tad'auko tasaka su ciki,
Tashiga tawatso ruwa shaf shaf tashirya abaya ma tasaka har kasa, dama kuma tana yawan sakawa,
Tafito takulle dakin tatafi,
Maigadi tacewa idan su mama sundawo kace masu naje indawo duk Wanda yazo kace bakowa gidan"

Tatari taxi tatafi gabanta fad'uwa yake batason suzargeta tun yanzu,
Tafison sai takoma hunkuy wajen iyayenta sannan kami zaifaru yafaru,

Har bakin gidan yasauketa babban gidane sosai,
Yahad'u sosai batai mamaki bah,saboda taga babu laifi Mai kud'ine sosai,

Shiyafito yashigo da ita don maigadin baya nan,
Har falonsa dayasha kayan alatu yakaita zama tayi yana niyyar kawo Mata shayi,
Tace "jabeer bazan sha komiba sauri nake wasu evidence nasamu zasuyi mana anmani sosai,
Gasunan zamansu wajena jabeer akwai matsala,
Kakula dasu sune zasu saka muyi nasara insha Allah."

Ansa yay yana mamaki yace"kinyi kokari Allah yatai maka,amman ina makullin akwatin kobandashi"

"Wallahi jabeer shine bansamuba kuma dole saida makulinsa saboda kaga ba irin sauran akwatin nan bane,
Da alama dady yayi ajiya Mai muhimmanci aciki, nasan komi keciki, zai iya warware wannan kullalliyar,zanyi k'ok'ari wajen samo keys din"

"Yace Allah yabada Sa,ar hakan"

"Tace Amen, cikin satin nan zankoma garinmu wajen iyayena, dama zaman dady nake kuma baya raye, sun matsa saina barmasu gidansu,nima kuma tafiyar zatafiye kwanciyar hankali"

"Bari Natai banason sudawo ban nan zasu zargi wani abu,
Bakamar idan sukaga jaridar daukaka karar,"

Rakota yayi har bakin get,
Yatarar Mata Mai napep yabiya kudin Sukai sallama tatafi,
Addua take Allah Yatai maketa ta isa basudawo bah"

Cikin ikon Allah har ta isa basu dawo bah,
Don har ta gama hada masu abincin rana sannan suka dawo.

Afalo suka zube suna maida yanda akai,
Mama ce kecewa wallahi garama kishiga taitayinki yarinya,
Wallahi saina saka anrabaki dashi,
Allah yakaimu lokacin girman Sa ya isa markadewa,"

Anan jannat tasan cewar akwai cikin baidai isa zubar wabane kawai,
Tajinjina rashin imani na mama,

Ita takawo masu abincin suna ci suna tsine Mata albarka,
Mama tace yaushe kika shiriya tafiya kauyenku,

"Murmushi tayi tace mama kin k'agu natai ko"

"Tace eh na k'agu banson ganinki agidan, don banson ma araba gadon kinanan"

"Kiyi Hakuri mama zuwa jibi insha Allah zantafi,amman nasan zaku neman, dole mah"

Zainab tace muyi maki me, wallahi bamuda buk'atar komi awajenki,

Murmushin tayi tace anty Zainab wallahi zaku neman kibar cewa baku buk'utar komi, uhm shikenan nad'uka zakuyi kewata ai"

Tsaki sukaja basu sake bi takanta bah,
Itako cikin ranta dariya take masu don tasan dole zasu nemeta idan suka rasa abunda suka ajiye.

Dad dare sunata kallo afalo,
Sama,ilah yashigo,
Rai b'ace yana huci yace mama wai kunsan abunda yake faruwa kuwa,

"Azabure tatashi lafiya sama meyake faruwa, badai wani kaje kajawo fad'aba,"

"Yo mama wane irin fad'a ai idan shine dasauki,
Wai kinsan menagani jaridu ke yawo agari tun safe akan daukaka karar mijin mubee,
Da akai zuwa kotun abuja,

"Cikin bala,i da tashin hankali Zainab tace wane shegen ne, wane Dan iskan ne yayi mana haka,so ake atona mana asiii........."

Faske Mata baki mama tayi don ta na neman sakin layi gaban mubee da jannat,
Don idan zasuyi magan ganunsu basu bari suji,

"Yace waye zaihaka daya wuce wan dan iskan jabeer d'in"

"Babbar bu........kayyasa wakace jabeer....."

*TAUFAH WANNAN IRIN ASHARIA MAMA*

KARKUDAMU FANS MUHAD'U PAGE NAGABA.

TAKUCE MAMAN MUHSEN.✍🏻✍🏻

Comment and share.
[1/12, 1:30 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: 🔴🔴🔴
🔴🔴🔴🔴
*RAYUWAR AMEERAH*


*_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*

_*(MRS BB)*_

_*[MAGAJIYAR KAINUWA]*_

*_LITATTAFAN MARUBUCIYAR...._*

RAI DA BURI
_(yake mutuwa)_
SAFAH DA MARWAH
SAINA DAUKI FANSA
RAYUWAR AMEERAH
AND NOW
A KWAI BAMBANCI.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

12/1/2020.

13&14.

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM

"Wallahi mama shine ai don ma kuga zahiri yasa yasiyo jaridar, nataho da ita kugani.
Ya mika masu yana cewa saboda bala,I nera dubu haka zaka siyeta,"

Jikin mama har rawa yake take duba jaridar,
Bakinta sai rawa yake takasa fad'ar wani abun,
Zubewa tayi cikin kujera takasa cewa komi,
Don inhar tacigaba da magana to babu makawa zata fallasa abunda yake b'oye.

Zainab takwalawa mubee kira ta na d'aki,
Tafito ta na turo baki don taji abunda suke tattaunawa akai,[1/14, 12:12 PM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: 🎀🎀🎀🎀
*AKWAI BAMBANCI*
🎀🎀🎀🎀


*_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*
_*(MRS BB)*_

_*[MAGAJIYAR KAINUWA]*_

_*LITATTAFAN MARUBUCIYAR....*_

RAI DA BURI
_(yake mutuwa)_
SAFAH DA MARWAH
SAINA DAUKI FANSA
A KWAI BAMBAN CI
AND NOW
RAYUWAR AMEERAH.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

15&16.

"Ka tabbatar gidan su mufidar kakaita, sannan kasan yadda kayi kagano inda tayi daga nan"

"Sama kafita idona inaganin take takenka akan wannan tsigaggar yarinyar,Zan iyayin komi don rufuwar asirina, kasaman ido kanta kana jina"

"Wai mama zargin me kakewa jannat, bayan batasan komai akaiba,ki kwantar da hankalinki jannat bazata yi Abunda kike tunani bah.......,
"Kai dallah rufeman baki, mekasani akan haka nadai gaya maka kasaman ido sosai"

"Shikenan sai na dawo"

Yafita yasamu jannat bakin mota tanaji ransa,
Murmushi yake Mata Mai kyau Wanda ita tuni tagano inda yanufa,
Da ace baifito daga wannan ahalinba Zan iya amunce masa saboda baisara komai da mace kesoba,

Shiga tayi taja sukatai,
Janta yayi tayi da hira har sukaje gidan,
Bakin get din gidan ya sauketa,
"Tace nagode sosai yaya sama"

Murmushi yayi yace"bakida matsala idan kintashi tafiya kikirani zanzo na d'aukeki"

"Shikenan idan naga banyi dareba zankiraka byy tad'aga mashi hannu"

Saida tahango yawuce sannan tashiga,
Agurguje tashiga suka gaisa da maman sannan tashiga wajen qawar tata,
"Lalalala jannat kece yau shigo shigo, dama inacewa kwana biyu bamu had'uba"

"Mufee babu lokacin hira yanzu don inada babban uziri gabana yanzu ma fakewa nayi danan d'in, idan nakoma gida zankiraki don gobe zankoma hunkuy"

"Gobe kuma, haba jannat meyayi zafi har haka,kuma shine sai yanzu kike gayaman"

"Kiyi hakuri qawata wallahi inacikin wata chakwakiya,akan shariar rasuwar dadyne anyanke hukunci wanda hakan na shine dai dai bah,shine muka d'aukaka k'ara zuwa kotun Abuja,
Yanzu haka wajen Adam d'in zanje can prison"

Cikin mamaki tace"Amman jannat bakida hankali,Wanda yakashe wan babanki zaki nemi cetowa,shin saboda me kikehaka kingani matarsa ma tabarsa saboda haka saike da bakida alk'a dashi mekike shirin aikatawa"

"Kinga mufee, wannan A bun fah akwai wata mak'ark'shiya aciki saida na anshi case d'in na tabbatar dahaka, kedai tunda kikaga har na anshi case d'in kisaka ido kiyi kallo,fatan zakuzo keda mama"

"Dole ne Ai wannan Karon ne fah karonki nafarko, zanso inga yanda zakiyi nasara Allah yatai maka"

Wayarta tayi k'ara,
Jabeer ne dayake amota tagaya Mai inda zaisameta,
Mikewa tayi"mufee gashinan Wanda muke binciken tare, zamuje mudawo don ansaka man mat akan tsaro,
Sai nadawo"

Tara kota har bakin motar sannan sukatai,
"Meyafaru naga text d'inki d'azu"

"Uhmm kaidai bari, wallahi mutanen gidanmu sunfara zargina,don saida nayi dubara Amman duk da haka ban tsirabah,"

"Allah yatsare to, yanzu kenan goben dole zakitai"

"Dole na kuwa don idan suka ganoni ina cikin matsala don mama zata iyayin komai akan ganin bantona masu asiriba"

"Allah yakaimu"

Sun isa wajen hakanan taji gabanta yana fad'uwa,
Tun bayau bah duk sanda zata had'u da Adam sai gabanta yashiga fad'uwa,
Duk sanda zaizo zance wajen mubee itace take kai mashi snacks da lemo,
Jikinta har rawa yake idan zata shiga dakin, saboda aduk sanda suka had'a ido wannan kallon wulakancin dayake Mata shiyake tsaya mata arai,

Lumshe ido tayi tanajin gabanta yana tsananta fad'uwa,
Magana jabeer yake ma Mai kula dasu Wanda yasamu ne rannan dayazo,
Yauma kud'in yabashi yatafi don zuwarmasu dashi,

Kallonta yayi yaga idonta alumshe,
Yace"yadai barrister"

Bud'e idon tayi ta na murmushi "mekagani engineer"

"Kin Rama kenan, naga kin yi shiru kinrufe ido mekike tunani"

"Babu komi engineer, naji gabana yana fad'uwane shine nake addua"

"Subhanallahi lafiya dai ko"

"Lafiya lau insha Allah"

Shiru Sukai hango shi dasukai,
Gabanta yatsananta duka,
Adam ne haka shine yakoma kamar wani almajiri,Kai ko almajiri yafi karfin haka,
Innalillahi acikin sati biyu yakoma haka,sanda akai shariar baikai haka lalacewa ba,
Tabdijam, Adam din Mai gayu Mai isa da tak'ama Mai shegen miskilamcin tsiya,
Idan yawuceka dole saika lumshe ido don tsananin kamshin turarens,
Komai nashi Mai class ne,
Ko awancen lokacin bakomai yake burgeta dashiba illah wankanshi ya iya saka sutura, ko ko tsumma yasa kyau yake,
Shine yazama haka yarame yayi wani irin bak'i,
Adam d'in da har wani Ja yake saboda hasken sa Amman yanzu ji yanda yakoma, kamar k'warangwal
Jitai idonta yaciko da k'wallah,
Bata tabajin makamancin irin haka gameda Adam bah sai yau,
Bai tab'ata bata tausayi bah sai yau,
Saida tayi jarumtar gaske kafin tasamu tamaida k'wallar,

Suduka shiru Sukai,
Don Adam wani shock yakamashi ganin yarinyar da baitab'a zato bah agabansa,
Meyakawo jannat wajensa,
Kardai jabeer itace ya d'aukar mashi matsayin lawyer d'insa,

Yakasa kallonta don kunyarta yakeji bilhakki dagaskiya,
Jabeer yayi gyaran murya yace"Adam kullum k'ara lalacewa kake, wai wane irin aikine Mai wahala haka suke saka, basu tausayinka kalli yanda kakoma,
Adam kakakuwa ganka,
Wallahi ko zanyi yawo babu kaya sai natabbatar kabar wajen nan."

"Shikanshi kwallar ce cike da idonsa yace ina kuka had'u da jannat"

Jabeer ya kalleta ta sadda Kai k'asa,
Yace"itace wacce zata taimaka mana wajen ganin munkub'utar dakai, yanzu ma tazone don Ku tattauna,jannat yakamata kuyi maganar dazakuyi saboda kurewar lokaci,"

Jakarta tafiddo tadauko jotter da biro,
Tad'an zauna saman bencin dake kusadasu
Bazata iya kallon sabah zuciyarta zata karye,
Cikin muryanta datayi sanyi k'alau tace"labarin rayuwarka zakaban Amman kata k'ata saboda lokaci,"

Baiyi musubah yashiga bata labarin Abubunwan dasuka faru da rayuwarsa Amman hak'ikanin gaskiya yayi Mata hiding din wasu dayawa,
Yabari sai anje kotun,

Tad'auki abubuwa dayawa sannan tace mashi,
"Me dady yafad'a kafin yarasu"

"Yagaya man inda ya ajiye wasu muhimman abubuwanshi dazasuyi man anfani, sannan yagaya man inhar na samu nasarar d'auko wannan shaidun to zansami komi aciki,
Yaceman yana cikin d'akinsa cikin drower kayanshi.........
Cikin sauri tajiyo ta na kallonshi tace"Tabbas shine akwatin Dana d'auko d'akin dadyn,amman nanemi makullinsa bansamu bah,

"Yana wajena zanba jabeer shi yana tare dani, don banyarda dakowa bah balle nabashi,"

Jinjina Kai jabeer yayi yace"yanzu komai yazo dasauki,zakitafi gida hankalinki kwance saijiran ranar shiga kotu"

Kallon ta Adam yayi yace"jannat meyafaru ne agidan zaki tafi"

Kanta akasa tace"saboda gudun karsu lahanta ni, saboda sunfara zargina akan abunda ya far u,
Yanzu ne Nagane bakai ne kayi abunda ake zarginaba cikin gidan nan akwai abunda suke b'oyewa,
Sunada masaniyar wanda yayi kisan, lura da mama tayi kamar nasaka masu Idone yasaka tafara korata, akan in tattara nakoma kauyenmu,don gudun Karna to na masu asiri,
Ban tabbatar da cewa mama nada saka hannu cikim kisan bah sai dana samu wasu takaddu anmasu wani irin boyo adakinta,nakara yarda zurma ka akai"

Sadda Kai yayi yana jin wata wutar tsanar mubee da mamanta takara Kama shi,
"Yace yanzu mubee tasan wannan tayi man k'azafi saboda cikar burinsu,lallai nayarda mubeenat bata kaunata,"

"Mubee batasan abunda sukeyi bah,sundai sakata tayine itakuma tabiyema son zuciyarsu tasaka ka cikin wannan halin,
Kuma tayi nadama"

"Mutumen yadawo yace lokaci yayi fah,yakamata akoma dashi"

Kallon ta yayi yanason yabata hakuri irin Abubuwan da yaringa yi Mata agidan,
Yakasa yace wa jabeer"Amman yakamata ka kaita gidan goben saboda tsaron hanya"

"Yace insha Allah Adam, sai na sake dawowa kan ranar shiga kotun"

Haka Sukai sallama dashi suka tafi,
Zuciyar jannat babu dad'i rayuwar da Adam d'in yayi itace taketa Mata yawo akai,
Ta na jin babu dad'i cikin zuciyarta.

Batajira sama yazo yadauketa ba tatafi gida,
Binta Sukai da kallo cike da tuhuma,
Saida gabanta yafad'i don basu tab'ata Mata irin haka bah,

Tunda tashiga takasa fitowa,
Saidai duk wani motsinsu ta na jin shi,
Saida taji yunwa zata kassarata sannan tafito tashiga kitchen d'in,

Mama tagani,
Wani kallo tayi Mata tace"wai karfe nawa zaki tai ne goben"

"Cikin tsoro tace mama safi ya zanyi wajen takwas nabar kano insha Allah"

Tsaki mamar tayi tajuya tabar kitchen d'in,
Mamaki da faduwar gaba suka sako jannat gaba,
Daker tazuba abincin tafito,
Jikinta yakasa saki rawa yake Mata,
Har tagifta Zara wuce d'akin dakinta,
Tajiyo k'us k'us gabanta ya sake fad'uwa ta kasa kunnenta donjin meke faruwa,

"Mama wallahi itace zata d'aukesu idan ba itaba ubanwa yake zaryar fita, wallahi nalura da ita akwai munafurcin datake yi aboye"

Gabanta yabada dassss kardai sungano ta,
Nashiga uku ni jannat,
Mama taji ta na cewa"nasan abunda zanyi wayar ta tad'auko tashiga yin Kira zuwa can taji tafara magana,

Jannat tayi saurin kunna recording,
Jikinta yana rawa
"Barau Inason daya daga cikin yaranka yayi man maganin wata yarinya,
Gobe karfe takwas kabi hanyar kaduna, inason a batar mun da jannat yarinyar gidana ce takeson to na man asiri,
Bana tunanin zata bi motar haya,
Banason ta da rai kasanya tabar duniyar don nema take tatona man asiri"

Aguje takoma d'akinta jikinta rawa yakawai yake hawaye sunb'ata Mata fuska,
Wayar jabeer takira ta na kuka,
Kewaye tashiga tafashe da kuka bayan ya dauka,
Cikin tashin hankali take gaya mashi halin da ake ciki,

"Kwantar da hankalinki nasan abunda zanyi, karkiyi yunkurin guduwa kibari har lokacin tafiyar yayi,
Zanzo hargidan nad'aukeki alokacin zanbasu takardar sammacin,
Akwai abunda nakeson nayi, kinatsu insha Allah babu abunda suka isa suyi maki,
Kiman alkawarin zaki natsu tunda ina nan karkidamu kinjiko,
Zankula dake kamar yanda Adam ya bukata"

Ya lallasheta sosai tasamu natsuwa sosai Sukai sallama,

*KUKACENCE DANI TAKUCE MAMAN MUHSEEN*

COMMENT AND SHARE PLSS

_MAGAJIYAR KAINUWA CE_😉
[1/19, 11:03 AM] MAGAJIYAR KAINUWA😄: 🎀🎀🎀🎀
*AKWAI BAMBANCI*
🎀🎀🎀🎀


*_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*
_*(MRS BB)*_

_*[MAGAJIYAR KAINUWA]*_

_*LITATTAFAN MARUBUCIYAR....*_

RAI DA BURI
_(yake mutuwa)_
SAFAH DA MARWAH
SAINA DAUKI FANSA
A KWAI BAMBAN CI
AND NOW
RAYUWAR AMEERAH.


*بسم الله الرحمن الرحيم*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

19/1/202.

17&18.

Wannan rana bata yi wani bacci bah,
Data fara sai tafarka saboda ta na ganin kamar har nan zasuzo su kasheta.

Ana kiran Sallar farko ta asuba tatashi, tashiga tattara yanata yanata ta na zubawa ga akwatinta,kayanta nasawa wasu takalma jakunkuna,komai takwashe ta kaddunta na makaranta suma duk ta tattara.
Saida taji ana kabbara sallah masallacin unguwar, sannan tayi Alwallah tazo tahau sallah babu b'ata lokaci.

Ta na gama wa wanka tashiga,
Bata jimaba ta fito tahau shafa Mai, shikad'ai ta shafa sai man baki ta zira kayan ta, ta matsu taga lokaci yaja, so take kawai tabud'e idonta taganta Gaban babanta da maman ta.

Wayarta ta jare daga caji tashiga kiran jabeer,
"Allah yasa kinsamu bacci dai jannat wannan sammako haka"

"Wallahi bansamu baccin yanda nakeso bah,Har k'agara nayi gari yawaye"

"Inata magana banma gaisheka bah, ina kwana yagajiya kuma"

"Haba gajiya tabi lafiya,yanzu kinshirya ko"

"Ai Jannat engineer take jira kawai,"

dariya yayi yace"to ga engineer nan tafe insha Allah"

Wanka nafito ina shiryawa bari na k'arasa idan na iso zankoraki,"

"OK sai ka iso d'in"

Taka she ta na tuna wa da sahibinta sagir,
Idan suna waya komi yakeyi zai sanar da ita,
"princess zanshiga wanka, princess nafito shafa Mai nake, kozaki taya ni.
Ganinan break nakeyi bud'a bakinki nasamaki,koda yake ma princess d'ina tafison nabakin hayaty d'inta ko"
sune Kalamam daya maidasu kamar ruwan shan shi, bayajin komi yagaya Mata zai shiga wanka,baidamuba don bak'aramin so yakeyi Mata bah,
Idan kuwa tayi fushi dashi har kuka yake Mata awaya, kokuma idan yazo zance,

Wasu hawaye suka ziraro Mata masu zafi,
"Allah sarki sagir, Allah yajik'an ka da Rahma, Allah yayafe maka, duk Wanda yayi sanadiyyar rabaka da numfashinka Allah kasaka ma, karya yabar Wanda yayi wannan A bun yahuta, kuka tafashe dashi don batajin yanzu akwai wani namiji irin sagir d'inta,
Don shi is very simple man, baid'auki kanshi da zafibah haka rayuwarsa yana yinta saisa saisa,
Haka A bun duniya bai damai bah,idan yana son Abu zai mashi wani irin so na gaske gaba D'aya zuciyarsa yake baka, ga ririrtawa ga iya soyayya zata iya cewa batasan komi akan love bah saida ta had'u da sagir, duk wani salon soyayya Ya koyar da ita, gashi yatafi yabarta da mikin kaunarsa...........wayarta ta katseta daga cikin shaukin soyayyar marigayi sagir,
Engineer Tagani tayi saurin d'auka.

"Zan iya shigowa kiyimam iso ga mutanen gidan"

"Ok"

Tatashi tafito falon babu kowa kamar ma bawanda yatashi,
D'akin mama tayi wa tsinke ta same ta tayiwa d'akin filla filla da alama akwai Abunda take nema,

"Mama ina kwana."

Cikin fad'a tace"lafiya"

"Mama ga jabeer yana son yashigo zai magana daku."

"Yayi magana damu yace mana uban me, nace mezai cedamu munafuki Algungumi Mai son tada zaune tsaye."

"Kiyi hakuri mama nifah sakone ya bani yana son yashigo."

Zainab ce tafad'o kamar ankirata,
"Mama kyaleshi yashigo muje dame yake tafe, takalle ta cikin kallon k'ask'anci tace kina iya shigo dashi ai"

Fita tayi Takirashi tare suka shigo,
Ga mama ga sama ga Zainab,
Sai mubee data tatashi saboda hayaniyar mamar.

Kallon wulakanci suke Mai,
Bakamar mama jitake kamar ta shak'eshi yamutu.

"Mama ina kwana, ya aka k'araji da hakurin wannan rashin.............. Kai dagata man kajiko bana ciki da iskanci,meyaka woka nan gidan har kake son Magana damu"

bai magana naba, ya fiddo zareriyar takardar sammacin, yamik'awa mubee dake kusa dashi.
"Yace ga dalilin zuwan nan,don haka kunada sauran kwanaki biyar sai mun had'u kotun."

Wata irin zabura mubee tayi ta na wullar da takaddar,
"Tasha gabanshi, mekake nufi jabeer, gayaman mekuke shiryawa kaida wannan Annamimiyar yarinyar"

Bai bata Amsaba yace"jannat muje ko lokaci yana tafiya"

Kamar jira take tashige gaban, yarufa Mata baya saida yaje k'ofa yace"Abunda Kika kasayiwa mijinki shine ita zatayi,don haka kisama ranki ruwan sanyi kinji Abunda zatayi"

Wata ma haukaciyar ashar Zainab ta k'unduma,
"Babbar bala,in nan mama kinaji kinajin Abunda yake fad'a,jannat zata kare Adam,mama kenan duk wasu evidence tagama samunsu bamu sanibah, wayyo Allah wallahi bazai yuwubah"

Waya mamar ta d'auko,Cikin wani irin fushi tafara kiran wayar,
Sama yafizge"haba mama mezakiyi,badai suma sawa zakiyi akashe subah, Aa kibarmu muji da wannan ma idan kika sake aikata wani shikuma wa zamu lik'amawa,sannan tahaka asirin mu zai tonu kibarta ta tsaya mashi mana ina da tabbacin lawyer da na d'auka bazai barta tayi wani nasara bah"

"Dallah kauce man nan, muddin wannan yarinyar ta tsira da hujjojinta mungama yawo gamucan gidan yari, don haka yau saitabar duniyar"

Maigadine yashigo yakawo Mata number motar jabeer,
Dayake Zainab takirashi lokacin da jannat tafita don shigo da jabeer din.

Murmushi mamar tayi tashiga yin kiran wayarta,
"Barau ba gaisuwa nakira na ji bah,ga number motar nan zanturo maka, yanzu haka sun d'auki hanyar kaduna,katabbatar kazo man da labarin mutuwarsu karka barsu da rai barau wannan karon har bashin dakake bina zan had'a inbiya ka"

Idonsu yarufe basu San mubbe na wajen bah,
Saidai sukaga tafad'i tim kamar gawa............

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

"Ki kwantar da hankalin ki jannat babu Abunda suka isa suyi mana, insha Allah kizuba ido kigani."

"Wallahi jabeer nasan halin mama, batada imani zatayi komi don ganin bayan mu, burinta

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment