Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

don da mama na da babanshi uba suka had'a"

"Haba shiyasa kuke Kama sosai.............jannat ga mutanen nan fah sunabin mu abaya"

Wata irin zabura tayi"nashiga uku na jabeer yazamuyi sai kuka,
Shi dariya ma tabashi belt yasaka itama yasaka Mata,wani gudun suka fara hakan yabasu damar suma suka shiga binsu da wani gudun,

Waya jabeer yayi daidai suna cikin wani gari, Wanda dagashi sai hunkuy,
Kamar wasa motocin yan sanda suka zagayesu guda hudu,

Duk yanda sukaso guduwa hakan yagagaresu,
Tsayar da motar su yayi jannat fuskar nan tayi kaca kaca da hawaye,

Fitowa tayi lokacin da y'asanda suka kamo su, sunsamu bindugu uku awajensu,
Dayake su uku ne suka taho,
Jabeer yace"yallabai kutai dasu station na cikin garin Zaria,zuwa dare zanzo na same Ku zamuyi magana insha Allah"

Haka aka tusasu gaba cikin motar yansanda suka tai dasu,
Sai lokacin tayi shiru, dariya kawai yake Mata,
"Dama haka kike da tsoro jannat, gashi kuma aikin ki baya buk'atar haka"

"Wallahi engineer ni ba wai tsoron na haka nan nake yi bah,kawai banason ban cika wannan burin bah ne akasheni,idan har sukaga bayana ayanzu,babu Wanda zai ceci Adam kila haka zai dawwama cikin wannan halin sannan kuma bancika alkawarin danayi bah na daukar fansar ran dady shiyasa duk nake Atsorace wallahi"

"Haka ne insha Allah komi zaitafi yanda akeso"

Tafiya Sukai bamai nisaba suka iso cikin garin hunkuy,
Yace"ina mukayi daga nan kuma"

Kwatan ce tacigaba dayi mashi,
Yana tunanin ai indai wajen datake Mai kwanace ne to ai gidan baba mamuda Dane,
Baigama tunani bah tace" yawwa kaga gidanmu can Mai gareji kalar ruwan toka."

Parking yayi ya kalleta yace"dama nan gidan kike, kodai rik'onki akeyi gidan don ni kaf y'an gidan nasansu, Amman basan dake bah"

"Ina kasan y'an gidanmu to"
Murmushi yayi yace"to Ai Alhaji malam kanen mama na ne"

Zaro ido tayi cike da mamaki,
"Kace k'anen mamanka ne, taya yazama k'anenta to"

"da mama na da Alhaji malam ubansu guda, kamar yanda nake da Adam, haka nake dake"

Kallon mamaki da al,ajabi take Mai,
Kenan Adam yayanta ne najini duk A bun nan itadasu y'an uwane kenan, to taya haka tafaru bamuda masaniya.................
[1/23, 3:49 PM] Maman M.: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALKALAMIN*


*_AISHA ABUBAKAR_*
*_(MRS BB)_*

_*(MAGAJIYAR KAINUWA)*_


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM```

19&20.


✍🏻Jikinta sanyaye tace"kenan Adam d'an uwana nane bansani ba"
"Ba Adam kad'aiba har jabeer ma"
Kallonsa tayi cike da mamakin Abun to ya haka itadai iyakar saninta dady tasani sai inna labuda,Amman waye mahaifin Adam to,
Bata da Mai bata wannan Amsar sai Alhaji malam, don haka dole ne ya bata labarin rabuwar kawunan dasukai,

Wani yarone yafito dagudu yana gara taya,
Tabishi da kallo tace ma jabeer"kasan wancan"
Murmushi yayi yace"mai sunan malam kenan (Mahmud),kina mamaki ko uhm bakisha mamakin bah sai munshiga don haka fito muje,"
Bata da zab'in daya wuce yin hakan, yabud'emata kofar tafito aiko malam karami yana hangota yafallo da mugun gudu ya cakumeta yana tsalle,
"Anty murja kece kikazo"
Dariya tayi tashafa kanshi tace"malam kenan har yau bakabar gudu bah Ko,baka tsoron kafad'i kaji ciwo"
"Murnan ganin kine Anti murjah,kallon jabeer yayi yace"Laa yaya Kaine kakawota"
Riko hannun yaron yayi suka nufi cikin gidan yana cewa"nina kawota zaka biyani kud'in Mai me"
Dariya tayi masu tana Jaye da trolyn ta jabeer yana d'auke da jakar tah.
Sallama sukai tsakar gidan yasha suminti gashi anshare yayi fes cikin tsafta,

Wata yar budurwace zatayi tsarar jannat Amman batakai shekarun jannat d'in bah,
Tafito daga kitchen"lalalaala mama! mama!!Kifito ga yaya jannat wallahi dama nace maku yau inaji ajikina tana dawowa,Amman yah kabir yace nacika shirme to gashi nan gaskiya tayi halinta"
Mamar ce tafito daga cikin d'aki ta na rike da baki, cike da murna"jaberu Kaine tafe kaida wannan yar Ina kuka had'u haka"
"Haba labuda yako zama basuyi bah zakihau tambayar taki, ke Nafeesa dauko tabarma asanya nan suzauna kika kamata Kika mak'ale"
Dariya tayi tashiga d'akin ta ta d'auko ta shimfid'a,
"Zauna yaya jannat kezan Fara tarba, tafad'a tana hararar jabeer cikin wasa"
"Nima banson taki ga uwata nan tatarbeni hakan ya wadatar dani"
Dariya Alhaji malam yayi shida jannat d'in,
Gaishe gaishe ne yabiyo baya kafin Alhaji malam yace"jabeer Ina kuka had'u haka"

Murmushi yayi yace"Ai Alhaji malam,nina d'aukota tunda ga can gidan baban,"
Cikin mamaki yace"yo ya haka"
"Wallahi baba Ina neman lawyer da zai tsayawa Adam ne akotu sai akabani no. Dinta mafarin had'uwar mu kenan, Ashe bansani bah yar uwata nake tare da ita, kuma duk zaman nan batasan cewar Adam ma d'an uwanta bane, shine take mamaki nima nake taya ta mamakin saboda duk sanin da nayiwa nan gidan nidai bantab'a ganin tabah kuma tace nan gidan take"

Mama ce tayi ajiyar zuciya takalli Alhaji malam,
"Kaga illar Abunda nake gaya maka kullum,zumunci ba abun wasa bane yanzu daba hakace tafaruba bansan yaushe yar nan zata gane cewar tana da dangin ubad'aki"
"Labuda ya isa haka don Allah,yanzu AI gashi tasani banason tashe tashen Abunda yariga yazama tarihi,Nafeesa kawo masu Abincin tashi takwarana jeka siyo lemu shagon lawandi,"

"Bari nayi sallah ni, sai naci Abincin"cewar jabeer yamik'e yana masu sai yadawo.
Shima Alhaji malam d'in binshi yayi zuwa masallaci don anata sallar azahar ne,
"Yaya murja kece yau akwai labari,"cewar nafeesa data dire kular abinci da plets da lo kula,
"Kekuma sarkin zuba bakida abun so sai surutu ai kinbarni na sarara haka nan ko"
"Ayya to sarara sai kiban labarin"
Dariya duk sukai ta mike don shiga d'akin dayake na nafeesar,
Itama tarufa mata baya
D'auke da kayanata,
"Dakin nan yayi kyau nafee, waya gyara maki shi haka yakoma na babbar budurwa"
Dariya tayi tace"wallahi yaya Usman ne yayi wannan aikin (Dan yayan mamarsu ne dake Abuja).
"Aiko yakyauta wallahi AI bama d'akina kad'aiba duk gidan yasaka aka gyara bakiga d'akin mama bah,yacanza Mata kayan d'aki sabbin kujeru,harda gado"
"Sainagama salla nahuta zansha hira kenan,"
"Aikuwa yaya bari naje naraba abinci kiyi sallar ga kewayem d'aki can ma tanuna mata tafita.

Bayan sungama cin Abincin itadashi,
Alhaji malam yace"dama jira nake kugama,magana zanyi daku"
Duk suka maida hankalinsu wajensa,
Yagyara zamanshi yace"jabeer murjanatu bazata kare wannan shad'anin yaron akotubah,Kai ma kuma nahaneka da sake shiga cikin wannan shariar,don Adamu yacanci duk irin hukincin da kotu tayanke mashi,"
Cikin rud'ewa da batasan ta miyeba take kallon baban nata,
Tace"baba mekake fad'ahaka kasan kuwa mebakin ka yake fad'a, kaga don girman Allah baba karkayi haka, Adam fah d'ane awajenka kamar yadda muke wajenka,kenan bazaka bamu goyon bayan ganin munceto shi daga wannan azabar"
"Nadai gaya maki kicire wani burin taimakonshi don wannan ba Wanda za,aji tausayi bane balle har ayi yunk'urin tai makonshi,"

Kamar wasa taji idonta yacika tab da kwallah saboda tuno irin wahalar da Adam d'in yake ciki,
Yadda taganshi da kuma labarin daya bata,
Idan bata manta bah yace babanshi sace shi akai.
"Ta share hhawayen tace baba don girman Allah kabari agama sharia nan gabanka kaga komi sannan kayankewa Adam hukunci,
Adam abun tausayi ne don Allah jabeer kafahim tar dashi"
Kallonta yayi cike da mamakin irin yadda ta rude haka da nuna damuwarta sosai akan Adam d'in.
"Baba maganar jannat akan daidai take,duk abundance kuke tunani duk bahaka bane, zanso kuzo kallon wannan karar zakusha mamaki, don haka Ina rokonma Adam alfarma akan kabar jannat takareshi idan ba itaba wallahi babu Wanda zai Cece shi don kowa haushin Sa yakeji,don Allah baba"
Daker da jib'in goshi yace shikenan zasu zuba ido sugani akotun ranar litinin d'in"
Yayashi yabar wajen.

Dahaka shima yayi masu sallama don zuwa gaida mamarshi kasancewar tun yanada shekara biyar babanshi yarasu kuma shikadai ne wajen mamanshi,
Tayi aure mijin yasake mutuwa,har yanzu bata sake ba.

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

*RANA BATA K'ARYA SAIDAI UWAR D'IYA TAJI KUNYA*

yau yakama za,a shiga kotun tun asubah jabeer ya iso garin daga kano,
Shida wani Abokinsa kowa cikin motarsa,
Gidan su jannat yafara sauka,
Lokacin har sunshirya tsaf da nafee da mama sai Alhaji malam za,Atai kabir da salima da maisunan malam su gida zasu tsare,

Motar jabeer da jannat sai nafee kawai zasutai,
Motar abokinsa kuma Alhaji malam gaba mamarsu jabeer baya itada kakarshi sai mamarsu jannat,

Haka sukai wannan tafiya tun karfe shidda sukatai,
Don karfe uku za,afara sauraren k'arar,
Jikinta babu dad'i don bata San ya sharia zata kasancebah,
Lura yayi da yanayin datake ciki yasakashi cewa"kikwantar da hankalinki insha Allah babu Abunda zaifaru sai alkairi,muda mikeda shaidu masu zafi ga hannun mu."

Ajiyar zuciya tayi tace"duk da haka jabeer inajin fad'uwar gaba wallahi,
"
Addua zakicigaba dayi babu Abunda zai faru nagaya maki"

Shikenan Allah yayarda,
Bata sake magana bah saidai shida soda uwar magana nafee suketayi,
Har bacci ya sace ta bata saniba.


*kuyi hkr wlh nagaji insha Allah page nagaba akotu zamutashi*

TAKUCE MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻


Comment dinku shine ladan mu awajnku.
[1/25, 12:00 PM] Maman M.: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALKALAMIN*


*_AISHA ABUBAKAR_*
*_(MRS BB)_*

_*(MAGAJIYAR KAINUWA)*_


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM```

21&22.

*KOTU*

Kotun mak'il take don duk Wanda bakai tunani bah yazo kallon wannan sharia Mai matukar d'aukar hankali,
Mutane dayawa suna bukatar jin yadda za,a kaya da wannan sharia wasu nagoyon bayan Adam yayin da dayawan mutane suke kware mashi baya,
Don suna ganin wannan babbar cin amanace kakashe sirikinka babu gyara babu dalili.

Motarsu ce ta tsaya bakin kotun don daker suka samu wajen yin parking,
Tuni su jannat sun iso kowa yana nan taaye ba akai ga shiga karar bah,
Anajiran alkali da Kuma shi Adam din,

Su mubee ne suka iso tana bud'e motar idonta yasauka akan jannat sanye da kayan lawyers,
Wani bak'in ciki da takaici yakamata batasan sadda ta kwace daga hannun Zainab bah tayi wajen,
Babu Wanda yaga tahowarta saidai sukaganta takaiwa jannat din wata irin shak'a tana cewa"karya kike wallahi baki isaba kinci karya kinkwana da yunwa,billahil lazi babu Wanda ya isa yacece ki wajena saina kasheki kasheki zanyi shegiya,babuke babu mijina yafi karfinki wallahi shine kika bullo da cewar kezaki tsaya Mai don yasoki KO to karya kike naga Wanda zai Hana ni kasheki anan wajen"
Ba karamar shak'a tayi Mata bah Wanda yasaka idonta har yafara ja,
Hankalin mutanen wajen yatashi, cikin su mama da Zainab babu Wanda yayi yunkurin hanata don su suka had'a bom d'in,
Alhaji malam da jabeer suka k'araso wajen daidai isowar motor da aka d'auko Adam ciki,
Idonsa akansu mubee ta shake jannat da karfin tsiya,
Duk yadda jabeer da Alhaji malam sukai su kwaceta hakan ya gagara,
Saidai taji wani mahaukacin Mari afuskarta,
Bata dawo hankalinta bah tasake jin wani,
Still bai sake saurarawa bah yasake wanketa da wani.

Wata mahaukaciyar kara tafasa wadda tajawo hankalin mutane dayawa,
Kallon shi take cikin kunan zuciya da bakin ciki,
"Adam Adam ni kamara kasaka hannu kadakeni har sau uku"......"namareki idan da inda damar yin abunda yafishi zanmaki don bakida wani kima da sauran mutuci agareni,saboda kiyayyar da kikeman bakison kowa yatsaya man don ceton rayuwata ko,bakida waniburi daya wuce nabar maki duniyar ko,to baki isaba Kwana na basu karebah keda duk Mai Neman ganin bayana wallahi saidai suyi hakuri......dan sandan suka kamashi suka shiga dashi yayin da kowa yake rige rigen samun gaba,

Jabeer yace"karkidamu babu abunda suka isa suyi nina gaya maki insha Allah daga yau tasu tak'are"
Ajiyar zuciya tayi tace"Amman kana ganin za,ai shariar yau agamata"
"Maizai Hana tunda munada kwararan hujjoji kinga ma key din da nace Zan ansa hannun Adam jiya naje shekaranjiya naje na ansoshi,
Kisama kanki kwarin guiwa kinjiko"
Da wannan tasamu natsuwar zuciya nafee tace batadai jimaki ciwo bah KO yaya"
Murmushi tayi Mata takama hannunta suka nufi cikin kotun ta na cewa"ko kadan batajiman ciwo bah, karkidamu yar uwata"

Kowa yasamu waje ya hallara Ana zuba ido,
Alkali yazauna sannan kowa yazauna,
Karar aka karanto mashi yace"lawyers sugabatar da Kansu,"
Cikin jarumta lawyer dasu sama suka d'auka ya Mike yace"sunana barrister Nurah Halilu, nine lauyan daya tsaya ma marigayi Alhaji Muhammad"

Jinjina Kai Alk'ali yayi sannan yazauna,
Cikin natsuwa ta mik'e tace"sunana barrister murjanatu Mahmud nice lauyan dake kare Wanda ake zargi"

Yayi yan rubuce rubuce yace"kuna iya fara gabatar da Aikinku,"

Tashi yayi yace"mai sharia inason kotu taban damar zanyiwa Adam tambaya"

"Alkali yace kotu tabaka dama"

Inda adam yake yatunkara,
Yana mashi kallon kaskanci yace"kozaka iya gaya ma kotu sunan ka"

Kanshi na kasa yadago idon nan sunyi matukar jaa yace"sunana Adam mudassir"

"kagayawa kotu alakarka da Mai rasuwa"

"Baba na ne kuma sirikina baban matata"

"Dakyau ko Zan iya sanin Meyasa kakasheshi"
"Bani na kashe shi bah"
"To meyakaika haurawa gidanshi ta sama kuma Matarsa ta ce taganga ido da ido sadda kakasheshi,"

Akwai dalilin dayasa ni zuwa irin wannan lokacin,
"Ko za ka gayawa kotu dalilin naka"
"Anturo man sako awaya ne cewar idan Ina son ran sirikina intaho yanzu inceceshi don gasunan zasukasheshi,Alokacin Ina Abuja naduba time karfe biyu na dare sai nayafi"

"Suwaye wadan nan mutanen kuma meyasa aka kamaka da bindiga taya kasameta,kuma ya akai kasan da wannan kofar ta sama har ka iya bi tanan"
Shiruyayi kafin yace"mutanen ashekarun baya munyi wani aiki dasu shine nafita daga cikinsu dalilin dayasa sukeson kashe sirikina don sud'oraman laifi,
Bindigar kuma saboda irin haka nake ajiye da ita don sunsha bibiyata Ina tserar tar Dakaina,kofa kuma muntaba shiga gidan ne da niyyar fashi sai naga diyarsa aranar sai muka fasayin fashin"


"Wane irin Aikine kukai dasu har don kafita sukeson kasheka"

Bai yi jinkirin bashi amsaba yace"munyi fashi da makami ne dasu dadadewa"
Aikamar jira ake yafada akahau Cece kuce da hayaniya kowa nafadar alabarkacin bakinsa,

Saida alkali ya tsawatar sannan akai shiru,
Lauyan yace"ya mai sharia kaji dai dabakinsa yace yayi fashi da makami kuma har gidan suntaba shiga, kenan kaga tun bayanzu bah Adam yaso ya kashe marigayi Allah bai bashi damaba saida yasamu ya aure Mai diya yabiyo dare yakasheshi,
ya Mai sharia kayi duba dakyau akan wannan magana don ita kadai ta isa ayankewa wannan azzalumin hukuncin kisa"

Yayi godiya yakoma yazauna,
Dadi kamar yakashe su mama don ganin sunfara nasara,
Alkali yadago daga rubutunsa yace"lauyan dake kare Wanda ake tuhuma tana da Abun cewa"

Cikin girmamawa ta mike tace"eh yamai sharia Ina da abun cewa inason aban dama Zan magana dashi"

"Anbaki damar"

Kallonshi tayi zuciyarta tana bugawa hakika Adam yayi wata irin rama yayi baki sosai,
Kasa cigaba da kallonshi tayi don idonsa babu kyan gani saboda yadda yacanza launi, ga jijiyoyin kanshi sunfito sunyi rad'o rad'o,

Cikin dakiya tace mashi"ko zaka iya bama kotu labarin ka"

Kallonta yayi tayi saurin d'auke idonta,
Shiru yayi kafin tasake maimai ta maganar
Cikin sanyin muryarsa data karyewa jannat zuciya jitai kwallah suncika idonta tayi saurin maidasu,
"Yafara da cewa kamar yanda nafad'a d'azu sunana Adam mudassir mahaifina malam mudassir haifeffen garin Kaduna nane Amman bayan rasuwar iyayenshi sai yadawo cikin marabar hunkuy bashida wata sana a face cinikayyar hatsi don gonarsa guda babba aciki yake noma duk hatsin dayake so,malamine awannan gari duk dare kofar gidanmu cike da matasa da dattawa Ana d'aukar karatu,
muntaso cikin rashin dangi da mataimaki mahaifiyar mu tarasu,daman tun data haifeni bata da lafiya kullum tana kwance yayata ce kekula da komai na hidimar gida da hidimata,
Inda shekara goma lokacin nagama primary mama na ta rasu,
Munshiga maraici sosai gashi kuma yayar tawa tazo tayi Aure,
Dagani sai babana kuma baisake auren wata bah yacigaba da kulawa dani,
Kodayaushe Ina tare da babana ko makaranta zani shiyake kaini akan kekensa har cikin garin hunkuy,
Acan nayi secondary dina da taimakon babana,
Haka rayuwar taita tafiya har zuwa lokacin dana gama secondary Dina alokacin kuma mukasake shigawani tashin hankalin,
Yayata datai aure tarasu wajen haihuwa don dama shekara takwas bata haihuba sai lokacin,
Da ita da abunda tahaifa suka koma ga Allah."

"Munyi kuka sosai bakamar ni saboda banida kowa sai ita da babana,
Sunake gani inajin dadi mundade kafin mu fawwala ma Allah wannan kaddarar rayuwar datasamemu,
Ban samu halin cigaba da karatu bah, don lokacin nasamu zuwa kasar waje karatu, saboda kokarina amakaranta yasa sadda zamugama akai mana sendpost taron yaye dalibai Wanda akai quiz da divet duk nina zo na daya,
Wannan dalilin yasaka wani babban mutum dayazo yace yad'auki nauyin karatuna nagaba da secondary, naji dadi sosai don inata murna inje ingayawa Baba da yaya ta,
Sadda naje sai wannan labarin yariskeni.
Sai naji bazan iya tafiya nabar babana shikadai bah bansani bah shima idan natafi wani Abun yasameshi,
Tsoran hakan yasa duk yadda babana yaso natai nace wallahi bazanjeba mutumen yayi yayi amman nace nayafe wallahi.
Dole ya hakura yakyaleni nacigaba dataya babana aikin gona gakuma karatu Ina d'auka wajenshi don har nayi sauka hadda nake alokacin,
Ahaka ahaka mukaita rayuwarmu mubiyu munason Junan mu sosai bamuson wani abu yatab'a dayanmu don jimuke kamar mukadai muka rage aaduniyarmu.

Kwatsam wata rana nawayi gari babu babana......... Kuka yakucce ma Adam Mai cike da ban tausayi babu Wanda baiji tausayin halin dayake cikiba,
Jannat dake gabanshi ita kanta kukan take daker yatsagaita da kukan,
Bayan kowa ya sake natsuwa ya share hawayensa yacigaba da cewa.

"Nashiga tashin hankalin daban tab'a shigarshi bah,nayi kuka har hawayena suka k'afe,
Nazama kamar wani Mahaukaci don bazan iya kwatanta irin tashin hankalin danake cikiba don jinake da gawar Sa nagani bazan shiga irin wannan halin bah,
Bayan kwanaki bakwai nashiga binciken dakinsa don InJi ajikina akwai Abunda yafaru.

Don anagobe Zan nemai in rasa yace man kar najirashi wajen cin Abinci, idan naci inyi kwanciyata zaije wajen maigari yadawo,
Nace mashi to don nasan bashida wani Aboki Bayan Mai garin.

Nayi bincikena nagama bansamu wani Abu dazai anfane nibah,
Nakoma d'akin litattafanshi nafara dubawa,
Umdatul ahkam da yake koyardani na d'auka nashiga duba kawajen da yatsaya man akaratun in buda wajen naga wata Takarda konace fuliskaf da rubutun larabci rabin takaddar,
Anan cikin takadar komi yafaru............

*MASU KARATU KUBIYONI DONJI MEKE CIKIN WANNAN WASIKAR*

TAKUCE HAR KULLUM MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻

Comment dinku yana d matukar muhimmanci agaremu.

*_magajiyar kainuwa ce_*
[1/27, 5:06 PM] Maman M.: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALKALAMIN*


*_AISHA ABUBAKAR_*
*_(MRS BB)_*

_*(MAGAJIYAR KAINUWA)*_


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM```

23&24.

Zama nayi don karanta wannan wasikar Mai dauke da rubutun larabci,
Naji dadin koyon larabcina da baba ya matsaman alokacin saida nakoya,
Ina kuka ina karanta wa ga abunda yace man

******
Adamu karkasha wahalar nema na antafi dani ne bansan inda zasukai nibah,asanina banyi masu komi bah,tsawon shekaru da rasuwar iyayensu muka rabu dasu saboda gadon da sukabar mana,ban tab'a gaya maku inada dangiba saboda basuda wani anfani awajena,babanmu yabar mana dukiya iyakar dukiya,bayan mutuwarsa wannan dukiya tazama fitina, don babban yayanmu yace bawanda ya dace da wannan kudin saishi saboda shine yayi karatun boka, abashi yajuyasu su karu kafin wani lokaci araba gadon aba kowa nashi, kasancewar ni mamata daban tunda tahaifeni tarasu,itam kuma Mariya mamarta da babanmu auren zumunci ne shiyasa ita suka dauketa tamkar tasu, bansan mama naba balle wani d'an uwanta, bansanta bah natashi hannun mahaifiyar yan uwana Muhammad da Mahmud sun hade man Kansu basayin komi dani kasan cewar ni har ita mariyar, banida d'anuwa damuke ciki sadda Muhammad yafadi wannan shawara nace nidai abani hakkina ban amunta da hakaba,yasaka sukai man taron dongi sukai man dukan tsiya,
Sukace zasubar garin da dukiyar ai sai idan nagansu ma zasuban kasona ko,
Wannan abun dasukai ya tunzurani nikuma nayi alkawarin bazasu ga kudin bah,don alokacin baban mu duk dukiyar daya tara
Dagani sai Muhammad din mukasan inda yaboyeta,
Kansuyi aune nasaceta nabar garin,
Nadawo marabar hunkuy anan nayi aure har na haifeku,tunda nazo da wannan kudin nayi gini sosai cikin gonata nai masu kyakkyawar ajiya, kuma daga mahaifiyarku har Ku babu Wanda nataba gaya ma abunda yafaru arayuwata,kaji abunda yafaru tsakanina da yan uwana shine mahmuda yagano inda nake zaune yafara bibiyata, yana turo mutane sunaman barazana nikuma nace bazan bayar da wannan kudin bah har sai idan sunyarda zasu zo ayi sulhu aba kowa nashi, yace bazai yuwu bah,daya matsaman sai nace Muhammad yazo ya ansa Ashe nahada tashin hankali sukaje sunata fada tsakaninsu Wanda yasaka kawunan su yarabu,
Kowa yakama gabanshi duk abun nan babu Wanda nabari yasan da wannan abun,
Ranar dana cemaka zanje wajen maigari aranar ne nataho wajen dawowa aka bankeni da mota suka saceni suka tai dani Karka saka kanka cikin wannan fitinar Adamu kabarni da dangina komi zasuyi man ina sonsu ahaka.

Ajiyar zuciya yayi yana sauke numfashi,
Yacigaba tunda nagama karanta wannan wasikar naji wani kwarin guiwa yashigeni akan daukar wa babana fansarsa,
Ranar ina zaune kofar gida nayi tagumi,
Wannan mutumen dayaso tafiyata kasar waje karatu yazo man jajen b'atan babana kuka nayi tayi mashi hakan yabashi tausayi ganin halin danake ciki yasaka yace idan inason zama dashi nahado kayana nabishi,
Banyi musuba don Alokacin banida wani zabi.

Haka mukatai dashi gidanshi maikudi ne sosai,
Acikin garin Kaduna yake dazama matarsa batason zamana dashi kasancewar bashida yara dayawa yasa yake son su sosai, su biyu ne mace da namiji macen tayi aure namijin ma haka,
Haka yasakani nayi jamb nashiga makaranta,
Nayi digree dina akan computer na lak'anci computer sosai nagama Alhajin yasamar man aiki awani company,
Nasamu kudi sosai da wannan company din,
Kwatsam shima wani iftila,i yafada masu b'arayi suka shiga gidanshi suka kaseshi damatarsa kuma suka kwashi dukiyarsa,
Wannan al,amari yajijjigani nashiga tashin hankali sosai,
Har saida nayi ciwon sati biyu nawartsake,
Hankalina yakoma kacokan wajen babana ta ina zanga mu da Alhaji Muhammad musa don naci burin sai yagane kuskurensa nasace mahaifina dayayi,

Haka na hada kayana nabar garin kaduna,
Har aikina na ajiye don yanzu bana bukatar sa,
Nashiga cikin garin kano wadda kaddarata tasakani haduwa da wannan mutumen Wanda shine asalin shigata harkar fashi da makami,
Nayi suna nayi fice bakowa bane face *BALA*
Bala bakowa bane face gawurtaccen d'an fashi da ya iya sata yakuma kware akan harkar kisa,
Shine Wanda yabani wajen zama adakinsa nasauka,
Anan nake komi nawa amman sai insati banga bala bah,
Kullum idan natambayeshi inayake zuwa sai yace man wani aikine,
Haka tafiya tayi nisa ina zaune babu aikinyi,
Duk kudadena nabanki suka kare,
Har takai da bana samun abunda zansaka ga bakina
Sai nawuni da yunwata,
Bala yalura da halin danake ciki sai yaringa barmun kudi
Idan sunkare zaikuma bani wasu,
Saida takai bala babu abunda baya siyaman takalma kayan sakawa masu tsananin tsadar gaske,
Agogo turare karshe rannan saigashi da dalleliyar mota sabuwa vibe maikyau,
Yace tawace awannan ranar nayi murna sosai domin ina bala,in son mota kamar hauka amman sai nace mashi don Allah wane Aikine haka Mai kawo kudi masu yawa haka,
Don Allah kakaini nagaji dazaman vanzar nan kozansamu na kashewa nawa nakaina,
Murmushi yayi yace man indai kanaso maizai Hana kanada zarrar dazakayi irin wannan aikin, amman fah yanada sharadi Wanda idan kaji kowane aikine to yazama wajibi kayi don ba,a fadarsa abanza,
Cikin zakuwa dason inji don nan take naji kwadayin sonyin aikin saboda abunda zansamu.
Jinai yace *fashi da makami*
Wata irin razana nayi har inaja baya,
"AI babu batun jabaya don kariga kaji kuma babu gudu babu Ja dabaya,
Karkayiwa kanka bakincikin wannan gara basar, Adam kanada fasaha ka kware akan harkar computer bazan iya gaya maka iyakar adadin kudaden dazaka mallaka bah awannan lokacin,cikin dare daya zakasha mamakin irin daukakar dazakai,
Bakuma hakanan muke wannan aikinba muna duba masu kudin da suke zaluntar al,ummah ne mufarmasu,muna anshe kudaden azzaluman masu kudi wadanda Kansu kawai suka Sani, Adam nikaina dakagani nan badan inaso nakeyi bah saidan hakan shine yazamar wa rayuwata dole ne,
Tadalilin wani azzalumin Mai kudi narasa iyayena, narasa kanena,
Ina Neman kudin da za,ai wa mahaifina aikin zuciya naje wajenshi don Neman taimako haka ya wulakantani yakoran,
Banyi fushi bah na sake komawa ina komawa yasaka akaiman dukan tsiya,
Gashi ranar ne karshen kwanakin da sukabukaci ai Mata aikin,
Sadda nakoma ina cikin halin taimakon nima amman nasamu tarasu,
Babana saboda mutuwar ta bugai washe gari shima yacega garinku nan,
Bayan sati biyu kuma kanena yadawo daga makaranta wani Mai kudi yabankeshi amman ko waigowa baiba,
Yansanda basuyi komi akaiba saboda yana da babban matsayi,
Karshe kanena akacire Mai kafa ranar da akai aikin shima yarasu,
Wannan shine silar shigata wannan harkar Adam,
Don haka nabaka kwana biyu kayi tunani.

Wannan labarin da Bala yabani yayi masifar tab'ani don yatada man mikin rashin ahalina,
Cikin kwanakin biyu ban tsaya sairaren zuciyar dake Hanani bah kawai na amunce ma bala...........


*KUKASANCE DANI DON JIN CIGABAN WANNAN SARK'AK'K'IYAR*

Takuce maman muhseen.✍🏻✍🏻


_MAGAJIYAR KAINUWA_
[1/30, 2:57 PM] Maman M.: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*DAGA ALKALAMIN*


*_AISHA ABUBAKAR_*
*_(MRS BB)_*

_*(MAGAJIYAR KAINUWA)*_


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*


```BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM```

25&26.


Washe gari mukatai dashi yakaini wajen ogansu maisuna *barau* nan akaiman register matsayin member,
Cikin kankanen lokaci nazama babban Dan fashi duk gidan dazamuyi fashi ni nake gano mana hanya mafi sauki da zamushiga gidan muyi abunda zamuyi cikin kankanen lokaci mufita,
Dandanan na zama attajirin mai kudi oganmu yabarmun ragamar komi idan zamuje operation ninake fidda yaran da za,atai dasu oganmu yana sona sosai ganin yadda daga zuwana yasaka harkarsu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment