Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kar asirinsu yatonu nikuma inhar nacika yar halak bazan bar hakkin ran dady bah,saboda wannan mutuwar babana na can kauye har yanzu kwance yake bashida lafiya,duk da irin Abunda dady yayi mashi hakan bai saka yashare shi bah,"

"sannan nayi alkawarin fitar da Adam daga halin dayake ciki,"

"Allah yabaki iko, yakuma tai makemu baki d'aya, yakamata mutsaya muyi break ko"

"Jabeer kawa Allah kayi hakuri dawani break,muna ta tserar da rayuwarmu kai ta wani breakfast kakeyi"

Dariya yayi yace"wallahi ninan hankalina kwance yake kema kuma zaki nemi Abincin bari dai tafiya tayi nisa."

Gudu yake shiyasa sukayi sauri,
Don har sunyanke hanyar Kaduna kallonshi take tace" wai nufinka Kaduna zanje"

"Aa nasan Zaria kike ko"

Murmushi tayi tace"to ni hunkuy nake"

Da mamaki yake kallonta,
"Yo aini ma d'ancan ne,"

"Dagaske kake"

"Sosai kuwa, kinga nida Adam fah yan uwane sosai, don da mama na da babanshi uba suka had'a"

"Haba shiyasa kuke Kama sosai.............jannat ga mutanen nan fah sunabin mu abaya"

Wata irin zabura tayi"nashiga uku na jabeer yazamuyi sai kuka,
Shi dariya ma tabashi belt yasaka itama yasaka Mata,wani gudun suka fara hakan yabasu damar suma suka shiga binsu da wani gudun,

Waya jabeer yayi daidai suna cikin wani gari, Wanda dagashi sai hunkuy,
Kamar wasa motocin yan sanda suka zagayesu guda hudu,

Duk yanda sukaso guduwa hakan yagagaresu,
Tsayar da motar su yayi jannat fuskar nan tayi kaca kaca da hawaye,

Fitowa tayi lokacin da y'asanda suka kamo su, sunsamu bindugu uku awajensu,
Dayake su uku ne suka taho,
Jabeer yace"yallabai kutai dasu station na cikin garin Zaria,zuwa dare zanzo na same Ku zamuyi magana insha Allah"

Haka aka tusasu gaba cikin motar yansanda suka tai dasu,
Sai lokacin tayi shiru, dariya kawai yake Mata,
"Dama haka kike da tsoro jannat, gashi kuma aikin ki baya buk'atar haka"

"Wallahi engineer ni ba wai tsoron na haka nan nake yi bah,kawai banason ban cika wannan burin bah ne akasheni,idan har sukaga bayana ayanzu,babu Wanda zai ceci Adam kila haka zai dawwama cikin wannan halin sannan kuma bancika alkawarin danayi bah na daukar fansar ran dady shiyasa duk nake Atsorace wallahi"

"Haka ne insha Allah komi zaitafi yanda akeso"

Tafiya Sukai bamai nisaba suka iso cikin garin hunkuy,
Yace"ina mukayi daga nan kuma"

Kwatan ce tacigaba dayi mashi,
Yana tunanin ai indai wajen datake Mai kwanace ne to ai gidan baba mamuda Dane,
Baigama tunani bah tace" yawwa kaga gidanmu can Mai gareji kalar ruwan toka."

Parking yayi ya kalleta yace"dama nan gidan kike, kodai rik'onki akeyi gidan don ni kaf y'an gidan nasansu, Amman basan dake bah"

"Ina kasan y'an gidanmu to"
Murmushi yayi yace"to Ai Alhaji malam kanen mama na ne"

Zaro ido tayi cike da mamaki,
"Kace k'anen mamanka ne, taya yazama k'anenta to"

"da mama na da Alhaji malam ubansu guda, kamar yanda nake da Adam, haka nake dake"

Kallon mamaki da al,ajabi take Mai,
Kenan Adam yayanta ne najini duk A bun nan itadasu y'an uwane kenan, to taya haka tafaru bamuda masaniya.................


*NIKAU NACE BAKIDA MAI BAKI WANNAN AMSAR JANNAT SAI IYAYENKU,KISHIGA ZAKUJI KOMAI*

*MUHAD'U PAGE NAGABA INSHA ALLAH*

TAKUCE MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻


_COMMENT D'INKU SHINE KWARIN GUIWARMU MU WRITTERS_

"Mama ni banga a bun tashin hankali anan bah,idan kunsan kuna da gaskiya why not kubada goyon Bayan kub'utar Adam daga wannan masifar, kubari Abayyana Wanda yayi kisan mana,wallahi nafara zargin wani Abu akai"

"Cikin masifa Zainab tace dalla wawuya rufe mana baki,
Wacce batasan inda kemata ciwo bah,
Don ubanki idan bashine bah gayaman waye, kuma zargin uban me kike iye"

"Haba Anty wallahi duk wani nuk'u nuk'u dakuke yi ina Lura akwai abunda kuke b'oyewa"

Sama yace"uwarki muke b'oyewa,to duk abunda zakiyi saidai kiyi Amman wannan Karon ma kece zakisake tsaya mana"

Zama tayi tafashe da kuka,
"Idan nayarda shegiya nake wallahi bazanba nagaji da abunda kukeman,kuna sakani dole inayin abunda bai daceba, inayiwa mijina k'age ina fad'ar a bun da bahaka yakeba,
To narantse da Allah banyi bazanba,
Sai dai kukasheni,Kuje kunemo Wanda zaiyi bazanba zanjira gaskiya tayi halinta Inbi mijina, nagaji dazama daku zaku saman ciwon zuciya"

Mama dai tashi tayi tabar wajen,
Ganin mubee tana ta zaro maganganu idan akacigaba da tilastata zata to na abunda suka sata tayi,
Ita kuma mama bata yarda da jannat bah,
Don rashin kulawar ta akan wannan A bun yana d'aure Mata Kai matuk'a.

Mama ta ce masu kar Wanda yasake Mata maganar,
Sukyaleta tukun sai nan gaba,
Sunajiran suga sammaci ne.

Jabeer ya samu ganawa da kotun,
Duk Abunda yakamata ayi anyi,
Anbashi takardar sammacin yataho da ita,ankuma saka ranar shiga Kara,
15/1/2017.

Hunkuy ya tsaya don gaida iyayensa,
"Ah aha yau kuma jabeer ne agidan namu"

"Wallahi kuwa goggo nine da yammacin nan,
Yafad'a tare da jawo kujera yar tsugunni yazauna"

"ina wuni goggo"
"Lafiya lau jabeeru, yakake ya kwana dayawa kuma"

"Alhamdulillah,Angode Allah ina mama bata nan ne"

"Wallahi taje gidan malam babanku mamuda,akan mutuwar nan,
Kasan tunda akayita bashida lafiya sosai"

"Ayya Allah yabashi lafiya lafiya,nima daga abuja nake na anso takardar sammaci za,koma wata kotun don cigaba da gudanar da shariar"

"Tsaki taja, yo jabeeru ai babu buk'atar sake wani zaman sharia,tunda Mai laifi ya amsa laifinsa"

Girgiza Kai yayi yace"Dan dai kawai kuna jin haushin Adam ne goggo,Amman wallahi bashine yayi bah,bai aika taba"

"Kai tafi can,anhad'a kai dashi ankashe ubanshi saboda dukiya,Wallahi wannan yaro yaban mamaki,ina tausayawa rayuwarsa Ashe shiyanacan yana hangen abunda yahango"

"Shikenan goggo tunda bazaki yarda bah,Amman inason ranar da za,ai wannan karar kuhalarci wajen saboda ganema donku gaskiyar Wanda ya aikata wannan kulalliyar"

"Zanwuce kanon sai nan da sati za,ashiga, zanturo ad'aukeku keda mama da duk Maison zuwa"

"Bakasha ko ruwaba jabeeru zakatai"

"Babu komi goggo dama nabiyo inganku ne, sai nasake dawowa,kicema mamar zamuyi waya"

Yafita yad'auki hanyar kano
Wayarsa yad'auka yakira jannat,

Ta na ganin kiran taje tasama k'ofar Key tadawo tazauna,
"Hello badai kadawo bah"

"Aa inadai kan hanya nabiya kauyenmu ne wajen tsaffina"

"Ok Allah ya iso dakai lafiya,
Ansamu Sa,a ko sunbaka takaddar"

"Eh yanzu haka gata nan sunbamu one week ne, sai muyi k'ok'ari muga munsamu abunda muka samu kan ranar"

"Insha Allah zuwa lokacin mun shirya,
Saidai wallahi bansan yanda zanyi nasamo key d'in akwatin nan bah"

"Karkidamu zansan yanda nayi nabud'eshi kobada key bah,
Yanzu zakisamu lokacin ganawa dashi yau kosai gobe"

"Gaskiya sai gobe, don yangidan mu sunga jaridar nan banmason kakawo takardar sammacin har sai nasamu ganawa da Adam,
Inason ranar dazaka kawota zanbar kano zankoma gidanmu dazama,"

"Shikenan gobe dayaushe zaki samu lokacin fitowa"

"Eh to zankiraka don dole mubi a bun asannu, don wallahi nasan mama ta na ankare dani,banson tazargeni bamukai ga shirya komiba,"

"Shikenan sai na iso, din sai muyi magana"

"To Allah yatsare hanya"

Sukai sallama ta ajiye wayar ta na ajiyar zuciya,
Don atsorace take da mama wallahi ta na iya yin komi don gudin tonuwar asirinta,

Kofita cin dare batayi bah har saida taji jabeer ya iso lafiya,
Sannan tasamu natsuwa,
Fita tayi tahad'a tea da cake taci,
Ta na kallon news Ana nuno labaran shariar Adam da tasu.

Zainab tace"hankalinki kwance ko jannat"

Murmushi tayi"Anti zainabu kenan, to yazamuyi Wanda yamutu fah bazai dawobah,
Duk wani nuna damuwa dazakai da tada hankalinka,hakan bazai saka yadawo bah,Abu guda zakai Wanda shine zai nuna kadamu da mamaci kanuna kaunarka gareshi, itace Addua"

"Kina nufin don mun nemi hakkin ran mahaifinmu kenan bamu damu dashiba kenan"

"Niba haka nake nufiba,kince hhankalina kwance bandamu bah shine nabaki ansa"

Mama tace"wannan karon jannat zata tsaya mana akotu"

Ta na tauna cake d'in bakinta tace"aa mama nida Zantai gida jibi, kefa ke korata kinacewa kingaji da ganina, Aa bazan iyaba gaskiya kunemo wani"

Duk kallon mamaki suke binta dashi,
"Jannat nikike gaya ma haka,bazaki iyabah kina nufin duk hallacin da Alh yayi maki yaraboki da kauye cikin bak'ar wahala yakawoki cikin iyalinsa,badan kin cancanta bah shine zaki sakama shi DA haka"

Tashi tayi tace "saida safenku mama bacci nakeji"
Tawuce d'akinta tabarsu nan cike da mamaki.

"Mama wallahi wannan yarinyar akwai abun da tataka, kina ganin A bunda tayi"

"Nagani Zainab dani take zance, Zan saka ido sosai akanta,don naga kwata kwata bata tare damu"

"Don haka nasan abunda zanyi dole akwai abunda take shiryawa"

Haka sukatashi da wannan shawarar,

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

Shiryawa tayi kamar dai koda yaushe,
Babu wata kwalliya Mai yawa silent make up ne afuskarta,bayan manta carotone datake shafawa,tasaka powder,kwalli, lipstick, riga da siket tasaka na atanfa sunyi matukar yimata kyau sosai,
Tasaka turarenta oud and explore.

After tasaka wadda tunda Alh yaje makka zuwansa na uku yasiyo Mata su Kala uku, sai dogayen riguna Kala uku,
Amman mubee ta anshe rigunan tabarta da guda,wai ai ita ta dace dasu ba jannat bah"
Murmushi tayi data tuno lokacin, tace"Allah yayafe maka dady don nasan kayiwa mutane dayawa laipi cikinsu harda babana,mijin dazan aurah"

Rollyn tayi tad'auki Jakarta da jotter dazata dauki bayanan Adam,
Wai yau itace zata kare mak'iyinta tsaki taja
"Bakai zankareba gaskiya zanbayyana"

Wayarta ta d'auko takira jabeer,
"Allah yasa kana kusa, don nashirya Zan fito yanzu"

"Ai bana da aikin dayawuce wannan yanzu,don haka hajiya jannat zata iya fitowa tasaman agida sai muwuce"

Murmushi tayi tace"shikenan rankayadad'e"

Dariya yayi yakashe wayar,
Tafara tunanin mezata cewa mama,
Ina zatace zata, karfa tasaka abita don mama zata iya koma miye,
Wata idear tafad'o Mata tai saurin fita don taji sama nacewa zaifita da yamma"

Mamace kawai falon,
Na gaidata nad'an zauna
Kallona tashiga yi sama dak'asa,
Ta tab'e baki zuwacan kuma tace"ina zaki haka"

Murmushi tayi tace"wallahi mama zanje gidansu mufida don yi Mata sallama, itada mamarsu tunda gobe sabko zanyi natai"

"Wai dagaske jannat tafiya zakiyi, bazaki Tsayawa Alh bah,lallai nayarda d'an Adam butulu ne"

Sama ne yafito yana gyara hula,
"Lafiya mama kike ta fad'a kedawa"

"Gata nan wai dagaske tafiya zatayi bazata tsayawa Alh bah,garinsu zata koma"

"Kik'yaleta mana tatafi mama,bake kecewa tatafibah
Kingaji da ganinta gara takoma wajen iyayenta haka ko tahuta da azabar da kuke Mata, tunbata da wayau"

"Au kaima goyon bayanta kake sama, ai shikenan sai muzauna babu lawyer"

"In dan ta lawyer ne zansamar mana akwai wani Abokina,
Zanb'arar dakud'i don ganin munsake nasara"

"Yah sama don Allah katafi dani ka ajiyeni gidan su mufida"

Murmushi yayi yace"bakida matsala muje,"
Har yayi gaba mama tace zo nan mana kai"

"kikatsaya kina kallonmu kije mota kijirasa mana"

Murmushi nayi Abunda nake zargi gaskiyane,
Mama bata yarda daniba sotake asamata ido Kai na,
Dariya tayi mai kyau,
Uhm nima na I ya takuna mama, idan ke sabko kikai ni ahanya nakwana naga mai nasara wannan karon"

*LALLAI INASO INA YANDA ZA,AI DAKUMA HAD'UWAR JANNAT DA ADAM*

KUKANSACE DANI
MAMAN MUHSEEN.✍🏻✍🏻

COMMENT AND SHARE PLS.


*MAGAJIYAR KAIMUWA*πŸ˜‰[1/14, 12:12 PM] MAGAJIYAR KAINUWAπŸ˜„: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*
_*(MRS BB)*_

_*[MAGAJIYAR KAINUWA]*_

_*LITATTAFAN MARUBUCIYAR....*_

RAI DA BURI
_(yake mutuwa)_
SAFAH DA MARWAH
SAINA DAUKI FANSA
A KWAI BAMBAN CI
AND NOW
RAYUWAR AMEERAH.


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM.

15&16.

"Ka tabbatar gidan su mufidar kakaita, sannan kasan yadda kayi kagano inda tayi daga nan"

"Sama kafita idona inaganin take takenka akan wannan tsigaggar yarinyar,Zan iyayin komi don rufuwar asirina, kasaman ido kanta kana jina"

"Wai mama zargin me kakewa jannat, bayan batasan komai akaiba,ki kwantar da hankalinki jannat bazata yi Abunda kike tunani bah.......,
"Kai dallah rufeman baki, mekasani akan haka nadai gaya maka kasaman ido sosai"

"Shikenan sai na dawo"

Yafita yasamu jannat bakin mota tanaji ransa,
Murmushi yake Mata Mai kyau Wanda ita tuni tagano inda yanufa,
Da ace baifito daga wannan ahalinba Zan iya amunce masa saboda baisara komai da mace kesoba,

Shiga tayi taja sukatai,
Janta yayi tayi da hira har sukaje gidan,
Bakin get din gidan ya sauketa,
"Tace nagode sosai yaya sama"

Murmushi yayi yace"bakida matsala idan kintashi tafiya kikirani zanzo na d'aukeki"

"Shikenan idan naga banyi dareba zankiraka byy tad'aga mashi hannu"

Saida tahango yawuce sannan tashiga,
Agurguje tashiga suka gaisa da maman sannan tashiga wajen qawar tata,
"Lalalala jannat kece yau shigo shigo, dama inacewa kwana biyu bamu had'uba"

"Mufee babu lokacin hira yanzu don inada babban uziri gabana yanzu ma fakewa nayi danan d'in, idan nakoma gida zankiraki don gobe zankoma hunkuy"

"Gobe kuma, haba jannat meyayi zafi har haka,kuma shine sai yanzu kike gayaman"

"Kiyi hakuri qawata wallahi inacikin wata chakwakiya,akan shariar rasuwar dadyne anyanke hukunci wanda hakan na shine dai dai bah,shine muka d'aukaka k'ara zuwa kotun Abuja,
Yanzu haka wajen Adam d'in zanje can prison"

Cikin mamaki tace"Amman jannat bakida hankali,Wanda yakashe wan babanki zaki nemi cetowa,shin saboda me kikehaka kingani matarsa ma tabarsa saboda haka saike da bakida alk'a dashi mekike shirin aikatawa"

"Kinga mufee, wannan A bun fah akwai wata mak'ark'shiya aciki saida na anshi case d'in na tabbatar dahaka, kedai tunda kikaga har na anshi case d'in kisaka ido kiyi kallo,fatan zakuzo keda mama"

"Dole ne Ai wannan Karon ne fah karonki nafarko, zanso inga yanda zakiyi nasara Allah yatai maka"

Wayarta tayi k'ara,
Jabeer ne dayake amota tagaya Mai inda zaisameta,
Mikewa tayi"mufee gashinan Wanda muke binciken tare, zamuje mudawo don ansaka man mat akan tsaro,
Sai nadawo"

Tara kota har bakin motar sannan sukatai,
"Meyafaru naga text d'inki d'azu"

"Uhmm kaidai bari, wallahi mutanen gidanmu sunfara zargina,don saida nayi dubara Amman duk da haka ban tsirabah,"

"Allah yatsare to, yanzu kenan goben dole zakitai"

"Dole na kuwa don idan suka ganoni ina cikin matsala don mama zata iyayin komai akan ganin bantona masu asiriba"

"Allah yakaimu"

Sun isa wajen hakanan taji gabanta yana fad'uwa,
Tun bayau bah duk sanda zata had'u da Adam sai gabanta yashiga fad'uwa,
Duk sanda zaizo zance wajen mubee itace take kai mashi snacks da lemo,
Jikinta har rawa yake idan zata shiga dakin, saboda aduk sanda suka had'a ido wannan kallon wulakancin dayake Mata shiyake tsaya mata arai,

Lumshe ido tayi tanajin gabanta yana tsananta fad'uwa,
Magana jabeer yake ma Mai kula dasu Wanda yasamu ne rannan dayazo,
Yauma kud'in yabashi yatafi don zuwarmasu dashi,

Kallonta yayi yaga idonta alumshe,
Yace"yadai barrister"

Bud'e idon tayi ta na murmushi "mekagani engineer"

"Kin Rama kenan, naga kin yi shiru kinrufe ido mekike tunani"

"Babu komi engineer, naji gabana yana fad'uwane shine nake addua"

"Subhanallahi lafiya dai ko"

"Lafiya lau insha Allah"

Shiru Sukai hango shi dasukai,
Gabanta yatsananta duka,
Adam ne haka shine yakoma kamar wani almajiri,Kai ko almajiri yafi karfin haka,
Innalillahi acikin sati biyu yakoma haka,sanda akai shariar baikai haka lalacewa ba,
Tabdijam, Adam din Mai gayu Mai isa da tak'ama Mai shegen miskilamcin tsiya,
Idan yawuceka dole saika lumshe ido don tsananin kamshin turarens,
Komai nashi Mai class ne,
Ko awancen lokacin bakomai yake burgeta dashiba illah wankanshi ya iya saka sutura, ko ko tsumma yasa kyau yake,
Shine yazama haka yarame yayi wani irin bak'i,
Adam d'in da har wani Ja yake saboda hasken sa Amman yanzu ji yanda yakoma, kamar k'warangwal
Jitai idonta yaciko da k'wallah,
Bata tabajin makamancin irin haka gameda Adam bah sai yau,
Bai tab'ata bata tausayi bah sai yau,
Saida tayi jarumtar gaske kafin tasamu tamaida k'wallar,

Suduka shiru Sukai,
Don Adam wani shock yakamashi ganin yarinyar da baitab'a zato bah agabansa,
Meyakawo jannat wajensa,
Kardai jabeer itace ya d'aukar mashi matsayin lawyer d'insa,

Yakasa kallonta don kunyarta yakeji bilhakki dagaskiya,
Jabeer yayi gyaran murya yace"Adam kullum k'ara lalacewa kake, wai wane irin aikine Mai wahala haka suke saka, basu tausayinka kalli yanda kakoma,
Adam kakakuwa ganka,
Wallahi ko zanyi yawo babu kaya sai natabbatar kabar wajen nan."

"Shikanshi kwallar ce cike da idonsa yace ina kuka had'u da jannat"

Jabeer ya kalleta ta sadda Kai k'asa,
Yace"itace wacce zata taimaka mana wajen ganin munkub'utar dakai, yanzu ma tazone don Ku tattauna,jannat yakamata kuyi maganar dazakuyi saboda kurewar lokaci,"

Jakarta tafiddo tadauko jotter da biro,
Tad'an zauna saman bencin dake kusadasu
Bazata iya kallon sabah zuciyarta zata karye,
Cikin muryanta datayi sanyi k'alau tace"labarin rayuwarka zakaban Amman kata k'ata saboda lokaci,"

Baiyi musubah yashiga bata labarin Abubunwan dasuka faru da rayuwarsa Amman hak'ikanin gaskiya yayi Mata hiding din wasu dayawa,
Yabari sai anje kotun,

Tad'auki abubuwa dayawa sannan tace mashi,
"Me dady yafad'a kafin yarasu"

"Yagaya man inda ya ajiye wasu muhimman abubuwanshi dazasuyi man anfani, sannan yagaya man inhar na samu nasarar d'auko wannan shaidun to zansami komi aciki,
Yaceman yana cikin d'akinsa cikin drower kayanshi.........
Cikin sauri tajiyo ta na kallonshi tace"Tabbas shine akwatin Dana d'auko d'akin dadyn,amman nanemi makullinsa bansamu bah,

"Yana wajena zanba jabeer shi yana tare dani, don banyarda dakowa bah balle nabashi,"

Jinjina Kai jabeer yayi yace"yanzu komai yazo dasauki,zakitafi gida hankalinki kwance saijiran ranar shiga kotu"

Kallon ta Adam yayi yace"jannat meyafaru ne agidan zaki tafi"

Kanta akasa tace"saboda gudun karsu lahanta ni, saboda sunfara zargina akan abunda ya far u,
Yanzu ne Nagane bakai ne kayi abunda ake zarginaba cikin gidan nan akwai abunda suke b'oyewa,
Sunada masaniyar wanda yayi kisan, lura da mama tayi kamar nasaka masu Idone yasaka tafara korata, akan in tattara nakoma kauyenmu,don gudun Karna to na masu asiri,
Ban tabbatar da cewa mama nada saka hannu cikim kisan bah sai dana samu wasu takaddu anmasu wani irin boyo adakinta,nakara yarda zurma ka akai"

Sadda Kai yayi yana jin wata wutar tsanar mubee da mamanta takara Kama shi,
"Yace yanzu mubee tasan wannan tayi man k'azafi saboda cikar burinsu,lallai nayarda mubeenat bata kaunata,"

"Mubee batasan abunda sukeyi bah,sundai sakata tayine itakuma tabiyema son zuciyarsu tasaka ka cikin wannan halin,
Kuma tayi nadama"

"Mutumen yadawo yace lokaci yayi fah,yakamata akoma dashi"

Kallon ta yayi yanason yabata hakuri irin Abubuwan da yaringa yi Mata agidan,
Yakasa yace wa jabeer"Amman yakamata ka kaita gidan goben saboda tsaron hanya"

"Yace insha Allah Adam, sai na sake dawowa kan ranar shiga kotun"

Haka Sukai sallama dashi suka tafi,
Zuciyar jannat babu dad'i rayuwar da Adam d'in yayi itace taketa Mata yawo akai,
Ta na jin babu dad'i cikin zuciyarta.

Batajira sama yazo yadauketa ba tatafi gida,
Binta Sukai da kallo cike da tuhuma,
Saida gabanta yafad'i don basu tab'ata Mata irin haka bah,

Tunda tashiga takasa fitowa,
Saidai duk wani motsinsu ta na jin shi,
Saida taji yunwa zata kassarata sannan tafito tashiga kitchen d'in,

Mama tagani,
Wani kallo tayi Mata tace"wai karfe nawa zaki tai ne goben"

"Cikin tsoro tace mama safi ya zanyi wajen takwas nabar kano insha Allah"

Tsaki mamar tayi tajuya tabar kitchen d'in,
Mamaki da faduwar gaba suka sako jannat gaba,
Daker tazuba abincin tafito,
Jikinta yakasa saki rawa yake Mata,
Har tagifta Zara wuce d'akin dakinta,
Tajiyo k'us k'us gabanta ya sake fad'uwa ta kasa kunnenta donjin meke faruwa,

"Mama wallahi itace zata d'aukesu idan ba itaba ubanwa yake zaryar fita, wallahi nalura da ita akwai munafurcin datake yi aboye"

Gabanta yabada dassss kardai sungano ta,
Nashiga uku ni jannat,
Mama taji ta na cewa"nasan abunda zanyi wayar ta tad'auko tashiga yin Kira zuwa can taji tafara magana,

Jannat tayi saurin kunna recording,
Jikinta yana rawa
"Barau Inason daya daga cikin yaranka yayi man maganin wata yarinya,
Gobe karfe takwas kabi hanyar kaduna, inason a batar mun da jannat yarinyar gidana ce takeson to na man asiri,
Bana tunanin zata bi motar haya,
Banason ta da rai kasanya tabar duniyar don nema take tatona man asiri"

Aguje takoma d'akinta jikinta rawa yakawai yake hawaye sunb'ata Mata fuska,
Wayar jabeer takira ta na kuka,
Kewaye tashiga tafashe da kuka bayan ya dauka,
Cikin tashin hankali take gaya mashi halin da ake ciki,

"Kwantar da hankalinki nasan abunda zanyi, karkiyi yunkurin guduwa kibari har lokacin tafiyar yayi,
Zanzo hargidan nad'aukeki alokacin zanbasu takardar sammacin,
Akwai abunda nakeson nayi, kinatsu insha Allah babu abunda suka isa suyi maki,
Kiman alkawarin zaki natsu tunda ina nan karkidamu kinjiko,
Zankula dake kamar yanda Adam ya bukata"

Ya lallasheta sosai tasamu natsuwa sosai Sukai sallama,

*KUKACENCE DANI TAKUCE MAMAN MUHSEEN*

COMMENT AND SHARE PLSS

_MAGAJIYAR KAINUWA CE_πŸ˜‰
[1/19, 11:03 AM] MAGAJIYAR KAINUWAπŸ˜„: πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€
*AKWAI BAMBANCI*
πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€


*_DAGA ALK'ALAMIN_*

*_AISHA ABUBAKAR_*
_*(MRS BB)*_

_*[MAGAJIYAR KAINUWA]*_

_*LITATTAFAN MARUBUCIYAR....*_

RAI DA BURI
_(yake mutuwa)_
SAFAH DA MARWAH
SAINA DAUKI FANSA
A KWAI BAMBAN CI
AND NOW
RAYUWAR AMEERAH.


*Ψ¨Ψ³Ω… Ψ§Ω„Ω„Ω‡ Ψ§Ω„Ψ±Ψ­Ω…Ω† Ψ§Ω„Ψ±Ψ­ΩŠΩ…*
___________________________________


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________

19/1/202.

17&18.

Wannan rana bata yi wani bacci bah,
Data fara sai tafarka saboda ta na ganin kamar har nan zasuzo su kasheta.

Ana kiran Sallar farko ta asuba tatashi, tashiga tattara yanata yanata ta na zubawa ga akwatinta,kayanta nasawa wasu takalma jakunkuna,komai takwashe ta kaddunta na makaranta suma duk ta tattara.
Saida taji ana kabbara sallah masallacin unguwar, sannan tayi Alwallah tazo tahau sallah babu b'ata lokaci.

Ta na gama wa wanka tashiga,
Bata jimaba ta fito tahau shafa Mai, shikad'ai ta shafa sai man baki ta zira kayan ta, ta matsu taga lokaci yaja, so take kawai tabud'e idonta taganta Gaban babanta da maman ta.

Wayarta ta jare daga caji tashiga kiran jabeer,
"Allah yasa kinsamu bacci dai jannat wannan sammako haka"

"Wallahi bansamu baccin yanda nakeso bah,Har k'agara nayi gari yawaye"

"Inata magana banma gaisheka bah, ina kwana yagajiya kuma"

"Haba gajiya tabi lafiya,yanzu kinshirya ko"

"Ai Jannat engineer take jira kawai,"

dariya yayi yace"to ga engineer nan tafe insha Allah"

Wanka nafito ina shiryawa bari na k'arasa idan na iso zankoraki,"

"OK sai ka iso d'in"

Taka she ta na tuna wa da sahibinta sagir,
Idan suna waya komi yakeyi zai sanar da ita,
"princess zanshiga wanka, princess nafito shafa Mai nake, kozaki taya ni.
Ganinan break nakeyi bud'a bakinki nasamaki,koda yake ma princess d'ina tafison nabakin hayaty d'inta ko"
sune Kalamam daya maidasu kamar ruwan shan shi, bayajin komi yagaya Mata zai shiga wanka,baidamuba don bak'aramin so yakeyi Mata bah,
Idan kuwa tayi fushi dashi har kuka yake Mata awaya, kokuma idan yazo zance,

Wasu hawaye suka ziraro Mata masu zafi,
"Allah sarki sagir, Allah yajik'an ka da Rahma, Allah yayafe maka, duk Wanda yayi sanadiyyar rabaka da numfashinka Allah kasaka ma, karya yabar Wanda yayi wannan A bun yahuta, kuka tafashe dashi don batajin yanzu akwai wani namiji irin sagir d'inta,
Don shi is very simple man, baid'auki kanshi da zafibah haka rayuwarsa yana yinta saisa saisa,
Haka A bun duniya bai damai bah,idan yana son Abu zai mashi wani irin so na gaske gaba D'aya zuciyarsa yake baka, ga ririrtawa ga iya soyayya zata iya cewa batasan komi akan love bah saida ta had'u da sagir, duk wani salon soyayya Ya koyar da ita, gashi yatafi yabarta da mikin kaunarsa...........wayarta ta katseta daga cikin shaukin soyayyar marigayi sagir,
Engineer Tagani tayi saurin d'auka.

"Zan iya shigowa kiyimam iso ga mutanen gidan"

"Ok"

Tatashi tafito falon babu kowa kamar ma bawanda yatashi,
D'akin mama tayi wa tsinke ta same ta tayiwa d'akin filla filla da alama akwai Abunda take nema,

"Mama ina kwana."

Cikin fad'a tace"lafiya"

"Mama ga jabeer yana son yashigo zai magana daku."

"Yayi magana damu yace mana uban me, nace mezai cedamu munafuki Algungumi Mai son tada zaune tsaye."

"Kiyi hakuri mama nifah sakone ya bani yana son yashigo."

Zainab ce tafad'o kamar ankirata,
"Mama kyaleshi yashigo muje dame yake tafe, takalle ta cikin kallon k'ask'anci tace kina iya shigo dashi ai"

Fita tayi Takirashi tare suka shigo,
Ga mama ga sama ga Zainab,
Sai mubee data tatashi saboda hayaniyar mamar.

Kallon wulakanci suke Mai,
Bakamar mama jitake kamar ta shak'eshi yamutu.

"Mama ina kwana, ya aka k'araji da hakurin wannan rashin.............. Kai dagata man kajiko bana ciki da iskanci,meyaka woka nan gidan har kake son Magana damu"

bai magana naba, ya fiddo zareriyar takardar sammacin, yamik'awa mubee dake kusa dashi.
"Yace ga dalilin zuwan nan,don haka kunada sauran kwanaki biyar sai mun had'u kotun."

Wata irin zabura mubee tayi ta na wullar da takaddar,
"Tasha gabanshi, mekake nufi jabeer, gayaman mekuke shiryawa kaida wannan Annamimiyar yarinyar"

Bai bata Amsaba yace"jannat muje ko lokaci yana tafiya"

Kamar jira take tashige gaban, yarufa Mata baya saida yaje k'ofa yace"Abunda Kika kasayiwa mijinki shine ita zatayi,don haka kisama ranki ruwan sanyi kinji Abunda zatayi"

Wata ma haukaciyar ashar Zainab ta k'unduma,
"Babbar bala,in nan mama kinaji kinajin Abunda yake fad'a,jannat zata kare Adam,mama kenan duk wasu evidence tagama samunsu bamu sanibah, wayyo Allah wallahi bazai yuwubah"

Waya mamar ta d'auko,Cikin wani irin fushi tafara kiran wayar,
Sama yafizge"haba mama mezakiyi,badai suma sawa zakiyi akashe subah, Aa kibarmu muji da wannan ma idan kika sake aikata wani shikuma wa zamu lik'amawa,sannan tahaka asirin mu zai tonu kibarta ta tsaya mashi mana ina da tabbacin lawyer da na d'auka bazai barta tayi wani nasara bah"

"Dallah kauce man nan, muddin wannan yarinyar ta tsira da hujjojinta mungama yawo gamucan gidan yari, don haka yau saitabar duniyar"

Maigadine yashigo yakawo Mata number motar jabeer,
Dayake Zainab takirashi lokacin da jannat tafita don shigo da jabeer din.

Murmushi mamar tayi tashiga yin kiran wayarta,
"Barau ba gaisuwa nakira na ji bah,ga number motar nan zanturo maka, yanzu haka sun d'auki hanyar kaduna,katabbatar kazo man da labarin mutuwarsu karka barsu da rai barau wannan karon har bashin dakake bina zan had'a inbiya ka"

Idonsu yarufe basu San mubbe na wajen bah,
Saidai sukaga tafad'i tim kamar gawa............

πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€πŸŽ€

"Ki kwantar da hankalin ki jannat babu Abunda suka isa suyi mana, insha Allah kizuba ido kigani."

"Wallahi jabeer nasan halin mama, batada imani zatayi komi don ganin bayan mu, burinta kar asirinsu yatonu nikuma inhar nacika yar halak bazan bar hakkin ran dady bah,saboda wannan mutuwar babana na can kauye har yanzu kwance yake bashida lafiya,duk da irin Abunda dady yayi mashi hakan bai saka yashare shi bah,"

"sannan nayi alkawarin fitar da Adam daga halin dayake ciki,"

"Allah yabaki iko, yakuma tai makemu baki d'aya, yakamata mutsaya muyi break ko"

"Jabeer kawa Allah kayi hakuri dawani break,muna ta tserar da rayuwarmu kai ta wani breakfast kakeyi"

Dariya yayi yace"wallahi ninan hankalina kwance yake kema kuma zaki nemi Abincin bari dai tafiya tayi nisa."

Gudu yake shiyasa sukayi sauri,
Don har sunyanke hanyar Kaduna kallonshi take tace" wai nufinka Kaduna zanje"

"Aa nasan Zaria kike ko"

Murmushi tayi tace"to ni hunkuy nake"

Da mamaki yake kallonta,
"Yo aini ma d'ancan ne,"

"Dagaske kake"

"Sosai kuwa, kinga nida Adam fah yan uwane sosai,

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment