Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gaba araina nace saikace kullum dashi mukekwana indai wanna duminne banaso.saiyagyara zamansa yasanya hannu mukacigaba dayin break din tare,koda muka gama saina kwashi kayakin nakaisu kitchen kodana dawo dakin saina taddashi tsaye rikeda mayafina ahannu yanaganina saiyayi saurin masowa inda nake yasanyamin gyalen akaina saiyariko hannuna yanafadin taho mutafi lokaci zaikuri"binsa dakallon tanbaya nayi kannace wani abu Mommy dayanzu shigowarta tarigani fadin ina kuma zaka kaita bayan kasan balafiya garetaba,yace Mommy wani rashin lfy kuma kokinmance 11:30pm zamubar kasan,kiduba kiga yanzu 11:19pm,zatakuma magana saiyayi saurin sakin hannuna yakariko na nata yace Mommy da itazamutafi dole saboda wanna time din bazan samu damar kuma zuwa Nigeria dawuriba Mommy to taya zanyi natafi nabarta,dan ALLAH Mommy kada kihana intafi da ita pls,bakaramin dadi Mommy tajiba aranta dankuwa tasan RUMAINA tasamu babban muhalli acikin zuciyar dan nata bazatamance lokacinda Nazeerat take kuka akan zatabishi shikuma yaki harsaida itada kanta tatirsasashi kafin yatafi da ita saigashi yau shiyakeson tafiya da RUMAINA har yana magiya,saitayi hamdala ga Ubangiji daganin dannata yasami farinciki ga matar nasa,saitadan batarai sanna tace,kada katafimin da diyata kaje karika wahalarmin da ita kokuma karikayimata mugunta har idan nasami labari tofa dakaina zanji nadauki yata,dasauri yace ALLAH Mommy nayarda saiya sanya hannunsa a aljuhu yazaro waya ,yace wanna wayar natane dazunna nasaimata shi kinga tawanna hanyar zaki rikajin komai daga gareta,cikin jin dadin kalamansa saita jawo ni tahadamu gabadaya tarungume tanafadin ALLAH yayimuku albarka yadauwamar da farinciki arayuwarku, ameen muka amsa dashi,nan tariko hannumu mukafito waje har parking lot takaimu ,kaman anyi usur wa yangidan sukarika fitowa sunaimana fatan alkhairi nida Ummee da Basma rungume junarmu mukayi saikuma mukafashe dakuka dakyar Mommy tajanyeni tashigardani cikin motar sanna ta umurci driver yaja mutafi"nan motocin sojoji sukarufamana baya da jiniyarsu,muna fita daga gidan saiyajanyoni jikinsa yarungume yana bubbuga bayana,lamo nayi ajikinsa sai sauke ajiyar zuciya nake,batareda bata lokaciba muka isa airport munasauka anakiran sunanmu,driver yadau akwatinmu ya isaga ma ay katan jirgin,jama'a saitururruwar zuwa suke sunata gaisuwar da kirarin bangirma,sunafadin ALLAH yakare NAKOWA yatsaremaka hanyarka,shiko sai daga musu hannu yake yanabinsu da murmushi,yana rikeda hannuna muka haura matattakalar jirgin.saiware ido nake waiyau nice acikin jirgi mamakina bai karuba harsaida mukashiga cikin jirgin,nan nashigayiwa Ubangijin hatittu tasbihi lallai ALLAH maigirmane kuma mai daukaka maiyin abundayaso gabawansa,lallai wanna rahamar daga ubangijinane,sit dindayake tacan baya mukazauna ni inata gefen window shikuma yanagefena, koda ma ay'katan suka fara sanarwa akan adaura belt's jirgi zaitashi nidai ido nakurawa sarautar ALLAH dan bansan ta inada zanfaraba,saibin mutanecikim jirgin nakeda ido ganin kowa natakorin daura belt's insa araina nace yau akeyinta,ban inda tunaniba sainaji hannuna ajikina yana sakalamin belt' in,nasauke numfashi ahankali,yana gama dauramin shima yadaura nashi,batareda batalokaciba jirginmu yadaga.......
4:00pm na Nigeria wanda yayi daidai da 2:00pm abirnin Switzerland ,jirgin yasauka ababban filin saukar jirgi dakecikin birnin Switzerland.
Bayan minti 15 dasaukar jirgin asannu jama'arciki sukafara sauka,muma mukarufamusu baya"ya'ilahi yalillahi fatubarakallah masha ALLAH"abunda nafurta kenan lokacinda nasinci kaina acikin birnin Switzerland, fadar tsaruwansama batalokacine, dagacan wasu mutane masu sanye dakakin sojoji nakasar Nigeria dakuma na nan kasar Switzerland din sukafito daga cikin wasu motoci wanda akalla yawan mutanen sunkai 30 cikin sauri sauri gudu gudu sukanufomu gamanyan bindigogi ahannunsu sunkuma daddaga bakin bindigar kamar masushiga filin daga.cikin firgici da kidima narike hannunsa da karfi jikina narawa nakifa fuskata jikin damtsen hannunsa,cikin hanzari yadagoni tareda juyodani gabansa yace menene meyasameki??zillewa nayi nashige cikin kirjinsa sainasaki kuka cikin muryar kuka nace banason ganinsu tsoro sukebani,dada rungumeni yy yanafadin sojan susuke baki tsoro?" cikin sauri narika nagyada masa kai"murmushi yy maisauti saiyace kedayau zakisa kayan soja kokinmance kematar soja ce to amma kike tsoron soja,saiyashiga bubbuga bayana alamun lallashi,nidai dada cusa fuskata nayi cikin kirjinsa...
Suna isa dafdamu sukatsaramasa tareda kamewa guri guda,wani dagajikin sojan narikedawata riga Wanda tun durowarsu daga saman motocin rigar dakuma hula rigar irin nasune,cikin girmamawa irin nasoja yakima tsaramasa sanna yamikamasa rigar"shikuma yamika hannu yakarba nan sojan yakuma kamewa,asannu yacironi daga cikin kirjinsa yanayimin magana cikin kasa damuya yace idan kikabari sukagane tsoronsu kikeji tofa harbeki zasuyi dan haka yanzu kiboye tsoron nasu kinuna kamar bakijin tsoronsu zakiga su yanzu sundawa jin tsoronki kinji?cikin dardar nagyada masakai yace good girl, rigarda kerike ahannusa yasanyamin gabanrigar abudeyake ana iya hango kayana wanda dama yake jikina sanna yakuma daura hular akaina saman gyalena" saiya juyar dani kamar yanda yake tsaye muna fuskantarsu,jinayi kamar nakwalla ihu dana kalli jikina nakuma kalli gungun sojojin dasuke tsaye agabana,danatuna cewa idanfa naji tsoronsu tofa harbeni zasuyi saina tattaro duk wata jarumtata nahadeta guri guda nakankame hannunsa dakecikin hannuna,yana juyo dani gabadayansu suka kuma tsarawa hadeda kamewa"hannusa yasaka daidai saitin kunnensa alamun tsarawa saiyacemin kema kiyi yanda nayi dakyar na iya daga hannuna nayi kamar yanda naga yayin"saisuka daga bakin bindigoginsu sama suka saki harbi tas..tas.."cikin rudu da dimaucewa nacakumeshi tareda kwalla kara,dasauri yarirrikeni taredayima sojojin nuni dahanu sutafi,nanma saida sukadada tsaramasa kafin sukajuya sukaje jikin motocinsu,
Mannani yadadayi akirjinsa nace wayyo ALLAH zasu harbeni nidai kamaidani gida bazan zauna ananba,yarankwafo dakansa yakawo bakinsa saitin kunnena yace gaisuwafa sukeyimiki ba harbinki zasuyiba,nidai kin sauraransa nayi Dan gabadaya nagama firgicewa, saiyajanyo hannuna muka isa jikin wata mota kan mukaraso aka bude marfin kulle idanuna nayi harmukashiga motar wani soja dakecikin motar yaja muka haura titi...........



Comments and Share




MOMMYN TWINS CE

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

ALFARMA

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼



*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*






🅿99👉🏻100😥👋🏻


T.H Hospital mukatafi, muna isa direct labour room akawuce dani,Ya IB narike da hannuna koda akazo shigadani room d'in saida Mommy tayi dagaske kafin Ya IB yasake hannuna dan kafewa yayi yace sam saidai mushiga tare,Mommy tace masa akwai matan aure dayawa aciki suma labour sukeyi baikamata yashiga kansuba, zuwa lokacin fadar kalar azabar danake ciki bazai misaltuba,

Minti 30 da shigata kand'a yasako kai wayyo ALLAH! Ubangiji yakarawa mata juriya da jarumta,yau nad'an-d'ana azabarda duk wata uwa takesha kafin tahaifo d'iyarta, dataimakon nurses dan ya idda fita,suna zaroshi wata sabuwar nakudar tatashi,cikin ikon ALLAH banwani dau lokaciba wani dan yakuma sakokai,nan suka kuma janyoshi,nan take yaran suka gauraye room d'in da kuka,numfashi nashiga saukewa inayiwa ubangiji godiya,saida akakai yaran gun manyan likitoti sukaduba lfyrsu kafin suka dawo dasu suka shiryasu cikin kayan tsanyi,saida suka gama kafin sukafito sukasanarwa su Mommy cewa nahaiwu tahaifi Baby twins,ai dasauri Ya IB yakusa kai zaishiga labour room din nurses d'in sukadakatar dashi,tahanyar cewa bamatarka kadai cikin room d'inba kajira yanzu za'akaita dakin hutu,
Mommy kam bakinta yakasa rufuwa sai hamdala takewa sarkin halittu,

Bayan sun kimsani da duk wata kula dayadace subani sai akayidani dakin Hutu,nan Ya IB da Mommy sukasami damar ganina,yakwashe yaran yarungumesu akirjinsa yakasa boye tsantsar farincikinsa agaban Mommy yahad'ani dayaran yarungumemu.yace UMMU RUMAINA kingamin komai arayuwa yara biyu kika haifomin lokaci guda.saiya sakeni yajuya gun Mommy yace Mommy kitayani yawa Baby godiya kiduba kiga kyawawan y'ay'an da tahaifamin,murmushi Mommy tayi takarbi d'aya ahannusa tanafadin masha ALLAH ubangiji yaraya manaku da imani,

Kankace me y'an uwa da abokan arzikin familyn IB NAKOWA suncika Hospital din, ganin haka yasa Dr zuwa yaduddubani ganin babu wata matsala saiya bamu sallama, muka tarkasa mukakoma gida.

Tuni labarin haihuwar ya'iske su Mama,sunyi farinciki mara misaltuwa, washe gari Umma Halima tazo nayi murna sosai daganinta,Hajja Umma da Mommy da Hajiya Maryam kanwar Mommy sai Umma Halima dukansu suke kuladani, Ya IB kuwa kullum muna tare dashi saidai idan yan barka sukazo,bayanda ya'iya haka zaifita,yanafita kuwa zaikirani awaya yacewai nasanyawa yaransa wayar yarikajin numfashinsu..

Gata iya gata nagansa ahaihuwarna sai nan da nan akedani motsi kadan za'atanbayeni kodawata matsalace,

Amarya Ummee sunzo da angonta Anas, Khadija ma tazo,sai dare mazajensu suka maidasu gida.Basma kam kullum muna tare da ita tanalike ajikin yaran,
Kwana uku da haiwuwa Ya IB yayiwa yaran huduba,Hassan akasanyama Basheer wato sunan mahsifinsa,yayinda yasanyawa Hussain sunan Babana wato Adam,
Za arika kiransu da Juhaim da Junaim,


Tun ana saura kwana uku suna Ya IB yasa akarika kawo kayaki d'aki guda akaware nashirge kayan,har ranar suna ba'afasa shigowa da kayakiba,ganin yanda ake shigo dakaya kamar bada kid'i aketsayaba,nakirawosa awaya nace kayanna sun isa haka meza'ayi dasu haka?yace akwai wasuma dayasa asaya a Switzerland sunacan.nace todai abarsu haka,yace angama madam duk yanda kikace hakan za'ayi.


***********
Ranar suna anyi bidiri da bured'e dankuwa duk girman BAUCHI saida tadauka,bakaramin kudi Ya IB" da Mommy suka narkaba,
Su Mama ma ba'abarsu abayaba suma sunyi kokari sun zuba bajintarsu dai-dai iyawarsu,
Kyaututtuka kam nasamesu ba'adadi,dan hatta gwomnatin BAUCHI, nasami kyauta daga gareta tasanadiyar Ya IB"

Anyi taro anwatse cikin kamala da mutunci,bayan suna dakwana biyu Ya IB yatafi Switzerland sakamakon kiran dayasameshi na gaggawa,
Yan uwanmu da sukazo daga Bokos sukanimi tafiya dani naje nayi wankan gida,Mommy tasanarwa "Ya IB yace sam baiyardaba yara basuyi kwariba suje susha iskar mota harsudebi wata cutar,baitarda atafi masa dayara ko inaba yanzu,

Mommy dai hakuri tabasu Umma Halima tareda alkawari har idan mukayi arba'in zanzo..

Kullum muna makale da Ya IB akwaya munazuba soyayyarmu son ranmu,


**********

Bayan arba'in

Ranar da mukayi arba'in,nashirya kayana nazuwa Bokos, washegari Mommy tasa driver yadaukemu nida Basma tarike Juhaim,maisunan daddynsu,nikuma inarike da Junaim, maisunan Baba, batareda bata lokaciba muka haura hanya.

Koda muka iso Bokos narika baza idanuna ahanya,muna isa unguwarmu kuwa nasha mamakin sauyin da akasamu tundaga farkon layin harzuwa kofargidan da driver yayi horn abakin get d'in gidan,
Wani dattijo yataho dagudu yawangale get d'in, a parking lot yadaidaita Parking mukafito nabude baki zan tanbaye driver inda yakawomu, saina hango Hafsat dagudu tafito tanafadin oyoyo Aunty RUMAINA sun'iso.ta'iso takarbi Junaim tace sannunku dazuwa, tayi gaba mukabita abaya,zuciyata cikeda tanbayoyi shin wanna wani gidane,munashiga nagama Mama tsaye atsakar gida tana ganinmu tafad'ad'a fuskarta da murmushi,tace lale sannunku dazuwa, kushiga tanunamana wata kofa,wata lafiyayyiyar parlour muka shiga cikinta muka zazzauna saman lafiyayyun kujerunda suka Kawata parlour, Mama tashigo takawomana abubuwan ci dasha,mukaci mukasha,kankace me yan'uwa da abokan arziki sukarika tururruwan zuwa yimana barka dazuwa dakuma tayamu murnan samun karu,
Yamma lis Baba yadawo gida shima yayi farin ciki daganinmu, yadibi yan jikokinsa yayita sanyamu albarka.
Da daddare baya kowa yawatse muka kebe da Mama nan take sanarmin tulin alkhairin da "Ya IB yayi mana take kuma sanarmin shiyaturo ma'aikata akarushe gidanna akagina wanna ginin,nasha mamaki dankuwa Ya IB baitaba yimin hirarba,nan naji sonsa nadad'a yimin yawo acikin zuciya.koda nakoma dakin dazamu kwana nakirasa dannayimasa godiya akan alkhairin dayayi mana sai cewa yayi indai bawata magana nakeda itaba to sai anjima..

Kwananmu uku Basma suka koma da driver sukabarni anan,
Nazaga gidan yan'uwa sosai.kwanana 20 agidanmu Ya IB yazo babu sanarwa.haka aranar yace bana kuma kwana sai a BAUCHI,nayitayimasa magiya akan yabari mukara koda kwana d'ayane yace baiyardaba, su Mama ko komai basuceba,haka yakwashemu muka tafi.

Kodamuka isa duk yanda yaso mukeb'e firnaki dan ina cikedashi,kwananmu hud'u da komawa yashigo bedroom in Mommy inazaune abakin gado ya isa yazauna kusa dani,batareda yakalleniba yace kishirya gobe idan ALLAH yakaimu zamu koma Switzerland,nakar da kaina gefe nayi kamar banji abinda yafadaba,shiko baikuma cewa komaiba saima mikewa da yayi yaje gaban gadon Juhaim da Junaim,yarika lilasu harsaida sukayi barci yagyaramusu rufuwa yatofesu da addu'a kafin yafita.......

Karfe 4 na asuba jirginmu yatashi zuwa Switzerland,koda muka isa masu taranmu suka debebu zuwa gida,tun isarmu gida dayafita bankuma ganinsaba sai bayan sallar isha, lokacin har Juhaim da Junaim sunyi barci, nima nayi shirin barci inakokarin kwanciya yashigo da sallama,na'amsa tareda hayewa gado nakwanta najuya fuskata tacan, tube kayan jikinsa yy yafada bathroom yy wanka sanna yafito yasanya rigar bacci mai madaurin igiyoyi tagaba,sanna yahaye gadon,yadagoni cak yadaura samansa yasanya hannunsa yazagayeni dashi,asannu yayi magana acikin kunnena,kitaimakeni kidaina fushi dani kiyimin wanna AL'FARMAN narokeki,kaina najuya nahadefuskarmu yanayin yanda yayi maganar saida tsigar jikina yatashi yarrrrr,nace Ya IB nima nakasa jure fushi dakai dan ALLAH kayafemun naroki AL'FARMAN ka,goga fuskarsa yy anawa sanna yake dan ALLAH kicigaba da yimin AL'FARMA irin haka Baby,nace Ya IB indai wanna shine AL'FARMA to zanci gaba dayimakashi har karshen rayuwata,cikin tsananin farin ciki yahade bakinmu daganan zancen tasauya muka lula duniyar maji dad'i.


TAMMAT BIHAMDILLAH👏🏻

TO MASU KARATU AYAUNE NAKAWO KARSHEN WANNA LABARI NAWA, MASOYANA INAYIMUKU FATAN AL'KHAIRI SAIMUN SAKE HADUWA DAKU A LITTAFINA NAGABA,NGD NGD NGD MATUKA DA SOYAYYAR DAKUKA NUNAMIN RABBI YABAR KAUNA💓


MOMMYN TWINS ZANYI KEWARKU👋🏻😥

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment