Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

masaukina zan koma,saikuma allah yy ikonsa" shigo muje kikaini gidanku,ai ma gagidanmu na banisa nanunamata da hanu"
Nayi gaba sukabiyoni damotar ahankali har muka isa kofar gida,
Saida nasaya tafito tukun nayigaba tabiyoni abaya, da annashiwanta shinfede akan fuskarta tayi sallama,baba nazaune akan taburma mama kuma na kitchen mama tafito daga kitchen tanafadin sannu dazu.baba yace ikon allah sannu dazuwa hajiya maraba lale,kallon baba nayi jin ya am'baci hajiya todama yasantane.mama tadauko taburma tashinfida mata tanacigaba dayimata sannu"tareda nunamata taburman tanafadin bismillah cikinsakin fuska take am'samusu"tazauna bisakan taburmanna babu nuna kyama agaremu irin wanda wasu kasukudi kenunawa talaka,tabaje mayafinta akan taburman.mama tasami gefe bisa taburmanda baba kezaune tazauna.nan sukafara gaisawa
Nima guri nasamu nazauna,bayan sungama gaisawa "hajiya tanisa tace,sunana hajiya amina.nice wacce takade RUMAINA kwanakin baya datawuce,dukda cewa na ai kata laifi tuntuni hakan bazaihanani zuwa inbada hakuri yanzuba dannasan ban kyautaba dan allah kuyi hakuri akan sausayinda tafaru shikara daya datawuce, kuma nagaza tako kafata tuntuni saiyanzu,kuyimin afwa"mama tace ikon allah baiwar allah ai alokacinma bataji rauniba kuma tafadamin saida kk kaita asibiti kafin kk barta tazogida, inaga wayanda suke kashemutum sukumaja abinhawansu suyi tafiyarsu, ai bakomai wlhy abinda yawuce tuntuni.baba yakarbi zancen hajiya mungode sosai danmu yakamata muyimiki godiya bakeba,hakika bazan taba mance alkairinki garemuba,hajiya taji dadin yadda su mama suka karbeta matuka,mama tamike tadibo mata ruwa akofi ta aje gabanta araina nace yaushe zatasha wanna ruwan mutanen dasuke rayuwa da faro mezai zaisa tasha ruwan rijiya...bakinabude danganin tadau kofin takafa abakinta tasha ruwan kuwa dadan yawa.nan suka fara hira jifajifa.acikin hirar tasune take tanbayar ina aji nawa amakaranta,mama tace kwana ukunna data wuce sukayi gasar gama islamiya.boko kuma tasaya a aji uku na sakandiri,baba yadaura dafadin insha allah yanzukuma zataci gaba dan dama jira nake sugama yayenna hankali yakwanta sai takoma makarantarta da da yasaya ahanya sakamakon halin rayuwa"hajiya tace allah sarki nafahimta,saitadanyi jim kadan cankuma tadago tadubi su mama"am idan da zanbada shawara takarbu da nabada akan karatun RUMAINA" baba yace muna sauraronki" takyara zama,mezai hana asama mata makaranta acikin birni bawai danna rainawa karatun kauyeba bakuma zantaba ba dankuwa nima akauye nayi karatun"mace kamar RUMAINA yadace ace abirni zatayi karatu dan gogewa da wayewa kudubi irin baiwar halitta da allah yy mata,inayimata sha'awar cigaba arayuwa.bawai dan narainawa irin cigaban datakedashi ayanzuba"
Kubani ita naje nasanyata amakaranta dan RUMAINA zatayi kyau da Dr "
Ai bansan sanda murmushi yasubuceminba danaji tace zanyi kyau da Dr,aduniyarna bb wanima aikacinda yafi burgeni samada likita,shiyasa nake burin zama likita" gashi yau hajiya tasosamin inda yakemin kaikayi....

Baba da mama suka kalli junansu "hajiya tayi murmushi taciro kati daga jakarta tamikawa baba "kamar yanda nafada muku sunana aminatu bashir inadazama acikin garin bauchi unguwar G.R.A" tamike saye tanan zaka iya samin cikakken labarina tanuna masa katinda tamikamasa.kayi bincike akaina,nidai dan allah kada kuhanani RUMAINA wlhy tunranda nafara ganinta naji takwantamin arai" kuma insha allahu nayimu alkawari RUMAINA zatazamo cikakkiyar likita"zan tafi idan allah yakaimi gobe zandawo kafinna anyi bincike akaina,tayiwa su mama sallama tafita.kasa cewa komai sukayi saizuwacan baba yy gyarar murya,hakika wanna matar tayin abunda bazan taba mancewa dashiba,mama tace wainikam menene wanna matar tayi makan aina kasanta?kintuna ranarda nafita nadawo da kudi masuyawa gidanna tun lokacin munacikin halin rashi?.ranarda nafita danzuwa gona na nome yan ciyayenda suka fito acikin masarar dana shuka mudu biyu,bayan nagama nazo zanhau kekena sai kaca tatsinke narasa yanda zanyi gashi lokacin yamma tayi gakuma hadari.haka narika tafiya akafa inatura kekenna ,wata mota tazo tawuceni saikuma motar tadawo dabaya,matarna tafito daga cikin mota tacedani nazo susaukeni acikin gari dafari kinyarda nayi dan kinsan wasu mutanen ba abun yarda bace,tafahimci hakan saitacedani insa allah daya araina nashiga,hakan kuwa akayi bayan sun kawoni bakin hanya,tasa direbanta yasaukemin kekena wacce akasa abayan but nayimata gdy harna juya zanwuce.tacedani dansaya malam.tasa hannu cikin jakarta taciro kudi masu yawan gaske tamikamin nakalleta dahalamar tanbaya.
Tacemin rike mana inakarba direbar yatada mota.atakaice tacemin nabaka.kafin nanumfasa saiganin motar nayi cangaba" indada tunamiki da kyau bayan nadawo gida nashaidamiki abunda yafaru"nanimi shawarinki akan me kk ganin za'ayi dawadanna kudin.nan mukayi shawari nayi nomar shinkafa,cikin ikon allah shinkafar tayi albarka wacce gashi tasanadiyar kudinda tabani yazamemana rufin asiri"muna walwala muci musha harmu taimaki wadanda basadashi hankalinmu kwance...
Allah akbar dama itace matar allah mai iko lallai wanna mata zuciyarta farine tass,
Azamanin yanzu ba'acika samin irinsuba cewar mama,baba yace hakane,amma zanyi bincike akanta kamar yadda tace,dannima inada burin ganin mamana tayi karatu...

Tun yammacin baba yafara bincike akan hajiya har wayewan garinyau.duk wani labari akanta yagama tattarowa,zaune suke adaki shida mama.nagama bincike akan hajiyarna,ashe matar alhj bashir nakowa"ne ita.da mmk mama tace wani alhj bashir nakowa"wanda nakejin labarinsa agidan radio margayi mai gidajen man fetur kaf Nigeria har kasarwaje?" kwarai shine mijinta,alabarin dana samu shine kafin yarasu yawakiltata duk shekara tarika zuwa garinna tana bada zakka.............




Comments and Share




MAMYN TWINS CE
12/30/19, 14:53 - 拼ar Gatan 茦ainuwa: 馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲
ALFARMA
馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

by鉁嶐煆�
Rasheeda S' Director




Page 8



"""""Shiyasa duk shekara take hanyar zuwa garinna.mama tace allah mai iko 'wanna mutumin hakika yajidadin rayuwa kaduba kaga tunyanada rai yakegudanar da ayyukan alkhairi harkuwa yakoma ga mahaliccinsa.sadakatujjariya tana dadagudana.ubangiji allah yajikansa,ameen baba yace sanna yadaura dacewa hakika inamatukar son naga yata guda daya tayikaratun boko, amma tafiyarta wanigari danyin karatu sai inaganin kamar bazai yuwuba tawani gefen kuma idan naduba irin halaccinda hajiyarna tamana sai inji bazan iyahanata wani abu datanima agurinaba,yanzuke menene shawarinki akan wanna zance?mama tasauke numfashi agaski tarbiyan yamace sai iyaye ,dukda cewa natabbata tarbiyarda mukabaiwa RUMAINA koda ace ayanzu mun ajeta natabbata zaicigaba dagudana harkarshen rayuwarta,damin kuwa RUMAINA yace dakowata uwa take burin samun irinta shiyasa akoda yaushe nake godewa ubagiji" daya azirtamu da ita"yanzu idan tatafi wazamu rikagani madadinta tunda bawani dan mukedashiba,amma nibazance komaiba duk abinda kayanke shine daidai... .baba yy shiru nadan wani lokaci sanna yace, inaso mamana tayi karatu kodun tataimakawa al'umma,ni inaga sutafin da'ita, dan irin shaidar kirki da nasamu akan hajiyarna dakuma wanda nikaina nashaida,zatarike yarna da gaskiya da amana har lokacinda zatagama karatun tadawo..to allah yatabbatar mana da abindayafi alkhairi cewar mama...sunacikin haka sukasinkayo sallamar hajiya .mama tafito tareda amsamata sallamar sannu dazuwa hajiya,yauwa sannummu tunkan mama tabata gurinzama taje dakanta tadau kujera yartsuguno mama nafadin a'a kibari nakawomiki.tayi murmushi bakomai" tazauna,sukashiga gaisawa"baba yafito shima sukagaisa, shuru yadan gudana"can hajiya tace inafadai angama bincike akaina dansaboda yaunakeson komawa gida"saboda wasu ayyuka dakegabana,allah dai yasa za'abani yata mutafi"baba yace bbdmuwa allah yasaremuku hanya,sansar jindadi yabaiyana afuskar hajiya,ngd ngd matuka in allah yyrda zan rike RUMAINA irin rikonda uwa takewa yanta nayimuku alkawari"baba yace ai mune dagodiya"
Mama takwalamin kira na amsa tareda fitowa.hajiya naganina tasakarmin murmushi nima namaida mata na isa inda take zaune nadurkusa.inakwana hajiya.fuska tadaure ni kkcewa hajiya tobazan amsaba har idankuwa kinaso in amsa tosai kinkirani irin kirarda basma da khadeejat sukemin"nasunkuyarda kaina kasa inawasa da yasun hannuna,ahankali nace to mezance miki?
Mommy hakasukecemin kemakuma hakanakeso kkrani kinjiko?tayi tabbayar tana kallon fuskata,kai nagyada mata,oya bakai zaki gyadaba fada naji,ahankali nace mommy.yauwa kokefa kekanki zakiji hakan yafiyemiki..
Ido su mama sukabimu dashi cikeda burgesu,hajiya ko ince mommy tace tashi maza kishirya karmuyi tafiyar dare.baba yace ai kam tafiyar dare sai idan yazama dole amma babu dadi...namike nashiga daki nafara hada kayana....



Kodanagama zama nayi acikin dakin,jinayi duk jikina yymin wani iri nakasa fassara yanayin danakeciki,tun adaren jiya naketamurna zantafi karatu awani gari harkuwa wayewar garinyau saikuma gashi yanzu datafiyar tazo sainaji kamar karnafi.jin nabata shiru adaki yasa mama shigowa,waike haryanzu bakishiryan bane kinsanfa jirarki ake kinzauna kinata batamata lokaci..nagama mama nadago kaina nakalli mama sainaji hawaye yacika idona nayi kokarin maidasu amma hakan baisami yuwuwaba saida sukazibo,ahan kali mama ta isa tazauna dafdani tariko hannuna.
RUMAINA bakison tafiyarne?nagirgiza kai hawaye nacigaba dabin fuskata,mama tacigaba to meyasa kk kuka?mama banaso nayi nesa dakune, to inbanda abinki kefa macece karki manta watarana gidan miji za akaiki"wanna kuma tafiyace nadan wani lokaci dazaran kin kamla karatunki zakidawo,ita kanta mama tafadane kawai amma itama abinda keraina shine anata...
RUMAINA abinda zan jaddada miki shine kirike mutuncinki,kirike martabarki,kirike kimarki kikumarike darajarki,kada kisake ruden duniya tacanzaki.kirike mutuncinki RUMAINA idan kk sake kksakeshi abanza batahanyar aureba to ina tabbayarmiki zakiyi kuka da idonki kukanda bazai taba karemikiba,dan duk watamace batada burin dawuce tarike mutuncinta takaisa hargidan aurenta,RUMAINA banayimiki mummunar fata dannasa kedin yatagarice..mama tamike tariko hannuna inayimiki fatan alkhairi,ngd mama,tayi mirmushi tareda sheremin hawayena tadau jakar kayana mukafita...mommy tamike saye tanafadin to mubarku lfy su baba sukayitama addu'a harbakin mota shima baba baibarni saida yymin natsiha mairasa jiki kafin muka shiga mota direba yaja muka tafi...haka mommy tarika jana dahira tun ina daure jikina harna danfara sakewa...




WELCOME TO BAUCHI STATE馃憥馃徎

Tunshikowarmu garin nakebin ko ina dakallo tabbas bauchin yakubu danaji akefada lallai garin yahadu bakarya..saida mukayi tafiya maisawo kafin muka sauka daga titinda kuke kai muka kuma haurawani,tundaga barkon titin nafahimci wanna unguwar namusanmance tsarin gineginensu shikansa kadai abin kallone,araina nace wanna unguwar itace G.R.A inda akefadar dama ashe akwai irin wadanna gineginen a Nigeria nadauka akasashen waje kadai ake samu..................





Kuyi manaje dawanna bayawa 馃憣yau ina busy ne




Comments and Share



MAMAYN TWINS CE
12/30/19, 14:53 - 拼ar Gatan 茦ainuwa: 馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲
ALFARMA
馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

BISMILLAHIRRAHMANURRAHIM

by鉁嶐煆�
Rasheeda S' Director



Page 9



"""""Munyi tafiya maidannisa,kafin akashari wata kwana, tunfarkon wanna kwanar ginice mai matukar sawo wacce samanta akabitada wasu nannadaddun karafuna masukamada kifiya.munyi tafiyarda yakai 20mins kafin muka isa get in wanna katafarin gidan"wacce ha茩an yakenunida rabin genin kena.karashinsa kuma kokarshensa bana iya hanguwa daga inda nakezaune acikin motar,
Horn direbar yy saiga get din tabude dakanta motar tashige ciki.sabar mamaki bansan sanda nabude baki ba,
Kafinna ankara saiganin munkuma isa dafda wani get din. Still shima dakansa yabude.
Nidai ido nabude inaganin ikon allah kowani get kuwa sojoji sassaye rikeda bindiga kamar masu jirar kiris,dasauri nasunkuyarda kaina kasa gabana nafaduwa.korahama babu aidon wadanna sojojin" saida mukawuce get hudu,tafiya mukayi wanda akalla zai iya kaiwa 18min sakanin get nahudu izuwa get inda yanzu muke saye wato na biyar kena dukdakuwa gudunda direbar yake kamar wadda ba'a cikin gida mukeba"ahankali wanna get din yashiga budewa haryakai karshe.ya ilahi menake gani haka, nan motar takusa hancinta ciki. nantake wani irin sauti yakarade gidan tareda wasu irin koyayen kuta dasuke bada kalolin haske masu ban mamaki cikeda al'ajabi, direct ya isa yafaka motar acikin jerin motoce dasukakai guda 12,alhmdllh allah yakawomu cewar mommy tadubeni sannuko yau kinsha zamafa murmushi nayi inawasa da yan yasuna.direban yazago dasauri yabude mata nan tacedani sauko muje,yazago tahefenda nake yabudemin nafito.ina daidaita sayuwata ai bansan sanda na lumshe ido tareda shakar wani irin sanyayyen kamshiba,nabude idona cikin wanna gida maikamada gari guda, sai alokacin sautin kararna yadauke"hayaniyar danaji yasani joyowa"wasu matane sukanufo inda muke sunafadin sannu mommy dahanya nan sukarika gaidata tana amsawa cikin sakinfuska"
Wata yar budurwar yarinya batadai kainiba amma takusani tamaso tarike hannun mommy"taturo bakigaba welcome mommy"mommy tayanyota jikinta yauwa autar mommy ykk lfyrki kalauko?mommy tayi tanbayar tana kallon fuskarta,baki takuma turowa gaba mommy nidai' I feel sick and tired "tayimaganar cikeda shagwaba" mommy tayi saurin cewa meyasameki muje ciki kifadamin,
Yarinyar tana dagowa muka hada ido tasaki hannu mommy tanafadin laa mommy wanna wacece tatako indanake mommy ai na kksamo wanna maikyau inna"mommy tayi murmushi antynkice RUMAINA sunanta,sai alokacin hankalin mutanin gurin yadawo kaina, wata daga cikinsu tace masha allah sunanta kalarta maikyau,yarinyar tamikomin hannu sunana basma amma friend's ina sunakirana bisy so kema zaki iya cemin hakan tariko hannuna tana girgizawa,dariya tabani bansan sanda nadaraba, beautiful tafada tareda dago hannuta sama kanfuskata tasa yasarta cikin kumatuna daidai kan dimple ina ,daga yau dake zamu rika kwana tunda kinada irin wanna abun konima zai fito afuskata,dariya akayi duka.mommy tace kibarta mushiga tahuta tagaji,basma narike da hannuna muka bibayan mommy harmuka isa bakin wani kofa na glass mommy nadaidaita sayuwanta dafda kofar,sai glass in ta bude tashiga muma mukashiga nidai cikin soro nake sanya kafata dan kuwa lamarin gidan yafara bani soro wata hanyace mikakkiya agun haka mukarika tafiya saiwaige waige nake wasu Flaw's ne namusamman agun abin mamaki suma acikin glass suke gawani irin kamshi namusamman dake tashi ko ba afadaba nasan kamshin daga jikin wadanna Flaw's inna kefita"tundaga inda muke nake hangen wani kofa na glass irin wanda muka wuce amma wanna yafi kayatuwa sosai.nan shima mommy nasayuwa dakansa yabude,mukashiga"
Ya'ilahi ya'subhanallah"falo ce rambasheshiya nakarshe,humm zan iya kirar wanna falon da aljannar duniya" set in'kujeru biyarne dauke acikin falon" kayan alatu iridakala gasunan irin kayan kasashen wajenna ba abunda babu "sayuwa lissafowama batalokacine fans kuhango saruwan wanna falo dakyau a'idonku saikunfi fahimtar yadda nake nufi"
Dana shiga falonna saigani nayi kamar ina kasar turai" mommy tanimi guri adaya dagacikin kujerun tazauna"basma tadubeni zauna bari nazo tashige tawata kofa.nan wasu yammata sukafito sukayiwa mommy sannu dahanya suka koma"
Mommy rakira daya dagacikin wadanna yammatar,Rukayya zoki tafida RUMAINA dakindake kusa danaki dan zatafi sakewa acan tanajin hayaniyarku,to rukayya tace,mommy tadubeni kije kihuta nima barina'isa"rukayya tace taso muje nace to,namike saye nabi bayanta.muka shiga wani kofa dake gabar da falon saida muka dantafi kadan sanna mukayi kwana saiga dakuna guda uku biyu ajere dayakuma natadancan gefe tanunamin daya dayake gefe dakuma wanda suke jeri acikinsu wanne kkso,danjim nayi saikuma na nunamata wanda yake gefen"tace to zomuje kici abinci muka shiga daya daga cikin daki biyunna,dasallama nashiga yammata raihudu acikin dakin amma acikinsu dayace ta amsamin sallama rukayya tacemin zauna ana tanunamin bakin gado na zauna" sannuku nace dasu ko kallona bawacce tayi bari nasami damar amsawa wacce ta amsamin sallama cema tadan juyo tace yauwa ykk,sukaci gaba da cin abinci dakuma hirar dasuke"
Rukayya tazubo abinci tamikamin na aje gefena itama takoma gefe tazauna tana lasa waya... aunty RUMAINA aunty RUMAINA daga waje nakejin kirar basma takaraso cikin dakin"kai aunty RUMAINA kinaji ina takwadamiki kira kedanace kijirani yanxu zandawo"tazauna kusa dani"toko abincinma bakiciba, taso muje kici.tadau plt in,yauwa kuje gadakinta can saikuje taci acan in cewar rukayya" mukafita basma saizubamin surutu take tanawni karairaya niko abinnata dariya yake bani,koda mukashiga dakin tadire plt in saman table in gaban gadon.masha allah dakin yasaru"tazauna bakin gadon nimahaka,takafeni da ido "kici abincin kirikayi kina murmushi ko dariya dan narika ganin dimple inna,haka tarika jana dahira harna saki jikina nantake naji yarinyar tashigamin rai"yanayinta yanayin mommy ce basa nuna isa dan sunada dukiya"
Tajima sosai adakin kafin tafita.namike nashiga bathroom inda kecikin dakin,saida nayi sayuwan yan mintuna nakare wa bayin kallo.tunani nafarayi ta inda zan fara amfani da kayakin ciki"nan nafara lalume cikin duhu.ahaka harnafahimci wani abun,sanna nayi alaula nafito inafitowa naji anabuga kofa.na isa nabude sainaga direban dayakawomu daukeda jakar kayana yamikamin nakarba tareda yimasa godiya,namaida kofar narife naje na aje jakar.sanna nagabatar da sallolindake kaina"ina idarwa namike nahaura kan wanna makeken gadon "nadan rakube gefe nakwanta nan kuwa bacci yadaukeni
"bani nafarkaba saidaf magrib"saida naje nayi wanka tareda dauro alaula nazo nayi salla"tilawar al'qur'an "na yi da hadda"harsaida naji kiran salla kafin namike" lokacin basma tashigo dataga ina sallah saita zauna harsaida na idar,sanna tacedani aunty RUMAINA waikizo inji mommy,to nace namike mukafita,mukashiga cikin falon da dazu mukazauna nadauka anan zamu tadda mommy sainaga tawuce "muka kuma shiga wani babban falon sararre nakarshe "nan mukatadda mommy zaune nakarasa inna takenayi nazauna kasa kusada kafarta.taso kizauna anan bakyau mace tarika zama'akasa"namike nazauna inda tanunamin,
Akayi sallama matar tashigo dauke da madaidaicin basket tadire bisakan table inda kegabanmu..............




Comments and Share



MAMYN TWINS CE
12/30/19, 14:53 - 拼ar Gatan 茦ainuwa: 馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲
ALFARMA
馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

BISMIL LAHIR RAHMANUR RAHIM

by鉁嶐煆�
Rasheeda S' Director



Page 10




"""""matar tadan risina 'barkada dare hajiya, mommy tace yauwa goggo larai.hajiya abincifa yakamla nakaisa dinning ko akawo nanne? Eh akawonan "toh hajiya tayuya tashige saigata daukeda kayakin abinci,koda tazuba mana,ganin yadda nake sakurar abincin yasa mommy cewa kisaki jikinki kici abinci sosai,kisaki jikinki nan gidankune kinjiko?nagyadakai nacigaba da sakurar abincin.
Basma nagamawa tamike,mommy aunty RUMAINA good night nace tun yanzu"wanna ai ba'ahira da'ita cewar mommy" allah barci nakeji kuma kunga gobe Monday ne nidai natafi tashige tana dariya,
Muna zaune mommy nata jana dahira,can wayarta tayi kara,tadauka tareda cewa kina lfydaiko to ya karatun?nan sukaita hira nakuma fahimci da khadeeja sister din basma ce suke wayar, sallamar da akayi yasani juyowa tareda amsa sallamar "takaraso ciki ta aje kwanon hannuta gaban mommy tazauna bisa kujerar danake har saida mommy tagama wayar,tagaidata sanna tace mommy waigashi inji umma"tajanyo kwanon kai umma dai bata gajiya yaukuma kwadon zogalece to madalla kice ngd"taceto tatashi hartaje bakin kofa,mommy takirata,am ummee sayakujeda RUMAINA kiceda umma takaramin kulinna baijiminba,RUMAINA tashi kuje saiki karbo kikawomin kekuma ummee saikisata ahanya tadawo"dukammu muka amsa nida ummeen namike nabi bayanta mukafita"masha allah, idan kadaga ido kklli sararin samaniya shine kawai zaishaida maka darene yanzu, amma ilahirin gidan kamarrana sakamakon wasu kalolin koyayen wuta namusamman dake zagaye adukkanin lungu dasako nagidan" daya daga cikin part dinda sukegefecan muka shiga"
Wata mata yardattijuwa nazaune afalon mukarisa nagaidata,ummee tace ,umma wai'inji mommy kikaramata kulin baijimataba,umma tayi murmushi allah sarki hajiya halinta yana matukar burgeni,dan bata dauki duniyar dafadiba,araina nace hakanekam duk tulin tarin dukiya datake dashi hakan baisata girman kaiba" tadibi kulin tabani zanjuya tace zokici zogalen kema,a'a nakoshi ngd" ummee tasha gabana, ba'ddo' har idan kinaso narakaki kikoma tokuwa saikinci .nayi murmushi allah nakoshine kumani sunana ba 'bad'do' bace RUMAINA sunana,tayi dariya to ai dukadayace duk wacce nakiraki dashi duka sunankine, 'bad'do' kizauna kici saina rakaki.haka ummee da ummanta suka sa saidanaci"nayiwa umma saida safe mukafito.harbakin kofafar falo tarakani kafin tajuya,nikuma nashiga nakaiwa mommy aikenta nayimata saida safe nakoma daki..


BAYAN SATI BIYU...
zuwa yanzu nafara sabawa dagidan musamman ummee damuka shakuwa da'ita sosai acikin yan kwanakinna,tanazuwa dakina nima inazuwa part insu muyi hira,lokacin kuwa har mommy tagamamin komai nagame da makarantana sati maizuwa zanfara zuwa makarantar da su ummee suke"""

2month later

AHA FAN'S馃憥馃徎


8:pm
Dasauri namike nasauko daga saman bed,nanufi hanyarfita nabude labulen falo nasako kai zanfita "saijinayi nayi karo da abu saikuma naji faduwar abu akasa tim,nayi hanzarin kallon kasan ai bansan sanda naware ido ba,nayi kasa dasauri nashiga tarkasa kudaden dasuka fice daga cikin jakardaya fadi.nayi saurin cusasu cikin jakar..nayunkuro zanmike.wata sanyayyeyar murya yadoki kunnena,
Ke bakyaganine koke makauniyace? dazaki rikatafiya baki kallon gabanki kiduba kiga yadda kk bigeni kamar bakigani ko bakida hankali...,ahankali nadago daga sugunen danake"namika masa jakar yamiko hannu yakarba.batareda nasake masaba nace,idan harni makauniyace bana gani to yatabbata kaima haka kk dankuwa kaiyadace kasan dafitowata baniba" in kuwa hakane tokuwa kaine makahon..inakaiwa na nasakemasa jakar nashige nabarsa nan saye,tundaga can nahango ummee ganin tana tahowa yasani sayuwa,hartakaraso.
Yabaki karasaba kk saya anan,ganin kinazuwane yasani sayuwar ai.ummee tace tozo muje .nace a'a nidagananma zankoma dangabadaya yagama batamin rai"sakare ummee tayi tana kallona cikin mamaki tace kedawa kuma,dahar yabata mikirai?saida nayatsina fuska tareda kallon hanyar danafito,hmm inbanda sabar yarainamin hankai wainiyacewa bani gani kuma banida hankal"shidayake zuwa baiganniba sainida nake fitowa shine zan gansa"allah mutuminnako hmm" ummee tace idan nafahimceki karo kukayi dashi mutumin towaye shidin? Oho ba nima bansanshiba yananandai wani baki mummuna dashi yazo zaishiga falo nikuma zanfita shine mukayi karo"dariya馃槀ummee tayi kai RUMAINA aina kikaga baki mummunar kuma kkce zaishiga falo"todai gidanna babu baki mummuna"nima dariyar nayi"dannasan fada kawai nayi bakine amma ba mummunaba dukda dai bakallon saf namasaba"
allah ummee yabatamin rai..todai hakuri zakiyi tundadai ke ba iya batamasa ran zakiyiba,bakiji ance fadarda yafi karfinka saikamaidashi wasaba"nadago daniyar yin magana aiko nahangoshi yafito yana kokarin binwani hanyar,yauwa ummee kingansa shine"la'ilah yanzu shine kkcewa mummuna,tintsirewa dadariya takumayi,kai amma kinci abinci akan Anas"aikuw anas baxama akirasa da bakiba saidai chocolet
ammadai kinmasa kallon soro "sunansa anas"manager gidajen manfetur in mommy ne nagarinna acikin gidanna yakeda zama,bakidai taba ganinsabane'nakawar dakai gefe"to saime allah yasa madarace shi ba chocolet ba saime"ni wuce muje nagaida umma yau tunsafe bamu gaisaba"gashi yau banje nadau jinjirar aunty aisha ba..banbar part insu ummee ba sai 10.............



馃憣馃憦馃ぇ


Comments and Share




MAMYN TWINS CE
12/30/19, 14:53 - 拼ar Gatan 茦ainuwa: 馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲
ALFARMA
馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

BISMIL LAHIR RAHMANUR RAHIM

by鉁嶐煆�
Rasheeda S' Director




馃吙11馃憠馃徎12






Ummee tarakoni munatafe muna hira"daga cikin parking space nahangosa yana kulle marfin mota,yafito zaiwuce lokacin muma muka iso gurin,ummee tace barka da dare' Anas"yace yauwa ummee ykk?tace lfy lau nake"haushi yagama cikani,nayi gaba abina saikuma nasaya dan inajin soron shiga lungun dazai sadani da part in.cikin hasala nace ummee ni kinshanyani kinsaya kinawani surutu.inbazaki rakaniba intafi abina.cikeda tsiwa nayi maganar"cikin muryarsa mai sanyinna yace
To kitafin mana wayarikeki ana"naja karamar tsaki nashige,inaji yanacewa ummee wuce kikoma abinki" ahankali nake tafiyar dansoro yagama rufeni dukda haskenda ke mamaye dagidan hakan baihanini jin tsoroba,musamman idanna waiga naga duk girman gidan bakowa saini"gashi sakanin part insu ummee danamu akwairata"dasanda nashiga lungun aiko inasa kainaciki mukayi ido hududa dawani jibgegen kare saikumri dahura hanci yake"wani irin juyi nayi aguje,aiko karen naganin najuya shima yabiyoni aguje yana haushi,gudu nake da'i ya karfina nima ina ihu...dasauri yafito danjin ihuna dakuma haushin kare,tunkan yakaraso yadakawa karen tsawa,cak kuwa yasaya"
Dagudu nazonashige bayansa nasaya inahaki"yakumayiwa karen magana saitajuya tatafi"shima yajuya yarabe tagefena yashige"ai da sauri nasha gabansa"dan allah kazo karakani nayi maganar hawaye nasauka daga idona,dan natsorata matuka,yakawarda kai gefe tareda fadin wazai rakakin?muryata narawa nace kai dan allah,allah tsoro nakeji.kataimakamin"
Shuru yy saikuma yakalleni dasauri yakawar dakansa akaina"sai yy gaba"niko nayi saurin binbayansa" kafin ya isa kofar falon yaja yasaya,sakanin kofar da inda yasayan bawanin rata maiyawa,ganin yasaya sainima nasa"zoki shige yacedani"kallonsa nayi amarairaice nace dan allah kakarasa dani"daganan ba inda zankuma masawa zokishige,yanunamin hanya,inkuma bahakaba natafi inyaso karan yacinyeki.kut yacinyeni lallaima wanna bayada imani'nafada araina.ganin dagaske yake,yasani wucewa ahankali inatafiyar ina waigensa.yananan saye"inazuwa bakin kofar nashiga dagudu... Yakai 5mins saye agun daga bisani yajuya.koda nashiga daki haka nadunkule guri guda akan gado.ahaka har barci yadaukeni"
Washegari bayan nayi sallah nakuma komawa barci"karfe bakwai daidai,nafarka naje nayiwanka,kodana fito nashafa mai doguwarriga nasaka,nafito direct falan mommy nanufa danna gaidata,inashiga falon nagansa zaune saman kujera.wucesa nayi na isa bakin kofar mommy,nakai hannuna kan handle naji yanacewa.kicewa mommy inajiranta karlokaci yakure'sarai nasan dani yake"nayi shigewata dakin mommy"bayan nagaishita nafito'nakumazuwa zan shigesa.yace ke nacemiki kicewa mommy zanmakara shine bakifadaba dannasan inda kinfada data fito"nakalli gefendayake nace tokaje kafadamata mana"wanna mutumin baisan dahaushinsa nakwanabako,hardacewa wai inyaso karen yacinyeni"tuno hakan danayi,saina sinci kaina damurguda masa baki.nashige"bayana yabi dakallo tareda girgiza kai alamar zamu gamu"daki nashige nayi kwanciyata,banjima dakwanciyarba,ummee tashigo inajin shigowarta najuya bayana tareda rufe idona,tahayo gadon tanafadin' ba'd'do meye zakiwani yuyamin baya,takai hannu tajuyoni"nature hannuta inafadin'to tunda so kuke namutu keda wanna mutumin to meye nazuwa gurina.ido taware mutuwa kuma haba RUMAINA mekuma yakawo wanna zancen,namike daga kwanciyar danake nadubeta nace"jiya yahanaki rakani sanna kuma yace inyaso kare yacinyeni to inbaso kuke namutuba aida jiyan kinrakani"shikuma dabaice kare yacinyeniba"
Dariya ummee tayi tace kai RUMAINA kedai akwaiki da rikici tome wani abun damuwa'ana. kuma jima abundayasa nakoman 'dansaboda naga munkusa isa part innanne shiyasa"watodai jiya kare yamiki rakiya kena"takuma fashiwa da dariya" nadau pillow nawurgeta dashi,nace allah mutuminna yabani haushi shine yau hardawani aikena waina yimasa magana da mommy niko naki"kai ba'd'do banfa sanki dawana halinba,hakashima Anas' in narasa gane wanna yartsamar dake sakaninku,nidai da dukanku nasanku babu ruwanku da hayaniya,amma saigashi kudin kuma kukeyi asakaninku,nayatsina fuska nace.ai shi'ne yafara nimata nikuma haka kawai naji bazan iya hakuriban ramaba"
Tace'dai kitashi kishirya kada mumakara,nace to namike nabode wardrobe naciro uniform ina nasaka,sanna muka fito a falo muka hadu da basma itama tashirya"mukayiwa mommy sallama muka nufi parking space direba yadibemu sai school...sai 6 muka baro school.direba yamaidomu gida"inashiga bedroom natube uniform nashiga bathroom nayi wanka"kodanafito rigada wando na material nasaka rigar tawuce goiwata.na saka dankwalin akaina batareda

Please Login or Register in order to submit comment