Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kawo izuwa sa'adda ya ga gawar Jairul ya fusata
ainun ya sami gagarumin karfin da ya doki fuskar Zaidur
da kafarsa harma ya kaishi kas ya karya masa wuya.
Lokacin da Husnaila taji wannan labari sai ta cika da
tsananin murna ta dubi Muraisu ta ce, "Ya kai dana hakika
kayi gadon mahaifinka wajen dakewar zuciya da kuma
Jarumtaka ta bazáto, gami da sa'a, domin ba zan taba
mancewa da ifin gagarumnar jarumtakar da ya yi ba sa'add a
na ce yaje ya z0 mini da kan rikakken Zaki a matsavin
sadakin aurena.
Ina tabbatar maka da cewa Zakin da ya kashe ya
ninka Zaki Jindal girma da karfi sau uku.
Hakika mahaifinka ya cika jarumin įarumai, kuma ga
dukkan alamu kaima ka gado irin jarumtakarsa.
Lallai ina son sadakin da za ka kawowa matar da za
ka aura yafi wanda mahaifinka ya kawo mini wuya".
Koda jin wannan batu sai Muraisu ya yi murmushi ya
ce, "Ina fatan na iya abinda kike son nayi kada na baki
kunya.
Amma dai ki sani cewa kamna da wane bata wane,
lallai akwai dumbun bambancin jarumtaka da dakewar
zuciya tsakanina da mahaifina kamar yadda ya kasance
tsakaninsa da nasa mahaifin.
Kafin Muraisu ya kara fadin komai sai Husnaila ta
kama ka fadunsa ta tashesbi tsave ta ce, "Je ka ka dauki
kahon BUSA A MUTU ka je ka cika aikinka"
Cikin sanyin jiki da karayar zuciya kamar zai lashe da
kuka yaje ya dauki kahon ya saba a bayansa sannan ya ice
daga cikin gidan ya durfafi tsakiyar dajin Kirzula.
Lokacin da ya iso tsakiyar dajin sai ya sa kahon a
bakinsa ya dagashi sama da nufin ya busa, amnma sai ya
kasa.
Nan take idanunsa suka ciko da kwalla hawaye ya
fara kwarara
Ba komai ne ya janyo faruwar hakan ba face tsananin
tausayi domin Muraisu ya tabbatar da cewa da Zarar ya
busa kabon sai ya zamo sanadin raba babban da da mahaifi
ko dan uwa da dan uwa.
Duk sa'adda Muraisu ya tuna cewa shima fa ya taso a
matsayin maraya wanda bai taba ganin ubansa ba sai ya ga
cewa to wai shin saboda me zai mayar da wani marayan?
Lokacin da Muraisu ke kan zubar da bawaye sai
kuma ya tuno da irin cin amanar da dan uwan mahaifinsa
Huraisu ya yi ya hada kai da Sarki Imsar ya kashe dan
uwansa Muraisu, nan 1ake zuciyar Muraisu ta kama
tafarfasa kamar za ta kone yaji babu abinda yake so sama
da ya dauki fansa kuma ya karbi karagar mulki a hannun
Sarki Huraisu.AA misau ke magana
Nan take Muraisu va busa kahon busa a mutu. Sautin
kahon ya cika nabiyar gaba daya ya haifar da gagarumin
tashin hankali, mutane suka kama guje-guje da iface-iface.
Wannao shi ne sbinda ya faru a dajin Kirzufa bayan
jarumi Muraisu ya fafata yaki a karon farko a rayuwarsa,
kuna shi ne karon farko da ya fara ganin dan uwansa
bil Adana in ban da mahaifiyarsa da ya zauna tare da ita a
cikin dajin Kizufa isawon shekara da shekaru.
A CAN BIRNIN Lairuf kuwa, gimbiya Sulaiza ta
taso da matukar kyawu gami da tsananin jarumtaka irin ta
mahaifinta, har ma ake kyautata zaton tafi mabaifin na ta
sadaukantaka saboda wadansu abubuwan al ajabi da tayi
guda biyu.
Abu na farko da tayi shi ne, akwai wani tsafaffen
kogon isai wanda ya gagara shiga tun a zamanin Sarki
Salmar saboda akwai wata tsobuwar Macijiya a ciki mai
tsananin girma da tsawo wacce a lokaci guda tana iya
hadiye mutum goma.
Babu komai a cikin kogon tsafin face wadansu
kayayyaki na dukiya masu yawan gaske wadanda aka yi su
da zallan zinare da lu'u-lu'u.
Asalin wannan dukiya ta wani takadarin bakon boka
ne da ya sauka a brinin Lairuf wanda ya yaso ya yiwa Sarki
Salmar juyin mulki. Da kyar da sidin goshi Sarki Salmar da
boka Rufyan suka taru suka hada karfi da karfe sannan
suka kashe bokan bayan sun kwana bakwai suna fafata
kazamin yaki da shi.
Bayan an kashe bokan ne kogon ya zauna ya gagara
shiga saboda ya bar wannan Macijiya a ciki. Sau bakwai
Sarki Salmar yana tura Dakaru cikin kogon domin su kashe
wannan Macijiya su debo dukiyar da ke ciki, amma sai abu
ya gagara.
Har sai da Sarki Salmar ya taka kafarsa ya shiga cikin
kogon ya yi yaki da Majiyar amma ya kasa hallakata kuma
tayi masa rauni har guda uku da kyar ma ya samu ya tsira
da rayuwarsa ya fito daga cikin kogon.
Lokacin da Sarki Muraisu na shima ya jarraba kashe
Macijiyar sau biyu ya kasa. Shi kuwa Sarki Huraisu bai ma
taba jarraba shiga kogon ba domin zuciyarsa ta karaya ya
tabbatar da cewa ba zai iya da wannan Majiya ba.
A gaba daya birnin Lairuf babu wajen da mutane
suke tsoro sama da wannan kogo inda wannan Macijiya take.
Kai sai da ma ta kai cewa mutane sun daina bin hanyar da
kogon yake gaba daya.
Tun gimbiya Sulaiza tana yarinya karama take jin
labarin kogon Macijiyar kuma ta aiyana a ranta cewa duk
sa'adda ta grima sai ta magancewa mutane wannan bala'i da
ya addabesu a birnin Lairuf.
Ko kadan zuciyarta bata taba karaya ba ko kuma taji
wani tsoro bisa al'amarin.
Kullum Sarki Huraisu ne ke koyawa gimbiya Sulaiza
yadda ake yaki, amma bayan sun rabu sai kuma ta ci gaba
da baiwa kanta horo tana koyar wadansu abubuwan
sababbi wadanda ma bata taba ganin mahaifinta ya yí ba.
Baya ga haka, Sulaiza ta kan batar da kamanninta ta
fita bayan gari tayi ta gudu tana motsa jinin jikinta. Sai ta
zagaye birnin gaba daya kamar sau hudu a rana.
Bugu da kari, kullum tana koyon fadan hannu da
kokawa bar ya zamana cewa ta kware ainun har ma sai tasa
a tara ma ta karti kimanin mutum arba'in ita kadai tayi fada
da su, sai dai ka ga duk ta bazar da su a kasa daga wanda ta
fasawa baki sai wanda ta fasawa hanci.
Babbar baiwar da Allah Ya yiwa gimbiya Sulaiza shi
ne, tana da tsananin zafin nama da matukar juriyar wahala
fiye da kima.
Sannan tana da matukar naci gami da sa'a bisa duk
abinda ta sa a gabanta.
Duk wannan matsayi da gimbiya Sulaiza ta samnu ta
sameshi ne a lokacin da ta cika shekara goma sha hudu.
A ranar da gimbiya Sulaiza tayi niyar zuwa kogon
Macijiya bata sanar da kowa cewar za ta cje ba hatta kuwa
mahaifiyarta Sabirat.
Kuma sai da yamma likis sannan tayi bad da kama ta
rataya takobinta a bayanta ta hau doki ta sulale izuwa
bayan gari.
Kai tsaye ta durfafi inda kogon Macijiya yake ba tare
da fargabar komai ba.
Da zuwanta bakin kogon sai taja tunga ta sauko daga
kan dokin ta daureshi a jikin wata bishiya sannan ta karewa
kogon kallo ta ga gaba dayan kofar shiga kogona lullu6e
take da yana kai da gani ka san cewa fiye da shekanu
arba'in ma baya ba a shiga kogon ba.
Nan take gimbiya Sulaiza ta zare takobinta sannan ta
saro ice ta yaye yanar da ke jikin kofar shiga kogon, kuma
ta kunna wutar icen ta shiga cikin kogon lana tafiya a
hankali tana haska hanya tana waige-waige da dube-dube
gami da kasa kunnuwa domin taji daga inda zata fara jiyo
motsin wannan Macijiya.
Bisa mamaki sai gimbiya Sulaiza taji shiru bata ji
motsin komai ba har ta isa tsakiyar kogon inda ta iske
wannan dukiya mai tarin yawa ta lu'u-lu'u da zinare.
Kwatsam! Sai ta daga kanta sama, ai kuwa sai tayi
arba da wannan murtukekiyar Macijiya ta kanannade dutsen
da ya rufe saman kogon tayi gammo kuma ta fasa kai.
Ashe dama tun sa'adda Sulaiza ta shigo cikin kogon
tana saman tana kallonta.
Koda Sulaiza tayi arba da wannan Macijiya sai ta
firgita ainun taji tsoro ya dabaibayeta a karon farko a
rayuwarta, domin ko a wajen masu zana taswira bata taba
ganin an zana Majiya mai girma da tsawon wannan ba.
Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin Macijiyar da
Sulaiza, Majiyar ta fara sauko da kanta kas a hankali itama
Sulaiza sai ta zaro takobinta a hankali ya zamana cewa
kowannensu zuciyarsa cike take dá mugun ufi.
A dai-dai lokacin da Macijiyar ta kawowa Sulaiza
mugun sara ne ita ma ta gama zato takobinta cilkin zafinAA misau ke magana
nama Sulaiza ta daka tsalle ta kaucewa saran Macijiyar,
kuma ta dankara ma ta takobi a ka.
Nan take tartsatsin wuta ya tashi sakamakon hadu
takobin da kan Macijiyar.
Bakin Macijiyar ya sari wani dutse da ke daf da inda
Sulaiza tayi tsalle ta bari.
Nan take dutsen ya ragargaje tamkar da katuwar
guduma aka dokeshi.
Kawai sai Sulaiza ta ga kaifin takobinta ya dakushe.
Al'anarin da ya matu kar dugunzuma hankalinta ke
nan domin ta fahimci cewa sara da suka ba za su yi tasiri ba
a jikin waunan Macijiya.
Nan take zuciyarta ta karaya, kuma tayi nadamar
wannan ganganci da tayi ta kawo kanta cikin wannan
kogon Majiya.
Abu na farko dai ta san cewa ba za ta iya gujewa
Macijiyar ba,domin kafin ta juya tayi taku daya tuni Macijiyar
ta makota da kanta ko jelarta.
Nan fa Sulaiza ta fara tunanin hanyar da za ta bi ta
ceci rayuwarta amma sai ta rasa irin dabarar da ya kamata
tayi.
Tana cikin wannan tunani ne Macijiyar ta kawo mata
fyada da jelarta.
Sulaiza ta sake daka tsalle ta bar inda take, ielar
Macijiyar ta dira akan wani katon dutse, nan take shima
Wannan dutse ya rugurguje.
Nan fa aka kacame da masifaflen artabu tsakanin
Macijiyar da Sulaiza ya Zamana cewa Maicijyar tana kai ma ta
hare-hare da kanta da jelarta, ita kuma ta dinga kauce-
kauce da tsalle-tsalle.
Nan da nan suka birkita kogon gaba daya, ya fara
rushewa.
In ba don gimbiya Sulaiza tana da matukar zafin
nama da jarumiaka ba gami da juriya da cikin kankanin
lokaci Macijiyar za ta ballakata.
Sai da aka shafe sa'a uku cur ana wannan dauki ba
dadi, har ya zamana cewa kogon dutsen gaba daya ya
rugurguje ya baje a kasa.tamkar bai fa6a wanzuwa ba a
wajen saboda dukan da Macijiyar ta rinka yiwa duwatsu da
jelarta da kanta amma ko SAu daya bata sami nasarar taba
jikin gimbiya Sulaiza ba.
Ita kanta Majiyar tavi isananin mamakin ganin irin
jarumtakar gimbiya Sulaiza
gami da juriya da zafin namanta, domin bata taba
haduwa da wani jarumi da ya wahalar da ita ba haka.
Lokacin da gimbiya Sulaiza ta ga kogon duisen gaba
daya ya ruguje ta sami hanyar da za ta iya gudu, sai tayi
tunanin guduwar amma kuma sai vwani tunani ya fado ma ta
a rai cewar wannan Macijiyar za ta iya afkawa cikin gari
ldan kuwa ta shiga cikin gari babu wanda ya isa ya
tareta don baka bata san iya adadin miliyoyin rayukam da
Za a yi asara ba.AA Misau ke magana
Nan take gimbiya Sulaiza taji zuciyarta ta kekashe ga
dukkan isoro ta gwammace ta mutu a kokarin kawar da
wannan Macijiya mairmakon ta barta ta afka cikin gari.
Nan take gimbiya Sulaiza ta daina guje-guje ta fara
kaiwa Macijiyar sara da suka amma kuma sai ta ci gaba da
tsalle-tsalle har ma tana hawa da sauka kan gangar jikin
Macijiyar tana saran kowanne Gangare na jikin Majiyar
domin ta gano inda lagon Macijiyar yake.
Koda Majiyar ta ga Sulaiza ta sauya wannan salon
fada sai itama ta fusata ta fara amfani da dukkan karfinta
domin ganin ta hallakata.
Al'amarin da ya janyo fadan nasu ya kara tsamari
ainun ke nan.
A CAN CIKIN birnin Lairuf kuwa, tun sa'adda aka
fara gumurzu a can kogon Majiya mutanen gari suka san
cewa lallai yau babu lafiya, domin tun daga can din ana iya
jiyo karar Macijiyar da kuma karar rushewar kogon.
Al'amarin da ya dugunzuma hankalin kowa ke nan,
mutane suka firgice aka kama guje-guje da iface-iface,
domin ijama'a sun zata cewa tuni Macijiyar ta fito daga cikin
kogon ta barko cikin gari.
A wannan lokaci Sarki Huraisu na zaune a fada ana
tafivar da harkokin mulki. Koda ya jiyo rurin Majiva da
karar fashewar kogon da take sai ya mike zumbur ya bada
umarnin a shirya Dakarun yaki masu yawa.
Cikin gidan sarautar ya
Nan take shima ya ruga izuwa
isa turakarsa ya yi damarar yaki ya fara debo makamansa.
Yana cikin wannan shiri ne Sabirat ta shigo cikin
turakar cikin dimauta tana zubar da hawaye.
Ta dubeshi ta ce, "Ya kai mijina kayi sani cewa yau
fa tun safe ba a ga gimbiya Sulaiza ba anya kuwa ba ita
bace taje kogon sihiri ta tsokano wannan Macijiya ba?"
Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Huraisu ya
kara dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, ya ce, "Tabbas
biri ya yi kama da mutum.
Ki tuna cewa fiye da shekaru arba'in baya da suka
shude ba a sake jin duriyar wannan Macijiya ba a wannan
birni.
Kakana da dan uwana ma Muraisu sun fafata da ita
basu sami nasarar komai ba. Lallai kuwa nima yau sai na
fuskanci wannan tsinanniyar Macijiya.
Idan har ta kashe mini 'yata ba zan saurara ma ta ba
sai dai nima ta kasheni!"
Koda gama fadin haka sai Sarki ya gama kimtsawa
cikin gaggawa ya fita kofar filin fada ya hau dokinsa ya
jagoranci Dakarun yaki, mutum dubu dari biyu suka fice
daga cikin birnin suka durfafi inda kogon Macijiya yake.
Tafiyar rabin sa'a suka yi suka iso kogon.
Da isowarsu suka ga abin al'ajabi irin wanda basu
taba gani ba, domin sun iske gimbiya Sulaiza tana ta yin
mugun artabu da Macijiyar.
A wannan lokaci Sulaiza ta sami raunika har guda
uku a jikinta. Gashi dai jini na zuba a jikinta amma bata
sare ba tana dada ci gaba da yakar Majiyar.
Koda Sarki Huraisu ya ga halin da 'yarsa ke ciki sai
ya fusata ainun ya zare takobinsa ya duro -daga kan dokinsa
ya falfala da gudu izuwa kan Macijiyar da nufin ya kaiwa
Sulaiza dauki.
Su kuwa sauran Dakarun yaki, lokacin da suka yi
arba da wannan Macijiya suka ga tsananin girmanta da
tsawonta kuma suka ga yadda take rugurguje duk dutsen da
ta maka da jelarta ko kanta sai suka firgice ainun suka
dimauce.
Wasu ma basu san sa'adda suka fara sakin fitsari ba a
wando. Masu karfin hali ne suka iya fara ja da baya
wadanda kuwa suka razana ainun sai dai ka ga sun sume
daga tsaye.
Lokacin da Sarki Huraisu ya kaiwa Sulaiza dauki
suka ci gaba da yakar Macijiyar su biyu sai artabun ya kara
tsamari fiye da farko, domin Macijiyar ta kara fusata.
Cikin shammace kuwa Macijiyar ta make Sarki Huraisu
da jelarta. Nan take yai tsalle sama kamar an cillashi daga
cikin baka ya maku a jikin wata bishiya ya fado kasa cikin
mugun hali mai kama da suma, har jini na bul6ulowa ta
cikin hancinsa da bakinsa.
A jikinsa kuwa inda Macijiyar ta doka da jelarta tamkar
adda aka sa aka yi masa wawan sara guda biyu, domin
wajen ya dare, jini na zuba.

TopA Nima Ganin Wannan Jini dake zuba yasa zan dakata anan saikuma wani lokaci
Admin
AA Misau ke magana
Domin shiga group dinmu na whtsap danna blue din rubutun nan

Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30QBUSA A MUTU!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part C.

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke magana

NAN TAKE GIMBIYA SULAIZA TAJI ZUCIYARTA TA KEKASHE GA
DUKKAN TSORO TA gwammce ta mutu a ko karin kawar da
Wannan Macijiiya maimakon ta barta ta afka cikin gari.
Nan take gimbiya Sulaiza ta daina guje-guje ta fara
kaiwa Macijiyar sara da suka amma kuma sai ta ci gaba da
tsalle-tsalle har ma tana hawa da sauka kan gangar jikin
Macijiyar tana saran kowanne 6angare na jikin Macijiyar
domin ta gano inda lagon Macijiyar yake.
Koda Majiyar ta ga Sulaiza ta sauya wannan sa lon
fada sai itama ta fusata ta fara amfani da dukkan karfinta
domin ganin ta hallakata.
Al'amarin da ya janyo fadan nasu ya kara tsamari kenann
A CAN CIKIN birnin Lairuf kuwa, tun sa'adda aka
fara gumurzu a can kogon Macijiya mutanen gari suka san
cewa lallai yau babu lafiya, domin tun daga can din ana iya
jiyo karar Macijiyar da kuma karar rushewar kogon.
Al'amarin da ya dugunzuma bankalin kowa ke nan,
mutane suka firgice aka kama guje-guje da iface-iface,
domin jama'a sun zata cewa tuni Majiyar ta fito daga cikin
kogon ta barko cikin gari.
A wannan lokaci Sarki Huraisu na zaune a fada ana
tafiyar da harkokin mulki. Koda ya jiyo rurin Majiya da
karar fashewar kogon da take sai ya mike zumbur ya bada
Umarnin a shirya Dakarun yaki masu yawa.
Nan take shima ya ruga izuwa cikin gidan sarautar yana
isa turakarsa ya yi damarar yaki ya fara debo makamans
Yana cikin wannan shiri ne Sabirat ta shigo ci
furakar cikin dimauta tana zubar da hawaye.
Ta dubeshi ta ce, "Ya kai mijina kayı sani cewa
fa tun safe ba a ga gimbiya Sulaiza ba anya kuwa ba ita
bace taje kogon sibiri ta tsokano wannan Macijiya ba?"
Koda jin wannan batu sai hankalin Sarki Huraisu
kara dugunzuma ainun fiye da ko yaushe, ya ce, "Tabba
biri ya yi kama da mutum.
Ki tuna cewa fiye da shekaru arba'in baya da suka
shude ba a sake jin duriyar wannan Macijiya ba a wannan
birni.
Kakana da dan uwana ma Muraisu sun fafata da ita
basu sami nasarar komai ba. Lallai kuwa nima yau sai na
fuskanci wannan tsinanniyar Macijiya.
Idan har ta kashe mini 'yata ba zan saurara ma ta ba
sai dai nima ta kash eni!"
Koda gama fadin haka sai Sarki ya gama kimtsawa
cikin gaggawa ya fita kofar filin fada ya hau dokinsa ya
jagoranci Dakarun yaki, mutum dubu dari biyu suka fice
daga cikin birnin suka durfafi inda kogon Macijiya yake.
Tafiyar rabin sa'a suka yi suka iso kogon.
Da isowarsu suka ga abin al'ajabi irin wanda basu
taba gani ba, domin sun iske gimbiya Sulaiza tana ta yin
mugun artabu da Macijiyar.
A wannen lokaci Sulaiza ta sami raunika har guda
uku a jikinta. Gashi dai jini na zuba a jikinta amma bata
sare ba tana dada ci gaba da yakar Macijiyar.
Koda Sarki Huraisu ya ga halin da 'yarsa ke ciki sai
ya fusata ainun ya zare takobinsa ya duro daga kan dokinsa
ya falfala da gudu izuwa kan Macijiyar da nufin ya kaiwa
Sulaiza dauki.
Su kuwa sauran Dakarun yaki, lokacin da suka yi
arba da wannan Majiya suka ga tsananin girmanta da
tsawonta kuma suka ga yadda take rugurguje duk dutsen da
ta maka da jelarta ko kanta sai suka firgice ainun suka
dimauce.
Wasu mna basu san sa'adda suka fara sakin fitsari ba a
wando. Masu karfin hali ne suka iya fara ja da baya
wadanda kuwa suka razana ainun sai dai ka ga sun sume
daga tsaye.
Lokacin da Sarki Huraisu ya kaiwa Sulaiza dauki
suka ci gaba da yakar Macijiyar su biyu sai artabun ya kara
tsamari fiye da farko, domin Macijiyar ta kara fusata.
Cikin shammace kuwa Macijiyar ta make Sarki Huraisu
da jelarta. Nan take yai tsalle sama kamar an cillashi daga
cikin baka ya maku a jikin wata bishiya ya fado kasa cikin
nugun hali mai kama da suma, bar jini na bul6ulowa ta
cikin hancinsa da bakinsa.
A jikinsa kuwa inda Macijiyar ta doka da jelarta tamkar
adda aka sa aka yi masa wawan sara guda biyu, domin
wajen ya dare, jini na zuba.
fusata ainun ta kwarara mugun nama ta
daka wawan tsalle ta dira akan Majiyar ta caka 'yan yatsu
hannayenta biyu a cikin idanun Macijiyar.
Koda Sulaiza ta ga abinda ya faru da mabaifinta sai ta kurma uban
ihu. Cikin zafin zama
Sai gashi ta kwakule idanuwan Macijiyar ai kuwa sai
jini ya 6alle tamkar an saki ruwan teku. Nan take Macijiyar
ta sulale kasa matacciya.
''Kai Ko ni AA Misau sai da na dan razana amma da na tuna jarymine ni sai na dake hhh"
Koda ganin wannan gagarumar jarumtaka da Sulaiza
tayi sai Dakaru suka rude da shewa da ihuwa suka kama yi
ma ta jinjina.
Ita kuwa Sulaiza ko kallonsu bata yi ba, sai ta ruga
izuwa inda mahaifinta yake ta rungumeshi tana mai rusa
kuka.
Cikin gaggawa aka dauke Sarki Huraisu aka komna
cikin birnin Lairuf aka kaishi cikin turakarsa aka
shimfideshi, Likitocinsa kuwa suka taru a kansa suka kama
aiki.
Sulaiza bata motsa ko ina ba sai da ta ga Sarki
Huraisu ya farfado sannan hankalinta ya kwanta. Koda
Sarki Huraisu ya bude idanunsa ya tsinci kansa a raye sai
ya cika da tsananin mamaki da farin ciki.
Cikin matu kar karfin hali ya budi baki yana mai
duban Sulaiza ya ce, "Ya ke 'yata me ya faru ga Macijiya?",
Koda jin wannan tambaya sai Sulaiza tayi murmushi
ta ce, "Na kasheta".
-Da jin haka sai Huraisu ya kara cika da mamaki ya
Ce Ke kuwa ya ya aka yi kika kashe macijiyar da ta gagari
Ubana da dan uwana Muraisu
Nan take Sulaiza ta zaiyane masa duk abinda ya faru.
koda jin bakan sai Sarki Huraisu ya sake cika da tsananin
Farin ciki ya ce, "Ya ke 'yata, kiyi sani cewa tabbas kin
Ajive abin taribi wanda har abada ba Za a iya mantawa da
ba, saboda baka lallai Zan sa aje a saro kan wannan
Macijiya a ratayeshi a jikin gunkin da ke cikin fada domin ya
Zamo abin tunawa da wannan gagarunmar jarumtaka da kika
Kamar yadda Sarki Huraisu ya fada haka al'amarin ya
Kasance, wato sai da aka je aka saro kan wannan Macijiya
za kwakule komai na jikinsa ya zamana sauran
Kwaarangwal din kan, sannan aka ratayeshi a jikin wani
Gunki da ke cikin fada wanda aka sassakashi cikin
Kamannin gimbiyaa Sulaiza.
Kai idan ma mutum bai taba shiga fadar ba idan ya ga
Wannan gunki sai ya yi zaton gimbiya Sulaiza ce a tsaye a
Wajen sai dai idan ya ga bata motsi, sannan zai gane cewa
Gunkinta ne ba ita bace.
Fatar wannan Macijiya kuwa, sai aka daukota aka yi
don bango da ita a cikin fadar gaba daya.
Wannan shi ne dalilin da ya sa aka kasa mantawa da
wannan gagarumar jarumtaka wacce gimbiya SulaizZa tayi
Domin ta shiga cikin kundin tarihin kasar kuma al'amarin
na nan a rubcue har yau gar gobe.
AA Misau ke magana
Jarumtaka ta biyu wacce gimbiya Sulaiza tayi
bayan birnin Lairuf akwai wani tsohon kogi wanda shin,
fiye da shekaru arba'in baya ba a iya shan ruwansa,
ba a iya shiga cikinsa domin duk abinda shiga ci
ruwan sunansa gawa.
Ba komai ne ke hallaka mutane da dabbobi ba a ci
kogin face wata hatsabibiyar halitta mai siffa iri biyu.
kan balittar izuwa cibiyarta siffar mutum ce amma da
cibiyarta zuwa kasa siffar Kada gareta.
Jelar halittar tana da tsananin kaifi tamkar zabira, duk
abinda ta sara da ita sai ta darashi gida biyu. Kuma farat
hannayenta kaifi ne da su tamkar bakin takubba, kuma su
da tsini tamkar na mashi.
Wani abin ban haushi shi ne, halittar tana da siffa
irin ta 'ya mace domin kirjinta a cike yake, kuma fuska
na da tsananin kyau ga gashi dogo baki sidik gwaninb
sha'awa, amma duk wannan kyawu nata banza ne irin
dan maciji ne, domin ta kasance azzaluma.
Ita dai wannan halitta ta kasance mai tsananin
mugunta da rashin imani, kuma bata da wani abinci fa
jini walau na mutum ko na dabba.
Babbar illar wannan halitta shi ne, KAIFI DA TSINI
baya tasiri a jikinta, haka ma tsafi. Fatake da Dakar
birnin Lairuf sun sha kokarin yakar halittar domin
kawar da ita amma sun kasa, domin komai yawansu sai
karkashesu ta shanye jininsu.
Sarki Salmar da Sarki Muraisu ma sun jarraba yakar
wAnnan haitta amma duk basu sami nasara ba, da kyarma
suka tsira da rayuwarsu bayan sun sami mugayen raunika
tamkar ba za su rayu ba.
ne
da kashe wannan
Bayan kwanaki arba'in
hatsabibiyar Macijiya Sarki Huraisu ya sami lafiya ya warke
sumul daga raunikan da ke jikinsa wanda Macijiyar tayi masa
a lokacin da yaje ceton rayuwar Sulaiza.
A ranar ne Huraisu ya sami damar fitowa fada ya
ZAuna akan karagar mulki. Zamansa ke da wuya sai ga
gimbiya Sulaiza ta shigo cikin fadar a cikin shigar yaki
fuskarta cike da murmushi da annuri. Al'amarin da ya
matukar baiwa Sarki Huraisu mamaki ke nan domin bai san
dalilin da ya sa tayi shigar yaki ba.
Koda shigowar Sulaiza cikin fadar sai Marokan Sarki
Huraisu suka shiga yi ma ta kirari suna cewa:
"Ga BASADAUKIYA yar SADAUKAI".
"Makashin hatsabibiyar Macijiya"
Sulaiza ta karaso daf da karagar Sarki Huraisu ta
risina ta kwashi gaisuwa, sannan ta dago kai ta dubi sauran
fadawan da ke zagaye da Sarki tayi gyaran murya ta ce,
"Ran Sarki ya dade nazo ne domin na nemi wata alfarma
guda daya a wajenka".
Koda jin wannan batu sai fadar ta sake yin tsit, kowa
ya zuba ido kuma ya kasa kunne domin yaji abinda
gimbiya Sulaiza za ta bukata.
Sarki Huraisu ya ya ce
"Fadi duk irin bukatarki ya ke 'yata, kowacce iri ce
c in da
ya dubi Sulaiza cikin murmushi
ina da ikon biya miki ita, lallai zan biya miki, domin ki
fito mini da darajata, ba ma anan kasar ba har a gaba daya
wannan nahiya sakamakon kashe shedaniyar Macijiya da
kika yi domin a baya wanzuwar Maxijiyar ya haddasa
tsananin tsoro a zukatan jama'ar gari har ma da baki masn
shigowa.
A halin yanzu harkokin kasuwancinmu sun
bunkasa fiye da da can ainun."
Sa'adda Sarki Huraisu ya zo nan a zancensa sai
Sulaiza tayi murmushi ta ce, "Zancenka dutse ne ya
Abbana. Bukatar da na zo maka da ita yanzu ita ce, ina son
kayi mini izini naje kogon SAIJUL na yaki wannan
muguwar halitta dake cikinsa na kawar da ita kamar yadda
na kawar da hatsabibiyar Macijiya domin ita ce kadai mugun
abun da ya rage a wannan birni namu wanda yake kawo
cikas a harkokin kasuwancinmu gami da barazana ga
jama'a bisa rashin samun kwanciyar hankali".
Koda Sulaiza tazo nan a zancenta sai hankalin kowa
da ke fadar ya dugunzuma aka rude dak hayaniya aka hau
ka ce-na ce.
Shi kuwa Sarki Huraisu saboda hankalinsa ya birkice
sai ya sunkui da kansa kas ya yí tagumi kawai, kuma yai
shiru yana tunani har izuwa tsawon 'yan dakiku. Daga can
sai ya dago kai ya dubi Sulaiza a sannan ne fadar ta sake AA Misau ke magana
Shiru tamkar mutuwa ta gifta domin aji abinda Sarki zai
Huraisu ya yi gyaran murya sannan ya dubi Sulaiza
on nutsuwa ya ce, "Ya ke 'yata ina son ki janye wannan
Hukata taki domin ina tabbatar miki da cewa wannan karon
baza ki tsira da rayuwarki ba muddin kika ce za ki je
Kogon Saijul ki yaki wannan halitta, domin hatsabibancinta
8 ninka na waccan Macijiya da kika kashe sau uku.
Magaifinmu ma da bakin cikin wanna halitta ya
mutu, domin ya tsaneta ainun fiye da yadda

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment