Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da
yarima Hasnalu.
Koda Sabirat tayi arba da gimbiya Lushaira sai ta
yanke jiki ta fadi kasa sumammiya, domin a zatonta matar
marigayi Sarki Muraisu ce ta dawo.
Shi kuwa Sarki Hruaisu bai san sa'adda ya mike tsaye
ba daga kan karagasa domin shima zata ya yi Husnaila ce
ta dajin Kirzufa ta dawo.
Gaba dayan jama'ar da ke fadar kuwa sai kowa ya
cika da tsananin mamaki. Sulaiza ce kadai bata ankara da
abinda ke faruwa ba, kuma ita ce ta farga da halin da
mahaifiyarta ta shiga, don haka sai ta ruga izuwa kanta ta
shiga yi ma ta fifita har sai da ta farfado sannan ta tasheta
tsaye ta mai da ita kan kujerarta tana mai memakin abinda
ya sa Sabirat ta suma.
Tabbas Sulaiza ta ga lokacin da Sabirat ta kuráwa
Lushaira idanu kuma ta san cewa dalilin ganinta ne ta suman

Nima kuma a dalilin ganin ta suman ne zan dakata a nan har sai mun farfada mata ruwa ta dawo hayyacin ta lolx

Zan dakata anan saikuma Allah ya kaimu gobe Insha Allah Zamu Ci Gaba
AA Misau ke maganaBUSA A MUTU!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part E.
Takun Karshe

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke magana

(Ina yima Daukacin Mutanen Gidan Nan Fatan Alkhairi Barka Da Safiya)

DON HAKA SAI TA AIYANA A RANTA CEWA LALLAI SAI TA TAMBAYETA
dalilin Wannan suma na ta.
Shi kuwa yarima Hasnalu tun da suka shigo fadar yana
yin arba da gimbiya Sulaiza sai yaji nan take yea kamu da
tsananin sonta, don haka sai ya kura ma ta idanu ko kiftawa
beya yi
Sa'adda Sulaiza ta lura da irin kallon da yarima Husnalu
ke yi ma ta sai ta daka masa harara.
Ai kuwa ba shiri ya kau da kai ga barin kallonta amma
duk da haka bai daina satar kallonta ba.
Sarki Huraisu ya tafi izuwa Sarki Imsar suka rungume
Juna cikin tsananin farin ciki tamkar babu tunanin komai
cikin zukatansu.
Sarki Huraisu ya janye jikinsa daga cikin na Imsar suka
fuskanci juna ya ce, "Mun dade bamu hadu ba ya kai
abokina".
Imsar yai murmushi ya ce, "Zancenka dutse ne, lallai
akwai bukatar mu zauna mu yi doguwar hira domin ga
dukkan alamu akwai labarai a bakin kowannenmu."
Koda jin haka sai Sarki Huraisu ya bushe da dariya ya
ce, "Tabbas haka maganarka take".
Nan take Sarki Imsar ya gabatar da yarima Hasnalu da
gimbiya Lushaira a ma tsayin 'ya'yansa ga Sarki Huraisu.
Shima Huraisun sai ya gabatar da gimbiya Sulaiza a
matsayin 'yarsa.
Yana cikin gabatar da gimbiya Sulaiza ne Sarki Imsar
ya tari numfashinsa ya ce, "Ai ba sai ka yi cikakken bayani ba
akan Sulaiza, domin babu inda labarinta bai kai ba a cikin
wannan nahiya tamu.
Ina da labarin cewa ita ce ta kashe hatsabibiyar maciiiv
da muguwar halitta ta cikin kogin Saljas wadanda suka addak:
birnin Lairuf sama da shekaru arba'in baya da suka gabata.
Ya kai Abokina, kayi sani cewa kayi matukar sa'a da ka
sami wannan BASADAUKIYAR 'ya, domin in banda ita ba
rayuwarka na cikin mugun ha dari."
Sarki Huraisu ya hade rai ya ce, "Mu bar wannan zance
dai yanzu sai mun kadaita".
Nan take Sarki ya dubi gimbiya Sulaiza ya ce, ta tafi da
gimbiya Lushaira izuwa turakarta."
Lokacin da gimbiya Sulaiza ta kama hannun Lushaira ta
ja ta suka shige izuwa cikin gidan sarautar a lokacin da
gimbiya jama'a suka bi Lushaira da kallo cikin dimauta bisa
ganin tsananin kyawunta wanda ya ninka na gimbiya Sulaiza.
Shi kuwa yarima Hasnalu sai aka tafi da shi izuwa nasa
masaukin dabam.
Sarki Huraisu yaja Sarki Imsar izuwa cikin dakin cin
abinci suka zauna aka kawo abinci da abin sha iri-iri suka yi
hani'an.
Bayan sun nutsu sai Sarki Huraisu ya yi gyaran murya
ya dubi Imsar cikin alamun tsananin damuwa ya ce, "Bani
labarin kwalbar sihiri. Shin ka sami nasarar ciro wannan gasht
da ke cikinta?".
Sa'adda Sarki Imsar yaji wannan tambaya sai ya bushe
da dariya sannan ya hade rai ya dafa ka fadar Sarki Huraisu ya
ce, "Kwantar da hankalinka ya kai abokina, kayi sani cewa ba
Zan taba iya ciro wannan gashin sihiri ba daga cikin wannan
kwalba ba, kuma ina tabbatar maka da cewa duk duniya babu
wanda zai iya wannan aiki face mutum biyu.
Daga dan da Husnaila ta haifa a dajin Kirzufa, sai kuma
yarka gimbiya Sulaiza. Ina mai ja maka kunne akan kada ka
Kuskura ka ce za ka sanar da gimbiya Sulaiza batun wannan
hirin tsafi yanzu domin kana sanar da ita za tayi bincike
akansa ta gano yadda aka yi ka zamo Sarkin garin nan. Idan
kuwa ta gano hakan sai ta tsaneka kuma ta gujeka har abada
ba za ta taimaka ba da ka mallaki wannan sihirin tsafi da za ka
cika bablban burinka na duniya.
Ka sani cewa a halin yanzu bamu da wani zabi wanda
ya h mu ci gaba da jira har izuwa sa'adda dan Husnaila zai
fito daga cikin dajin Kirzufa bayan ya gama busa KAHON
BUSA A MUTU sau adadin dabbobin dajin a sannan ne zamu
Iya samnun nasara akansa'",
Sa'adda Sarki Imsar yazo nan a jawabinsa sai hankalın
Sarki Huraisu ya dugunzuma fiye da ko yaushe a rayuwarsa
ya dubi Sarki Imsar a fusace ya ce, "Ta ya ya zamu sami
nasara akan wannan yaro alhalin ance zai fito cikin gagarumar
jarumtaka ?"
Sarki Imsar ya yi murmushi ya ce, "Bincikena ya gano
cewa idan har na sami digon jinin dan Husnaila zan iya
amfani da shi wajen ciro wannan gashin sihiri daga cikin
kwalbar.
"Yarka gimbiya Sulaiza za ta iya tarar dan Husnaila tayi
yaki da shi har tayi masa rauni mu sami digon jininsa. Lallai
dukkan burinmu yanzu a kanta yake".
Koda jin wannan batu sai Sarkı Huraisu ya yi shiru yana
tunani.
Daga can kuma sai ya dago kai ya dubi Sarki Imsar
cikin tsananin damuwa ya ce,"To yanzu kuma ta ya ya
ya'yanmu za su tsira daga sharrin kahon BUSA A MÜ
wanda har yanzu ba a gama busashi ba, kuma ina da labarin
cewa a halin yanzu tuni 'ya'yan Sarakai uku sun mutu.
Na ji ma ance dan Sarki Zaidur ya muu, har ma shi
Sarki Zaidur din ya fusata ya debi Dakaru dubu saba'in su
tafi dajin Kirzufa, kuma tunda suka tafi har yau basu dae
ba."
Koda jin wannan batu sai Sarki Imsar ya yi mumushi
ya ce, "Tabbas duk abinda ka fadi gaskiya ne. Ina
tabbatar maka da cewa Sarki Zaidur da duk Dakarunsa sun
Mutu a cikin dajin Kirzufa, dayansu bai tsira da rayuwarsa ba
kuma ba wani ne va kashesu ba face 'yar uwata Husnaila da
danta wanda ta radawa suna Muraisu.
Ka sani cewa Muraisu yaro mai kahon busa a munu
kamanninsa iri daya ne sak da na dan uwanka marigayi Sarki
Muraisu tamkar an tsaga kara. Nima gashi na haifi ya mai
tsananin kama da 'yar uwata Husnaila, kuma ina tabbatar
maka da cewa na tsani wannan ya tawa kamar yadda yar
uwata Husnaila ta tsaneni.
In ba don dana yarima Hasnalu da nake mutuwar so ba
shi kuma yana mutuwar son 'yar uwar tasa da tuni na hallaka
gimbiya Lushaira."
Sa'adda Sarki Imsar ya zo nan a bayaninsa sai Sarkı
Huraisu yaji hankalinsa ya kara dugunzuma ainun, kuma nan
take yaji tsohuwar soyayyarsa akan Husnaila ta motsa, banda
ganinta babu abinda yake son yi tunda dai yaji cewar har
yanzu tana nan a raye a doron kasa.
Tsawon 'yan dakiku dayansu bai kara cewa uffan ba.
Daga can sai Sarki Huraisu ya dubi Imsar ya ce., "To yanzu AA Misau ke magana
mene ne amfanin wannan taro da
zamu yi da sauran
Sarakunan kasashe na wannan nahiya akan yadda za a
magance wannan annobar mutuwa ta 'ya'yanmu?"
Koda ia wannan tambaya sai Sarki Imsar ya kyalkyale
da dariya ya ce, "Ai masu iya magana Sun ce idan jifa ya
tsallake kanka
to ya ma fada kan kowa. Tunda mun tabbatatar
da cewa wannan masifa ba za ta iso kanmu ba ai mu babu
ruwanmu.
Kawai idan an zauna wannan taro ana tattaunawa mumna
mu nuna matukar damuwarmu kuma mu bayar da hadin kai
bisa duk irin gudunmawar da za a bukata daga garemu, don
kokarin kawar da annobar".
Koda Sarki Huraisu yaji wannan batu sai hankalinsa ya
kwanta ya kamu da tsananin farin ciki, bai san sa'adda ya
rungume Imsar ba yana mai kyalkyala dariya. Shima Sarki
Imsar din sai ya kama kyalkyala dariyar.
Amma a can karkashin zuciyar Sarki Huraisu bai
aminta da Sarki Imsar ba.
Tunanin da yake yi shi ne ya za a yi ya mallaki wan nan
gashin sihiri, domin ya cika babban burinsa na duniya. Lallai
idan ya mallaki shirin sai ya auri Husnaila ya daukota daga
dajin Kirzufa ya dawo da ita birnin Lairuf.
Wannan shỉ ne abinda ya taru tsakanin Sarki Huraisu da
Sarki Lmsar a ranar da gaba dayan Sarakunan nahiyar suka
taru a birnin na Lairuf domin a tattauna akan yadda za a
magance matsalar Yaro mai kahon BUSA A MUTU

AL'AMARIN YARIMA Hasnalu kuwa, lokacin da ta
kaishi masaukinsa sai ya kasa samun sukuni
domin begen gimbiya Sulaiza ne ya addabi zuciyarsa
Hatta abincin da aka kawo masa sai ya kasa ci ya kama
zarya a cikin dakin.
Yana cikin wannan hali ne Hadimin da ya kawo masa
abinci ya sake shigowa cikin dakin dauke da 'ya'yan itatuwa
kala-kala bisa faranti.
Da shigowarsa ya ga yarima bai ci abincin da ya kawo
masa ba sai ya cika da mamaki ya ce, "Ya shugabana shin
abincin ne bai yi maka ba a sauya maka wani kalar?".
Yarima Hasnalu ya bude jakarsa ya debo dinare mai
yawa ya mikawa wannan hadimi. Hadimin ya karba hannunsa
na karkarwa saboda tsananin mamaki ya ce, "Me za a siyo
maka?"
Hasnalu ya ce, "Babu abinda za a sayi mana. Wannan
kudi duk naka ne na baka kyauta, amma ina son kayi mini
wani aiki guda daya jal!
Idan bukata ta biya zan kara ninka wadannan kudade
wadanda na baka yanzu".
Koda jin haka sai Hadimin ya rude yana mai zaro idanu
ya ce, "Fadi bukatarka naji ya shugabana".
Hasnalu ya ce, "Ba komai nake so kayi mini mini ba
face ka san dabarar da za ka yi na gana a sirrance da 'yar
Sarkinku a yau din nan kafin dare ya yi".
Koda jin wannan batu sai Hadimin ya cika da murna, ya
yi murmushi ga yarima Hasnalu ya ce, "Ai wannan aiki mai
sauki ne, tamkar cire silin gashi ne daga cikin tandun Mai. Ka
jirani daga nan zuwa yamma.Lallai Zan dawo nayi maka
jagora izuwa bangaren da gimbiya take ku gana.
Koda jin wannan batu sai Hasnalu ya cika da farin ciki.
Nan dai suka yi sallama shi da hadimin ya tafi bisa alkawarin
Zai dawo gareshi da yamma
A CAN bangaren gimbiya Sulaiza kuwa, lokacin
ta kai gimbiya Lushaira turakarta sai ta nuna
ma ta kewaye. Lushaira taje tayi wanka sannan a
koma cikin dakin barci ta sauya tufafi ta caba ado. Ta dawo
falo inda ta iske gimbiya Sulaiza a zaune tana jiranta ga abinci
iri-iri da ababan sha a gabanta.
Nan dai suka zauna suka kama cin abincin cikin
nutsuwa saboda nishadi tamkar sun dade da sanin juna.
Bayan sun gama kintsawa ne gimbiya Sulaiza ta dubi
Lushaira ta ce, "Ya ke kawata ni kuwa ian son na yi miki wata
tambaya idan ba za ki sani damuwa ba."
Lushaira tayi muinushi ta ce, "Ai kuwa matambayi
baya bata. Lallai zan sanar da ke iyakar abinda na sani".
Gimbiya Sulaiza tayi gyaran murya sannan ta ce, "A
dazu lokacin da ku ka shigo fada ke da dan uwanki da
mahaifinku na ga mahaifiyata ta kura miki idanu, a dalilin
haka ne ma ta yanke jiki ta fadi kasa sumammiya? Shin akwai
wata alaka ne tsakanin danginmu da naku?".
Koda jin wannan tambaya sai Lushaira ta cika da
marmaki ta ce, "Ai ni tunda nake tare da iyayena basu taba
bani labarin ku ba sai yanzu da na zo na ganku.
A ranar da zamu baro can birninmu Huraira na ji
mahaifina na cewa zai zo birnin Lairuf ya ga abokinsa wanda
Suka jima basu ga juna ba tsawon shekara da shekaru."
Ya yin da gimbiya Sulaiza taji haka sai tayi shiru tana
jinjina kai gami da nazari a cikin kwakwalwarta, kawai sai ta
mike tsaye ta dubi Lushaira ta ce, "'Ki jirani 2an je yanzu na
dawo mu ci gaba da hira. Ki saki jikinki tamkar a gidanku
kike".
Lushaira tayi murmushi ta ce, "Ina sauraronki domin ina
Son mu yi hira sosai ki bani labarin irin jarumtakar da kika yi
a lokacin da kika yaki hatsabibiyar macijiya da muguwar
halita ta cikin kogin Shaljus, domin a rayuwata babu abinda
ke birgeni sarma da jarumtaka".
Gimbiya Sulaiza tayi murmushi ta ce, "Nimna haka,
kuma na yi alkawarin cewar duk namijin da zan aura dole ne
ya fini jarumtaka kuma sai ya yi irin jarumtakar da ta fi tawa
duniya sannan zan aureshi".
Koda gama fadin hakan sai gimbiya Sulaiza ta juya ta
fice daga cikin turakar ta bar gimbiya Lushaira cikin tsananin
fargaba sakamakon jin wannan furuci na karshe da tayi.
Tabbas Lushaira ta lura da irin kallon da ta ga yarima
Hasnalu ya yiwa gimbiya Sulaiza dazu a lokacin da suka
shigo fada, kuma ta gane cewa ya kamu da tsananin sonta nan
take.
Lushaira ta san cewa yarima Hasnalu bai kasance jarumi
ba, kuma bai ma taba fita yaki ba bare ya yi wani abu na
jarumtaka.
Ashe kuwa har abada ba zai taba samun soyayyar
gimbiya Sulaiza ba.
Lokacin da gimbiya Sulaiza ta baro Lushaira a can
turakarta bata wuce ko ina ba sai can furakar mahaifiyarta
Sabirat.
Da shigarta ta iske Sabirat zaune a gefen gado ta hada
kai da guiwa.
cikin firgici gimbiya Sulaiza ta kira sunan
Ummin tata.
gimbiya Sulaiza sai tayi sauri
Koda Sabirat taji muryar
ta goge hawayen idanunta sannan ta dago kai ta dubeta cikin
fara'a ta ce, "Ya ke yata lafiya kika kawo miní ziyara
wannan lokaci da baki saba zuwa ba?"
a
Koda jin wannan tambaya sai gimbiya Sulaiza tayi
ajyar zuciya sannan ta zauna daf da ita suka fuskanci juna
cikin yanayin damuwa gimbiya Sulaiza ta dubi Sabirat ta ce,
Ya ke Ummina ki sani cewa ba tun yau ba na fuskanci kina
boye mini wadansu al'amura naki. Yanzu haka kin yi kuka
mai yawa domin ga alamar nan a cikin idanunki duk sun kada
sun yi jawur. Tabbas akwai wani abu da ya faru a baya wanda
kika tuno da shi a yanzu.
Shin za ki iya gaya mini dalilin da yasa kika suma dazu
a afda sa'adda kika yi arba da gimbiya Lushaira?".
Koda jin wannan tambaya sai Sabirat ta murtuke
fuskarta kamar an aiko ma ta da sakon mutuwa ta ce, "Ni dai
kawai ji nayi jii ya đebeni na fadi, darna tun da sassafe nake
jin jikina babu dadi, amma ba wai don na ga gimbiya
Lushaira bane wannan abu ya sameni".
Sa'adda gimbiya Sulaiza taji haka sai tayi ajiyar zuciya
sannan ta mike tsaye ta nufi bakin kofa. Kafin ta fice daga
cikin turakar sai ta waigo ta dubi mahaifiyar ta ta ta ce, Ya ke
Ummina kiyi sanio cewa kunnuwana sun ji ansar tambayar
da na yi miki yanzu, amma zuciyata bata gamsu ba.
Da sannu abinda kika binne a cikin zuciyarki zai fito fili
na ganshi. Ina tsoron ranar da za ki ji kunyata bisa wannan
al'amari da kike ta 6ove mini shi tsawon shekara da shekan
Koda garma fadin hakan sai Sulaiza ta fice da sauri daos
cikin turakar. Ita kuwa Sabirat sai ta fashe da matsanaicin
kuka saboda tabbas ta san cewa ta boyewa Sulaiza babban
sirir wanda idan ta baiyana ma ta shi a yan zu tamkar ta ruguzą
farin cikin kowa da kowa ne a cikin birnin Lairuf.
Lokacin da gimbiya Sulaiza ta baro turakar mahaifiyarta
ta nufi 6angaren da ta ta turakar take sai tayi kicibus da
wannan Hadimi wanda ya kaiwa yarima Hasnalu abinci. Suna
haduwa sai hadimin ya sha gabanta ya Zube ya kwashi
gaisuwa sannan ya ce, "Ya shugabata, yarima Hasnalu dan
Sarki Imnsar na birnin Hutaira yana neman alfarmar ganawa da
ke a lambun Sarki".
Koda jin haka sai gimbiya Sulaiza ta dubeshi a fusace ta
ce, "Shin ka taba ganina na gana da wani saurayia rayuwata
har da
ka ZO mini
Hadimin ya sake risinawa ya ce, "Ki gafarceni ya shugabata,
da Wannan sako?".
ki dubeni da adalcinki idan baki anmsa wannan gayyata ba ta
yarima Hasnalu zan yi asarar dukiya mai
Koda jin wannan batu sai Sulaiza tayi murmushi ta ce,
"Shi ke nan yarima Hasnalu ya ci albarkacinka. Lallai ba zan
bari kayi asara ba",
yawa".
Koda gama fadin hakan sai ta juya ta nufi inda lambun
Sarki yake.AA misau ke magana
Lambu ne mai giman gaske wanda ke cine da furanni
iri-iri masu kyau da kamshi. Akwai dabbobin daji da
tsuntsaye kala-kala a cikin lambun masu ban sha'awa suna ta
kai kawo suna kiwo abinsu.
Yarima Hasnalu na zuane bisa wata kujera ta zinare sai
ya hango gimbiya Sulaiza ta shigo cikin lambun amma
fuskarta a murtuke take babu annuri ko kadan.
Tun kafin ta karaso inda yake ya mike tsaye dan
girmamata har sai da tazo ta zauna a kujerar da ke fuskantar
tasa sannan shima ya zauna.
Zamansa ke da wuya sai Sulaiza ta budi baki ba tare da
ta kalleshi ba ta ce, "Me ka ke son ka gaya mini?".
Koda jin wannan tambaya sai Hasnalu yaji zuciyarsa ta
buga da karfi, domin wannan ne karo na farko a rayuwarsa da
na fara yiwa budurwa magana.
Ita kanta Sulaiza ta lura da cewa lallai Hasnalu bako ne
shi akan soyayya, dariya ma take yi masa a can karkashin
Zuciyarta.
Cikin rawar murya Hasnalu ya budi baki ya ce, "Ranki
ya dade ba wani abu bane yasa na bukaci na gana da ke anan
ba face domin na sanar da ke cewar a yau da na kyallara
idanuna na ganki zuciyata ta kamu da tsananin kaunar..."
Kafin Hasnalu ya garma furta wannan batu sai Sulaiza ta
tari numfashinsa ta ce, "Ya kai wannan dan Sarki kada ka
bata harshenka ka furta sirrin zuciyarka a inda ba zai yi tasiri
ba, domin kuwa har abada ruwa da wuta ba za su taba haduwa
ba.
ldan har kana son ka sami yardata ka koma kasarku ka
koyi yaki da jarumtaka sannan kayi jarumtakar da tafi wadda
nayi anan birnina har ka shahara ko ina a cikin duniya kamar
yadda jarumin da ke cikin dajin Kirzufa ya zamo dodo a
wannan nahiya tamu gaba daya.
Duk da cewa jarumin yana busa kahon da ake mutuwa
sai naji ya burgeni tun gabannin na ganshi. Tabbas wannan
jarumi shi ne irin wanda nake son na aura a rayuwata domin
ya yi gagarumar jarumtaka wacce har abada ba za a manta da
shi ba a wannan duniya.
Ina da labarin cewa Sarki Zaidur ya debi Dakaru dubu
saba'in ya tafi da su izuwa dajin Kirzufa domin su kashe
wannan jarumi su kone kahon da yake busawa amma dayansu
bai dawo ba gida a raye.
Lallai wannan jarumi ya cika abin kwatance, kuma abin
alfahari. Idan har za ka iya zuwa dajin Kirzufa ka kamo
wannan jarumi a raye kaz0 mini da shi lallai ka kawo mini
sadakin aurena kamar yadda tsarin aure ya gindaya anan
birnin Lairuf."
Koda gama wannan jawabi sai gimbiya Sulaiza ta mike
tsaye ta fice daga cikin lambun ta bar yarima Hasnalu a zaune
cikin tsananin tashin hankali da damuwa, amma saboda ya
dimauce a cikin sonta sai ya aiyana a ransa cewa ta kowanne
hali sai ya kamo jarumin da ke cikin dajin Kirzufa mai kahon
BUSA A MUTU ya zowa Sulaiza da shi duk da cewar shi bai
kasance jarumi ba.
Wannan shi ne abinda ya faru tsakanin yarimna Hasnalu
da gimbiya Sulaiza Sarkin yakin birnin Lairuf bayan sun gana
a lambun Sarki Huraisu.
KASHE gari da hantsi gaba dayan Sarakunan nahiyar
suka hadu a cikin babban dakin taro na gidan
Sarautar birnin Lairuf.
Bayan kowa ya hallara sai Sarki Huraisu ya mike tsaye
ya yi jawabin barka da zuwa ga dukkan Sarakunan sannan ya
ce, "Ya ku 'yan uwana Sarakai, kowa a cikinmu nan ya san
annobar da ta barko a wannan nahiya tamu ta mutuwWar
manyan 'ya'yayenmu.
A halin yanzu 'ya'yan sarakai uku sun mutu. A dalilin
haka ma Sarki Zaidur da Dakarunsa dubu saba'in duk sun
hallaka a dajin Kirzufa.
Yanzu a cikinku wane ne zai bamu shawarar da za ta
fisshemu mu kawo karshen wannan yaro mai kahon BUSA
A MÜTU? domin a yau ma idan lokacin busa kahon busa a
mutu ya yi sai ya busashi, kuma lallai sai dan daya daga
cikinmu ya mutu?"
Sa'adda Sarki Huraisu yazo nan a jawabinsa sai dakin
taron ya yi tsit! Aka rasa wanda zai ce kala.
A wannan lokaci Sarakuna biyu wadanda 'ya'yansu
suka mutu sun sunkui da kawunansu kas suna zubar da
hawaye.
Wani Sarki da ake kira Jamal ibini Thisar wanda ke
mulkin birnin Hubbar sai ya mike tsaye yai gy aran murya
sannan ya ce, "Ya ku 'yan uwana Sarakai, kun sani cewa
fiye da shekaru arba'in baya dajin Kirzufa 'baya shiguwa
domin duk mahalukin da ya shigeshi baya fitowa a rave
Masu iya magana sun ce mai laya ya kiyeyi mai zamani '
Ni a tawa shawarar zai fi kyau mu taru gaba dayanmu
mu duka Sarakan nan tare da dukkan bokayenmu da kuma
Dakaru dubu saba'in-saba'in daga kowanne Sarki mu durfafi
dajin Kirzufa.
Lallai ba zamu fito ba har sai mun tabbatar da cewa
mun kashe dukkanin abinda da ke da rai a cikin dajin, sannan
mu kone komai na dajin har sai ya zama toka!!!"

Topa Ganin Wannan Gagarumin Shiri da ake na zuwa dajin kirzufa Yasa Sadauki AA MISAU Nima zan je na shirya tsaff ko da mai rakani nehhh cikinku

"SHIN SAURAN SARAKAN ZA SU YARDA DA
WANNAN SHAWARA DA SARKI JAMAL YA BAYAR?

*YAUSHE NE GIMBIYA SULAIZA ZA TA GANO
SIRRIN DA MAHAIFANTA KE BOYE MA TA?

SHIN YARIMA HASNALU ZAI IYA CIKA
KA IDAR DA GIMBIYA SULAIZA TA GINDAYA MASA
KAFIN YA SAMI SOYAYYARTA?

*YAUSHE NE JARUMI MURAISU DAN MURAISU
ZAI GAMA BUSA KAHON BUSA A MUTU HAR YA
FITO DAGA CIKIN DAJIN KIRZUFA?

*YAUSHE NE GIMBIYA LUSHAIRA DA JARUMI
HURAISU ZA SU GA JUNA, KUMA MAI ZAI FARU
IDAN MURAISU YA GA LUSHAIRA TANA TSANANIN
KAMA DA MAHAIFTYARSA?

Mu hadu a BUSA A MUTU littai na biyar (5) domin
jin ci gaban wannan kayataccen kasaitaccen labari
Daga mai debe muku kewa a kullum da ko yaushe.
ABDUL'AZIZ SANI M GINI

Mai Magana
Al Amin Ahmed Misau
Nake cewa sai mun hadu a littafi na 5 Insha Allah
Shin Ana tare dai koh??
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment