Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya tsani
Waccan Macijiiya, dalili kuwa shi ne ita wannan halitta ta
kashe mutane da yawan gaske, babu wanda ma ya san iya
Bdadinsu kuma har kwanan gobe bata daina barna ba tun da
bakin da basu san da wanzuwarta ba in dai suka je bakin
kogin sai ta hallakasu.
Ita kuwa waccan Majiyar fiye da shekaru arba'in baya
ba a kara in ta kashe wani ba tunda babu mai zuwa inda
ake"
Lokacin da gimbiya Sulaiza taji wannan jawabi daga
bakin Sarki sai tayi ajiyar zuciya sannan ta ce, "Ya kai
Abbana kamar yadda baka taba tsammanin cewa zan iya
kasbe waccan Macijiya ba ina tabbatar maka da cewa zan iya
Kashe waccan muguwar halitta saboda ina ji a jikina
Cewar sa'a na gareni.
Ka tuna fa cewa mahaifinku da kakanku duk sun kasa
Kawar da wannan Macijiiya haka ma dan uwanka Muraisu
Shima sai gashi ni a Zamanina na kawar da wannan Macijiya.
Ina mai
rokonka bisa darajar karagarka ka bani
wannan dama ka ga bainda zan yi.
Ina tabbatar maka da cewa har abada hankalina ba zai
kwanta ba kuma zuciyata ba za ta taba samun sukuni ba
face na kawar da wannan muguwar halita ta cikin kogin
Saljas."
Ya yin da Sarki Huraisu yaji wannan batu sai yai
shiru ya kara shiga cikin kogin tunani har izuwa lokaci mai
dan tsawo sannan ya dago kai ya ce, 'Ya ke 'yata kiyi sani
cewa na amince ki je ki yaki wannan muguwar halitta ta
cikin kogin Saljus amma bisa sharadi biyu.
Sharadi na farko shi ne, ke kadai za ki je, kuma ko ni
ko Dakaruna babu wanda zai biyo bayanki domin ya kawo
miki dauki.
Sharadi na biyu shi ne, idan har kika tafi daga
wayewar gari zuwa faduwar rana muka ga baki dawo ba
mun san kin hallaka, don haka zan sa a rushe gunkinki da
ke tsaye a nan cikin fadar, sannan zan sa a kone
kwarangwal din kan hatsabibiyar Macijiyar da kika kashe da
fatar jikinta domin a manta da tarihinki da ta jarumtakarki
bar abada.
Hatta labarinki da ke cikin kundin tarihin masarautar
nan sai na sa an yage iya shafin labarin naki an konashi"
Lokacin da Sarki Huraisu yazo nan a zancensa sai
yaga gimbiya Sulaiza tayi murmushi, nan take ta ce, "Ta
amince da duk wannan sharadi, kuma ta kara da
rantse da darajar mahaifiyata a gobe daga wayewar safiya
AA Misau ke magana
kafin faduwar rana sai na dawo wannan fada dauke da kan
wannan hatsabibiyar halitta".
Gama fadin hakan ke da wuya sai Sulaiza ta juya ta
fice daga cikin fadar gaba data. Shi kuwa Sarki Huraisu sai
ya bita da kallo kawai cikin tsananin tashin hankali domin
bai taba zaton za ta yarda da sharadin da ya gindaya ma ta
ba.
A zatonsa idan taji wadannan sharadai guda biyu za
ta janye bisa kudurinta.
Gaba dayan fadawan Sarki da sauran jama'ar gari sai
hankalinsu ya dugunzuma bisa jin dagewar da gimbiya
Sulaiza tayi akan sai taje kogin Saljus ta yaki wannan
muguwar balitta.
Ba komai ne yasa hankalin mutane ya dugunzuma ba
face tsananin kaunar da suke yiwa gimbiya Sulaiza bisa irin
taimakon da take yi musu.
Tun da Sulaiza ta fara girma sai ya zamana cewa ta
hana Sarki Huraisu duk irin mulkin zaluncin da yake yi a
garin. Sace-sace ya ragu ainut ya zamana cewa mutane
suna samun zaman laliya da kwanciyar hankali.
Duk irin shawarar da Sulaiza ta baiwa Sarki Huraisu
yana aiki da ita saboda Allah Ya jarrabeshi da tsananin
kaunarta ko kadan baya son abinda zai sOsa ma ta Zuciya.
Farin jinin gimbiya Sulaiza ya bazu a ko ina cikin
kasar Lairuf birni da kauye.
Mutane basu da wani buri wanda ya fi su ga Sarki
HHuraisu ya mutu Sulaiza ta hau kan karagar mulki.
Tun da Sulaiza ta taso bata taba sanin yadda aka yi
mabaifinta ya zamo Sarki ba, kuma mahai fiyarta Sabirat
bata ta6a shaida ma ta al'amarin ba, haka ma sauran
mutanen gari.
Ba komai ne ya janyo hakan ba face tsananin tsoron
Sarki Huraisu da ake ji. Kowa ya san cewa wanda duk ya
kuskura ya labartawa Sulaiza wannan labari sai an sami
sabani tsakaninta da Sarki, domin halayenta gaba daya sun
bambanta da na Sarki.
Sulaiza ta tsani zalunci da azzalumai. Tabbas idan taji
cewa mahaifinta sai da ya kashe dan uwansa Muraisu
sanann ya bau karagar mulki za ta tsaneshi, kuma ta
gujeshi.
Dama tun Sulaiza na jaririya Sarki Huraisu ya sa aka
yi shela a cikin birni da kauye cewar duk wanda aka ji ya
sake furta batun marigayi Sarki Huraisu daga sannan har
izuwa karshen mulkinsa to a bakin ransa.
Bisa wannan dalili ne tarihin Sarki Muraisu ya shude
tamkar ma bai taba wanzuwa ba. In banda a bakin Sarki
Huraisun ma babu a inda Sulaiza ta taba jin cewa
mahaifinta yana da dan uwa wanda ya taba yin sarautar
kasar.
Duk sa'adda Suzala ta bijirowa Sarki Huraisu da
batun labarin dan uwansa Muraisu sai ya kawar da zancen
ya nuna mata cewa baya son tuno da abinda zai jefashi
cikin tsananin bakin ciki. Haka ma duk sa'adda Sulaiza ta
tambayi mahaifiyarta Sabirat batun labarin Sarki Muraisu
ai ta ga hankalinta ya dugunzuma ta kama kuka, don haka
SAi
sai jikinta ya yi sanyi, ba za ta kara yi ma ta maganar ba.
Lokacin da gimbiya Sulaiza taji Sarki ya aminta da
bukatarta wato ya amincewa ta tafi kogin Saljus ta yaki
wannan muguwar halitta sai ta cika da tsananin farin ciki ta
ruga izuwa turakar mahaifiyarta.
Da shigarta cikin turakar sai ta iske Sabirat zaune
gaban madubi tana caba kwalliya.
Sulaiza ta rungume Sabirat ta baya cikin tsananin
murna ta ce, "Ya ke Ummina ki tayani farin ciki Sarki ya yi
mini izini gobe naje na kashe wannan muguwar halitta ta
cikin kogin Saljus."
Koda jin wannan batu sai Sabirat ta mike tsaye
Zumbur cikin tsananin firgici ta daga hannu ta sharawa
Sulaiza mari.
Cikin tsananin fushi ta ce, "Ashe baki da hankali ban
sani ba. Wancan karon ma inda na san cewa za ki je kogin
macijiya ai ba zan barki ba."
Koda Sabirat ta zo nan a zancenta sai kuma ta fashe
da kuka ta ce, "Ki gafarceni ya ke 'yata, domin yaune ranar
farko da na ta6a dukanki da hannuna kuma hakan ta faru ne
sakamakon tsananin dimautar da na yi bisa jin inda kike
SOn Zuwa".
Koda jin wannan batu sai Sulaiza tayi murmushi ta
kama hannayen Sabirat ta ja ta izuwa kan wata doguwar
kujera sulka zauna suna masu fuskantar juna, Sannan ta ce,
Ki gafarceni ya ke Ummina, hakika na yi kuskure kuma inda nasan zuciyarki zata sosu to tabbas ba zan nemi izini Ba a wajan sarki ina tabbatar miki da cewa Yanzu na jaanye wannan bukata tawa domin hankalinki ya kwanta...

Nima kuma domin hankalina ya kwanta Zanje NemAn Abin Duniya hhhh
Domin Samunmu a WhatsApp Group ga link dinnan
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q
Admin AA Misau
Ke MaganaBUSA A MUTU!!!
Littafi Na Hudu (4)
Part D.

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke magana

Idan Allah Yakaaimu Gibe Zan Saki Part Na Karshe cikin littafi na 4 Insha Allah Dafatan Kowa Ya Tashi lafiyA

INDA NA SAN CEWA
ZUCIYARKI ZA TA SOSU HAKA TABBAS DA BAN
NEMI WANNAN IZINI BA A WAJEN SARKI. INA TABBATAR MIKI DA
CEWA YANZU NA JANYE WANNAN BUKATA TAWA DOMIN
HANKALINKI YA KWANTA."
Koda jin haka sai Sabirat ta kamu da matukar farin ciki kuma ta saki jikinta suka ci gaba da hira cikin nishadi da walwala.
Da lokacin cin abincin dare ya yi sai Sabirat ta mike
tsaye taje ta karbo musu abinci da kanta tazO suka ci abinci
tare da Sabirat har sai da suka koshi.
Suna gama cin abincin ne Sabirat ta bingire akan
wannan doguwar kujera ta kama barci mai nauyin gaske.
Ba komai ne ya baddasa hakan ba ashe Sulaiza ta zuba
banju a dai-dai inda Sabirat ta rinka debo abincin tana ci.
Koda Sulaiza taga mahaifiyarta ta kama barci mi
nauyi sai ta kura ma ta idanu tana mai cewa, "Ki gafarceni
ya ke Ummina tabbas ba zan iya janyewa ba bisa wannan
manufa tawa. Lallai gobe sai na je kogin Saljus na yi yakı
da muguwar balitta ko an kasheta ko kuma ta kasheni."
Koda gama fadin haka sai Sulaiza ta mike tsaye
kwalawa kuyangin Sabirat kira.
suka shigo cikin turakar suka jeru a layi a gaban Sulaiza.
Nan take gaba dayan kuyangin suka yi ma ta gaisuwa
Sulaiza ta dubi kuyangin su duka fuskarta a murtuke
ta ce, "Ya ku hadiman mahaifiyata ku yi sani Cewa an zubawa Ummina banju a cikin abinci ta ci, don haka za ta
ci gaba da barci mai nauyi har izuwa gobe da Yammaci,
haka ne domin na sami damar tafiya kogin Saljus na yaki
Wannan muguwar halitta ba tare da ta sani ba.
Lallai ku yi shiru da bakinku ku bar wannan al'amari
cikin sirri har na je na dawo kada ku gayawa kowa koda
kuwa Sarki ne.
Duk wacce ta baiyana wannan sirrii kuwa a bakacin
ranta domin ina dawowa daga kogin Saljus takobina za ta
sha jininta.
Koda gama wannan jawabi sai gimbiya Sulaiza ta fice
daga cikin turakar Sabirat ta tafi izuwa 6angaren da gidanta
yake.
Maimakon gimbiya Sulaiza ta kwanta tayi barci sai ta
fito filin farfajiyar gidan nata ta kama nutso a cikin ta fkin
da take yin wanka kullum ta rinka yaki a cikinsa tana mai
dada baiwa kanta horon fada har ya zamana cewa tana
koyon da dadewa a cikin Rarkashin ruwan ba tare da ta
dago samna don yin numfashi.
Duk wannan abu da Sulaiza ke yi Hadimanta sun
kewaye wannan tafki suna kallon abin al'ajabi. Lokacin da
gimbiya Sulaiza tayi nutso izuwa can karkashin ta fkin suna
kallon abin al'ajabi.
Lokacin da gimbiya Sulaiza tayi nutso izuwa can
karkashin tafkin ta dade ba ta taso sama ba sai hankalin
hadiman na ta ya dugunzuma ainun suka firgice suka fara
tinanin su ruga su je su sanar da Sarki abin da ke faruwa.
Wasu daga cikinsu kuma sai suka ce ai kamata ya yi su
Shiga cikin karkashin kogin su fara daukota tukunna domin
tabbatar da halin da take ciki. Har sun fara kwabe
jikinsu za su fada cikin tafkin ke nan sai suka ga gimbiya
Sulaiza ta taso saman tatkin CIkin kOshin lafiva tan
dadewar da tayi
jan dogon numfashi sakamnakon
Alamarin da yai matukar basu mamaki
karkashin ruwan.
ke nan basu san saadda suka kama yiwa Sulaiza tafi ba.
Sat do dare va raba sosai sannan gimnbiya Sulaiza ta
fada a cikin wannan tafki sannan
gama bajwa kanta horon fada
taje ta kwanta.
Kashe gari kuwa da sassafe bayan gimbiya SulaizA
tayi wanka ta ci abinci sai ta sake yin gagarumar shigar
yaki ta rataya takobinia a gadon bayanta sannan ta dauki
kwari da baka ta hau wani farin ingarman doki ta fice daga
cikin gidan sarautar ba tare da ma taje ta yiwa Sarki
sallama ba.
Kai tsaye Sulaiza ta nufi bayan gari ta durfafi inda
kogin Saljus yake ba tare da shakkar komai ba.
Ita dai wannan hanya wacce ake bi aje inda kogin
Saljus yake ba ma mutane ba. hatta aljanu da dabbobi sun
daina bin hanyar sama da shekaru arba'in baya domin ko
alamun takun sawun wata halittar mutum a zai gani ba akan
hanyar, amma da yake Sulaiza ta cika jaruma mai
dakalkiyar zuciya ko kadan bata ji tsoron komai ba (Ni kuma AA Misau ina buye da ita hhh) ta ci
gaba da tafiya akan hanyar cikin takama.
Koda ta ga dokinta ya firgita ya fara tsayawa yana
Tutsu da haniniya yana kokarin komawa da baya sai
ta sauka daga kansa ta kadoshi baya ta ci gaba da
kasa bar ta iso bakin kogin Saljus.
slya a
Da isowarta daf da bakin kogin sai ta takarkare ta
Tara uban ihu wancda ya cika dajin gaba daya da amsa
Kuwwa.
Inda ace akwai dabbobi da tsuntsaye a wajen da gaba
dayansu sai sun firgice sun kama guduwa daga cikin
Mafajarsu da barin shekarsu.
Bayan Sulaiza ta gama wannan ihu sai ta dubi cikin
kogin Saljus ta daga muryarta da karfi tana mai cewa, "Ya
ke wannan azzalumar halitta da ke cikin wannan kogi kiyi
sani cewa yau kwananki ya kare domin ga Sulaiza yar
Huraisu jikar Sarki Salmar tazo ta kawar da ke. Idan kin isa
kuma kin yarda da kanki ki fito mu yi gaba da gaba! Na
rantse da darajar iyayena da Kakannina yau sai na Zare
miki ruhin numfashinki".
Koda gama wannan jawabi sai Sulaiza taji an tsala
wata irin gagarumar kara wacce ta cika dajin gaba daya har
izuwa cikin birnin Lairuf.
Babu shiri Sulaiza ta durkusa kasa ta toshe
kunnuwanta da hannayenta biyu domin ji tayi kamar ta
kurmance. Gaba dayan mutane da dabbobin da ke cikin
birnin Lairuf sai da suka firgice suka dimauce domin basu
taba jin kara mai ban tsoro ba wacce ta kai wannan ba face
a kahon BUSA A MUTU, Wacce suka fara jinta a kllum
lsawon kwanakí uku da suka gabata.
Bayan sautin karar ya dauke cak, sai kogin Saljus ya
kama hautsina yana tambal-tambal tamkar zai kwaranyo
gaba dayansa izuwa cikin dajin, wata irin iska mai karfi ta
fara fitowa daga cikin kogin ta addabi Sulaiza wacce ke
tsugunne a gefen kogin.
Koda ganin haka sai Sulaiza ta mike tsaye ta zare
takobinta, kuma ta kura idanu izuwa cikin kogin tana jiran
ta ga ta inda halittar za ta fito.
Kwatsam! Sai ta ga wata iriyar shirgegiyar halitta
siflar mutum da kada tana tasowa sama tana tsiri sama
tamkar tsauni kai ka ce tokarewa za tayi da sararin
samaniya.
Tun da Sulaiza tazo duniya bata taba ganin halitta
mai girma da tsawonta ba.
ldanun halittar sun kasance jajur tamkar wuta ce ke ci
cikinsu. Gashi dai daga kanta zuwa cibiyarta siffa ce da
ita ta kyakkyawan mace amma hannayen zankala-zankala
babu kyan gani domin sun wuce kamu arba'in-arba'in,
kuma suna dauke da dogayen farata masu kaifi da tsinin
gaske tamkar takubba.
Duk sa'adda halittar ta daga jelarta ta makata a cikin
kogin sai dajin gaba daya ya yi rawa tamkar ana girgizar
kasa.
Nan dai aka fara kallon-kallo tsakanin Sulaiza da
wannan halitta a lokacin da Sulaiza ta kamu da tsananin
tsoro, domin bata taba zaton cewa haka halittar take ba.AA misau ke magana
Nan take nadama tazo mata bisa wannan ganganci
vi na fitowa domin yakar wannan halitta.
Tta dai halittar tsan anin mamnki ne yasa ta fito gaba
daya da jikinta domin ta ga tsageria da yazo har inda take
Va ke wannan kuri da cika baki.
Duk iya tsawon shekarun da halittar tayi a cikin
wannan kogi bata ta6a fitowa ba da jikinta gaba daya ba
haka sai a wannan rana. sai dai kawai ta leko da iya kanta,
sai kuma hanayenta da jelarta wadanda take yaki da su.
Bayan balittar ta karewa gimbiya Sulaiza kallo daga
sama har kasa sai ta bushe da mahaukaciyar dariya sannan
t& ce, "Ke karamar halitta, kiyi sani cewa yau shekarata
dari da sittin ke nan ina raye a cikin wannan kogi. Mayaka
da matsafa sun sha yin ayari su zo daga sassan duniya
domin su kawar dani amma sun kasa, sai ke kadai 'yar
mitsitsiya da ke kike ganin za ki iya.
lyayenki da Kakanninki ma sun yi iya kokarinsu sun
kasa. Lallai yau kin bakanta mini raina, domin kece mutum
ta farko da ta fara ganin gaba dayan siffar jikina don haka
Sai na mai da ke abin misali ga sauran bil'adama masu
tsaurin ido da rashin kunya. Yanzu take zan yi filla-filla da
sassan jikinki sannan na ajiye kokon kanki akan tsakiyar
tsaunin da ke cikin wannan kogi domin ya zamo kwanon
shan jinina".
Sa'adda halittar tazo nan a zancenta sai Sulaiza taji
Zuciyarta ta kama tafarfasa. Nan take taji dukkan tsoro ya
kau daga cikin zuicyarta, kawai sai ta tari numfashin
halittar
tana mai daka ma ta tsawa ta ce, "Ai ga fili ga mai
doki, sai mu zuba mu gani ni da ke aga wanda zai yi
nasara",
Koda jin wannan batu sai halittar ta bushe da dariva
sannan ta ce, 'Na sami labarin cewa kece kika kashe
hatsabibiyar macijiya ta cikin kogon sihiri. Tabbas kin yi
dan guntun kokari amma ki sani cewa wannan macijiya da
kika kashe bala'inta da Rarfinta bai kai rabin nawa ba.
Yanzun nan za ki gane kuskurenki.."
Kafin Sulaiza ta budi baki ta kara cewa wani abu tuni
halittar ta shammaceta ta kawo ma ta wawan mangari da
hannu. Cikin tsananin zafin nama Sulaiza ta sunkuya domin
ta kaucewa dukan amma sai da kaifin faratanta ya dara
rigar karfen da ke jikin Sulaiza, ya yi ma ta yanka biyu a
kasan cibiyarta tamkar da takobi aka sareta.
Nan take jini yai tsartuwa, Sulaiza ta kurma ihu
sakamakon tsananin zafi da zogin da taji, tayi tsalle can
gefe daya ta fumu da kasa cikin tsananin galabaita tana mai
dafe raunin.
Koda ganin abinda ya faru sai halittar ta bushe da
dariyar mugunta ta ce, 'Ai dama na gaya miki. Lallai ba zan
yi miki kisan farat đaya ba domin so nake na fara yin kaca-
kaca da sassan jikinki tukunna sannan na kakkarya duk
wata gaba sai kuma na cis-cisgeki har sai na daidaitaki."
Koda gamna fadin hakan sai halittar ta fito gaba daya
daga cikin kogin ta durfafi inda Sulaiza ke kwance tana jan
ciki irin tafiyar maciji.
Nan take nadana tazo mata bisa wannan ganganci da
tayi na fitowa domin yakar wannan halitta.
Ita dai halittar tsananin mamaki ne yasa ta fito gaba
daya da jikinta domin ta ga tsagera da yazo har inda take
ya ke wannan kuri da cika baki.
Duk iya tsawon shekarun da halittar tayi a cikin
wannan kogi bata taba fitowa ba da jikinta gaba daya ba
haka sai a wannan rana, sai dai kawai ta leko da iya kanta,
sai kuma hanayenta da jelarta wadanda take yaki da su.
Bayan halittar ta karewa gimbiya Sulaiza kallo daga
sama har kasa sai ta bushe da mahaukaciyar dariya sannan
ta ce, "Ke karamnar halitta, kiyi sani cewa yau shekarata
dari da sittin ke nan ina raye a cikin wannan kogi. Mayaka
da matsafa sun sha yin ayari su zo daga sassan duniya
domin su kawar dani amma sun kasa, sai ke kadai yar
mitsitsiya da ke kike ganin za ki iya.
Iyayenki da Kakanninki ma sun yi iya kokarinsu sun
kasa. Lallai yau kin bakanta mini raina, domin kece mutum
ta farko da ta fara ganin gaba dayan siffar jikina don haka
sai na mai da ke abin misali ga sauran bil'adama masu
tsaurin ido da rashin kunya. Yanzu take zan yi filla-filla da
sassan jikinki sannan na ajiye kokon kanki akan tsakiyar
tsaunin da ke cikin wannan kogi domin ya zamo kwanon
shan jinina".
Sa'adda halittar tazo nan a Zancenta sai Sulaiza taji
zuciyarta ta kama tafarfasa. Nan take taji dukkan tsoro ya
kau daga cikin zuicyarta, kawai sai ta tari numfashin
Ita kanta muguwar halittar sai da ta cika da tsananin
mamaki bisa ganin irin jarumtakar Suiaiza gamii da
juriyarta da nacinta.
Babu abinda zai fi dada baiwa mutum mamaki face
yadda Sulaiza ta ci gaba da gumuzu bata sAre ba duk da
cewa jini bai daina zuba ba a kasan cibiyarta inda halittar ta
dankara ma ta sara guda biyu da kaifin faratan hannunta.
Abinda ya daurewa halittar kai shi ne, ya ya ita da
take yaki da miliyoyin Dakaru ta karkashesu a lokaci guda
amma yanzu mutum daya jal zai gagareta?
(Kai nima dai AA Misau abin mamaki yake bani)
Lokacin da masifa ta kai mnsifa gumu ya kai gumu,
halittar ta ga ta kasa hallaka Sulaiza sai tayi tunanin cewA
wata kila saboda bata cikin ruwa ne shi yasa karfinta ya
ragu.
Nan take kuwa halittar ta juya da sauri ta kona cikin
kogin Saljus, ai kuwa sai ta ga SulaizA ta biyota a guje,
itama ta daka wawan tsalle ta fada cikin kogin
Nan fa suka fara sabon azababben yaki. ldan halittar
tayi nutso izuwa can karkashin ruwan sai ta ga itama
Sulaiza tayi nutson ta bita ciki sun ci gaba da gumurzu
kamar akan doron kasa suke har izuwa lokaci mai tsawo.
Haka dai suka ci gaba da artabu har izuwa tsawon
wata sa'a gudan a lokacin ne gumurzun nasu yai tsamari
ainun domin kowa ya samo lagon koWa.
Ita dai Sulaiza ta gama gano cewa halittar ko kadan
bata son a taba kanta izuwa wuyanta, amma duk inda
sara ko aka soka a saurań jikin ta ji take yi kamar susa
ake yi ma ta.
Ita kuwa halittar ta gamo cewa idan tana yiwa Sulaiza
luguden duka da hannayenta biyu da kuma jelarta Sulaiza
bata iya maida martani sai dai kokarin kare kai.
A haka ne balittar ta sami nasarar kara yankar Sulaiza
har sau biyu. Yankan farko akan cinyarta ta hagu, yanka na
biyu akan damtsen hannunta na dama.
Koda Saiza taji tsananin zafi da zogi sun shigeta
kuma jini ya fara dibarta sai ta fusata ainun ta shamnmaci
halittar ta dan kara ma ta sara a kumatu.
Take wajen ya yi muguwar darewa jini yai tsartuwa
ya kama kverara a cikin kogin. Kafin a jima gaba dayan
kogin ya rine da jinin halittar.
Koda halittar ta shafa kumatunta taji yadda ya dare
kuma la ga uban jinin da ya zuba daga jikinta sai ta fusata
ainun ta afkawa Sulaiza da dukkan karfinta suka ci gaba da
mummunan yaki.
Koda aka sake jimawa ana wannan gumurzu yamutsi
sai duk su biyun suka shiga cikin mugun hali na jiri da
maye sakamakon jinin da yake ta zuba a jikinsu bai tsaya
ba.
Ana cikin haka ne halittar ta sami nasarar cafko
makoshin Sulaiza da hannunta guda ta shaketa.
Nan take Sulaiza ta fara kokarin mutuwa

ta rinka
ganin taurarin wuya a idanunta.
Tun da Sulaiza ta kori dokinta tun sa'adda ya firgita
dole ne ta shafe wannan tafiya da kafafunta

A Can fadar birnin Lairuf kuwa, hankalin kowa a tashe yake, domin rana na daf da faduwa amma har a
Sannan ba a ga gimbiya Sulaiza ta dawo daga kogin Saljus
ba. Al'amarin da ya dugunzuma hankalin Sarki Huraisu kenan ya kasa zaune da tsayuwa a waje daya, kawai sai ya
kama kai kawo a cikin fadar zuciyarsa cike da tsananin
bakin ciki har ma idanunsa suka ciko da kwalla kamar zai
fashe da kuka.
A wannan lokaci gaba dayan mutanen da ke fadar sun
sunkui da kawunan su kas suna jimami. Wasu ma zubar da
hawaye suke yi domin sun san cewa idan har gimbiya
Sulaiza ta hallaka to fa karshen zaman lafiya da kwanciyar
hankali ya zo a kasar.
Ana cikin tsakiyar wannan hali ne aka jiyo takun
Sawu an shigo fadar. Nan take kowa ya dago da kansa,
kawai sai aka yi arba da gimbiya Sulaiza rike da kan
Wannan muguwar halitta duk jikinta yai jina-jina tana tafiya
da kyar cikin halin maye.
Cikin tsananin farin ciki Sarki Huraisu ya ruga izuwa
gareta a lokacin da fadar ta rude da shewar mutane. Kafin
Sarki Huraisu ya riski Sulaiza tuni ta sume zata fadi kasA
sai yai caraf ya tareta da hannayensa. A gigice Sarki ya
dauki Sulaiza ya ruga da ita izuwa cikin gidan Sarautarsa
Vena mai kwalawa Likitocinsa kira.AA misau ke magana
Sai da Likitocin suka shafe sa'a biyu suna aiki akan Sulaiza
ya zamana cewa har aka gama dinke raunikan
ke jikinta ba ta farfado ba.
A sannan ne hankalin Sarki Huraisu ya dugunzuma
fiye da ko yaushe ya kama kuka, donin a zatonsa Sulaiza
ta mutu ba za ta tashi ba.
Bayan an gama dinke raunikan jikin Sulaiza an shafa
ma ta magani kuma an dura ma ta ruwan maganin a bakinta
da kamar tsiran rabin sa'a sai ta farfado daga dogon suman
da tayi tana mai kiran sunan Abbanta da Ummanta.
Cikin tsananin farin ciki Sarki Huraisu ya sumbaci
goshinta a lokacin da hawaye ke zuba bisa kumatunsa ya
ce, "Gaisheki uwar SADAUKAI! Daga yau kin zama
Sarkin yakin kasa ta."
Ya yin da Sulaiza taji wannan batu sai ta kamu da
tsananin farin ciki ta ce, "Godiya gareka mara adadi ya kai
Abbana. Ina labarin Ummina?"
Koda jin wannan tambaya sai Sarki Huraisu ya yi
murmushi ya ce, "Ai har yanzu banjun da kika zuba ma ta a
cikin abincin da ta ci bai saketa ba, tana nan tana ta shara
barci."
Cikin tsananin mamaki Sulaiza ta dubi Sarki ta cê,
"Ya ya aka yi ka san wannan al'amari?".
Huraisu ya ce,
kuyangin mahaifiyarki domin ni da kaina ne na gano
wannan shiri naki lokacin da na tura a kirawo mini
mahaifiyarki aka gaya mini cewa barci take yi.
"Kada ki zargi daya daga cikin
Tun da na auri mahaifiyarki bata ta6a fashin zuwa
turakata ba ko sau daya sai a jiyan, bisa wannan dalili ne na
tashi da kaina na tafi turakartata. Ai kuwa ina zuwa na
isketa a kwance tana yin barci mai nauyi irin wanda ba
ta6a ganin tayi shi ba.
Koda na shinshina bakinta sai naji warin banju. Na yi
shiru ina tunani sai kawai na yi murmushi domin na gano
cewa aikinki ne, kuma kin yi baka ne don kin san cewa ba
za ta barki ki tafi kogin Saljus ba."
Lokacin da gimbiya Sulaiza ta ji wannan jawabi na
mabaifiyarta sai tayi dariya ta ce, "Tabbas babu wanda ya
karanci halayena sama da ke. Tabbas ko gyaran murya na
yi ka san manufata,"
Da jin haka sai Sarki Huraisu ya yi murmushi ya ce,
"Kin yi gaskiya ya ke 'yata".
Sai da gimbiya Sulaiza ta kwana arba'in tana jinyar
raunikan da ke jikinta sannan ta warke sumul. A ranar da ta
warke ne aka kirawota izuwa fada inda ta ga kan wannan
muguwar halitta ta kogin Saljus rataye a jikin gunkinta
kusa da kan hatsabibiyar macijiya.
Nan take aka yiwa Sulaiza sarautar Sarkin yakin
birnin Lairuf, kuma sai da aka kwana goma sha hudu ana
shagalin bikin nadin sarautar ya zamana cewa ko ina a
kasar birni da kauye mutane na cikin shagali da farin ciki
irin wanda ba a ta6a yin kamnarsa ba.

RANAR da za ayi taron gaba dayan Sarakunan
da ke nahiyar ne bimin Lairuf ya batse da
manyan baki. Kowanne Sarki idan ya zo sai a tarbeshi cikin
girmamawa a kaishi masuakinsa. Amma da Sarki Imsar ya
iso sai aka wuce da shi kai tsaye izuwa fadar Sarki domin
dama Sarki Huraisu ya bayar da umanin hakan.
Sarki Huraisu na zaune bisa karagar mulki Sabirat Da
damansa, a bagunsa kuwa Sarkin yaki ce jaruma Sulaiza
ga fadawa da sauran mutanen gkari sun kewayesu ana ta
tafiyar a harkokin mulki.
Ana cikin wannan hali ne Sarki Imsar ya shigo cikin
fadar rike da hannayen 'ya'yansa biyu gimbiya Lushaira

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment