Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

BABBAN GORO
-------------------------
Littafina daya
.
Part 1A
.
With shuraih 99%
Typing by :- Shuraih Usman
.
Zaku sha karatu har ku gaji
.in naga bakwa respond toh zan ajiye littafina agefe
.
.
Awani zamani can baya anyi wani attajirin sarki wai shi
abul dinar ,wanda matsafa da masu harsashe suka
tabbatarda cewa babu attajiri kamarsa a duniya ,saboda
tarin dukiyar da Allah yabashi wannan sarki yana da
matan aure guda goma sha shida kuma yana da kuyangai
tamanin gabaday wayannan mata nasa babu wadda ta
raba haihuwa sai guda daya ,
Wata mace da ake kira hauziya
Duk acikin matan abul dinar hauziyace yar talakawa
,domin duk sauran daga yayan sarakuna sai yayan mayan
attajirai na duniya
.
A ranar da aka fuskanci hauziya ta sami ciki ,sai sauran
kishiyoyinta suka cika da bakin ciki .
Batare da da bata lokaci ba suka shiga bin hanyoyin da
zasu tabbatar da cewa cikin ya zube ,masu tsafi nayi
,masu surkulle nayi, kai wasu ma kiri kiri a fili sukka ringa
yin abubuwan da zasu sa cikin ya zube amma ubangijin
musulunci shine mai yin yadda yaso ,sai ya kare hauziya
daga sharrin kishiyoyinta .
Shikuwa sarki abul dinar koda yaji cewar hauziya ta sami
ciki , sai yadauki son duniya ya kwallafa a akanta . Domin
zata share masa hawaye a bisa bakin cikin daya addabi
rayuwarsa ta duniya ,wato rashin magaji ,
Dayake ya tabbatar da cewa sauran kishiyoyinta bazasu
kyaleta ba, sai ya dauketa ya kaita wani gidansa dake
bayan gari .
Ya ajiyeta ita kadai ,
Daga ita sai bayi masu yi mata hidima .
Gidan ya zama ba'ashiga da fita ,in ba shi kansa ba .sarki
abul dinar ya tare wajen hauziya , tare suke ta rainon
cikin har wata takwas .
A ranar da cikin ya cika wata takwas da kwana shirin da
biyar .
Ciwon nakuda ya kama hauziya .
Cikin yan dakiku kadan ta haifi sankaceciyar 'ya,
Wadda atun tana jinjiniyar aka tsorata daganin kyawunta.
.
Sannu sannu akayi ta rainon yarinyar wadda aka sawa
suna Mabaruka ,har ta girma .
Ta zama cikakkiyar budurwa ,
Wadda saboda tsananin kyau labarinta ya cika duniya .
Jarumai da matsafa da dama sun hallaka junansu a kan
soyayyarta
.
.
Wata rana gimbiya Mubaruka ta fita rangadi , don
shakatawa cikin wata babbar gona ta mahaifinta ,kuyangi
da barade na take mata baya.
.
Kwatsam sai ga wata katuwar macijiya mai girman gaske ,
ta bayyana a gabansu .
.
Koda ganinta sai barade da kuyangi suka kwalla ihu, suka
ruga baya da gudu ,
.
Baraden nan suka yi ta rige rigen gudu ,sun mance da
aikinsu na tsare lafiyar 'yar sarki .
Ita kuwa mabaruka sai ta tsaya kyam ta kasa gudu , don
tsananin razana , hawayen bankwana da duniya suka
tsiyayo daga idanuwanta .
.
Katuwar macijiyar ta wangame baki zata hadiyeta , kawai
sai mabaruka taga wani bakin bawa yai tsalle ya rungumi
wuyan macijiyar
.
Nan fa suka kama kokawa shi da macijiyar su fadi can su
tashi can.(Ni kaina shuraih sai dana kusan....basai na
karisa ba)
.
Shi yana kokarin ya turmusheta ya rarumi wani icce dake
waje guda ya soketa ita kuma tana kokarin
kannannadeshi ta karairaya kasusuwan jikinsa . Haka dai
suka yi ta dauki ba dadi har tsawon rabin sa'a , macijiyar
nan tai masa fata-fata , duk jikinsa ya rune da jinin
raunuka
Amma hakan bata sa ya saketa ba ,
A hakan dai Allah ya bashi iko , hannunsa ya kai kan
wannan icen cikin zafin nama ya dauki icen ya caka
abakin macijiyar , ya bullo ta tsakiyar kanta .
.
Nan take macijiyar ta sulale ta fadi kasa matacciya,
Shi kuma bawan yafadi kasa a sume .
.
Koda ganin haka sai gimbiya mabaruka ta ruga gareshi ta
rungumeshi tana kuka ,
Gaba daya jikinta ya baci da jininsa .
Ahaka sarki abul dinar da dakarunsa suka zo suka sameta
.
.
Nan da nan aka ban bareta daga jikin bakin bawan , aka
tafi da ita shi kuma aka yayyafa masa ruwa ya farfado
daya ke shi bawa ne marar gata ,
Sai aka tuhumeshi da laifin rungumar 'yar sarki ,
Ba'ama duba sai da ran dayayi ba, dan ceton 'yar sarkin.
.
Saboda haka aka kaishi dakin tuhuma ,aka dauddaureshi
da sarkoki aka yita gana masa azaba iri iri.
.
A iya tunanin Mabaruka wannan bawa ya mutu wannan
dalili shi yasa tai ta kuka har hankalinta ya gushe ta suma
bayan ta farfado ta mike zaune daga kan gadon data ke
kwance ,
Inda tai arba da mahaifiyarta hauziya zaune a gefen
gadon idanunta cike da hwaye .
Koda ganin mikewar mabaruka sai farin ciki ya kama
hauziya.
.
"Mama ina gawar bawan daya ceci rayuwata?"
Mabaruka ta tambaya fuskarta cike da alamun bege
.
"Waya ce miki ya mutu? Ai dogon suma yayi kum, kuma
anzuba masa ruwa ya farfado ,yanzu haka yana can
daure a dakin tuhuma"
.
"Me yayi za'a kaishi dakin tuhuma?"
.
Batare da mabaruka ta saurari karin bayani ba ta mike
tayi waje da gudu ,
Mahaifiyarta tana kira amma taki dawowa , bata tsaya
ako ina ba sai a kofar dakin tuhuma,
Da zuwa ta dakawa masu gadin tsawa tace "su bude mata
kofa kofar "
.
Jikinsu na rawa suka bude kofar ta shiga , inda ta iske shi
kwance magashiyyan cikin jini .
Nan take tasa aka kwance sarkar dake jikinsa , tasa aka
kaisa gidanta inda taimasa wanka ta sama magani a
raunukan jikinsa sannan tasa aka kawo masa abincin
sarauta , ya cika tumbinsa ! Daga nan aka kaishi wani
dakin hutu ya kwanta yai barci, har sai da rana ta fadi
sannan ta shiga dakin ta tashe shi , duk su biyun suka
kurawa juna ido
.
"Yakai wannan jarumi menene sunanka"
.
Bawa yayi murmushi yace "ni sunana Ashwar "
.
"Ya akai kana matsayin bawa a gidanmu na sarauta
amma ban taba ganin kaba ?"
.
Ashwar yasake yin murmushi yace "yake gimbiya kisani
babu yadda za'a yi ki taba ganina , domin tun da aka
haifeni ban taba fitowa ba daga cikin lambun sarki na can
bayan gari sai ayau .
Mahaifina shine bawan dake kula da wancan lambu na
sarki , tun yana saurayi yake wannan bauta harya tsufa ya
mutu , nikuma na gajeshi
Mahaifiyata ma acikin wannan lambu ta rasu yanzu haka
kabarinta na cikin lambun
A yaune sarki ya aika mini naje daya lambun nasa nayi
aiki wanda shine kika ziyarta don rangadi
To ina cikin aikine na hango shigowarku keda kuyangi da
barade .
Kuma sai naga wannan katuwar micijiya ta tarwatsa
kuyanginki da baraden
Duk sun gudu sun barki shi yasa na sai da raina don ceto
rayuwarki".(Ni 99% nace lallai kacika sadauki)
.
.
Koda jin haka mabaruka tai ajiyar zuciya hawayen tausayi
kauna suka zubo mata tace "ya kai Ashwar kasani daga
yau bawani namiji da zan aura in ba kaiba
.
Cikin razana Ashwar yaja da baya ya takure jikinsa ga
bango yace" ranki ya dade ki rufa min asiri , ki tuna fa ni
bawane , bawan ma bakin fata ,ke kuwa gaki balarabiya
'yar sarki,ina ni ina aurenki"
.$
Mabaruka tayi murmushi tace "ai babu ruwan so da
matsayin jinsi ko launi ,idan duk duniya zata taru banga
wanda ya isa ya raba ni dakai ba , abu daya nake so na ji
daga bakinka kawai , kana sona ko baka sona?"
.
"Haba gimbiya ai babu wani namiji da zai ganki yace baya
so , amma ai wutsiyar rakumi tai nesa da kasa kuma
BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE"
.
"Kwarai kuwa"wata murya ta amsa daga bayan su.
.
Mabaruka da ashwar suka dubi bakin kofa a tsorace ,
sukayi arba da sarki Abul dinar fuskarsa a murtuke wasu
kartin barade shida na tsatsaye a bayansa suna muzurai
tamakar saci babu.
.
Cikin fushi ya dubi mabaruka yace "haba gimbiya shin kin
mance da martabar gidannanne ?kin manta da
matsayinki na 'yar sarki ne?har zaki wulakanta kanki ki
dauko bakin bawa ki shigo dashi har cikin gidanki mai
Albarka.
.
Maimakon mabaruka ta nutsu kota firgita da wannan
tambaya sai ta kyalkyale da dariya sannan tace "haba
Abba ka runa fa mahaifiyata ta fito daga dangin talakawa
,me yasa ka aurota har kuka haifeni? Shin baka
tsammanin zubar martabar sarautarka ne? Hakika sone
yasa idanunka suka rufe , tunaninka ya gushe ka manta
da matsayinta......"
.
Cikin hanzari abul dinar ya tari numfashin mabaruka
yace" yata kada ki yi la'akari da wannan , domin inki kai
tunani akwai alaka ta jinsi da jini tsakanina da
mahaifiyarki amma tsakaninki da wannan bakin bawan
babu alakar komai"
.
"Abba ni dai Ashwar nakeso"
(Shuraih 99% ke magana)
.
Wannan bayani ba karamin girgiza Abul dinar yayi ba ,
don tsabar takaici sai da yaji kwalla ta zo masa amma sai
ya juya baya yayi shiru yana tunani , daga can ya juyo ya
dubi mabaruka yace" na amince da niyyarki amma bisa
sharadi "
.
Cikin mamaki mabaruka tace "wane irin sharadi ne?"
.
"Zakiji sharadin gobe da a fada gaban dukkanin jama'a.
.
Nan take sarki ya juya ya fice daga dakin ,barade suka
take masa baya.
.
Ashwar da mabaruka suka dubi juna cikin tsananin
damuwa
.
"Ai daman na san wannan al'amari bazai taba yiwuba ,
nagaya miki cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE"
.
Mabaruka tayi murmushi tace "ashwar ina so ka kalli
cikin kwayar idanuna kaga ya mini abinda ka gani aciki "
.
Ashwar ya kura mata ido har tsawon 'yan dakiku kadan
sannan ya kawar da kai
"Me kagani acikin idanuna?"
"Banga komai ba face digon baki da zagayen fari"
.
"To wannan zagayen farin daka gani ba komai bane face
fadar zuciyata , wannan digon bakin kuwa daka gani guda
daya tilo ba komai bane face kai Ashwar Kai kadai nake so
bazan so wani ba yan kai ,idan kuwa aka aura mini wani
ba kai ba saidai ya zauna da gawata"
.
Haka dai Ashwar da mabaruka sukaci gaba mahawara
yana ta kokarin nuna mata matsala har zuwa gabannin
magariba ,sannan ya tafi gidan gona ita kuma taci gaba
da tunanin hanyar dazata bi ta shawo kan al'amarin .
Wannan shine abin daya faru tsakanin jarumi ashwar da
gimbiya mabaruka .
.
Shuraih ke magana
.
Al'amarin sarki abul dinar kuwa lokacin daya bar gidan
'yarsa mabaruka sai hankalinsa ya dada dugunzuma ya
rasa abinda yake masa dadi aduniya , har ya isa turakarsa
yana cikin wannan hali , ya kasa zauni ko tsaye sai da
dukkanin barorinsa da fadawansa suka fahinci lallai akwai
abin da yake damunsa .
Bayan yayi dogon tunani sai ya tura aka kirawo masa yan
majalisarsa cikin turakarsa daga cikin yan majalisarsa
sarki Abul dinar akwai waziri, galadima ,wambai da
Gulmanu sarkin matsafa na garin.
.
Bayan dukkaninsu sun zauna , sai sarki Abul dinar ya basu
labarin abinda ke faruwa tsakanin 'yarsa mabaruka da
kuma jarumi Ashwar, sannan yace
"Kunsani cewa abin kunya ne ace 'yarmu ta auri bakin
bawa ,tabbas idan akai martabar masarautarmu ta zube ,
sauran kasashe ma dake makwataka damu sai sunzage
mu sun raina mu ku sani idan muka sanar da mabaruja
kuru-kuru cewa ba zamu amince ta auri ashwar ba ,
tabbas zata iya hallaka kanta, nidai nace da ita zan bata
shi amma bisa sharadi ,sharadin kuma nace sai gobe da
safe zan tara jama'ar gari na fadi a gabansu .
.
Toh ku sani sharadin nan fa ni kaina ban san shi ba ,
wannan shine dalilin dayasa na tara ku anan, inaso muyi
tunani mai zurfi mu kafawa ashwar sharadin nemo wani
abu mai tsananin wuyar samu a duniyar nan, wanda a
sakamakon neman sa ma zai hallaka in yaso kun ga dole
mabaruka ta rungumi kaddara"
.
Yayin da 'yan majalisa suka ji wannan bayani na sarki
abul dinar sai duk suakayi shiru suka shiga tunani aka
rasa wanda zaice kala , har ya zuwa wani lokaci daga can
sai gulmanu sarkin matsafa ya mike yace
.
"Ya sarkin sarajkai hakika ni ina da mafita akan wannan
al'amari kuma na rantse da wata sharadin da zan dora
Ashwar akai bai is ya haye shi ba ina so ku yi hakurin jin
wannan sharadi har zuwa gobe da safe "
.
Koda abul dinar yaji wannan batu sai fuskarsa ta fadada
da murmushi yace na yarda dakai sarkin matsafan
duniya gulmanu , shikenan na sallameku, kowa ya tafi
gida sai gobe da safe mu hadu a kofar fada
.
Nan take 'yan majalisa suka watse batare da wani daga
cikinsu yace kala ba aka bar sarki acikin dumbin farinciki
.
Birnin sarwaliya babbar garine mai tsohon tarihi ,wanda
a halinm yanzu sarki abul dinar yake sarauta a cikinsa
gaba daya al'ummar farin ma'abota Addinin bautar wata
ne , duk sa'adda wata ya cikja kwana goma sha biyu gaba
dayansu maza da mata yara da manya sukan fito tsakar
dare , suyi sujjada ga watan suna masu fadin bukatunsu
da rokon gafarar kurakuransu, wannan abu ne wanda ya
yi matukar tasiri zukatunsu
.
Bayan sarki yagama shawara da yan majalisarsa sai yasa
akayita shela da yekuwa aka sanar da jama'ar gari cewar
gobe da safe ana gaiyatar kowa a fada ba ayafewa ko da
yara ba . Masu shela basu daina sanarwa ba har sai da
dare yayi , sannan suka je suka kwanta.
.
Shuraih 99% ke magana
.
Kashe gari jama'a sukayi ta tururuwa suna zuwa fada
kungiya kungiya ,ayari ayari ,har daga kauyuka,kai wasu
ma saga makotan kasashe sai da suka zo don son ganin
kwakwaf,saboda labari ya bazu cewa akan maganar 'yar
sarki ne da bakin bawan data nace tanaso.
A cikin wadanda suka halicci wannan taron akwai wasu
jarumai kimanin su shida masoya mabaruka , wadanda
suma ashirye suke dasu salwantar da rayuwars son ganin
sun sami aurenta.
.
Bayan sarki abul dinar da'yan majalisarsa sun hallara , sai
aka tura wani bafade yaje yakira ashwar daga gidan gona
. A sannan ne gimbiya mabaruka ta iso tare da kuyanginta
da baradenta , nan take taje ta zauna bisa kujerar dake
daf da karagar sarki ,
Sarki ya dubeta yai murmushi .
Hakan keda wuya kuma sai ga ashwar tare da da bafajen
da aka aika ya kirawo shi sun iso, da zuwa aswar ya fito
tsakiyar filin fada , ya fadi yayi gaisuwa ga sarki , bayan an
amsa gaisuwar ne aka yi masa izinin mikewa tsaye , yana
mikewa ne yayi ido biyu da abar begensa tana mai yi
masa wani irni murmushi mai tona asirin zuciya .
Cikin karfin hali ashwar ya yiwa mabaruka murmushi ,
sannan ya kau da kai ga barin kallonta don tsoron kada
tsananin kyawunta ya rinjayi zuciyarsa ya kamu da sonta
.
Tun daga ranar da ashwar ya fahimci cewa gimbiya
mabaruka na sonsa , tsoro da damuwa suka cika
zuciyarsa .
Badon komai ba sai don ya tabbatar mahaifinta ba zai
maraba dashi ba , wannan dalili yasa ya danne sha'awar
bege da so a zuciyarshi ,har a halin yanzu ashwar bai
yadda son mabaruka ya shige shi ba , kai in ba don ma
bin umarnin sarki ba da tabbas ba zaizo wannan kira da
akayi masa ba.
.
.
A cikin wannan gona ta sarki wadda ashwar ki aiki , akwai
wani dattijo abokin aikinsa wanda ake kira makabul.
Makabul tsohone sosai , domin shekarunsa sun kai
kimanin tamanin da doriya . Makabul aminin baban
ashwar ne , don asali ma tare aka siyo su a matsayin bayi
daga nahiyar kasar bakaken fata,
Tun suna samari yan shekara sha tara.
Tun ashwar na yaro karami ya taso yake ganin abotar da
ke tsakanin mahaifinsa da makabul, don haka bayan
rasuwar mahaifinsa sai ya rike makabul tamkar
mahaifinsa komai zaiyi sai ya shawarce shi . Yanzu
hakama makabul dinne yabashi shawarar yazo fada don
amsa kiran sarki kuma yace dashi kome aka bukaci da
yayi akan mabaruka kada yaji tsoron komai ya amsa
cewar zaiyi, komai wahalar al'amarin. Koda ashwar ya
tambayi makabul dalilin da yasa yace ya sai da ransa.
.
Sai yace dashi" tun mahaifinka nada rai mun taba zuwa
wajen wani boka wanda yayi bincike akan ka , bokan ya
sanar damu cewa zaka shahara a duniya , kuma zaka auri
'yar sarki, amma sai ka karbi Addinin musulunci
.
Koda jin wannan batu sai ashwar yayi shiru yana tunani
daga can yace" kai baba makabul yanzu a ina zan sami
ma'abocin wannnan addinin daka fadi? Kasani cewa babu
masanan sa anan garin dakuma kasa shen kewayenmu"
.
Makabul yayi murmushi yace "kada ka damu akwai tafiya
da zakayi tabbas zaka hadu da ma'abota Addinin
musulunci,da zarar kun hadu ka karbi Addinin, in da
rabon mu ma zaka dawo gida ka sanar damu wannan
Addini mu karbe shi, don tabbas shine Addinin gaskiya ,
amma kiri kiri sarakunanmu sun ki shi don kwadayin
duniya , da son mulkinsu na kama karya "
.
,
Duk wannan hira ta wakana ne adaren jiya tsakanin
ashwar da makabul.
.
Yayin da ashwar ya karbi umarnin mikewa tsaye gaban
sarki a tsakiyar fada, sai sarki Abul dinar da sarkin
matsafa gulmanu suka dubi juna , nan take gulmanu ya
mike tsaye , yayi gaisuwa ga jama'ar gari sannan yace
.
"Yaku al'ummar sarwaliya kun sani cewa sarkinmu ya
dade da rashin samun haihuwa sai bayan shekara da
shekaru ya sami mabaruka,
Yau gashi Allah ya yarata takai mun zalin aure, ku sani
cewa 'ya'yan sarakuna jarumai, da mtsafa sunzo da yawa
ba adadi sun nemi aurenta , amma basu samu ba saboda
tace bata sonsu .
To yau an wayi gari gimbiya mabaruka ta budi baki ta fadi
wanda takeso ,kuma bawani bane face bakin bawannan
dake tsaye agabanku wato ashwar"
.
Nan fada ta rude da hayaniya sai da aka yi tsawa sannan
kowa ya yi shiru.
.
Boka gulmanu yaci gaba da cewa " to mu muna da
ka'idoji a wannan masaruta ta mu muna kafin mu aurar
da yar mu duk wanda zai auri 'yar sarauta dolene ya
kasance daya cikin uku, abu na farko shine sai ya
kasance. Mashahurin mai arziki , abu na biyu dole ne ya
kasance dan sarauta , abu na uku dolene ya zama
jarumin da yayi mashahuriyar jarumtaka a duniya . Kun
sani cewa wannan saurayi ashwar dake tsaye a gabanku
bai kasance cikin daya daga cikin wadannan ka'idoji dana
lissafa ba saboda haka yanzu dama daya gareshi dole ne
yaci jarabawar da zamu yi masa akan jarumta , indai yaci
wannan jarabawar to zamu amince mu aura masa
gimbiya mabaruka"
.
.
Ehem shuraih 99% ke magana muje zuwa
.
Koda jama'a sukaji wannan batu sai akayi shiru kai kace
mutuwa ce ta gifta ,
Kowa ya kasa kunne don yaji wace irin jarabawa ce za'ayi
wa jarimi ashwar.
.
Boka gulmanu yayi shiru zuwa 'yan dakiku kadan sannan
ya nisa yace"Abin da muke so ashwar yayi don mu
tabbatar da jarumtakarsa shine , munasa kaje birnin
Duma ka shiga fadar sarkin Aljanu kifyan, ka dauko mana
Bishmalu dan sarkin Misra wanda tun yana jariri sarki
sarki Kifyan ya sace shi, ahalin yanzu Bishmalu ya cika
shekara ashirin da biyar. A duniya .
Kasani indai kayi nasarar dauko Bishmalu , sarkin Misra
yayi alkawarin zai raba kasarsa biyu yabaka Rabi , mu
kuma take zamu aura maka gimbiya mabaruka , kaga ka
jefi tsuntsu biyu da dutse guda kenan wato ga sarauta ga
auren 'yarsarki
.
Boka gulmanu na gama wannan jawabi fada ta sake
rudewa da hayaniya, kowa na cewa wannan aikora da
haline , dan tabbas an san cewa babu wani mahaluki daya
isa yaje birnin Duma don gari ne na Aljanu zalla , Aljanun
ma bakake mazalunta kuma kafirai, sarkinsu kifyan shine
ubangijinsu don shi suke bautawa.
.
Ragowar jaruman nan guda shida , wadanda suka zo da
niyyar sallama rayuwarsu son aurar Gimbiya mabaruka
sai duk suka zare jikkunansu suka boye a cikin jama'a
don sun tabbatar da cewa ba zasu iya cin wannan
jarabawa ba, dominn labari ya bazu ko'ina a duniya cikin
wannan zamani cewar sakin Aljanu kifyan ya zama gagara
badau, ya Addabi dukkan aljanu da bil'adama dake doron
kasa.
.
Littafin :- king of Adventure stories(Abdulaziz sani
madakin gini)
.
.
WANE NE BISHMALU
.
YA AKAI SArKIN ALJANU KiFYAN YA SACESHI
.
SHIN AShWAR ZAI YADDA YA AMINCE DA WANNAN
JARABAWAR
.
IN MA YA AMINCE SHIN ZAI SaMU NASARAR DAUKO
BiSHMALU DAGA FADAN SARKI KIFYAN
.
.
Domin jin wayannan amsoshi sai ku tareni a babbar goro
part 1 B
.
.
ώяįттєй άηđ ρðšтєđ вч
Shuraih Usman
νįά● Shuraih 99%
Fðя мðяє
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%
ℓįкє : Shuraih 99%

Domin dauko/download na Ebook din wannan littafi dama wasu littatafan sai ku ziyarci shafinmu akan adireshi
www.hausaebooks.cfBABBAN GORO
.
Littafina daya (1)
Part 1B
.
With shuraih 99%
Typing by Shuraih Usman
.
Sarki abul dinar ya mike tsaye da kansa ya daka tsawa
, nan take akayi tsit.
.
Sarki ya dubi ashwar cikin murmushi yace" ya kai
ashwar kaji jarabawar dake gabanka shin zaka iya ?"
.
Gaba daya idanun jama'a suka zubo kan ashwar.
Ashwar yayi shiru yana kallon jama'a har idanunsa
suka kai kan gimbiya, inda ta mike zumbur tana mai
kokarin tace ya amsa, amma sai ya da kansa ya dubi
tsho makabul, nan take makabul yayi masa inkiya ya
amsa.
.
"Ran sarki ya dade na amince da wannan jarabawa ,
kuma nayi alkawarin zan zo da bishmalu dan sarkin
misra cikin wannan fada taka"
.
Cikin tsananin farin ciki ta daka tsalle sama sannan ta
rugo da gudu ta rungume ashwar agaban jama'a ,
nan take fada ta sake rudewa da hayaniya ,
Sarki da 'yan majalisarsa suka mike suka shiga cikin
gidan sarauta ,
Ita kuma gimbiya sai ta tafi da ashwar izuwa gidanta .
Surutai iri iri daga bakin jama'ar gari suka yawaita.
Wasu suce hakika ashwar mahaukacine, wasu kuwa
suce yarinta ce ta dibeshi yayi wauta, wasu ma har
zuwa sukai suna yiwa tsoho makabul ta'aziya suna
cewa"dan ka ya zama gawa"
.
Shi kuma sai dai yayi murmushi kawai agaresu su tafi
suna gulmarsa.
.
Farin ciki wajen gimbiya mabaruka a wannan rana
yafi karfin misaltuwa .
Nan take tasa aka shiryawa ashwar walima ta
musamman , inda kuyanginta suka shiga hidimar
girke girke .
.
Cikin kankanin lokaci aka samar da abinci iri iri da
ababan sha kala kala .wannan walima an yi tane
awani daki ta musamman cikin gidan gimbiya
mabaruka ,
Kuma ba'a gaiyaci kowa ba face ashwar shi kadai, sai
kuma abar begensa wato gimbiya , ma'ana su biyu
kadai.
Suka zauna karkashin wani dogon tebur mai dauke da
kujeru hamsin, akan wannan tebur aka shirya
dukkanin wannan abincin da ababan sha bisa farantai
, akan kowane faranti akwai kuyanga tsaye rike da
cokali , da zarar gimbiya ta bukaci abincin sai
kuyangar ta garzayo ta kawo, ta zuba a cikin wani
babban faranti dake gabansu ita da ashwar anan fa
mabaruka ta nuna tsantsar soyayyarta ga ashwar
domin da hannunta ta dunga bashi abincin yana ci ,
ganin haka shima sai ya dunga ciyar da ita da
hannunsa, har suka ci suka koshi.
.
Nan take mabaruka ta kama hannun ashwar ta kaishi
cikin falonta inda take saukar manyan baki suka
zauna. Dayake ashwar bai sa ba da ko'ina ba in ba
gidan gona ba ,sai ya zama dan kauye yayi ta kalle
kalle a cikin falon
.
Mabaruka ta bushe da dariya tace"haba masoyina ya
zaka dunga kalle-kalle kamar wanda ya fito daga
kauye.
.
Wannan batu yasa ashwar yayi murmushi yace "ranki
ya dade dolene ki ga kauyanci a tare dani domin
tunda aka haifeni a cikin gidan gona na ke rayuwata ,
ban taba shigowa cikin gari ba sai ranar dana hadu
da ke , hatta sa'adda aka kaini dakin tuhuma
hankalina ya gushe ban taba shiga wajen ba sai a
ranar. Hakika kece sanadin shigowata cikin Al,umma ,
tun tasowata ban san komai ba face bauta da biyayya
ga sarki abin dana ga iyayena nayi , ban san sanya
sutura mai kyau ba irin wadda nake gani yanzu ajikin
su, bansan kwanciya ba akan shimfida sai ciyawa da
harawar doki.tabbas kin sauya komai na rayuwata
bazan taba mancewa dake ba "
.
Yayin da ashwar yazo nan a zancensa sai ya ga
idanun gimbiya mabaruka ya ciko da kwalla , nan da
nan hawaye ya fara zuba bisa kuma tunta .
Wannan yasa hankalin ashwar ya tashi, yadan matsa
kusa da ita ya durkusa bisa guiwowinsa cikin
kaskantar da kai yace
.$
"Ya shugabata ki yimin gafara idan

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

Please Login or Register in order to submit comment