Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kyaleta da rashin kunyarta da gadara gami da takama gashi ita kuma ba "yar gidan kowa ba!




Da kyar bushira ta hangi Sarki! Daga can nesa sai ta riqa mamakin ganinshi jin Balaraba nace da ita ae yaro ne Lallai Balaraba da son girma take cikin zuciyarta tace gaskiya yana da kyau wai!! Dole yaji dakanshi duk da cewa bai fiye haske ba amma kalar fatarshi abin kwatance ce ga wani uban saje da yabi ya kewaye fuskarshi a tsare hade da mitsitsin bakinshi idonshi Manya farare tas dasu sun Dan risina kadan bazaka taba gane girmansu ba sai ya bude masu duka Amma idan ka kalli saman fatar idonshi zaka gane yana da Manyan idanuwa a sabila da dimun'da'iman idan nashi a lumshe yake ba yadda ya bude su sabida shi kanshi yasan Allah yayi masa baiwarsu .



Tun kan ta karaso gurin Balaraba take zabga mata harara tace"wallahi Sam Sam ba kuyi ba kun zubar mana da qima kuna mata kuriqa rububin zuwa kallon wancan waishi Dan sarki Mtssss Wallahi babu da Namijin da zanyiwa wannan rawar jikin ba'a haifeshi ba tafada a zafafe tanaji tamkar taje ta gaggaurawa matan dake rububin zuwa ganin shi.




Kallonta Bushira tayi tana Mamakin Balarabar da yadda ta dauki kanta ita ba "yar kowa ba I dillalin kashi.


Tace"laifi ne Dan munje ke tunda bazaki ba ae shikkenan ,humm gaskiya ya hadu duk da banganshi sosai ba tabbas nasan yana da mugun kyau.



Tsaki Balaraba taja tace kyawunshi din baza bai dameni ba ni nan Sam Sam kyauwun wani Namji bazai rude ni ba ko wata sarautarsa tafada tana girgiza jiki gami da ji da kanta



Dariya Bushira tayi kadan tace" Wallahi wannan Abinda kekeyi yana mutukar bani Mamaki wai ko Dan kinga kina da kyau ne?


Banza Balaraba tayi mata tana hura hanci!



Bushira tacigaba dacewa Dan kinsan bazaki taba samun kamarshi bane a matsayin Miji shiyasa kike ta wannan Abin"



"Wani kallon Tara shaura kwata Balaraba tayiwa bushira tana ya mutse Fuska tace " Billahillazi kika sake yimin wannan Furucin sai na fasa miki baki ae kin San zan iya ko"!





*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_


*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€




*✍🏻Written by*
_*Binta Umar*_
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


~*MRS AHAMAD GWADABE*~




_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA DARI BIYU IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_
08089965176



*πŸ…Ώ6*


Bushira tace"idan baki fasa basa min baki ba kya tsoran Allah Mtss ke daga anyi magana sai kiriqa nunawa mutane gadara Aikin kawai!


Shiru Balaraba tayi mata ganin rantaya baci Sam bata son bacin ran Bushiran sabida ita kadai ce ta iya zama da ita take jure halinta ,tace"Ai sai ki shige mutafi ni wallahi nagaji da tsayuwar gurin nan wai sai yaushe za'a tashi tunda dai Maimartaba ya tafi ba shikkenan ba kowa sai ya yi nasa guri" Tafada tana wani daga kai!



"Sai dai ke kiyi tafi Amma ni bazan biki ba ke kullum ba kya gudun Abin Magana duk da halinki Amma haka A ka karramaki gurin nan gashi kina nema ki watsawa mutane qasa a ido"Bushiran tafada tana dauke kai daga kanta


Gaba tayi kawai ta kyaleta tsaye a gurin tace "Sai kin tawo ae wallahi bazan zauna ina bata lokaci Na ba kinsan su Sadiya nacan A takure babu Mai basu Abinc......kafin ta karasa Sallau ya tari gabanta Cikin yaqe yace"diyata yarinyar Albarka ina Alfahari dake"



Gabanta ya fadi!! Sai ta dake tace"Kawu Ashe kazo gurin saukar banganka ba sai yanzu"



Washe hakoransa yayi yace"ae nazu tuntuni a gaban idona Maimartaba ya fito duk ina kallonshi har ya koma cikin gida yafada yana ta dariya Mara dalili domin kana ganin yadda yakeyi kasan karfin hali kawai yake



"Allah sarki Kawu wato kazo Ashe Amma kanajin lokacin da Maimartaba yake fadin ina waliyyina yake yafito domin ya karbar min kyautittika Na kayi shiro ko? Tana sane tayi mashi Magana domin taga Halin da zai shiga sanin da tayi basu da Makiyi sama dashi da iyalinshi duk da yana Amatsayin wan Mahaifinta.


Duk sai ya diririce Sabida yasan yarinyar "yar zafin kai ce duk da cewar bata masa rashin kunya Amma yana shakkar ta yasan kallonsa kawai takeyi gashi shi kullum nuna mata yake Ubanta ne shi tunda ba ran Mahaifinta, Amma duk wani hakkinta yakasa daukewa Asali ma da hadin bakinsa A ke muzguna musu a gidan ita da "yan Uwanta.


Sai ya hau dudduba jikinsa yace"dube ni fa Balaraba babu sutturar Arziqi kunya nakeji shiyasa ban fito ba"yafada bakinshi na rawa kai daganin yadda ya yi maganar kasan tsari ne kawai da Rashin gaskiya


Bata ce komai ba kawai ta hau duba kayan jikinshi.


Tace"Kawu kenan kowa ae da sandar hannunsa yake kai duka maye laifin tufafinka yanzu gaskiya banji dadi ba wallahi ni kai dai a guri kowa da "yan Uwanshi da iyayenshi ban dani duk su Kawu Habu da Kawu Maman da Kawu Salisu babu Wanda yazo gurin
Harsu Safiya da Mabaruka ma haka ai shikkenan tafada tana daga kafada ,



Duk sai ya rasa Abin fada Sabida babu gaskiya yace"kin San wa "yan nan basa son Zumunchi kowane shege sai yace kasuwa zai tafi su kuma su Safiya da kike magana a kan su kin sansu da shegen son kudi kamar jaraba suna can suna Aikin A wara da kulelensu kamar ko da yaushe"

"To Kawu ina Uwa da Iya su mai yasa basu zo ba? Tafada domin taji mai zai ce domin tasan bata bakinta takeyi sabida tasan bazuwa zasuyi ba Lokacin da sukaji Labarin saukar cewa suka dinga yi ae saukar zuqu ce wannan.

Yace "ke ma dai Balaraba kin san wa"yannan tsinannun Matan baza su zo ba su Neman kudinsu ya fiye musu komai ki rabu da waddanan "yan hassadar ,yafada yana kokarin karbar Allon hannunta gami da kyautitikan hankalinshi na kan Mukkalan gidan da shagon sai faman washe baki yakeyi





*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻Written by*
*Binta Umar*
~*MAMAN ABDUL WAHABU*~


*MRS AHAMAD GWADABE*


_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE NAIRA 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_
08089965176


*πŸ…Ώ7*


_Bissimillahi_



Sakar mishi tayi tana bin shi da kallo ganin yadda jikinshi yake rawa Humm Kawu kenan tariga ta Fahimchi Abinda yake wa

Yace"Diyar Albarka gaskiya ina Alfahari dake da Dan Uwana Ayuba da ya hafeki Allah yajikanshi ya gafarta masa


"Ameen Balaraba tace taci gaba dacewa Kawu Naji kayiwa babanmu Addu'a banda Mamana"


Bata Fuska Kawu yayi yace "Allah yajikanta itama daga haka yaja bakinshi yayi shiru ita tarasa wace irin qiyyaya Kawu yakewa Mama ta duk da bata raye.



Yace"ae sai mutafi ko gaskiya naji Farin ciki sosai Balaraba zakije Makka Aikin Hajji mu Na zaune,


Dariya tayi tace "Kawu kenan kar kadamu Nabar maka kaje kai kawai Tafada babu damuwa tattare da'ita.



Wani farin ciki ne ya ziyarce shi A zucci yace "ja'ira mai kama da tsohowar Karuwa ae ko baki bani ba baki isa kije Makka ba in dai INA raye a doran duniyar nan.


A zahiri kuwa yariqa washe baki tamkar me sai shi mata Albarka yake kamar babu gobe.



Jin shi kawai Balaraba takeyi domin tafi kowa sanin waye Kawu.

Haka suka ran kaya suka nufi gida Kawu sai hirarraki yake mata Na babu gyara babu dalili.



Wani gida Nafara hangowa cikin wani surqoqin lungu Wanda kwatoci sukayi wa yawa gasunan duk sun bi hanya babu kyawun gani gefe ga tarin bola da tarkace da wata tsiya ce yara duk sun Tara kayan gwangwan da Alama yaran Layin suna fita Sana'ar gwangwan domin ga Alamu nan tarin robobin qarafuna da buhunhuna.



Haka sukai ta tsallake shirgin gurin Kafin su shiga cikin gidan da babu kofar arziqi duk ta lauye ko tsayuwa batayi da kafarta sai an kare da dotse ko kujera,Kawu sai zage zage take yi kafin ya shiga gidan fadi yake shegu tsinannu "yayan Allah bani duk sun zo sun cika mana layi da kayan sata "yan iskan yara kawai"


Wani kallo Balaraba taiwa Kawun Mai kama da Harara tace"Haba Kawu wannan zage zagen bashi da Amfani Shiyasa suka rai naka ina ruwanka dasu ,sai La'antarsu kake yi ta'ina zasuyi Albarka kar ka Manta fa harda su Babaye da Walidi cikinsu shikkenan tunda ka hadasu ka zage babu ta yadda zasuyi Albarka ,Neman halak dinsu sukeyi yafi suje su dauki Na wani " ta qarashe maganar Cikin bacin rai!


Gyaran Murya yayi ko kunya babu domin shi yanzu lallaba Balaraban yakeyi so yake ya kwace mata duk Abinda ta samu gurin saukar.
Yace"Rabu dasu diyar Albarka kinji ko shige muje ciki Ae ke kaman Dan Uwana yayi sa'ar Haihuwa ba wa"yannan "yan iskan ba"

Yaran dake gurin suka kwashe da dariya suna nunashi da hannu domin dai dama yaran duk sun rai nashi sakamakon zubar da Mutunchin shi da yakeyi gurin in sunje gwangwan dinsu sun dawo yabi yana kar6e musu kudi.

Balaraba taja tsaki ta shige ta barshi gurin tace"ae kaga Abinda nake gudar maka nan gashinan sun mai da kai mahaukaci"


Walidi ne yafito a guje su ka ci karo da Balaraba yayi mata wata bangaza tamkar zai yadda ita kasa,yayi gaba ko saurararta bai yi ba.

Da sauri ta jawo hannunsa ta zabga Masa Marika hagu da dama tace" Dan Uwarka ni sa'arka ce zaka bangaje ni ka huce ko kallo ban isheka ba ko ka ga INA shiga sabgarku ne"?


Kuka Walidi yafashe dashi yayi cikin gida da gudu yana cewa"Allah ya isa ban yafe ba Shegiya "yar Karuwa"



Wani Bacin rai! Ya dirar wa Balaraba tayi cikin gidan A fusace yau sai taga da Wanda walidi yake taqama Lallai yau za'ayi rigima gidan nan domin tagaji da irin cin zarafin da yaran suke mata.


Da sauri Kawu yabi bayansu yana zagin Walidi ta Uwa ta Uwa ba


Uwa" Na zaune kan kujera "yar tsuguno tana wanki dake sana'ar tace kenan wankau Walidi ya shigo yana burara ihu tamkar Wanda a ka yanka ,Sai tambayarsa take menene da qyar yace waccan "yar karuwar ce ra mareni hagu da dama inaji ma ido na yafashe yafada tana rintse ido daya cikin sharri


Cikin Sababi! Da tashin Hankali! Uwa ta Mike tana gyara daurin zaninta tace "Lallai Yau zaci kambu a gidan nan Wallahi tallahi bazan lamunci wata "yar iska ta riqa dakar Min "yaya ba bara ta shigo inji meye dalil......kafin ta karasa tajiyo Muryar Kawu yana ta Surfawa Walidi zagi!
Abin Mamaki!




*BINTA UMAR ABBALE*



_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*


πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
[04/05, 02:52] +234 808 996 5176: πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻writting by*
*Binta Umar*
_*MAMAN ABUDL WAHABU*_


*MRS AHAMAD GWADABE*


_*WANNAN BOOK DIN NA SIYARWA NE 200 IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN*_



*πŸ…Ώ8*


"Yau kuma da Abinda kashigo da shi kenan Malam me walidi yayi maka kake ta surfa masa zagi haka? Kar dai a ce tarewa mutsiyaciyar yarinyar nan kake Balaraba"
Tafada tana nuna Balaraba dake jikin rijiya tana kallonta.



Kawu ya gyara tsayuwa gami da riqe Abubuwan dake hannunsa da kyau ,ya kalli "Uwa yace"Laifi ne Dan Na tare mata Yarinyar kirki haka ka wai kin bata yaranki kin sangar tasu basa ganin kowa da mutumchi a gidan nan yanzu a ce kamar Balaraba ita Walidi zai zage yayi ta zagi kina kallonshi kice in yi shiru"


Mugun Mamaki ne ya kama Uwa jin Abinda Kawu yake fada Lallai a kwai lauje cikin nadi kawun da yake zama a zagi Balaraba da ita da iyayenta da qannenta yau shine yake tare mata fada.

Ta gyara tsayuwa gami da gyara daurin dankwalinta ta kalli kawun tace Au! Ashe kai ma tafara baka cin hanci cewa zakayi kafara cin kudin zina da sata
Tafada tana wani girgiza jiki cike da Neman fitina,



Kifta mata ido Kawu yayi ganin har ta hasala

Duk Balaraba Na kallonshi.

Aiko dake "Uwa tasan Halin Mijinta nan da nan ta dago Abinda yake nufi kifta mata idon da yayi
[04/05, 02:54] +234 808 996 5176: πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻writting By*
*Binta Umar*
_*MAMAN ABDUL WAHABU*_



*πŸ…Ώ9*


"Ke kuwa Uwa wane irin Abu mai muni yarinyar nan tayi miki ? Kike jifan ta da Mummunan Al'kaba'i haka me yayi zafi kema fa kin haifa"
Iya take fada bayan fitowarta daga dakin ta tana tsaye ruqe da ha6a tana kallon Uwa cikin Mamaki

Kafin Uwa tace komai sai gasu Mabaruka sun shigo a guje ko wanne hannushi ruqe da Farin botiki Wanda suke zuba Awarar da suke Siyarwa da kwai suna kaiwa kasuwanni

Sai wasan banza suke suna dariya kamar wasu shashashai ko wacce taci janbaki gami da wani katon A cuci a kawunansu.


Sai suka tsaya ganin Iyayen nasu a tsaye dagani Fada a keyi.


Uwa tace "Yawwa "yayan Albarka dama tunda naji shiru nace Lallai yau Awara zata qare Allah dai yayi muku Albarka Ya Baku miji nagari duk Dan bakinciki sai ya mutu ehe!!
Tafada tana kallon gefan da Iya ke tsaye tana kallonsu,


Shamsiyya tace"wai meye ne ? Naga duk kunyi wani cirko cirko tafada tanawa Balaraba Wani Dan iskan kallo.


Uwa tace"Wannan mai ido a tsakar kan ce take zagina bay an ta mari Walidi shine babanku yake cewa wai laifin walidi ne kan nayi mata magana Shine yar Ubanta tafito zata tare mata .
Tafada gami da zama kan kujerar da tatashi ta ciga da wankinta tana sakin habaici ga Iya.
Mabaruka ta kalli Kawu sallau Mahaifinsu ,Cikin Raini da rashin kunya tace "Haba Kawu yanzu har ka fi son bare da Jininka yanzu a gabanka wannan jakar! Take zagin Maihafiyarmu baka ce komai iyi!? Kawai sai ta aje botikin Awarar a Fusace tayi kan Balaraba gadan gadan!

Dama sun saba dambe Dan su Shamsiyya basu da Hankali in dai Abu ya hadaka dasu Abu kadan sai a fara dambatuwa.

Balaraba tayi saurin kaucewa daga jikin rijiya ta tari Shamsiyya tun kafin ta karaso suka kacame da kokawa Abin Mamaki!!

Mabaruka tafara daukar Abubuwa tana dukan Balarabar dashi ganin ta kayar da Shamsiyya tana duka .
Sai dura mata Ashar Mabaruka take ta Uwa ta Uba.

Iya ta shiga tsakani tana rabawa gami da ruqe Balaraba Amma Ina!! Balaraba taqi rukuwa domin dama in tai zuciya fadanta baya rabuwa.

Shiko Kawu sallau barin gurin yayi yana tsitstsinewa su Shamsiyya a zuciyarsa domin babu Halin yayi a fili sabida tsoran Masifar Uwa.


Uwa dataga Ana cutar "yarta sai kawai ta daga ruwan daudar da take wanki dashi cikin roba ta kwararawa Balaraba a jiki tundaga tsakiyar kanta har zuwa qafarta tana ta zabga Mata zagi gami da mugun fata!!


Da kyar Iya ta janye Balaraba daga kan shamsiyya tana bata hakuri gami da yi mata Fada,


Shamsiyya da tasamu ta mike sai taciga ba da zagin Balaraba tana jin fan ta da kwanonisu Na cin Abinci Wanda suke gefe Dan qazanta har yanzu ba'a wanke ba qudaje sai bi suke gami da ruwan wanki da Uwa ! take kwara musu


Har tasamu nasar jifanta a kanta gurin ya tasa ,cewa"take Wallahi sai naga bayanki Dan Uwarki karuwa Uwar tamu zaki dinga zagi shegiya wacce ba'a san Asalinta ba"


Bakinci tamkar ya kashe Balaraba sai tafashe da kuka, a gurin su Sadiya da Shamsu kannanta suna taya dawowarsu kenan daga makarantar Allo,yara duk sun cika gidan,


Iya ta janye Balaraba ta kai ta dakinta tana rarrashi tace"ko da yaushe ina fada miki ki daina Daka ta tasu Mabaruka su ba hankali garesu ba gashi yau a cikin farin ciki kike kinyi saukar Alku'ani mai girma Amma zaki bata wayonki Dan Allah ki daina kulasu.



Cikin kuka tace"iya kinajin zagin da suke min fa wai mai Na tsarewa Uwa ita da yaranta suka tsane ni ,nifa basa bani ci basa bani sha komai bi nakewa kaina ni nake fita in nema in ciyar da kaina da kannena to gaskiya nagaji zan siyar da gado Na kawai in bar musu gidan gwara inje in kama haya sai yafi min"


"Aa Balaraba kina nufin zaman kanki zakiyi bazai yihuba dama yaya Lafiyar kura kullum cikin yi miki sharri suke duk Wanda yaji cewar kin gama daki shikkenan sai zancensu ya tabbata ,ki kara hakuri kinji ko kwana nawane zaki yi Aurenki .



"Aa Iya ki kyaleni kawai "tafada tana share hawaye.


Iya tace"Aiko bazan kyaleki ba Balaraba yin hakan yana nuna cewar cin Amanar Dan Uwana Ayuba ,Sam baicancanci haka ba bayan haka kuma zumunchi bai CE haka ba



Share hawaye tayi ta kalli su Sadiya da shamsu Wanda suke zaune sun zuba mata ido suma suna share hawaye,tace "kunci Abinci"?


Girgiza kai sukai Alamun A'a.

Mikewa tayi ta karbi mukullin dakinta gurin iya tace"Ku taso Ku je Ku siyo indomee sai in dafa muku kafin in daura girki"





*BINTA UMAR ABBALE*

_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
08089965176
[04/05, 03:04] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻writting by*
*Binta Umar*
_*MAMAN ABDUL WAHABU*_



~*MRS AHAMAD GWADABE*~


*πŸ…Ώ10*


Dakinsu Na gado ,ta bude musu ,suka shiga ,tana jin su Mabaruka da Shamsiyya ,sai zaginta sukeyi har yanzu ,sai tayi musu banza,

Tafito da kudi gudar Dari biyar Sabuwa dal! Tabawa Sadiya ,dake tafi Isyaku ,wayo ,tace maza taje ta siyo musu indome guda hudu ,sai ta dafa musu kafin ta Dora musu Abincin dare.
Cikin Farin ciki Sadiya ta kar6a ,ta tafi kantin Abbah ,dake bakin layinsu siyowa Sai Murna takeyi dake yarinyar ,tana son. Indomee sosai ,shiyasa kullum said tayiwa Aunty tasu Addu'a in tayi Sallah,sabida duk Abinda suke Nema tana musu .

*wannan kenan*


*ASALIN LABARIN*

___________________


Malam Tanko Makeri
Shine Ai nihin sunasa ,Wanda jama'a suke kuranshi dashi ,Amma A salin sunansa dayyabu " to tun yana yaro Mahaifinshi ya sanya masa Tanko kasancewar sunan Mahaifinshi ne dashi
Shiyasa sunan ya buya idan ba Tanko Makeri kace ba babu Wanda zai gane.


Mutum ne shi Wanda Allah yayi masa baiwa da Fasa ta qere qere duk Abinda ya kalla sau daya to in sha Allahu nan take zai qera makashi ,tamkar daga kamfani


Shi kadai Mahaifinshi ya haifa ya koma ga Allah.

Shi kuma tun tasowarsa mutum ne mai Auri saki ,Matarshi ta Farko Lantana itace Uwarsu Kawu Sallau da Kawu Maman ,Matarshi ta biyu "yayanta duk mata ne su biyar ,haka ta zubesu gaban Lantana ,tayi tafiyarta ,Lokacin da Auran ya Mutu.


Lantana wata irin mace ce mai zuciyar kafurai bata da imani ko miskala zarratin,ita ke daura yaranta a kan mumun dabi'a

Idan Tanko ya fita sana'arsa sai ta daurawa "yayan kishiyarta ,mata talla ,tace duk inda zasuje suje su siyar mata tallah har da daddare daura musu take ,idan suka qi kuwa tasa Sallau ya Zane su.

Tun Tanko bai Sani ba har yazo ya sani ,yayi tai mata fada,budar bakinta sai cewa tayi itafa baza ta zauna da gurda gurda "yan mata gida daya ba batare da ta more su ba idan baya so ta daura musu tallata to yayi musu Aure,

Dake Tanko Jan wuya ne a gidanshi ,ya tsawar mata ,yace "gidansa takyale masa yara suyi karatu ,tukkuna idan Miji ya fito ai za'ai musu Auran.


Lantana taqi ji ,Tanko yana sa kafa yana fita zata fafaki yaran da faratin tallah ,suna kuka suke tafiya,


Karshe Suka yanke shawarar guduwa gurin Uwarsu,


Aiko ranar da Asubah suka fito dukkaninsu suna labewa suna jiran babansu ya fita sallah su gudu


Tanko ya fito kamar yadda ya saba ,ya tsaya shagon su Sallau ,domin tashinsu ,suje massalaci ,daga bakin kofa ya tsaya gami da bubbuga kyauran ,ya wucewarsa


Su sallau ko sunajinsa ,da suka fahimci ya kauce daga gurin sai suka cigaba da baccinsu ,dakin sai tsami ne yake tashi ,sabida ,dama bawata tsaftace dasu ba ,sai su fi sati basiyi wanka ba.



Su Atika kuwa bayan sun tabbatar da wucewar babansu ,sai suka fito sadaf sadaf zasu gudu.


Abin Mamaki ! Sukayi gware da Tanko ya dawo domin daukar chazbah ,

Sai ya kara haske fitilar dake hannunsa yana kallonsu daya bayan daya,ga Atika riqe da katuwar jaka.


Yace"INA zakuje ne"?

Sai suka fashe da kuka dikanninsu ,

Kukan da yayi sanadiyar Farkawar Lantana daga Barci duk da tana cikin Uwar dakinta,

Tafito da sauri jin kukan da soro ,tana Addu'a Allah yasa ba daya daga cikin "yayanta bane ya mutu ,kanta ko Dan kwali babu.


Me za ta gani su Atika ne tsaye riqe da jaka suna zabga kuka ,ga babansu a tsay"


Tace"Malam Lafiya dai in ce ko "? Wa"yan nan shashashan yaran sun tashe ni daga bacci"


Ko sauraronta bai yi ba ,ya cigaba da tambayar su Atika ina zasuje da Asubar nan.


Atika tace "babah mungaji da Azabar da ake gana mana ,zamu tafi gurin babarmu,


Lantana tayi salati kamar gaske tace"Au!sharri zaku kullamin gurin Ubanku "ooo ! Ni Lantana Na hadu da "yayan zamani,
Sai ta hau kwala Sallau kira.
"Sallau" Sallaau!! Sallau"!!




*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_


*NANA KHADIJA*


*YARO DA KUDI*


*GIMBIYA BALARABA*

πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
_in kana bukatar cigabansi ga number nan_
08089965176
[04/05, 03:05] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻writting by*
*Binta Umar*
_*MAMAN ABDUL WAHABU*_



_Bissimillahi _Rahamanir rahim_


*πŸ…Ώ11*


Sallau ya taso a fusace Sallau ,yafito gami da cewa "wai menene kin tashe ni ina bacci"


Sai tafashe da kuka tana nuna su Atika da hannu tace"ga sunan suna kulla min sharri a gurin Ubanku ,har da zagina"


Ai ko sallau ya yi tsalle ya gaurawa Atika Mari yana zaginta ta Uwa ta Uba,kwata kwata bai lura da Malam Tanko dake tsaye a gurin ba.


Tanko yace"yanzu Lantana yaushe yaran nan suka zage ki Dan sharri" to tunda Abin ya zama haka zan dauke yaran nan daga hannunki ,ya mai da idonsa kan Sallau dake tsaye yace"kaji kunya sallau ,da zaka din ga biyewa Uwarka da duk Abinda tace da kai , Allah ya shirye ka,ya mai da idonsa kan su Atika yace su koma ciki ,kafin yadawo daga masallaci.

Yana fita Sallau ya riqa zaginsu shi da Lantana,sukayi masu shiru ,Lantana tace baza su koma ba cikin gidan ba tunda suka fito sun fito kenan ,sai subari Ubansu mai daure musu gindi ya dawo sannan.



Bayan Sun fito daga Massalaci Tanko ya tsaya shida Amininsa yake fada masa halin da a ke ciki.

Budar bakin Malam iliyasu yace"mai zai hana muha da Atika da Yunusa mana ina ganin hakan zaifi.

Malam Tanko yaji dadi hakan ,ai nan suka tsayar da Magana.

Bayan sun karya da kansa ya fita dasu yasa su a mota ban da Atika domin yafada halin da ake ciki.
Tana kuka suka rabu da "yan Uwanta.


****

Lantana kamar ta mutu jin cewar Atika zata Auri yunusa Dan gidan Malam iliyasi ,ita San samunta yaran suyi tazama babu Aure sabida tsabar qiyyaya.



Ranar daurin Aure Abin sai yabawa jama'ar dake gurin Mamaki jin ana daurawa Uba da "ya Aure.

Da Labari ya iski Lantana gurin daurin Auren tafito tamkar mahaukaciya tariqa dure duren Ashar
Da kyar su Sallau suka jata suka mayar da ita gida.
Tace"Yanzu Sallau Abinda Malam zai yimin kenan ,ya muna furce ni ,Ashe Aure zai yi ban sani ba niko mai zan yiwa Malam in wuce bakin cikin da ya kunsa min"
Sai ta fashe da kuka har dasu fyatar majina.

Sallau yace"ki rabu dashi Lantana,mune maganin Matar tasa wallahi ,tunda tasa ki zubar da hawaye Sai mun hanata zaman lafiya"
Maman yace "kwarai kuwa sai mun daukar miki fansa a kanta"

Sai tai ta shi musu Albarka ,tace"ai dama nasan zaku share min hawaye shi kuma Malam din zai shigo ya same ni wallahi"


****

Lantana babu irin cin mutumchin da bata yiwa Malam Tanko ba ,ya share ta ,kawai bai kulata ba ya cigaba da hidimarsa,


Gidan Malam Ilayisu nan a ka kai Atika,sosai Tanko yayi mata kayan daki babu laifi ,nan ma da labari ya iski lantana ,tai ta zuba ruwan bala'i a gidan ,tana cewa Tanko ya kwashe dukiyar "yayanta yayiwa wata banza kayan daki ,ai "yaya maza sune "yaya
A takaice dai ranar Lantana bata barsu sun rintsa ba.

Ashe Abu Na gaba,
Sabida kayan dakin Amaryar Malam Tanko iri daya ne da Na Atika ,da Alama duk shi yayi musu.



Wata makociyarsu tazo tana tsoguntawa Lantana ,Aikuwa "yan jeran nafita ,suka shiga dakin Amaryar ita dasu Sallau ,duka wargitsa shi,gami da debo kwata suka yaba jikin gadon da tsakiyar dakin ,sannan suka dinga kuza ruwa a tsakiyar gadon da dakin,sai da suka jiqa katifar jagab sannan suka futa daga dakin ,gami da barinshi a bude.


Ko da "yan kawo Amarya suka zo Lantana Na kuryar dakinta ta tasa redio tana ji ,tana jin shigowarsu sai ta rage redio n tayi lif tana jiran me zai faru.



Abin Mamaki gami da daure kai dak in suka gani a bude ,suna San ya kafafunsu ciki suka ga Abin mamaki ,Komai a fashe ga katifa jagab dakin yana ta warin kwata,

Matar Liman ,ta ce"innalilahi wa'ina ilayi rajiun"! Ai ba haka muka bar dakin nan ba,kai! Jama'a wai kishi hauka ne?

Lantana Na jiyo Abinda take cewa sai tafito a fusace tana gyara daurin zaninta ,Dan kwali a hannu,
Ta nuna Matar liman da hannu tace"ke Shattu bana son munafurci da kankanba ,ehe! Duk wata kutun gwila da kuka hada naji labari da sanya hannuku gurin bawa Malam ,waccan Mutsiyaciyar yarinyar tsintaciyya wacce ba'a San daga in da take ba ,wato ni za ai wa rufa rufa ,an lullube kura da fatar Akuya ,an dauko

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment