You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
kayi Auran Uwa Na fita kofar gida ta dasa kasko Na suyar Awara gefe ga gyada nan cikin Faratin A quq-qulle a leda marau da tubes! Haka take Tara matasa ai ta shirme ,idan har kan dillanci tazo nan ma tana tabawa
A takaice ita ce take ciyar da Sallau domin shi ya zauna zuciyarsa A mace yaqi ya fita ya nema ,Gwara Maman shi ya kan fita yayi buge bugensa ya samu Na kashewa,ita ko Lantana Kasuwanni take bi tana tallan zogale da kuli ,Da wannan suke Samun Abinda zasu kai bakinsu.
To shiyasa daga Lantana Har Sallau! Suka taso Ayuba a gaba da kyashi gami da hassada,Wanda hausawa sukance (Hassada ga mai rabo taki ce)
Ayuba ya shaku da "Yar Uwarshi Atika ,domin duk wani Sirrin shi tasani ita da Gwaggo Shatu marikiyar shi ,
Haka ya cigaba da Rayuwa ,tare da Kiyyaya da tsangwama gurin "Yan Uwanshi,Amma duk da Haka shi bai fasa Zumunci da su ba,
Hafsatu ita ce Ayuba ya Amince da tazama Uwar "Yayanshi, Domin ya yaba da tarbiyar ta gami da nutsuwa da kamun kai,"Yar Makotan Su Atika ce Yayarshi Ita ma haifinta ya rasu,to haka dai Malam Liman ya tsaya Masa tsayin daka ganin Tabbatuwar Auran
Nan ta tare gidansu ,Bangaran shi Na gado,Uwa da Lantana suka ce dawa Allah ya hadasu,suka sanya ta a gaba Babu irin Muguntar da basai Mata,yarinyar duk ta kwar zane,kullum cikin Aikin Awarar Uwa take tamkar ita take Auranta,inda Allah ya tai maketa ma ,Lantana,bata yini a gida Sai Yamma take dawowa daga zarar ta dawo ,zatai ta kwala Mata kira tana zagi! Tai ta sanya ta Aikin Wahala ,ko da ta Samu ciki basu bar ta ta huta ba, Kullum idan Ayuba ya shi go gidan yaga irin wahalar da take sha,sai bakin ciki ya kamashi gashi bashi da Bakin Magana,Lantana ta tsigale shi, Kullum in sun shiga daki yai ta Rarrashin ta yace"tayi hakuri Shima ba yason Wannan Wahalar da take sha Da yana da Hali da sai ya kama mata Haya ko daki guda ne,to Babu Hali domin duk wasu hanyoyin Samunsa Sallau ya shiga ya fita ,ya rabashi dasu da Asiri da kuma Ziga ga Mutane ,cewar kar Wanda ta hada hurda dashi domin ko ba Dan gari ba ne,Zai cuce su ya gudu
To Lokacin A kwai qarancin Ilimi gami da Wayewa Sai Jama'a suka dinga gudun Ayuba,
Tunda ga Lokacin ya dai na sana'a sai dai ya fita tayi buge bugensa ya dawo gida
A lokacin Uwa! Tana da Yara Biyu Namiji da Mace'Iro da Shamsiyya, To iro tun yana shekara Uku ya iya yawon Talla kusfa kusfa,haka zata kasa masa a faran ti tun Safe ,ba bu Maganar zuwa makaranta
Haka ake Zaman doya da Manja a gidan Domin Maman ma ya yi Aure shima Matarshi Na gidan , Mai suna Halima inda ta kasance mace mai sauqi hali gami da Hankali ,kwata kwata bata kaunar Abinda Su Lantana sukewa Hafsatu Matar Ayuba ,sai ta riqa Jan ta a jiki tana tausar ta,nan ko Uwa!! Tace dawa Allah ya hada su ,shiga fita Dari sai ta Zubda musu Ha baici ta dauki gaba da Halima ,duk dai a kan tana kula Hafsatu,ita ko Lantana dama Macace mai mugun kwadayi kasan cewar Maman duk ya fisu Samu yasa bata son Laifin sa ko Na Matarshi shiyasa ta kyale ta take Kula Hafsatun Dan kar ta dai Na bata Abinci da kayan dadi in Maman ya siyo Domin ,shi kwata kwata ya Manta da wata Lantana ta Matarshi yake,in Anyi Magana yace ai tana fita Nema taci da Kan ta,shima yanzu Nauyi yayi masa yawa.
*Allah ka azirtamu da "Yaya masu Albarka ,duk Dan da zai zame mana fitina a rayuwarmu Allah kar ka bamu,Allah ka sa mufi qarfin zuciyoyinmu*
*BINTA UMAR ABBALE*
_MARUBUCIYAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
08089965176
[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: π§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββ
*πΎGIMBIYA BALARABAπΎ*
π§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββ
*βπ»Writing by*
_Binta Umar_
*MAMAN ABDUL WAHABU*
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_π€π»
*π Ώ19*
_Bissimillahi_
Cikin Hafsatu ya isa Haihuwa , Halima Matar ,Maman ce ta tsaya Mata a gidan Lokacin Gwaggo Shatu babu Lafiya Abinka da jikin girma, Iya" Atika ita ce ta karbi Haihuwar ,su Lokacin Domin Lantana ta tafi tallanta Hakanan Uwa! Na waje tana Soyar Awara Tamkar ba matan Aure ba
Cikin ikon Allah ta haifi diyar ta Mace Sak! Mahaifinta Kamar an tsaga kara dashi Fara tas!! Ga hanci har baka, Ayuba ya ruqa Murna ,A take yayi wa jaririya huduba da Sunan Mahaifiyarshi, wato Suwaibah ,sai ya ke ce Mata Balaraba kasancewar An haifeta ranar Laraba
Ko da Lantana ta dawo taga jaririya tace ,Haushi Kamar ya kashe ta ganin Baiwa da kyau da Allah yayi mata ga Hafsatu Lafiya lau,ita San samun ta Hafsatun ta mutu kamar yadda Suwaibah ma ta Mutu , A ranar kwana tayi tana zage-zage Kamar ba tsohuwa ba,
Ita ko Uwa!! Tsabar kyashi bai bar ta ba ma ballan ta ta shi go ta ga Abinda Hafsatu ta Haifa ,ta dai tura Iro gulma! Domin yaje ya gano mata ,Aiko Yaron ya dawo Yana Fada mata kyawun "Yar jinjinyar ,Bakin ciki kamar ya kasheta,ta waiwaya ta kalli Yarinyar ta Shamsiyya,a zaune ,duqun duqun!! Daga ita sai karamin ,Wando ga Wani Uban zarni! Da take yi,Yarinyar Baqa ce Sosai gashi Mummuna Dan Har Iro yafi ta kyau tunda shi ya Dan dauko kammanin Mahaifinshi,ito ko Shamsiyya Kamarsu daya da Uwarta!
Nan taci Alwashin Sake Haihuwa ,Domin tana Zaune Wata baza tazo tafi ta "Yaya a gidan Ba, kuma in sha Allah ita ma sai ta haifi Fari ,sabida Sallau yana da Haske dai-dai gwargwado
*Ni ko nace kuji ni da Uwa! Da tsabar jahilci don Allah*π€£
Har a kayi Suna Uwa! Da Lantana basu leqa sun ga Abinda a ka Haifa ba,Balle Sallau" Wanda ya tsiri gaba! Da Ayuba babu gaira babu dalili ganin yadda yayi komai Na Haihuwa ,Hatta hakika, biyu ya yankawa Maijego,shine yake Bakin ciki ,yana tunanin a ina ya samu kudin da yayi wannan Hidimar
****
Kafin Hafsatu tayi Ar'ba'in Uwa! Ta samu Ciki sai tun qaho take tana hora hanci ita zata haihu ,Shiga Dari fita Dari sai ta yadda Habaici tamkar Wacce bata taba Haihuwa ba ,Ita ko Hafsatu bata ce Mata komai ,in tagama Ai kace Aikacen ta ,sai ta tafi bangaran ,Suyi zamansu Har Magari ba
*Balaraba* ta saba da Halima Sosai in Kusan Kullum tana Hannunta ,in ko bata gurinta tana can gidan ,Iya Atika, Haka jama'a suke Kaunar ta daga An fita da ita kowa son ta dauke ta yake,Sabida farin jinin ta, Uwa! Ko babu shiri ta bazama, Gurin Malamai a kan Yarinyar ,Wai a Sanya Mata Bakin jini a ida nun Jama'a kuma a saka Ta ta fandare ta zama ga gararriya, Malamin nata yaga Tsubbu bace Tsubbacan Sa ya yi Mata Baya nin Yadda zata yi da kayan Aikin da ya bata Mutukar ta kuskure to babu Makawa "Yayanta zasu Lalace domin Aikin kansu Zai kuma,
Haka ta dawo gida tana Haki ga tsohon Ciki a jikinta, Sai da ta bari dare yayi Sosai kowa ya shige dakinshi ,sannan ta Fito ta daga Manyan dutsinan da suke girgi dashi ta tona Gurin da Wuqa yayi zurfi Sosai ,sannan ta saka Wasu Manya Manyan Layu! Guda biyu ,tayi Sauri ta Mayar da kasar gurin ta Binne ,sannan ta Dora dotsen a kai.
Ashe tayi shuka a idon Makwarwa Domin dai tun lokacin da tafito ,Halima ta ganta ita ma ta ta shine domin Zuwa ban daki har ta fito sai ta Ja da baya ,ta labe jikin kofar ta ganin Uwa!! A Gurfa ne a gaban Murhu ta dage tana To na wa.
*BINTA UMAR ABBALE*
_MARUBUCIYAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
08089965176
[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
π§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββ
*πΎGIMBIYA BALARABA*πΎ
π§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββ
*βπ»Writting by*
_Binta Umar_
*Maman Abdul Wahabu*
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_
*π Ώ20*
_Bissimillahi_
Uwa! Na gama binne Layun ta Mike ,tana karkade jikinta sai wai ge wai ge take Na rashin Gaskiya, tayi Sauri ta shige dakin ta
Ita ko Halima sai ta bari ta dai najin Motsin Uwa! Daga dakin ta,Sannan ta fito a hankali,ta aje botar hannunta gefe ,ta Dauke katon dutsen ,sannan ta sa Wuqa tafara tone Abinda Uwa ta Binne! A gurin
Can ta tonu Layu daure jikin Wani Jan yanki, tayi Bissilimih gami da sanya Hannunta ta dauke ta aje gefe ,ta fara mai da kasar gurun tana Rufewa,Tsaf ta Gyara gurin ,ta mike tana Addu'oi ta dauki Layun ,ta je ta aje a gurin ta,Sannan ta dawo tayi Uzirin ta dama Abinda ya tashe ta kenan,
Jin Motsin bude kofar ban daki ne yasa Uwa futowa da Sauri ,Tana kallon Bakin Murhu,Ajiyar Zuciya ta Sauke ganin Babu Abinda ya faru yadda ta bar gurin haka yake, Kallon- kallo sukayi ita da Halima,Sai ta buga tsaki ,ta joya ta shige dakin ta ban ko kofa!
Girgiza kai! Halima tayi kawai,tana Mamakin Zuciyar Uwa Tamkar ta kafurai, A fili tace Allah ya shirye ki Uwa!"
Ta shige dakin ta ita ma
Safiya nayi Uwa! Ta fito ta aza tukunyar Awara ,A wuta ta dinga Hura huta Sosai sabida Malam yace Mata ,In ta binne layun ta saka Wuta sosai a gurin yadda Aikin zai fi saurin kamawa, Ai kuwa haka tayi sai Faman Saka ice take, duk a kokarin ta Na taga *Balaraba* ta lalace,
*Allah ka sa muda ce*
Can Bangaran Halima kuwa ,babu Wanda ta fadawa Abinda ya faru ,kawai Safiya nayi ta boye Layun Cikin Hijab din ta ,ta fita daga gidan,kai tsaye gidansu ta nufa,dama kusa ne,ta sanya kannenta ,suka kwance Layun ,tare da yi musu futsari Sannan tace ,su jefa a Masai!
Ai kuwa haka yaran sukayi Abinda ta Umar cesu, Nan ta rarraba musu Goma-Goma suka tafi suna Murna,
Maihaifiyar ta take Tambayar ta Mai nene"?
Nan ta warware mata komai
Tace "Gaskiya Uwa! Bata da imani Wallahi narasa Abunda Hafsatu ta tsare mata,Bai wuce ita tayiwa Asiri ba"
Halima tace"Tabbas ita za tayi wa ,in sha Allahu sai dai sharrin ta ya bi ta,tunda ita ba ta nufe ta da shi ba,
*****
Wannan Shine sanadiyar Lalacewar Iro ,Uwa!Na zuba Ido taji an ce Balaraba tafara sace-sace sai Hakan tafaru kan Dan ta Iro, Kwatsam! Suna Zaune daf da Magariba dukkaninsu a tsakar gida har Lantana ,ta dawo daga yawon Tallanta, Tafito da ciniki tana lissafawa Sallau! Ma shigowar sa kenan ,yana gyara tsayuwar Kekensa, Ita Kuma Tana Aikin Awara Wacce Shamsiyya take Zama gidin bishiya tana Soyawa da daddare,
Kawai! Suka ji ihu! Ana barawo barawo Kafin suyi Wani yunkuri! Iro yafado gidan Yana Haki! Gashi sai Warin ganye! Yake yi,idonshi yayi ja,da gudu ya shiga dakin Lantana ya kulle ,
Matasa ne suka shi go sun kai su goma ko wannesu riqe da Abin duka! Suka Zagin Iro ! Wai sai ya fito sun dake shi,
Lantana ta Mike a zabure! Tana gyara daurin Zaninta bayan ta Kwashe kananun kudinta da ta baza a kasa tana qirgawa ta boye cikin ,Wani burgujejen Sket din ta Mai Aljihuna,Wanda take sanyashi a ciki kafin ta daura Zani, takarasa In da suke tsaye Suna Hayaniya! Sallau Sai Rarrashin su yake Sabida ,dama shi tuntuni yaji Labarin Abinda Dan shi yake Aikatawa.
Tace"Ku tsinannu! "Yayan Mutsiya ta, Mai jika Na yayi muku ,kuka biyo shi da Abin duka sai kace ,Wanda kuka kama shi da kayan Wani!
Daya daga cikinsu, Yace "ke! Tsohuwa Kar ki rainawa mutane Hankali mana! Eh! A kwai tsinanne irin Iro! barawo Mai kwatar Wayoyin Mutane, Kinga Wannan Yaron ya fizgewa Waya,yanzu An ai keshi ya kai chaji ,Sabida haka kushiga Ku fito dashi ,Billahillazi Ku mu balla kofar! Mu Saba masa Kammani,dama ya ishe mu da Sace-Sace' A Unguwa babu dama a Aiki Yara da kudi ,sai ya kwace.
*BINTA UMAR ABBALE*
_MARUBUCIYAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
08089965176
[04/05, 03:15] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
π§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββπ§π»ββ
*πΎGIMBIYA BALARABA*πΎ
*βπ»Writting By*
_Binta Umar_
*MAMAN ABDUL WAHABU*
_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels