Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mayya an kawo min gida salon tazo ta leshe ni da "yaya Na,to wallahi baza ta sabu ba ehe!! Tafada tana buga cinya cike da neman tashin hankali!




*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*


_IN KANA BUKATAR CIGABANSHI GA NUMBAR NAN_
08089965176
[04/05, 03:05] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€


*✍🏻writting by*
_*BINTA UMAR*_
*Maman Abdul Wahabu*




_Up_
_up_
_up_
*BINTA UMAR FAN'S*

_INA MUGUN YINKU SOSAI DA SOSAI INA JIN DADIN YADDA KUKE KAUNAR NOVELS DINA ,NAGODE DA GOYAN BAYANKU DARI BISA DARI_

_*HAKIKA BANI DA BAKIN DA ZAN YI AMFANI DA SHI GURIN GODE MUKU ,SAI DAI IN CE ALLAH YABARMU TARE ,ALLAH YABAR KAUNA TA DAN ALLAH*_
❀



*"YAN QUNGIYAR ZAMANI WRTERS ASSOCIATION*

_INA YINKU OVER ,MUSSAMAN ,RAEL SHAXXI ,HUSAIN 8K "YAR MUTAN ARKALLAH ,HAFSAT SISI ,HALINKU YANA BURGE NI HALINKU ABIN KOYI NE_


*ALLAH YAQARA DAUKAKA ZAMANI*


*πŸ…Ώ11*


Shattu tace"kinga lantana mu ba tashin hankali ne ya kawo mu ba Alkairi ne ya kawo mu duk dai wannan da yayi nagari kan shi," takarashe magana tana kama hannun Amaryar Malam Tanko
Da nufin shigar dai ita cikin dak in'


Mutanen dake ciki suna ta faman tsane ruwan dake kwance gurin ,suka ce "Aa shattu yanzu in kinshigo da ita nan ina guri ,ki kai ta makota tukkuna mugama gyara gurin.
Duk abinda mutum yayi kansa.


Shatu tace "to bara muje gidan Baba Laraba I Dan kun gama sai kuzo Ku fada,



Da sauri Lantana ta tare hanya tana buga cinyarta tace"Ahayye nanaye Akin bur in ji tusa ,dole Dan ace da Mijin iya baba ni warki CE daidai da qungun kowace shegiya,ihe! Muna fukar Banza kawai!


Shattu tace"wai Lantana Lafiyarki kalau kuwa kishi fa ba hauka bane"A tunani Na zaki dauki Suwaibah a matsayin "yarki tunda kin San kome ya faru da rayuwarta"




"Ke!! Dakata shatu" Lantana tafada ta na turo dauri gaban go shi

Tace"dadin baki zaki yi min Dan bake a kaiwa kishiyar ba.


Baki San yanda zafin Abin yake bane shiyasa kike shishshigi a kan Maganar,
Nafada Na kara fada ni Lantana,in dai ina raye babu macan da ita sa in zauna da ita ,ko wacece kuwa"
Ta karashe maganar tana buga cinya.

Shatu kawai sai taja hannu Suwaiba ,wacce take ta kuka tsora ya cika ta,dama tuntuni take jin labarin matar a bakin mutan gari.



Lantana ta koma ta zauna ,gami da kunne redion ta tasaka kasat din wakokin bar mana coge tana ta zubda habaici a gidan,jira kawai take su tanka ayi wace za'ayi


Su dai sukayi mata shiru suna Aikinsu,

Bayan da suka gama ne daya ta tafi domin Kiran shattu ta shigo da Amarya dakinta.


To can kuwa gwaggo laraba ta sanya Suwaibah a gaba tana ta yi mata fada tace"duk Abinda lantana zatayi babu ruwanki da'ita idan mijinku ya fita kine mi izinin zuwa nan gudun fitinar laraba ,sai miyi zamanmu idan ya dawo sai ki koma,
Kinji ko?


Suwaibah ta daga kai tana zubar da hawaye gami da tuno Dan ginta da "yan Uwanta ,Rayuwa kenan



Kafin su watse sai da shatu takara yi mata fada sosai San nan tafito ta tafi



Lantana Na zaune tsakar gida tana jiran shigowar ,malam Tanko ,Domin yau ko me za'ayi sai dai ayi taci Alwaashin bazai kwana da Amaryarsa ba tunda ya munafurce ta,

Sallau ya shigo fudun! Fudun! Dashi kayan jikinsa duk datti tsabar kazanta jikinshi in banda tsami babu Abinda yake yi


Ya zauna kusa da Babarta sa gami da cewa"lantana me kikeyi har yanzu baki je kin kwanta ba ,goma fa ta wuce yanzu"


Tace"INA jiran babanku ya shi go Ayi wacce za'ayi"


Yace"to Ina Abinci Na"?


Lantana tace "kaga sallau !!wane irin Abinci kuma ,zan baka? Da girmanka da komai ,ni yau ban yi girki ba,ka kyale ni inji da Abinda ,ya dame ni"



"Gaskiya dole in yi Aure nima nagaji da wannan Abin da a ke mana a gidan nan Abinci ma sai a hanaka"
Dubi Yunusa dake shi Ubanshi yana sonshi ai yayi masa Aure ya bashi Abin yi da gurin zama,Amma mu muna zaune, gaskiya da sake ,bari Baban ya shigo yasan wacce zaiyi, shikkenan sai mu zauna muna kallonshi yana Aure Aure ,duk kudinshi su kare ta nan gurin. Sai bayan ya mutu mu tashi a tutar babu"



Lantana ta gyara zama tace"Yo dama ai tuntuni nake fada muku Ku San Abin yi wallahi domin Malam baya tataku ,kaima kaje ka nemo matar Aure ,ihe! Duk in da kudi suke yafito dasu yai maka kuma dole ya baka jari da gurin Zama"



Sallau yace "ai Abinda zan yi keanan kuma zan fara binkicen a dakarsa ta waccan dakin nasa da baya son Abude nasan da a kwai Abubuwansa a ciki masu Amfani ,zan bi dare Na sacesu ,a kan ya Qarar dasu a banza ba mu mori ko kwabo ba"



Wata dariya Lantana ta fara yi cike da Farin ciki tace"shiyasa nake son ka Sallau ,ai kai ne maganainsa wallahi"



Sallau tace"wai har an kawo masa Amaryar ne"?



Dakin Suwaiba lantana ta kalla tana zabgawa harara ,tamkar da mutum take tace"tana ciki tana jinka munafukar banza!





*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*

*YARO DA KUDI*

*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
_in kana bukatar cigabansi ga numbar nan_
08089965176
[04/05, 03:08] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€


*✍🏻writting by*
_*BINTA UMAR*_
*Maman Abdul Wahabu*


_RABBI SHARALI SADARI WAYYASIRLI AMRI WA'ALAL UQUDATUN MIN LISANI YAFQAHU KAULI_



*πŸ…Ώ13*



Tashi sallau yayi yaje ya dinga buga kyauran dakin ,cikin sigar rashin mutumci ,yana zagin Suwaiba Matar mahaifinshi

Lantana tace" kayi min daidai ni dama nasan zaku share min hawaye Na"



Sallau yaciga ba da ciwa Suwaibah mutumci yace"Tsintacciya wace tafito yawon karuwanci ,Dole sai kin koma garinku ,Na gado mai sifar bararoji nan ba Nijar bace ,kin zo zaki lashe mu mayya kawai"


Suwaiba Na ciki tana kukan wannan cin mutumchi da ,salau ya ke sirfa mata!

Motsi yaji daga waje ,yayi saurin barin kofar ,Suwaibah yaje ya zauna kusa da lantana ,duk a zatonsa malam tanko ne,

Maman ne ya shi go fudun! Fudun! Yadawo daga yawonshi Na gidan kallo
Ya zauna bakin rijiya,yana hamma yace Lantana ina Abinci na?



Ban dashi!! Lantana tafada a zafafe tacigaba da cewa"gantalalle gama yawon Na ka zaka tambaye ni Abinci ai ko ina dashi bazan bayar ba"


Maman yace"to kar ki bayar mana ai nasan in da yake zanje in diba"


Tace"zagina zakayi ne Maman" wato baza ka dai Na yi min rashin kunya ba ko kana gananin Abinda mahaifinku yayi min"



"To me zan miki "yafada babu damuwa a fuskarsa yacigaba da cewa "karkari kawai duk abinda matarshi tayi min ko tayi miki in Zane ta ciki da waje"



Lantana tayi dariya gami da gyara zama tace" yawwa Dan arziqi irin albarka ,dama haka nakeso nasan kuna sona ,sabida haka. Mutaro mu takura mata kamar yadda mukaiwa wa"yancan yaran suka gudu ,har sai tagaji itama ta gudu da kafarta.


Sabida Azabar mu


Tace "kai kuma Sallau kabi dare da rana ka kwashe duk wani Abu da yake taqama dashi mu boye, domin baza mu tashi a tutar babu ba"


Sallau yace ai ba sai kin fada ba Lantana"

Dariya Maman yayi yace"gaskiya Lantana kin San ta kan Mugunta"

Ita ma dariyar ta sheqe da ita tana gyara zama tamkar wata sabuwar mahaukaciya tace" ai duk a gurina kuka koya"

Tace"bara Na kawo muku Abinci "yayan Albarka"

Ta mike tayi kchin tana sambatu kamar tababbiya


Suwaibah Na makale jikin kofarta tana jinsu ,Da duk Abinda suke kullawa,tausayin Malam tanko ya kama ta,sai tace"in sha Allahu Allah bazai Baku iko ba"


Goma da dara bi Tanko ya shi go gidansa,ya kulle gidan ,


Abin mamaki Su Sallau ya gani zaune sun kewaye uwarsu kamar masu Neman gafara


Yayi sallama
Suka Amsa ,ban da Lantana tana can tana kallon Abinda yake hannunsa!


Sallau yace Barka da dare?

"Barka kadai" Tanko yafada yana kokarin shiga dakin Amaryarshi


Sai lantana ta mike taje ta tari hanya ,cikin Neman tashin hankali tace"Malam baka isa ba fa"


Cikin nutsuwa Tanko yake kallonta ,Tamkar mahaukaciya yace"lafiyarki kalau kuwa lantana"


Rasss!! Nake tafada gami da buga cinya!

Tace "bani ledar hannunka ,tafada kamar wata Uwarsa!


Abin yabawa Tanko mamaki ,da yake tanko ba ya son raini ko kadan yace"bazan baki ba Lantana ranki zai yi mummunan baci idan baki kauce kin bani hanya ba"


Ta buga cinya! Cikin rashin mutumci da rashin kunya tace "bacin rai Na yaushe kuma ,Tanko kajima baka bata min ba,har kaje ka daura Aure batare da sanina ba sabida tsabar muna furci da Annamimanci kuma karasa wazaka Aura sai mayya kuma karuwa wacce ba'san daga in da take ba"
To sai dai kazaba ko ni ko ita ihee!!!!





Wani bacin rai ne ya turnike Tanko ,wai shi Lantana take zagi a gaban yaransa da matarsa,kawai sai ya fidda hannu ya tsinka mata mari ,ya hankade ta ,tafadi a gurin ya shige dakin Amaryarshi ya mai da kofa ya rufe gamma!!


Kuka Lantana ta rusa tana dukan kofar dakin da kafarta gami da zagin suwaibah ta uwa ta uba,makota Na jinta,



Sallau ya taso yana kokarin janye ta daga gurin tana fincikewa tace"sallau kaga yadda Malam ya fasa min hanci jini Na zuba ko"



Da sauri sallau ya lalubi Cocilan din shi da yake yawo da ita a Aljihu yana haska fuskar Mahaifiyar tashi


Ai kuwa ya sata habo gurin marin gashinan jini yana zuba a hancinta.

Da sauri yace"Maman zo kaga n"

Maman ya taso a fusace ya karaso gurin.yana dubawa


Tabbas jini ne yake fita a hancin mahaifiyar tasu,

Ganin yadda Maman yake huci yasa Lantana kara lanjarewa tana kuka sabida ta San halin Maman da bakar zuciya!

Suka janye ta daga bakin kofar suna rarrashinta ,nan suka yi mata Alkwarin daukar mata fansa a kan Suwaibah tunda duk a dalilinta Malam tanko ya zubar mata da jini ,Abinda bai taba faruwa ba ,
To suma sun dauki Alkwarin sai sun zubarwa da Suwaibah Joni


*******

Tun daga ranar Su Sallau suka matsawa Suwaibah in har suna gidan bata isa ta fito ba sai su hau jifanta ko su sanya mata kafa tafadi ,ko du zuba karkashi kofar dakinta da ta fito tafadi kasa,
Su kuma Na gefe Na faman kyalkyala mata dariya

Ko idan tayi girgi ,suje su kwashe su cinye tai magana su zageta

Ranar Sallau ya dauki cokali mai ya tsu ya kai mata jifa a goshin ta,bayan ta fito daga ban daki,ai kuwa kan kace kwabo jini ya tsinke sai ta saki butar hannunta,ta dafe gurin tana jin wani mugun zafi



Lantana dake zaune kan kujera "yar tsuguno tana tsintar shinkafa ta kyalkyale da dariya,tace kayi min daidai Sallau!!






*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
_in kana bukatar cigabanshi ga number nan_
08089965176
[04/05, 03:09] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻Writting by*
_*BINTA UMAR*_
*MAMAN ABDUL WAHABU*


_BISSIMILLAHI RAHAMANIR RAHIM_


*πŸ…Ώ14*



Suwibah ta dago kai tana kallon Sallau ,dake tsaye , zuba mata ido yana jiran ta tanka masa ,yayi mata wankin babban bargo!
Tafi minti biyar tana kallonshi ta gaza furta ko kalma daya,sabida tana tunin yin magana ,a yadda suke su kadai a gidan zasu iya yi mata duka,

Sai kawai ta wuce shi ta nufi dakinta jini Na diga a goshinta,

Suka kwashe da dariya suna nuna ta da hannu Lantana kamar ta tuntsira kasa Dan dariya
Tace "in kin sa kiyi magana mana"
Maman yace"wallahi Na dauka ma ramawa zatayi da naga tana kallonka.
Sallau ya zabura! Yace ta rama? Lallai da ta tarowa kanta Masifa tana cikin gidan Uban nawa"

Lantana tace "duk Ku rabu da ita a kwai Abinda zamu kulla mata idan an kwana biya"
"Zo kaji" tafada tana yafito sallau da hannunta


Rada tayi masa wacce ko Maman dake gurin a zaune bai jiba.
Su LA fashe da dariya murya kasa kasa ,Sallau yace"gaskiya Lantana dole a Sara miki'
Lantana tace ba dole ba! ai ni duk Wanda yaci tuwo miya ya sha dani

Ko da Malam tanko ya dawo yaga goshin suwaibah a fashe yayi tambayar duniya yaya haka tafaru taqi fada masa,sai ya rabu da ita kawai ya samo mata magani ,ta sha ta kwanta nan da nan bacci ya dauke ta,kwananan tana yawan yin bacci tarasa meye dalili.


*****

To haka rayuwa tai ta tafiya har cikin suwaibah ya fito ,lantana ta daga hankalinta,sosai Amma da ta tuno Abinda suka shiryawa cikn ita da sallau sai hankalinta ya kwanta.


Cikin suwaibah Na da wata tara tana dab da haihuwa ko yau ko gobe, ta fito zata ban daki ,da kyar take taka kasa sabida tsabar nauyin da cikin yayi mata bayan haka kuma Mararta Na mata ciwo


Ta juya baya tana jawo ruwa a rijiya Sallau ya fito daga dakin mahaifiyarsa ya hankade ta ,tayi taga taga zata Afka cikin rijiyar tayi saurin dafa bango ,Amma INA!! Santsin gurin ya kwashe tafadi ,gurin rigijff!!
Cikinta ya bugu da murfin rijiyar dake jin gine jikin bango Duk yayi tsatsa ,dalili kenan da yasa yaqi zama a rijiyar shine Lantana ta jin gine shi gurin


Suwaibah ta kwala ka!! Tana fadin wayyo Allah cikina
*innaliliahi wa inna ilaiyi rajiun*
Lantana tafito a suk wane tana fadin "ke lafiya ne kike yi mana ihu?

Sai taga nta zube bakin rijya gurin wanke wankensu,

Cikin zuciyarta tace Sallau ya cika ai ki kenan

Suwaiba ta dinga daga mata hannu Alamar ta temake ta,
Tabe baki lantana tayi "tace Abinda ya dame ki kenan ,nima lokacin da nake haihuwa babu wacce take te makamin ,sabida haka kije can ki karata,ta koma cikin dakinta,tana waqe waqe.

Sallau ma ficewa yayi daga gidan babu Abinda ya dame shi.




*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_
*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMIBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
_in kana bukatar ci gabanshi ga number nan_
08089965176
[04/05, 03:09] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?

πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻Written by*
_*BINTA UMAR*_
*MAMAN ABDUL WAHABU*




_MALUKAL MULKI ZULJALALI WAL IKIRAM_



*πŸ…Ώ15*




Suwaibah ta ruqe cikin ta tana fidda numfashi Sama Sama ,sai ko karin tashi take yi a gurin ta kasa ,sai kawai ta koma ta kwanta tana salati gami da Addu'oi tana fatan idan mutuwarta ce tazo to Allah yasa ta cika da Kalmar shahada.

Murqususu take tana jin wani mugun ciwon Mara kwankwason ta tamkar ya balle daga jikinta,tun tana iya yin Addu'ar afili har ta gazayi ta dawo yi a zuciyarta

Lantana tafito daga dakinta hannunta riqe da bota da Alama ban daki zata shiga,
Sai taga Suwaibah kwance a bakin rariyar Bandaki kamar ma bata numfashi,
Wani farin ciki ya kamata ,ta karaso gurin ta daki cikin Suwaibah da kafar ta tana dariya ,tace" shegiya "Yar mutsiyata "yar dadi miji ,yanzu shi malam din ai sai yazo ya karbar miki haihuwar ,shida ya dirka miki cikin,in sha Allahu dake da duk Dan da zaki Haifa sai kun muto kowa ya huta da jaraba"
Tafada tana kara dukan cikin a karo Na biyu ganin suwaibah bata motsa bah.

Nan ma shiru

Sai ta daga botar dake hannunta ta kwara mata ruwan ciki.

Suwaibah tasaki Ajiyar zuciya Wanda yayi dai dai da tsinkewar jini ,a jikinta kwarara yafara bin rariya

Gaban Lantana ya fadi ,ganin yadda jini yabi bin makwarara tamkar Wanda a ka kwance famfo ,tayi sauri ta tsallake Suwaibah ta shiga bandaki tayi uzirinta ,tafito da sauri ta shige dakinta ,tabar Suwaibah ,Akwan ce Rai a hannun Allah.


Atika ta shigo gidan Cikin Sallama ita ma da nata tsohun cikin,dama tare suke jerawa ,kusan kullum ta kanzo gidansu gurin suwaibah ,si ta hirarrakinsu duk a kan Haihuwa, Lantana tai tajin haushi tana zubarmusu da habaici,basa kulata


*innalilahi wa'ina ilaihi rajiun*!!

Shine Abinda Atika tafada ta yi kan suwaibah tana kokarin tashin ta ,Amma ina!!ina takasa sakamokon yadda jikin Suwaibah ya shika bubu kwari wuya ya langwabe,
Bakinta a bushe tace"Atika mutuwa zanyi ki cewa babanku ya gafarce ni bani da rabon kumawa ga Dan gina ,Dan Allah duk Abinda Na haifa ki riqe min shi a hannunki Na baki Amanarshi


Atika ta fashe da kuka tace"bazaki mutu ba in sha Allahu zaki goya danki da hannuki"

Suwaibah ta rimtse ido tana cije baki! Cikin Wahala jin wani Abu da yake kokarin dannowa ta kasanta ,ta riqa sakin Nushi a galabaice!!

Atika ta kwantar da ita a gurun ta mike cikin zafin Nama tayi dakin Lantana da Sauri.

Tana zaune kan tabarma da mifici a hannunta ,ta ware wakokin bar mana coge cikin redion ta sai ji take cike da Nishadi tana bin wakar cikin kwarewa ,tamkar ita ce ta rerata.


Atika taga labule fuskarta jike da ruwan hawaye Ciki tashin Hankali tace"Lantana ki kawo temako Dan girman Allah,ga suwaibah can zata haihu jini yana kwarara a jikinta"



Lantana tayi mata kwallon banza tace"ke Fice min A daki munafukar banza da wofi ni ce nai Mata cikin zaki zo kice in temaka mata kowa ai da haka ya haihu,lokacin da nake haihuwa Uwarki! Ta taya ni ne"?


Da sauri Atika ta fita daga dakin tana Mamakin Rashin Imanin Lantana

Ta yi hanyar waje da sauri domin taje ta kira Gwaggo Shattu matar Liman,


Ita ko Lantana tana jin ficeawr Atika daga gidan ,sai ta mike ta je ta daga labulenta tana keqen Suwaibah a kwance har yanzu batasan Wanda ke kanta ba

Taja tsaki!! Ta saki labulen ta har da sake gyarashi sosai ta zauna ta cigaba da jin wakokinta,babu Abinda ya dameta.





*BINTA UMAR ABBALE*


_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“šπŸ“š
08089965176
[04/05, 03:10] +234 808 996 5176: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation?


πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€



*✍🏻writting by*
*BINTA UMAR*
_MAMAN ABDUL WAHABU_



_*ZAMANI WRTES ASSOCIATON*_🀝🏻





_*ALLAH KAI MANA MAGANIN ABINDA YA DAME MU ,MUGUN JI DA MUGUN GANI ALLAH KA TSARE MU*_



*πŸ…Ώ16*


_Bissimillahi_



Gwaggo shatu da Atika suka shigo cikin tashin hankali, Haryanzu suwaibah Na kwance bakin rariya, jini Na fita ta kasanta, Numfashinta sai kaiwa yake yana kawowa,tana ganin zuwan gwago shatu ,ta daga mata hannu tana motsa bakinta,da sauri Gwaggo ta karasa gurin da take kwance ta dago,sosai tana nanata innaliliahi a fili tace"Atika maza zo ki kama min ita mu shiga daki haihu zatai yanzu,


Atika tazo suka kama suwaiba suka shiga da'ita dakinta sai nishi! Take cikin garari da Tsabar wahala ga kan da yafito ya Amma tsabar galabaita ya hanshi yunkurin fitowa ,ita ma Suwaiba duk wani qarfinta ya kare nishin wahala kawai take,


Lantana Na dakinta sake da labule tana jin wake-waken ta babu Abinda ya dame ta



Gwaggo tace"Atika jeki karbo Rubutun gurin Malam Nasan yanzu ya gama"


Atika Na kuka ta fita daga dakin tana tausawa Suwaibah ganin yadda take shan wuya ,tace dama haka mata suke wahala gurin haihuwa, ita sai tafara jin tsoran ranar da tata zata zo


Ta Na fita suka ci karo da Sallau ya shigo gidan ,saura kadan ya buge ta ta kauce,
Sallau ya ja ya tsaya yana dura mata Ashar!! Yace"ni ba wanki bane da bazaki gaishe ni ba"


Tace"Sallau suwaibah babu Lafiya zata haihu kaje ka kira babanmu"


Dariya Sallau ya fashe dashi cikin mugunta yace "Allah yasa ta mutu in dai sai naje Na kirashi ne ai kema kinsan gurin Aikinshi kije ki kirashi,mana"
Yayi wucewarsa ciki ya barta tsaye,

Sai ta fita da sauri tana share hawaye tana tur! Da Bakin Hali irin Na lantana da yaranta,



Tuni Malam ya kammala rubutun Na kuda ya fito da kanshi ,ganin yara zasu bata masa lokaci,sai ya hangi Lantana ya tsaya ta karaso,ta gaishe shi,yasan Rubutun zata karba sai ya mika mata yace maza a je bata in sha Allahu zata sauka lafiya"

Atika ta kar6i rubutun ta Na godiya,har ta joya zata tafi sai ta tsaya ta ce"Malam Babanmu yana gurin Aiki bai San halin da ake ciki ba"


"Ashsha""! Malam yafada yana jinjina Kai yace"yanzo zan tashi yara suje su fada masa ko in je da kai na,kedai maza jeki kai rubutun"


Da sauri Atika tatafi tana taiwa Suwaibah Addu'a Allah ya sauke ta Lafiya



Gwaggo shattu sai gumi take sharbawa ganin duk iya bakin kokarinta tayi Akan Suwaiba tayi wani yunkuri!! Ko yaron ya fado Ta kasayi Asabili da qarfinta ya kare, ita dai tana kwance Batasan wace duniyar take ba,sosai Gwaggo ta firgita,ganin yadda jini yake fita har yanzu gashi ba a haihuba,tabbas fitar jini ga mace mai naquda hadari ne,ba'aso Anfison in mace ta haihu sai jinin ya fita,duk da a lokacin da qaracin wayewar kai,Gwaggo shatu ta fahimci Suwaibah tana cikin hadari ba karami ba shiyasa ta tsinke da Almarin ,sai addu'oi take tofa mata,ta mike ta fita domin baza ta iya aikin ita daya ba,tanajin tsoran fita taje ta kira unguwar zoma, Sai ta daga labulen dakin Lantana,


Lantana ta rage Karfin Redion ta ,tana mata wani kallo gami da ya mutse fuska



"Lantana kiji tsoran Allah kiji tsoran ranar kumawarki ga Allah ,Lantana meye duniya,kishiyarki Na naquda kika bari har ta gala baita batare da kin je kin sanar ba duk Wanda yayi nagari kanshi"



Lantana ta harziqa!! Tace"kinga shattu banason kinibibi kunsan Yarinyar baza ta iya haihuwa da kanta ba kuka kulla mata Aure duk domin ku bata min rai!, to Ta Allah ba taku ba,Sai kije ki nemi Wanda yayi mata cikin yazo ya karbi haihuwar Amman ni karki kuma saka ni a lamarin Ehee!!!!

Sallau dake gefe yana cin wake da shinkafa cikin Langa,ya fashe da dariya,jin Abinda Uwartasa tace wai aje a nemi Wanda yayi mata cikin yace "in banda Abin baba Mu kadai mun isheshi "yayan Asali ba sai yaje ya hada jininshi da bara gurbi ba"

Lantana tace"ai Abinda Akeso ya gane kenan yaqi yagane sabida muna fukai sun zigashi"



Sallamar Atika ce ta sa Gwaggo shattu bata tanka musu ba sai tasaki labulen dakin da sauri ta karbi rubutun hannun Atika,suna rige-rigen shiga dakin Suwaiba



Abin Mamaki jinjiri ne kwance cikin jini yana motsi Igiyar cibiya ta sarqe masa wuya,ga shi mahaifar bata fado ba


Da sauri Shattu taje ta dauke shi gami da since masa zaran cibiyar ta sanya reza ta yanke gami da daurewa,tana tai wai Allah tasbihi,ta mika wa Atika yaron ,taje tadago Suwaiba tana kokarin bata rubutun domin asamu mabiya ta fado sai taga Suwaibah ta koma Sharaf! Ta kwanta ,Rai yayi Halinshi!!





*BINTA UMAR ABBALE*



_MARUBUCIYAR_

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
πŸ“šπŸ“šπŸ“š
08089965176
[04/05, 03:13] +234 808 996 5176: πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€πŸ§β€β™€




*✍🏻Writting by*
_Binta Umar_
*Maman Abdul Wahabu*


_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_🀝🏻


*πŸ…Ώ17*


_Bissimillahi_


*inalillahi Wa inna ilaiyi rajiun!*

Shine Abinda Gwaggo Shatu take Fada, Jikin sai rawa yake yi ta kalli ,Atika dake tsaye a gurin gabanta yana Faduwa! Tace "Suwaibah ta rigamu gidan gaskiy...
Kafin ta karasa Malam Tanko ya daga Labulen Dakin cikin tashin hankali,
Ya ga Suwaiba Kwance a kasa lullube da Zani ,da Sauri ya dauke Zani yana kiran Sunanta,Gwaggo Shatu ta fashe da Kuka! Tace"Malam Suwaiba Babu Allah ya raba ganawa"

*Innalillahi Wa'ina ilaihi rajiun*


Malam Tanko ya fada Bakinshi sai rawa yake yi Da Sauri ya Fita daga dakin ya tsaya kofar Dakin Lantana,Daga Waje yace"Lantana ki fito ,Suwaibah Allah ya karbi Abinshi, Burinki ya cika"
Yana gama Maganar Yayi waje Cikin Zafin Nama,Bakinshi dauke da Addu'oi Ga Suwaiba Matar Arziqi


Da Sauri Lantana ta bankada Labule,ta fito kamar gaske ta tsaya tsakar gidan Tafashe da ihu! "Wayyo Mun shiga Uku! Ihu! Take Sosai Sai kace Mahaukaciya ,Cikin Ziciyarta Sai murna take

Nan Makota suka dinga Shigowa Cikin tashin Hankali ,Masu kuka nayi masu salati nayi ,kar dai Lantana taji Labari


Malam Suka shi go dashi da Liman da Sauran dattawan Unguwa,

A ka sutturce Suwaiba a ka kai ta gidanta Na gaskiya, Sosai mutuwar ta ta ba zuqatan Mutane banda Lantana da yaran ta



Bakin ciki Kamar yakashe Lantana Lokacin da ta Fahimci Da Namiji Suwaibah ta haifa,suka riqa tsara yadda zasu kashe jinjirin ita dasu Sallau,Fahimtar Hakan yasa Malam Tanko ,daukar jinjirin Bayan kwana ba kwai ya Miqashi ga Gwaggo Shattu ,yace ya bata Amana

Gwaggo tace ta karba Allah ya tayata riqo ,A lokanci A kwai qan warta da take Shayarwa sai ta bata,Jaririn Wanda yaci Sunan Ayuba,da zumar in ta yayashi Sai ya dawo Hannuta,



Lantana taji ciwon Abinda Malam Tanko yayi ,nan ta Sanyashi a gaba ta rika cin mutumcinsa bai ce Mata komai ba


To A taikaice dai rikon Ayuba ya dawo Hannu Gwaggo Shatu yana da Shekara Uku ,Sharasa Bakwai a duniya Allah ya dauki Ran Malam Tanko Sakamakon Rashin Lafiya tafarar daya,

Ayuba ya shaqu da Mahaifinshi Sosai Shiyasa Yaji Dacin Mutuwarsa,inda Kiyyaya da tsana gami da tsangwama,ce Tsakaninsa da "Yan Uwansa don ko da a kazo rabon Gado Sallau da Lantana ,Cewa Sukayi Ayuba Bashi da gadon Ubansu Domin Ba Dan Halak! Bane ,Sai da Malam Liman ya tsaya tsayin Daka A kan Lamarin Sannan A ka fitarwa da Ayuba gadonsa a gidan Ubansa.
Duk Rayuwarshi gidan Liman yake yin ta ,inda ya kasance *Yaro* mai zafin Nema,a wancan lokacin duk Abinda ya ta6a sai ya zama kudi.

Sallau ya sakoshi a gaba Da bakin ciki da hassada ,duk inda yasan yana zuwa Nemansa sai ya je ya batashi.
[04/05, 03:14] +234 808 996 5176: πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€
*🐾GIMBIYA BALARABA*🐾
πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€πŸ§πŸ»β€β™€


*✍🏻Writting by*
_Binta Umar_
*MAMAN ABDUL WAHABU*

_*ZAMANI WRITES ASSOCIATION*_🀝🏻

*πŸ…Ώ18*

_Bissimillahi_



A lokacin Sallau yayi Aure inda ya Auri "Yar yayar Lantana Mai Suna Fatsima suna kiranta da (Uwa!) Yarinya ce Mara kunya inda bata ganin girman kowa ,babba da Yaro ,Har Mahaifiyarta fito Na fito take da ita,Bata da Aiki sai yawon tallace Tallace to har a

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment