Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

RIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Biyar (5)
Part A

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana

Ina Yima Daukacin Mutanan wannan gida barka da wannan lokaci Dafatan Muna lafiya
Mun kammala littafi na hudu a baya yanzu zamu cigaba Insha Allah

Labari Ya isowa Shagala Cewa🥰
Marubucin yaci gaba da cewa...

KO DA GANIN HAKAN SAI DAKARUN SARKI TARYAN SUKA BISHI domin su kamoshi, dan su a zatonsu ma so yake ya gudu.
Nan fa aka kasa tsere tsakani jarumi Imhal da dakarun sarki Taryan.
Su kuwa dakaru birnin Kisra masu rakiyar gawar gimbiya Lamirat ko da suka ga jarumi Imhal ya durfafosu a guje rike da takobi da garkuwa sai su ma suka zare makamansu suka tsaya cak suna jiran isowarsa.
Da isowar Imhal sai ya tsaya cak ya dubi dakarun sarki Gurzalu ya ce, ba yakı na zo yi ba kawai nazo ne na ga gawar gimbiya Lamirat. Ko da jin wannan tambaya sa sarkin yaki ya yi wuf ya matso gaban jarumi Imhal ya dubeshi a fusace ya ce, sarki bai bamu umarnin mu bar wani ya ga wannan gawa ba don haka sa dai kayi hakuri.
Ko da jin haka sai jarumi Imhal ya juya kamar ya hakura amma sai ya juyo cikin bazato ya daka tsalle sama ya doki kirjin sarkin yaki yayi sama da baya ya fada kan sauraran dakarunsa, ya sake daka tsalle sama da nufin ya dira akan keken doki dake É—auke da gawar Gimbiya, kawa sai yaji an yi masa wani wawan naushi a kirjinsa, saboda karfin naushin sai da yay sama sosai sannan ya fado kasa tamkar takarda aka jefo sannan ya fado kasa tim yana kakarin amai.
Yana dago da kansa yayi arba da sarki Gurzalu tsaye a gabansa cikin shigar yaki. A cikin tsananin mamaki Imhal ya mike tsaye ya kuma kurawa sarki Gurzalu idanu ya kasa cewa komai.
Kawai sai yaga hawaye ya zubowa sarki Gurzalu ya dubeshi ya ce akan wane dalili zaka bukaci ganin gawar 'yata alhalin kai ne ka kasheta. To ka sani cewa ka rura wuta kiyayya a tsakaninmu ninkin ta da sau dubu kuma lallai sai na Ä‘auki fansar kisan da ka yiwa "yata a gobe idan har ka rayu a wannan gasa.
Ko da sarki Gurzalu ya Zo nan a zancensa sai kan jarumi Imhal ya daure ya kamu da tsananin mamaki. Shi dai a saninsa bai kashe gimbiya Lamirat ba to amma kuma yanzu ga ta a cikin akwatin gawa.
Ai kuwa in dai tana raye babu yadda za a yi a sata a cikin wannan akwati a rufe tunda ba za ta shaki numfashi ba.
Nan take jikin jarumi Imhal ya yi sanyi ainun ya juya da baya a lokacin da dakarun sarki Taryan masu tsaronsa suka karaso daf da shi suka kewayshi.
Nan dai suka sashi a gaba suka har aka isa filin gasar da shi a lokacin da sarki Gurzalu ya bisu da kallo kawai.
Filin gasar ya cika ya batse da 'yan kallo, attajirai, sarakai da manyan masu fada aji a nahiyar gaba daya.
Babban abin da ya daurewa kowa kai shine tun da aka fara wannan gasar kambun jarumta ba a taba cikowa irin ta yau ba domin har akan katangar filin gasar mutane ne a zazzaune, ko ina ka duba babu masakar tsinke sai dai kaga kawunan bil adama rututu ba adadi.
A wannan lokaci sarki Taryan na zaune a can saman gini inda ya saba zama tare da 'yarsa gimbiya Shumaira amma sai hangen bakin kofar shigowa yake domin yayi matukar mamaki da bai ga sarki Guzalu ba a filin gasar. Har ya yunkura zai kira wani badakare nasa ya.aikeshi yaje ya dubo sarki Gurzalu sai ga sarki Gurzalun ya shigo cikin filin, dakaru na take masa baya, daga can kuma sai gashi an shigo da jarumi Imhal, ai kuwa sa filin gasar ya rude da shewa, aka fara buga ganguna ana kodasu gami da yi masa kirari.
Har sai da sarki Gurzalu ya je ya zauna kusa da sarki Taryan, shima jarumi Imhal ya shiga tsakiyar filin gasar ya tsaya sannan aka buga tamburan fara gasa.
Nan fa kowa ya zuba idanu izuwa kofar da jaruman gasa ke fitowa domin a ga ko wanene jarumin da zai kafsa da jarumi Imhal a wannan zagaye na hudu na gasar.
Tsawon dakika casa'in da biyu shiru ba a ga kowa ba. kwatsam sai ga sadauki Marrasu ya fito yana taka kasa kamar wani toron giwa, yana rike da wadansu zabga zabgan adduna guda biyu.
Ko da ganinsa sai gaba dayan "yan kallo suka mimmike tsaye suna bude baki saboda tsananin mamaki. Kai wasu ma firgita suka yi suka fara yunkurin guduwa domin a zatonsu fatalwa ce ta shigo fili.
Abu daya ne ya sa mutane suka dan nutsu suka fasa gudu, ba komai bane face ganin tabon katon dinki akan makoshinsa. Nan fa hankalin attajiran caca ya dugunzuma musamman wadanda suka zabi jarumi Imhal a matsayin gwaninsu.
Ko da jarumi Imhal ya yi arba da sadauki Marrasu sai ya firgita ya ji Zuciyarsa ta buga da ƙarfin gaske a karon farko tunda ya shiga wannan gasa. Ga shi dai sauran jaruman da ya fafata da su a baya sun fi sadauki Marrasu girma da kwarjini amma kuma kallo daya mutum zai yiwa sadauki Marrasu ya gane cewa sadauki ne na gaske domin kirar zaki gareshi saboda yana da kirji mai fadi da tudu cike da gashi kuma gaba dayan jikinsa a murde yake cike da jijiyoyi da kwanji.
Kai tsaye sadauki Marrasu ya durfafi inda Imhal ke tsaye, ko da ganin haka sai Imhal ya fara dan ja da baya baya. Ai kuwa sai attajiran gasar da suka zabi Marrasu suka fara ihu suna murna saboda sun san waye sadauki Marrasu, sun san irin tsananin zafin namansa da karfin damtsesa.
Yayin da marrasu ya ga jarumi Imhal ya tsorata da shi sai ya kyalkyale da dariya, lokaci guda kuma ya turbune fuska ya dakawa Imhal tsawa, ya ce, guje gujen me kuma kake yi. Shin ba kai ne jarumin da ya kashe sadauki Darwaz da sadauki Zambaru ba?
AA Misau ke Magana Wadannan sadaukai manyan yarana ne na jikina
don haka zan dauki fansar ransu a yau a kanka, a gobe kuma na dauki fansa mafi girma akan maigidanka sarki Gurzalu.
Ko da gama fadin hakan sai sadauki Marrasu ya daga kansa sama ya dubi inda sarki Gurzalu yake, suna hada ido sai suka hau hararar juna, kowannansu jikinsa ya kama tsuma, fuskokinsu na yatsiñewa kamar su rugo izuwa kan juna su kacame da yaki.
Kai da ganin irin kallon da suke yiwa juna kallo ne na tsananin kiyayya da gaba.
Sadauki Marrasu ya dauke kai, ga barin kallon sarki Gurzalu ya dawo da hankalinsa izuwa kan jarumi Imhal sannan ya gyara tsayuwarsa yana mai bude hannayensa rike da wadannan adduna guda biyu.
Shima jarumi Imhal sai ya gyara, tsayuwarsa ya rike garkuwarsa daidai kirjinsa kuma ya daga takobinsa sama, duk su biyun suka kame kamar gumaka kuma suka kurawa junansu idanu sunamnazarin irin harin da zasu kai.
Ko da ganin haka sai jama'a suka rude da shewa kowa na koda gwaninsa.
Ba zato b a tsammani kuma sai jaruman biyu su ka taso da gudu a lokaci.guda izuwa kan juna. Suna haduwa sai suka kacame da azababben yaki, ya zamana cewe suna kaiwa junansu sara da suka ciki i tsananin zafin nama, juriya da jarumta ka ta ban al'ajabi da ban sha'awa.
Al'amarin da ya yi matukar burge kowa ke nan, aka yi tayi musu tafi da jinjina.
Ana fara wannan gumurzu ne hankalin jarumi Imhal ya dugunzuma ainun domin tunda yake karo da maza bai ta6a jin sadauki mai karfin damtse gami da zafin nama ba kamar sadauki Marrasu. Tababs idan har suka dan jima a cikin wannan yanayi zai iya galabaitar da shi ainun, ya gama dashi farat daya.
Nan fa jarumi Imhal ya rude kuma ya kidime domin ya ma rasa irin dabarar da ya kamata ya yi domin ya ceci kansa daga hannun sadauki Marrasu har ma ya sami nasarar kasheshi.
A can bayan garin birnin Misra kuwa lokacin da dakarun birnin Kisra wato suka ci gaba da tafiya sai da suka shafe rabin sa'a suna tafiya cikin kwanciyar hankali ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Kwatsam sai suka jiyo motsi mai yawa ta gaba ta baya kuma gabas da yamma, kudu da arewa an durfafosu ta cikin duhuwar ciyayi.
Sarkin yakin Gurzalu ne ya fara zare takobinsa kuma ya bada umarnin da a tsaya.
Nan take kuwa, sauran dakarun nasa suka tsaitsaya suna masu zare takubbansu kuma suka yiwa keken dokin dake dauke da gawar Gimbiya kawanya don bashi tsaro.
Faruwar hakan ke da wuya sai wadansu dakarun sumame suka dako tsalle daga cikin duhuwar ciyayi suka dira daf da su.
Gaba dayan dakarun suna sanye da bakaken tufafi ne kuma sun rufe fuskokinsu, idanunsu kadai ake iya gani, kowannasnu na dauke da makaman yaki. Hatta takalman kafafunsu bakake. Sai da dakaru suka gama dirga a gabansu sarkin yaki kimanin su dubu shida suka yi musu kawanya ba tare da sunyi yunkurin cutar da su ba, sannan sarkin yaki ya dubi shugabansu cikin nutsuwa ba da fargabar komai ba ya ce da shi.
Me kuke bukata daga garemu Dukiyarmu kuke so ko rayuwarmu?
Ko da jin wannan tambayar sai shugaban dakarun Sumamen ya yi murmushi a cikin boyayyiyar fuskar tasa ya ce ba ma bukatar daya daga cikin abubuwa biyun da ka fada. Abin da muke so kawai shine ku bude mana akwatin gawar da kuke dauke da shi muga gawar da ke ciki domin mu tabbatar da ko gawarce ko mai rai.
Ko da jin wannan batu sai sarkin yaki Gurzalu ya bushe da dariya sannan ya ce, ai cire silin gashi a cikin tandun mai yafi wuya akan abin da kuke bukata.
Ko da gama fadin hakan sai sarkin yaki ya sa aka dauko wannan akwatin gawa aka bude ta, ai kuwa sai ga gawar Gimbiya Lamirat a ciki ko alamar rai babu a tare da ita.
Shugaban dakarun sumame ya zo Kan gawar ya tsuguna ya kara hancinsa daidai hancin gawar har tsawon yan dakiku amma sai ya ji shiru babu alamar numfashi. A sannan ne ya mike tsaye ya juya da nufin su tafi shi da yaransa sai sarkin yaki ya sha gabansa ya ce da shi idan ka koma wajen maigidanka ka gaya masa cewar maigidana murucin kan dutse ne bai fito ba sai da ya shirya.
Ko da jin haka sai shugaban dakarun sumamen yayi murmushi ya ce, ai ba a sanin maci tuwo sai ta kare, daga haka Shugaban dakarun sumamen bai sake tankawa ba kawai sai yayi wa yaransa yaransa inkiya suka ruga izuwa cikin duhuwar bishiyoyi suka bace bat tamkar basu taba wanzuwa ba a wajen ba.
AA Misau ke Magana
A can filin gasa kuwa al'amura sun sauya sai kuma suka rincabe domin kuwa lokacin da aka shafe kusan rabin sa'a ana wannan bakin artabu tsakanin jarumi Imhal da sadauki Marrasu sai jarumi Imhal ya fara gajiya ya zamana cewa da kyar ma yake iya kare hare haren sadauki Marrasu har takai cewa ma yana faduwa kasa. Cikin hanzari yake mikewa tsaye ya ci gaba da kare kansa.
Shi kuwa sadauki Marrasu lokacin ne ma yake kara zage damtse
tamkar a sannan ya fara yakin kuma a sannan ne ya fara samun damar kaiwa Imhal naushi da bugu, hannu da kafa har ya hada masa jini da majina a hanci da baki.
Nan fa jarumi Imhal ya fara shiga wani irin mugun hali, ko da sadauki Marrasu ya ga yana samun wannan nasara sai ya ji kansa ya kara girma wato ya dauki girman kai, maimakon ya yi amfani da makami ya kashe Imhal sai ya ci gaba da dukansa gami da naushinsa, duka yake mashi na nuna bambanci tamkar
babba da yaro. Sai dai kaga Imhal yana layi jini na feshi ta cikin bakinsa.
Ko da gimbiya Shumaira taga jarumi Imhal ya shiga wannan hali sai ta kamu da tsananin bakin ciki ta kuma fashe da kuka. Gaba daya mutanen dake filin gasar ma sai da suka lura da halin da take ciki.
Lokacin da sadauki Marrasu ya ga yayi laga laga da jarumi Imhal yanda ba zai iya kare kansa da komai ba sai ya cafi makoshinsa da hannu daya ya dagashi sama ya shakeshi. Nan da nan idanun Imhal suka yi luhu luhu ya fara kakarin mutuwa.
A daidai wannan lokaci ne sadauki Marrasu ya dubi sarki Gurzalu suka hada idanu ya yi masa nuni da cewar shima haka zai yi masa.
Nan take ran sarki Gurzalu ya baci ainun, zuciyarsa ta kama tafarfasa kamar zata kone. Jikinsa ya kama kyarma ya ji kamar ya mike zumbur ya ruga izuwa cikin filin gasar a yi dashi.
Ko da lmhal ya ji numfashinsa na neman daukewa gaba daya sai ya yi wani irin mugun yunkuri iya ragowar karfinsa ya doki fuskar sadauki Marrasu da tafin kafarsa ta dama. Saboda karfin dukan sai da Marrasu yaga taurarin wuya kuma ya dimauce a lokacin da hancinsa da bakinsa suka fara zubar da jini, bai san sa'adda ya saki wuyan Imhal ba ya tsuguna kasa yana ganin dishi dishi.
Imhal ya fadi kasa a matukar galabaice yana numfashi, da karfi kamar ransa zai fita.
A wannan lokaci ne filin ya rude da shewa da tafi kuma aka cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda jarumi Imhal ya sami karfin da ya ceci rayuwarsa.
Cikin tsananin karfin hali jarumi Imhal ya mike tsaye yana dafa kasa kuma ya sunkuya ya sunkuci garkuwarsa da takobinsa amma sai ya kama rangaji a tsaye saboda tsananin jigatar da ya yi don idanunsa ma lumshewa suke yi yana gani dishi dishi.
Shi kuwa sadauki Murrasu sai da ya shafe sama da dakika arba'in sannan ya dawo cikin hayyacinsa. Ko da ya sa hannunsa guda ya shafi hancinsa da bakinsa ya ga jini sai ya takarkare ya kwarara uban ihu cikin tsananin fushi da kunar zuciya.
Cikin hanzari ya ruga izuwa inda ya yarda addunansa guda bıyu ya suresu sannan ya sake rugawa izuwa inda jarumi Imhal ke tsaye.
Ko da jarurni Imhal ya ga sadauki Murrasu ya nufoshi gadan gadan rike da makamansa a fusace sai shima ya tareshi suka ruguntsume da sabon azababban yaki tamkar ma a sannan suka fara gumurzun.
Wohoho bala'i ba a sa masa rana, kuma wanda ya iya ya huta. Tunda aka kirkiri wannan gasa ta kambun jarumta ba a taba yin wasan da 'yan kallo suka more ba irin wannan domin sun ga inda tsagwaron yaki, karfi da jarumtaka ke aiki.
Sai da jarumi Imhal da sadauki Marrasu suka dada shafe wata rabin sa'ar suna kaiwa juna sara da suka cikin bakin zafin nama, ammna a tsawon rabin sa'ar sau daya jal jarumi Imhal ya sami nasarar saran sadauki Marrasu a cinya.
Shi kuwa Marrasu sai da ya sari Imhal sau shida ya sareshi a kirji, gadon baya, cinyar hagu da ta dama, sannan a damtsen hannun
hagu da na dama.
Ga shi dai jini na ta zuba a jikin Imhal jiri na dibarsa amma saboda bakin naci bai yarda ya je kasa ba, sa'ar da ya samu kawai ita ce saran da ya yiwa Marrasu a cinya ya yi zaurfi har ta kai cewa Marrasu baya iya taka kafar sosai sai janta yake yi kuma shima jini na dibarsa amma saboda naci dada kaiwa Imhal hare hare yake iya karfinsa, ya rinka kuntatashí domin ya karar da karfinsa duka ya hallakashi cikin gaggawa.
A wannan lokaci hankalin kowa da kowa a filin gasar ya dugunzuma ainun domin babu wanda yake da tabbacin cewar ga jarumin da zai lashe wannan gasa, sai dai fa kowa ya yí mamaki
matuka da irin taurin ran jarumi Imhal da irin tsananin kokarin da ya ke yi.
Tabbas ya nuna cewa shi jarumi ne kuma daban a cikin jarumai domin ba a taba ganin mai irin juriyarsa da nacinsa ba tunda ga shi a zahiri an fishi karfi da jarumtakar amma an kasa gamawa da shi.
Shi kansa sarki Gurzalu sai da ya sha jinin jikinsa ya ce a cikin ransa tabbas ko nine na hadu da wannan yaro komai zai iya faruwa.
Sarki Gurzalu na ckin wannan tunanin zuci ne ya ga sadauki Murrasu ya shammaci Imhal ya gabza masa wawan naushi a kunnensa na dama. Nan take Imhal ya sulale kasa sumamme.

Topah Nima Kuma Ganin Suman Nan Yasa naa dakata kyam a wannan waje kuma nake cewa sai wani lokaci idan Allah yakaimu

Karku manta zaku iya Samun mu a WhatsApp group dinmu
Ta hanyar wannan link din
👇👇👇👇👇

https://chat.whatsapp.com/E0GMznXcaxwC0avNVdF30Q

AA Misau ke Magana


RIJIYA GABA DUBU
Littafi Na Biyar (5)
Part B

Na Abdulaziz Sani M Gini
AA Misau ke Magana
Labari Ya Isowa Shagala Cewa 🥰
Marubucin Yaci gaba Da cewa

Nan take Imhal ya sulale kasa sumamme.
Maimakon Marrasu ya soke Imhal da addarsa guda ya kasheshi nan take sai.ya daga addunansa sama ya kama kururuwa yana ihun farin ciki, bisa ganin cewa ya gama lashe wannan gasa.
Abin da bai sani ba shine yayi babban kuskuren da nadama a rayuwarsa.
Sai da Marrasu ya dubi 'yan kallon da ke gabas da yamma, kudu da arewa yana ihu da kururuwa sannan ya juyo izuwa kan Imhal ya sunkuyo da nufin ya sokawa Imhal adda a cikinsa.
Ko da ya kai masa suka sai kawai ya ga Imhal ya goce, addar ta nuse a cikin kasa. Kafin Marrasu ya yi wani yunkurin tuni Imhal ya zaro wata siririyar wuka a kugunsa ya sokawa Marrasu a idonsa na hagu. Take wuka ta lume ta faso ta keyarsa. Marrasu ya kurma uban ihu yayi baya taga taga kamar zai fadi kasa amma sai ya tsaya cak ya sa hannunsa na hagu ya zare wukar daga cikin kwarmin idonsa, sai ga kwayar idon ta fado kasa, jini na feshi. Duk da haka sai da Marrasu ya kaiwa Imhal mugun taku a kirji amma sai Imhal ya mirgina can gefe daya ya dafa kasa da hannu daya ya yi sama.kamar sifirin. Kafin Marrasu ya daga kansa sama ya dubi Imhal tuni Imhal ya sa takobinsa ya sare masa hannu kuma ya lafta masa sara a kasan cibiyarsa.
Take cikin Marrasu ya farke sai ga hanjin cikinsa ya zazzago. Nan take ya fadi kasa matacce. Koda ganin haka sai filin ya rude da shewa da hayaniya. Hatta sarki Gurzalu ma bai san sa'adda ya mike tsaye zumbur ba cikin farin ciki ya kama yi masa tafi.
Shi kansa sarki Taryan sai da ya ji yana matukar farin ciki da lashe gasar da jarumi Imhal ya yi duk da cewar zai.yi gagarumar asara ta miliyoyin dinare kuma irin asanar da bai taba yinta ba.
Ana cikin wannan shewa da farin ciki ne aka ga jarumi Imhal ya sulale kasa. Suma ya yi ko mutuwa yayi babu wanda ya sani.
Ko da ganin abin da ya faru da jarumi Imhal sai gimbiya Shumaira ta dafe kai da hannayenta biyu ta kurma uban ihu kuma ta sulale kasa sumammiya.
Nan fa sarki Taryan ya ciccibeta yana mai kwalawa likitansa kira ya ruga da ita izuwa cikin gidan sarauta.
Shima jarumi Imhal sai dakaru suka daukeshi suka ruga da shi izuwa cikin gidar sarautar a lokacin da likitoci suke lullubesh ana gudu da shi ana kuma yi masa magan domin a gano ko yana raye ko ya mutu.
Kai a wannan rana sai da gaba daya birnin ya Misra ya zama kamar makabarta, wato yayi tsit kamar mutuwa ta zo kasuwa kai ka ce babu mutane a garin.
Bakomai me ya janyo hakan ba face rashin sanin halin da mutane biyu ke ciki Jarumi Imha da gimbiya Shumaira wadanda aketa jita jita akansu. Wasu Suce duk su biyun sun mutu Wasu kuma suce ana kikarin ceto rayuwarsu.
Da yawa daga cikin mutane cewa suke babu yadda za ayi jarumi Imhal ya tsira da rayuwarsa sakamakon manyan raunikar dake jikinsa har guda shida Haka dai aka ci gaba da zama a cikin wannan dari dari amma har rana ta fadi babu wani cikakken labarin abin da ake ciki.
A can cikin daji kuwa dakarun dake dauke da akwatin gawar gimbiya Lamirat basu ya da zango ba har sai da rana ta fadi, gari ya yi duhu sannan suka tsaya a cikin wani daji mại fadi suka sauka a gaban wata karamar korama, mai dauke da wani ruwa garai garai mai ban sha'awa wanda ke kwaranya daga kan wadansu dogayen duwatsu. A sannan ne kowa ya sauko daga kan dokinsa, aka ci aka sha kuma aka kafa tantuna.
Wannan akwati kuwa mai dauke da gawar gimbiya Lamirat sai aka fiddota daga cikin keken doki aka sanyata a cikin tantin sarkin yaki don tabbatar da tsaro, duk da haka kuma sai da dakaru dubu suka kewaye tantin.
Ashe duk abin da ke faruwa da Gimbiya Lamirat likitan sarki Gurzalu ne ya bata wani magani ta sha wanda zai sata yin barci mai nauyi hàr na tsawon kwanakin da za a isa birnin Kisra da ita ba tare da ta farka ba kafin cikar lokacin, kuma babu yadda za á yi a gane cewa tana da rai domin ko alamạr numfashi ba za a gani ba a tare da ita.
Kafin sarkin yaki ya baro birnin Misra sai da sarki Gurzalu ya gaya masa cewar da zarar sun isa birnin Misra a tsaye gimbiya Lamirat a cikin turakarta kuma a daureta da sarkoki a hannu da kafa yadda ba zata iya kwance wa ba domin tana farkawa zata yi yunkurin dawowa birnin Misra saboda ta kamu da tsananin son jarumi Imhal.
Ai kuwa sarkin yaki yana kula da wannan umarni, don haka bai yarda an shafe sama da rabin sa'a ba a bakin wannan korana ya sa aka tashi aka ci gaba da tafiya.
A cikin kwanaki

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

5 Comments On RIJIYA GABA DUBU 5
avatar
abdulmudallib-8

1 year ago

Reply

I already paid N1000 why don't you allow me to download the document

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I an sorry this is a technical issue i am resolving it now you can download

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I an sorry this is a technical issue i am resolving it now you can download

avatar
abasu-kala

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

I just check now i am unable to saw your payment can you send me receipt if the payment through WhatsApp 08140419490

avatar
taskar

1 year ago

Reply

Replying to abdulmudallib-8

Alhamdulillah now you can check and see that your subscribtion is active, and you can download any of your desire book here. feel free to contact me anytime you face any minor or big issue related to our site Thanks for using our services

Please Login or Register in order to submit comment