Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bude wani kundi dake kusa dashi ya jaro takarda mai kunshi da rubutun ajimi da kuma bayani da fassarar boko a bayan tajardar Www.bankinhausanovels.com.ng

Gashi, kamar dai wancan ne da nabaka ka dawo min da shi” Adamu ya karba ya shiga dubawa, sai can ya dago ya dubi Malam, “Eh na gane irin wancan ne?” Malam yace, – “Ai dama ba ka kawo min turaren ba, koka salwantar nabaka wani?”’ Adamu ya girgiza kai, – : “Yana nan Malam” ° : Malam ya dubi agogo,–: ~~” “Shikenan sai kaje, abinda baka gane ba ka dawo gobe, yanzu dab ake da fara kiran salar“ magariba. Adamu ya fara godiya yana ” kokawar sa hannu a aljihu,, cikin ransa yana fatan Allah ya lsa kamar wancan lokacin Malam yace ya bar shi, don Allah ya sani duk bogi ne sa hannu a aljihun, naira hamsin ce a aljihun nasa. “A’a ka bar shi kawai, zamu hadu wani lokacin? In ji Malam, addu’ar Adamu ta ci kenan. Ya Kara wata godiyar sannan suka tashi -gaba daya Adamu nayi masa sallama. Www.bankinhausanovels.com.ng

*************

“Na kira ka ne in ji yadda aka yi ka san _gaibu”

Ko gaisawa da Yayansa ba suyiba, ya tare shi da wannan maganar cikin daure fuska, alhalin takanas ya aika aka yi kiransa._ –

Ya zaci ma wani abin kirk ne ashe wulakancin da aka saba za’a yi masa.

Kansa na sunkuye yana zaune kan kujera yayin da Yayan nasa ke tsaye Kerere a kansa. Sai dai duk bacin rai da rashin kunyarsa ya hadiye kayansa a ciki. Jiki a sanyaye ya daga kai ya dube shi,

“Alh, Ban gane na san gaibu ba fa, a ina na

fadi hakan?” Yayansa ya amsa masa ba tare da ya juyo ya dube shi ba, Shekaranjiya ka fada wa Hajiya”™ “Na ce mata gobe za a tashi kiyama?” ’ Ya amsa cikin cin mur da dakewa. Www.bankinhausanovels.com.ng Dama tun shekaranjiya bayan ya ji kudurin Husna na kin auren mara sana’a ko kuma mai karamar sana’a ya ji ya tsani kowa a duniyarsa, musamman ma Yayan nasa wanda ya fi kowa gina masa Katanga da sana’ar, kuma tun shekaranjiyan yake atisayen yiwa kowa bore, bai yarda a shigo rayuwarsa a tauye masa Husna a cikinta ba. “Karatu ne na bar shi kuma babu shegen da ya isa ya kuma sawa na yi Kalmomin da yaké ta maimaitawa kenan tun daga jiya zuwa yau,.da ma yanzu da yake gaban Yayansa cikin zuciyarsa.

‘Yayan na sa ya sha mamakin wannan baKar maganar da Adamu ya yarfa masa, amma dai ya hadiye yadda ta bata masa rai, yana kallonsa kai tsaye ya ce, ‘ “To ko hakan ma ka fada mata ne? gaskiya na ganka da wannan zabgegen carbi mai ‘ya’ya dubu kana neman gafarar ubangiji…

Takaici ya kama Adamu na ganin an canja – masa ma’anar wuridi..

“Ni ba Istigfari nake ba” , Ya tare Yayan a kuntace.

Www.bankinhausanovels.com.ng

“Oh Hailala kake kenan, musamman tunda gobe za’a tashi kiyama, shi ne kake sabunta shahada?” !

Adamu ya sake yin fuska yana murza ‘ya’yan carbin hannunsa daya bayan daya tare

da yin mus-mus da baki………: “Kalas! Da alama ta wannan hanyar kake iya hango abinda zai faru gobe”. In ji Yayan cikin nuna halin ko in kula.

– Har yanzu Adamu yaki ya tanka illa fuskarsa da take iyakarta na cin magani

bakinsa kuma ya dukufa da motsi. _

Yayan ya basar inda ya jira shi yayi adadin da yake bukata yana yi masa kallon tura aniya, sai da don kansa ya gaji da kallon da kuma murza carbi sannan ya ajiye, sai dai bai ce — komai ba.

_Yayansa ya fara safa da marwa a tsakiyar – _ falon cikin yanayin mazantaka,

“Hajiya ta sanar da ni cewa wai ka hango baka da abinci a karatun boko, haka ne?”

.. Adamu ya jima kafin ya tsinka. Har yanzu yanayinsa na nuna akule yake, – “Duba nayi kenan?” Www.bankinhausanovels.com.ng “Ah! To wa sani? Abinda nake tambaya tun dazu kenan rashin muhimmancina ya hana ka . bani amsa”’. – , Adamu ya dan fara mutsu-mutsu yana KunKuni,

“Ai ka ji matsalar, shiyasa ma babu amfani na batawa kaina lokacin yin karatu, domin idan zan zama Mongo park ba zaku taba yarda an halicci kwanyata da iya Kirkirar abin kirki ba”. Yayan ya Kara janye annurin fuskarsa yana. duban adamu, “Uhum! Cigaba ina jinka”

Adamu ya sake muskutawa rai a Bace yana. gyarawa. carbinsa zama, ba tare da ya dubi Yayansa ba ya ce, –

“Alh. Yadda kuke Kaddarawa ni ban iya wani abin arziKi a duniya ba, haka na kalli

kwanyata da rayuwata na gane sam babu abincina a karatun boko, don haka a daina yimin Kagen cewa na san gaibu’, “Kage? Uban wa yake maka Kage Adamu?” ‘ Adamu ya motsa ya sake motsawa cikin dauke kai, amma bai tanka ba. Www.bankinhausanovels.com.ng. Ya jima yana yi masa kallo mai fassara iri-iri, bai gamsu ba sai gashi a gaban Adamu cikin zafin nama, ya sunkuya ya dago habarsa -ya shinshina tsawon wasu sakanni sannan ya ture shi ya mike yana ja da baya cikin kallonsa, — “Babu alamun shaye-shaye a numfashinka Adamu, amma me yake cin kanka yau?” Adamu ya sake cin magani ya cigaba da jan carbinsa, sai jikin Alh. Yayi sanyi ya jima ~ tsaye yana nazarinsa cikin kasa’ hankula, bai ~ kai ga warwara ba ya zauna kujerar kusa da – Adamun ya dafa hannunsa yayi masa Magana da tattausar murya, ; , “Ka kasa gane nufina Adamu, Kudurorina akan ka sami kyakkyawan ilmi mai zurfi duk ba ni zasu amfana ba kai zasu amfana, babbar sakadanre bata isa komai ba da har zaka mallaketa kaja ka Bame, ina laifin ko ‘yar diflomar ka yarda ka samu tunda ka fara?” Yayi jiran cewar Adamu, amma har yanzu babu alamar zai tanka, sai dai ya rage cin magani da yake. Www.bankinhausanovels.com.ng Alh. Bai yi fishi ba ya cigaba da magana ‘ cikin taushin murya da sassaukan harshen fahimta.

| “Hajiya Uwa da mahaifinmu Mal. Musa mu biyu kadai suka mallaka wato ni Kabiru da kai Adamu wanda na bawa tazarar sama da shekaru goma., Lokacin kurucityata kafin kai’ kai bai waye da neman ilmin boko sosai ba don haka ban sami hasafinsa ba, lokacin taka ‘Kuruciyar kuma kuncin rayuwar . talauci . ya hana su maida hankali.akan karatunka” – Adamu ya: muskuta alamar nuna gajiyawa da gundura da wannan dadaddan tarihi da kullum Yayansa ya tashi yi masa nasiha sai ya hado masa da shi, sai kace mai gwada masa shiga kabari a fito. . Alh. Ya fahimci gundurarta Adamu amma sai ya share shi ya cigaba da maganarsa,

“Tun kana mitsitsinka na fara buga-buga ta neman kudi, yau wannan sana’ar gobe waccan . har ajalin mahaifinmu ya riske shi. Duk da ina da sauran Kuruciya bai hana nauyinku kai da’ Hajia’.ya dawo kaina wanda hakan ya sani Kara Www.bankinhausanovels.com.ng zage Kwanjin neman na kai, ‘Allah kuma ya dafa min har ya tsayar min da sana’ar nan ta safarar Goro daga kudu zuwa arewa, har kawo – yau da rufin asirin Allah ya lullube mu ta silarta har ni da Haj. mun shiga sahun wadanda za’a kira Alhazai” Ya dan nisa kamar alamun rashin alamun abin fadar ne-ya Kare har Adamu yana murna da tsaki cikin ransa, amma sai murnar ta koma _ ciki lokacin da Alh. Ya sake nisawa, Ba gorin kushe nake maka ba Adamu, amma tabbas na ci kashinka yadda idan ka bijire min ko kayi-min butulci Allah zai bi kadin hakina, na soka shigen son da Uba yake wa dansa, shiyasa burikana akan ganin cigaban rayuwarka suka yi Kamari. Burina ka zama likita,, amma da naga hankalinka baya kan katatun sai na sauke farashi, aKalla ko malamin makaranta ka zama. Haka kawai ni dai naji akwai buKatar ka tanadi ilmin ko da kuwa kafi sha’awar zama dan kasuwa, shiyasa ma na bayar da shawarar ka karanta kasuwanci kamar – yadda ka yarda ka fara bayan ka share shekaru |da dama kana zaman kasha wando. Www.bankinhausanovels.com.ng Na ci burin ka tsaya da kafarka yadda ko

bayan raina zaka iya cigaba da daukar nauyin kanka da mahaifiyarmu sannan ga nawa iyalin wadanda basu da kowa sai kai……”

Adamu ya muskuta cikin mita da kunkuni, inda yake cewa, “Kana tunanin abi maka kadin hakkinka a kaina, amma ka kasa tuna za’a bi nawa hakKin a kanka saboda. takurawar .da kayi. min da cukwikwiye ni sai nayi wata rayuwa wadda bani da sha’awarta saboda kawai na dauki nauyin rayuwar iyalinka inka rasu….” “Me kake cewa?” Alhaji ya tambaya cikin fuskar mamaki. “Cewa nayi Allah ne kadai ya san gawar fari” Adamu ya amsa cikin nuna gundura. . Alhaji Yayi kasake yana kallon Adamu, ya shafa abin dorawa ya rasa, sai kawai ya. rangwada kai yayi shiru. Hakan da Adamu ya gani ya sanya jikinsa . Yin sanyi, ya dan yi kame-kamensa sannan ya fara magana, Www.bankinhausanovels.com.ng “Wallahi duk na fahimce ka Alhaji Amma kai ma abind aka kasa ganewa shi ne, shi . karatu ba a sanya masa Karfi dole sai kwanya — da ra’ayi suna da sha’awa, Ni kwata-kwata idan ina da ra’ayin karatun boko Allah ya tsine min, shiyasa ma shekarun nan biyu na dinga samun kari oba, kuma wannan shekarar ma idan an matsa min Kila abin yafi haka..” “Allah ya kyauta” .° Alh. Ya fada cikin alamun gajiya da takaici. Suka jima cikin shiru kafin alh. Ya nisa, “Shikenan maganar karatu a barta in Allah . yaso amma fada min, menene Kudurinka, ~ menene burinka, menene ‘abinda kwanya da ra’ayinka suke sha’awa ba wanda ake musu~ sha’awa ba?” ai Da sauri adamu ya amsa, “Ni .sana’a nake so, Allah ya sani. ina so nayi aure” Zuciya tazo wa Alh. Wuya, amma ya dinga shanye kayarsa har ya hadiye fiye da rabinta. “Na san kana son aure tun tuni, amma a tsammanina zan iya tare ka har lokacin da idan Www.bankinhausanovels.com.ng kayi ba zai zame mana matsala ba, ban sani ba ashe Karya naci na kwana da yunwa” Adamu yayi shiru.

– Can.jimawa Alh. Ya sake nisawa, “An ce min Salma na sonka, in haka ne gara ayi ‘yar gida musamman da yake baka da _ KwakKwarar sana’a sannan ka san komai akanta, “yar yar mahaifiyarmu ce da ta rasu tun tana karama riKonta ya dawo hannuna don haka ta san ciki da bai a samu da rashinka kafin sana’arka tayi Kwari’. . Ba don wata fuskar tafi gaban mari ba babu abinda zai hana Adamu tura ashar. Sai kumburi yake kamar ya fashe ya tari numfashin yayan nasa, . “Wa yayi min sharrin cewa ina son Salma?” .“Cewa aka yi Salma na sonka, ba cewa aka yi kana son Salma ba” . . Alh. Ya amsa cikin tausasawa. – Adamu ya Kara bata rai, **Wa ya fada? Ni bata taba fada min ba” Alh. Ya sake daurewa Www.bankinhausanovels.com.ng “Sa’ adatu ta sanar da ni Babu kunya Adamu ya sake tare numfashin Alh. a sike, “Gaskiya ni bana sonta, wata yarinya nake so na aura” Alh. Ya gama kai wa bango, tsawon lokaci yana jinjinawa, “Ba ka sonta?” Adamu baitanka ba, iyaka ya cafko carbinsa ya fara ja. . } ~ Alh. Ya sake kada kai, “To da kyau! Nan ma an wuce, na yarda kaje ka auro yarinyar da kake so kuma kake son aure. Sai mu fado maganar sana’a, wacce kwanya da ra’ayinka suke sha’awa?” Hantar cikin Adamu ta kada daya fahimci turin Jeka-ka-mutu Alh. Ya shirya yi masa, ko kuma debi inga hankalinka, Ta ina zai sami sana’a babu hannun yayan nasa a ciki, in sana’ ar ba ta aikin Karfi bace ina zai nemo jari? Yana tuno tauhidi sai ya sami harshensa na bawa Alh. Amsa, “Muna nema wajen Allah?”

To babu laifi Allah ya zaba mafi alkhairi. idan an samo sana’ar a sanar damu mu taya murna tashi kaje

***********

Hmm ko me zai faru ku dai ku kasance damu a koda yaushe Www.bankinhausanovels.com.ng

Www.bankinhausanovels.com.ng

A JIYA MUN TSAYA

To babu laifi, Allah ya zaba mafi alkhari. Idan an samo sana’ar sai a sanar damu mu taya Murna. Tashi kaje”


ZAMU TASHI

******

Garin Kano garin kasuwanci, unguwar kurawa unguwar sarakai. kuma unguwar maķotaka da kasuwar rimi bakin asibiti. – An ce duk mai makotaka da kasuwa baya tsiya, amma da alama wannan Kaulin ya tsame Adamu ciki, domin a Kurawa aka haife shi, ya girma a cikinta amma yau ya laluba sana’ar yi ya kasa ganowa ko kuma ita ta kasa ganinsa, – saboda haka kamar makotaka da kasuwar ta kasa yi masa rana. ° Bayan alhinin awa daya kacal~ wanda yayi bayan turin je-ka-ka-mutun da Alh. Yayi masa, ya dawo gida ya dinga cakuda rayuwa da mutuwa a hakuri da son Husna da kuma sauran rayuwarsa, da kyar ya wafto jarumtar tashi ya “nemo sana’a don kar ya mutu a matsayin ragon soyayya da rayuwa, tunda aikin malam ba lallai nan take zai ci ba.

Www.bankinhausanovels.com.ng Amma kaico! Kwana da yini kenan ya kulla lissafin sana’o’I sun fi a Kirga amma har yanzu ya kasa fitar da amsar ko guda, ba don rashin iyawa ko rashin sanin makamarta ba face don wadanda suke da saukin samu shi sam! Basu dace das hi ba kamar dai yadda me markade bai dace da zama mijin Husna ba. – Ya yarda tun daga yammacin jiya bayan sallamar da yayansa yayi masa’ kawo yammacin yau, Kwakwalwarsa ta fara karatun nemo mafita, hartayi digirgir amma ta fito fanko! » Kwance yake rashe-rashe kan ‘doguwar kujerar dakinsa da yammacin ranar cikin tunani a halin yanzu, sai gashi a halin zahiri an – wangale kofar dakinsa an shigo “Ho! Gayun gidan nan suna kusa?” Wani shegen takaici ya Kume shi, amma ya shanye shi ya dago kai ya dubi mai shigowar lokaci daya kuma zuciyarsa ta rubuta ~ wata addu’a tana biyawa, “Ya Allah ka tsari gatari da saran shuka, Ubangiji ka tsare ni ko hada hanya da gajeriyar mace bare ta kai ga gina mata gida in ajiyeta Www.bankinhausanovels.com.ng matsayin matar aurena, Allah ka san ni baki ne, amma bana son macen da ta fiye baki Allah ka. tsare ni da ita. Idan na ga-‘ya’ya masu idanuwa _ dakwa-dakwa Allah ka sani har jaje nake wa iyayensu to Allah ka tsare ni da macen da zata haifa min irinsu. Duk mace mai saurin murya * bana Kaunarta, Allah ka san wannan in ka jarrabe ni da irinta zuciyata zata iya fashewa…. Gaba daya Allah ka san doguwar mace nake so wankan tarwada mai, kyakkyawar fuska da kyakkyawan murmushi bana son mai yake, ina son mai kyawawan idanu mai dogon gashi, mai fara’a in so samu kuma mai suna Husna…. ita nake so, Allah ka mallaka min kayi min tsari da wannan da take tsaye a gabana yanzu’”’. . Salma ta Karasa shigowa dakin sosai tana nazarinsa tamkar wani baKonta. Dakin ya wadata da duk wani kayan more rayuwa daidai – matashi mai matsakaicin rufin asiri irin Adamu, Dakin na shimfide da shudin kafet, akwai dindimemiyar katifar sauko mu gaisa daga can_ Kuryar dakin wadda ta cika da shirgi kama da bargo kayan sawa wankakku da masu dauda Www.bankinhausanovels.com.ng litattafai har da wasu allunan rubutun sha guda biyu kamar yadda suke watse ciki da gefen akwatunan dake jere a nasu gefen ba. Daga wani gefen kuma ga fakej din kayan kallo masu dirma-dirman sifiku da kuma . Karamin firji a gefe. komai dai a dakin baya cikin hayyacinsa duk kyau kuwa da tsadarsa, can kwalbar turare nan filasan abinci, can bel nan kwalaben lemo. Abu bako a idanun Salma .*cikin dakin shi ne, wata shimfidaddiyar sallaya daga can bangaren gabas a karshen dakin “sannan ga wani jibgegen carbi zaune kan sallayar yana shan nasa sharafi. Kodayake iyakar sanin da tayi wa Adamu ma’abocin son ibada ne wato sallah akan lokaci da kuma yawan nema a wajen Allah, idan duk halayensa na kushewa ne to tabbas a nan bangaren ya sami na yabo. Ta dade da sanin Adamu tun suna yara, in dai yana jarabar son abu, to ya dinga kafa’ goshi yana fadawa Allah kenan ba dare ba rana. Lokacin da yake neman tsarin Allah da ita cikin zuci, ita kuma daidai lokacin take nazarin dakinsa sai akayi sa’a suka gama kusan lokaci daya guda, kuma kamar masu tseren Magana suka dago suka fuskanci juna, —_ “Ke matsalarki fadowa dakin mutane babu . Sallama” Ya riga ta Magana cikin matukar daure | fuska. | Duk da kusan a tare suka yi maganar ita ma ce masa tayl,“Lafiya kai da dakin naka na ganku duk a hargitse? Dayake kafin ta dire taji nasa furucin sai ta zarce da amsa masa, “Au yanzu ban yi sallama ba na shigo? Kawai dai ka ce baka ji ba ka lula cikin tunani’.na |Haba ya ji kamar zai tura mata ashar, amma ya matse ya kawar da kai, “kin manta ne, ai ba daki kika shigo ba, Turu kika shigo… : Ta wuce ta zauna kujerar dake kusa da kafarsa tana dariya, : Allah ya baka haKuri Akaramakallahu… Ya tare ta a Kufule, don bai gama fanshe maganar data sosa masa gyambo a kirji ba Www.bankinhausanovels.com.ng “Tunanainki? To Kila ma ni gabadaya baa halicce ni da zuciya ba bare a bata lokacin da zata bata wajen tunaninki” Salma ta katse shi cikin dariya da mayar da komai ba komai ba, “Kar ka damu, tawa zuciyar ta ishe mu tunana komai da ya shafe mu, yadda nake bata lokaci wajen tuna ka haka nake. Bata lokaci wajen tuna maka kaina……” -“Ba na son iskanci da wulakanci Salma… Ya sake tare ta.a zafafe saboda tsakani da Alla hadiyar bakin cikinta ya fara gagararsa. Salma ta shafe sama da minti biyar tana dariya cikin kallonsa kafin ta shanye dariyar cikin goge hawayen da dariyar ta samar mata. Ta jima tana kallonsa a nutse sannan ta tanka, “Komai ya ji a kai Adamu, gaye har gaye matsalarka daya baka san wasa ba. Wai kai a zatonka ko daura min kai a Kafa aka yi zan ja? Ai gara na yanke kafar ko ta katako ce na aro na yafa” Ya tashi zaune cikin rage damuwar fuskarsa | yana sauke numfashi, Www.bankinhausanovels.com.ng Ai kece kike neman zunguro wa mutane sama da kara, ‘yar wannan rahar da kike kin janyo manya sun sa mana ido, suna zaton son juna muke. Abin ma sam babu tsari, ko ina zan dauki gundumemiyar mace irinki in kai a matsayin mata?”’. – Duk kawaici da kai zuciya nesa irin na Salma sai da wannan maganar ta Adamu ta Bata mata rai, don haka ta jima kafin ta gama hadiye ta. Cikin murmusbin yaKe ta ce, “Kar ka damu, kai zaka samo wanda zai iya daukar irina a matsayin mace ka aura masa, na san Kila kai ne waliyyin don haka in ka tashi tallatani sai ka dinga cewa, Baka ce kuma gundumemiya™ Adamu ya dan yi saroro da jin wannan bakar maganar tata, amma dai ya takura fuskarsa kar ta bada maza, sai ma ya kada kafada nuna halin ko-in-kula, | “Ba ba’a ce ta kar uwar gizo ba Karar kwana ce, ni ba kushe ki nayi ba, ainihin halittarki na fada menene na jin haushi na? in ni-baki yi min a matsayin matar aure ba wani ai yana nan yana cin layar in ba ke ba sai rijiya”Www.bankinhausanovels.com.ng Salma ta so ta hasala, amma sai ta binne da Siyasa, “Haushinka na ji Adamu?” “Ni bana son janjanin magana don Allah” To an bar maganar’ Ta fada cikin saduda sannan ta koma bin dakin da kallo’ kusurwa bayan kusurwa musamman shimfidar sallayarsa mai jibgegen carbinsa a kai. Adamu na biye da ita da nasa idon tamkar yana gadinta ne, zuciyarsa a Kuntace domin yaĶinin wannan kallon Allah tsine uwar mai Karyar da take wa dakinsa sai ta jangwalo abinda sam bata da ruwa a cikinsa. Don haka ya katse mata hanzari, “Kin ga malama duk maganar da zata fito daga bakinki ya zamana ni da ke duk muna da hakki a cikinta, idan ba ruwanki ko ba ruwana to kar ki kawo mana ita, ato!” Ta sauke ido a kansa cikin murmushi tana jin ciwon hanzarinta da ya katsewa Idan ba idonta ke gizo ba a can kusa da jibgegen carbin nan ta hangi kwalbar turaren wurudi, cike take da fargaba amma dokokin Adamu na mata Www.bankinhausanovels.com.ng burkin tambayoyin da zata fanshe, dole ta tattare ta hadiye da cin alwashin jiran wata haduwar kafin ya kafa dokar. Ta ciro Jakarta da ke rataye a kafadarta ta zaro wasu kyallaye guda biyu na les da na atamfa ta mika masa, Amina Kawar nan tawa! To bikinta ne ya taso saura sati biyu, wannan anko ne na kawo ka sai min, kunyar Alh. nake ji wallahi kullum na dinga damunsa da dawainiya”’ Da Adamu ya kalle ta sai ya. fahimci tsakaninta da Allah take Magana, don haka ya yayyafawa ashar din da ke turereniyar -fitowa daga makogwaronsa ruwan salama ya hadiye su. Yana bin hannunta da kalllon gefen ido ya ce,“To ajiye su nan, dama jiya-jiyan nan na siyo sabuwar Gariyo tare da AK 47, dare kawai nake jira ya tsala na fita” Duk da ta gane baKar maganar-da ya cinna mata sai tayi fuska, .“Ban gane nufinka ba” Kafin ta rufe baki ya mayar mata,Www.bankinhausanovels.com.ng dama kin zo ne ki gane nufina ko kuma dan na sai miki anko?” – “Anko ya kawo ni_ Ta fada a sanyaye. Ya nuna mata Kofa, “To ki ajiye ki je za a siyo’ Ta bi umarninsa ta hanyar miKewa tare da yi masa sallama, amma maimakon ta nufi Kofa kai tsaye sai ta zarce kan sallayar nan ta sunkuya ta dauki turaren wurudin nan ta hau sunsuna. | Adamu ya Kara cin magani ya kawar da kai daga kallonta, can ta juyo ta dube shi, tana -kallon fuskarsa ta tabbatar ashar dinsa a kan harshe take Karamin motsi bakinsa yake jira ya antayo ta waje. Ta so su hada ido ko dan ta gasgata zatonta, ‘ daya Ki-sai ta haKura tare da ajiye turaren ta juyo a sanyaye kai tsaye kuma ta nufi Kofa ta. fita ba tare da ta sake tankawa ba. A soro ta tsaya domin bawa Kwallar da ta cika cikinta dammar fitowa Wani iri mugun ciwo ne ya kama Kirjinta? Ta tambayi kanta ba tare da sa ran samun amsa ba Www.bankinhausanovels.com.ng don ta sha kai wa kirjin nata duk wani lissafi a akan Adamu. Adamu ban da son’ sallarsa kulliyarsa bai cancanci a so ba, ashe ma bayan wannan ita kanta bai dauke ta a matsayin mace _ ba, Baka gundumemiya, wannan ce inkiyarta a — wajen Adamu wanda ta kwashe shekaru da saninsa saboda haka ta ga ko wane irin aibu nasa daga halittar jiki zuwa hallitar hali amma dukda haka ko kadan Kirjinta bai ji rauni a sonsa ba. | Ta ci kuka mai hadiye shassheKa a ciki sannan ta goge hawayenta daidai lokacin da zuciyarta ta cilla lissafin Adamu da zabgegen carbi hadi da turaren -wuridi, nan da nan kwanyarta ta rushe da canki-cankin Allah ya sa ba zargin da zuciyarta tayi ya tabbata da Adamu ba. Tana cikin share hawaye Adamu ya fito daga dakinsa da nufin shiga cikin gida. Ya kula hawaye take tana sharewa, amma sai ya basar, “Au ashe ke ce baki tafi ba, haba tun dazu nake jin kwashar-kwashar”’.Www.bankinhausanovels.com.ng Ta fara girgiza kai cikin rudewa da kokarin kwato furuci daga kwanyarta, amma ya gagara Kawai sai ta sa masa ido da kallon Kurilla. Suka yi kallon-kallo tamkar kowa na hango cikin zuciyar kowa, amma shi sai ya basar ta hanyar kawar da kai yayi fuska, * “Ina abincina, kin taho min da shi?” Ta amsa da kyar cikin numfarfashi tana nuna masa cikin gida, ~“Tun dazu Sajida ta kawo maka ina tsammanin ba ta san kana ciki ba ta kai wa Hajiya” Ya kada kai ya wuce cikin gidan ba tare. da ya tanka mata ba, ita kuma ta bishi

Please Login or Register in order to submit comment