Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

bin umamin Anti Sa’a, musamman da ta dubi Salmanu ta ga ya aika da rabin abincin kuma har yanzu yana kan ci. Anti Sa’a ta fara yaudaro Adamu da cewa,
Ni fa na zaci kun shirya da ‘yar tawa har na ji ka sai mata anko, amma yanzu takanas mun zo duba ka kana ta faman wani shassharewa, wai ko kalion fuskarta ba zaka yi ba bare ka ci abincin _ da ta kawo maka?” . Adamu yayi fuska ya tsurawa Anti Sa’an ido maimakon Salma da suke son ya kalla,
“Menene sabo a fuskar tata da ake son na. kalla? Ga abokina‘nan ya fanshe ni ya kalla, ba -shikenan ba” Duk su biyun suka ji kamar ya rusa musu guduma a Kahon zuci, na Salma dai-yafi bayyana saboda dama a tsorace take da cewa ta zubawa Adamu tsafaffen maganin bokan da ba ya Karya, abokinsa ya ci abincin. Www.bankinhausanovels.com.ng Sun Kara rikicewa lokacin da Salamanu ya debo murmushi yace,
Ga, shi yau Salma ta yi kyauwun da bata taba > yi ba, kuma ta yi girkin da ban taba cin mai dadi irinse: ba” “to ai sai ka yi mata abinda suke son ni na yi mata” Adamu ya Kara yin fuska ya fada. Sawu a likkafa Salma ta sa kai ta fice daga dakin, inda Salmanu da ma Adamun suka bi ‘ Keyarta da kallo. | . “Babu dadi cin fuska” . Anti Sa’a ta fada cikin takaici, ta Kara dacewa, : ‘ . “Duk tsiya mai sonka ya fi mai Kinka” “Me ya kawo wannan maganar?” In ji Adamu rai abace, AntiSa’a tace, . “Abinda ka yi ne ban ji dadi ba, Salma fa ba neman kai muke da ita ba, kuma ba wani laifi bane dan ta nuna sonka a matsayinka na dan gida wanda ba wani abu ya mallaka ba bare ace ba son Allah da annabi take maka ba, ka je ka tuna wannan’. ” Www.bankinhausanovels.com.ng
Tsaki kawai Adamu yayi ya kawar da kai. Hakan ya sanya Salmanu yin shiru alhalin da yayi niyyar saka baki. “Ina ankon nata”’ Tatambaya. . Da sauri Salmanu ya kalli Adamu yana dokin jin Karyar da zai zabga. . Kai tsaye Adamun ya amsa, “Wa yake ta wani anko? An sace shi a nan inda hadarin ya faru. Ai maganinta kenan ma da na ce ta zo ta karba ta ce-min sai ni zan kawo |n mata, Allah Kara”
Murmushi kawai anti Sa’ a tayi ta basar da zancen suka kamo wani, har lokacin ziyara ya kusa Karewa sannan ta yi masa sallama ta tafi. A waje ta ci karo da Salma zaune a baranda cikin damuwa. Ta ce mata, “Yi maza ki Kara goga hodar ki je ki yi masa sallama kar ki damu’’. Cikin sanyin jiki Salma ta goga ta shiga
dakin, tana riKe d Karfen gadon Adamu tace, “To yaya Adamu zamu wuce, Allah Kara lafiya” Www.bankinhausanovels.com.ng Ya dago ya dube ta fuskarsa babu yabo babu fallasa ya dago ya dube ta, ita kuma ta sakar ~ masa wani murmushi, sai ya ji wani dum! Tun daga idonsa har cikin ransa, amma dai bai bayar da maza saboda canjin da yaji ba, cikin nutsuwa _ ya amsa mata, To sauka lafiya, na gode”
Ta dan yi dum! Da zaton bai kalle ta da kyau ba, musamman da yake ya kawar da kai. Amma babu yadda ta iya haka ta juya tana ficewa. Salmanu ya bi ta da kira, Ki zo ki tafi da wannan abincin da yaki ci kin ga yau za’a sallame mu” Salma.ko ta juyo bare ta nuna alamun ta ji abinda yake cewa. . _

***********

_ Adamu ya saba tsayuwar dare, amma yau bai. _ yi niyyar tsayawar ba dan har yanzu jikinsa ba Kwari, sai dai kuma baccin ya gagari idonsa da ma. zuciyarsa gaba daya, a kuntace take iyakar Kuntacewa, haka kawai ransa ya dinga – mugun baci cikin daren nan ba tare da dalili ba, Www.bankinhausanovels.com.ng ya kuma rasa wa yake jin haushi ko kuma abinda. – ke bata masa rai. Haka kuma Salma da Husna suka dinga tsere cikin zuciyarsa suna nuna masa kansu.
Ya san cewa shi ma‘abocin tunani ne, amma na Husna zalla! Salma ba ta taba samun ko a bonus ya zauna musamman ya tunana ta ba, tunaninsa a lokutansa na rana na yadda zai mallaki Husna ne da mafarkin yadda zasu shifida rayuwarsu, tunaninsa da’ lokutansa na dare na mika dukkan imani ne ga ubangiji da roKonsa ya mallaka masa ita yana mai cike da fatan Ubangiji ba zai juyar da rokonsa ba.saboda haka yake yi cikin dadin rai na jiran lokaci. Amma yau komi ya canja, shi da zuciyarsa neman sa Karfi suke su bar Allah, ba don su sami Husna ba sai dan su sami Salma ba tare kuma da sun dena son Husna ba, abin da bayar da mamaki! . Fiye da rabin dare haka yayi ta juyi kan katifarsa rayukansa babu. dadi suna kuma ta damfara masa kala-kalar mamaki Bai tashi yayi sallar ba bare ya fadawa Allah, bai ma yi Sha”awar hakan ba saboda kasala da rashin dadin
Www.bankinhausanovels.com.ng zuciya, kai da ma rashin tabbas din in ya tashi me zai cewa Allah? Shi da ya shafe watanni yana neman Husna a wajensa yau kuma sai ya durkusa neman abinda baya so wato Salma? Ita . wadda yake so ya kai ta ina, kuma Salman ma yaya zai yi da ita? : Duniyar ta taru tayi masa zafi har Karshen dare, musamman da ya Ankara duk yadda yaso ya nesanta ransa da Kawancen Salma hakan yaku° samuwa, Kara samun muhalli: take mai shegen zurfi a cikin zuciyarsa. Sai ga shi zaune da kuka shabe-shabe da hawaye har da sauti, yana yi yana ambaton, “Na shiga uku!” Ya ci kukansa ya Koshi,, amma Salmanu da ke kishingide kan Kafet yana sharar bacci bai san yana yiba. Kasancewar ba’a sallamo su kan kari ba ne ya -sanya shi kwana a nan, abinda ya cewa su Hajiya kenan, amma gaskiyar ita ce, sammakon aikinsu _Suke son dokawa, a cewar Salmanu, ko babu . kudi yakamata su fara aikin da ba kudin yake. -bukata ba. Www.bankinhausanovels.com.ng Musamman ‘Adamu ya tashi zaune. yana “zungurinsa cikin kuka. – A firgice Salmanu ya farka ya tashi zaune, Adamu jikin ne?” Adamu ya sake carkewa da kuka, ; “Zuciyata ‘yar ta’adda ce Salmanu, ta kwaso ta’addanci ta kawo wa raina, sun hana ni bacci da Alama ma har Karshen rayuwata suke bukatar kar na runtsa” to
Salmanu duk da bai gama fahimtar Adamu ba fuskarsa ta nuna iyakar damuwa, ya ce, .
Waime yafaru?”.Wai Salma muke so”. _ Ya amsa cikin shassheKa. Salmanu ya sake tare gira nuna alamun rashin _ fahimta, Kaidawa?” “Ni da banzar zuciyata mana”. . . – Kamar Salmanu zai tuntsire da dariya, amma ‘har ga Allah ya ji tausayin Adamu musamman_ yadda ya ga yana kuka da hawayensa, a sanin da _ yayi masa jarumi ne daidai misali, kadayake shi halittar so na saurin sanya shi kuka, haka wancan
Www.bankinhausanovels.com.ng neman auren da ya taba rakitowa Karfi da yaji ya mayar da shi wani Baure, Ya jima yana kallonsa cikin nazari sannan ya tanka, Da mamaki gaskiya, to me ya janyo hakan?”
“Oho! Nima na sani! Zagi nake so in rusa amma na rasa wanda zan zaga, ni ko zuciyatada_ haka kawai muka rakito son abinda bai cancanta – ba? Allah ya tsine wa Salma wallahi, ni ban san abinda zan so a ita ba” Ga dariya ga kuma son yin nazari suka taru suka murkushe.Salmanu, sai ya hada su duk biyun yana ji dasu, :lCikin tsananin dariya.ya.ce da. Adamu, Jiya Salma ta sako kwalli? In ta saka saimu yi tsammanin Kifil ta sako maka” ‘“Allah ya isa ban yafe ba wallahi” . -Salamanu ya sake tuntsurewa da dariya yayin da Adamu ya sake sakin shassheKar kukan da ya tsayar da Salmanu dariyar da yake,
Wai baka yi bacci ba? Na san ka da sallar dare yau me ya hana ka? Ai da ka kai wa Allah Karar Salma yayi mana maganinta” ——Ya Kara da tuntsirewa da dariya. _

Hmmmmm LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGA JIYA MUN TSAYA

neman auren da ya taba rakitowa Karfi da yaji ya mayar da shi wani Baure, Ya jima yana kallonsa cikin nazari sannan ya tanka, Da mamaki gaskiya, to me ya janyo hakan?”
“Oho! Nima na sani! Zagi nake so in rusa amma na rasa wanda zan zaga, ni ko zuciyatada_ haka kawai muka rakito son abinda bai cancanta – ba? Allah ya tsine wa Salma wallahi, ni ban san abinda zan so a ita ba” Ga dariya ga kuma son yin nazari suka taru suka murkushe.Salmanu, sai ya hada su duk biyun yana ji dasu, :lCikin tsananin dariya.ya.ce da. Adamu, Jiya Salma ta sako kwalli? In ta saka saimu yi tsammanin Kifil ta sako maka” ‘“Allah ya isa ban yafe ba wallahi” . -Salamanu ya sake tuntsurewa da dariya yayin da Adamu ya sake sakin shassheKar kukan da ya tsayar da Salmanu dariyar da yake,
Wai baka yi bacci ba? Na san ka da sallar dare yau me ya hana ka? Ai da ka kai wa Allah Karar Salma yayi mana maganinta” ——Ya Kara da tuntsirewa da dariya

ZAMU TASHI

Asamu ya tsayar da hawayen yana duban salmanu
Kabar mayar da lamarinnan wasa wallahi da gaske nake zuciyarnan taci amanarmu sai abin ya fara bama salmanu mamaki yayi sukukwitare da neman tashar da zai kamo
Amma ya rasa har lokacin da yaga adamu ya miqe daga kan katifar tasa ya fara kaiwa da komowa a tsakiyar dakin salmanu ya daga kai ya bishi da kallo yana sauraronsa a tsanake lallai akwai wani abu dake shirin faru damu nida rayuwata abu mafi daure kai ta inda makomar husna zata bullo a rayuwata abu mafi muni shine kaddarar rayuwata ta zamo babu husna a cikinta dukda ina ceke da yakinin da wahala husna bata zamto mata gareni ba


Maiya kaika cin wannan alwashin dan allah salmanu ya tareshi cikin mamki da al,ajabi tare da zaton kamar ba cikin hayyacinsa yake ba adamu ya amsa cikin murmushin yake Www.bankinhausanovels.com.ng
“Akwai kyakkyawar alaka tsakanina da Ubangjina Salmanu, in dai na yi masa irin roKon da na yi akan Husna yana ba ni abinda na roKa,
shiyasa nake cike da fatan kutsen da Salma ta yi cikin zuciyata ba zai hana ni zama mijin Husna ba”
Har yanzu Salmanu cikin mamaki yake, sai ma ya rasa abinda zai ce. , Adamu ma ya kulle hira daga haka, ta hanyar ‘ ficewaya dauro alwala ya tayar da sallah. Yayin da Salmanu ya koma ya kishingida. ; Duk sammakon ficewar da suka doka sai da Salma ta riske su da farfesun dubiya ga Adamu. A bakin Kofa suka yi kacibis da Adamu bayan Salmanu ya fice waje, duk suka dubi juna da wani baKon kallo wanda ba su saba shi a tsakaninsu ba, a cikin wasu sakanni Kalilan, Salma ta riga shi tankawa, “Sai ina da sassafen nan?” Ya so ya tara gira ya kuma daure murya – amma sai yaji ya kasa. Ya jima bai tanka ba cikin
Www.bankinhausanovels.com.ng kallonta a sassauce sannan ya nisa cikin sanyin murya yace, — .
“Ke ma‘ me ya fito da ke da wannan – sassafen?” Ta fara KoKarin shiga dakin da yake son -rufewa kamar zata ture shi, da sauri ya bata _ hanya sannan ya bita cikin dakin yana sauraron ‘ amsar da take ba shi, “Dan abin sashe baki na kawo maka a matsayinka na maras lafiya” ~ uhm kawai ya iya tanka mata da ita. Ta zauna kan kujera shi ma ya nemi dandaryar kafet ya zauna suna fukantarjuna. ~~ “Yajikin?” . Ta tambaya tana dubansakaitsaye.. . Shi ya kawar da nasa idon ya amsa,_. , ~ “Athamdulillahi” Ta cigaba da kallonsa. tana son kore mamakin sauyawarsa don ita ta san dalilin sauyawar, “Kuma daga fitowarka jiyan nan daga asibiti Yaya Adamu sai ka kwashi jiki ka fice yanzu da sanyin safiya ba zaka bari ka warware ba? Www.bankinhausanovels.com.ng in kai baka damu da lafiyarka”ba fa akwai irinmu da muka damu da ita” .Yayi KoKarin fada mata mai daci ya ji harshensa ya kulle, mai dadi yake son furtawa zuciyarsa kuma tana Kyashi, don haka ya Kyale aka yi biyu babu. — Yau wai ya na gan ka duk asanyaye?” Ta tambayae shi cikin dariyar da biyu. Ya dago kai ya dube ta kawai, amma bai tanka ba. Haka ta yi ta ‘yan sambatunta yana bin tada ido harta sauke kular farfesunta ta samo filet ta zuba masa ta kai masa har gabansa, . “To dan taba wannan tunda sauri kake in ka dawo ka Karasa sauran” Ya dubi agogo sannan ya mike yana cewa, . “To bari na kira Salmanu ya taya ni” Ta yi KoKarin shan gabansa,
‘ “A ‘haba dai ka ci mana ba sai ka zuba masa wani ba tunda farfesun da yawa?” Fuskarsa ta dan nuna damuwa duk da yana yi .mata fada kar ta batawa Salma, ya kewaye ta ya nufi Kofa yana cewa, Www.bankinhausanovels.com.ng ai baza,ayi wasa tare da ci bambam bari. dai na kira shi” Ta bi shi suka bar dakin tare tana cewa ~ . “Shikenan, ni ma zan koma Allah ya Kara – lafiya” – : Ya amsa cikin fara’ar da Salma ba ta taba gani a wajensa ba A Kofar gida suka tarar da Salmanu zaune_.
kan dakali, suka gaisa da Salma ta wuce, shi_. kuma Adamu ya ja shi cikin gida suka fara kwasar garar farfesu. -Wai sai da suka ci suka side sannan Salmanu ya ce cikin zolaya,_ . . ‘ “Mu fa samari a irin wannan kwadayin namu_~ake neme mu, ka san mata da barbade-barbade”’ Da takaici ya kulle Adamu sai ya rasa da _abinda zai fanshe face kai wa Salmanu wani wawan mari, Allah ya taimake shi yakauce yana dariya. , – : ai“Kai wallahi KwanKwararren mugu ne, kasan’” da hakan sai da muka cinye zaka fada min?” . Salmanu ya ce, Www.bankinhausanovels.com.ng “Kai ma yakamata ka san hakan don kai kadai ka san abinda kake ji a Kirjinka game da Salma” – Sai kuma Adamu ya ga gaskiyarsa, amma daga daren jiya zuwa yau zuciyarsa ba ta da zabin tunani na kanta sai abinda aka zaba mata, ko ta fara sai ta tsinke, don haka yanzun ma tsinkewa tayi daga gasKata Salmanu da ta fara. Sai Salmanu ya canja Bari, “In muka fara sana’ar nan zaka ce na sanar da kai, zaka gane halayen mata da yawa” Adamu dai yayi shiru, daga shi har zuciyarsa ~ ba a nutse suke ba, ko ragon tunani ba za su iya ba bare su yi wanda za’a yaba.


**********

Sati daya a tsakani Adamu na shan wahala_ iyakar wahala, tun daga zuci har zuwa gangar jiki. Duk wani tsari da fata wanda yayi shekaru yana shiryawa a matar aurensa da iyalinsa cikin sati daya sun bi ruwa. Zuciyarsa ta zama fanko babu wani tanadi a cikinta sai jiran tsammanin abinda rayuwa zata zabar mata. , Www.bankinhausanovels.com.ng
Zuciyasa ta bude makeken fili ta share a son Salma ko ciwon shigowarta rayuwarsa, Husna na can loko sakaye da tata matsananciyar Kaunar wadda ya fara jin yawa ne da ita kawai, amma ~ tabbas zuwa yanzu ba ta da tasiri, tare da yakinin rashin tasirin nata nakasu ne a kulliyar:tasa rayuwar.: . .
Abin ya zo masa, da sauki ne, kasancewar tsawon satin suna ta fama da kujiba-kujibar ‘harKallar da suka cacimowa kansu, shiyasa dare kawai yake mallaka yayi kukansa yayi roKonsa ga ubangiji kuma ya tinana abinda zai iya tunanawa a mafiyayyen son Salma da kuma dan asalin son Husna.

Sun gyara muhallin da zasu fara bokancinsu, – yanzu suna cikin atisaye ne na dabarun karbar kostomomi yadda bokayen gaske suke, da kuma koyar rufa idon da zasu dinga yi wa maziyarta, ga Adamu kenan wanda bai san kan garin ba. _~


Zuwa yanzu dai ya haddace rufa idon da ake da Kwai, Tiyo, kyandir da kuma karkashi. Sun samo wani abokinsu taKadari irinsu mai suna Tanimu, tafiyar ta koma ta mutum uku, Salmanu ne ‘Boka, Adamu zai dinga aiki biyu, Www.bankinhausanovels.com.ng muryar aljanu yayin da yake boye, in ya bayyana = kuma ya zama dan kore ga Boka, Tanimu kuma
shi ne mai nemo kostomomi, wataran kuma yayi shigar burtu a zuwan kostoma ya yi ta koda boka ‘a gaban bakin kostomomi, sun shirya in harka ta kankama zasu nemai Karin yara. Yadda suka dauko tafiyar sun’ hango mata samun tsabar kudade da nasarori, don haka . dukkansu hankalinsu kwance suke komai.

************

Ranar juma’a da yamma yana zune a dakalin

+ Kofar gidansu zuciyasa a mugun Kuntace, ya

, dinga ayyana, ina ma shi yaron goye ne, tabbas

yau da uwarsa ta shiga uku da tsinannen kukan da zai.balle. mata hancinsa, a yau sai ta ~

gwammace bata haife shi ba. Kuma da girman
Nasa ma ya so ya kwatanta har ya shiga daki ya
fara gwaji, amma da ya fahimci aikin baban giwa
yake babu wanda ya san yana yi kawai sai ya


share hawayensa ya fito waje yana rarraba idanu. — Kamar daga sama ya hango Husna ta‘nufo shi kai tsaye, ta ci kwalliyar da bai: taba ganinta Www.bankinhausanovels.com.ng cikin irinta ba, kai bai ma taba ganin wata ‘ya © mace mai daura zani a hannun hagu tayi ba. – – Kawai sai ya saki baki yana kallonta cikin . matsanancin bugun zuciya har ta Karaso gare shi, sannan ne ya lura tana dauke da wata leda Kunshe da kaya. _ _ Ya sauke wata wawuyar ajiyar zuciyar da ya so hadiye ta amma ta sanya masa Karfi, yakawar_ . da kai cikin jin gaba daya ma ya san ya gama – – bayar da maza. , Da sassanyar muryarta ta yi masa sallama. Ya amsa da tasa dakusasshiyar muryar ba tare . da ya dube ta ba, ya kuma rasa dalilin da ya sa ya kasa duban nata. “Ranka ya dade wannan gimbiyar taka kuwa ~ ” tana gari? Na ga ba ka nemi dinkin nata ba gashi . kuma tun jiya muka fara bikin” Ta fada cikin matsananciyar fara’ar da tayi awon gaba da dukkan fargabar da ke kaKale a . Zuciyarta . Cikin Kumaji ya juyo yana dubanta kai tsaye, – Kirjinsa na dakan uku-uku amma Karfin halinsa ya gama bayyana ilahirinsa, yayin da soyayyarta ta fito daga saKon da Kaddara ta bayar da ajiyarta Www.bankinhausanovels.com.ng tayi awon gaba da ta Salma wadda ta yi gida ta tare, . “Duk wata gimbiya ai bayanki zata bi ranki ya dade” , Ya fada cikin sanyin murya yana yi mata – kallon.da shi kansa ya san Karya ne a ce bai bayyana tsantsar Kaunar da yake mata ba.


Ta dora dan alinta a Kirji tana bude da baki cikin shauki da yi masa kallon mamaki, amma bakinta ya kasa furta kalma, . Ya kada kai mai nuna tabbatarwa, _ “Na rantse da Allah dama kayanki ne” . ” Ta ji tsaiwa na neman gagararta, sai ta doge, ta rausaya kai har yanzu ta rasa bakin Magana. —
To yaya hidimomi?” : Da kyar cikin sarkewar numfashi yanzu ta – daure ta tanka, – . -“Alhamdulillahi, komai na gudana yadda ake so” a “To masha Allah, dama yanzu da nake zaune tunanin yadda zan riske ki gidan bikin nake” . Ta sake dubansa galala. . Shirunta ya cigaba da bashi Karfin halin Magana, musamman yadda take dubansa cikin Www.bankinhausanovels.com.ng sanyin jiki yana da yakinin tabbas ita ma So yayi mata wawurar da yayi wa zuciyarsa da ilahirinsa, “Zuwa yanzu na gama juriyar hadiye soyayyata da zuciyata take miki, in ban samu na _ furta ba ina da tabbacin, zamu iya shari’ a da _ zuciyar™, Tamkar jiri zai tike ta garin kuma ya dauki haramar zagayawa. Da ita.
Cikin haka ta Kwato furucin, ‘Nikakeso?” Ya amsa, “Menene na shakka?” – Ta yi saurin girgiza kai. Ba shakka nake ba,.amma me yasa. saida naz0 Kofar gidanku zaka fada min? ka ragewa son da ka ce kana yi min daraja” . _ Ya girgiza kai cikin sanyin jiki, “Kar ki fadi haka, son da nake miki ina da yakinin ba a taba irinsa ba, amma sai jiya na san gidanku kuma a yau din nan nakeda niyyar Zuwa Farin ciki ya rufe Husna, sai ta kasa tankawa. Suna tsayen nan kowa sai ‘numfarfashi da murmushi.. , yake Www.bankinhausanovels.com.ng Kwatsam sai ga Salma tamkar an jefo ta, ita ma ckin kwalliya tane sanye da irin Kayan dake. jikin Husna. Adamu na ganinta. ya ji tamkar an ruguzo masa dutsen dala a Kirji, jikinsa yayi sanyi Kalau, zaciyarsa kuma ta dakata da zabi, “‘~ . Aka yi gaisuwar mutumci tare da ambatar sunan juna tsakanin Husna da Salma na shaidar an san juna, kai tsaye kuma Salma ta fara gabatar da Adamu a wajen Husoa a matsayin dan uwanta, sannan ta zarce da cewa, . * + “Kuma shi ne wanda zan aura in Allah ya so” . Duk da Husnha macace mai siyasa, amma siyasar tata ta kasa galaba a wannan muhallin, » sai da idanunta suka KanKance suna.shirin fara zubar da hawaye, ta bi Salma da kallo wadda fuskarta ta nuna alamar da gaske take. Da ta juya ta dubi Adamu shi nasa.arzikin ma sai ya ci uban na jiya, domin kada mata kai yayi cikin tabbatarwa ya kuma amsa mata da baki.’ “Haka ne, za mu yi aure cikin Kankanin lokaci” Www.bankinhausanovels.com.ng Husna ta dauke kai daga kallonsa lokacin da – wani malalacin hawaye ya sulmiyo mata ta yi ~ dabarar gogewa da mayafi.
Ko Adamu ya san tarkon sonsa ta fada ne shiyasa takanas ya shiryo mata wannan cin fuskar? , Sai ta daga kai ta cigaba da tsura musu ido su duka dan ta gane siyasar ce, cin fuska ce ko kuma iyakar gaskiyarsu kenan? . : Kamar sun manta da ita sai suka lula cikin hirarsu da ke bayyana son da suke wa juna kai tsaye.. .

MU HADU A LITTAFI NA BIYU
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels

Please Login or Register in order to submit comment