Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

  " Sannu da zuwa yaya DanAllah kayi hakuri wallhi bazamu kara ba DanAllah dubi yadda karame...

    " abban muh'd please we are sorry please...

    " Babu abunda yace musu sai ce musu yayi ina turaren da mamee ta kawomin ramlat...

   " Tashi tayi ta dakko tace gashi...

    " yasmin ce taji kirjinta ya buga tace mamee kuma??

   " Ramlat tace eh ita takawo masa...

    " haba duk turaren sa me zakayi dashi darling..??

      Budewa yake kokarin yi babu shiri dabara tazo mata tayi hanyar bene zana hau sai tayi kamar zata wade babu shiri yace yasmin cikin sauri ya dagata yana mata wani kallo so kikeyi kiyimin wata asarar  DanAllah muje kaci abinci kayi wanka...

     " okay natafi kikawomin abincin...

      " Sauri tayi taje ta dauke turaren hanyar waje tayi tace baba mai gadi danAllah kazubar da turaren nan acan waje...

    " Tohm hajja ju abinci ta kaimasa sannan yace bani abaki...

     " zama tayi tabashi har lemon..cikin shagwaba tace me kakeso kuma ayimaka tambayar ki kuma zanyi DanAllah kina sona yasmin???

    " Dariya tasaka tace So mai sonka...

      " Au dariya nabaki lallai yasa mijin...

    " kwantowa tayi akan kafadarsa tace abunda ke raina zan tona ba son rai ba,dukkan tunani na shine in rayu dakai, ko bayan raina zan alfahari da kai mijina, sannan hawaye ya zubo mata..kai ne burin ruhina kai ne zabina mijina..babbar burina mutuwa zata rabamu,Ni nayi dacen samun ka mijina iya wuya ina tare dakai..kaunarka ta ratsa cikin jiki da kalbi,duk Umarnin ka zanbi..

    " Wani dadi yaji yace azuciyata ni ke nake muradi,tunda nasameki hankali ya kwanta,kisa aranki kece mamallakin raina...son da nake miki wasu suke tunanin wani abun kin cancanci fin haka matata inasonki...

      Wayarsa ce tafara ringing yana dauka yace ina yini mamee??

    " Lafiya lou..nace turaren nan kayi amfani dashi kuwa???

    " Yasmin tayi masa Alamar eh..eh dadi kamshin nagode Allah yakara girma...

    " mamee ce tace yauwa sageeru Allah ya taimaka nagode agaidasu takatse wayar...

   Alhaji haruna ne yace yayi ko??

      " Mamee tace zance ai yagama kafin gobe ansako yasmin shikuma bazai kara samun lafiyar tafiya ba wayyoo dadi...

     " yasmin me isa kikayi karya?? " Hakan ina ganin yafi Alheri mijina ko? Saboda mutanen kirki su akeyiwa shaidar abun arzuki muna zaune lafiyar mu kaga bazaiyihu a hargetsa mana zama ba duk da komai sai Allah yayarda Amma muma yakamata mu kiyaye...

    " To ki zubar dashi ashara Allah yashirye su...

     " Ameen bari naje nayi sallah, rikota yayi yace A'a nefa babu inda zakije kiyi anan..murmushi tayi tace ai sai nayi wanka...toh muje nayi miki,.." A'a yaya da girmana tayi saurin fita..

    Da daddare bayan ta kwanta ta lulluba taji ana shafa cikin ta cikin zabura tadago fuskarta yaya me kake nema??

     " Baby na nake shafawa daga nan yafara zarci gona da iri tana bude bakinta zatayi magana yafara kissing dinta yayi adduar saduwa..hanakalin ta bai tashi ba sai dataga halin da dr yashiga babu kukan da batayi ba amma bai kula taba abun mamaki har 2 sannan ya saketa,..cikin wata kasallaliyar murya yace Ai hutawa zanyi ke kikajawo da kike vari yana taruwa i really miss u my wife bari nayi wanka sai nayi miki...

     Yana fita tatashi tayi wanka jikinta kamar tamutu dan gajiya kwanciya tayi bacci yana kokarin surar ta taji yana kara tabata tace DanAllah yaya kar na mutu kataimaka..." Yanzu please kadan ki taimaka yasmin i really miss u... " Da safe saboda tsabar gajiya kasakomai tayi ranar babu yadda ba'ayi dashi ba yace shi ba babu inda zaije bashida mara lafiya...

      " ramlat ce ta hada breakfast yasmin tanayiwa muh'd wasa dr yace saura naki twins din... " hmm tace batace komai ba ta salallaba tayi sama bacci ke damunta dama bayan tayi nisa yazo ya kunna mata ac sannan ya kwantar da ita a kirjinsa shima ahaka baccin ya koshi sa...

    Ramlat ke zaune tana kallo taji sallama muryar rabia taje..

      " Me kikazo yimun agida??  " ke dallah sabon boka nasamu wannan kizuba wa kishiyarki zakiga aiki da cikawa..

       " Babbar jahila asararriyar kawa nayi danasanin saninki rabia Allah ya'isa duk abunda kike saka ni kuma wallhi kije da Allah zai isar mini...

      " Hahaha banza jaka cewar rabia ai sai na fitar dake daga daular nan sai kin koma yawo atiti da mota kuma sai na shigo gidannan ko kinaso ko bakyaso dan haka ki tsaya ki gani...

     " Fitar min daga gida kuma nakara ganin kafarki wallahi sai na karyata...

      " Zan fita Amma kema kiyi ready kin kusa fita nice fa Rabia uwar munafukai...

 

Assalamu alaikum

   *how was the page??*

YAKUKAGA SOYAYYAR DOCTOR DA YASMIN??

      *ina fata kuna daukar darasi acikin wannan littafin kunga sharrin kawa da illarta da makircin ta...

Kuna tunanin Ramlat zata shiryu baki daya?? Ya rikicinta da rabia??

  Ya zancen kuma kara auren dr..??

    NA SADAUKAR DA WANNAN PAGE DIN GA DUKKAN MASOYAN LITTAFIN NAN UBANGIJI ALLAH YASA KUNA ANFANA DA ABUNDA YAKE CIKI NA DARASI ABUNDA BANYI DAIDAI BA ALLAH YAYAFEMIN...

INA GODIYA DA SOYAYYAR DAKUKE NUNAWA WANNAN LITTAFIN ALLAH YASAKA DA ALHERI...

    Please do vote comments and like 👏

👆🏼👆🏼GO AND SUBSCRIBE TO THAT YOUTUBE  CHANNEL GA SHI CAN NAYI POSTING A FARKON PAGE DIN...FOR THOSE WHO WANT TO LEARN  FOOD,SNACKS AND DRINKS....👆🏼

👆🏼👆🏼please click the link and subscribe  ..

   Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo. com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:20 PM] ‪+234 703 475 7034‬: 97-100

  *DOCTOR*
           *SAGEER*

_NA NANA DISO_

      https://www.youtube.com/channel/UCvopCYalw1ooSYq-rMhjm5g

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Tun lok'acin da rabia ta fita hankalin ramlat bai kwanta ba tunanin abubuwan datayi abaya takeyi tabbas tayi nadamar haduwa da rabia bata taba tunanin *MUGUWAR KAWA* bace tabbas duk wanda yace zai biyewa kawaye domin suji dadi a duniya kullum basa tunamasa lahira zaiyi asara ba karama ba tabbas kawa ta rudeni datuno na kashewa kai na aure Allah na gode maka Allah ka yafemin duk abunda nayiwa Dr sageer sannan tasaka kuka, Muhammad dake jin yunwa ta dauka tabashi abincin sa sannan tashiga kitchen don hada abinci....

    " yasmin Sai gurin 4:00 saura tatashi bata nufi ko'ina ba sai toilet wanka tayi sannan tasa kaya doguwar riga ga cikinta da yadan fito, sallah tayi sannan ta matsa kusa da dr sageer tana latsa hannunsa cikin k'ankanin lokaci yafarka bude idonsa da zaiyi yaganta akusa dashi murmushi yayi yace lokacin sallah yayi ko??

    " Eh yayi katashi kaje masallaci kada ka makara ko??

    " Tohm yace bai tsaya ko'ina ba sai masallaci...

   Yasmin ce tasakko taga har ramlat tajera komai a dinning samun guri tayi ta zauna tace sannu maman muhd nabarki da aiki yau dinne banajin dadi...

    " Murmushi ramlat tayi tace ni sau nawa ina barinki da aikin ai ko kaso daya banyi ba daga cikin abunda kikayi duk kin kwashe ladan..

    " Hmmm yasmin kawai tace bata kara cewa komai ba ramlat ce ta kunna tv shirin tambaya mabudin ilimi na aminu daurawa...

    " Dr sageer yana dawowa daga masallaci ya zauna sunayi masa sannu da zuwa muhd ya dauka yana my boy sai wayo kakeyi Allah yayi maka albarka...

    " yasmin ce tace Ga abinci a dinning kutashi muje muci...

    " Suna cikin ci sai sukaji anci malam tambayata itace kullum idan na nemi matata sai tak'i sai nayi mata magiya wani zubin kuma idan na bata mata rai sai tadinga ramawa da hanani hakk'ina..
    Malam yace kamar yadda yazo a hadisi cewa duk maccen da mijinta yanemeta taki amincewa batare da tana cikin larurar da aka haramta kusantar juna wata ko  tsanin cuta ba to mala'iku zasu kwana suna tsine mata, mata kusan wannan tabbas babban kuskure ne dakuma asara dumin aljannar mijinku tana tafin kafarsa akwai hanyoyi da yawa na ramuwa amma banda wannan tunda zatajawo wa kanta tsinewar mala'iku kuma babbar asara ce wannan, tabbas rayuwar Aure sai hakuri dole in zaa zauna sai wani ya cuce wani ko wani ya kware wani ko wani ya batawa wani danhaka hakuri shine babbar ribar wannan zama dan duk wanda kuka sundade to su kadai suka san hakurin da sukayi,kuma Allah da kansa yace kuma kuyi bushara ga masu hakuri,kuma kusani Allah baya zalunci koma duk wanda aka zalunta zai saka masa kuma Allah baya yafe hakk'in wani..

   " Yasmin dake cin abinci tayi saurin kwarewa, cikin sauri dr sageer ya mikomata ruwa sannu sannu...

    " ramlat ma shiru tayi batace komai ba domin ada ta wahalar da dr sageer tabbas lokaci yayi dazata bashi hakuri..

      Dr sageer yafi kowa jindadin wa'azin nan don halin da yake ciki kenan cikin fara'a yace yakamata mufara tulawar al kurani ko zuwa gobe da daddare ne..

     " Sukace toh Allah ya kaimu..

 
Alhaji haruna ne yace to wallahi kusani boka yasanar dani cewa indai basuyi amfani da turaren nan ba duk mu ukun cutar baras ko kuraje masu wari zasu samemu ina fatan kun tabbatar sunyi amfani dashi...

   " mamee ce tace amfani na nawa ai yanzu babu mamaki yasmin tana gidanta dr kuwa balafiya...

    " Alhaji isa yace kwarai kuwa don jiya a gabana kika kirasu awaya kuma sunji sunyi amfani dashi...

     " Toh shikenan kar mushiga matsala shiya bamu da mai bamu magani...

    " mamee tace matsala ai sun dade da shigar ta amma mu bazata samemu ba...

     Da safe dr ya shirya zai fita yanata sauri yasmin tace honey yace yes menene sakkowa tayi ta sumbaci bakinsa tace please zan dan lika gidan anty hauwa kanwar mama anjima kaji?

    " Banson fita yasmin innadawo maje, Nan da nan din haba yayana please nikadai fa agida...

    " okay tohm sai kin dawo dear ki gaisheta ki kula da kanki ..

     " rike hannun sa tayi tace thank you ban yarda kowacce mace ta kallarmin kai ba kaji please ka kula da kanka i love u so much..

      " murmushi yayi yafita yaja mota yasmin ta samu guri ta zauna kogin tunani tashiga abu na farko da tafara tunawa shine irin rayuwar talauci da sukayi da irin tsanar da yayan baffa suka nuna musu ashe dama baffana zai samu sana'a tayi murmushi tare da fadin tabbas mai hakuri yana tare da nasara, wani kukane ya kwace mata cikin ranta tace bantaba tunanin zanyi aure ba nasha wulakancin samari su zo su gudu ashe lokaci na ne baiyiba Allah nagode maka kaicon wanda baiyi hakuri ba, duk samarina akorar min ayimin sharri nazo nagam jamia ashe inada rabo daga karshe nazo na aure wanda ko amafarki ban taba tunanin zai soni ba Allah mai girma kayi mana afuwa Allah ka yafemana kakara mana hakuri ta shafa cikinta tana murmushi gashi baby na yakusa zuwa Allah kayi masa albarka sannan ta hau sama...

   Sai karfe hudu yasmin ta shirya zata fita tacewa ramlat ni nafita ynzu zandawo..

    " Toh kawai tace mata batare da ta bata doguwar amsaba tunanin rabia kawai takeyi domin shaidancin rabia yafi karfin tunanin ta...

     Yasmin batayi wata doguwar tafiya ba ta'isa gidansu fadila..anty hauwa ce tace sai yau?? Ai nayi fushi...

     " gaisheta tayi sannan taga wasu matan guda biyu ta gaishesu, anty kenan mijin nawa ne bayason fita shiyasa...

    " Fadila tace yasmin ya gida ya kishiyarki?? " yasmin tayi dariya tace tana gaisheki.." ina amsawa...

     " Wata ta kusa da fadila ce tace kinsan Allah anty hauwa duk zafin ran namiji da yawan fushinsa yana gani kinci kananan kaya ko'ina ajikinki ya matsu ga turare nan danan zakiga ya sakko...

    " tace tabbas especially idan kikayi shigar sannan kika bashi hakuri dai kiji labari ya canza daga fada zuwa tarairaya...

    " yasmin tace ai rayuwar ce komai zakayi sai dai da hakuri... " fadila tace hakane yasmin bikina saura 3weeks fa...

     " A'a Allah yakaimu bari natafi kunga har 6 takusa sukayi sallama fadila ta rakota suna tafi suna hira sai gani sukayi ansha gabansu da mota...

   " Fadila ce tace haba malam da hankalin ka daka bugemu fa...

    " Allah ya huce zuciyar ku yasmin nakeson yiwa magana please..

     " Cikin sauri ta dago uncle jabir?? Ko cikin bacci bazata taba manta muryar nan ba...

    " yasmin nine ashe kinyi aure wallahi nadadi ina nemanki nabaki hakuri wallahi ba yaudararki nayi ba ummata ce ta matsamin sai na aure fatima gatanan ku gaisa kiyi hakuri...

     " Murmushi tayi mai cike da takaici dr sageer da yashigo layin yaganta tare da jabir cikin zazAfan kishi yakara jan motar yashiga cikin gida...

    " yasmin tana ganin haka tace nagode bakomai sai anjima fadila nagode duk ta rudi takarasa cikin gida tana shiga palour taganshi sai jujjuya key yake tana shigowa cikin tsawa yace da uban wa kika tsaya kina yimasa dariya wanene...

     " yasmin da kuka ke kokarin kwace mata tace uncle jabir ne ....

      " Taina yazama uncle dinki ko muharramin ki ne yama zaayi ku gaisa for what reason??

    " Wallahi bakomai yace min ba ha..

     " is okay daman nasan u don't love me she kikeso ko harda yimasa fara kina kallonsa ohh my god my wife yaza'ayi yatsaya dake for what reason baisan hukuncin aure ba??

   Shiru tayi Sannan tace Allah yabaka hakuri wallahi batsaya dashi don komai ba kayi hakuri inshaa Allahu bazan kuma ba nayi kuskure sannan ta durkusa har kasa...ramlat ce duk jikinta yayi sanyi tace kayi hakuri baban muh'd...

    " Wallahi yasmin  bazan iya jure ganin ki da wani ba inasonki ina kaunarki too much Amma na hakura danAllah karki ki kara kinji???

    Yadda yafada har cikin ranta tace too inshaa Allahu bari naje nayi sallah sannan ta hau sama kuka tasaka sai tayi mai isarta sannan ta ta saka kayan bacci tare da addua ta kwanta...

Ramlat ce tace tun dazu yasmin fa bata sakko ba ni bari naje na kwanta sai da safe...

    " Allah yakaimu samn ya hau yaje yayi wanka shafa'i da witr yayi sanna ya nufi dakin yasmin gani yayi har ta kwanta bude bargon yayi shima yashiga cikin sauti kasakasa yace yasmin dita...

    Naam yayasanna tasa kuka ai kaine baka yarda dani ba kawai hakuri bani wallahi babu abunda yacemin...

   Dr sageer ne ya rungumeta sannan yace akanki zan shiga kowanne yanayi ke dayace na kira ki sarauniya , Nashiga yanayi lokacin da naganki dashi kiyimin uzuri kiyi hakuri,Ni nadamu dake kema ki damu dani DanAllah...

    " murmushi tayi tace ina alfahari dakai mijina sannan ta sumbace sa ahaka ya rungumeta har sukayi bacci...

    
   Da sassafe mamee tafito tana ihu tana nashiga uku na lallace kuraje kuraje innalillahi yau nashiga uku na lallace??

Alhaji haruna ne yafito da sauri yace kutmar wallahi sai dai ki barmin gida kije nasakeki saki uku....

     Amma kacika shege mara mutunci azzalumi zan barmaka gida amma ban yafe maka ba...

     " zatashiga daki yace Wallahi bazaki dauki komai ba bazaki shafa mana ba kitashi kitafi ya hankadata...

   " Tana ihu tana kuka takama hanya..

Assalamu alaikum

BARAKALLAHU FIYKUM BAZAN KUMA DAINA GODIYA AGAREKU BA BISA SAKONNIN KU ALLAH YABIYA BUKATU NA ALHERI.._

*_How was the page???_*

    _*I can't stop apologized for the spelling and grammar mistake's*_

    _Please do vote comments and like.. And I call my silent readers please do vote and comment my story really need your comment and vote#TEAM .....DS....DS LOVER'S__

    Please do vote comments and like 👏

👆🏼👆🏼GO AND SUBSCRIBE TO THAT YOUTUBE  CHANNEL GA SHI CAN NAYI POSTING A FARKON PAGE DIN...FOR THOSE WHO WANT TO LEARN  FOOD,SNACKS AND DRINKS....👆🏼

👆🏼👆🏼please click the link and subscribe  ..

  *Ya zo a Hadisin da aka karɓo daga Abi Huraira RA yace: Manzon Allah SAW yace: (( Mai yin zina bã zai yi zinar ba alhãli yana mumini, kuma mai yin sãta bã zai yi sãtar ba alhãli yana mumini, haka mai shan giya bã zai shã giyar ba alhãli yana mumini...))*
Bukhary & Muslim

  Wato duk lõkacin da bãyi za suyi waɗancan ɓarna to sai a cire imãni daga zuciyarsu a sanda suke yin ɓarnar.

Allah SWT ya haramta zina sannan kuma aka sanya uƙuba mai tsanani ga mãsu aikata zinar, kai har ma kusantar zina sai da Allah SWT ya hama kamar inda yake cewa:

(( Kuma kada ku kusanci zina. Lalle ne ita ta kasance alfãsha ce kuma tã munãna ga zama hanya )).

Bisa ga haka duk wani abu da ke ita kai wa kusa da zina to haram ne kamar sumbanta da shigar banza/nuna tsaraici da bayyanar da kwalliya a fili don tãyar da sha'awa da yãɗa hoton banza da faɗar maganar da ta shãfi tãyar da sha'awa.

Wani mai hikima yana cewa: "Abu shida shi ke haifar da zina: Kallo, murmushi, sallama, zance/magana, wajen haɗuwa sai kuma yin ɓarnar". Shi ya sanya addini ya hane tushen zina wato kalle-kalle !

*Allah Ya dãtar da mu*


   Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo. com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment