Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Allah ya isa tsakani na dakai Alhaji haruna kai kajawo min kaine mugun miji kuma ka dorani akan mugunta wallhi van yafi maka ba...

" Inna ta kalli isa tace to babban azzalumi nima anjima gaba zanyi garin mu ke kuma mamee bakiga komai ba, khalil kuma dashi zan tafi nagyara yarona ka cuceni ka lallata masa rayuwa Allah yaisa tsakanina da kai...


Lokaci daya nakuda tazowa ramlat sai kara takeyi tana ihu yasmin ce ta cere abun hannunta ta liko nan ta ganta sai ihu takeyi ba'a dadi ba ta shirya taja mukullin motar ta dakyar tasamu suka isa mota tsaka ramlat sannan taja mota cikin kankanin lokaci suka isa asubuti nan Likitoci sukayi ciki da ita nan yasmin taketa kokarin samun dr sageer awaya amma shiru bata shiga...

Linda ce ta shigo tace yasmin ko??

Eh nice ya akayi..

Yanzu akayi mana waya dr sageer ba lafiya anyi gida dashi batasan lokacin da ta shiga mota ba taja sai da ta'isa gida taganshi kwance babu alamar buguwa Amma baya hankalinsa dan ko ganeta baiyi ba kuka tasaka tanata addua tana kallonsa mijina wayyo kamar daga sama taga mama da baffa akanta..

" na shiga uku wannan ba asiri bani ba kuwa?

" baffa ne yace asirin lafiya?

" Antaba yiwa mahaifin mu...

" yasmin dake faman kuka tace baffa akaishi asubuti aa yasmin wannan abun bazamu fitar dashi ba sai mungwada na musulunci mungani...

Ina ramlat?? " tana asubuti tatafi haihuwa..

" Nan mama takira mum tagayamusu ramlat na asubuti ta kuma gayamusu suyi gida daita idan ta haihu.....

" Baffa yagayawa hajiya Da ita da Aisha ba shire suka shirya ..

" Mama ce tace wai ke bakida hankali yasmin wannan uban kukan maganin me zaiyi miki??

" Toshi bakinta tayi tahau sama babu shiri tayi alwala sallah take tanayi wa Allah kirari yabawa abokin rayuwarta lafiya...

Kamar daga sama taji ance ke ke ke...

" Atsoraci tace Allah yafiku azzalumai...

Kika kara yiwa mijinki Addu a samun sauki sau kema mun hallakaki...

" cikin kidimewa tafara karatun Alkur'ani aguje ta sakko kasa mama mama sune sune zasu kashe shi wallahi sune...

Baffa ne ya riki hannun ta ta zaunar da ita kusa dashi yana tofa mata addua kuka kawai takeyi...

" Nan aka sanar ramlat ta haihu yarinya mace amma sanadiyar wasu magunguna da ramlat ke faman sha yarinyar babu lafiya ita walau tayi rai walau ta rayuwa...

" cikin ihu yasmin takara jin muryar dazu saura ke muntaba yarinyar kishiyar ki kuma mijinki bazai arzuki ba ba zai same matsayi ba hahaha....

" ihu takara sakawa tace sune sune sune...

" mama ce ta su wanene...

"Zatayi magana aikuwa sai ta sume...

" mama ce tasaka kuka wallahi duk wanda ya illatar dasu Allah bazai barsu ba...

Ki kwantar da hankalin ki cewar baffa bari nafara samo ganyen magarya...

Ramlat dake faman kuka ance yarinya ba lafiya miji ba lafiya mumy ce tace kidaina kuka komai zaizo karshe kinji...

" Dazu fa muka rabu dashi ...

Ai daman hukuncin Allah babu yadda bayayi...

Su hajiya da Aisha sai bayan magariba suka tawo tare da wani babban malamin kur'ani malamin ruqya...

Suna shiga yasmin ta zabure tafara ihu tana kafita nace ko kazo abanza bazamu fita ba...

Mama ce ta riketa bayan yasa anyi mata alwala sannan yazauna mintuna talatin yana karatun Alkur'ani yasmin tanata ihu shima a firgice ta mike dr sageer ya watsa musu wani ruwa sai maganganu zamu fita zamu fita ka daina zamu fita...

" malamin yace me kukazo yi a jikinsu?

" wallahi zamu fita turo mu akayi akace mu hanashi tafiya da magana saboda za'a bashi babban mukami a America jibi...

" Ita kuma matarsa mu muka saka tayi bari muna samun shiga jikinta idan bata sallah kuma muna shiga jikinta idan tana sauraron kida...

" wanene ya turo ku??

" munyi alkawari bazamu fada ba... " yanzu zan konaku yafara karanta surorin azaba sai suka fara haruna ne da isa da nazifi da Abokinsa auwal sune zamu cire ajiyar mu a kafarsa daman yasmin tafi karfin mu tana azkar sai bata cikin ibada muke samun shiga amma Zamu barsu mun ma dauke ajiyar da mukayi wa jaririyar..

" Malamin sai yacigaba da karatu sai sukace muncire a ajiyar mu kuma zamu fita wallhi mutanen kirki ne kuma su dage da addua dan mutanen da suka turo mu basuda imani su dinga azkar da zama da alwala da zama da dankwali ko sunzo bazasuyi nasara ba kuma su dinga sauraron suratul bakara acikin gidan su Aljanu bazasu zo ba.....

" Wannan bayanin dakuka gama kashe ku zanyi saboda agaba zaku iya shiga jikin wasu ai kuwa yaja wasu surori minti talatin sai yasmin tace dr...

" Dr sageer kuwa baice komai ba sai salati da yayi...

Hajiyar sageer ce take kuka tana tabbas zamani yazo da yan uwanka zasu cutar da kai, sageeru inshaaAllahu sai Allah yayi maka albarka kuma zai tsareka sharrin magauta....

" Hajiya yaushe kikazo yayi wannan fara'ar tasa mai bayyana wushiryar sa....

Malamin ne yace yakamata kuji tsoron Allah ku daina wasa da ita ko dan samun tsira ballanta na yanzu makiya sunyi yawa ka dinga karatun Alkur'ani akankai da yawan salati ke kuma ki guji wasa da sallah kidinga sauraron Alkur'ani da kuma yawan zama da alwala kuma kirage jin waka kidinga zama da dankwali kinji...

" yasmin ce tace inshaaAllahu...

Baffa ne yace ku dage da az'kar na safe da yamma..

Nan akayi asubuti gurin ramlat ....

Yasmin ce tace ina zakaje mijina?

" gurin baby na mana...

" To katsaya kaci abinci kayi sallah sai muje tare...

" Tohm yace yayi wanka ta dakko masa shadda tasaka masa turare sannan tace oya kaci abinci sai kayi sallah mu tafi binta yake da kallo kawai Allah yabashi mace tagari sai 9 sannan suka tafi asubuti dr sageer ne ya dauki yarinyar sannan yayi mata kiran sallah yayi mata huduba yace ai da ke take kama...

" yasmin ce tace aikam dai Allah yaraya mana ita..

" mumy ce tace to ni zan tafi su hajiya har sun tafi fa...

" ramlat ce tace nidai dr zanbi mutafi gida sai abu tazauna agurina...

" Mumy ce tace tunda Allah yabata lafiya kuma sun sallameku ai Alhmdlh sai ayi gida ko...


Yau kwana biyar da haihu dr sai nan nan yake dasu duk wasu aikin gida yasmin keyi ita da baki har abinci ma yau da anty aisha tazo ta kawo mata wani maganin mata tunda tasha duk wata kasala da Sha'awa ta rufeta bayan tayi sallar isha'i tasaka wata bodyhug ta kamata ko ina na jikinta ya bayyana cikin siyasa ta nufi dak'insa...

" cikin kissa tace au aiki kakeyi ko kace nazo na tayaka zama tayi kusa dashi sannan ta sumbaci bakinsa...

Cikin kankanin lokaci idonsa yayi ja kallonta yayi yace ina mutukar ji dake yau dinnan sai nasamar da baby inshaa Allahu..kara narke masa tayi ajiki tace nidai kayimin a hankali...

" yasmin idan ina tare dake ina shiga halin sha'awa da kauna hankali yakan gushe danAllah kisoni ni yadda nake sonki...

" cikin murmushi tace bari kaga tafara kissing dinsa daga nan suka fada birnin soyayya....

Bayan sunyi wanka suka sauka gurin mai jego dr sageer yana kusa da'ita ke 'yan bakwai zaki haifa min...

" ramlat tace dan daya ma ina mutum yacika ramlat tace daman ke ba lallai kiyi juriya ba...

" yasmin tace ai naga lokacin juriyar ki kina ta ihu suka saka dariya...

" Dr sageer ne yace jibi zanje karin matsayi dawa zamu tafi...

" yasmin tayi saurin cewa da ramlat zaka itace uwar gida..

" Ramlat tayi shiru to ai aini jego nakeyi kuje dai...

" kunga sai da safe da ke zai tafi ni banson zuwa fa..

" binta yayi har daki yace au dama bakyason a yasmin su kike nadinga sha'awar wasu matan?

" murmushi tayi tace kafata kafar mijina...


Assalamu alaikum

*Kuyi hakuri da rashin rubutuwa akan lokaci..!!!*

*_Sak'onin ku suna isa garine wannan shafin sadaukar GAREKU MUTANEN GIRKI..


Please do vote comments and like 👏

Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo. com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:19 PM] ‪+234 703 475 7034‬: 80-85

  *DOCTOR*
           *SAGEER*

_NA NANA DISO_

      http://nanadisoo.blogspot.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*


Murmushi tayi tace kafata kafar mijina...

Kallon ta yayi yace sai da safe sai kifara shiri ko??

     My dear inason zuwa gidan mama kaga babu nisa damu..

    No! Kibari idan mundawo sai kije ina tunanin zaifi...

    DanAllah mijina kataimaka wallahi nayi missing ummata please..

     Kinga babu inda zakije yafita tare da rufe kofar bai tsaya ko'ina ba sai dak'in ramlat tana zaune tana ta kallon boy dinsu...

    " cikin mamaki tace ya naganka anan??

    "Nifa bazan iya nisa da baby naba nagayamiki bani shi...

    " murmushin mugunta tayi tabbas tasamu wani makaman kuntatawa yasmin...

      " Sunan sa muhammad, bayan mundawo daga tafiyar tun 3 days zamuyi sai ayi sunan zanmiki transfer duk abunda kike bukata sai ayi ko??

     " kwanciya ramlat tayi ak'an kafadarsa inbanda murna babu abunda takeyi ina alfahari dakai mijina ina mutukar sonka wallahi akanka zan iya komai..

   " Ramlat kenan nima ina mutukar sonki sosai..

   Yasmin da takaici ya isheta kuka tasaka sai gurin 2 sannan bacci ya dauketa da safe bayan ta hada breakfast tashirya cikin wani material goduwar riga ya kamata tayi rolling sannan tasa janbaki...

   " ramlat ce tafara cewa irin wannan kwalliya ina zakije??

     Matsowa tayi ta karbi boy tace yarona sannan ta sumbace shi..

    Juyawa tayi tace ina kwana yaya??

      " sai da yadan jima sannan yace lafiya lou..

     " yadda ya amsa mata ita kanta bataji dadi ba ramlat kuwa sai faraa takeyi...

     " yasmin kuwa tahada komai na breakfast sannan ta zauna..

    " ramlat tace yaushe zakije gidan su mama ne??

       " Yau zanje inshaa Allahu..

     " Ki gaishe su in kinje please.." dr sageer dake danna waya yajiyo yace babu inda zakije fa..

     " wani malolo ne yatsaya mata a wuya cikin takaici tace Tohm...

       Tashi tayi zata hau sama.." dr ne yayi saurin kiran sunanta sai tajiyo zo ki zauna ina zakije??

     " Bacci nakeji idonta cike da hawaye zo to kikwanta kusa dani..

     " Shiru tayi bataci komai ba.." ramlat tace karfe nawa jirgin zai tashi ne??

   " karfe biyu yanzu karfe 12 ai...

     " To bari naje nayi wanka nima...

       " Yasmin da takasa magana tashi tayi itama dak'inta tashiga wayar ta ta dauka ta kirawo hajiya tana kuka...

    " Lafiya yasmin lafiya??

  " Hajiya yaya sageer yahanani zuwa inga su baffa tunda suka tare banje ba babu magiyar da banyi masa ba yaki, kuma ni banason nabishi kasar wajen nan danAllah kiyi masa magana sannan tasaka kuka...

    " Daina kuka tagurina inshaaAllahu zan kirasa kuma kwana 2 ma zakiyi agidan..." goge hawayenta yasmin tayi tace hajiya nagode sosai...

Yasmin na zaune akan gado taje dr sageer yaturo kofa yace mata au baki shirya ba??

    " Tace ina zanje?? " Au Tambayata kikeyi? Wato yasmin ban isa nasaka ki abu ba ki bazanji dadinki ba kenan? Da ramlat ce nace tashirya datuni tashirya ko so kikeyi indinga neman mata?? Kinsan yanayi na...

    " kuka tasaka ta fara ciro kayanta sai kuma wayar hajiya ta shigo cikin murna ta kallisa dataji yana gaidata...

     " Ko amsawa batayi ba takamashi da fada kuma kabarta taje ta gaida iyayenta taje tayi kwana biyu in zakadawo sai ta dawo... " doctor bashir da ransa ya bace yace hajiya amm... " Umarni na baka ta kashe wayar...

    " Kallon yasmin yayi idonsa duk yayi jaa yace kishirya kije kiga su umma..

     " Cikin fara'a tace kwana nawa zanyi???

     " Duk yadda yayi miki... "har da dantsallen ta nagode my habiby...

     " Tsako yajaaa sannan yafita shiryawa yayi sannan ya rungume ramlat yace inasonki uwargida na kiyimin addu'a kinji...

     " Ramlat cikin mamaki tace ina yasmin din?? " No ni kadai zantafi sai nadawo 3days kawai zanyi tunda babaa tananan to sai ku zauna ita yasmin zataje gurin baffah..

   " Ramlat ce take kokarin yin kuka ni kadai?? ... " DanAllah Ramlat kada kisani cikib tunani pls.." tohm Allah yatsaremin kai yadawo dakai lafiya...

    " Yasmin kuwa sai ibar kaya takeyi ta dauki kusan kala 7 sannan ta rufe koina ta sakko bata tarar da kowa a palour din ba abunda yabata haushi ko sallama dr sageer baiyi mata ba tana isa gida ta rungume mama lallai baba ya zuba dukiya agidan nan mashaaAllah..

    " Yasmin yanaganki da akwati??

     " sati daya zanyi mama ..." haba auta sati daya yayi yawa kwana biyu dai...

    " Toh mama nan tashiga dakunan..

  
  Mamee ce tace yanzu Alhaji babu wani boka dakasani ma aiki kamar yankan wuka???

     " Alhaji isa ne yace to inma akwai bokan ina kudin aikin...

       " Khalil ne yace DanAllah mutuba mudaina abunda mukeyi tun ina yaro kuke illatar da baffa Amma kullum gaba yakeyi...Dr sageer kunyi masa asiri kan kar yasamu karin girma gashinan asirin ya karye kukallah ya kunna musu wayarsa yadda turawan America suka girmamashi tare da kyaututuka...

     " Basu gigice ba sai dasukaji uban kudin da suka bashi tare da motoci..

   Alhaji haruna ne yayi cilli da wayar tare dacewa wallahi sai munga bayansa bazaiyi kudi ba...

    " inna ce tace kudi na nawa kuma ku dai da zuciyar ku ta mutu kai kuma isa Allah ya'isa tsakanina da kai khalil katashi mutafi ka koma makaranta kayi noma agarenmu idan kasamu mata sai kayi auren ka Ai yanzu kaji jiki kakuma gane sharri dan aike ne ko karufe kofa sai ka bude masa...

   " Khalil ne yace tabbas hakane inna zan biki kukuma Allah yaganar daku...

    " Mamee tace to waya rikiko?? "Ku tafi mana kunga Alhaji isa asaida gidan dasuka tashi sai akaiwa boka ko???

    " Alhaji isa yace gaskiya kin kawo shawara mai kyau sai Haruna ya samo dillalai...

  
    Bayan Angama karrama Dr sageer da karamasa girma wani hotel suka kaishi yana kokarin cire safa wata baturiya tashigo tasaka wasu shaidanun kaya bakinta dauke da red lipstick tana bude kofa tace...excuse me please Dr sageer...

    Dagowa yayi da kansa yace ...hope fine??
      " she smile and say am happy for your success...

    " he reply to her by saying thanking...

       " am juliet am here to help you sleep well..

      " I don't understand...

" she just smile and started to remove his shoes...

     " cikin gigicewa yace thank you please i appreciate...

   " she smile again and say okay let me bath you please....

     " Dr sageer shout and said i don't need any it please u can work out...

     " she reply to him by saying do u need some kiss???

     " cikin zafin nama yace getout...

     " cikin tsoro tafita innalilahi kawai yake ambata da'irin shigar datayi...

   Wayansa ya dakko yafara neman lambar yasmin har zai buga yakatse..yakirawo ramlat sukafara video call...

    " Mashaa Allah dr na yazama tauraron taurari Alhamdulilahi naji dadi..

      " nagode matata kinyi wankan tsarki??

     " No kofa sati baayi da haihuwar ba banyi ba meke damunka??

    " Hawaye ne ke zuba a idonsa tare da fadin kinsan matsalata kinsani ai...

     " Cikin rashin jindadi tace shiyasa nace ka tafi da yasmin ai...  " yasmin batasona bata kaunata ba nine agabanta ba...

     " Shiru tayi tace ai jibi zaka tawo dear kayi azumi mana...

    " Tohm nagode kikularmin da kanki da muhammad kinji...

    " Tohm tace tare da fadin ilove u so much... sannan ta kashe..

    " Hoton yasmin yafara kallo yana hucewa cikin jindadi yace Allah ne yasamin sonki... wasu magunguna ya hadiya sannan yayi sallah yayi bacci...


  Fadila ce tashigo gurin mama ta zauna tanata dariya mama yau baki nemi ne ba...

    " yasmin ce tace sannu..

   " mama tace fadila ga yarinyar tawa laa itace yasmin din kice kinzo mana..

   " mama ce tace yasmin wannan yarinyar kanwata ce hadiza kinganeta kusa damu take kullum tana tayani aiki da zama...

    " Murmushi yasmin tayi hankalin ta duk yana kan dr sageer bai kirata ba har ynzu...

    Mama ai kallo natsaya yi ingayamiki wani matashin mutum america ta karrama kinga yadda kawaye na suketa ihu dama zai aure su gaskiya yayi bawan Allah kinsan ya sunansa??

   Mama tayi dariya tace dr sageer ko???   " fadila ce tasaka dariya tace ashe kema kinkala..

    " D'a nane ai , shine mijin yasmin...

    " yasmin wani kishinsa taji , " fadila tace wallahi ki rikeshi hannu bibbiyu don baki yadda yanmmata ke sonsa ba...

    " shiru tayi tashiga daki duk sai taji ta tsane gidan ma tabbas miji wani niima ne daga Allah wayanta dauka ta dinga kiranshi amma bai dauka ba message babu wanda bata turaba bai kulata ba..

   Washegari ana karyawa baffa yace gobe mijinki zai dawo misalin 6 na yamma sai ki tafe gida da wuri koh?

    " sauri tayi tace inshaa Allahu baffa...

  " baffa yace kunyi waya ko??

   " Cikin sauri tace eh munyi azuciyar ta kuma kuka take kokarin yi...wayan mama ta dauka ta shiga wani room takirawo shi bugu daya ya dauka yace mamata ina yini??

    " kuka tasaka tace yaya nicefa danAllah kayi hakuri wallhi nayi kuskure.. " sauri yayi yakatse wayar sannan yace yasmin bazaki illatamin rayuwata ba sannan yafita...

  Washegari da safe tasa fadila ta nemo mata mai kunshi da kitso sannan tasa aka siyo mata kwakwa tayi lemo dayawa sannan tayi white rice da farfesu tayi hadin salad duk tasa aka kaimata gida ita gurin 5 ta shirya tsaf mama tace kiji tsoron Allah yasmin kije tsoron Allah kikula da dr kiyimasa biyayya danAllah...

     Tohm mama inshaaAllahu..." Allah yayimiki albarka.." Ameen!!!

  Yasmin nakarasawa cikin gidan taga ramlat tanata video call da dr harda su kiss cikin kishi tace sallamata nakeyi...

   " ramlat tace ina nan muna soyewa da mijina banjiki ba sannunki da zuwa...

   Tsaki tayi tahau sama ta bude dak'inta turaren wuta tasaka sannan ta gyara dakinsa tayi waka wata riga da siket tasaka duk saman kirjinta abude siket din duk yadameta dankwali ta daura tanajin shigowarsa ta rungumesa tureta yayi ahankali sannan yace ina muhammad gobe suna inshaa Allahu...

   Ramlat ya sumbata ta mika masa yaron yasmin kuwa duk jikinta yayi sanyi dakyar tace sannu da zuwa ya hanya??

    Banza yayi mata ya kalle ramlat sunata hira..

   Yasmin da batasan lok'acin da kuka yacita ba tatashi ta hau sama kallonta kawai yakeyi dr duk jikinsa ya mutu, kuka tayi sosai sannan tayi sallar isha'i tafesa turare ta nufi dak'insa tana shiga taga yana kwanci cikinsa nata ciyo sa juye yakeyi a tsoraci tace lafiya yaya tasaka kuka...

    Maganin da yake nunawa ta dakko tabashi...kuka tasaka tace DANALLAH kayi hakuri wallhi nayi kuskure DanAllah kada kayi fushi dani zanshiga wani hali...

   Bakyasona ko? zan iya shiga mugun hali  yasmin bakya kaunata? Zan sakike sai ki aure wanda kikeso... sai ya sume..

     " A furgice ta mike tana A'a A'a A'a yaya ina sonka ina sonka Tasa wani mahaukacin ihu ai kuwa sai tawadi aguje ramlat tashigo....



Assalamu alaikum

   *Kuyi hakuri da rashin rubutuwa akan lokaci..!!!*

      *_Sak'onin ku suna isa garine wannan shafin sadaukar GAREKU MUTANEN GIRKI..


    Please do vote comments and like 👏

   Urs *Nana diso*

Email:kabba43@yahoo. com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO
[11/6, 1:19 PM] ‪+234 703 475 7034‬: 85-90

*DOCTOR*
*SAGEER*

_NA NANA DISO_

http://deejarhberver.wordpress.com

© *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

A furgice ta mike tana A'a A'a A'a yaya ina sonka ina sonka Tasa wani mahaukacin ihu ai kuwa sai tawadi aguje ramlat tashigo....

Hank'alin Ramlat bai tashi ba sai dataga doctor sageer baya motse kwata kwata batasan lokacin da ta ajiye muhammad ba tana kuka takirawo dr khalifa dakyar ya dauka yace matar dr ya'akayi??

" kuka tasaka tace mijina ya mutu, wallahi yasmin ce wayoo ka taimakeni danAllah...

" Kashe wayar yayi yajuya kan motarsa sai gidan dr sageer yana shiga ya hau sama hankalin sa bai tashi ba sai dayaga yasmin akwance bai bi takan dr sageer ba yafara dubata...

" Dr khalifa yazaka biyewa wannan mahaukaciyar yarinyar batason shi bata kaunar shi, itace sanadin komai tasa kuka...

" dakata ramlat karya kikeyi wallahu yasmin bazatayi haka ba da dai kece kowa yasan zaki aikata haka, bazaki fadi kyakyawar kalma ba haba sai kace ba musulma ba...

" Ai daman nasan haka zakace yayi mata banza ya dudduba yasmin nan yasa ramlat ta kwantar da'ita wata allura yayi mata sannan yayi hanyar fita..

" Dr mijina fa dr kataimaka, mijinki nan da minti biyar ma zai watsake matsalar sa mai sauki ce wallahi kuji tsoron hakkin yasmin kuji tsoron hakkin ta yarinya karama ace jininta yana hawa...

" Ramlat ce tajaa tsaki ta mutu mana sai me sai me kuma ai nasanar dasu mama duk abunda takeyi..

" Bai saurareta ba yatafi...

Mama ke faman sintiri apalour tana innalillahi..

" fadila tace haba mama wallahi yasmin bazatayi haka ba sharrin kishiya ce wallahi bazatayi ba, to kinkirawo ta kinji ta bakinta???

" Mama cikin fada tace ai tasan tayi laifi bazata dauka ba...

" DanAllah mama kidaina fadin haka please...

" Wani numfashi mama tajaa sannan ta goge hawayenta so kikeyi ace ninake zugata idan ta kashe musu yaro fa...

" Makiyi ai duk abunda bayaso babu sharrin da bazaiyi ba kiyi hakuri danAllah...

Tunda doctor sageer ya tashi idonsa yayi jajir wanka yayi ramlat sai sannu takeyi masa...

" Kallon yasmin dake kwance yayu yace wannan fa??

" ina tunanin bacci takeyi, tsaki yajaa sannan yace yunwa nakeji sosai cikin murmushi tace katashi muje kaci abinci..

" murmushi yayi yace ina babyna??

" yana gurin iya bari nakarbo shi suna hira yace abinci sannan ya zauna kallo nan ramlat da matsa kusa dashi tana ta bashi labarin budirin da za'ayi gobe yanata dariya...

" wasa yake tayi da muhammad yace ita bazata tashi ba kenan???

" ramlat ce tace uhm kaikama damu da wanda bai damu dakai ba..

" Shiru yayi baice komai ba..

Yasmin dake kokarin bude idonta hawaye ne yabiyo bayan budewa tashi tayi zaune tace tabbas da namiji hankaka ne gabansa fari bayansa baki, yaya baya sona baya kaunata gashi yace zai sakeni yanzu in yasakeni ina zanje mama bazara barni na zauna gurinta ba hajiya kuma yaronta ne tasaka kuka mai cikin da kuna, A hankali tace inshaa Allahu bazan sake cewa komai ba daga gaisuwa sai kuma in yace nayi wani abun... hannun ta tazata daga taji alamar alura zafi taji nan taje dakinta tayi wanka sannan ta zauna ga yunwa da takeji...

Hijjabi tasaka har kasa sannan ta sakko daga benen tana kallon su sunta hira ramlat rungume da muhammad dining ta duba taga shinkafa jallop haka ta zuba ta zauna taci, wata kasala taji sannan tace sai da safenku...

" Ramlat tasa dariya tace yauwa...

" yasmin tana shiga dakinta tace tabbas dr baya kaunata baya sona har yaushe mukayi auren yafara wulakanta ni wayoo Allah na tasaka kuka mai cike da kunci tare da fadin tabbas wannan shine KUNCIN RAYUW ramlat bata kyauta ba tunda tasaka SON ZUCIYA acikin aikinta wayarta tadakko number mama tagani kusan kira 20 cikin tashin hankali ta bi kiran to ko ya sakeni naga bai kalleni ba shikenan nashiga uku takara saka kuka ....

Alhaji haruna ne ke cikin dokar daji yanata wasu abubuwa har ya'isa bayan wani dutse yana zuwa boka yace nasani nasani ka ajiye dubu hamsin zamu gama maka dasu..

" Murmushi alhaji haruna yayi yace ga dubu hamsin nan muna godiya boka..

" tashi katafi zamuyi hahahaha...

" yana tafiya boka yace ai ku matsalar ku kenan kada wani yafiku bansan komai ba yasa dariya yau dilu zataci kaji inba da harkar karyarba babu mai bani dubu hamsin haha yashige gida...

Alhaji haruna tunda yakarasa gida yake fadin ai kawai sai dai kuji labarin mutuwar baffa da sageeru...

" mamee ce tayi guda tace damun zama masu arzuki...

" Alhaji isa dake faman washe baki yace ai bokan yafa'iya aiki sosai karku damu..

Yau kwana 5 kenan tsakanin yasmin da dr sai kallo tun tana sakkowa taci abincin har ta daina takama azumi tabbas mai samun kulawar miji dan gatane don ranar suna ma sai da momy tace tazo ayi hoto da ita sannan ta dan sakko...

" Hankalin dr sageer baitashi akan yasmin ba sai dayaga bata bude ko kofarta tabbas yasan bai kyauta ba amma kuma haka shine daidai kodan ya hukuntata kuma irin kalaman da

Please Login or Register in order to submit comment