Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sunan ka sageeru ina jimaka tsoron zamanin nan mutum yayi auren ya yacika ballantana ku yaran zamani...

     " Hajiyata ki kwantar da hankalin ki wayata tagaba dake inshaa Allahu ak'an aure nace...

    " Yauwa ko kaifa Allah yayi maka Albarka yakuma tsaremin ku sharrin mutum da Aljan..

   " Ameen hajiyata Allah yakara lafiya agaida su hammad da nazifi inanan tafe inshaa Allahu...

    " Yauwa dan kirki zasuji kahuta lafiya kace ina gaida baffa da yasmin..

   " Tohm inshaa Allahu..

   Yusra ce tace oh tasmin akwana atashi babu wuya kinga saura shekara daya mugama, muna dawowa kuma sai waec da neco ko?

    " Shiru tayi tana tunanin baffa tasan bashida kudin biya mata tayi jarabawa hawayenta ta goge tace eh hakane...

    " Wallahi yasmin akwai abunda ke damunki sosai ke mutuniyar kirki ce Dan Allah ki taimaka kigayamin bakisani ba ko nakawo miki mafita kinga daga yau bazamu kara haduwa ba sai bayan hutu...

    " Cikin murmushi mai kama da damuwa tace yusra bazan dawo makaranta ba...

    " saboda me yasmin??

" saboda baffa na baida kudin biyan jarabawa idan yasamu nan gaba sai nazana dan bazan matsa masa ba wallhi....

    " haba yar'uwata kada ki damu kamar kin zana jarabawa menene amfanin k'awancen mu idan bazamu taimaki juna ba...

    " Allah sarki yusra nagode to Allah yabiyaki ke da iyayenki da irin dawainiyar da kukayi dani,wanda mukazo tare ma basa kulani ballantana kuma ita yayartawa...

     " Bakomai ai daman naka yaki ka wane ya soka!..

   " Tabbas hakane zomuje muyi alwala sai mu huce masallaci ko?..
 
   " Ehhh..

    " Ameen yace..

Barister wai yau lafiya kuwa ba walwala gashi kamar baki da lafiya??

   " Wallhi munyi fada da dr na shiyasa nakasa sukuni yak'i daukar wayata yau kusan 5 mouth ko ta kaina bai bi nayi masa text akallah sunyi 50 wallahi "no reply i really love my dr i don't think zan rayu babu shi wallhi I so much lurv him kinsan dai kauna to itace a raina kuma ta dr ce wallahi"..

  " Ayyah ni zan kokarta naga na shiryaku inshaa Allahu bani number dinsa  na kirasa naji...

    " cikin rawar jiki tabata sannan tace amana Amal karki yaudareni kiji tsoron Allah...

    " Ramlat kenan nifa saura 1mouth biki na kuma dan Allah zanyi miki wallhi...

   " Nagode nagode sosai...

  
   Daidai misalin karfe 3 yasmin ta sauka a mota bismillah tayi sannan ta bude gate din gidan su cikin annashuwa da kuma farin ciki, maganganun da suka dak'i kunnuwanta yasa ranta ya bace cikin sauri tafara tafiya...

   " Alhaji isa ne kefaman cewa wallhi yau sai kabani dubu 50 d'ita idan bahaka ba wallahi kotu zata rabamu banza asararre mai jinin tsiya wanda dubu daya take gagarar sa...

     " cikin hawaye baffa yace haba dan uwana kayi hakuri dan Allah wallhi ina samu zanbaka...

    " bilal ne yace kaji tsohon banza hhahaha...

   Yasmin ce ta ajiye akwatin tacikin zafin nama (Daman bahaushe yace mai hakuri  bai iya fushi ba) kai bilal iya bakin ka kasan wazaka zaga idan zasuyi kabarsu suyi su biyu...

    "  Gaba daya suka jiyo suna kallonta takara ktau ga wata kiba datayi ga halittu ko'ina sun ciko abun dai bazaka ce yasmin bace sai ka kara kallonta sosai...

    " ke yasmin ni kike gayawa haka...

    " nunashi tayi da hannu tace kai bilal idan kanacin kasa to ka kiyayi ta shuri ubana ba sa'anka bani kuma kakara zagensa sai ranka ya baci wallahi...

    " Alhaji isa ne yace shigeya 'yar iska yimun shiru dangin talakawa idan kin cika kinason uban naki to sai kibiya masa kudin. ...

   " Jakarta ta zuge tabashi dubu hamsin sannan tace tozarci badai akan mu ba kuma ni inada tarbiya bazan ci maka kala ba Amma ina fata Watarana ku gani abunda kukeyi...

     " kallonta yayi yace shigeya karuwa inba karuwanci kike ba a'ina kika samu kudin nan...

    " tsaki tayi tace nanawa kenan ance da bunsuru dan akuya?

   " baffa ne yace shige muje shige muji yasmin...

    Bilal kuwa ranshi ya baci shida mahaifinsa suka fita basu so hakan ba...

   " mama ce tace daman malam nagaya maka kasamo musu kudinsu gashi kaga yadda takaya...

  " yasmin ina kika samu kudin nan har dubu hamsin???

    " Nan tabashi labarin yusra da kudin da mahaifinta yabata yace tabawa babanta abiya mata kudin jarabawar ta..

   Allah sarki mutanen kirki mungode nan baffa yace banson fitsara yasmin ko gaba kada kikara tanka musu kinji? Duk abunda sukeyi zasu kwashi kashin su a hannun su...

   " Tohm baffa bazan karaba inshaa Allahu..

   Bayan sallah magriba yasmin da mama suna bangaran su a soro a zaune dr yana dai dai kofar zai shigo sai yaji yasmin tana fadin..

   " Ni nahakura da jarabawar mama zamana zanyi bazan koma ba kudin dasuka bani naje nabiyawa baffa bashi domin kare mutuncin sa...

   " karki damu yamin Allah zai hore kinji murmushi tayi tace kems ga chanjin kudin kya siya wani abun...

   " yasmin kenan Allah yayimiki Albarka...

   Doctor tunda yaji kalaman yasmin hankalinsa ya tashi nan ya sanar da principle din yaturo masa da Account number yatura kudin jarabawar kamar daga sama yaji wayar ramlat cikin yanayi yace hello?

   " kuka tasaka masa kayi hakuri dan Allah hubby please nasan nayi maka laifi wallhi u are my life..

   " Ya huce ramlat Nima ina sonk'i sannan ya katse wayar...

" Yasmin tana zaune a k'an k'ujera sallama taji sannan ta daga k'anta yaya ina yini???
 
    " ah kanwata k'inzama 'yar dumama ke da boarding ke ramarwa ke kinyi kyau...

    " Murmushi tayi tace Allah yaya?

    " Wallahi kam nayi missing dinki sosai...

   " Shiru tayi sannan tace yaushe ne bikin naku ne da barister?

    " Gobe za'akai k'udina nida barister inshaa Allahu...

    " kai mashaa Allahu, Allah yasanya alheri zamusha biki ashe?

    " inshaa Allah please ki dafamin indomie zandawo anjima kinji??

    " Tohm shikenan..

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

   GOD BLESS YOU OLL....

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:22 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 15-20

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Yasmin kin dora abincin dai ko?

     " Eh mama,har nagama ma dr ne yace na dora masa indomie yanzu zai dawo...

    " Ke dai jininku ya hadu da sageeru bakamar su abida ba?

    " Suma dan basajin magana ne..

    " Lallai yasmin kinsamu bakin magana, Naga kema jiya fad'a kukayi da bilal?

    " haba mama yaza'ayi ina gani ana zagin baffa nayi shiru ni wacce irin yarinya ce?

    " Ai gwara da kikayi masa magana wallahi bilal bashida kirki babu wanda yake gani da gashi agidan nan...

   Kamar daga sama sukaji sallamar Aisha dagudu...

    " oyoyo oyoyo yaya Aisha sannu da zuwa cewar yasmin..

    " Ai bakida kirki yasmin ace kina kanwata sau biyu kika taba zuwa benin dubi yadda kikayi kyau, kuma wai mama kina ganin ta?

    " ke dai shiga muji ki huta ke da kikasha hanya...

    Suna shiga palour ta durkusa har kasa tace ina yini mama?? Kuna lafiya??

     " wallahi lafiya kalou yasu mujibat da hamid duk suna lafiya dai??

     " lafiya kalou wallahi ina baffa?

    " baffa yana gurin aiki ai sai yamma ke da ganinsa...

    " yasmin ce tace kinsan garin naku ne nisa shiyasa baya burgeni...

     " k'injiki ai ke a kaiki mambila naga tsiya..

    " ke dai dakikayi auren nisan inshaa Allahu ni bazanyi ba!..

    Dr sageer ne yashigo direct kitchen ya huce dan yasan yasmin tagama ta ajiye masa...

    " Mama ce tace ke yasmin ba kauri nakeji ba??

   " wayyoo indomie din dr cikin sauri ta isa kitchen din ta tarar dashi atsaye yama kasa magana...

      " cikin garaje ta riki tukunyar ai kuwa sai tasaki saboda zafi sauri yayi ya riki hannu subhnlhi badai ki kone ba ko??

    " Kayi hakuri wallahi ina hira ne shiyasa ta kone...

   " Kallonta kawai yakeyi cikin wani irin salo da sai da taji wane yanayin dabata taba jiba acikin jikinta...

     " Murmushi yayi yace bakomai bari naje na siyo wani abun...

    " sai tace ai mungama abinci kaje daki bari nazubo maka...

    " jikin wani salo yace mijinki yahuta yasmin...

     " Shiru tayi masa batare da tace masa k'alaba..

Mamee ce tace wai ke maryam menene haka tun safe kike abu daya in anyi magana kiyi shiru meke damunki??

   " Gyara zamanta tayi tace cikina ke ciwo..

     " bari nakirawo sageeru sai yabaki magani inaji yana cikin gida ai...

     " can tace mamee nawa aka kai kudin auren dr?

   " dubu dari biyu mana, ansaka wata daya bikin...

    " Cikin sanyin murya tace Allah sarki ...

    Aisha ce tashigo part din su mamee tare da yasmin dr yana bayansu Assalamu alaikum hajiya mamee menene duniya???

    " Tsaki tayi tace kin bayana kenan uwar magana lafiya dai kikazo ince ba auren naki ne ya mutu ba??

    " Aisha ce cikin siyasa tace ina auren mu zai mutu naku bai mutu ba kuna soyewarku...

    " Ai nayi tunanin auren ne ya mutu ai kizo kukarawa baffan ku wani hawan jinin???

    " Ina ai igiyar aure Allah kadai ke rabata mutum komai shidancin sa bai isaba...

    " Tsaki takaraja ciki da tsanar Aisha da yasmin can tace sageeru Maryam babu lafiya fa?

     " Yasmin ce tace yaya ana magana?

    " Allah yabata lafiya anjima tashirya driver sai ya kaita asubuti ai..

     " To shikenan ina surukar tamu??

    " tananan tana gaidaki...

      yasmin ce tace yaya Aisha tashi mu tafi...

    " Sum sum sum dake uwar munafukai daga zuwanta zakice tatashi ku tafi to takiya...

    " yasmin dai batace kalaba, Aisha tace ohh naga ranar da zaku gani wallahi in banda zumunci mai zai shigo damu??

    " Ai kun tsosa agurin uwarku dole kuyi fitsara...

      " tashi sukayi suka fita suna fita sukaga Alhaji haruna nan Aisha ta gaidasa..

     " dangin tsiya kice kin bayyana bakar kadara haihuwar asara...

    " Ko sauraran sa basuyi ba haka suka huce suka huce part dinsu sannan suka fashi da kuka...

    " Mama ce tace ke aisha daga zuwanki sai kuka??

   " Mama wannan wacce irin rayuwace ta kunci haba mama wannan cin mutuncin ace shi iyayena suke ji...

    " Yasmin ce tace ai kadan kikagani yaya wallahi inkinga yadda suka tozarta baffa jiya sai kinyi kuka kuma wai ace bazamuyi magana ba???

   " Mama itama taji haushin abun amma sai ta dake tace ai sai hakuri watarana zai zama labari ...

   " Aisha ce tace ni ko atatsuniya ban taba ganin irin tsanar nan ba?
 
    Hakuri dai zakuyi Allah yana sane damu...

Mummy ce tace Allah yanunamin ranar auren nan naki barister yau dai ankawo kudi...

    " Murmushi tayi tace mumy kinga gidan dayakeyi kuwa anjima zai turomin dan haka kisanar da dady asakamin hadaddun kayan daki please...

    " Oh wannan wacce irin Amarya ce lallai zamani...

    " mumy kenan Wayar tace tafara ringing cikin sanyin murya ta dauka darling dafatan kana lafiya?

    " ke zan tambaya dafatan kina lafiya? Tun dazu tunanin ki kawai nakeyi acikin office , Ramlat ina tsananin sonki DanAllah ki kula dani?

    " Har cikin ranta taji tace mijina bakada matsala ba, nima ina kaunarka dr zan iya komai akanka kuma zanyi maka hidima,zuciyata bazan bude wani yashigo ba ko kadan bazan so naga kayi fushi ba...

    " Ramlat banason wannan aikin naki please ki rage saboda ina bukatar kulawar ki...

    " DanAllah Mubar maganar aikina darling..

   " Shiru yayi yace to sai anjima.." cikin juyi ta rungume wayar tare da murmushi, cikin mintuna taja motarta sai office tana iss tace kawata kinsan me??

   Sai kinfada ince dai mutumin zai sakar mana kudi??

   " ke ba wannan ba kinsan yace wai na jiye aiki!!!

    " mtseww bashida hankali ke doluwar inace dazaki ajiye aikin ki ke yana zura kafarsa kema ki zura duniya fa sai da wuta bakiga yadda manyan mata ke shakstawarsu ba???

    " Dadina dake kinaso ayi dani wallahi kam daman yaudarar sa zanyi nace zanbari sai nashiga daga ciki nacigaba...

    " Yauwa ko kefa, barister lawal yana kiranki kije yana office...

     " Tohm ina zuwa kawata bari naje nadawo nadan maganar case dinnan ce.

    " Rabia ce tayi dariya mugunta tace ai sai najawo kinsa  yasake ki da kanki banza tazata sonta nakeyi? Duk duniya na tsaneta yadda kika samu miji bansamu ba kema bazan barki kiji dadi ba.

    " Barister ramlat ce tadawo tace kawata me muke cewa ma?

   " Uhm daman zancen kudine million uku yakamata yabaki nagyaran jiki karki yarda ko million daya yabaki mugune fa dr yana samun kudi sosai....

     " kinaso kiga nafito kawata kinaso kiga ina harka ban mutafa sannan suka tafa.

Yasmin ce ta dawo daga gidansu fatima tun akan titi wani saurayi ke binta amota har tayi sauri tashiga gida, A dai dai lokacin Alhaji haruna yaganshi sannan ya karaso yace lafiya kuwa??

    " har kasa matashin ya durkusa yace ina yini baba? Daman wata yarinya nagani tun dazu shine nazo gurinta yanzu tashiga ciki..

    " fara ko baka lukutar ko siririya??

    " yadan rissina yace yanzu dai ta shiga.

   " To ina zuwa, daman kafin yakarasa yasmin tafito nan tace sannu ina yini? Lafiya dai ko?

    " wallahi lafiya kalou daman inason mudan tattauna ne ina yawan ganin ki wallahi kuma naji kinshiga raina inason kitaimaka kibani dama in shiga sahun samarin danAllah?

   " Shiru tayi batace komai sai ji sukayi Alhaji haruna yana kai yaro wannan yarinyar dakake gani cikakkiyar karuwace bin maza da mata agurinta yadda kasan dabba, dama daya daga cikin yarana kace kanaso da yafi dan sunfita tarbiya...

    " kuka tasaka tace Allah shaida ne kifa mata mari yayi yace zaki yaudari yaron mutane shigiya 'yar iska..

     " matashin saurayin ne yace kaji tsoron Allah katuna tsayuwar ka da Allah sannan ya shiga cikin motarsa ya tafi..

    " Ke kuma bakiga komai ba sai mun saka miki bakin jinin kare...

    " Da kuka tashiga cikin gidan tagayawa mama komai Aisha tace kyalesu yar kanwata Allah shaidar ki ne Ai kuma shi zai cigaba da karemu karki damu da maganarsu.

   Baffa ne yayi sallama Aisha tayi masa sannu da zuwa nan suka gaisa yace auta wayatabaki? " Dariyar karya tayi tace babu kowa baba.." To kinji ankafe sunanki amasu zana jarabawa ran monday zaku fara sai ki shirya. " cikin mamaki tace baffa wa yabiyamin? " sageeru ne sai kiyi masa godiya. " inshaa Allahu. " Mama tace aikuwa angode.

   " Aisha ce tace kasan ina koyarwa baffa kuma ina daukar kudi masu yawa gakuma business da nakeyi wallahi baffa bana taba komai acikin kudin sai dai ko idan zanyi taimako Allah yabani miji nagare komai shi yakeyi min bana siyar komai kuma nasan gar da adduar da kukeyi min duk da bana kusa daku domin ku iyaye nagari masu koyar da hakuri da yadda da kaddara.. " yasmin ce tace hakane yaya Aisha. " wannan jakar million 4 ce aciki da dubu dari 3 duk kudin aiki na da sana'a tace nakusan shekara 10 danake tarawa wannan gaba daya nabar maka baffa kaja jari domin tarbiyar da kake bani wallahi banda abunda zangode maka duk da bana kusa dakai komai kanwata tasa sai ka turamin duk da munyi nisa kuma mahaifiyata batasaniba, hatta kudin makarantar da kabiyawa yasmin naga kasiyamin atampa duk dan karka fifita wani acikin mu, kaja jari baffa ina fatan wanna kudin yazama dukiyar da Al'umma zasu amfana da'ita ..

    " yasmin ce tasaka kuka ta rungume aisha tare da fadin tabbas nayi wani sabon karatun Anan idan kanason d'anka yatashi cikin tafarkin gaskiya to kasanar dashi ilimin addini kakuma zama babban misali nagurin koyar tarbiya,kar kuma kanuna masu bambanci , abunda zamuci miki shine Allah yayimiki Albarka yaya inasonki wallahi...

    " Mama ce tasaka kuka tace tabbas mai hakuri shikeda riba, ako da yaushe baffa kana fadan Allah yana sani damu kuma zai dubimu yau gashi ranar tazo ranar da mai hakuri zai ci riba, Allah yayi muku albarka aisha Allah yasaka muku da Alheri halinki nagari yasa 'yar uwarki tagado halinki...

    " Baffa ma yayi musu addua tare da godiya sannan yace yadda kikace naja jari zan koma sana'ar mahaifina wato atampofi tunda tun ina karami na iya sana'ar daman ba lallai kayi ilimi kakuma samu sanaar da kake tunani ba wane sain sai kaga alkhairin ka yana inda baka tunani especially idan kana addua ...

   " Tabbas hakane..

Yau Aka kai lefen dr sageeru akwati goma sha biyu kaya masu kyau, wani satin za'a fara biki yasmin kuwa ta hada kayanta zata koma boarding tun karfe 8 baffa yasa aka kaita gida ya cika da hidimomi kalakala..

    " Da daddare dr sageer yaje gurin ramlat taci kwalliya bakace ita bace ba daman irin siraran matannan ne ga ido amma batada hanci sosai kuma ita chocolate colour ce sai dai iyayi acikin ta kamar me tana zuwa tace ya muradin zuciyata..  " Cikin kayataccen murmushin sa wanda ya bayyana hushiryar sa da hakorin makka yace Amincin Allah ya tabbata agareki ya ruhin zuciyata amaryata kuma muradi
na...

    " yauwa mummy tace in gayamaka kayafa sunyi sai sai Allah yabiyaka kuma gobe zasuje jiran kayan dak'i ..

    " Dariys yayi yace tohm shikenan na riga nacika saman ku kwacika kasan kitchen dinki katoto kinsanni da son abinci...

    " Haha lallai kam..

   To ni inada aiki yanzu sai zuw gobe in Allah yakaimu..

   " kagaida gida sannan tashiga cikin gida..

 
Baffa ya bar aikinsa yasamu babban shago ya zuba kaya aciki, da magriba yana dawowa yayi sallah, Dr sageer yana shigowa yace baffa naga yanzu kana yin yamma??

    " Eh da yake yanzu nakoma shago nazuba kaya.. " shago baffa? Ina kasamu kudi?? " Wanda ya yarda da Allah ai shi zaisha kallo, ga dubu dari tukwuicin bikin ka Allah yasaka albarka a auren ku kuma kaji tsoron Allah kariketa dakyau..

    " To baffa nagode Allah yakara budi sannan yatafi, " mama tace gaskiya nayi dacen miji wallhi mai boye sirrin gidan sa akwai da babu..

   " Murmushi yayi baice mata komai ba...

    Yau jumma'a yau aka fara biki sunyi kamu da dinner sai dauren aure abun ba a magana sai wanda yaje biki dai yayi kyau sosai kuma manyan mutane sun halacci bikin su abida da maryam da bilal basu haukace ba sai da sukaga gida kowa baisan yana ginin ba kallon kolo sukeyiwa dr sageer nan suka dawo gida suma zagin. " mumy da dady sunyiwa ramlat fada abisa gaskiya da amana sannan aka tafi da ita hajiya suwaiba itama tayi mata sannan akayi gidanta..

   Lokacin da aka kaita bayan kowa ya watse tayi kwanciyar ta sai bacci lokacin da dr sageer ya shigo yaganta ta kifa cikinta sai bacci takeyi yana kokarin tashinta sai kuwa tace please darling bacci sai da safe shima haka yayi shafa'i da wutir sannan ya kwanta da asuba kuwa bayan yafita tayi sallah rabia ta kirawota tace kada fa kisake kice zaki zauna kiyi tawowarki office kinga munada case mai zafi..." eh daman zanzo sannan ta kashe wayar...

   " Hajiya suwaiba tare da aisha suka koma benin , yasmin kuwa batasan abunda ake ba tana can tanata karatun ta..

    Su abida kuwa yanzu aka kara samun kofar yawo, mamee tace kowannen su yaje ya dangwalo mata babban arzuki dan bazata aurawa talaka ba..

   Ina zakije ramlat??

" wacce irin tambaya ce dr inada aiki mai mahimmanci a office i neef to live kafin na makara..

   " Ai ban baki izini ba ko ni na dauke hotu a office.." sai ka koma kaga matarka tafita itama..

    " Ramlat ban baki izini ba nagaya miki...

    "  hmm kaga sai nadawo...

   " zama yayi kan kujera tare da takumi...

_*Love you oll for being this awesome readers..please do vote and comment...*_
  
  _Let me know what you think about this page...Ku gayan ra'ayoyin ku..._

    *i request you to avoid spelling and grammar error....#TEAM DS*

   *WANNAN SHAFIN SADAUKAR WANE GAREKU FACEBOOK READER'S ALLAH YASAKA MUKU DA ALHERI SAK'ON NINKU SUNA ISA TA, INA KUMA GODIYA SOSAI...*

   GOD BLESS YOU OLL....

Ya zo a hadisin Mu'ãz d'an Jabal (RA) yace: Manzon Allah (SAW) yace:
(( Ka ji tsõron Allah a duk inda kake, sannan ka bibiyar da kyakkyãwan aiki a kan mummuna; sai ta shãfe/guge ta -ita mummunar-, kuma ka yi mu'ãlama da mutãne da kyãwawan d'abi'u )).
Imãm At-tirmizy, kuma yace: "Hadisin Hasan ne".

Wato ana son bãwa ya yawaita kyãwawan ayyukan alheri, musamman ma ace ya yi wani aikin kuskure ko sã'bo, to, sai yayi sauri ya tuba kuma ya yi kyakyyãwan aiki.

Sai jin tsõron Allah a duk inda mutum yake, kuma inda tsõron Allah yake, shi ne zuciya; sai dai ayyukan fili suna nuna abin da mutum ya qudurce a zuciyar, dã wani zai ce shi yanã tsõron Allah, sai kuma aka ganshi yanã abin da ya sã'bãwa taqawar; to, qarya ya fad'a kenan !

Abin da ke sanya bãwa yin taqawa kuwa shi ne tsananin kulãwa da zuciya da hanã ta bin son zuciyar, sa'an nan a tilastã mata wajen tsantsar biyayya ga Allah da kuma Manzon tsira (SAW).

Ana son bãwa yayi kyakkyãwar mu'amala da 'yan uwansa 'yan Adam kai har ma dabbobi, shi Allah (SWT) yanã duba aiki mai kyau ne wanda zuciya ta tausaya yayin gudãnar da aikin, sannan duk wanda aka kyautatãwa su ne suke yiwa mutum adda'a musamman bayan komawa gidan gaskiya.

*Urs Nana diso*

Deejarh berver

http//:deejarhberver.wordpress.com

Email:kabba43@yahoo.com

Gmail:nanadiso100@gmail.com

Wattpad:NEIRNAHDISO

  
[11/6, 8:23 AM] ‪+234 703 475 7034‬: 20-25

*_DOCTOR_*
        _*SAGEER*_

_NA NANA DISO_

      http://deejarhberver.wordpress.com

   © *HASKE WRITER'S ASSOCIATION*

Dr sageer da yakusan rabin awa azaune ya rasa me yakeyi masa dadi,tabbas wahalar da yasha acikin rayuwarsa bazata faduba shi a tunaninsa yasamu mata tagari wannan zaiji dadi da'ita Amma ina brstr ramlat ta yaudari shi da k'alaman ta Yana, cikin sanyi jiki yace ya Allah kaganar da Matata tabbas inason ramlat....

     " sallama tayi acikin office din tace kawata kinga nafito ko?

    " rabia ce tace yaya kukayi da mutumin naki??

     " Wallahi baiji dadi ba harda cewa bai bani izini ba...

    " Dallah kyaleshi ke kike tashi ai yanzu lokaci ne da account dinki zai kara nauyi fa?

   " kamar yaya??

     " Rabia ce tace ke komai bakya kawo wuta ina nufin lokacin da zaki tatse kudi agurinsa yazo ke hatta dariyar ke kice sai ya siya if not ki kuntata masa...

    " haba kawata mijin nawa?? " lahh kinjiki sai kace ba barister ba ai tahaka ake kwace miji ai abinci ma kice baki 'iya ba..

    " Hahaha rabia kina bala'in sona fa ina godiya kudin adinga yimiki transfer kema koba haka ba??

     " yauwa bestie kokefa bari mu tattauna akan wane case...

Mamee ce ta kalli abida da maryam tace shigen raina mutune da kukeyi kukalli dai gidan da dr sageer yagina yadda kikasan 'dan shugaban kasa...

   " maryam ce tace wallahi mamee har Allah yaisa sai danayi azuciyata da ban aureshi ba ashe yanada kudi sosai da sosai...

    " Alhaji haruna ne yace ai sageeru babu maijin cikinsa ba'asan me yake samu ba shiyasa Amma nasan ta yadda za'ayi zan rance kudin nasa sannan mucinye mu hanasa...

    " abida ce tace yauwa Alhaji gwara haka dan mu gaskiya bama jindadin da yakeji kwatakwata naga mama ma sai sababbin kaya take sawa inaji shi yabata...

    " Aikuwa zaizo yasameni inji mamee..

   Mama ke zaune ak'an tabarma ta kalli baffa tace ya cinikin naka kuwa???

 

Please Login or Register in order to submit comment