Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

*🔥BAKON YANAYI🔥*


*D/AUTA NOVEL*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*🔥BAKON YANAYI🔥ya shigo mani babu zato kaina in da rai da rabo ni da ku mutu kan raba har raina💃🏻INA MASOYA LITTAFAN HADIZA D/AUTA 😝ku marmatso ga 🔥BAKON YANAYI 🔥NA KUD'I NE MAI BUK'ATAR BOOK D'IN TA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 Da d'ari biyu kacal zaki mallaki book d'in 🔥BAKON YANAYI🔥 tun daga farko har k'arshe idan ALLAH ya ara muna rai da lafiya tareda lokacin gaba d'aya sayen nagari maida kud'i gida😹Nagode🤝🏻*

Free page 1.

**********************

A guje ta shigo d'akin ta tana kuwwar fad'in,

"Wayyo ALLAH *munawwa* yanzu ya kirani ya kusa k'arasowa" tana maganar tana tub'e kayan jikinta ta fad'a toilet jikinta sai rawa yake saboda d'oki, wadda aka kira da suna *MUNAWWA* ta bita kallo a cike da mamakin rawar jikin da takeyi akan zuwan wannan guy, duk da tasan yanda *MUNARA* take bala'in son shi amman dai duk da haka taga rawar jikin tayi yawa, idan kuma tayi duba da wannan ce had'uwar da zasuyi ta farko, dole ne tayiwa 'yar uwarta uzuri don ko ita kanta guy d'in yan ma burgeta sosai.

A cikin kuzari ta tashi ta bud'a wardrobe d'insu ta zab'owa munara wata had'ad'd'iyar doguwar riga ta shadda coffee color , wadda aka tanada domin wannan ranar kawai, sannan ta d'auko mata wata sark'a da 'yan kunnenta wad'anda zasuyi matching daidai da color d'in stone work din da aka yiwa shaddar, gyale ma kanshi mahad'in shaddar ta ajiye mata akan gado tareda talkaminta.

Sannan ta sami gefen gadonsu ta zauna tareda janyo wayarta ta fara chatt, a cikin sauri munara ta fito toilet d'in sai tsallen jin dad'i takeyi, ganin kayan dake kan gadon yasa tayi turus tareda b'ata fuska, a cikin fushi ta fara fad'a tana cewa, "Hajiya wa kika fitowa da wad'annan karikitan haukar?, dafatar dai ke zaki saka ba ni ba.?"

Munawwara ta kai dubanta a gareta a cikin sanyin muryarta tace, "Ni dad'i na dake ba'a yimaki gwaninta, sannan halan kin manta mummy tace dole ne ki saka d'aya daga cikin kayan da aka d'inko muna.? "

Munara tayi zaune akan stool ta fara shafa mayuka a jikinta tana mere tace, "Nifa bana son shishigi malama ku barni da ra'ayina, kowa yayi abunda yaga zai fidda shi yanzu ke ubanwa yake hanaki saka dogayen rigunan da kike faman zunbulawa a jikinki?, sai NI za'a takura to wallahi bazan saka kayan ba kinji kuma na rantse."

Sanin halinta yasa munawwara taja bakinta tayi shiru taci gaba da chatting d'in da takeyi, munara ta k'are shafe shafenta da ba wani cika kwalliya a fuska takeyi ba, taje ta bud'a wardrobe ta jawo wasu kananan kaya riga da wando sababbi k'al ta saka, sun bala'in kamata tsan tsan a jiki ta dubi kanta a standing mirror tayi murmushi har sai da dimple d'inta duka biyu suka lotsa, taje ta janyo wasu talkama masu bala'in tsini ta fara sakawa, sai ga kira a wayarta ya shigo a cikin zumud'i ta d'auki wayar tace, " hy honey." sannan tayi shiru na d'an lokaci sannan tace, "Eh gidan ne k'araso kawai yanzu gani nan fitowa."

Tana k'are maganar tayi saurin jawo wata after dress sharara baka mai hula tareda adon duwatsu a saman hular da gaban rigar, bayan ta saka taje ta fara bulbula turaruka sunfi kala biyar, kowane da kalar k'amshinshi inda suka had'u suka bada wani kalar k'amshin da duk kwakuwar mutum bazai tab'a tantance wane kalar turare ne ta fesa ba, tana k'ara gyara fuskarta tace da munawwara, "malama ke nike jira fa.?"

Munawwara tayi kamar bata ji taba taci gaba da latsar wayarta saboda haushin k'in bin umurnin mahaifiyarsu da tayi, aiko munara taji haushin k'yaletan da tayi a zuciye tace,

"Kada ALLAH yasa kije daman ni ba wanin son kije nikeyi ba don dai kawai bak'in fad'an da ake saka mutum ayi ta yimasa ne, shiyasa nace dake muje tare huta da wani shan k'amshi."

Tana k'are maganar ta fice kamar zata tashi sama minti biyu a tsakani sai gata ta tadawo da aguje ta shige toilet d'insu, munawwa ta bita da kallo wanda ko tantama batayi Mummy ce take yiwa wannan b'oyon, aikuwa sai ga mummyn ta bud'e k'ofar d'akin nasu ta shigo, idanuwanta suna kai kan kayan dake zube a saman gadon tace da munawwara, "idan ta fito wankan ki tabbatar ta saka kayan."

Munawwara tayi murmushi tace "to mummy amman ai tana jinki ma."

Mummy tace, "to ai ta fito ta saka kafin inje in dawo. " tana fita munawwara ta sauke ajiyar zuciya taci gaba da latsar wayarta, munara dake lab'e a jikin k'ofar toilet d'in tana jin mummy ta fita, ta fito da sauri zata fice d'akin, munawwa ta kai kallonta gareta tareda d'aga murya tace, "bakiji abunda mummy ta fad'a bane halan.?"

Munara ta juyo tareda galla mata wata jar harara ta fice d'akin da sauri, munawwa ta ajiye wayar tareda yin tagumi tace, "Ya ALLAH."

Sannan ta tashi ta jawo d'ankwalin doguwar rigar dake sanye a jikinta ta yafa, sannan ta saki wasu talkami plat a kafarta ta fice tabi bayan 'yar uwarta.

Munara ko da sand'a ta fito d'akinsu ta lek'a bata hango mummyn ba aiko da sauri ta fice , abun mamaki koda taje tazo harabar filin gidansu bata ga kowa ba aiko jikinta yana rawa ta lek'a har wajen get d'insu, a nan ma bata ga kowa ba, sai wani mutumi dake zaune a kan wasu manyan duwatsuna dake gefen k'ofar gidan nasu, wannan mutumin ko yana hango fuskarta ta lek'o ya fad'ad'a fuskarshi da murmushi mai kama da yak'e, saboda yanayin fuskarshi da ke tattakure alamun yunwa k'arara sun bayyana a jikinta, sannan ga wani bak'i da fuskar take dashi tamkar anyi masa fenti, sai dai kuma sock's farare k'al dake sanye a tafin hannunshi dana k'afafuwanshi.

Munara tayi mashi kallon sama da k'asa sannan tayi tsaki tana waige waigen ta inda bak'onta zai b'ullowa, shi kuwa ganin yanayin kallon da tayi masa yayi murmushi tareda yunk'urawa ya tashi daga kan dutsin da yake kai, ya fara taku a hankali zuwa wurinta, ganin yana nufota munara tayi baya da sauri zuciyarta a cike da mamakin zuwanshi wurinta.

Ba shiri tayi saurin rufo 'yar k'aramar k'ofar get d'insu, wanda yayi daidai da zuwan munawwara tana tambayarta baizo bane? Munara ta gwalalo mata idanuwa tareda nuna mata k'ofar, a cikin mamaki munawwa ta bud'e k'ofar ta lek'a aiko itama tayi arba da wannan mutumin, duk da ta d'an so taji tsoro amma dai ta dake tama k'arasa fitowa duka, sannan ta fara gaidashi a mutunce don ita mace ce wadda tasan darajar d'an adam, tana girmama duk matsayin da taga wani a ciki, mutumin yaji dad'in gaisuwar da munawwara tayi masa sannan a cikin muryarshi tattausa yace da ita, "wurin 'yar uwarki nazo amma naga ita kamar ma tsorona takeji."

Munawwa tayi murmushi tace, "A'a ba wani tsoro kawai dai don bata sanka bane ba amma yanzu bari inje inyi mata bayani kayi hak'uri kaji."

Yace "ba damuwa nagode da kulawarki"

Munawwa ta shige get d'in inda ta iske munara sai faman kiran wayar honey d'inta takeyi, amma wayar tak'i shiga hankalinta a tashe sai kai da komo takeyi tana yarfa hannu tareda buga k'afafuwa tamkar wata 'yar yarinya, wanda anan take hawaye suka taru a k'wayar idanuwanta saboda damuwa, munawwa ta kalleta taso tayi dariya amma ta mazge tace,

"Wannan mutumin fa wajenki yazo kije kiji me ya kawoshi."

Munara ta galla mata wata k'atuwar harara tace, "Wallahi da kin k'ara yiman maganarshi sai mun dambace dake yanzu a nan wurin ."

Munawwa ta zaro idanuwa a waje tace,

"Hajiyar honey ba ni na kar zomon ba don ko rataya ma ni ba'a bani ba."

Ta k'are maganar tana dariya ta shige cikin gidansu ta barta anan cikin takaici, munara ko da taga wayar tak'i shiga ba shiri sai ga hawaye sharrr suna gudana akan fuskarta, a zabure ta fito k'ofar get d'insu tareda taku kamar hud'u zuwa biyar tana lek'a dama da hagu, tana so taga ta inda motar honey'n nata zata b'ullo, wannan mutumin yana tsaye yana kallonta ganin ta nuna kamar bata san dashi a wurin ba, yasa yayo tattaki ya k'araso inda take tareda yimata sallama a cikin sanyayyiyar muryarshi.

Munara tayi saurin juyowa ta galla masa harara bata jira taji abunda zai fad'a ba ma, ta fara balbaleshi da ruwan masifa tana cewa, "Wai kai wani irin kulafuci ne wannan?, miye tsakanina da kai ne da kake so ka shiga rayuwata ne?, a'ina ka sanni ma wai da har ka wanke k'afa kazo gidanmu?, ka kalleni dakyau ka kalli kanka baka ji kunyar zuwa wurina ba? kai kanka kasan ni ba sa'ar ka bace, don ALLAH ka tafi ni ko fuskarka ma bana son gani, idan kuma naci ne sana'arka to ka jira kad'an zaka ga irin wad'anda suke daidai dani ba kai ba mai fuskar kashin shanu."

Mutumin yayi murmushi kamar baiji zafin maganganunta ba yace, "Yanzu don nazo in nuna maki irin son da nake yimaki laifi ne?"

Munara tayi saurin ja da baya nesa dashi tace, "so? Wa kake so d'in ni din?cab! Lalle k'wak'walwarka kanka ta toshe, kuma notukan saman kanka duka sun kwance amma wallahi kama rena ni. "

Mutumin ya k'ara matsowa a kusa da ita yana murmushinshin shi mai kama da yak'e yace, "Tun da na d'ora idanuwa na akanki naji ba wadda nike so irinki, don ALLAH ki daure ki soni koda kad'an ne kinji.?"

Aiko a zabure munara ta d'aga hannu ta wanka mashi wani haukataccen mari tareda da nuna shi da d'an yatsa tace, "Ko a unguwar nan ka sake na k'ara ganin k'afarka sai ka yabawa aya zak'inta."

Tana k'are maganar hawayen bak'in ciki suna zuba ta shige gidansu tareda bugo k'ofar get d'in da k'arfi tace garammmm!!!!.

Mutumin ya bita da kallon mamaki yayi murmushi yace, "sweetyna ce ta d'aga hannu ta mareni a zuwana na farko a gidansu."


Yana k'are maganar ya mik'e wata hanya yana tafiya har yasha kwana, sai naga ya nufi wata kafurar dunkulalliyar mota sai k'yallin sabunta takeyi, ya bud'e ta ya shiga ba shiri na lab'e jikin motar na lek'a, aiko me zan gani sai naga ma ashe akwai wani a cikin motar, yana shiga suka baiwa juna hannu sukayi shaking, sannan d'ayan mutumin ya kalli fuskarshi ya kyalkyale da dariya har da buga hannunshi akan starring motar, a hankali naga wannan bak'in mutumin ya saka hannu ya fara k'ok'arin cire bak'ar fuskar dake manne da tashi, yana sauke bak'ar fuskar naganshi wani had'ad'd'en guy fari sol da sumar kanshi bak'a k'irin hadda wani murd'e murd'e tayi saboda tsananin sulbinta, da hancinshi har baka mai tareda madaidaicin bakinshi mai d'auke da d'an k'aramin gemun da wayayyun samari suke ajiyewa, ga wani bak'in saje da ya kwanta luf luf a gefen fuskarshi.

Ina lab'e ina kallonshi ya cire safar hannunshi mai d'auke da dogayen yatsu farare sol da gashi kwance luf a bayan yatsun shi, ya ciro safar k'afar itama ya had'a su a waje d'aya ya jefa a bayan sit, d'ayan mutumin da suke tare yana dariyar k'eta yace, "haba basarake kayan aikin kake wulak'antawa.?"

Wannan guy d'in da aka kira da Suna basarake, ya galla masa harara yace,
"Me zanyi da kayan da suka janwo aka kwad'a man mari."

Aiko abokin tafiyar tashi me zaiyi ba dariya ba har ya tada motar suka bar unguwar bai bar dariyar ba.





Tofa d'and'ano ne daga litrafin🔥 BAKON YANAYI🔥tafe yake da zafinshi har kunar hannu yakeyi, amma ku sani na kud'i ne a filin talla yake wadda take bukata ga number ta ta tuntubeni 09032685442.



Akafta






Ni d'in dai ce 😹

*🔥BAKON YANAYI🔥*


*D/AUTA NOVEL*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*🔥BAKON YANAYI 🔥ya shigo mani babu zato kaina inda rai da rabo NI daku mutu kan raba har raina 💃🏻INA MASOYA LITTAFAN HADIZA D/AUTA 😝ku marmatso ga 🔥BAKON YANAYI 🔥NA KUD'I NE MAI BUK'ATAR BOOK D'IN TA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 Da d'ari biyu kacal zaki mallaki buk d'in 🔥BAKON YANAYI🔥 tun daga farko har k'arshe idan ALLAH ya ara muna rai da lafiya tareda lokacin gaba d'aya sayen nagari maida kud'i gida😹Nagode🤝🏻*

Free page 2.

**********************

A cikin wani bajimin kuka munara ta shiga gidansu idonta a rufe taci karo da mummy, wadda daman cen jiran shigowarta takeyi saboda ganin kayan da tace ta saka ajiye akan gadon, aiko a zafafe mummy tayi mata wani rik'o munara tana d'aga ido taga mummy ta fara kukan neman ceto, sai d'aga murya takeyi sai kace wadda za'a cirewa rai tana fad'in,

"Don ALLAH mummy kiyi hak'uri bazan sake ba."

Kururuwar hak'urin da take baiwa mummy ne yasa Daddy yayi saurin saukowa daga sama, ranshi a b'ace yake kallon mummy tareda yi mata gargad'i da idanuwa akan ta saki munara, mummy ta d'aga hannu zata kaiwa munara duka daddy ya rik'e a hannu a cikin b'acin rai yace, "wai har yaushe zaki barin yarinyarnan ta huta?, a kullum aka jiyo tashin muryarki da ita ne, to ni ban matsa ma yarana ba don haka wallahi bazan zura idanuwa a takurasu ba, sake ta kar ki karya mata hannu."

Ya k'are maganar tareda fisge munaya da rik'on da mummy tayi mata, mummy ta bishi da kallo baki a sake kamar wata sakarya tace, "Shikenan ni yanzu banda ikon tayi laifi inyi mata hukunci.?"

Daddy ranshi a b'ace yace, "to me tayi maki ne yanzu da zaki yimata hukuncin duka da girmanta?, tunda ta zama sarkin laifi kullum ita kad'ai ce keyi a gidan."

Mummy tana nunata da d'an yatsa tace, "kika yarda na koma cewa ga abunda zakiyi kika k'i, wallahi sai na karya ki a gidannan ki daina ganin an d'aure maki gindi kina abunda kike so, wallah tsaf zan saka bulala in zaneki ras!"

Daddy ya kai dubanshi ga munara da ta lafe a bayanshi sai muzurai takeyi, yana murmushi yace, "me kika yimata ne? da zaki jawa kanki duka a banza."

Munara tayi k'wal k'wal da idanuwa tace, "wai don nak'i saka kaya shine."

Daddy yana dariya yace, "to dole ne saka kayan? tunda ba kyaso ba sai a kyaleki ba, yanzu ina bak'on har ya tafi ne?."

Munara ta zunb'uro baki tana hawaye
Mummy saboda haushi kasa magana tayi, tayiwa munara wata k'atuwar k'wafa ta wuce su fuu ta shige kitchen, saboda bata son ta furta kalmar da ba mai kyau ba, don bata son su raba wa kansu abunc kunyar cikin lamarin, don zai ga tayi masa rashin kunya a gaban yayansu.

Daddy Kam zaunar da MUNARA yayi cikin tausasa halshe yayi ta lallashinta har ya samu ta saki sannan yace da ita taje d'akinsu cikin natsuwa taji me ya hanashi zuwan kamar yanda yace.

Ta mike tana dariya tace ,. "Nagode Daddy I love you so much amman don Allah kace kada Mummy ta dakeni kaji?"

Ta k'are maganar cikin shagwaba Daddy yana Murmushi yace,

"Ai ba ma zata fara ba itama tasani jeki abunki"

MUNARA ta shige d'akinsu zuciyarta cike son jin abunda ya hanawa Haidar d'inta zuwa gashi ya janyo garin nemanshi ta had'u da mai fuskar shanu.

Tana shiga d'akin ta fad'a kan gadonsu ta fara dealing numbar Haidar d'in Aiko sai gashi an d'auka, cikin zumudi ta tashi zaune tace

"Haba Honey haba Honey shine kace ga ka a unguwarmu kasa na fita bulayin nemanka amman kaki zuwa to ai ba komi ka jirgani kaji dad'i"

Daga cen bangaren ya bata fuska kamar da gaske yace,. "Bayan nazo tun daga nesa na hangoki da bak'o to bana son in takuraki shiyasa na juya abuna"

Munara ta dafe Kai tace, "Oh sheet ba fa bakona bane ba almajiri ne ya zo wajen Daddynmu neman sadaka shine fa na karb'o na kawo masa"

Haidar Kam daga bangarenshi ya kumshe dariyarshi yace, "Au haka ne ai ban sani ba"

MUNARA cikin jin haushi "to yanzu ka sani amman ai da ko kirana ka yi ko daga nesan mun gaisa, to yanzu Ni dai ya kenan gobe zaka dawo ko?"

Yayi Yar dariya yace

"A'a bazan dawo ba amman in kina b'ukatar ganina mu had'u a Zambia park gobe da k'arfe hudu da rabi na yamma"

Munara ta yi tsalle tace,. "Serious fa!"

Yace "of course"

Tayi juyi akan gadon cike da jin dad'i tace,. "Promise"

Yace

"Promise"

Tayi wata kara tace,

"Yeeee amman don Allah honey kar in zo banganka ba ka kawo man wani uzuri"

Kai tsaye yace,.

"Ki zo kawai at Right the time d'in da na fad'a maki I will give you surprise"

Tace " I love you so so much honey" yace "me too" tace "Ok bye bye"

Ta kashe wayar sai faman Murmushin jin dad'i take yi, Munawwa da ke zaune gefen gadon tana duba litrafanta ta ajiye littafin ta kalleta cikin jin haushin wannan azarbabi nata akan Namji ta Kira sunanta a hankali tace

"MUNARA yanzu ribar me kikaci da kika yi masa karya? Ai da kin sanar dashi gaskiyar cewa Saurayinki ne yazo don ya gano cewa ba shi kad'ai ne Mai sonki ba, sannan abun haushi abun takaici wai yanzu ke zaki cira k'afa kije wajenshi, yanzu ke ko a hakan ai yakamata ki gano cewa ba son tsakani da ALLAH yake maki ba, tunda har yaki bayyana gidanku iyayenki su San dashi, to Wallahi kika je sai na fad'awa Mummy tunda ke kullum sai kin bata Mata Rai kike jin dad'i"

MUNARA Kam Baki sake take kallonta har ta k'are sannan tace,. "Ni mamakina da wasu a kullum shine shiga sharu ba shanu ba'a kasa da mutum ba amman yace shi Dole sai ya kwasa, to bud'e kunnuwanki da kyau kiji WALLAHI tunda na yi niyyar fitar nan sai na fita sai dai idan na dawo a sakani tukunya a dafani"

Tana kare maganar ta buga mata wani uban tsaki ta maka mata wata harara ta shige toilet, Munawwa ta bita da kallo ranta a zagule tace

"ALLAH ya ganar da ke gaskiya amman muddin kika je wajenshi sai na sanarwa Mummy tunda ke baki San ciyon kanki ba"

Munara ta lek'o kanta daga toilet d'in tace

"Idan naje ki tanadi ki wuk'a a ajiye idan na dawo a kasheni kar a barni da raina"


Munawwa ta girgiza Kai tace,. "ALLAH ya kyauta"

Haka suka kwana kowa baya kula Dan uwanshi.





Princess Dija
*🔥BAKON YANAYI🔥*


*D/AUTA NOVEL*



*TAURARI WRITER'S ASSOCIATION*


*INA MASOYA LITTAFAN HADIZA D/AUTA 😝ku marmatso ga 🔥BAKON YANAYI 🔥NA KUD'I NE MAI BUK'ATAR BOOK D'IN TA TUNTUBENI TA WANNAN NUMBER 09032685442 Da d'ari biyu kacal zaki mallaki buk d'in 🔥BAKON YANAYI🔥 tun daga farko har k'arshe idan ALLAH ya ara muna rai da lafiya tareda lokacin gaba d'aya sayen nagari maida kud'i gida😹Nagode🤝🏻*

Free page 3.

**********************

Ko da safiya ta waye Munara cike da d'okin zuwa inda suka yi zasu had'u take, tun safe har zuwa k'arfe uku da rabi, tana bugawa dam ta fad'a wanka a gurguje ta fito ta fara shiryawa cikin farin ciki , amman ta b'oyewa Mummy bata sanar da ita ba, Munawwa ce ta san da tafiyar kuma tun da taga tana ta faman shirin fitar, a cikin mamaki tace da ita,

"Wai yanzu kina nufin da gaske ba zai zo gidannan ba kece zaki fita kije ku had'u a wani gun.? " Munara tayi mata wani kallon renin wayo tace, "Ko zaki hana NI fitar ne uwata.?"

Munawwa ta galla mata katuwar harara tace, "zan dai fad'awa mummy ta hana ki fitar, idan ni ban isa hanaki ba ai ita ta'isa dake ko. ? "

Munara ta buga wani uban tsaki sannan ta ci gaba da shirinta har sai da ta gama zanzarewa cikin shigarta ta k'ananan kaya, wad'anda suka kama ta tsantsan ko ina ya yaji, breast sun fito tamkar su tsone idanuwan mai kallonsu, d'uwawu sun fito bumbum masha ALLAH, sannan ta d'auko d'an k'aramin gyale ta yafa a kanta ta kalli munawwa tace, "To ni zan fece idan na dawo kice kar a barni da rai na."

Munawwa ta kalleta sama da k'asa sannan tayi tagumi tace, "ALLAH ya shiryeki Munara tunda ke a kullum idan baki b'atawa Mummy rai ba bakya jin dad'i."

Tana k'are maganar ta bud'e d'akin ta fita Munara ta bita da harara tace, "kije da munafuccinki fita dai ce sai nayi."

Aiko da sauri ta d'auko makullin motarsu da ta sato d'akin Mummy, ta saka talkaminta masu tsinin gaske ta k'wama wani k'aton glass bak'i, da sand'a ta fito cikin gidan ta fad'a mota tareda bata wuta sai dai tashin motarta su Mummy suka jiyo, a tsiyace ta taci ribas mai gadi ya wangale

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

1 Comments On BAKON YANAYI
avatar
mukhtar-naziratu-sani

9 months ago

Reply

Thanks

Please Login or Register in order to submit comment