Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sun kulata ba, suna ƙoƙarin buɗewa su shiga.
Da sauri Iman ta ce "Kai, fita fa zan yi, zai kai ni unguwa ne"

Ɗaya daga cikin su ta kalleta ta ce "Saboda ta ki fitar zamu fasa tamu ne?"

Iman ta ce "A'a ba haka nake nufi ba, na ga kun iya driving, kuma ga wasu motocin, ni Ammi ta hanani tuƙi ne, kuma na yi magana da Gali tuntuni a kan zai kai ni unguwa"

Cikin tsawa ɗaya daga cikin su ta ce "Shut up! Mu ki ke kallo ki ke gayawa haka, kin manta a tuna miki ne?"

"Me ku ke yi haka a tsatstsaye?" Gaba ɗaya suka waiwaya suka kalli mai maganar.
Jikin Iman ne ya yi sanyi, tare da shiga wani yanayi mai wuyar fassara, bayan sanya idanuwanta a cikin nasa.

Fauziyya ta cire glass ɗin fuskarta ta ce "Bro, wannan ƙanwar ta ka ce take yiwa mutane rashin kunya, duk motocin gidan nan ta rasa wadda za ta hau, sai da muka zo muka ce a kai mu unguwa, wai ita ma tilas ita zata hau a fita da ita"
Ya tsuke fuska ya kalli Iman ya ce "Wato ke tsagerancin naki har ya kai ki din ga yiwa na gaba da ke rashin kunya ko? Sa'anninki ne su?"

Jiki a sanyaye ta kallesu, sannan ta mayar da idonta kan sa, sai dai ta kasa magana, sai hawaye da suka cika mata ido.

"Ina magana zaki yi mini kuka, get out from my sight, stupid girl"

Gaba ɗaya ta rasa meya kamata ta yi, jiki a sanyaye ta nufi hanyar fita daga gidan.
"Ke zo nan" ta ji muryarsa ba tare da ta yi tsammanin hakan ba.
Ta juyo ta dawo in da yake tsaye.

"Ina zaki?"

"Napep zan je na hau"

"Wuce ki koma, ba zaki fita ba" yayi maganar cikin bayar da umarni. Ta kalli yadda motar da su Fauziyya suka shiga ta bar gidan. Ba ta ce masa ƙala ba, ta koma sashin su, sai dai duk yadda ta so ta riƙe hawayenta abin ya faskara, tuni hawayen suka wanke mata fuska.

"Subhanallah, abar ƙaunata ya haka? Meyafaru? ya baki tafi ba?" Ammi ta yi mata tambayoyin a jejjare cikin ruɗewa bayan ganinta ta na kuka.

Iman ta share hawayenta ta ce "Bakomai Ammi, kawai fasawa na yi"

No ban yarda ba, gaya mini"

"Ammi su Fauziyya ne da Yaya Mahmud".

Nan da nan Annurin fuskar Ammi ya ɗauke gaba ɗaya ta ce "Mahmud again? Tura fa ta fara kaiwa bango, meya yi miki?"

Iman ta share hawayenta ta ce "Ammi dan Allah ki bar maganar, kar ranki ya ɓaci, bana son ki damu"

Ammi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "Na ji, amma me suka yi miki?"

"Dan Allah kar ki damu Ammi, bakomai ki yi haƙuri"

Jinjina kai Ammi ta yi sannan ta ce "Yanzu shikenan, kin fasa fitar kenan?"

Iman ta ɗaga mata kai alamar eh. Ta ja hannun Iman suka bar falon.

****

Cikin rarrashi mama take magana, "Ruma, aiken ki nake son yi, amma bana son ki je ki yi mini shirme, ko ki tsaya a in da ban aike ki ba"

"In sha Allah mama, ba zan tsaya a ko ina ba, fiii zan ware dogayen ƙafafuwana da bala'in gudu na je na dawo"
Mama ta ce "Wane irin gudu kuma? Kalen ki watasar mini da kayan aiken, ki tafi a hankali, ki yi sauri ki je ki dawo"

"In sha Allah zan yi sauri, na je na dawo"

Mama ta gaya mata in da take so ta je, tare da abin da za ta kai, ruma ta sauya kaya ta saka hijjabi, ta fita yi wa mama aike, ta ƙuduri aniyar za ta je ta yi sauri ta dawo ko dan ta farantawa maman.
Tashin farko ta bi ta cikin unguwa, tana tafe tana kalle-kallenta, duk wani lungu da saƙo idan ta bi sai an kira sunanta, dan kusan kowa ya santa.

A ƙofar wani shagon aski ta ga keken Huzaifa, hakan ya tabattar mata da yana cikin shagon.
Murmushi ta yi ta nufi ƙofar shagon askin, da sallama ta buɗe ta shiga cikin shagon.
Duk maza ne a ciki, ga Huzaifa ya zauna a kan kujera za ayi masa aski, jin sallamar mace ya sanya dukkansu suka juya suna kallonta.

"Ohh Huzaifa yau Allah ya yi zaka cire wannan sumar kenan? Kuma wallahi aka yi maka askin 'yan iska kai da mai sunan Baba"

A ƙule Huzaifa ya ce "Ke uban me ya kawo ki nan? Ba ki ga shagon aski bane?"

"To ni ina ruwana da wani shagon aski, ba dai mutane ne a ciki ba, keken ka na gani a waje na san kana nan, na ce bari na leƙo na ganka"

"To na ji na gode, fita ki bar wurin nan"

"To sai ka tsaya na gama kallon kalandar askin nan, sai na tafi " tayi maganar tana riƙe ƙugu, tare da zubawa kalandar ido.

"Ni wannan yarinyar ba ke na taɓa rabaku faɗa da wasu yara ba, kun dawo daga makaranta?" Cewar wani da yake zaune shima yana jiran askin.

"Eh nice, me na yi kuma?"

Ya ce "A'a gane ki kawai na yi"

"To yanzu da ka gane ni lada nawa aka baka?"

Mai aski ya ce "Deluwa, dan Allah ki yi haƙuri, wurin nan duk maza ne, ki je aiken da aka yi miki, ko kuma in saka a riƙe mini ke na yi miki aski"

"Aikuwa da sai ka kasa zaman Ɗorayi, sai na saka yayyena sun kakkaryaka sun zubar, ni zaka yiwa aski?"

Huzaifa ya miƙe tsaye rai a ɓace ya ce "Bi ƙofar da ki ka shigo ki fita"

Ta ɗan kwaɓe baki ta ce "Huzaifa ba ayi maka gwaninta, daga ziyara?"

"Ki fita na ce, wallahi na zo in da ki ke sai na gwara kan ki" ja ta yi ta tsaya cike da taurin kai tana kallon idonsa, hakan ya ƙara tunzura shi, yayi kanta amma suka riƙe shi, ta fita da gudu daga shagon.

Tana fita ta yi ƙwafa, ta tura keken sa ta ji bai rufe ba, keken ya fi ƙarfinta, amma ta haye ta yi gaba.

Wani ya leƙa shagon askin ya ce "Huzaifa ƙanwarka ta ɗau keken ka fa ta tafi"

Da sauri ya miƙe ya leƙo, ai tuni ta kusa ƙarshen layin, ya san ko da ya bita ba zai cimma ta ba.
Kawai yayi tsaki ya koma ya zauna, zuciyarsa na tafasa, 'yan cikin shagon suka din ga dariya, kowa na tofa albarkacin sa a kan halayar ruma.

Haka nan tun da ruma ta fita, mama ta kasa nutsuwa, kawai dai gata nan ne dai, ta fara dana sanin dalilin ma da ya sanya ta aiketa.

Tun tana saka ran ta ga ta ina za ta shigo gidan, har ta fara fidda rai, yanzu ba ta fiye ɗaga hankalinta ba, idan ruma ta fita makaranta ko aike ba ta dawo da wuri ba, sai dai fargabar mai za azo ace mata ruman ta aikata.

Aikuwa ilai, tana cikin wasi-wasi sai ga sallamar wata matashiyar budurwa da wata yarinya, yarinyar bakinta a fashe, jikinta duk kwata ga fasashshiyar roba, da sauran gari a cikin ta, yarinyar sai kuka take, yawu da jini yana zuba daga bakinta.

Cikin kaɗuwa mama suka gaisa da matashiyar yarinyar, mama ta hau tambayar ba'asi.

Babbar ta ce "Dama cewa aka yi na zo gidan su na faɗa, ruma ce ta taho a kan wani ƙaton keke kashe gardi, ta taho da gudu, ƙanwata ta karɓo niƙa, ta bugeta da keken ta faɗa kwata, ita ma ta faɗi a gefe, ta tashi ta karkaɗe jikinta ta hau keken ta gudu, kuma ba iya ƙanwata ta buge ba, tun da tana tafe tana faɗuwa a kan keken"

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ya Allah kai ka jarrabeni, Allah ka dube ni, ka bani ikon cin wannan jarrabawa" mama ta kamo hannun yarinyar da aka jefa kwatar, ta wanke mata jiki, ta basu dubu ɗaya tare da basu haƙuri ta ce zata zo har gida ta basu haƙuri.

Gwaggo kuwa ta hau masifa "Wallahi mutanen maraya ba ku da kara a kan ɗa, yanzu saboda wannan ɗin aka wani aiko yawon kan ƙara, ai ɗa na kowa ne, kuma fitinar maraya ai daban take"

Kamar mama za ta yi kuka ta ce "Ba wnai fitinar maraya, dama can haka ake fama da ita, a ina ta samu keken da ta hau ni da na aiketa wuri daban, kullum sai ruma ta sakani asarar kuɗi da yawon ban haƙuri, nan gaba idan ba ayi wasa ba, sai wasu sun kai ƙararmu ga hukuma"

"A'uzubil'ahi kina uwa ba zaki faɗi alkhairi a kan yarinyar ki ba, ƙuruciya ce, kowa da irin ta sa" mama ba ta kuma cewa komai ba, idan ta biyewa zuciya, za ta iya musayar yawu da Gwaggo, wanda ba za ta so hakan ba.

Huzaifa ya shigo a kumbure yana bala'i "Mama! Ina ruma take wallahi yau sai na tattakata, sai na ci mutuncinta"
Mama da take a ƙule ta kalle shi ta ce "A ina ka ganta?"

"Mama shagon aski fa ta bini, na koreta shi ne ta ɗauke keke na ta gudu, ni sa'an wasanta ne ita duk wani halin zubar da mutunci ta iya"

Mama ta safe kai ta ce "A ina da ta samu keken kenan? Za ta gane ba ta da wayo da Baba zan haɗata bari ta dawo"

"A'a ke wace irin uwa ce, wannan mugun ɗan na ki, haka kawai ya kassarata a'a ban lamunta ba "

Huzaifa ya harari Gwaggo ya ce "Wallahi ko ba a gaya masa ba, da hannun nawa zan ci ubanta, sai na girgiza ƙashin haƙarƙarinta "

Har gefin magariba babu ruma babu alamarta, tun mama tana jurewa, har ta saka aje a nemo mata ruma.

Aliyu Allah ya bawa sa'a, ya ganota a wata tawagar 'yan d.j, ana biki an kunna d.j, ta shige tsakiyar manyan mata, ana rawar sabada, ta gantsare sai rawa take, tana wani juye-juye sai ka ce an saka mata batir, ga ta a shafe ba gaba ba baya ama sai karkaɗa jiki take.
Cikin 'ya'yan Mama, Aliyu Ustaz ne, ba shi da ra'ayin wannan abubuwan, amma yau a saboda ruma, sai gashi a tsakiyar mata, ya samu bayan ruma da take ta juyi, ya tsula mata tsumagiya.
A zafafe ta ƙandare ta juyo, a zaton ta yaron mai D.J ne ya daketa, dan dama yana ta korar yara daga cikin filin rawar taƙi tafiya. Ba kuma rawar kawai take yi ba, har da satar kuɗin liƙi tana sakawa a cikin hijjabinta, sai ta gantsare tana rawa idan aka liƙo sai ta wayance ta ɗauke kuɗin.

Cak ta tsaya tana kallon Aliyu, ta ɗaga kai ta kalli yadda gari ya yi duhu.
"Sannu 'yar makaɗa, aike da aka yi miki kenan ko? Fita ki wuce mu tafi"

Kasa magana tayi, a take tayi saranda, da jin za ta iya ɗaukar kowane hukunci, saboda ita kanta ta san ta tafka ta'asa.
Ta janyo keken Huzaifa, da Allah ya sa ba a sace ba, ta hau turawa, Aliyu ya haske keken, tayoyi duk sun sace, dan ɗayar ma fashewa ta yi, ga kaca ta zube keken duk wani gurin ya lotse, adon fitulun da ya yiwa keken kuwa, suma wasu duk sun fashe.
Yana tafe yana kallon ruma, yana tunanin anya ruma mutum ce, fitinarta ko su da suna kamarta ba su yi haka ba, su dai akwai dambe kamar zakaru, kamar su cinye juna, amma rashin ji a gida, rashin ji a unguwa rashin ji a makaranta wannan sai Ruma ƘANWAR MAZA.

A ƙofar gida suka tarar da Uamar, yana tsaye yana waya, tana ganinsa ta fara kuka, tana cewa "Kashina ya bushe"
Aliyu ya ingiza ƙeyarta zuwa cikin gidan, da sauri Huzaifa ya taso, dan ta kekenaa yake yi, sai dai yana kallon keken ya san ko a wurin 'yan gwan-gwan wannan keke ba zai daraja ba, kamar yayi shekara da shekaru.
A ka rasa wanda zai ce mata komai, duk suka zubo mata ido.

Mama ta ce "A ina ka ganota?"

"Ga ta nan ku tambayeta"

Cikin muryarsa mai razanata musamman idan ba ta da gaskiya ya ce "Daga ina ki ke?"

Jikinta ya hau rawa ta ce "Dan Allah mai sunan Baba......

"Daga ina ki ke fa kawai na ce?"

Gwaggo ta ce"Ya zaka razanata da wannan muryar ta ka, ka tambaye ta cikin nutsuwa mana"

Huzaifa ya daɗe bai ji abin da yake shirin sanya shi kuka ba irin yau, ya kasa ko tari tun bayan tozali da kekensa.

Rarraba ido kawai take tana kokowa da numfashi, ganin yadda kowa ita yake kallo yana jiran amsarta.

Wata irin gigitacciyar danƙa Uamar ya yiwa kunnenta, ta kurma ihu, ya janyota har tsakiyar tsakar gidan, ya dungurar da ita, ya naɗe hannun rigarsa cikin tsawa ya ce"Ina ki ka je da aka aike ki?"

Cikin kiɗima da razani, ruma ta wassafa komai, ba ta ɓoye ba ciki har da zuwa wurin aski da yadda ta ɗau keke tana tafe tana faɗuwa, duk ta gurje gwiwa, da yadda bayan ta dawo daga aike ta tsaya wurin 'yan bikin da ba ta san suwaye ba ma, tana rawa tana satar kuɗin liƙi.
Sai a lokacin ta faɗi har faɗa suka yi da yaron dj yana ce mata shegiya ɓarauniya.
"Yanzu ina kuɗin da ki ka ɗebo ɗin?" Yayi maganar yana miƙa mata hannu.
Aikuwa ta zura hannu a rigarta, sai ga kuɗi, a ƙalla idan aka ƙirga sun kai dubu uku da ɗoriya.



(SORRY FOR THE LATE UPDATE, AYYUKA SUN YI YAWA NE, INA GODIYA DA TARIN ADDUOI DA ƘAUNAR DA KU KE WA BOOK ƊIN ƘANWAR MAZA)

Ayshercool
08081012143
[13/07, 9:01 pm] JAKADIYAR AREWA: ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels

Ku yi subscribing  YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.






12

Mai sunan Baba ya kalleta a tsanake ya ce "Sata ki ka koma yi kenan ko?"

Ta girgiza kai da sauri ta na zazzare ido.

"Ba zaki buɗe baki ki yi mini magana ba?"

"A'a Yaya wallahi ba sata nake yi ba"

"To idan ba sata ba, me ki ka yi, kin san su masu bikin ne, ko kuma sun sanki, idan ba sata ba baki suka yi, ko nan aka aike ki?" Ta girgiza masa kai.

Ya ce "Good, tashi ki je ki yi alwala ki yi salla, zan gauraya da ke, tashi maza ina jiran ki"

Huzaifa da yake ta huci, ya cika ya batse kamar ya sha yeast ya ce "Wallahi yau sai na lallasaki, za ki gane baki da wayo"

Gwaggo ta ce "Ku dai din ga haƙuri yarinya ce, ƙuruciya ce kawai take damunta"

Huzaifa ya yi ƙwafa ya ce "Ba ƙuriciya da yarinta ba, Allah ya sa ɗanyar ƙwaƙwalwa ce a kan ta da ba ta nuna ba, sai na lallasata na koya mata hankali"

Duk da tana cikin tashin hankalin rashin sanin hukuncin da za ta fuskanta, hakan bai hanata murguɗawa Huzaifa baki ba, tana harararsa, duk da laifin da ta tafka masa.

Daga shiga banɗaki alwala ta tsiri kashi, duk dan ta ɓata lokaci kar ayi mata hukunci mai wahala, ta na fitowa, Umar ya ce a tsakar gida za ta yi sallar, dan haka ta ɗau hijjabi ta tayar da salla.

Ita kanta ba ta san adadin raka'ar da ta yi ba, kawai yin sallar take cike da zullumi, a sujudar ƙarshe kuwa kai kace neman gafara take ko bacci tayi, amma babu ɗaya nazari kawai take.
Haka ta idar ta saka addu'a, abin da ba ta saba ba, ko sallar ta yi sai mama ta yi ta faɗa sannan take zaman yin addu'a.

Ganin taƙi sallame addu'a ne ya sanya Umar yi mata wani irin kallon, da babu shiri ta shafa addu'a ta tashi.

Ya ce "Oya, kamun kunne"

Cikin marairaicewa ta ce "Dan girman Allah Yaya.....

"Shut up! Zaki abin da na ce ko kuwa?"

Jiki a sanyaye, ta durƙusa ta kama kunnenta, nan da nan jikinta ya hau rawa, ta fara gajiya ta saka kuka.

Gwaggo ta ce "Kai ina mace ina wannan goho, kai meyasa ba ka tsoron Allah ne? Ke tashi dalla wannan wace irin azaba ce?"

Ruma ta ce "A'a Gwaggo, ba zan iya tashi ba sai ya ce dan Allah ku tayani bashi haƙuri"

Mai sunan Baba yayi shiru, ya ƙi kula Gwaggo, ta dubi mama ta ce "Ke ba zaki saka baki ya ce ta tashi ba, tun da ni ban isa ba?"

Mama ta ce "Ba haka bane Gwaggo, ai gara a din ga hukunta ta idan ba haka ba, sangarta da rashin jin da zata yi sai Allah ruma ba ta ji sam" ƙarshe mai sunan Baba ya tashi ya bar gidan ma gaba ɗaya ruma kuma ko da wasa ba ta tashi ba daga kamun kunnen, sai dai ta cika musu gida da koke-koke da magiya.

"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, dan Allah mama ki saka baki, na tuba na bi Allah, dan Allah ki bashi haƙuri ya ce in tashi"

"Babu ruwana, ba dai ba kya ji ba, ai na gode Allah da ya bani waɗanda zasu hukunta ki idan ki ka yi ba dai-dai ba, kuma kar ki sake kiran sunana"

"Wayyo Allahna na shiga uku, wallahi mama zan iya rasuwa, kaina da wuyana ciwo suke yi mini, bana son na mutu yanzu, bana nafila karatun Alqur'ani ba kullum nake yi ba, gashi ina yi miki abin da ba kya so, bana son na mutu yanzu ban tuba ba, wallahi mama zan iya rasuwa a wurin nan"

Yasir ya ce "Ba ki jigata bane ba, da ki ke iya wannan surutun"

Gwaggo ta ce"Ji min kafirar yarinya, ba nace ki tashi ba kin ƙi, ni babu abin da ya ƙular da ni, irin wannan goho da ya saki kina 'ya mace, kema da azababben taurin kai na ce ki tashi kin ƙi".

Ruma ba ta kula Gwaggo ba, sai cigaba da rusa kuka da tayi, tana magiya da neman taimako.

Cike da ƙuluwa Yaya Aliyu ya ce"Ki yi mana shiru dan ubanki, tun da ba wani ne ya aike ki ki aikata abin da ki ka yi ba" haka ruma ta ja bakinta ta tsuke, tana kuka ƙasa-ƙasa dan wasu lokutan yaya Aliyu ma ba daga nan ba wuri8iya tsare gida da hukunci, dan daga yaya Umar sai shi a zafi.

Har mai sunan Baba ya dawo ruma tana nan tana aikin kamun kunne, tana yi tana faɗuwa tana tashi.

Sai da ya dawo sannan ya ce ta tashi, kuma ya ce mata washegari za su gauraya.

Tana miƙewa tsaye jiri ya kwasheta sai amai, Gwaggo ta fito da sauri ta kama ruma, kanta sai juyawa yake saboda azabar wahala.

A zaune ta yi alwala tayi sallar isha'i, ko abinci ba ta nema ba, ta kwanta saboda galabaita, cinyoyinta sai azabar ciwo suke yi mata, dama da fari suna ciwo saboda hawan keke, gwiwoyinta na raɗaɗi saboda duk ta ƙuje su saboda keke, yanzu kuma ga kamun kunne, jikinta kamar an mata duka haka take jin ta, a take wani irin wahalallen bacci ya kwasheta.
Sai dai kwana ta yi da wani irin zazzafan zazzaɓi, wanda ita kanta ba ta san ya hau ta ba, jin surutan ta ya yi yawa a baccin ne ya sanya mama zuwa ta taɓa jikinta, ta ji da zafi sosai.

Duk da mama a ƙule take da ruma, haka ta fita ta ɗebo ruwa ta sanya ɗan ƙaramin towel, ta din ga shafawa ruma ruwa a jikinta.
Tun asubar fari kuwa, ruma amai ne ya tasheta, saboda har a lokacin jiri take yi.
Yanzu ma a zaune ta yi sallar asuba, ta nemi wuri ta kwanta.
Tun mama na basar da ita, har kuma ta fara damuwa, Gwaggo kuwa ta samu wuri ɗaya ta zauna sai mita take na masifa a kan mama tana gani aka bawa ruma gwale-gwale amma ba ta ce komai ba.

Bayan gari ya gama wayewa, Gwaggo ta karya ta yi haramar tafiya, sai dai a lokacin ruma ta samu bacci, dan a galabaice take. Gwaggo ta ce kar a tasheta, Abdallah ya tafi rakata tasha, suna ta murna zasu huta, dan dama Gwaggon ta ishe su,  ruma ce kawai take son zamanta a gidan.

Mama ta tashi ruma, ta matsa mata a kan lallai ta ci Abinci, ta na ci tana kuka ta ɗan sha tea kaɗan ta kuma kwanciya, sai dai ko mintuna goma ba ayi da cin Abincin na ta ba, ta tashi ta cigaba da amai.

Ba shiri mama ta ce Aliyu ya zo ya kai ruma chemist a dubata.

Da ƙyar take iya tafiya, suna tafe tana kuka, har sai da ran Aliyu ya fara ɓaci, amma ya shareta suka cigaba da tafiya a hankali. Cikin sa'a kuwa suka tarar ya fito, kasancewar asabar ce, ranar ba ya zuwa aiki.

Ya na ganinsu cikin kulawa ya ce "Subhanallah, 'yar gidan mama yau ke ce ba lafiya?" Ita dai ba ta iya magana ba ta nemi wuri ta zauna. Aliyu ya zauna ya rungumeta, saboda ƙoƙarin faɗuwa take yi.

"Meya sameta haka?"

Aliyu ya ce "Ina ga zazzaɓi ne dai, da amai ta fara jiya"

Bakinta bai mutu ba, ta ce "Kamun kunne aka sakani, kusan awa goma shine ya sani rashin lafiya"

"Subhanallah, waye ya saki kamun kunne kuma?"

"Mai sunan Baba ne"

"To ki yi haƙuri, yanzu dai zan ɗibi jininki na yi miki gwaji, in duba meye ya haddasa zazzaɓin"

Ɗiban jinin da za'a yiwa ruma, tamkar za a cire mata ido, ta dinga kurma ihu, tana fizge-fizge, ga ta da shegen ƙarfi, da ƙyar Aliyu ya riƙeta aka ɗebi jinin nan.
Kuka har da majina, Aliyu ya dinga dungure mata kai yana zaginta.

Ya gama gwaje-gwajen da zai yi mata, ya ce "Malaria ce ke damunta, dan haka akwai buƙatar ayi mata allurai, da kuma magunguna"

Ruma ta yi masa zuru da ido, tana jiran ta ga a ina za ayi allaurar.

Ya haɗa alluransa ya nufo ta, ta miƙe tsaye.

"Ke malama ki tsaya, dan ba zaki sake wahalar da ni ba"

"To a ina za ayi mini allurar?"

Mai chemist ya ce "Ai a baya ake yin ta"

"Wai bayana" tayi maganar tana nuna bayanta.

Nasiru mai chemist ta ce "A'a a mazaunai"

"Suwaye mazaunan?"

Aliyu ya haɗe rai ya ce "Ke juya ki tsaya ayi miki allurar nan mu tafi, kin san sarai a in da za ayi".

Ta riƙe skirt ɗin ta gam ta ce "Ni wallahi ba zai ganni ba"

Aliyu ya fizgota, ya riƙeta da ƙyar suka danneta suka yi mata, Aikuwa ta din ga zunduma ihu, kamar sun mata wani abu.

Haka aka gama yi mata treatment, suka taho gida, ban da uban kuka babu abin da take yi.
"To subhanallah, ko me aka yi mata kuma take wannan uban kukan haka oho" mama ta yi maganar tana fitowa tsakar gida.

Aikuwa suna shigowa, ta nufi mama tana kuka.

"Meye haka, kukan me ki ke haka,ki ke ɓare baki?"

"Mama yaya Aliyu ne da Nasiru mai chemist"

"Suka yi miki me?"

"Bayan ya ɗibar mini jini, kuma suka buɗe mini tsiraici na aka yi mini allura"

Mama ta ce "Subhanallah"

"Mama ba ke ki ka ce ɗuwawu tsiraici bane ba, amma har da Yaya Aliyu ya riƙe ni, Nasiru mai chemist ya ganni, wallahi ban yafe ba"

Mama ta girgiza kai, ta ƙiftawa Aliyu ido sannan ta ce "Haba Haidara, ya zaka yi mini haka, dan me za'a buɗe mata jiki ayi mata allura?"

Aliyu ya ce "To mama ai larura ce, ko a addinance ba haramun bane".

Cikin masifa ta ce "To shi yayana ne da zai ganni? Har da taɓani ya yi mini allura a wurin"

Aliyu ya ce "Sa'anki ne ni, uban me za a kalla a jikin naki?"

"Wallahi ba zan taɓa yafewa ba, Allah ya jijjigo bala'in duniya da lahira ya ɗora masa, tun da ya ganan mini tsiraici na"

Mama ta ce"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wace irin Addu'a ce haka, kar in kuma ji, baki san larura ba?"

Aliyu ya ce "Sakarya, kamar ba tsairaicin ki ka je kina kaɗawa a gaban mutane ba jiya"

Umar ya shigo ɗakin mama, suna magana, bai kula ruma ba amma dan ya duba jikinta ya shigo.

Tana kwance ga zafin ciwo, ga na takaicin allurar da aka yi mata, zafin allaurar bai dameta kamar ganinta da mai chemist ya yi.

Sai da yamma mama ta sakata ta yi wanka, ta canza kaya ta ɗan ji ƙwarin jikinta.
Sai da ta kwana uku tana fama, sannan ta ware gaba ɗaya, sai dai rashin lafiyar da tayi ya sanya aka mance da laifin da ta tafka, kowa sai lallaɓata yake, ban da Huzaifa.

Ta ware sarai har ta koma makaranta, kullum mama cikin nasiha take yi mata, tare da yi mata addu'a da fatan shiriya.
Tun daga ranar ruma ta daina bi ta hanyar chemist ɗin Nasiru, idan kuwa ta ganshi ko kallonsa ba ta yi, balle ta gaishe shi, a cewarta ɗan iska ne tsairaicin ta ya kalla.

"Mama

4 Comments On KANWAR MAZA
avatar
shemau-shafiu

12 months ago

Reply

Anayi munajin dadi

avatar
maryam-2-7-4

12 months ago

Reply

Anayi munajin ddi

avatar
maryam-2-7-4

12 months ago

Reply

Yyu kyau

avatar
hauwau-8-4

9 months ago

Reply

Dan Allah qarashen fa

Please Login or Register in order to submit comment