Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta ce "Ki na nufin bai warke ba dama?"

"Eh, mahaifiyarsa ta nemi na yi shiru da bakina, amma na kasa jurewa, sai da na ga iman tana ta shafa masa wani abu a fuska, sannan ya tashi, anya Mummy babu hannunki a ciki?"

Mummy ta yi wani murmushi sannan ta ce "Samha kenan, ke idan da hannuna a ciki zan kasa gaya miki ne, ai da ko a wurin mahaifiyarku zaki ji, babu ruwana a cikin lamarin nan, ni ban ma san haryanzu yana da wannan ciwon ba, a zatona tuni ya warke"

Samha ta rausayar da kai, sannan ta miƙe tsaye ta ce "Na tafi, dama sauri nake" bayanta mummy ta bi da kallo, sannan tayi wani irin murmushi ta ce
"Yarinya man kaza, wannan labari yayi mini daɗi da ki ka zo mini da shi, dama na daɗe ban ji labari mai daɗin wannan ba. Zan cigaba da amfani da wawancinki ina ruftaki, dole in je gidan Galadima, sai Hajiya Luba ta ji wannan zancen"

****
Ruma kuwa tuni ta manta abin da ta yi, dan ba ta ɗauki abin da tayin wani abu mai muhimmanci ba, sabgoginta ta cigaba da yi, sai dai tana iya ƙoƙarinta yanzu a kan kar ta yi wani abun da zai kuma haɗata da mai sunan Baba, dan karonsu babu daɗi sam.

***
Kamar ko yaushe, haka yanzu ma muryarta ta yake ji a kunnuwansa, a hankali ya buɗe idonsa, yana son tabattar da a ina yake, abin da ya iya tunawa shine ya shigo cikin gidan sashin Ammi, amma daga haka bai iya tuna komai ba.
A hankali kunnuwansa suka jiyo masa muryar Ammi tana karatun Alqur'ani.
Ya juya, ya kalli Ammi, ta na sanye da hijjabi, iman kuma ta ziro masa ido tana kallonsa.

Da sauri iman ta ce "Ammi ya farka"

Cikin kulawa Ammi ta dube shi, ta ɗora hannunta a goshinsa tana yi masa sannu.
Ya jinjina kai, Iman ma ta shiga jero masa sannu yana jinjina kai.

"Takawa, duk da na san ba ka so, amma ya zama dole ka yi haƙuri mu cigaba da neman magani, a baya abu ya lafa amma Kwatsam yau sai gashi ka faɗi, dole mu yi wani abu a kai kafin a farga a samu abin faɗa.

Shiruu Adam ya yi yana sauraron Ammi, ba tare da ya iya cewa komai ba.
Ammi ta kalli iman ta ce "Auta, duk da bani da matsala da ke, amma ke ma ki yi shiru, ko waccan ruɗaɗɗiyar Nusaiba kar ki gayawa"

Iman ta ce "In sha Allah Ammi, bari na je na mayar da maganin".

Zuwa washegari takawa ya ware, kamar ba shi ba,  ya cigaba da azalzala a kan a nemo masa mamallakin account ɗin nan da aka ce masa ɓarawo da shi.

A washegari Mummy ta shirya ta tafi gidan Galadima mai ci a yanzu, wato gidan su Jabir.
Hajiya Lubabatu na ganinta suka yi wata shewa, tare da gaisawa da junansu.
Hajiya Lubabatu ta ce "Ya akwai labari ne?"

"Da ɗumi-ɗuminsa ma kuwa, mu shiga daga bedroom.

Cikin ɗaki suka shiga, Mummy ta ce "Ya jikin Galadima ne?"

Hajiya Lubabatu ta ce "To ni me ma zance miki ne, a ƙarshen watan nan dai nake son ko ni ko jabir wani ya je, ance dai da sauƙi"

"To Allah ya ƙara afuwa, amma gaskiya Yakamata ki miƙe ki ɓata alaƙar da ke tsakanin Adam da Jabir, kin san idan babansu ya rasu sarauta gidanmu za ta dawo, ke sai ki zuba ido shikenan babu makoma, idan sarauta ta dawo hannun Adam waya san lokacin da zai mutu balle Jabir ɗin ma yayi sarautar, duk da ina ta ƙoƙarin ƙara rura wutar gaba tsakaninsa da Mahmud, sai dai Mahmud wawa ne, ya ƙi mayar da hankali a kan Sarautar, ba ta gabansa ".

Hajiya Lubabatu ta yi murmushi ta ce "Jamila kenan, ai kema kin san ba a zaune nake ba, kuma da sannu dukkaninmu zamu yi nasara, ai ke dama ba kya burin sarautar ta dawo gidanku"

"Ƙwarai kuwa, shiyasa nake ta son komai ya ɓaci, ko kin san ashe Adam bai warke daga wannan larurar da yayi ba yana yaro, mai kamar farfaɗiyae nan ba?"

"Haba dai, ya aka yi ki ka sani?"

"Samha ce ta zo ta titsiyeni, wai ta gani a sashin su, wai ko ina da hannu a rashin lafiyar ta sa, na ce mata ni babu ruwana, da ciwonsa na ganshi"

Hajiya Lubabatu ta ce "Kai samha ma akwai bin ƙwaƙwƙwafi, shareta kawai ai aiki yana kyau sosai"

"Haaa ke dai bari, idan har ina raye ko zan tafi tsirara sai Binta ta ɗanɗana kuɗarta in Allah ya yarda sai ciwon nan ya zame masa hauka tuburan, na kaɗa sauran yaran nata tare da wannan shegiyar yarinyar mai kama da larabawa"

Hajiya Lubabatu ta yi dariya ta ce "Shi dai wannan ɗa abu ya zame masa goma da ashirin, da hauka ko in ce farfaɗiya, ga kuma maita duk shikaɗai"

"Hmm ke dai bari, ina jiran lokacin da zan kwatsa zancen nan a cikin masarautar Kano, ɗan da suke ji da shi maye ne, da ya sha a nonon uwarsa, ta ta ba ta baiyyana ba sai ta shi"

Cike da rashin imani suke ƙyaƙyace dariya, kamar ba za su bar duniya ba.

Cikin dare da misalin ƙarfe biyu da rabi, Baba uwani ce ke sanɗa kamar 'yar fashi, ta buɗe babbar ƙofar sashen Ammi ta fita, kai tsaye ta nufi sashen Mummy, tana tura ƙofar sashin ta buɗe, ta kutsa tana waige-waige.
Hanyar kitchen ta bi, ta tarar da Mummy a wani ɗaki a zaune tana jiranta.
Baba uwani ta duƙa ta gaida Mummy, Bata amsa ba ta dubeta ta ce "Kin san dalilin da ya sanya na nemekk?"

Ta girgiza kai alamar a'a.

"An ce mini ɗan uwar ɗakinki Adam, haryanzu bai warke ba, ciwon nan da yayi da yarinta yana nan yana fama, jiya ma ya tashi haka ne?"

Baba uwani ta ce "Wallahi ban sani ba uwar ɗakina, jiya ta aikeni, kuma ina tunanin babu wanda ya sani, saboda da na dawo ban ji labari ba".

"Ba tambayarki nake dogon labari ba, ance mini akwai wani abu da aka shafa masa, ya tashi da wuri, wannan abin nake son ki sanya ido ki ɗauko mini"

"Ranki ya daɗe, ai ban san a in sa suke ajiyewa ba, ba ta sanya ni a sabgar neman maganin sa ba"

"Bai shafeni ba uwani, ki aikata abin da na ce kawai, tashi ki bani wuri"

Haka baba uwani ta taso, tana tunanin ta in da zata fara aiwatar da wannan aiki mai mugun hatsari.

****
Yau ruma fakar idon Yasir ta yi, ta ɗauki wayar nan ta jefa a jakar makarantar ta, ta yiwa mama sallama ta tafi makaranta. Sai dai da ta je makarantar babu wanda ta iya nunawa wayar, gudun kar yaran su tona mata asiri a ƙwace wayar, sai dai ta na jin kanta riƙe wayar nan da take yi, duk da ba wayar kirki ba ce ba.
Yau mama ba ta nan, ta je cikin gari za su kai wani kayan lefe na wani ɗansu, dan haka ruma sai lissafi take a kan ba zata islamiyya ba, ƙulewa za ta yi a ɗaki ta yi kallo a waya, kuma ta sha baccinta.

Ta tsaya ta sai gyaɗa a hanya, tana tafe tana ci, kamar ba ɗiya mace ba, dan ruma duk wani abu na jan aji na mata ruma ba ta iya ba, haka nan take rayuwarta kamar namiji.

Ƙarar mota ta ji a bayanta, sai dai kan ta kauce, ta ga an sha gabanta da motar, wasu ƙarti ne suka fito suka ce "Shiga mota"

"In shiga aje ina kamar a film ɗin indiya"

Cikin tsawa ɗayan ya ce "Ki shiga mota na ce"

Ruma ta cake ta riƙe ƙugu  ta ce "Wai saboda me, in shiga ka kai ni ina?"

"Kai dalla dannota kawai, za ta ɓata mana lokaci" sau ɗaya ya tankaɗa ƙeyar ruma, ta hantsila cikin motar.
Aikuwa ta din ga kurma ihu "Al'ummar ɗorayi an saceni, dan Allah ku kawo mini agaji" rufe motar suka yi, suka ja dama motar tint ce, sai dai ruma ta cika musu kunne da kururuwa.

"Ke, kin ishemu, zamu yanka ki da da wuƙa a motar nan"

"Wallahi ba zan yi shiru ba, kun satoni kun sakani a tsakiyarku bayan ku ba muharramaina bane ba".

Wanda yake tuƙa motar, ya dubi na kusa da shi, cikin harshen turanci ya ce "Anya kana ganin wannan yarinyar ce kuwa?"

"Oho, mu kai masa ita dai, shi zai tantance ".

"To ai gani na yi yarinya ce sosai, yaushe wannan zata iya wannan abu?"

"Kai wannan sai ta aikata, ji yadda take wa mutane ihu, dan ya ce ban da cin zarafi da sai na sakata a silent yanzun nan".

"Wallahi idan baku buɗe mini motar nan na fita ba, sai na tara muku jama'a, ashe ma ku ƙananan 'yan kidnapping ne, da kuka sace ni, to wallahi ni ƙanwar maza ce, idan yayyena suka gano ku, sai kun raina kanku" babu wanda ya kulata cikinsu, har suka isa in da zasu je, ba ta yi shiru ba ko na mintuna. Haka zalika idan za a kasheta ba ta san ta in da aka bi ba, saboda baƙin glass ne a motar.

Ita dai ta ji an tsaya, aka buɗe mota aka ce ta fito. Fitowa ta yi tana kallon harabar da aka paker motar.

Ingiza ruma suka yi, ta ƙanƙame jakarta tana kalle-kalle.
Wani falo aka shiga da ita, suna shiga wani irin sanyi ya daketa, ta ce "Wayyo sanyi" duk sai da suka kalleta kamar wata 'yar ƙauye.

Ita ba kawotan ne ya dameta ba, tsaruwar gidan da yadda aka narka masa dukiya ne ya burgeta take ta kallo.

Sanyin Ac ne ya fara damunta, saboda haryanzu babu wanda ya ce mata komai, tunani ta fara yi, idan mama ta dawo ta tarar bata nan fa, gaba ɗaya hankalinta ya tashi yayi gida, a yadda take jin labarin kidnapping dai ba haka ake yin sa ba, ko da yake dai ai babu maraba.
Miƙewa tayi ta dubi mutumin da yake zaune a bakin ƙofa ta ce "Bawan Allah dan Allah ku zo ku sallameni, kar babata ta dawo ta ga bana gida"

"Wuce ki zauna, kafin na fasa kanki da harsashi"

"A'a da bom zaka fasa mini kai, ni me na yi muku ne?"

"Wallahi ki ka cigaba da yi mana hayaniya, sai na saka igiya na ɗaureki"

"Kamar ya ya ka ɗaureni da igiya, sai ka ce ragon layya? Dan Allah ku zo ku mayar da ni"

Cikin tsawa ya ce "Ki koma ki zauna na ce".

Tsaki ta ja ta koma ta zauna, bin ruma ya yi da kallo jin yadda ta yi masa tsaki.

Zama ta yi ta ɗauko gyaɗarta ta cigaba da ci, tana ɓata wurin, mai gadin na ta kallonta yake, ita kamar ma ba ta damu da ɗaukotan nan da suka yi ba, gaba ɗaya ba ta da wata damuwa.

Ta gama cin gyɗarta, ta buɗe jakarta ta ɗauko rake. Duk ta ɓata wurin, ta gama ta gaji tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido.
Surutan mutane suka ji, alamar za a shigo. A cikin mutanen da suka shigo su uku, tana yiwa ɗaya kallon sani, sai dai ta manta a ina ma ta sanshi.

"Tana ina?" Ya faɗa a taƙaice.

"Gata nan a gabanka sir, ita muka samo, kuma ta faɗi wasu abubuwa da ya sake tabattar da ita ce" cewar ɗaya daga cikin wanda suka kawo ruma.

Mamaki ne ya kama shi, ta ina ƙaramar yarinya kamar wannan, ta samu waya, har ta iya yi masa wannan comment ɗin.

Ya zauna ya na ƙare mata kallo, sai wani haɗe rai take tana basarwa, tana harare-harare ta gefen ido.

Jabir ya ce "ka bi komai a sannu Please, ka ga ƙarshen abin ma ashe yarinya ce, dama haƙura kai kamar yadda na gaya maka da farko".

"Me na yi miki ki ka kirani da ɓarawo?" Yayi maganar yana tsareta da ido.

Mamaki ne ya kama ruma, ita a ina ta sanshi da zata kira shi da ɓarawo. Ya sake maimaita maganar amma tayi banza taƙi magana.

Jabir ya ɗauko wayarsa, ya shiga account ɗin da ruma tayi comment da shi ya nuna mata, ya ce "ke ki ka yi wannan comment ɗin?" Ta zubawa Jabir ido, shima ta ƙi kulashi, sai dai a yanzu ta gane in da ta taɓa ganin Adam, a Instagram taga hotonsa tayi comment.

"Wai kurma ce ne?"

"Sir wallahi ba kurma bace, yanzu ta gama magana iskanci ne, ka bari a casata kawai".

"Am talking to you, me na yi miki ki ka ci mutuncina, wai na saci kuɗin talakawa, ance miki ni ɗan siyasa ne?"

Jabir ya ce "Easy Adam, yarinya ce ƙarama, ki na ji ki san abin da zaki din ga rubutawa a social media, wanda ya baki waya ma shi ne babban mai laifi, da ya bawa under age waya. Babban mutum ne sannane, ɗan gidan marigayi Galadiman Kano ne, bashi da alaƙa da siyasa, amma kin yi masa ƙazafi shi mahaifinsa basarake ne, kuma ɗan kasuwa ba kuɗin tal.....

"Shut up Jabir, na meye zaka din ga yi mata wani bayani"

"A'a ka yi haƙuri, kin ga bashi haƙuri komai ya wuce" wani kallon zaka bushe ruma tayi masa, ta ƙara gyara jakarta ta ɗauke kanta gefe guda.

Mamaki ne ya cika Adam, shi da yake dodo ko a cikin manyan mutane, amma shi wannan 'yar shilar ke rainawa hankali, yana yi mata magana amma ta mayar da shi ɗan iska.

Jabir ya jinjina kai ya ce "Lallai gaba da gabanta, anya wannan yarinyar ba mahaukaciya bace ba?"
Kallon Jabir tayi ta galla masa harara, haka kawai tana ganinsa ta ji ta tsaneshi, wani mugun haushinsa ya kamata, ya fiye shishshigi.

Adam rasa abin yi ma yayi, dama wata babbace he knows how to deals with her, amma wannan ya hukunta ta ya ce ya yiwa wa?.

Ruma ta miƙe tsaye da jakarta, tana kallon wanda suka kawota, jinjina kai kawai suke, da ganin namijin ƙoƙarin da ubangidansu yayi.

Cikin ƙunƙuni ta ce "Ni a mayar da ni in da aka ɗauko ni" tayi maganar tana nufar ƙofar fita.

"Ku kamata ku ɗaure mini ita, sannan a nemo mini waye ubanta, in nuna wa babanta banbancin arziki da tsiya, shine dai-dai yi na, dan na fuskanci bayan talauci har da rashin tarbiyya a tare da ita.

Ba tare da ta waiwayo ba ta tsaya, dan ma kar ta kalleshi ya yi mata kwarjini ta ce "Shi baban nawa sai ka bishi kabari ka nuna masa ka fishi kuɗi, kuma Alhamdilillah ni dai an yi mini tarbiyya dai-dai gwargwado, kuma wallahi sai na saka yayyena sun yi maka bugun sakwara, har DPO na unguwarmu sai na gaya masa, ba sunanka Adam ba ɗan galadima ko wambai to wallahi sai na faɗa ka saceni ka kawoni cikin maza" tuni ya daskare a wurin, jikinsa ya hau tsuma, ga zafin maganganu da fitsarar Ruma, ga razani na jin muryar da take ta addabar kunnuwansa.

Cikin azama ya fizgota, ya juyo da ita gabansa, ya riƙe hijjabinta tare da rigar uniform ɗin ta. Kallon hannun takawa tayi, da ya sanya wani agogo mai kyawun gaske, amma babban abin da ya razana ruma, yadda ya riƙota ta wuya hannun ƙaton namiji a jikinta kan ƙirjinta, abin da aka ce ta ɓoye ta tattala, kar wani ya kai hannu wurin, idan ba haka ba za tayi ciki, amma hannun wani ƙato a wurin !!!


(Saura page ɗaya mu kammala book1, wanda za su sai book 2, an fara payment 500 ne, in sai an gama document 800.

0009450228
Aisha Adam
Jaiz bank.
Sai a turo shedar biya ta 08081012143)


Ayshercool
08081012143
ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

                      P22

*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*

Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su.
*1 Supplements na gyaran jiki*

*2 Supplements na gyaran gashi*

*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*

*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki  glowing skin*

*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress

*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*

*7 Supplements na masu  shayarwa*

*8 Supplements na tsofaffi*

*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*

*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*

*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*

*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14Supplement na whitening/glowing skin*

*15 Supplement for Acne, dark spots remover*

Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158

https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.







Wani mugun ɓacin rai ne ya kama ruma, kamar za ta yi kuka ta ce "Malam meye haka? Meyasa zaka taɓani ka cikani"

Cikin tsananin mamaki, da rashin abin yi yake sake sauraren muryar ruma "Da..d...dama kece, meyasa ki ke bibiyata mai na yi miki ne?"

"Ni yaushe na sanka ma? Ka cikani kafin na yi maka hauka da tijarar da zaka yi dana sani, ka sakar mini hijjabi"

Tsananta riƙon da yayi wa ruma ya yi, yana sake bin ta da kallo, yana jin tamkar ba shi bane ba, anya mutum ce yarinyar nan, ko kuma dai muryar ce ke cigaba da yi masa gizo.

Ganin yadda duk ya gigice kamar zai fita hayyacinsa, ya sanya Jabir ƙoƙarin cire hannun takawa daga jikin ruma.

"Takawa, dan Allah ka kula mana, yarinya ce fa ƙarama ba sa'arka ba, dan Allah ka saketa, sannan kamar yaya tana bibiyarka?"
Hankaɗe ruma yayi, ya koma gefe ya zauna, yana dafe goshinsa.

Kuka ruma take wiwi, ta ɗauki jakarta.

Jabir ya kalli wanda suka kawo ruma ya ce "Sidi ku mayar da ita".

Suka tasa ruma a gaba, ta waiwayo ta kalli takawa ta ce "Wallahi ban yafe ba ku....."

"Ke wuce mu tafi, kin samu an ƙyaleki kuma kina yi wa mutane iskanci, mara tarbiyya"

Cikin dakiya ta ce "Eh bani da tarbiyyar, ku tarbiyyar ce ta saka kuka ɗauko ni ba da sanin iyayena ba ku ka kawo ni nan, cikin maza Allah sai ya saka mini"

Jabir ya ce "Kar ka kuma tankawa yarinyar nan, mayar da ita"

Jabir ya zauna a kusa da takawa ya ce "Takawa, wa me yake faruwa ne, ka san ta ne?"

Adam yayi shiru bai motsa ba, kuma bai ce komai ba, Jabir ya yi masa tambayoyi har ya gaji, amma bai amsa masa ba.

Ruma kuwa suna zuwa unguwar su, suka ajiyeta suka tafi, ta samu wani borehole ta wanke fuskarta, sannan ta tafi gida.
A tsakar gida ta tarar da Yaya Aliyu, ya kalleta ya ce "daga ina ki ke?"

"Makaranta" ta bashi amsa tana ɓata rai.

"Ba jarrabawa ku ke yi ba?"

"Laifi muka yi aka saka mu punishment" ta bashi amsar tana tsoron kar ya ganota.

"Haka dai ki ka iya, kullum cikin laifi kamar ke kaɗaice ɗaliba a makarantar"

Ganin bai ganota ba, ya sanya ta shiga ɗaki, ta ajiye jakarta ta tafi gaban mudubi ta tsaya, ta ƙarewa kanta kallo, ta tuna yadda takawa ya shaƙeta hannunsa har yana taɓo ƙirjinta.
Wasu hawayen ne suka shiga ziraro mata. "Wallahi sai ka gane baka da wayo, ka zunguro sama da kara, ni za a ciwa mutunci? Wallahi sai na kuma rubutawa, zaka gane ba ka da wayo, ai talauci ba hauka bane, mai kyan banza" haka ta tsaya a gaban mudubi, ta cigaba da kuka.
Kamar zararriya ta ɗauko jakarta, ta ɗauko wayar ta kuma komawa kan account ɗin da Jabir ya saka hoton takawa, ta sake rubuta "Wallahi Allah ban yafe ba, sai na kai ƙararka wurin 'yan sanda, zaka san da ni kake yi" ta ajiye wayar tana fatan Allah ya sa kar idan mama ta dawo ta fuskanci wani abu.

****

Baba uwani ce ta shiga kitchen ta tarar da iman tana faten dankali.

"A'a mutuniyar ba kya gajiya da aiki, Ammin ake yiwa girki ne?"

Iman ta yi murmushi ta ce "A'a baba uwani, nice zan ci"

"Au yau ba za a ci abincin namu ba ne?"

Iman ta yi murmushi ta ce "Ba haka bane, kawai da wannan ɗin nake sha'awa bana son takura muku ne"

"A'a ai da kin faɗa ma babu wani abu, sai ayi miki, ni kuwa na ce takawa lafiya ƙalau kuwa yake?"

Cikin rashin fahimta iman ta ce "Me ki ka gani?"

"Ganinsa na yi duk wani iri"

"A'a lafiyarsa ƙalau, ina ga hakan ya na da alaƙa da yanayin aikinsa, kin san abubuwa su kan yi masa yawa"

Baba uwani ta ce "haka ne wallahi, ina tausayawa takawa yadda al'amura suke shan kansa Allah ya yi masa jagora"

Iman ta ce "Amin" a dai-dai lokacin ta juye dankalin a plate ta ɗauka ta fice.

Baba uwani ta yi tsaki ta ce "Kai wannan yarinyar kininabbiya ce ba wani abu da zaka samu daga wurinta".

Takawa fa abubuwa suka sake rikice masa, tun bayan haɗuwarsa da ruma, da ya ji muryarta da take masa yawo a kunne, yana ta tuntuntuni, mutum ce ko akasin haka, dan iya ƙwarin gwiwar ta, da rashin kunya da ayar tambaya a kanta.
Yau gaba ɗaya bai koma gida ba, ya wuce gidansa ya tura wa Ammi message a kan ba zai shigo gida ba, a gidansa zai kwana.
Bayan ya turawa Ammi saƙon, ya kuma komawa Instagram, ya duba comment ɗin da ruma ta yi a kansa, kawai ya ci karo da sabon saƙonta, ya tabatta kenan ita ɗin ce dai ta yi comment ɗin farko.
Kiran Ammi ne ya shigo wayarsa, ya saita nutsuwarsa ya ɗaga tare da yin sallama.
Ammi ta amsa sanna ta ce "Yanzu na ga saƙonka, ka sam yadda yanayin jikinka yake, amma ka ce zaka kwana a gidanka kai kaɗai, kar wani abu ya sameka fa"

"Ammi kar ki damu, babu abin da zai sameni in sha Allah, ina son gabatar da wani aiki ne"

"To shikenan, amma dai da ka ji wani abu ka kirani a waya".

Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, in sha Allah sai da safe" suka yi sallama ya katse kiran.

Ya rintse ido, yana jin muryar ruma na sake amsa kuwwa a kunnuwansa, ya tuna yadda ta danganta shi da sata, take ya ji ya tsani yarinyar, kuma daga uniform ɗin jikinta zaka gane 'yar talakwa ce, amma sai ƙarfin hali da rashin mutunci, to yayi faɗa da wannan 'yar ma ya ce ya yi da wa? Wani uban tsaki ya ja, ya koma ya kwanta yana ƙwafa. Ya kuma komawa ya na duba comment ɗin ruma, amma ya tarar Jabir ya goge posting ɗin gaba ɗaya.

***
Ko da mama ta dawo, ta tarar gaba ɗaya ruma ba ta da walwala, duk tayi wani iri, mama ta tambayeta ko ba ta da lafiya, ta ce ita lafiyarta ƙalau kan ta me yake ciwo, mama kuwa ta ƙayleta, amma ta cigaba da monitoring ɗin ta.
Yau ko wannan uban surutun da take kamar an jefeta a ka, babu ta yi shiru sai tunane-tunane take a ranta, a kan me za ta yi wa wannan ɗan tahalikin ta huce, gashi ita ba ta san a ina ma za ta sake ganinsa ba, balle ta gaggaya masa magana

4 Comments On KANWAR MAZA
avatar
shemau-shafiu

12 months ago

Reply

Anayi munajin dadi

avatar
maryam-2-7-4

12 months ago

Reply

Anayi munajin ddi

avatar
maryam-2-7-4

12 months ago

Reply

Yyu kyau

avatar
hauwau-8-4

9 months ago

Reply

Dan Allah qarashen fa

Please Login or Register in order to submit comment