Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

surutun da nake ba ka ma gane me nace ba?"

"Sorry" ya faɗa a taƙaice yana tsare Jabir da ido alamar yana son ya maimaita masa me ya ce.

Jabir ya ce "Well, cewa na yi, wai me ƙaninka yake nufi da Iman ne, yana takura mata da yawa fa"

"And so...?"

"Kana nufin ba ka damu ba kenan?"

"Kaga ni ka ƙyaleni da sabgar gidan nan, bana iya tunanin komai a kai, ko na fara ma kaina ciwo yake yi, gaba ɗaya bana son yin tunani a kan matsalolin gidan nan ".

Jabir ya yi ajiyar zuciya ya ce "Haka ne, ni auren Iman nake son ku bani, ka wuce mini gaba zuwa wurin Ammi mana".

Wani irin kallo Adam ya yiwa Jabir ya ce "Ba ka da hankali ne?"

"Ban gane ba ni da hankali ba?"

"Amma ka san ba abu ne da zai yiwu ba ko?"

Jabir ya ce "Saboda me, wai ni ko dai kai ne ka ke son ta ne?"

Tsaki Adam ya yi ya tashi ya ce "Ka san idan har zan auri Iman, zan iya auren su Nusaiba ko Fauziyya, kai ma ka san ba zan bari ka auri Iman ba, kuma ka san dalili".

"Amma a tunanina wannan bai kai hujjar da za a hanani aure ba"

A ɗan hasalae takawa ya ce "A ganinka ba"

"Amma....." Bai jira jabir ya gama maganar ba, ya fice ya bar Jabir.

****

Ruma ce a tsakar gida, ta zage tana ta dakan ƙuli-ƙuli, zata yiwa Yasir kafi kaza, dan ya ƙara samun ƙwarin gwiwar bata waya tana jagwalgwalo, dan wayar ta fara shiga ranta sosai, ga cacar kuɗin data yana yi mata, da na caji wasu lokutan, tayi kiran ƙawayenta a wayar iyayesu su yi ta shashashanci ta daina ɗaukar ta mama.
Mama tana ganin wayar a hannun ruma, tana mitar ba ta son yawan duba wayar nan da take yi, a zatonta wayar Yasir ce kawai yake bata ta yi game da wasanta ta bashi kayarsa.

Mai sunan Baba ya nutsu ya tattara hankalinsa a kan litattafansa, sai dai hankalinsa ba a kan litattafan yake ba, damuwa da tunani ne fal a ransa, zuwa yanzu yakamata a sake aikawa da Abubakar kuɗi ko babu yawa ne, dan har zuwa yanzu ya ce masa bai samu wani aikin ba, leburanci ne ya kan shiga cikin gari ya nema idan ba shi da lectures, kuma gashi ɗan abin da za a baka na leburancin nan, bashi da wani yawa ga wuni ana aikin ƙarfi.
Ga kuɗin saukar su Yasir, ga kuɗin Necon su, dan dai suma yaran suna da ƙoƙarin neman na kai, da karambani Yasir ya koyi gyaran fitila, da wayoyi gashi ya san kan computer sosai, yanzu zai kashe wata wayar  ya tashi wata yana da kai a wannan fannin.
Shi kuma Huzaifa big boy ne, shi baya tanadi, idan ya samu kuɗi kawai ya kashe su, a huta. Sai dai bashi da rowa, yana zuwa shagon ɗinki da na aski, amma mugun mashiririci ne na gaske.
Sallamar da aka yi ne, ta dawo da mai sunan Baba daga tunanin da ya tafi.

Wata yarinya ce sa'ar ruma, sai kuma wata 'yar budurwa suka yi sallamar.

Fuskarsu kawai ya kalla, ya san da ƙuyar idan ba ruma ce, ta yi wata tsiyar ba.

Suka gaida mama cikin ladabi, shi kuma ya mayar da hankali a kan littafin gabansa kamar bai san da zuwansu ba.

Zumbur ruma ta miƙe, za ta janye su, mama ta ce musu yaya aka yi, saboda ita mama a tarbiyyar ta ƙawaye ba sa biyo ruma gida, idan ba wani abu ne mai matuƙar muhimmanci ya kawo su ba.

'yar babbar ta ce "Kuɗin da ƙanwata take bin ruma, muka zo karɓa".

Cikin mamaki Mama ta ce "wane kuɗi kuma?"

Yarinyar ta ce "Ranar an aiki ƙanwata, suka haɗu da ruma, shi ne a canjin mamanmu, ruma ta ranci naira ɗari biyu ta bawa wani  tsoho almajiri, wai  ya bata tausayi da ga gani yunwa yake ji, wai zata bata kuɗin kuma haryanzu ba ta bayar ba, mamanmu kuma so take ta yi amfani da kuɗinta"

Mama ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, ita ruman? Uban waye ya ce ki karɓar musu kuɗi kiyi sadaka da su?"

"Wallahi mama tausayi ya bani, cewa yayi na taimaka masa, kuma idan na bayar da kuɗinki zaki yi mini faɗa, shi ne na ranci canjin babarsu, kuma malam ne ya ce mana sadaka maganin masifa ce"

"Ke a cikin wace masifar ki ke? Ko da yake akwai masifar da ta wuce ɗauko mini magana da ki ke yi ba yau ba gobe, baki yi sadaka da kuɗin uwarki ba sai na uwar wasu, saboda tsabar rashin ji?"

Abdallah ya ce "Wallahi mama yarinyar nan da ƙyar idan ba ta da taɓin hankali".

Mama rasa me zata yiwa ruma ta huce ta yi, saboda yadda take caza mata kai abin ya wuce hankali, sai ƙifta ido take kamar an kwashewa karya 'ya'ya, gefe ɗaya kuma tana hararar yaran.
Mai sunan baba ya kalli Ruma, ya ga tana yiwa yarinyar alamar idan suka haɗu sai ta yankata.
gashi yau Mama ba ta da wani kuɗin kirki, ga ruma zata ja mata fitar naira ɗari biyu ba dalili.

Mai sunan Baba ya saka hannu a aljihunsa, ya ciro naira ɗari biyu ya ajiye ya kalli yaran ya ce "zo ki ɗauka"

Cikin fargaba da tsoro yarinyar ta tafi ɗaukar kuɗin, dan fuskarsa ma kawai abar tsoro ce saboda kwarjini.

Har ta durƙusa ta ɗau ɗarin, ya kalleta sai da hantar cikinta ta kaɗa, ta dakata da ɗaukar kuɗin.

"Ke shashashar ina ce da wata za ta ce ki bata aron kuɗin babarki, ki bata ta bayar kina tsaye san sokwanci"

Jiki na rawa ta ce "Idan ban bata ba zata iya dukana"

"Idan ta dakekin ba zaki iya ramawa ba, ko ƙarfinki ta fi? Daga yau idan kuka kuma bata wani abinku, ku ka biyota gida kawo ƙara, da ku da ita zan haɗa na zane, ɗauki ki tashi ki bani wuri"
Kamar mai shirin ɗauko wani abu a wuta, haka ta miƙa hannu ta ɗauko kuɗin, ta tashi suka fice da sauri.

"Ke kuma zo nan" yayi ya yana kallon inda ruma take.
Jikinta har wata tsuma yake, ta taso ta zo in da yake ta durƙusa.

Ya ƙare mata kallo ya ce 'har kin manta sharaɗinmu ko?" Ta girgiza kai.

"Da kyau, nan da gobe in Allah ya ki nemo kuɗina da na bayar ki biyani, dan ba zan ɗau asara ba, kuma ban yarda ki tambayi wani a gidan nan ya baki ba, kuma ki ka je waje ki ka ɗauko magana sai na takaki a gidan nan, mara kan gado tashi ki bani wuri" da sauri ta zabura ta bar gabansa tana tsuma, ita yanzu a gidan uban wa za ta samo kuɗin da zata biya shi?.

Haka ta koma tayi zuruuu, kamar ruwa ya jiƙa mage, tana ji a ranta idan ta kama yarinyar nan sai ta daku, saboda ja mata damuwa da ta yi.

****
Samha ce zaune a falo, tana shan twa da biscuit tana yi tana kallon tv, tare da kaɗa ƙafa.
Wayarta ce ta fara ringing, dan haka ta ajiye kofin tean, ta ɗau wayar ta kara a kunnenta.

"Samha" ya kira sunanta a taƙaice.

"Waye?" Tayi maganar cikin ƙosawa.

"Khalifa Usman wakili"

"Wai meye haɗina da kai ne? Me ka ke so kuma?"

"Easy mana, a kan maganarmu ne dai da muka fara"

Samha ta ja tsaki ta ce "Wai kai baka ganewa ne? Ba mun gama wannan maganar da kai bane ba?"

Ya ɗan yi shiru sannan ya ce "Ina ƙara baki lokaci ne, gudun kar ki dawo kina cizon yatsa daga baya, kin fi kowa sanin halin sa da taurin kai, ke a tunaninki ta ina burinki zai cika, kina daga zaune kina shashashanci lokaci na ƙure miki? Kiyi abin da ya dace ki samu burinki ya cika, ganin bayan Adam baya na nufin yi masa illar da ba zai amfanu a gareki bane ba, amma ganin bayan nasa shi ne samun damarki na biyan taki buƙatar. Idan so nake na kawar da Adam, abu ne mai sauƙi a gareni, amma ni ba hakan nake buƙata ba, haɗin kanki kawai kiyi tunani amma".
Bai tsaya jin amsarta ba, ya katse wayar, Samha ta bi wayar da kallo, tamkar za ta ga Khalifa a ciki. A hankali ta ajiye wayar ta yi shiru tana jujjuya maganar sa, sai dai ta kasa gano cikakkiyar mafita a kan lamarin.

"Samha, me ki ke tunani ne?"

Samha ta kalli mai maganar ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"Ki yi sauri ki je ki duba kayan nan, bana son sai an fitar mutane sun gama zaɓa tukuna"

Samha ta ce "Shikenan" sai dai hankalinta da nutsuwarta sam ba sa tare da ita.

***
Sam ruma ta rasa sukuni, gaba ɗaya sallolinta addu'a take a kan Allah ya sa mai sunan baba ya huce, idan bai huce ba bata san in da zata samo ɗari biyun nan ba, gashi ya ce kar ta sake ta tambayi kowa a gidan.
Gashi har wayewar garin yau ba ta samu kuɗin ba, wunin ranar bai kulata ba, bai kuma ce ta bashi kuɗin ba, sai da dare yayi, ta rasa dalilin da ya sanya yake son hukunta ta da daddare ya hanata bacci.
Tana zaune zuruu ta takure, tana zancen zuci ta ga ƙafafuwan sa, tana ɗaga ido suka yi ido huɗu.
Take ta rikice ya fara "Wallahi yaya ban samo kuɗin nan ba, ban san a in da zan samo su ba, kayi mini rai dan Allah".

"Kin san ba ki da inda zaki samo kuɗin kika arar mata kuɗi, da uban wa zaki biyata da? Wato sata ki ke kenan"

Cikin kururuwa ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, wallahi ban taɓa ɗaukar kayan wani ba. Wallahi dama niyyata na tara mata, sai na biyata amma wallahi bani da kuɗin da zan biyaka dan Allah kayi haƙuri"

Cikin kaushin murya ya ce "Sai fa kin nemo kuɗina kin biyani, ko a ina ne"

"Wallahi sai dai in kayana za a sayar a biyaka, amma wallahi bani da su"

"Wallahi da kin samo kuɗin nan kin bani, sai na taka kanki, ta tabatta sata ki ke yi, ko a gida ko a waje, amma sai Allah ya ƙwace ki, kin yi sa'a da kin gane shayi ruwa ne, sai na sakaki a mari na kulle, kuma ki cigaba da abin da ki ke yi kar ki fasa, idan ki ka kaini bango sai dai ki ji an ɗaura auranki da malam Ladan, ko na sakaki a mari" jikin Ruma har ɓari yake, saboda wannan taratsin da yake yi mata kamar ta yi fitsari haka take ji. Ba ta samu damar shaƙar isashiyar iska ba, sai da ya bar ɗakin ta dinga ajiyar zuciya.
Mama kuwa sam ba ta tanka musu ba, dan a yanzu kowane hukunci mai sunan Baba zai ɗauka a kan ruma, ba zata nema mata sassauci ba, saboda ruma babu alamar shiriya a tare da ita.

Sai da wannan ƙurar ta lafa, sannan ruma ta samu nutsuwa, ta cigaba da harkokinta.

Kamar mai ɗaukar karatu, haka ta nutsu a kan waya, tana kallo a Instagram wani abun ta yi dariya wani tayi tsaki.

Kan wani hoto taje, wani kyakkyawan mutum, ya sha kayan graduation, yanayinsa bai yi yanayin fara'a ba, amma ya ɗan geɓare baki yayi murmushi, har za ta yi liking saboda a rayuwarta tana son ta ga mutanen da suka yi nasara, musamman ta kammala karatu.
Kawai sai ta sake wurgawa, ta ga wani hoton nasa a cikin turawa, ta dinga dubawa, sauran hotunan duk a cikin turawa, da kuma aji na karatu, ajin tamkar ofishin wani shugaban ƙasar.
Haushi ne ya kama ruma da tuno yadda ajinsu yake, sheranjiya da aka yi ruwan sama, suka je suka tarar ruwa ya cika ajinsu, murfin kwano ya yaye, sai haɗesu suka yi a wani ajin.
Ai babu tunani ta shiga comment section ta ce An ɗibi haramun an je karatu, Allah ya isa kuɗin talakawa, ɓarayin kuɗin mutane, bamu yafe ba muna fama ajinmu ko rufi babu.  daga haka ta ƙara gaba, ta cigaba da kallonta.

Ta gama abin da take, ta ajiye waya ta shiga nata shagali.

Sai da daddare ta dawo, ta sake ɗaukar waya, ta ga an yi mata reply a message, ta yi ta murna yau an kulata a Instagram, dan ganin mutanen Instagram ɗin take wasu mutane daban.

Sai dai tana dubawa ta ga wani yayi mata replying da 'Ya aka yi ki ka san da kuɗin talakawa ya yi karatun'

Cikin zafin rai ta rubuta 'Idan gaskiya ne meyasa ya tafi ƙasar waje karatun, su yi a Nigeria mana" ta rufe datar ta ajiye tana huci, tare da ɗan jin releif a ranta, dan ta daɗe tana son samun damar da zata isarwa irin wannan mutanen abin da yake ranta.
Yanzu take jin kallon waya yayi mata rana, da ta ƙi yin zuciya har ta iya yadda ake amfani da irin wannan abubuwan.

***
Takawa ne riƙe da waya a hannunsa, Jabir sai surutu yake yi masa, amma kasancewar suna da banbancin hali shi da Jabir, ya sanya Jabir bai damu da rashin amsawar Takawa ba, saboda shi mutum ne ba mai yawan magana ba.

Can Adam ya ɗago rai a haɗe ya ce "Kai, wai ban hanaka ɗora hotuna na a social media ba?"

Jabir ya yi dariya ya ce "Tuna baya ne, ya sanya na ɗora gashi ka yi kasuwa 'yan mata sai comment suke yi, waɗanda kuma suka sanka, suna yabawa tare da jinjina maka"

Adam ya yi guntun tsaki ya ce "Kana da matsala" har ya wuce account ɗin Jabir, kawai ya koma ya shiga comment section yana dudduba abin da aka ce.

Sai dai lokaci ɗaya annurin fuskarsa ya ɗauke, har wata zufar ɓacin rai ta fara tsatstsafo masa a goshinsa, duk kusan ko yaushe a cikin damuwa yake, amma ya daɗe bai ci karo da abin da ya daki zuciyarsa kamar wannan ba.
Ya ɗaga ido yana kallon Jabir, Jabir ya ce "Ya dai, ya na ga kana kallona?"

Riƙe wayar yayi, ya cigaba da kallon Jabir, Jabir ya miƙe ya duba wayar, ya yi tozali da abin da ya sanya Adam ɓacin rai.
Jikinsa ne yayi sanyi, dan sam bai san an yi wannan comment ɗin ba. Yana ƙoƙarin yin magana takawa ya ce "Kira mini Sidi a waya, ayi mini tracking ɗin account ɗin nan"



(Mun kusa kammala book1 in sha Allah, mai buƙata yana iya yin payment na book 2.
500 ne via 0009450228
Aisha Adam jaiz bank. Sai a turo mini evidence of payment ta 08081012143, zan ɗan bada time kan na cigaba da book2, sai an gama payment, hajiyata idan har kina iya sayen data ki saka a wayar ki, to ki tara kuɗi ki sai book ɗin Ƙanwar maza, you will never regeret tafiyar akwai ƙaruwa a cikinta. Ina alfahari da ku masoya)

Ayshercool
08081012143
                ƘANWAR MAZA
                

Na Aisha Adam (Ayshercool)

MIKIYA WRITER'S ASSOCIATES

                      P21


*MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE*

*SHI YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA? TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN FATA NE, KO INFECTION? KO KUMA SO KI KE FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI,
SANNAN YAN UWA KUSANI DUK SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO*

Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu.

👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin* su.
*1 Supplements na gyaran jiki*

*2 Supplements na gyaran gashi*

*3 Supplements mai da* *tsohuwa yarinya anti aging*

*4 Supplements na karawa* *fata kyau da sheki  glowing skin*

*5 Supplements na masu ciwon jiki da stress

*6 Supplements na masu ciki, da masu shayarwa*

*7 Supplements na masu  shayarwa*

*8 Supplements na tsofaffi*

*9 Supplements na karin ni'ima da tighteningn*

*10 Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc*

*11 Supplements na gyaran* *nono da mazaunai breast/hips*

*12 Supplements na gyaran* *HQ ciki da waje*

*13 Supplements na rage* *tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton*
*14Supplement na whitening/glowing skin*

*15 Supplement for Acne, dark spots remover*

Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158



https://www.youtube.com/@CoolhausaNovels
*Wai ina da ku fans, ace haryanzu ban haɗa 1k subscribers a channel ɗina ba, anya akwai amana kuwa😒*

Ku yi subscribing YouTube channel ɗin
@Cool Hausa Novels, domin samun daɗaɗan litattafan hausa na sauraro.






Jabir ya ɗan yi gyaran murya ya ce "Ka ga dan Allah ka kwantar da hankalinka, ka san ba a rasa irin waɗan nan a social media yaran talakawa ne kawai marasa tarbiyya amma dan Allah kawai ka share"

Takawa ya kalli Jabir ya ce "Ka kira mini Sidi na ce"

Jabir ya girgiza kai, wasu lokutan takawa akwai kafiya da gardama, da ga ganin comment ɗin mace ce, kuma koma menene ba zai huce ba tun da ta riga ta yi.

Ya lalubo lambar sidi, ya kira masa shi, ya bashi wayar.

Cikin zafin zuciya ya karɓi wayar, ya yi wa sidi bayanin abin da yake son ayi masa.
Yana gama wayar, ya jefa wa Jabir wayar, ya fice daga ɗakin gaba ɗaya.


Sosai samha ta ɓata lokaci wurin yin kwalliya, kasancewarta 'yar ƙwalisa, sai dai babbar matsalarta ta ƙware a iya shigar banza, tun da garin Allah ya waye, bayan sun kammala waya da khalifa ta ji ta na son ganin takawa, dan haka da la'asar ta shirya ta tafi gidan, domin ganinsa.

Sai dai cikin sa'a, da ta shigo kan ta kai sashin Ammi, ta ga takawa ya taho fiuuu. Yanayinsa na rashin walwala bai sanya ta damu ba, balle ta saurara da abin da ta yi niyya.

Kai tsaye ta tunkari in da yake, ta fara yi masa magana, ko kallon in da take bai yi ba, yayi gaba abin sa, mamaki ne ya cikata, amma ba ta haƙura ba ta bi bayansa zuwa sashin Ammi, sai dai a sashin Ammi ma bai tsaya a falo ba, ya wuce ciki. Gaba ɗaya zuciyarsa a cunkushe take, an daɗe ba a gaya masa abin da ya ƙona masa rai kamar wannan comment ɗin ba, danganta shi da sata ba.
Samha kuwa gani tayi da kunya ta bi bayan takawa.
Nusaiba ce ta fito cikin shiri, da alama fita za ta yi, tayi arba da Samha a falo a tsaye.

"Ya dai na ganki a nan a tsaye, ko zama baki yi ba?" 'yan kame-kame Samha ta hau yi "Amm, dama takawa yana nan ne?"

"Ban sani ba, amma meyasa ki ke nemansa?"

Tsuke fuska Samha ta yi ta ce "Ina ruwanki da dalilin da ya sanya nake nemansa, ba abin da ya shafe ki bane"

"Haka ne, amma kamar yayi banbarakwai da yawa, ko kin manta waye shi a wurinki, Anty Samha ai ana barin halak dan kunya"

"Shut up! Na ce miki akwai wani abu ne a tsakaninmu, kin san bana son raini ko? Kuma ko ba komai ai takawa ɗan uwana ne" Nusaiba ta ce "Haka ne, Allah ya taimaka" ta wuce ta bar Samha a falon.

Samha ta damu ta ga Adam sosai da sosai, domin samun ƙwarin gwiwar yanke hukunci a kan abin da Khalifa ya zo mata da shi.

Fitar Nusaiba babu daɗewa, Samha na tsaye na ta tunani, ma'aikatan sashin Ammi babu wanda ya tanka mata tun bayan gaisuwa, saboda sun san halinta na dizgi da wulaƙanta mutane da cin zarafi.

Iman ce tayi sallama a cikin falon, kamar kullum tana ganin Samha gabanta ya faɗi.
Salo-salo kamar mara lafiya iman ta ƙaraso cikin falon, ta kalli Samha ta ce "Anty Samha ina wuni?"

Samha ta ɗago kai ta kalli iman, ta yamutsa fuska, ta tsani iman fiye da yadda ta tsani 'yar uwatta. Ta ko ina iman kyakywar ce, ko da kwalliya babu, ko a wani yanayi yarinyar kyau ne da ita, ko kuka ko dariya, ko fushi ko fara'a komai kyau yake mata, ga tsananin kusanci da yake tsakaninta da takawa, bayan ɗaya katangar da ta yi mata shamaki da cimma burinta da take ta ƙoƙarin rusheta, iman ma wata babbar matsala ce a gare ta, dan duk tsanani akwai aure a tsakanin ta da takawa. Ba ta sake tabattar da Iman matsala ce a gare ta ba, sai da samarin 'yan matan gidan suke zamewa su ce suna son iman, sai da su Fauziyya suka yi da gaske, wurin damɓara mata mummunan fenti, da yayi mugun taka rawa wurin rusa farincikin rayuwar iman sannan suka samu sauƙi, ga yarinyar sumi-sumi kamar munafuka, tana da sanyin hali, nutsuwa da kuma girmama mutane, shiya sanya kowa yake sonta, ban da yanzu ma da ake janye jiki daga gare ta.

"Anty Samha, wai ya na ga kina ta kallona? Me na yi kuma?"

Wani mugun kallo ta yiwa iman ta ce "Zan yi maganinki ne, magani na har abada, idan har baki bar sabgar takawa ba" iman na shirin magana, Ammi ta fito da sauri daga sashenta tana ƙwalawa iman kira.

Ganin Ammi a ruɗe ya sanya iman bin Ammi da sauri, ba tare da tunnin komai ba, Samha ma ta rufa musu baya.

A ɗakin Ammi suka tarar da takawa a sheme a ƙasa.

Cikin ruɗu Ammi ta ce "Iman ina maganin sa"

Cikin rawar jiki iman ta ce "Ammi me aka yi masa kuma ciwon ya tashi?"

"Ban sani ba, kawai yana shigowa ya faɗi yi sauri ki ɗauko".

"Kin san ya daɗe ciwon bai tashi ba, sai na binciko shi a in da na ɓoye, bari na ɗauko"

Samha ta ce "Ammi meya same shi ne?"

"Bashi da lafiya ne" Ammi ta bata amsa a taƙaice.

Iman ta ɗan jima sannan ta kawo maganin, wani mai ne a doguwar kwalba ta zo da shi, ta buɗe tana shafawa takawa a goshinsa, jikinsa sai wani irin rawa yake yana ƙamewa kamar mai farfaɗiya.

Iman ta dinga shafa masa tana karanto adduoi daban-daban, kusan mintuna goma sannan ya daina abin da yake yi, da kansa ya tashi ba tare da ya cewa kowa komai ba, ya je ya hau kan gadon Ammi ya kwanta ya rufe idonsa.

Samha ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ammi bari na tafi, dama mama ce ta aiko ni wurin Mummy, na biyo na gaishe ki, bari na tafi Allah ya ƙara lafiya".

Har samha zata fita, Ammi ta kirata, Samha ta dawo gaban Ammi.
Ammi ta riƙo hannun Samha ta ce "Dan Allah Samha kar ki gayawa kowa takawa bashi da lafiya, waɗanda suka san yana da wannan rashin lafiyar sun zata tuni ya warke, dan Allah ki rufa mini asiri, ki yi shiru da bakinki" Ammi tayi maganar kamar zata yi kuka.

Cikin kulawa Samha ta ce "Ammina, kar ki damu, babu wanda zan gayawa in sha Allah, rufin asirinki ai namu ne, ba wanda zai ji in sha Allah "

Ammi ta jinjina kai, ta yiwa Samha godiya, iman kuwa tausayin Ammi yakamata, ammi haryanzu ba ta san halin samha ba, ko da yake ba wanda zai yadda da samha fuska biyu ce da ita.

Jiki a sanyaye Samha ta wuce sashin Mummy, sai dai sashin na ta shiru babu kowa. Kai tsaye ta nufi ɗakin Mummy.
Ta tarar da mummyn na waya, ta samu wuri ta zauna tana jiran ta kammala wayar.
Mummy ta kammala wayar ta dubi Samha ta ce "Samha 'yar ƙwalisa, ya aka yi ne, na ga duk jikinki a sanyaye?"

Samha ta dubeta ta ce "Mummy, wai dan Allah baki da masaniya a kan rashin lafiyar Adam?"

"Wace rashin lafiya kuma?"

"Rashin lafiyar da ake cewa yana da ita, yau na gani da idona"

Mummy ta waro ido waje

4 Comments On KANWAR MAZA
avatar
shemau-shafiu

12 months ago

Reply

Anayi munajin dadi

avatar
maryam-2-7-4

12 months ago

Reply

Anayi munajin ddi

avatar
maryam-2-7-4

12 months ago

Reply

Yyu kyau

avatar
hauwau-8-4

9 months ago

Reply

Dan Allah qarashen fa

Please Login or Register in order to submit comment