Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi Yana kokarin Kiran wayar wannan saurayin daya anshi wayar shi jiya.

A Bayan sun gaisa yake sanar da yaran idan baya komai yadan leko asibitin Dan shi zai ke gurin aiki zuwa da yamma zai zo su mayar da ita gida.


Da to ya amsa tare da yimai godiya kafin suka katse wayar.

Da haka ya wuce office dinsu dake Kan titin kabala.tun kafin yayi parking constable suka fara kwasar gaisuwa har zuwa ciki sai yaron shi dake dauke da jakar shi Yana take mai baya.har cikin office dinshi kafin ya fara gabatar da aikinshi cikin kwarewa da sanin makamar aiki.



Zulaihat kuwa girkin Rana ta dora saboda tana so driver ya kaima su Arfat islamiyya Dan sai karfe shida ake taso su.bayan ta idar wanka ta karayi tare da daukar wani sabon wankan Dan tasan mai gidan nata Yana hanyar dawowa.


Shiko A S P Habib daga office dinshi asibitin ya koma,acan ya tarad da wannan saurayi bayan sun gama komai na dokokin asibiti aka yi discharging nasu,dukansu suka nufi gidan su yarinayar.ta wurin inda ya kadeta suka nufa tana yimasu kwatance har suka karaso kofar gidan.

Wani Dan madaidaicin gidane baya da girma Amma ba laifi daidai zaman mutum daya da matarshi.sauka sukayi suka tsaya a jikin motar sai ita ta fara shiga.
A bakin fanfo ta iske innajo tana wanke kwanika.a hankali tayi sallama tana bin bango,saboda duk a tsorace take.innajo data juya baya waigowa rayi tana amsawa "Amin wa'alaikas salam wace......"sauran kalaman bakinta ne suka makale ganin Habiba kamar a mafarki.cikin kidima tana nunata da yatsa ta fara cewa "Yanzu Habiba sai yau kikaga damar dawowa daga yawon naki,daga na aike ki kika tafi baban ki Yana ta faman yiman ruwan masifa".

Itadai yarinyar da aka Kira da Habiba ta tankata ba sai dakin da take kwana ta wuce tana share hawayen fuskarta.



A waje ganin shirun yayi yawa yasa A S P ya cewa lado ya leka yaga ko lafiya.yana kwada sallama innajo Bata jiba tana ta masifa sai can ya ankare da sallamar da ake bugawa a bakin zuren gidan.

Lekawa tayi tana mitar wanene?

"Mune Wanda muka kawo Habiba yanzu shi ne bakon ya ce Yana son ganin mai gidan"cewar lado.


Habar zaninta ta gyara kafin tace "to.. to.. to ai mai gidan bayanan sai ni kadai a gidan ko?"tana kallan lado da yake mazurai.

"To ki leko daga nan zaure dai kuyi magana da shi"Yana juyawa Dan sanar da A P P.


A tare suka dawo zauren,bayan sun gaisa da innajo sannan suka yimata bayanin abinda ya faru da cewar shi ne ya kadeta bai gani ba,Amma ayi hakuri kudi ya Bata da sauran kayan abincin da suka rage a asibiti yayi mata godiya Yana cewa idan babanta ya dawo a sanar mai shima Kuma insha Allah zuwa jibi zai dawo Dan Kara duba ta.


Da haka suka rabu tana ta godiya.

Shima lado har kofar gida ya sauke shi yayimai ihasani kafin ya juya Kan motar shi ya nufi gidan nashi.


Itako innajo sai fada ya koma ciki ganin irin wannan kudi haka tayi ta washe Baki.



A wannan lokacin zulaihat ta Kara shiryawa Dan tarbar mai gidan nata.tana jin Karan motar shi ta fita da sauri bakin kofar falon.wasu riga da wando ne ta saka masu kyau sun kama jikinta das rigar Yar karama ce da kadan ta kawo kugunta daga gaban rigar kuwa anan hango kirjinta daya ciga makil da na shanu.

Tun daga nesa take hangota harya karaso Yana kallanta.rungumeshi tayi tana yimai sannu da zuwa,ciki bedroom dinshi suka wuce ruwan wanka ta hadamai ta ragemai uniform din kafin ya nufi toilet Yana ta murmushi.a Bayan ya fito ta zaba mai kananun Kaya na shan iska ya saka ta fesa mai turare.abinci ta kawo mai yaci sosai saboda yaji dadin irin tarbar da tayi mai.bayan ta kwashe kwanukan ta mayar Suka zauna suna Dan taba hira Daman yayi sallah tun a office.
Tana rungume jikinshi suna hira daga nan ya fara wuce gona da iri a ranta ta ce "Ai nasan hakance zata faru,ayi mutum shi baya gajiya da abu daya nan daya gama kashe ni zaije ya auro wata inaji ina gani zasu rinka soyewa bani da wannan damar,Dan haka da sauri ta kwace jikinta tana cewa "ehmmm Bari na gyara kitchen din yayi datti"tana mikewa tsaye.

Wani kololon bakinciki ne yaji ya tokaremai makoshi,Dan haka yayi banza da ita,Kan gado ya koma yayi kwanciyar shi Yana jin wani irin abu Yana yimai yawo a kanshi da kafafunshi.
Da sauri ta fita ta nufi kitchen tana sauke ajiyar zuciya.


Shiko A S P Habib wayar shi ya lalubo Yana Kiran wata nomber.bugu daya aka daga cikin mutuwar jiki ya ce "sweet kina Ina e?"banji me akace a dayan bangaran ba naji ya Kara cewa "mu hadu inda muka Saba haduwa yanzu,Kuma kinsan bana San Bata lokaci"kawai ya katse wayar.key din motar shi ya Zara sai wayar shi daya,dayar ya barta ana.ta kofar baya ya wuce saboda baya so ta ganshi a samu matsala bazai iya daurewa ba,Dan ji yake komai na iya faruwa.












✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*



👏👏👏👏.
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️


*Short story*

*true life story*

*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*




*MARUBUCIYAR* 📚🖋️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW*

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*


_Na sadaukar da wannan_ _book gareka_ _OGA SALISU KD_ _sakamakon sankamomin_ _data_ _da_ _kayi ngd Allah yabar_ _zuminci 🤝,Fns dina_ _suna gdy a gareka_ .🤣🤣 _suma sun shaida_ _kaunar dake tsakaninmu_ 💃💃💃💃.


*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*


*DA SUNA ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN KAI* .


PAGE3️⃣➡️4️⃣


📝A Kan hanya ya tsaya,shawarma da kayan malakushe ya siyawa su Arfat a wani wurin siyar da abinci
in ya nufi gidan.


Yarinyar ta dade tana bacci kafin a hankali ta fara kokarin motsawa.wadda aka kawo domin kula da ita ta lura da yadda yatsun hannunta suke motsawa.da sauri tamike tana matsawa jikin gadon.tari ta farayi babu sassautawa sosai take tari kamar mai cutar acma,ganin haka yasa ta fita Kiran doctor.kusan a tattare suka shigo da doctor.dubata ya farayi kafin yayimata allura ta koma bacci.


A Falo ya taddasu ita da yaran tanayimasu tilawar islamiyya.suna ganinshi yaran duk suka taso suna yimai sannu da zuwa,cikin farinciki yake amsa tare da tambayar sunyi salla amsawa sukayi da eh kafin ya Basu tsarabar daya kawomasu.cike da murna sukayi godiya suna komawa wurin zaman su.duk abinda sukeyi akan idanun zulaihat Amma Bata tankasu ba tana faman aikin Danna wayarta tanayi tana taunar cingom tasha kwalliya tayi Dora daurin dankwali n ture kaga tsiwa.

Dakinshi ya wuce Dan gabatar da salla kafin ya koma asibitin.


Sai bayan ya idar da sallah Yana lazimi ta shigo dakin,a bakin gadon ta zauna har ya mike daga wurin.jikin weardrop din ya matsa wasu kananun kaya masu taushi ya dauko ya dauko.toilet ya koma ya canza kayanshi.ya Kara feshe jikinshi da turare mai sanyin kanshi.
Wayoyinshi ya dauka Yana kokarin fita tayi saurin tare gabanshi tana huci.

"Haba Dan Allah Wai ni Meka mayar da nine,tun shekaran jiya kake yiman fushi,kaki kayi hakuri akan abinda ya riga ya wuce"tana tsareshi da idanunta.


Sosai ta bashi dariya,ita dai haka Allah yayita da *ZAFIN KISHI* ,sai tayi ta wulakanci Amma data ga dare yayi zai fita duk sai ta tayar da hankalinta.


Dan kawar da kanshi yayi ya ce "ki bani hanya in wuce"

"Wallahi bazan matsaba kaje gurin wannan Yan iskan yan"matan naka"tana Kara tare bakin hanyar.


Cikin kaushin murya yace "sai naje inda za'a bani abinda nake so tunda ke Baki iyawa da ni"cewar A s p Habib Yana kokarin tureta.

Rungumeshi tayi tana rushewa da kuka.

Dole tasashi tsayawa Yana sauraren kukan nata,dukda Yana jin kukan nata har cikin kahon zuciyar shi.Amma dole ya daure Dan ya nunamata kuskurenta.


A hankali ta fara rage sautin kukan ta,har tayi shiru sai ajiyar zuciya da take faman saukewa.
Kara rungumeta yayi suka zauna a bakin gadon.


A hankali ta fara bashi hakuri,duk Yana jinta yayi shiru bai tankaba sai can ya ce "yanzu kin shirya bani hakkina Kona tafi inda za'a shayar da ni fariciki"Yana Kara laluben bayanta itakuwa kanta Yana bisa kirjinshi.


Da sauri ta rufe mai baki da tafin hannunta,Dan ita duk duniya ta tsani ko a mafarki taga mijinta da wata barentana a zahiri to zata iya kashe koma wacece.

Tunda ya ji tayi lamo to yasan abinda take tinanin,Dan haka yayi kokarin tashi ta Kara rikeshi.a can kasan makoshinta ta furta na amince.sosai yaji dadi a ranshi Dan koba komai yau dai zai fanshe tsawon kwanakin data dauka tana gwarashi kamar wani karamin yaro.da haka dai ta lallaba shi har ya hakura da batun fitar da zaiyi.bayan sun gabatar da sallar isha'i abinci ta kawo masu suka ci dukda haka Yana faman Shan kanshi shi adole fishi yakeyi da ita.yaji dadi a wannan ranar domin kuwa ya more kasancewar da yardarta komai ya faru shiyasa ya ji ya gamsu.sosai yayita saka mata albarka.sai wurin karfe ukku kafin suka kimtsa suka kara komawa bacci.












✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*




👏👏👏👏👏👏
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️


*Short story*


*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* 📚🖋️


🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️ 🗡️

_______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*

```GODYA NAKEYI```

_Aunty safiyya_
_Aunty saudat_
_khady m ishak_
_siyada Umar_
_zule_
_Ummu A/jabbar_

*Dama sauran Wanda ban* *ambata ba* 😂😂🤣 *aradu kuna raina San* *so fisabilillahi* 🤝🌹🌷

*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*


*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .



PAGE7️⃣➡️8️⃣


📝Yana fita daga gidan ta jiyo Karan tashin motar shi,da sauri ta fito daga kitchen da ludayi a hannunta Amma Ina sai kurar shi ta gani,anan ta yada ludayin ta juya cikin gidan da gudu.dakin shi ta nufa Amma gani tayi wayam babu shi Babu alamar shi sai wayar shi daya akan gado.dauka tayi tana huci ta saka wancan nomber tashi ta fara Kiran shi tana ta ringing Amma yaki yin picking.a karshema switch off dinta yayi gaba daya ya aje Yana ta faman tsula gudu.tana Kara Kira taji a kashe kawai ta dora hannunta a kanta ta fara rusa kuka.sosai take kuka duk tayi wujiga-wujiga ta fita hayyacinta,ji takeyi Daman tasan inda ya nufa ta bishi da ba abinda zai hana ta kashe ko wace Yar iska ce ya tafi gurinta da yammacin nan.



Shiko tunda yasa kai bai tsaya ko inaba saida yaje unguwar kawo.A wani Dan matsakaicin gida yayi horn wani Dan matsakaicin saurayi ne ya leko ganin mai gidan ne yasa da sauri ya koma ya wangale mai gate din ya kunno hancin motar shi cikin gidan.da sauri ya nufi cikin gidan saboda sauri kamar zai kifa kasa.yana wuce Dan karamin falon da ba komai a cikin shi sai tiels a shimfide sai labulaye masu kyau da wani Dan karamin kafet a tsakiyar falon,wani bed room ya bude a konce ya hangota tana faman danne wayar ta.yana zuwa jikinta ya shige Yana sinsinarta kamar wani Dan akuya.ba laifi itama kyakkyawa ce Amma Bata kai zulaihat hasken fata da diri ba.ba tare da bata lokaci ba suka fara aikata abinda ya kawo su wurin.(Allah kasa mufi karfin zukatan mu).




Ita ko zulaihat tana nan inda take tana faman aikin kuka ko yara Bata san driver ya dauko su daga islamiyya ba,sai yarinyar da take kula da su ta saka sukayi salla ta Basu abinci suka ci ta kunna masu kallo a Falo.




A S P Habib sai karfe takwas ya kyale yarinyar shi,bayan ya kimtsa sallah yayi itako yarinyar Bata da niyyar yi,wayar shi ya dauko a Mota yayi mata alart na 50k kafin ya yimata sallama ya nufi hanyar gidan shi kafin itama ta wuce gidan su.

Tun a hanya yake zilimin yadda zasu Kare da zulaihat Dan yasan yau ba zasu yi bacci ba saboda bala'in ta,gashi ya manta bai koma gidan su yarinyar nan ba Dan kara duba lafiyar ta.da wannan tinanin ya karaso gidan shi dake cikin rigasa Yana horn aka bude mai ya shiga ciki.zulaihat tana jin tsayiwar Motar shi ta tashi tana jiran shigowar shi.yaranshi ya taras a Falo suna kallo anan yadan zauna Yana yimasu wasa yarinyar dake yimata aiki mai suna sakina cikin ladabi ta gaishe da shi,amsawa yayi Yana karemata kallo kafin ya nufi dakin nashi Dan yasan sarkin masifar tana nan tana jiran shi.


A tsaye ya isketa ta kama kugu,Yana shigowa yayi kamar bai ganta ba gaban shi Tasha tana hucin masifa ta ce "Wai Habib Meka dauke ni ne mahaukaciyar ko me?"


Da sauri ya kalleta ganin yadda ta tsareshi kamar wani tsaranta.cikin fushi ya ce "Duk yadda kika dauki kanki,to Nima haka na dauke ki,kina abu kaman wata jahila katsani ki bani wuri Kona Zane ki yanzun nan"Yana kokarin tureta.

Rikeshi tayi tana Kara karfin kukanta ba tare data Kara cewa komai ba kyaleta yayi saida ta gaji dan kanta kafin ta sake shi tana wucewa zuwa tiolet din cin dakin.da kallo ya bita Dan harga Allah Yana bala'in san zulaihat Amma kwata-kwata tana da dabi'u marassa kyau musamman *ZAFIN* *KISHIN* ta yayi yawa saboda duk lokacin da yayi yunkurin Kara aure sauta lalata al'amarin kafin daga baya tazo tana gwarashi,Kuma Bata kulashi yadda ya kamata....Karan wayar shi ne da yaji yasa ya dakata da tinanin da yake yi.yana received call din yaga ta fito daga toilet tana goge fuskarta alamar wanka tayi.

Da mamarshi yake waya cikin ladabi yake gaishe da ita, kafin take tambayar shi ko lafiya yau taga bai zo ganinta ba.hakuri ya bata akan uzuri ne yayi mai yawa,Amma gobe insha Allah zai shigo da safe kafin ya wuce office.da haka sukayi sallama ya aje wayar.


Kallanta yayi ganin tana sallah yasa ya mike, kitchen ya nufa.abinci ya zubo a plate da coc guda daya sai ruwan paro guda daya.a kasan kafet din jikin gadon ya zauna Yana ci harta idar da sallah ,duk Yana kallanta kafin ta fita.yabi bayanta da kallo.


Yaran ta iske a Falo ta tambaya sunci abincin Suka amsa da "eh munci"
"To ku muje ku kwanta da wuri saboda zuwa islamiyya"dakyar muryarta take fita saboda masifar kukan da tasha.sai Ahmed yake cewa "Ummah meya sameki muryarki take haka?"

"Kai ku muje ku kwanta kunji ko,mura ce take damuna shiyasa"tana jansu zuwa dakinsu.yarinyar ta gyara masu gadon kafin ta canza masu Kaya suka konta,dayan gadon Kuma Khadija ce da wannan Yar aikin .



A hankali ta turo kofar tana sadda Kai kamar wata munafika.yana kallanta ta kasan idonshi ya kyaleta Yana ci gaba da duba system din shi.a kusa da shi ta zauna tana kallanshi Dan ta rasa ta Ina zata fara yimai magana.



A fannin gidan su habiba kuwa lokacin da malam ya dawo daga wurin sana'ar kayan miyanshi,ya riski ta dawo yayi farinciki Dan ita kadaice Diyar da Allah ya bashi,Amma Mamanta ta rasu daga baya ya auro innaji wadda yana ji Yana gani take cutar da ita Amma ba yadda zaiyi dan shi kanshi zaman hakuri yake yi da ita.



Zulaihat ganin Ahmed yayi banza da ita yasa ta saka mai kuka.dariya ta kusan bashi ganin tana neman raina mai da hankali,dazu ya nemeta ta mai wulakanci yanzu Kuma tazo tana yimai kuka dan taga ya fita.

Kasan guyoyinta ta durkusa cikin kuka ta ce "Dan Allah kayi hakuri karka yiman kishiya,wallahi na tsaneta,Kuma Dan Allah karka bi matan waje insha Allah zanyi kokarin gyarawa bazan Kara guje maka ba"tana faman goge hawaye fuskar ta.

A hankali yadan dubeta ganin duk yadda ta fice daga hayyacinta,Amma sai yayi fiska Dan shi Yanzu zam yake jinshi taje ta rike kayanta baya so.

Kukan taci gaba da yi duk Yana jinta,domin Daman ta Saba yimai haka sai tayi abu tazo tana damunshi da kuka,daya hakura to Bata dadewa zata Kara maimaita irin laifin Dan haka yake kyaleta,shidai Yana ta addu'ar Allah yasa ya daina wannan mummunar dabi'ar ta bin mata,ita kadai ke daminshi wannan ma duk itace sanadin saka shi a ciki saboda San zuciya irin nata.

Rufe system din yayi ya mayar da ita,kayanshi ya canza zuwa na bacci Dan yaga har karfe goma ta gota.kan gadon ya haye yayi konciyar shi ya barta anan,gajiya tayi da kukan itama ta konta a bayanshi tana sauke ajiyar zuciya,Amma zuciyar ta cike falla da kishin inda yaje.

Bai cemata komai ba da haka har bacci ya dauke shi,ita ko indonta biyu tana ta faman saka da warwara a zuciyarta,kafin itama bacci ya dauketa ba tare data sani ba.




*Tofa koya zata Kaya muje zuwa* *fns* 😂





✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*





👏👏👏👏.
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️


*Short story*

*True life story*

*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*MARUBUCIYAR* 📚🖋️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW*

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

______________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*



*_Ya Allah ka jikan_* *_mahifina,ya Allah ka_* *_gafarta masa_* *_kurakurensa,ya Allah_ _ka_* *_kai haske__* *_kabarinsa,ya Allah_ _jikan_* *_dukkan_ _musulmi_* *_da_ _suka___ _rigamu gidan_* *_gaskiya,idan_ _lokacin_* *_mutuwar mu_* *_yayi_ _kasa_ _mu_ _cika_* *_da_ _Imani_ _da_ _kalmar_* *_shahada_* .


*GODIYA*
*Godiya ta tabbata* *ga* *Allah subahanahu* *wata'ala* ,
*tsira da amincin su* *tabbata ga cikamakin* *Annabawa,wato* *shugaban mu Annabi* *Muhammad (S A* *W),Allah ya Kara aminci* a *gare shi,tare* *da alayensa da* *sahabban sa* .


*SADAUKARWA*
_Na sadaukar da wannan_ _book_ ga _daukacin fns dina,ngd_ _da soyayyar ku gare ni,Allah_ _yabar zuminci 🤝,San so_ _fisabilillahi_ 🤣.


*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*


*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .


PAGE 1️⃣➡️2️⃣


Irin gudun da yake shararawa a saman titi shi zai tabbatar maka da cikin gaggawa yake,horn kawai yake faman dannawa ba kakkautawa,da sauri ya dafe kanshi Yana zaro manyan idanuwan shi.cikin zafin nama ya fara kokarin take birgi,Amma Ina aikin gama ya riga ya gama,da kyar ya samu motar ta tsaya,cikin fargaba da tsinkewar zuciya ya bude gambun motar ya fito,a hankali ya fara takowa inda yarinyar take yashe a kasa.daidai lokacin wasu samari da akan idon su al'amarin ya faru suka taso da sauri dan ganin meke faruwa.
A tare suka iso wurin yarinyar.Dan Allah ku taimaka min masaka ta a Mota,tana bukatar taimakon gaggawa Dan inaga kamar ta suma.cewar A s p Habib Ahmed Yana janye hannunta daga Kan cikinta.Ba tare da bata lokaci ba suka sakata a Bayan motar shi, inda daya daga cikin matsan ya shiga saboda taimakon hakan da A s p ya nema.cikin ikon Allah suka isa wani prabet hospital da ke cikin unguwar ta rigasa.da sauri aka amshe su,akan wellchairs aka shiga da ita emergency room.likitoci ne Suka rufu a kanta suna kokarin ceto rayuwar ta.

A bakin kofa yake ya kasa zama sai kaiwa da kawowa yake yi.yana addu'ar Allah yasa yarinyar ta farfado.karan wayar shi ya dawo da hankalin shi,hannun shi ya zura cikin ajjihun rigar yadin cufta dake jikin shi, screen din wayar yake kallo gaban shi yaji ya bada wani irin sauti mai wuyar farrasawa,hannun shi Yana karkarwa ya mayar da wayar cikin ajjihu Yana sauke ajiyar zuciya mai zafi.

A hankali ya zauna tare da dafe kumatun shi da hannuwan shi.tinani take yi a zuciyar shi irin kaddarar da take Kara tinkaro rayuwar shi.jin an dafa kafadar shi yasa ya dago jajayen idanuwan shi da sukayi kamar garwashi saboda tsabar tashin hankalin da yake hangowa.

Mikewa yayi ganin likitan Yana murmushi,hannun shi ya ruko cikin sanyin shi ya fara motsa labban shi da suka bushe saboda tsabar kaduwa ya fara cewa "Allah yasa ta farfado"Yana kallon koyar idon Doctor din.


"Ka kontar da hankalinka"cewar Doctor Yana Jan hannun shi zuwa office din shi.
Bayan sun zauna Doctor yakai duban shi Kan A S P Habib Ahmed Yana cire siririn farin galass din dake manne akan fuskar shi.
"Alhamdlillah munyi nasarar shawo Kan matsalar,Amma dole tana bukatar wani a kusa da ita saboda idan ta farka zata iya bukatar wani abun "Yana rubutu a jikin wata paper "Anshi wannan ka samo mata wadannan maganin kafin Karin ruwan ya Kare,Kuma sai kayi payment na kudaden.yana Mika mai hannu alamar sallama.bayan sunyi musabaha ya mike Yana fita daga office din.


A zaune ya tadda wannan matashin da suka taho tare,shiya taimaka mai suka yi clearing na komai kafin suka shiga dakin.

A bisa wani Dan karamin table ya aje kayan da suka shigo da su kafin ya nufi jikin gadon da yarinyar take konce.Kuramata ido yayi sosai ganin yadda take kama da little sister dinshi,har yanayin jikin nasu iri daya.

A hankali yakai hannun shi Yana goge mata zufar data tsatstsafo ta saman godinta.fita yayi zuciyar shi cike da damuwa.shima saurayin bin bayan shi yayi.a bakin motar shi suka tsaya agogo ya duba ganin har ukku tayi yasa ya cewa saurayin "Dan Allah Bari inje gida zuwa anjima zan dawo" Yana dauko kudi a walet din shi."ga wannan ka rike a hannunka koda za'a bukaci wani abu kafin na dawo.saurayin ansa yayi Yana cewa to ranka dade.

Cikin motar ya shiga Yana fita daga asibitin.

A hankali yake tukin inda ya kunna kira'a Yana bi,ko yaji sanyi-sanyi a zuciyar shi,da haka ya isa gidan shi dake cikin rigasa.
Horn yayi mai gadi ya bude mai yana yimai sannu da dawowa.

A bayan yayi parking ya dau tsawon lokaci kafin ya bude kanbun motar Yana goge kanshi da hankechef,kafin ya doshi kofar da zata sada shi da cikin gidan.

Sai a lokacin na samu damar Kare mai kallo,dogone sambal,Dan shalaulayi baya da jiki ko kadan, sai doguwar fuskar shi mai dauke da Dan siririn hanci,manyan eyes gare shi Hakan yasa suka karawa doguwar fuskar shi kyau,balck beauti ne,domin kuwa ba fari bane,Amma bakin shi mai kyau ne.akalla a shekaru zai iya haura arba'in Amma saboda yanayin jikin shi zaka dauka bai Kai wannan shekarun ba.


Cikin sanyin da yaji ya mamaye kaf bargon jikin shi ya murda kofar falon da sallama dauke a bakin shi.dukda yasan ba mai amsa mai,hakan kuwa ta kasan ce dan wayam yaga falon Babu alamar motsin mutum a wurin.

Bedroom ya wuce Yana jin wani haushin matar tashi.a hankali ya fara kokarin cire kayan jikin shi,yaji an turo kofar dakin nashi,dakatawa yayi Yana kallon wurin.ganin ita ce yasa yayi saurin kawar da kanshi Yana karasa cire karamar rigar shi,ya rage daga shi boxer dan karamin wanda da kadan ya rufe cinyar shi.

Hanyar toilet ya nufa ba tare daya tankata ba.tana ganin haka tayi saurin bin Bayan shi tana cewa "Haba Abban Arfat bansan ka shigowa"tana Shan gaban shi.

Hanuwan shi yasaka Yana matsar da ita gefe daya.yana yimata wani irin kallo a zuciyar shi ya ce "Koda kin sani hakan baya da amfani,Dan Babu wani abu da zaki iya tsinana min sai dai ki tayar min da hankali.

Gaba yayi ba tare da ya jiraba,Yana shiga yaja kofar da karfi jikake bammm.yana jingina da jikin kofar.

Tana ganin haka ta yatsina Baki tana make kafada alamar ko a jikinta.jikin weardrop ta nufa tana zabo mai kayan da zai saka.tana ajewa ta fita daga dakin ta nufi nata sashen.


Shiko A S P Habib ya dade a haka kafin ya fara gabatar da wonkan shi cikin sanyin jiki.dan Yana so ya koma asibiti kafin yarinyar nan ta farka.



Bayan ya fito ya hangi kayan data ajiye mai,mayarwa yayi ya fito da wani needy blue din yadi mai taushi ya saka Yana Kara feshe jikin shi da turaren gold mai kanshi.ko hula bai tsaya

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On ZAFIN KISHI
avatar
abasu-kala

11 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment