Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna ta janshi da wasa yaki kulasu dole tasaka Suka kyaleshi a karshema sallama yayi masu ya wuce gida zuciyar shi da kolwar shi cike da tunani barkatai.


Zulaihat ko tana shiga cikin gidan ta sakama dakinta key tana kunce ledar data anso.kowanne da takadda a cikin shi hakan yasa bata Sha wahala ba wurin gane yadda zatayi amfani da kullin maganin sai wani rubutu a cikin Yar karamar jarka.cikin sauri ta shanye rubutun tana Kiran sunan Habib,shiko maganin tayi amfani da shi yadda ta gani a rubuce kafin ta nufi falo dan jin hayaniyar yaranta sun dawo daga Islamiyya.daidai ta fito wurin yaran shima Habib ya dawo,Dan haka yace a canza masu Kaya sau suyi alwala ya wuce da su masallaci saboda an kusa fara Kiran sallar magriba,kafin shima ya wuce dakin shi danyin alwala saboda wata faduwar gaba da yaji da sauri da sauri.Binshi tayi da kallo ganin yadda ya wuce ba tare daya kalli inda take ba,kamar baisan da ita a wurin ba.cikin jin haushi itama ta wuce nata dakin a zuciyarta tana cewa "Anyakuwa Abban Arfat lafiyan shi kalau?kama wani abu Yana damunshi,Amma koma meye nasan baya rasa basaba da maganar da Malam ya sanarmin ta auren nan,bazai yiwu na tayar da hankalina ba tunda malam ya tabbatar min da Babu wannan maganar dolen shi zai rabu da ita.yanzu next target dina wannan shegiyar karuwar ce IHSAN ga dukkan alamu zata bani wahala kafin na rabata da mijina,Amma ya zama dole na jure duk wata gwagwarmaya dan ganin na rayu da mijina ni kadai ba tare da wata ta shiga tsakanina da shi ba.da wannan tunanin ta dauro alwala.bayan ta idar da sallah kitchen ta Kara komawa dan hadamashi kayan denner kafin su dawo.


Shiko Habib tunda sukaje masallaci bayan sun idar anan sukayi ta bitar karatu shida yaran shi Ahmed da Arfat har aka yi sallah isha'i kafin suka nufo gida.akan hanyama Yana ta Kara yiwa yaranshi nasiha akan su dage da karatu,Yana ta nuna masu amfanin ilimi da hasken dake cikinsa.


A gidan su Habiba kuwa tunda tayi sallar isha'i take rakube adan karamin dakinta Wanda ba komai a cikinsa sai wata Yar karamar katifa da bargonta Wanda yake fes dashi babu alamun datti,Dan Habiba akwai tsafta.ko leda babu a tsakar dakin sai labule da gana masgo ta kayanta da sauran Yan tarkacen ta a gefen katifar.sosai tayi zurfi a tunanin Innarta da yadda tayi rayuwa da ita cikin farinciki,Amma yanzu duk ta zama abin tausayi,abincima sai anga dama ake bata.tana cikin wannan tinanin taji muryar Malam Yana kwala Kiran sunanta.cikin sanyi ta amsa tana mikewa tare da linke abin sallar,bisa katifa ta dorashi kafin ta fita.
A kofar dakinshi yake zaune bisa tabarmar kaflba wacce akayi zanenta da ratsin dark blue mai kyau,sai kwanon tuwo a gabanshi da kofin ruwa.
A gefen shi ta zauna tana cewa "sannu da zuwa Babana abin alfahari na"tana kallon yadda yake yimata murmushi,Dan harga Allah tasan mahaifinta Yana kaunarta kullun burinshi ya sakata cikin farinciki.
"Yauwa Daiyar albarka,kinci abincin ki ko?"
Cikin jin dadi ta amsa da "A a Baba zanci sai anjima,yanzu inaso na linke kayan dana wanke Mana dazu"tana kokarin mikewa.
"A a Habiba zauna ki ci kafin kiyi aikin kin ji ko"
"Bata yiwa Babanta misu Dan haka ta wanke hannunta tana saka shi a cikin kwanon tuwon daya aje gabanta.
Sosai ta ci Dan daman duk yau rabonta da abinci tun da safe,shima kafin ya fita wurin siyar da kayan Miyan shi ya tsareta saida taci koko da kosai kafin ya fita.

Tana idarwa Innajo ta fito daga daki,Dan duk abinda sukeyi tana jinsu saboda ta kabbara sallah.tana Allah Allah ta karasa ta fito.
A jikin kofar dakin ta tsaya rike da kugu tana girgiza kaman wata karamar yarinya.cikin iya masifa tana kumfar baki ta fara ruwan bala'i "yanzu fisabilillahi malam abinda kake yiman a cikin gidan nan kana kyautawa,ace kullun na kawoma abinci saika tisata a gaba ka bata taci,yanzu idan mutane Suka gani sai suce bana bata abincin kirki ko?to wallahi ni bazan lamunta da wannan cin zarafin ba"haka tayi ta fadan ta.shiko malam shiru ma magana ce inji mai hankali.hakan da yayi ya Kara kular da Innajo Dan haka tayi ta masifa tana kumfar baki,itako Habiba dakinta ta shige tana addu'ar Allah ya kareta daga sharrin wannan mata.

Habib suna shigowa anan falo yabar yaran da nafisa tana kawomasu abinci,ya shige dakinshi dan duk jinshi yake yi wani iri jikinshi duk yayi sanyi.wanka ya karashi ya canza kaya zuwa jallabiya marar nauyi ya dauko system dinshi Yana dubawa saboda suna da wani kest da yake tunanin zuwa ranar Monday zasu Mika shi zuwa kotu Dan yanke masu hukunci.

Cikin sauri take gabatar da shirinta,saida ta kammala kakale-kakalenta kafin ta dauko wasu sleeping dress masu taushi da kyau pink color ta saka sosai suka anshi skin dinta tayi ras gwanin kyau.dogon hijaf ta Dora akan kayan kafin ta fito.jin falon tsit yasa ta fahimci yaran duk sun konta dan haka darect ta tura kofar dakin kafin can kasan makoshi tayi sallama.
Ba tare daya dago kanshi ba daga aikin da yake yi ya amsa mata.cire hijaf din tayi ta ajeta a bisa wata yar kujera kafin ta zauna kusa da shi.
Cikin kunnenshi ya ji tana cewa "sweety sannu da aiki"
"Yauwa"kwai ya ce Yana ci gaba da aikin shi.
Sun Jima a haka,Dan harta fara gajiya ga bacci tana ji kafin taga ya rufe system din Yana mayar da ita.fita tayi ta kawo mai abinci.
Har zuwa wannan lokacin bai tankata ba ya zauna.cikin yin Bismillah ya fara cin abincin tuwon semo ne miyar agushi da naman rago,Dan haka ya zage ya kwashi girki.kafin ya wanko hannunshi tare da Kara yin brosh.

Konciyar shi yayi Yana danne-dannen waya,da haka ta mayar da kwanikan ta dawo.kunya duk taji ta kamata ganin yadda yayi biris da ita.dan haka ta Kara matsawa jikinshi har suna jiyo numfashin junan su,duk Yana jinta Dan haka cikin salon iya barinki shi ya dago kanshi Yana cewa "Ince dai lafiya ko?ko kina bukatar wani abu ne?Yana kallon kwayar idonta,Dan shi yayi alkawarin zai rinka nesa da ita saboda ya fahimci tunda taga Yana yawan nemanta shiyasa take wani jan aji.
Sosai taji haushi ya kamata dan haka tayi kaman bata ji me yace ba.ta jima a haka kafin ta matsa gefe tana gyara konciyar ta.shima kyaleta yayi yana ci gaba da yin chat dinshi.





✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*




👏👏👏👏👏👏.
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*

*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* 📚🖊️


🤦 *ZAMANINMU* 🤦

*AND* *NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*


*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*


*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI* *JIN* *KAI* .


PAGE1️⃣5️⃣➡️1️⃣6️⃣


📝A hankali ya fara motsa labban shi,cikin sanyin jiki ya ce "Baba Amma kasan........"cikin sauri malam ya dakatar da shi ta hanyar cewa "kayi hakuri Habibu nasan abinda zaka fadaman duk na jiyoshi a gurin mutane,nasan bazai wuce matsalar matarka ba,to kasaka a ranka insha Allah ba abinda zai faru sai abinda Allah ne ya kaddara.koda can da baka Kara aure ba Allah ne bai kaddara ba,Dan haka abinda nake so ka kontar da hankalin ka sannan ka dage da Addu'ar Allah ya karemu daga dukkannin fitina"cewar malam Yana goge kollar datake silalowa daga fuskar shi.

Cikin yin kasa da murya Habib ya ce "kabani lokaci zanje na sanar da mahaifiya ta,zamu tattauna da ita insha Allah zanyima bayanin duk yadda mukayi da ita"

"To maddalla Habibu Allah ya jishemu alkhairi"daga haka sukayi sallama ya nufi gida.

malam Yana shiga ya tarad da Habiba tana Jan ruwa a rijiyar tsakar gidan baice komai ba ganin Innajo a gurin,sai kawai ya shige dakin shi.
Itama Habiba batace komai ba taci gaba da Jan ruwanta,dukda tasan Malam bayasan irin wannan ayyukan wahalar da Innajo take sakata,shima Dan ba yadda zaiyine tafishi iya masifa.

Zulaihat ko tun bayan tafiyar su masallaci ta dauko wayar ta bayan gidan ta nufa inda tabar Yar aikinta Nafisa a kitchen.

Cikin kasa da murya kamar mai yin rada naji tana cewa "malam nifa kasan damuwata kabar maganar kudi konawa ne zan biya,nidai burina kada wacce ta shigo min gidan miji,Dan wallahi na tsani kishiya a rayuwata,gwamma ace mutuwa ce nayi da in bude idona inga Habib da wata mace bayan ni"tana yarfa hannunwanta alamar ranta ya baci.
Banji me akace ba a dayan bangaran naji dai ta amsa da "to ba damuwa zuwa gobe ka karasa aikin sai kaba yaronka tunda yasan gidan ya kawomin,idan yazo kofar gidan saiya yiman text Dana gani zan fito"tana waige-waige Kamar marar gaskiya.

A karon karshe ta Kara cewa "to ai nasan indai akwai irinku to bazamiyi kuka ba ngd saika jini"tana katse kiran.

Tana karyo kwanar da zata sadata da hanyar falon taga mai gadi ya bude gata.tsayawa tayi dan ganin motar mai gidan nata tana shigowa,a zuciyar ta tace Allah kasa Nafisa tayi wasu ayyukan.


Shiko Habib Cikin mutuwar jiki da fargaba ya fito daga motar wayoyin shi kawai ya dauka ya rufe motar.ganin ya dosota a wannan yanayin taji gabanta ya buga da karfi,hakan yasaka ta nufo shi tana tambayar "Lafiya Habibina duk na ganka wani iri,Ina yaran ne?"tana kokarin kamo Hannun shi.
Dan lumshe idon shi yayi kafin ya fitar da iska mai zafi,Dan shifa harga Allah zuciyar shi da kolwar shi sun cinkushe da yawa."A a nothing karki damu ba komai na gaji ne, gashi ankusa Kiran sallah yanzu ki saka drever ya dauko su Khadija daga gidan Mama,ni Ina Dan bukatar na huta ne"daidai sun shigo falon.
Da "to"ta amsa tana rakashi dakin saida ta tabbatar ya shiga toilet kafin ta fito.
Wurin drever ta sanar mai kafin ta koma kitchen taci gaba da aiki.

Tunda ya shige toilet ya kasa yin alwala sai aikin tunani,dakyar ya daure yayi kafin ya fito.anan ya shimfida prayermate ya tayar da sallah.harya idar zulaihat bata Kara shigowa ba dan haka ya jingina jikin bango Yana tunanin Anya zai iya amsa bukatar malam?danya fahimci Habiba yarinya ce sosai,idan har ya kawota gidan nan to ba makawa Wataran saidai ya dauki gawarta,Dan yasan *ZAFIN KISHIN* zulaihat a kanshi komai Yana iya faruwa idan taga ya auro yarinya.dukda yasan Ihsan ita kadaice zata iya gogawa da zulaihat Amma bazai iya auren Ihsan ba.yana wannan tunanin ta shigo ba tare daya sani ba.kayan abincin data shigo dasu ta aje kafin ta tsuguna a gabanshi,cikin damuwa ta kamo hannun shi tana cewa "ni nasan akwai abinda yake damunka,Amma bakasan sanar min saboda banida matsayi a gurinka ko?"

Baice komai ba sai girgizamata Kai yayi alamar ba hakane ba.

Itama bata tanka ba sai fita tayi daga dakin ta nufi nata,a zuciyarta tana cewa "nasan maganar Karin aure ne,tunda malam ya sanar da ni to duk hanyar da zanbi Dan ganin auren nan bai faruba to saina bi".

Shiko Habib binta yayi da kallo harta fice.kafin ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa "Bazan iya sanar dake ba,Mama kadai zan sanarwa Dan ganin inda zan samu mafita"Yana a haka akayi kiran sallar isha'i ya gabatar da ita,ko abincin data ajemai bai bi ta kanshi ba yayi Shirin bacci ya konta Yana duba message din da Ihsan ta turo mai da shi tun dazu.bayan ya gama karantawa yayi shiru Yana tunanin irin gargadin da take yimai akan maganar auren to abin mamakin anan shi ne "itama Ihsan a Ina tasan yana Shirin Kara aure?kamar wadda take ganin abinda yake yi?Yana wannan tunanin har karfe 10 ta wuce bai sani ba.ganin da gaske zulaihat bazata shigo ba shima yayi konciyar shi ya kyaleta.

Zulaihat ko haushi ne yasa tunda ta tabbatar yaranta sunci abinci.ta rasa su dakin su bayan sunyi addu'ar konciyar bacci,itama ta shige dakinta.ta Dade tana waya da wata freind dinta akan matsalar kafin daga bisani sukayi sallama ,kafin ta buga tagumi tana tunanin yadda zata bullowa lamarin.Har karfe daya saura tana aikin tunani saida taji ta fara gyangyadi sannan ta konta zuciyarta cike da tunani.










✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*



👏👏👏👏👏👏.
[4/2, 6:17 AM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*

*true life story*

*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS* *BALAH*
*(AUTAH)*

*MARUBUCIYAR* 📚🖊️

🤦 *ZAMANINMU* 🤦

*AND NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*


*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*


*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN KAI* .


PAGE1️⃣7️⃣➡️1️⃣8️⃣


*WASHE GARI*


📝Washe gari haka masu gidan Suka kasance tunda ya dawo daga sallar asuba yayi konciyar shi.
Itako zulaihat shirya yara sukayi da kayan break ita da Nafisa .saida taga drever ya tafi da su tahafiz kafin ta nufi wanka,cikin doguwar rigar atamfa ta shirya green color mai ratsin read a jikinta.kwalliya tayi sosai kafin ta feshe jikinta da turare,ta dora daurin daukwalin da yayi das a kanta kallon kanta ta Kara yi a jikin mirro, gaskiya ita kanta tasan tayi masifar kyau Dan haka kayan abincin ta jera saman dinning area.kafin ta nufi dakin shi.


A hankali ta murda kofar dakin jinta abude yasa ta kutsa kanta ciki da sallama dauke a bakinta.shiru taji dakin sai Karan fanka dake shillawa.bakin gadon ta nufa ganin baya Kan gadon yasa ta nufi hanyar toilet.zata bude kofar sai taji Karan ruwa alamar wanka yake yi.komawa tayi ta fara gyran gadon da goge-goge.kaman daga sama ta fara jin vabration din waya a kasan filo.hannu ta saka ta lalubota Kan screen din take kallo Dan ganin sunan mai kiran.ware idonta ta Kara yi ganin an rubuta IHSAN da manyan baki.to ita dai tasan kaf familyn su Habib Babu mai wannan sunan.to idan ko haka ne kenan budurwar shi ce.tana wannan tunanin har wayar ta katse bata sani ba.cikin sauri ta fara duba nomber tayi sa'a kuwa wayar ba security akanta.wani biro ta hango saman mirro da sauri ta dauko shi.gani nayi ta daga cinyarta a jiki ta yi copyn nomber kafin ta dora wayar Kan site drower tana ci gaba da aikinta.Amma fukarta ta sauya alamar abin ya taba zuciyarta.

Jin motsi a bayanta yasa ta tabbatar ya fito.ba tare data waigoba ta ce "Ana Kiran wayanka".

Da sauri ya goge kanshi da karamin towel din kafin ya nufi inda wayar take.dauka yayi Yana dubawa ganin sunan IHSAN yasa yaji jikin shi yayi sanyi.kallon inda take aiki yayi ganin bata kallo shi ba sai yayi tunanin data ji ringing din bata duba ba.dan haka shima yayi fuska.

Tana gama aikin ta nufi jikin weardrop tana ciro mai kayan da zai saka.saida ta tabbatar ta gama gyaran komai kafin cikin sanyin jiki ta ce "idan ka karasa shiryawa abincinka Yana danning"bata jira amsar shi ba ta nufi hanyar fita tana murguda kugu.shiko kaman wani soko haka ya bita da kallo.

Tana fita ya sauke ajiyar zuciya Yana danna Kiran IHSAN.tana fara ringing ta daga.shiko cikin masifa ya fara cewa "Ihsan are you a mad?kinsan me kike Shirin jawomin ne?yaufa weekend ne Amma kike kirana a irin wannan lokacin?"

IHSAN ta kawo wuya gurin kulewa aiko cikin jin haushi da masifa ta ce "Nasan abinda zan janyomaka mana,kana gudun masifar matarka ko? saboda ta mallake ka sai abinda tace maka ko?to ka gayamata nace wallahi sainayi maganin *ZAFIN KISHIN* ta sai kace dan ita kadai aka hallicce ka"

Jin zata Kara Bata mai rai yasa ya katse kiran mtssssss Yana Jan tsaki.

Shiryawa yayi ya fita danyin break.

Itako IHSAN a lokacin tana cikin freind dinta.tana jin ya katse call din ta dauko wani uban ashar ta dora tana cewa "lallai Habib ni zaka katsema Kira saboda kasan ka gama da ni ko,to zan nunamaka ta sanadinka na fara harkar bariki,wallahi sai kayi Dana sanin sanina dakai da matsiyaciyar matar ka.daya daga cikin kawayen ta mai suna Hannatu ta kalleta tana aje wayar hannunta ta ce wallahi Ihsan ni kina bani mamaki ,yanzu ai an daina yayin fada ga duk wadda ta hana a auri mijinta,ta cikin ruwan sanyi zakiyi maganin su yadda koda ta kasa mijinta a kasuwa babu wadda zata kalleshi ballantana har tayi yunkurin auren shi.yanzu bariki ta koyar da mu yadda zamuyi maganin macen da take yin sihiri akan kada mijinta ya kara aure sai ita kadai zata zauna da shi.munyi alkawarin zamu barmata mijinta Amma sai mun............sai Kuma tayi shiru tana murmushin mugunta .rap rap rap dukan su suka hau tafawa suna ihu.

Sun Jima suna iface-ifacen su kafin sukayi shiru.ita ko Hannatu da hannu ta jinjina masu alamar ta gode ta shige wani daki tana tafe tana girgiza kugu saboda wandon dake jikinta da shi da babu duk daya ne.
Tana shigewa IHSAN tace shiyasa nake san Hannatu Dan kanta Yana kawo wuta da ideas.da sannu damuwata zata gushe burina zai cika na ganin na cusawa zulaihat bakincikin da har ta mutu Yana cin zuciyarta .
A tare sukayi shewa kafin kowa taci gaba da aikinta Dan sunsan zuwa dare Hannatu zata sanar da su yadda za'a gudanar da oppiration din.


Shiko Habib tunda ya gama break bai damu da rashin fitowar matar tashi ba,ya wuce gidan Mama.acan ya wuni Yana sanar da ita Alfarmar da Malam mahaifin Habiba ya nema a gunshi.cikin farin ciki Mama ta amince tana saka masu albarka.ganin ba yadda zaiyi shima saiya amince akan gobe lahadi zaije dan sanar da Malam cewar ya amince.

Daga haka yayi Mata sallama ya nufi majalissar su.


Zulaihat tana jin tashin motar shi daga gidan ta dauko wayar ta tasaka nomber IHSAN tayi saving akan phone din.nomber freind dinta ta Kira ta fara sanar Mata da abinda idonta ya gane mata.haka dai suka yi ta tatatuanawa yadda zasu kawar da Ihsan har saida taga text din yaron malam kafin sukayi sallama.Hijaf kawai ta saka sai kudin data dauka cikin Jakarta ta nufi hanyar gate.baba mai gadi Yana ganinta ya taso Hajiya ko wani abun kike bukata.
Cikin dakila ta ce "A a zan dan leka nan waje ne sako zan amsa"ta ficewar ta.
Shiko Baba mai gadi girgiza kanshi yayi Yana Addu'ar Allah ya shirya yasa ta gane abinda take aikatawa bazai fisheta ba.yana nan ta Kara wucewa bayan ta amso sakon ta nufi cikin gidan tana jin ranta Yana tafarfasa.








✍️✍️✍️✍️✍️✍️

*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*




👏👏👏👏👏👏.


[4/2, 11:24 PM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*

*true life story*

*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*


*MARUBUCIYAR* 📚🖊️


🤦 *ZAMANINMU* 🤦

*AND NOW* 👇


🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️


________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*



*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*



*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .



PAGE 2️⃣1️⃣➡️2️⃣2️⃣



📝Har wuraren karfe 11 idon shi biyu baiyi bacci ba,itako zulaihat zuwa wannan lokacin tayi nisa a cikin baccinta.kashe wayar yayi kafin ya kashe duk kayan wutar da suke a kunne.jikinta ya matsa Yana shinshinar kanshin humrar data shafa mai ratsa zuciya.kaman a mafalki taji ana tabata dan haka ta Kara mirginawa jikin shi ba tare da tasan tayi hakan ba.shiko sai ya Kara samun damar Kara shigewa jikinta,da haka dai shima baccin ya dauke shi.



Dan haka a washe garin lahadi sai wuraren karfe sha biyu bayan yayi break ya nufi gidan Mama.bayan sun gaisa yadan Jima suna tattaunawa kafin ya nufi gidan su Habiba.tunda yayi parking yake ta waigawa dan neman yaron da zai aika Kiran Habiba,Amma unguwar shiru ba yara.yana haka saiga Malam ya dawo a adaidaita sahu da kayan Miya a buhu Yana tsayawa Habib ya karasa kusa da shi Yana yimai sannu da zuwa.shiya sallami Dan adaidaita kafin ya dauki buhun kayan nashi suka nufi cikin gidan.a zaure ya tsaya shiko Malam ya karasa da kayan cikin gidan.jim kadan sai gashi ya fito da tabarma shimfidawa yayi Suka zauna.cikin kunya Habib suka gaisa da Malam cikin sanyin jiki ya fara da cewa "Am daman akan maganar da mukayi ne ba ..matsa....laa...na.... Amince..."Yana sauke ajiyar zuciya,Dan shi gaskiya yana jin tausayin yarinyar bayaso bayan ya aureta ta sanadin shi a cutar da ita,dukda Yana ta addu'ar Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakanin su.

Cikin nuna farin da jin dadi Malam ya ce "Amma Habibu na gode da wannan karamcin da kayiman nida marainiyar yarinyar nan,banida bakin da zanyima godiya sai dai nayimaka addu'ar Allah ya sakamaka da mafificin alkhairi,Allah ya Albarkaci rayuwar ku data iyalan ku"da murmushi dauke akan fuskar sa.
Sosai Habib yaji dadin addu'ar da sirikin nashi yayimai,Dan haka ya amsa da "Amin ya Allah,bakomai Baba Allah ya taimakemu,Kuma cikin satin nan zan turo a saka ranar,Dan banso a dau tsawon lokaci,gudun kar a samu matsala daga mai dakina saboda inaso na kaita wani karamin gidana dake a can cikin kawo"Yana Kara sadda kanshi alamun Yana jin kunya.

Malam cikin murmushin daya zame mai jiki ya amsa da "to maddalla hakan ma yayi,Allah yayi mana jagora"

"Amen ya Allah"cewar Habib.
Anan malam ya barshi Yana cewa "Bari na turomaka Habibar ku gaisa"ya shige cikin gidan.
Habib muskudawa yayi Yana gyara zaman shi tare da lumshe idanunshi.

A hankali ta shigo zauren cikin sando kaman marar gaskiya.kanshin turaren da yaji mai dadin kanshi yasa yayi saurin dako manyan eyes ball din shi.ganin ita ce yasa ya sauke ajiyar zuciya Yana kallon yadda ta rakube a gefe tana Kara rufe fuskarta da bakin hijaf din.

Cikin sanyi ta ce "Ina yini"

"Lafiya Lau"ya amsa mata a takaice.

Dukansu sukayi shiru kowa da abinda yake sakawa a zuciyar shi.da yaji shirun yayi yawa ya ce "Habiba kinyi karatu ne"

Dan kallon shi tayi tana kawar da kanta gefe daya,saboda ji tayi yayi Mata korjinin da bazata iya kallon cikin kwayar idon shi ba. Kamar bazata amsa ba sai can ta ce "nayi makaranta,Amma bakin J S C E ne"tana turo bakinta.

Ya jita sarai,Amma sai ya kyaleta a zuciyar shi yake cewa "Wai wannan Yar tsigigiyar yarinyar itama ta iya yanga kamar wata big girl"a fili yayi murmushi Wanda har saida hakoran shi suka bayyana kafin ya mike tsaye Yana cewa "zan wuce sai anjima ki shirya gobe kanwata zata zo kuje shagon dinki za'a gwada ki"yayi gaba.itama mikewa tayi tana cewa "To"Amma a zuciyarta mamaki take yi meye na wani aje a gwadata.juyawa tayi ta nufi cikin gidan da tabarma a hannunta.

Tunda ya shiga motar shi yake ganin Kiran IHSAN Yana ta faman shigowa wayar shi Amma yaki dagawa a karshe ma yayi switch off na wayar gaba daya Yana jin ranshi baby dadi,dukda yasan ya dace ace ya kulata kodan shi ne

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

1 Comments On ZAFIN KISHI
avatar
abasu-kala

11 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment