Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Habiba ce durkushe a gaban rijiya tana wanki,sai Innajo a tsaye tana ta ruwan masifa akan taki yin sauri ta karasa dan karta idar ta yimata shara.

"Kiyi hakuri Innajo,wallahi Ina ta yin sauri wankin ne Yana da yawa shiyasa"cewar Habiba da take goge zufar data tsatstsafo daga goshinta saboda wahalar aiki,tunda ta tashi da asuba bata zauna ba aiki kawai take yi.

"To nidai na fada maki,kiyi sauri Ina jiran ki"ta juya cikin dakin.



Haka Habiba taci gaba da aikin tana faman huci,ga wata azababbiyar yunwa da take addabar ta.sai goge zufa take yi.Malam tunda safe ya fita wurin sana'ar shi.



Wuri ya samu yayi parking din motar shi,kafin ya fito cikin kasala yake tafiya harya iso bakin kofar Doctor Hasan.wanda course mate dinshi ne tare sukayi karatu a zariya.


Kwankwasawa yayi daga ciki aka ce "yes come in"A hankali ya tura kofar tare da cewa "Assalamu Alaikum"Yana yatsina fuskar shi.

"Amin wa'alaikas salam"Doctor Hasan ta amsa Yana aje biron hannun shi.kallon shi ya tsaya yi ganin yadda abokin nashi fuskar shi tadan fada alamar baya jin dadin jikin shi.


Habib zama yayi Yana mikamai hannu sukayi musabaha,cikin raha irin ta abokai.yana janshi "kaga mijin mace daya,Amma yanzu mun kusa canza maka suna zuwa mijin mace Biyu"cewar Doctor Hasan Yana dariya.


Yatsina fuska ya karashi a karo na biyu,jin kanshi Yana Sara mai kaman zai fita.

Kallan shi yayi ya ce "kaga malam kayiman abinda ya kawo ni,baka dame ni da surutu ba,kuda bakwa gajiya da Yar cewa kaman mata"Yana dan lumshe idon shi,tare da mike kafar shi.


Cikin sauri Doctor Hasan ya fara dubashi jinin shi aka sauka bayan anyi mai awon Bp,da sauran gwaje-gwaje.bayan sun zauna Doctor Hasan ya kalle shi Yana cewa "kaga result dinka bazai samu ba sai zuwa gobe saboda gaba daya za'ayi maka kafin ranar daurin auren gobe sai kuzo tare da amaryar itama a yimata awon,saboda kasan yanzu sai an kaiwa limamai results kafin suke daura aure ko?

"Eh na sani"cewar Habib da yake dafe kanshi.


Bayan an rubuta magunguna ya siya,ya rako shi har bakin motar shi kafin sukayi sallama ya wuce.



Tun Bayan fitar shi Zulaihat taba direver kayan break ya kaiwa yara Scholl saboda tunda safe ya kaisu,a lokacin bata karasa girkin ba,dan kar su makara aka kaisu.


Bayan tayi break ta koma daki,inda tabar Nafisa tana gyara gidan da ketchen din.


Yanzu zulaihat ko abincin kirki bata iya ci,data fara ci zata ji ta koshi,saboda ta saka damuwa a cikin ranta.


















✍️✍️✍️✍️✍️✍️



*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*





👏👏👏👏👏.





[4/8, 11:57 PM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*




*true life story*



*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*MARUBUCIYAR* 📚🖊️



🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW* 👇


🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*





*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*




*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .




PAGE 3️⃣7️⃣➡️3️⃣8️⃣





📝Haka rayuwar Habib da Zulaihat take tafiya a cikin wannan satin,ga kwanakin bikin shi suna ta Kara kusantowa.tun randa taje gida Abban ya korota bata Kara komawa ba saboda tana tsoran shi.kuma tunda ta dawo ta dora daga inda ta tsaya ana sauran kwana biyu daurin aure da dare misalin karfe daya na dare Habib ya nufi dakinta.


Ya Jima tsaye jikin kofar dakin Yana so ya shiga,Amma Yana jin shakkun kada ta tara mai mutane da wannan tsohon Daren.Dole ya aro juriya a matsayin shi na namiji ya yafa a zuciyar shi kafin ya tura kofar dakin,cikin sa'a kuwa ya jita a bude.ganin duhun dakin yasaka yayi saurin kunna light din wayar shi.

Lokacin daya kunna hasken yayi daidai da tashin zulaihat tsaye.sosai suke kallon juna dan koba komai akwai kauna da soyayyar juna a zukatan tsaffin masoyan.

A hankali yake takowa zuwa gabanta,har saida ya kure mata.kasa tayi da kanta ganin yadda ya kureta da idanun shi.hakan da tayi ya gano cewa ya kashe Mata jiki dan haka yanzu zai yi Mata wayo.

Hannuwan ta ya kamo cikin yin kasa da voice kaman mai yin rada ya fara yimata magana"Haba Uwar gida sarautar mata,ki gafarce ni Mana,kada ki dauka wannan auren da zan Kara zai rage wata darajar da kike da ita a wurina Koda da kwayar zarrra ne,har karshen rayuwata soyayyar ki tana nan dakau a cikin zuciyata"Kara jan numfashi yayi jin tayi shiru bata tanka ba.
"Ki sani shi Karin aure Allah ne ya kaddara Mana,ba yin kanmu bane,Kuma umarni ne na Allah (S W A ), kada ki bari shedan yayi galaba a kanmu,kada kiyi sake da hanyar da zaki samu aljanna,insha Allah nayi maki alkawarin zaki sameni mai shimfida adalci a tsakanin ku,Amma ki kasance mai yiman biyayya tare da Addu'ar ku.to ni Kuma insha Allah duk abinda kuke da bukata daidai arzikin da Allah ya horeman zanyi maku".
tsura Mata ido ya Kara yi Yana kallon yadda take zubar da kollah.


Cikin fargaba Zulaihat ta rungumeshi tana Kara saurtin kukan ta.ba tare data furta komai ba.

Haka Habib yayi ta rarrashin ta Yana nusar da ita illar abinda take son aikatawa na kauracemai.A karshe dai dakyar ya samo kanta ta bashi hadin Kai.




Washe gari ta kama ranar juma'a,ya gobe daurin aure kenan.tunda ya fita bai dawo ba Yana ta faman hada-hadar biki.

Zulaihat bata gayyaci kowa ba sai kawarta Ikilima,kanwarta ma Jamila da aka turo korata tayi a cewar ta abin kunya ne tayi wata hidima dan za'a yimata kishiya.


Haka Habib yayi ta fama da abokanshi har zuwa dare kafin ya dawo.dan ko gidan su Habiba sai abokanna shi ya tura Suka bata sauran kayan bukata na biki.ya saka an jera komai a gidan da za'a Kai Habiba.


"Ke Ihsan ba inda Zaki je a gobe,dole ne ki zauna muga karshen game din nan"cewar Hannatu da take daura dankwali a gaban mirror.


I hanakli Ihsan ta sauke ajiyar zuciya tana kontawa bisa katifa.
"To kawata na hakura da tafiyar nan,Amma dole nexst week nabar garin nan gaskiya".


Juyowa Hannatu tayi tana kallon kawarta ta "Ba matsala zuwa next week din sai ki wuce.



Sai wuraren karfe 10 kafin Ikilma ta wuce gidan ta bayan ta gama kullawa Zulaihat abubuwan da ya kamata ta rinka yi Dan ganin ya saki amaryar da za'a kawo .


Shi Kuma Habib sai kafshe shadaya da rabi kafin ya samu sukunin shigowa gidan sa.


*RANAR ASABAR*

A ranar Asabar da misalin karfe Sha biyu na rana jama'a da abokan arziki Suka taru masallacin cikin unguwar ,kusa da gidan Malam Hadi mai kayan Miya domin daura auren Habiba da angonta Habib.

Amma Lokacin da aka bukaci a kawo results din su Dan nuna shedar cewa kowannen su Yana cikin koshin lafiya kamar yadda ake yi.Sai dai akasin da aka samu babu wannan results din Sannan babu Doctor Hasan Wanda shi ake faman jira.

Cikin jin Haushi Habib ya fito waje,sai kanin Baban shi kawu Aliyu shima ya biyo bayan shi.wayar Doctor Hasan yake faman kira,Amma matsalar network ta hana Kiran ta shiga.dakyar ya same shi bayan yadan matsa gaba dakan da jikin masallacin.


Cikin daga murya ya fara cewa "Wai Dr Hasan meyasa kake yiman haka ne,bacin Kai da kanka ka dauki alkawarin zaka kawo min"shiru yayi jin irin amsar da abokin nashi yake bayar wa.


Amsawa yayi da "To muna jiranka saika karaso"kafin ya kashe wayar Yana kallon kanin mahaifin nashi.

"Kuyi hakuri Baba ya ce gashi nan zuwa"

A tare suka Juya zuwa cikin masallacin.


Bayan minti goma Dr Hasan ya iso wurin da taimakon address din da Habib ya tura mai.

A bakin motar ya tsaya shi da wani abokin shi mai suna Muktar.

Cikin yin kasa da murya suke tattaunawa,Wanda ni kaina bana jin me suke cewa.


Mukhtar Naga ya shiga masallacin Jim kadan suka fito da limamin masallacin sai malam Baban Habiba da wani babban mutum.

Bayan sun gaisa Suka Mika masu takaddun.liman shiya fara dubawa kafin wannan babban mutumin ya amsa Yana cewa "A gaskiya kun bata Mana lokaci am..........."

Sauran maganar ce ta makale a bakin shi ganin abinda aka rubuta a jikin takardar.sosai fuskar shi ta nuna alamun tashin hankali.

Cikin sanyi yace" ku muje,Kai mukhtar ku biyo ni a baya"yayi gaba Yana gyara babbar riga.
Gaba dayan su suka rufa mai baya kowa Yana al'ajabin wanna rudadden al'amari.

Bayan kowa ya zauna an nutsu za'a fara gabatar da daurin aure.

Wannan babban mutumin naga ya dauko bandir din kudi ya aje a gaban waliyyan Amarya a maimakon su kawu Aliyu da zasu bayar.kowa shiru yayi Yana kallon ikon Allah.dan shi Habib shida zugar abokan shi suna can a bayan mutanen shiyasa basa ganin abinda yake faruwa.


Liman ya fara gabatar da daurin aure,cikin kankanin lokaci aka sheda daurin auren Mukhtar Muhammad da Habiba Hadi akan sadaki naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba.



Da sauri kawu Aliyu ya mike tsaye jin wannan lamari,dukda Yana tantamar kunnen shi bai jiyo mai daidai ba.Amma mai maitawar da akayi shiya tabbatar mai da gaske ne.

Daidai nan shima Habib ya mike Yana karkarwa cikin lokaci kalilan mutane suka fara rudewa Dan ganin wannan rudadden lamari da aka samu na lokaci daya.


Habib daidai saitin zuciyar shi ya dafe Yana kokarin yin magana,Amma Ina ya kasa saboda yadda jikinshi ya dauki kakkarwa sai numfashin shi da yake kokarin daukewa.kafin na kusa da shi su ankare Suka ji yimmmmmmmm ya fadi a kasa .gaba daya abokan shi sukayi kanshi suna Kiran sunan shi.Amma Ina Habib ba alamun numfashi a tare da shi..............











✍️✍️✍️✍️✍️✍️



*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*





👏👏👏👏👏.
[4/8, 11:57 PM] Hayat: 🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️

*short story*


*true life story*


*LABARI/RUBUTAWA*


*RUKAYYA IDRIS BALAH*
*(AUTAH)*



*MARUBUCIYAR* 📚🖊️




🤦 *ZAMANINMU* 🤦


*AND NOW* 👇

🗡️🗡️ *ZAFIN KISHI* 🗡️🗡️
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
____________________________https://www.facebook.com/104534761033461/posts
arewawritersassociation@gmail.com

https://youtube.com/channel/UC2en2LRwD-FljFg2U2OYhDQ

*Barka da zuwa tashar S ZARIA HAUSA TV ku danna mana Subscribe tare da kararrawar sanarwa domin samun sabbin shirye-shiryen mu mu gode.*




*BISMILLAHI RAHMANIR* *RAHIM*




*DA SUNAN ALLAH MAI* *RAHAMA MAI JIN* *KAI* .





PAGE 3️⃣9️⃣➡️4️⃣0️⃣






📝Duk wanda ke cikin masallacin saida hankalin shi ya tashi,ganin mutum kamar wannan a kasa,abokanshi sukayi kamo shi zuwa cikin mota da sauri suka nufi hanyar asibiti,saboda an zuba mai ruwa Amma babu alamar numfashi a tare da shi.

Shima kawu Aliyu da sauran dangin Mama bayan motar suka bi.


A cikin masallacin kuwa shi kanshi malam Hadi a rude yake sai faman tambaya yake yi "Wai meke faruwa "Amma ba Wanda ya bashi amsa,sai fitowa waje da sukayi.


Dr Hasan kamo hannun malam da Mukhtar yayi sai wannan babban mutum din Wanda ashe mahaifin mukhtar ne,wato Alhaji Muhammad mai turare.

Cikin sanyi Hasan ya nisa kafin ya fara cewa "kuyi hakuri abin ne ya zo a kurarren lokaci,Amma wannan ita kadaice hanyar da zamu taimaki Habiba,shi Kuma Habib idan ya farfado zamu San abin yi,yanzu malam kuci gaba da hidimar ku,mu zamu bisu asibitin mugan shi Idan mun dawo zanyi maku bayanin abinda ya faru "Yana kokarin Kiran wayar wani abokin shi.

"To shikenan,Amma nidai hankalina ya tashi,Dan Habibu mutumin kirki ne,dukda nasan shima mutarin zai riketa da Amana"cewar malam Yana share kolla fuskar shi.


Da haka su Dr Hasan suka bi bayan su Habib.



A cikin gidan su Habiba kuwa baiwar Allah tana cikin dakinta ita da wata kawarta da suke islamiyya daya mai suna Hafsat,shima ana ya jibi daurin aure Hafsat din ta kawo mata ziyara shi ne ta sanar da ita.


A cikin tsakar gidan kuwa Innajo ce da makota suna ta dora girki da hada zobo,masu yanka albasa nayi,da masu hada zobo da kankara,sai kanwar mahaifiyar Habiba da take ta shigi da fice.


Dakin Habiba ta nufa ,ganita zaune yasa ta kamo hannunta zuwa hanyar bayi bayan ta kaimata ruwan wanka.Hakan yasa Habiba ta fahimci abinda take nufi,wanka tayi sosai ta gurje jikinta.

Kafin ta fito Inna Lantana ta fitar Mata da akwatin kayan,ta saka Hafsat ta ciro Mata masu kyau dan tayi kolliya.



Saida aka shirya Habiba tsaf kafin aka fito da ita,inda aka nufi dakin malam da ita,su hudu ne a dakin Malam, mukhtar,Alhaji Muhammad,sai kanin malam Wanda suke uba daya.

A kasan tabarmar ta zauna kanta rufe da mayafi,cikin sanyi ta ce "Ina yinin ku?"
Cikin Kamala suka amsa Alhaji Muhammad Yana fadada fara'ar shi.


Gyaran murya malam yayi ya fara magana "Da farko Habiba Ina mai baki hakuri a matsayina na mahaifin ki,kasancewar yau an daura auren ki,Amma bada Habibu ba"shiru yadan ratsa tsakani.

Sosai Habiba taji gabanta ya fadi,Amma bata dago kanta ba daga duken da take.


Ci gaba yayi da cewa "Ga mijinki nan Mukhtar, insha Allah nasan ko bayan raina bazai bari kiyi kuka ba,Dan haka Ina umartar ki da kiyi masa biyayya,ban yarda daki saba mai ba kinji?,
insha Allah zakiyi dacen rayuwa"Yana goge hawayen da yaji suna kokarin zubowa.


Ita dai Habiba har zuwa wannan lokacin kanta Yana duke ta kasa furta ko a.Amma a zuciyarta tambayar kanta take yi "meya faru aka fasa aurenta da Habib?"Bata da Wanda zai bata wannan amsa.dole ta kawar da tunanin tana sauraren nasihar da mahaifin mukhtar yake yimata.


Haka suka ta yimasu nasiha,tare da wa'azantar dasu akan rayuwar aure.


A Asibiti kuwa motar su Habib na shiga aka anshe su tare da bashi taimakon gaggawa. Karin ruwa aka daura mai,da allurai.


Su kawu Aliyu da sauran abokan shi suna a resption zaune.


Kawu Aliyu fita yayi waje,Yana Kiran wayar Mama,tana fara ringing ta dauka.A lokacin tana tsakar gidan wurin masu dora girkin biki da saran hidima.cikin hikima ya fara yimata bayani.


Mama cikin lokaci kalilan ta rude jin babban danta a gadon asibiti .cikin sanyin jiki take tambayar Kanin mijin nata suna wane asibiti?

Kashe wayar tayi bayan ya sanar da ita.ta koma cikin gidan.



Hijaf kawai ta dauko sai Fatima data biyota tana tambayar ta "Mama lafiya?Ina Zaki je ne haka cikin yanayin tashin hankali?


Mama tsayawa tayi cikin zubar hawaye take sanar da diyar tata abinda ya faru.kusan a tare suke rige-rigen fita daga gidan.




A cikin mintinan da basu haura 25 ba suka dira a cikin asibitin.



Bangaren zulaihat bata San wainar da ake toyawa ba.ba kowa gidan daga yaranta,sai Yar aikinta Nafisa,sai Ikilima da ta zo tunda safe.








"That is good "cewa Ihsan da take makale da waya a kunneta,sosai ta fadada fara'ar ta saboda jin dadin labarin da ake fadamata.


Mikewa tayi tsaye tana cigaba da cewa "wallahi naji dadi yau zanyi bacci da saleba,kada ki sanar da kowa wannan sirrin namu,sannan idan ya dawo hayyacin shi zuwa gobe zamu gana da shi"da haka dai taci gaba da wayar tana faman gaggaba dariya.



Su Malam da Alhaji Muhammad sosai sukayi masu nasiha inda a karshe aka wuce da Habiba gidan mukhtar,a lokacin karfe biyu na rana ................










✍️✍️✍️✍️✍️✍️









*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*








👏👏👏👏👏👏.





✍️✍️✍️✍️✍️✍️



*~DAGA ALKALAMIN~* *~AUTAH~*









👏👏👏👏👏.




👏👏👏👏👏



Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels Group
Hausa novels and fashion Group
Cool novel, makeup and kitchen1 Group
And
WOMEN24 TV Group

WHATSAPP NO:+2349030159301



An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

1 Comments On ZAFIN KISHI
avatar
abasu-kala

11 months ago

Reply

Good

Please Login or Register in order to submit comment