Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dani ba tareda na ambaci wannan kalma ba....
Mahaifina Abdurrahim Suleiman, wanda nike kira da Abba, BARUMAYE NE, dan Asalin wani karamin kauyen Rumawa dake karkashin karamar hukumar Batsari dake a jihar Katsina, su hudu ne a wajen iyayensu, Rabi'u ne babba wanda suke kira da Rabe, sai mahaifina Abdurrahim, sai k'anwarshi Shamsiyya, sai autarsu Mufida, baki dayansu suna KAMANNI da juna shiyasa nike matuk'ar KAMANNI da yaya Abdurrahman... Babban yayansu rabe, da mahaifina da autarsu mufida wadanda suka aura en asalin kauyensu ne, Shamsiyya ce ta auri bare, wani d'an kasuwa, mai kudi wanda yake a birnin tarayya Abuja, a Kaduna iyayensa da danginsa suke amma yana zaune ne a Abuja, yaro guda daya suka haifa Abdurrahman wanda yake KAMANNI da mahaifiyarsa sak babu abun da ya baro a KAMANNI da ita, Alhaji Ahmad Almustapha ya rasu tun kafin a haifeni, saida Abdurrahman ya mallaki hankalin kansa ya kammala karatunsa sannan ya amshi gadonsa ya cigaba da kula da dukiyarsa.... Ni daya mahaifina ya haifa bayan shekara da shekaru da suka shafe babu haihuwa... Itama Mufida diyarta guda daya Nana Fiddausi wacce abokiyar haihuwata ce... Abba Rabiu shine kawai yake da y'ay'a maza da yawa amma shima diyarshi mace guda daya ce, Halima itama abokiyar haihuwata ce.... Bayan da Abdurrahman ya gaji dukiya da kamfafoni da kaddarorin mahaifinsa, ya tashi ne mutum mai son danginsa, ina good time dashi sosai, yana da tausayi sannan ya kasance mai yawan taimako, shine wanda ya dauko en uwan mahaifiyarsa ya maido dasu cikin garin Katsina, shine ya maidomu cikin gari, ya siya masu gidaje amma a lokacin ban da Mufida, sai daga baya sannan mijinta ya amince suka dawo cikin gari, ya samu sana'a yana rik'e da iyalansa, a lokacin da yaya Abdurrahman ya maidomu cikin garin Katsina, ina karama ne shekaruna daidai sakawa a makarantar boko don haka ya sakani a wata private school, yana iyakar kokarinsa domin ganin ya tallafawa su Abba, a bangaren Abba Rabiu yana sana'a amma duk taimakon da ya bashi yana amsa ne yayi godiya tareda saka mashi albarka amma a bangaren mijin Aunty Mufida wani lokacin yana amsa, wani lokacin kuma yace ya barshi ya gode, a bangaren Aunty Mufida kamar Abba Rabiu itama tana amsa ne tayi godiya, a bangaren Abbana shi mutum ne mai san dogaro da kai, ba ya da son abun duniya, ba ya shishshigewa mutane musamman masu kudi, saboda ba ya da kwadayi haka ya tsani a dangantashi da wannan kalmar ta kwadayi ko san abun duniya, ina goyon bayan wannan abu, a lokacin da yaya Abdurrahman ya fara taimakawa Abba, Abba saidai yace ya gode amma ba zai amsa ba, ya nemar mashi aiki kawai kuma ba'a karkashin kamfaninsa ko inda yake mallakinsa ba, yaya Abdurrahman yaso Abba ya rink'a amsar alkhairi da yake mashi amma abun yaci tura shine ya nemar mashi aiki a wajen wani friend dinsa amma da yake cikin kurarrran lokaci ne, aikin ba wani babba bane, daga baya ya samar mashi wani aiki wanda yafi wancen amma Abba refused, yace yana jin dadin aikinshi don haka bazai dainashi ya koma wani aikin ba, ba domin yaya Abdurrahman ya so ba ya barshi, yana mai cigaba da yunkurin taimakawa Abba amma sai Abba ya nuna b'acin ransa kuma ba ya amsa....
Ta bangarena duk idan zaizo garin nan yana min tsarabar kayan sakawa, duk abun da ya gani Rumana, I'm his favorite cousin, shekaru sun shud'e gidanmu ya fara lalacewa yana gurgurewa, yaya Abdurrahman yayi maganar gyara gidan amma Abba refused shine ya bari saida ya tafi saudia sannan ya saka aka gyara gidan ya koma yadda yake a halin yanzu, before gurgurarran gidan kasa ne, lokacin da Abba ya dawo yayi godiya ba tareda yayi korafi ba... Lokacin da na gama primary school, Abba ya nuna rashin amincewarsa akan cigaba da karatuna, aka yi juyin duniyar nan amma yaqi yarda yace tunda dai na iya karatun Hausa da na Turanci kuma na iya turancin a furuci, Alhamdulillahi karatun ya isa haka sai in cigaba da zuwa Islamiyya, ina gani Halima ta cigaba da karatun secondary da yake tare muke, Nana Fiddausi ce take a bayanmu amma sai ban damu ba tunda dai babu yadda zanyi, duk da ina son karatun kuma ina da buri a kai amma babu yadda zanyi, rashin cigaba da karatun secondary ya saka na koma zaman gida, bana son zaman hakanan shine na fara what'sApp, watching movies, season, karanta novels, sauraren audio novels da sauransu....
Sauran abun da ya biyo baya shine damuwar da yaya Abdurrahman yake ciki na rashin samun wacce zata soshi saboda Allah, ni kuma na yanke shawarar in rink'a tura mashi text message, sannan in bayyana kaina a daya daga cikin cousin dinsa mata dake a garin nan, ina fatan yayi tunanin Nana Fiddausi ce ko kuma Halima na tabbata kowacensu zata soshi saboda Allah koda kuwa ba shi da ko sisi... Amma wannan abun yana tare da damuwa musamman idan ya gano nice... I can't imagine abun da zai faru...".
A lokaci daya gabanta ya yanke ya fad'i, saida tayi kalaci sannan ta shirya cikin kayan islamiyya tareda rataya bag ta zura long hijab wadda har tana sharar kasa ta rufe fuskarta da niqab, ta fito tayi wa parent dinta sallama sannan ta wuce, saida tayi doguwar tafiya ta wuce manya-manyan gidaje, ta karasa makarantar, bayan an tadosu ta jero tare da wata cute fullo Babe, tun a class take shareta cox taji haushin abun da tayi mata, hakanan ta saka ya gama kalleta, Aysha tace,
"Please mana besty....".
Rumana tace, "Ayusher abun da kikayi min ya b'ata min rai, ta ya zaki bani number kice in tura hotuna bayan kin san ba wayarki bace, at least tunda brother dinki ne sai kice in tura hotunanki kawai... Wajen inyi voice message na danna video call kuma yayi picking ban lura, ya gama kalleni...".
Aysha tayi dariya saying,
"Ayyerh... Sorry... Kaina a kasa...".
Rumana ta tabe baki saying,
"Ace mutum magana daya biyu sai ya saka turanci...".
Aysha tayi murmushi kawai sunyi tafiya kadan sannan suka rabu kasancewar gidansu Aysha yana kusa ne da makarantar, tana shiga gida ta lek'a Umma sannan ta wuce bedroom dinta ta ajiye bag ta rage kayan dake jikinta ta wuce bathroom tayi wanka ta fito ta shirya cikin wani leshe cikin fittet gown ta fito heading to bedroom din Umma, wani yaro d'an neighbor dinsu ya shigo saying,
"Wani yana kiran Rumaaa...".
Rumana tayi turus tana kallonshi da mamaki, tace,
"Kuma Rumana yace maka...".
Yace, "Ehhh...".
Kafin ta samu zarafin k'ara magana, Umma tace,
"Kaje kace mashi gata nan zuwa...".
Yaron ya juya ya koma, Rumana tayi jim, Umma tace,
"Ki tafi tunda Abbanki yace ba zakiyi karatu ba, wannan yana nufin aure yake son yayi maki...".
Rumana tayi jim ta juya ta shige bedroom dinta ta zura long hijab har kasa....
Adeel ne yayi parking motarsa opposite da kofar gidan, yayi crossing kafafu yana kallonta yana murmushi, yana sanye ne da kananan kaya da sukayi suiting dinsa, rigar ta sanyi mai wani irin neck, da hular sanyi a kansa yayi mata style, yayi folding hannuwa looking breathtaking and hot, kyakykyawan saurayi bafullo d'an kimanin shekaru goma sha tara, kallo daya tayi mashi taga KAMANNI da yake da Aysha, ta tsaya a bakin kofa, saida yayi murmushi sannan ya k'arasa tareda tsayawa gefenta, da husky voice dinsa yace,
"Rumana...".
Ta d'aga mashi hannu saying,
"Yaa Adeel kayi hakuri, kafi karfina, wannan soyayya ba mai yiyuwa bace, bamu dace ba...".
Adeel ya dubeta da mamaki sannan yace,
"Saboda meyyy kika ce haka?".
Rumana tace, "Saboda kafi karfina...".
Adeel ya dubeta na tsayin wasu seconds sannan yace,
"Who told you that?".
"Yaa Adeel kai d'an masu kudi ne, ni kuma diyar talakawa, akwai dukiya a gidanku, ni kuma bamu da ita, kayi karatu ni kuma daga primary na tsaya, gidanku na alfarma ne, wannan kuwa gurgurarran gidan kasa ne ban da an gyarashi... Yaa Adeel kayi hakuri tsarin rayuwarmu ya banbanta, ka barni a inda Allah ya ajiyeni, kaje ka nemi daidai kai diyar masu kudi, ni kuma in auri talaka daidai ni...".

Adeel ya ware idanu saying,
"Aww dalilin kenan... Ashe baki da dalili...".
Rumana tace, "Meyyy? Na fad'a ba zan iya auren mai kudi ba, talaka zan aura, ni da k'anwarka Ayusher *KAWAYE NE* amma ko k'awance da mukeyi saboda bani da yadda zanyi ne amma koda k'awance nafi son inyi da diyar talakawa daidai ni, ka barni a matsayina, kadda ka kaini inda ban kai ba...".
"Rumana... Dama ya tab'a zama laifin don mai kudi ya auri talaka... Rumana zuciyata ta kamu da matuk'ar sonki, a kullum kaunarki tana k'ara girma ne a cikin zuciyata...".
"Koda ba laifi bane amma ni ba zan iya ba, ka rabu dani kaje ka nemi wacce rayuwarku take daidai, wadda kuke a level daya, kafi karfina, tsarin rayuwarmu ya banbanta, zamanmu a inuwa daya ba mai yiyuwa bane...".
Adeel ya dubeta da damuwa saying,
"Rumana... But I love you... I really do... Ina sonki... Ina matuk'ar sonki... Wannan ba dalili bane saidai ko wani hali marar kyau aka ce maki ina dashi, shiyasa kike guduna...".
Rumana tace, "Yaa Adeel baka da mugun hali, kuma babu wanda ya kawo zugarka, saboda koda sun fad'a nasan karya ne, nasan Ayusher, nasan tarbiyyar gidanku... Amma kafi karfina, BAN DACE DA KAI BA..".
Ta had'e hannayenta wuri daya alamar roko πŸ™ sannan tace,
"Na rokeka da Allah kadda ka k'ara zuwa gidan nan, ban iya wulakanci ba, kadda ka saka in fara a kanka... Koda kazo bazan fito ba... Ka rabu dani, ka manta dani, ka nemi wacce kuka dace, wacce danginta suke level daya da danginka... Aka ce kwarya tabi kwarya...".
Adeel yana kiran sunanta tayi banza dashi ta shige gida, ta rike kugu tana kallon gidan, ta zare hijab dake a jikinta ta rataya, saida ta share gidan sannan tayi mopping, ta fiddo kayan wanke-wanke, ta d'aura girki, tana gama girkin ta zuba a warmer ta wuce bedroom dinta saida ta duba lokaci sannan ta rage kayan dake jikinta ta d'aura towel ta wuce bathroom, ta jima sannan ta fito yayinda jikinta yake dropping ruwa, ta shirya cikin black arebian gown, ta zura long hijab ta tada sallah, bayan ta gama sallar zuhr, fitowarta daga bedroom yayi daidai da shigowar Abba hannunsa dauke da bakar leather, ta gaidashi tareda rusunawa ta amsa, ya sakar mata yana mai amsawa da murmushi akan fuskarsa....
"Sannu da dawowa...".
Abba yayi murmushi sannan yace,
"Yauwa er albarka... Na sameku lafiya?".
"Lafiya lau...".
Ya wuce dakinsa, ta bishi tareda dropping leather ta fito ta dauki silver cup ta zuba mashi ruwan randa masu sanyi da d'ad'i ta kai mashi sannan ta lek'a dakin Umma....
Umma ta fito heading to his room yayinda Rumana ta wuce kitchen ta zuba abinci ta wuce bedroom saida tayi full ta kora da ruwa, sannan ta k'ara gyara bedroom dinta, ta janyo bag dinta na Islamiyya tana memorising addu'o'e...
********
ABUJA,
Abdurrahman ne zaune a study room yana going through wasu papers, dogon trouser ne kawai a jikinsa, babu riga a jikinsa wanda ya bayyana kirar jikinsa na maza masu kira, seven peck, he's really hot, lokaci zuwa lokaci yana kallon wayarsa dake ajiye a gefe, ya janyota yayi dialing numbar saidai bata shiga, ya maida akalar kiran zuwa numbar Rumana....
******
Saida gabanta ya yanke ya fad'i ganin kiransa, ta dafe kirji saying,
"Na boni, kadda dai ya gano gaskiya ne...".
Saida ta tsinke ya k'ara kira sannan tayi picking, daya bangaren yace,
"Salaam alaiki...".
Tayi shiru yayinda gabanta yake dukan ukku-ukku, yace,
"Hello...".
Tayi firgigit tace,
"Ina jinka...".
Daga daya bangaren yace,
"A yau dai sai nayi maki turanci, hausar guduwa takeyi...".
Tace, "Uhmm...".
Yayi mamakin amsarta yace,
"Baki da lafiya ne?".
Da sauri tace,
"A'a, lafiyata lau...".
"How's your day?".
"Alhamdulillah...".
"Your voice is cracking anya kuwa lafiyarki lau, my favorite cousin...".
Samun kanta tayi da fashewa da kuka saying,
"No kaina ne yake ciwo kuma idan na samu bacci zai daina...".
"Daga ciwon kai sai kuka, kisha magani idan bai daina ba, kije kiga likita... I'm hanging, take care... Angel...".
Da sauri tace,
"What!...".
Yace, "Laifine don na kiraki da Angel...".
Da sauri tace,
"No ba da kai nike ba, na kusa b'arar da cup ne shiyasa... Bye, take care...".
Saida yayi dariya sannan yace,
"Yau Rumaaa ce take turanci... I'm surprise...".
Tace, "Babu ruwana...".
Tareda hanging kiran....
Abdurrahman yayi relaxing akan kujera tareda lumshe idanunsa....
**********
Rumana tayi jim tana kallon majigin wayar cike da mamaki, ta ware idanu sai kuma tayi dropping dinta ta cigaba da memorising du'a da takeyi, abun ne ya k'ara dawo mata, tayi zuru tana tunanin abun da zata tura mashi idan yayi mata reply domin ta kagara ta k'are wannan wasan koda ta samu sassaucin wannan fargaba dake damunta....
Umma ta lek'o saying,
"Rumana karatu kike?".
"Ehhhh....".
"Da fatan kinyi sallah?".
"Nayi sallah... Shine nike karatu...".
"Allah ya taimaka...".
"Amin...".
Umma ta juya ta koma, yayinda Rumana ta cigaba da karatun da takeyi....
Kafin lokacin Islamiyya, ta fito ta taya Umma with the house chores, kiran sallar asr ne ya tayar dasu ta wuce bedroom tayi wanka tareda dauro alwalla, tayi sallah, ta shirya ta wuce Islamiyya bayan da tayi wa Umma sallama....
Throughout the day tana kallon waya domin ganin amsar da zai maido mata amma shiru, sai bayan sallar Isha'i sannan ya turo mata reply tayi zuru tana kallon short message din, tana kitsawa tana kwancewa akan amsar da zata bashi....
Abun da ya turo mata kamar haka...
_Wacece ke a cikinsu?_
Saida ya dauketa mintina ukku tana rubuta tana gogewa kafin daga bisani tayi karfin halin tura mashi....
Cikin ranta tace,
"I'm really sorry yaya Abdurrahman, babu sonka a cikin zuciyata, taimako ne kawai domin in nuna maka a inda zaka samu wacce zata kaunaceka saboda Allah, kuma ta zauna da kai a kowanne irin hali... Ina fatan kayi tunanin Nana Fiddausi ko Halima ce ta turo sakon, domin ina da tabbas akan kowacce a cikinsu zata kaunaceka saboda Allah, sannan zaka samu farin ciki...".
Saida tayi wanka sannan ta dauro alwalla ta zura night gown tabi lafiyar gado, babu jimawa bacci yayi awon gaba da ita...
A daya bangaren,
"Barka da dare, wannan sako ne daga zuciyar da take matuk'ar sonka, bazan bayyana maka kaina ba, tunda har na baka haske, idan ka ganeni then we are destiny to be together, idan kuma baka ganeni ba, then we are not destiny to be together.... Watakila Nana Fiddausi Fuhad Ruma ce ko kuma Rumana Abdurrahim Ruma ko kuma Halima Rabiu Ruma... Tabbas akwai sunana a ciki amma who know's idan zaka ganeni, ban san shiga rumatsa don haka kayi nazari da kanka sannan ka gano wacece ni a cikinsu... Ka yarda Ina matuk'ar sonka... Ka huta lafiya... Daga zuciyar da take so da kaunarka... From your love... Your crush... Abdurrahman Angel...".
Tun da sakon ya shigo yake karantawa yana maimaitawa domin gane wacece a cikinsu, bacci ya dauracewa idanunsa, under his breath yace,
"Kadda ki damu, zan ganoki a daren yau amma ba zan nuna maki ba har sai naji ina maki kwatankwacin so da kauna da kikeyi min...".
(Akwai chakwakiya πŸ™€πŸ™€πŸ™€, a bangarenta tace babu sonshi a zuciyarta, shi kuma yace har sai ya koyawa zuciyarshi sonta sannan zai bayyana mata kansa πŸ™€πŸ™€πŸ™€)....
Nana Fiddausi, Halima, Rumana, rayuwarsu ta banbanta, dabi'unsu sun banbanta, wayewarsu ta banbanta, kowace tana da yanayi da take magana dashi, yanayi na yadda rubutunta yake, da maganganu da tunaninta zai bata....
Abu ya tuna wanda ya gani a lokacin da yake karanta sakon, da sauri ya bude idanunsa yana mai bin text message din word by word, idan ba gizau idanunsa sukayi mashi ba, tabbas yaga kalmar a d'azu, ya sauke ajiyar zuciya....
Shin wacece yake tunani? Shin miye zai faru a nan gaba? Shin ya zata kasance a tsakaninsa da wacce yake tunanin itace? Da alama akwai cakwakiya a nan gaba...
Tun da Rumana ta tura mashi wannan sakon ta kashe wayar ta wullata a bedside drawer, ta cigaba da al'amurranta....
**********
Adeel ya kasa samun nutsuwa, a kullum tunaninta ne manne a cikin zuciyarsa, yana matuk'ar sonta but she refuse to give him chance, chance da zai fahimtar da ita matuk'ar son da yake mata, chance da zai koyar da ita sonshi, su rayu a tare har abada, bata picking kiransa, bata replying message dinsa, karshe ya yanke hukunci akan ya sanar da brother dinsa Ashraim domin a nemar mashi aurenta....
Shin Waye Adeel?
Late Alhaji Abdul'azeez Muhammad, kafin rasuwarsa shararren d'an kasuwa ne wanda yayi suna a duniya, Allah ya azurtashi da tarin duniya mai yawan gaske, mutum mai k'ok'ari da jajircewa akan taimakon addinin musulunci, taimakon marayu, mabukata, biyan hospital bill ga marassa karfi, shekaru biyu kenan da rasuwarsa, ya samu shaida mai kyau a bakin mutane, kafin rasuwarsa yana da mata hudu, Zuwaira (Mama), Fadila (Ummi), Hauwa (Nene), Maryam (Aunty)....
Khalifa shine first born na gidan, late Alhaji Abdul'aziz yana da yara da yawa da jikoki, bayan rasuwarsa aka raba gado kowace mata ta koma separate gida tareda yaranta saidai babu abun da ya sauya akan zumunci dake a tsakaninsu, mahaifiyarsu Adeel itace mata ta ukku a wajen marigayi, bafullatana ce kyakykyawa, dukkanin y'ay'anta ita suka biyowa shiyasa suke matuk'ar KAMANNI da junansu kamar tagwaye, haihuwarta ukku, maza biyu da mace guda daya wacce itace autarta, Ashraim shine d'anta na fari followed by his little brother Adeel sai kuma autarsu Aysha....
Ashraim yana da shekaru ashirin da daya, yana aikin government wanda yake had'awa da kasuwanci wanda ya koya a wajen mahaifinsu, yana da tarin dukiya amma har zuwa wannan lokacin baiyi aure ba, yana da manya-manyan gidaje a jihohi daban-daban na kasar nan da kasashen ketare, yana zaune tareda mahaifiyarsu, yana da matuk'ar kyau, kamarshi daya sak da Adeel ban da shekaru da suka banbantasu da babu tantama mutane zasuyi masu kallon tagwaye ne....
Aysha k'awar Rumana ce, ajinsu daya a makarantar Islamiyya, shekarunta goma sha shidda....
Adeel kyakykyawan matashin saurayi ne d'an kimanin shekaru goma sha tara, good looking and hot, bafullo, fari ne sosai, yana da tsayi, dakkakken namiji mai suffar karfafa, yana da dogon hanci tareda madaidaitan idanu, cute lips, brow dinshi a kwance yake lub kamar rubber kuma yana da yawa, yana da yalwataccen gashi mai yawa wanda yake kullum a kwance kamar na Arabs, naturally yake haka, he's kind, yana karatu a matakin degree na farko....

Littafin the chasing my heart, a tsakanin so, na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057

*Pay via*
*9169472057*
*Aisha*
*Opay Digital Service*

*Sai a tura evidence of payment via WhatsApp 09169472057....*

*Ko kuma Katin MTN via WhatsApp 09169472057....*

Hafsat Hisham (Aysher Angel) πŸ₯°πŸ˜˜πŸ₯°
[22/11, 06:25] AngelπŸ’žπŸ’žπŸ’ž: πŸ’¨ *CHASING MY HEART* πŸ’¨
A Tsakanin So
By Hafsat Hisham
(Aysher Angel)

Page 5 to 8
Free page na karshe

*Wannan shine free page na karshe da zanyi maku, Littafin the chasing my heart, a tsakanin so, na kudi ne, akwai shi complete, duk wacce take son complete dinsa zata samu akan naira dari shidda 600, kuyi min magana via WhatsApp 09169472057...*

Ashraim yana zaune a bedroom dinsa yana aiki akan system, Adeel yayi knocking tareda salaam sannan ya murd'a handle ya shiga ya zauna akan stool yana murmushi, Ashraim ya d'ago yace,
"Ta samu ne... You are smilling...".
Da murmushi akan fuskarsa yace,
"Ta samu fa...".
Ashraim ya ture system dake gabansa tareda maida hankalinsa akan little brother dinsa sannan yace,
"Alright then... Ina jinka...".
Adeel yayi jim yana sosa kai sannan yace,
"I'm in love... Naga wata yarinya ina so... I love her so much...".
Ashraim yayi dariya saying,
"Aahhh silly boy, miye na kunya after all you are mature... Uhmm... Gist me... Daga nan sai aka yi mi?".
A lokaci daya murmushi dake akan fuskarsa ya gushe, Ashraim yace,
"Ya dai?".
Adeel yace, "Tana bani ciwon kai ne, har gidansu naje amma bata saurareni ba, tace bamu dace ba....".
Ashraim yace, "Baku dace ba?".
Adeel ya gyad'a kai alamar tabbatarwa sannnan yace,
"Saboda muna da kudi ita kuma talaka ce, duk yadda naso fahimtar da ita talaka da mai kudi duk daya ne amma bata saurareni ba, tace ita talaka daidai ita zata aura, ina matuk'ar sonta bazan juri rashinta don haka please kuje gidansu ku nema min izini a wajen mahaifinta in rink'a zuwa zance wajenta...".
Ashraim yace, "Wannan shine abun da ya kamata ka fara tun farko, ba wai kaje wajenta kai tsaye ba...".
Adeel yayi murmushi kawai, Ashraim yace,
"Wacece ita? Wacece wannan wacce take gudun abun duniya bayan a wannan zamani wasu en matan idanu a rufe suke neman mai kudi su aureshi no matter what they have to do, amma ita gudun mai kudi take tana neman talaka... Buddy... Meyyy sunanta?".
Adeel ya lumshe idanu ya bud'e yayinda smile yayi escaping akan lips dinsa yace,
"Sunanta Rumana Abdurrahim Rumah amma ana kiranta da Rumaaa, barumaya ce...".
Ashraim ya kalleshi da sauri yayinda gabansa ya yanke ya fad'i, kallonshi yake idanu a waje sai kuma yayi sauri ya gyara yanayinsa, yayi murmushi saying,
"Buddy kace aure kake so... Alright then zanyi magana da Hajiya da yaya Khalifa, kaga sai muzo mu tattara muyi maka aure tunda shi kake so...".
Adeel yayi kasa da kai yana murmushi, Ashraim yace,
"Ehhh mana...".
Ashraim yace, "No, yarinya ce sosai, she is still young, ba zata wuce sa'ar Ayusher ba, k'awarta ce, ajinsu daya a makarantar Islamiyya...".
Ashraim yace, "Alright...".
Yana mai cigaba da aiki akan system dake gabansa saying,
"Kadda ka damu zanyi maganar da yaya Khalifa sai mu samu wani muje gidansu yarinyar, mu nemo maka izinin, ga makullin mota akan bedside drawer ka dauka na sabuwar mota dake compound ne, motarka ce tana cikin sabbin motocin da nayi order naga ka nuna interest a kanta...".
Adeel ya mik'e da sauri tareda hugging dinsa saying,
"Thank you so much yaya Ashraim... Na gode sosai... Allah ya saka da alkhairi... Akwai chilling...".
Ashraim yayi murmushi kawai yayinda Adeel ya dauki makullin motar ya fice da smile akan fuskarsa, kyauta halin Ashraim ne, suna jin dadinshi sosai, ya maye masu gurbin mahaifinsu....
A ranar Ashraim ya samu Nene sukayi maganar sannan yayi maganar da babban yayansu Khalifa, washegari suka shirya sukaje gidansu Rumana tareda uncle Haruna wanda yake k'anin mahaifinsu....
Sunyi sa'a sun samu Abba a gida, ya saukesu a falonsa, bayan an kawo masu drinks, Abba yace,
"Saidai ban ganeku ba...".
Ashraim yace, "Hakane... Sunana Ashraim Abdul'aziz Muhammad, d'a a wajen marigayi Alhaji Abdul'aziz Muhammad, wannan shine babban yayanmu, wannan kuma k'anin mahaifinmu ne... Abun yake tafe damu shine k'anina Adeel ne yaga diyar wajenka Rumana shine muka zo nemar mashi izini ya rink'a zuwa zance a wajenta...".
Abba yayi shiru na wani lokaci, yasan mahaifinsu mutanen kirki ne wanda mutane suke yabon halinsa, saidai shi talaka ne su kuma masu kudi, yana gujewa diyarsa wulakanci, yadda take shiru-shiru....
"Naji abun da kuka zo dashi, mahaifinku mutanen kirki ne, Allah yayi mashi rahama...".
Suka ce, "Amin...".
Abba ya dora saying,
"Kuce mashi na bashi izini ya rink'a zuwa zance a wajenta, ya nemi so a wajen yarinya amma ku sani ban ce na bashi aurenta ba, na bashi izinin zuwa zance ne a wajenta, macece ita, allura ce a cikin ruwa mai rabo zai dauka, Allah ne kadai yasan mijin da zata aura, a matsayina na mahaifinta zanyi k'ok'arin hadata da miji na gari, ban damu ba koda yafi kowa talauci a garin nan, in dai zai riketa bisa amana akan tafarkin Addinin musulunci, Alhamdulillah... Koda zata kawo min shi a matsayin wanda take so, idan na duba naga bai dace da halayen da nike so ba, bazan bashi aurenta ba...".
Khalifa yaji dadin wadannan maganganun da Abba yayi, yace,
"Hakane, shi aure babu ruwanshi da kudi, ko sarauta ko kuma matsayi, hali na kwarai yake bukata da kuma soyayya, mun gode, kuma zamu fada mashi abun da kace...".
Abba yace, "Matar mutum kabarinsa idan Allah yayi matarshi ce, shikenan, idan kuma ba matarshi bace, sai yayi hakuri, kadda kuga laifina saboda na fad'a maku d'azu kuma yanzu zan k'ara fad'a maku, izinin zuwa zance a wajen Rumana kawai na bashi, ba aurenta ba... Allura ce cikin ruwa, mai rabo ka dauka... Allah ya shige mana gaba...".
A tare suka ce,
"Amin...".
Suka rufe taro da addu'a sannan suka wuce, Khalifa tareda uncle sun wuce a motocinsu....
Ashraim yayi wa motarshi key, call ya shigo wayarsa ya kashe motar tareda picking kiran....
Rumana ta shawo corner tana tafiya a nutse, ta dawo daga aiken da Umma tayi mata, tana sanye ne da long hijab har kasa ta rufe fuskarta da niqab, tunda daga nesa ta hangoshi ta glass, gabanta ne ya yanke ya fad'i she thought Adeel ne, direct ta wuce wajen motar tareda tapping akan glass din motar, Ashraim ya d'ago tareda zuba mata idanu, ya b'alle murfin motar ya fito tareda zuba mata idanu ba ya koda blinking, idanunta kawai yake iya hangowa....
Rumana wacce bata

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment