Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

lura da banbancin shekaru dake a tsakani ba, tayi sama da niqab dake fuskarta tana kallonshi cike da damuwa, Ashraim ya ware idanu yana kallonta, the more yake kallonta the more take k'ara mashi kyau, maganarta ce ta dawo dashi hayyacinsa....
"Adeel meyyy haka? Na fad'a maka kadda ka k'ara zuwa... Na rokeka da girman Allah ka rabu dani kaje ka nemi sa'arka ni talaka zan aura... Adeel... Meyyy haka ina maka magana ka zuba min idanu kawai...".
Ashraim yayi murmushi saying,
"Jasmine... Kin tab'a ganin inda mutum ya rabu da abun da yake so... Your are amazing and unique...".
Rumana ta zaro idanu tana kallonsa sai a lokacin ta lura da banbanci dake a tsakani, ta juya da sauri ta shige gida, Ashraim ya bita da kallo yana murmushi, babu shakka itace irin matar da ya dauki tsayin lokaci yana nema, ya zaro kudi ya aika wani yaro wajenta sannan ya juya ya shige motarsa ya wuce....
Rumana ta fad'a akan bed tareda dafe saitin zuciyarta, she don't know meyyy yake faruwa da ita, ji take bugun zuciyarta yana k'aruwa kamar wacce tayi tsere, salaam taji ta fito yaro ne d'an neighbor dinsu ya mik'a mata envelope tana bud'ewa taga wrapper din en dubu-dubu, yace,
"Wani mai mota yace in baki...".
Tace, "Ka maida mashi...".
Yace, "Ya tafi...".
Ta koma ciki ta dauko chocolate ta bashi, ta fad'a akan bed tayi lamo tana wani tunani, ta rasa dalili da ya saka take yawan tuna kallon da yake mata, wayarta ta janyo tayi dialing numbar Adeel, yana picking tace,
"Yaa Adeel... Kazo gidanmu yanzu...".
Daga daya bangaren Adeel ya ware idanu saying,
"In zo gidanku kuma, inyi maki mey bayan ranar da nazo korata kikayi, fatan magabatana sun zo gidanku...".
Rumana tace, "Ban san abun da kake magana a kai ba... Kazo ka amshi kudin da brother dinka ya aiko min dasu ka mayar mashi da abunsa...".
Adeel yace, "Wai yaya Ashraim, yanzu yake sanar dani yadda kukayi, you thought nine, ban ga laifinki ba muna matuk'ar KAMANNI ne amma he is older than me... About the money, zan turo maki numbarsa ki kirashi yazo ya amshi abunsa...".
Yayi hanging kiran tareda tura mata numbar Ashraim....
Rumana tayi shiru tana kallon majigin wayar sai kuma tayi dialing numbar....
Daga daya bangaren Ashraim dake zaune akan sofa idanunsa a lumshe yayinda yake tuna fuskarta da yadda take magana, ya janyo wayar tareda picking ya kanga a kunne, da sauri ya bud'e idanunsa jin muryarta....
A karo na biyu Rumana ta k'ara maimaita abun da tace dashi....
"Ka dawo ka amshi kudinka...".
Ashraim ya ware idanu tareda sakin murmushi har saida ta jiyo sautinsa, a tsawa ce tace,
"Nace maka ka dawo amshi kudinka...".
Ashraim ya lumshe idanu saying,
"Ohhhh... Jasmine... How rude of you... Nayi maki kyauta amma kina min ihu...".
Rumana tace, "Nace ka dawo ka amshi kudinka...".
Ashraim yace, "Jasmine ke wacce irin Inlaw ce...".
Rumana tace, "Rumana dai...".
Ashraim yace, "Uhmm... Jasmine...".
"Nace maka Rumana...".
"Huh... Jasmine...".
"Sunana Rumana not Jasmine...".
"Alright then amma nidai I prefer to call you Jasmine... That's my favorite flower...".
"Koma miye ka dawo ka amshi kudinka... Na gode Allah ya saka da alkhairi amma bazan amsa ba...".
Ashraim yace, "Alright tunda kin matsa, zan amsa, gani nan kwance a bedroom dina kizo ki kawo min...".
Rumana ta ware idanu, yace,
"Yeah gidansu k'awarki ne, idan kika zo babu wanda zai tambayi dalili... Yaushe zaki zo? Uhmmm...".
Da sauri tayi hanging kiran, Ashraim ya fashe da dariya saying,
"Jasmine you are really amazing...".

Washegari ta k'ara kiran Ashraim akan yazo ya amshi kudinsa amma ya bige da tsokanarta, dole ta rabu dashi, daga Islamiyyar safe ta biya Orphanage Home ta kai masu tareda ajiye mashi text message....
"Bana da buk'atar kudinka kuma kaki kazo ka amsa don haka na kaisu kudin marayu domin suna da buk'ata...".
Ashraim yayi murmushi yana kallon majigin wayar, tun daga lokacin bata k'ara bin ta kanshi ba....
A tsakaninta da Adeel, soyayya suke zubawa, suna manne a waya, suna waya ko suna chat, yana zuwa zance wajenta, cikin kankanin lokaci ya koya mata soyayyarshi mai zafi....
A wannan lokacin ne ta samu kanta a wata duniya mai tattare da farin ciki saboda yadda yake nuna mata matuk'ar so, tuni tayi zurfi a cikin RUMATSAR SONSHI awww RUDANIN SONSHI....
Bayan sun fito daga lectures yayi dialing numbarta, yana sanye da jeans da t-shirt ya daura jacket a sama, kafarsa rufe da takalma kirar gucci, yayi wanka har wanka, looking hot and breathtaking, yana tafiya a nutse a cikin korayen ciyayi da earpiece manne akan kunnansa yana murmushi yayinda yake motsi da lips dinsa yana mata kalaman soyayya....
A daya bangaren Rumana tana kwance akan bed idanunta a lumshe yayinda take jin sonsa yana k'ara ratsa zuciyarta....
*********
A bangaren Abdurrahman cikin wannan lokaci ya samu nasarar koyawa zuciyarshi sonta tareda kaunarta, so da kauna na wadda yake tunanin itace ta turo mashi text message, ya kamu da matuk'ar sonta, jinta yake har cikin ransa, yana mata matuk'ar kauna fiye da wanda ta bayyana a text message da ta tura mashi....
***********
Tun da daddare Adeel ya sanar da ita zuwanshi, opposite da gidansu yayi parking motarsa, yana sanye da ash yard dinkin zamani wanda yayi suiting dinsa, ya kamashi, ya rufe kafafunsa da cover shoes, sumar kanshi tana kwance tayi lub-lub tana sheki tareda daukar idanu, yayinda yake zuba kamshi, looking handsome and breathtaking, yayi dialing numbarta saying,
"Rumana... Na karaso... Alright then...".
Sai kuma ya kwaikwayi muryarta saying,
"Nidai sai nayi maki turanci...".
Tayi hanging kiran tana dariya....
Sanye take da dogon hijab har kasa, fuskarta dauke da simple makeup, ta tsaya a kofar gidansu yayi taking steps tareda tsayawa a gefenta, yace,
"Guess what?".
Tace, "A'a... Ka fad'a min dai...".
Ya zaro karamin akwati daga aljihunsa ya mika mata, ta amsa tareda bud'ewa wani diamond ring mai kyau ne yayi appearing, smile ne yayi escaping akan lips dinta tace,
"Kaga har hausata ta gudu... OMG... Wow... Ya hadu sosai... Thanks so much amma bazan amsa ba, yayi tsad'a da yawa...".
Adeel ya dafe kai saying,
"Rumana kina bani headache, nayi maki kyauta ne saboda ina sonki, baiyi tsad'a ba, idan baki amsa ba zanyi fushi, kuma muyi fad'a...".
Rumana ta ware idanu saying,
"Duk saboda ban amsa ba...".
Adeel ya murtuke fuska na wasa saying,
"Try me... Ki gani...".
Rumana tace, "A'a bazan yarda muyi fad'a ba... I will not... I will not dare, idan mukayi fad'a zan daina ganinka, zan daina jin muryarka mai dadi a kunnuwana, da fuskarka wacce a kullum idan kayi min murmushi yake tsaya min a zuciya...".
Smile ne yayi escaping akan lips dinsa yace,
"Yeah... That's my Rumana...".
Rumana tace, "Meyy shine kakeyi min bakar magana da turanci don kaga ban iya ba...".
A tare sukayi dariya, Rumana tace,
"Na gode, zoben yayi kyau, kayi gaskiya da kace kyauta ta musamman, ta musamman ce wacce bazan manta da ita ba...".
Adeel yace, "Rumana wannan zoben shi zai nuna min matsayina a cikin zuciyarki, ina son kasancewarshi a hannunki kamar yadda sona yake manne a cikin zuciyarki idan ban ganshi ba I will assume that kin daina sona ne and I will be upset with you...".
Rumana ta ware idanu yayi mata gwalo, ta zaro zoben tareda sakawa akan finger dinta, yayi mata daidai yayi suiting finger dinta, smile ne yayi escaping akan lips dinta tace,
"Na gode sosai... Yaya Adeel...".
Adeel ya kwaikwayi muryarta, ta turo baki saying,
"Ka daina murmuring muryana...".
Adeel yace, "I will not after all burgeni kikayi shiyasa nike kwaikwaya kema ki rink'a jin dadi, kamar yadda nike jin dadi idan kikayi min...".
Saida yaga shigarta gida sannan ya shige mota ya wuce....
Yana komawa gida suka dasa waya, tsinkar fure sukeyi babu kama hannun yaro....
Washegari kafin ya wuce school ya biyo ta gidansu, tsaye yake a soron gidan, yana sanye da expensive shadda dinkin fittet na zamani wanda yayi suiting dinsa, expensive wristwatch, ya murza hula kirar tangaram, kafarshi sanye da expensive slippers, looking gorgeous and breathtaking, yana zuba kamshi...
Tunda ta fito yake kallonta ba ya koda blinking, dariya tayi har hakoranta suka bayyana, ta ajiye mashi farar kujera dake hannunta, tareda zama akan wacce take opposite dashi, sanye take sa riga da skirt en kanti, tayi rolling veil looking gorgeous and lovely....
Ta saka hannuwa ta rufe fuskarta saying,
"Kallon ya isa haka...".
Smile yayi escaping akan lips dinsa ya zauna saying,
"Gorgeous and lovely, mai kyauna...".
Tace, "Kaima kayi kyau, handsome...".
Yace, "And breathtaking...".
Ta ware idanu saying,
"Ka barni in k'arasa mana...".
Yace, "Na hutar dake love...".
"Da fatan kazo lafiya?".
"Lafiya lau... Kina lafiya?".
"Lafiya lau...".
"Ina zoben yake ban ganshi a hannunki ba...".
Da sauri ta kalli hannunta idanunta a waje, Adeel ya fashe da dariya saying,
"Sorry, love, wasa nike...".
Rumana ta turo baki saying,
"Aikuwa yanzu zan cireshi...".
Yace, "Tuba nike kaina a kasa...".
"Alright, an yafe maka...".
"Please a cigaba da kula min dashi...".
"An gama...".
"Shin a tsakaninmu wanene yafi son d'an uwansa?".
"Nafi sonka...".
"Saboda mi?".
"Saboda kowa kansa ya sani, nima kaina na sani, a kullum cikin son jin muryarka nike, sauraren muryarka da kalamanka a lokacin da kake magana yana sakani a matuk'ar farin ciki...".
"How rude of you, kina nufin muryata kike so not me...".
Tace, "Kuma dai...".
Saida yayi dariya sannan yace,
"Wasa nike... Uhmm, tsokanarki nike...".
Tace, "Adeel...".
Yace, "Adeel...".
Tace, "Ka daina kwaikwayana...".
Yace, "Ki daina murmuring muryana...".
Tace, "Bana so...".
Yace, "Ina so...".
Rumana ta turo baki cike da shagwab'a tace,
"Yaa Adeel ka daina bana so...".
Adeel yayi murmushi yana kallonta idanu a cikin idanu yace,
"Rumana... Ina matuk'ar sonki... A koda yaushe sonki yana k'aruwa ne a cikin zuciyarta...".
Rumana tayi dariya saying,
"Na gode...".
Call yayi picking daga school, har mota ta rakashi saida taga tafiyarsa sannan ta juya ta koma gida, ta hade fararen kujerun ta shige dasu gida....
********
A safiyar wata rana, tana zaune a gaban dressing mirror, sanye da gown kirar bubu tayi rolling veil, simple makeup ce akan fuskarta looking cute and lovely, wayarta ce tayi blinking yayinda sunansa ya bayyana akan majigin wayar, smiles ne yayi escaping akan lips dinta ta mike tareda feshe jikinta da perfumes, ta zura takalma flat, yana jingine da motarsa, sanye da brown shadda wadda tasha aikin hannu, ya d'aura riga zabuni a samanta, expensive qube, wristwatch and shoes looking lovely and breathtaking....
Smile ne yayi escaping akan lips dinta tayi taking steps tareda tsayawa a gefensa saying,
"Shine ka barni ina ta jiranka...".
Ya hade hannayensa waje daya saying,
"Sorry love...".
Tace, "An yafe maka...".
A tare sukayi dariya....
"Kalmomin soyayya da kikayi min jiya nazo ki maimaita min fuska da fuska...".
Ta juyar da kai tana dariya, yace,
"Yeah, a maimaita min, ina son in k'ara ji...".
Bata juyo ba, ji tayi yace,
"Alright then, let me see your phone...".
Ba tareda ta juyo ba ta mik'a mashi wayar, ji tayi yace,
"Rumana... Ina zoben da na baki, ashe dama yaddashi kikayi domin ki nuna min baki damu da ni ba kuma baki sona...".
Tace, "Daga baya kenan, ay an shani na warke, ina jin zoben a hannuna kace min otherwise...".
Wata magana yayi mata ta juyo da sauri yayinda ya sakar mata murmushi...
Wata expensive Jeep mai tudu ce tayi parking opposite dasu, Abdurrahman ya fito, ya jingina da ita tareda folding hannuwa yana kallonsu, cotton trouser ne a cikinsa pink tareda t-shirt mai bottom itama pink amma light, ya d'aura sweater ta sak'a a samanta wadda take long-sleeve mai circle neck, expensive wristwatch tareda shoes, idanunsa rufe da white space, looking breathtaking, handsome and hot, yana zuba kamshi mai sanyi, ya jima tsaye yana kallonsu ganin yadda suka zubawa juna idanu basu koda blinking, wani wicked smile ne yayi escaping akan lips dinsa, yana tafiya cike da kasaita heading to the kofar gidan, da sauri tace,
"Yaa Abdurrahman...".
A lokacin da kamshinsa ya ziyarci hancinta, a lokaci guda murmushi ya bayyana akan fuskarta....
Abdurrahman ya tsaya cak, wani wicked smile ne yayi escaping akan lips dinsa, yace,
"Yeah...".
Ya koma tareda taking steps har inda take saying,
"Amma ya aka yi kika ganeni bayan kuma baki juyo ba?".
Tace, "Koda za'a yi shekara da shekaru bazan manta kamshinka ba, na rik'e dukkanin wani turare da kake amfani dashi, da yadda sukeyi idan ka had'esu...".
Abdurrahman ya kama hannunta yana murmushi saying,
"That's my favorite...".
Adeel ya kalleshi ya kalli hannunta da yake rike dashi, sannan ya maida dubansa akan fuskarta yaga bata damu ba, a take yanayinsa ya sauya....
Abdurrahman ya saki hannunta ya juya ya shige gidan yana murmushi....
Rumana ta juya tareda maida hankalinta akan Adeel gani tayi ya murtuke fuska, ranshi a b'ace yake kallonta, yace,
"Waye shi?".
Rumana tayi murmushi kawai, ya k'ara murtuke fuska saying,
"Tambayarki nike...".
Still bata bashi amsa ba, a tsawa ce yace,
"Rumana... Waye wannan mutunen?".


Tayi baya da sauri saying,
"How dare you? How dare you shout at me...".
Adeel yace, "Sorry...".
Tace, "Okay, amma daga yau kadda ka k'ara min tsawa, never...".
Yace, "Sure...".
Gani yayi ta fashe da dariya, ya zuba mata idanu fuskarsa dauke da mamaki, tace,
"Ka san meyyy? Murtuke fuska da kayi yayi maka kyau looking cute and handsome amma sai kayi murmushi sannan zan fad'a maka...".
Smile yayi wanda iyakarsa akan lips dinsa kawai ne, yace,
"Waye?".
Tace, "Dan uwana ne... Yaa Abdurrahman...".
"But you are the only child...".
"Adeel... Kishi... I mean my cousin... Bari inyi maka yadda bayani zaka gane, cousin dina ne, yana zaune ne a birnin tarayya Abuja, da Abba da mahaifiyarshi, uwarsu daya, ubansu daya, mahaifinshi d'an Kaduna ne amma ya rasu...".
"Miye a tsakaninki dashi?".
Rumana ta dubeshi da mamaki jin tambayar da ya jefo mata, tace,
"Na fad'a maka cousin dina ne, daga wannan babu wani abu a tsakaninmu... Idan kana tunanin akwai soyayya a tsakanina dashi, tou ka daina... That's impossible... Allah sarki, rayuwarsa tana tattare da abubuwan ban tausayi domin har wannan lokacin da nike maka magana ya kasa samun wacce zata kaunaceshi saboda Allah...".
Ta k'arasa maganar fuskarta dauke da damuwa wanda har a muryata ya bayyana, Adeel yace,
"Alright, amma idan har babu soyayya a tsakaninku, ya aka yi kika rik'e kamshin dukkanin wani turare da yake amfani dashi...".
Da mamaki take kallonsa ganin da gaske yake, yace,
"Yeah... Ai da bakinki kika fad'a...".
Kafin tayi magana wayarta dake hannunsa tayi ringing, ya duba yaga Abdurrahman ne, saida yayi jim sannan ya mik'a mata yace,
"Amsa... Shine yake kiranki...".
Rumana ta amshi wayar tareda kangawa a kunne yayinda smile yayi escaping akan lips dinta tace,
"Na'am... Shikenan yanzu zan shigo...".
Ta zare wayar daga kunnanta ta maida kallonta akan Adeel saying,
"Kayi hakuri, yace tsayuwar ta isa haka in koma gida don haka saida anjima...".
Adeel yace, "Alright, ki gaidasu...".
Rumana tace, "Za su ji...".
Sannan ta juya ta shige ciki, Adeel yayi still yana kallon kofar totally speechless, ya jima a haka kafin ya shige motarsa tareda mata key heading home....
Kai tsaye ta wuce dakin Umma inda take kyautata zaton zata sameshi, da smile akan fuskarta ta gaidashi tareda zama akan kujera, ta maida dubanta akan wayarta ganin message da Adeel ya turo mata....

_Ina kike yanzu?_

_Gani nan zaune a dakin Umma ina tunaninka_

_Rumana na sani kina sona amma ina so ki fad'a min yadda kike sona_

_Ina sonka ne kamar yadda uwa ta gari take son jinjirinta, ina sonka fiye da kaina, babu sonka a cikin jinin jikina saboda sonka wani bangare ne na jinin jikina, babu wata guguwar so da zata iya kawar da sonka daga cikin zuciyata_

_Rumana son da nike maki yafi haka, ina amanata i mean zoben dake hannunki_

_Yana nan a cikin kulawata, kamar yadda kace in kula dashi kamar yadda sonka yake manne a cikin zuciyata_

_Naji dadin hakan... Rumana ki cigaba da kula min dashi saboda hakan ne zai saka in samu kwanciyar hankali in daina waswasi akan son da kikeyi min, duk ranar da na dubi hannunka ban ganshi ba 😡 I will shout at you, 😂 sorry wasa nike amma ki kula min dashi_

_In shaa Aallah_ 😊

_Rumana... I love you_ 😘

_Adeel... I love you_ 😘

Ji tayi Umma ta kira sunanta, ta d'ago da sauri saying,
"Na'am... Umma meyyy kika ce, ban ji ba...".
Umma tace, "Dama ta ina zakiji kin duk'e kina wannan danne-dannen wayan da kika saba...".
Abdurrahman yace, "Bani wayar...".
Rumana tayi jim sai kuma ta mik'a mashi wayar ganin ya murtuke fuska....
Abdurrahman ya amsa going through chat da tayi da Adeel yayinda yanayin fuskarsa ya sauya....
Tace, "Umma ba karatun novel nikeyi ba, ina chat ne da Adeel...".
Umma ta dubeta da mamaki akan fuskarsa tace,
"Adeel dai... Mutumin da kike gama zance dashi babu jimawa shine har kuka dasa wata hirar a waya, lallai abun naku babba ne... Tashi ki zubowa Abdurrahman abinci...".
Abdurrahman yace, "Umma na koshi...".
Rumana tace, "Meyyy... Favorite food dinka ne don haka dole ka cinyeshi tas...".
Abdurrahman ya kalleta tareda danne dariya dake son kufce mashi yana hango abun da zaiyi mata, yace,
"Alright then, zanci...".
Rumana ta mike ta fita ta shiga kitchen ta zubo mashi dambun shinkafa wanda yaji kayan had'i ta saka mashi spoon tareda dauko drinks a bedroom dinta, ta ajiye a gabansa, zata mike ya mayar da ita, ko rabin abincin baiyi ba, ya tura mata plate din saying,
"Na koshi... Finish it...".
Ta ware idanu ta kalleshi ta kalli abincin, ya murtuke fuska, ta soma tsakurar abincin tana jin kamar cikinta zai fashe, ciki-ciki tace,
"Mugunta...".
Yace, "Kika ce?".
Tace, "Rumatsa... Ban yi magana ba, yaushe ake magana kuma idan ana cin abinci...".
Abdurrahman yace, "Hakane kuma...".
Ji tayi yace,
"Umma... Rumana zata rakani shopping...".
Umma tace, "Sai kun dawo... Allah ya kiyaye hanya...".
Abdurrahman yace, "Amin... Rumana ki tabbata kin cinye abincin sannan kiyi snapping empty plate din kiyi min sending in tabbatar, ina jiranki a mota...".
Ta bi bayanshi da mugun kallo, da gayya ta rink'a tsakurar abincin kadan-kadan, saida ta gama b'ata mashi lokaci sannan ta mike ta wuce bedroom dinta, ta fad'a bathroom ta sakarwa kanta shower, tana ganin miss calls dinsa tayi banza dashi, ta shirya cikin gown mara nauyi tareda zura long hijab ta rufe fuskarta da niqab, ta fesa turaruka masu saukin kamshi ta fita, bayan da tayi sallama wa Umma....
Abdurrahman yana zaune a mota ya zuro kafafunsa waje yana danna waya, ta b'alle murfin motar ta shiga, ya tsareta da idanu saying,
"Shine kika shanyani, ina kira kika ki picking...".
Rumana ta turo baki saying,
"Na tsaya emptying plate din ne kuma abincin da yawa...".
"Then wa yace ki tsaya kiyi wanka...".
Tace, "Ni...".
Ya girgiza kai tareda wa motar key, yana driving a nutse, lokaci zuwa lokaci yana juyowa ya kalleta, gani tayi ya gangara yayi parking a gefen titi, babu zato babu tsammani saidai ji tayi ya rik'e hannunta, ta dubeshi da sauri, smile yayi mata tareda zare zoben diamond dake hannunta wanda Adeel ya bata, zatayi magana ya tsareta da idanu, tayi kasa da kanta ba tareda ta samu zarafin magana ba, ya saka zoben a pocket din wandonsa, ya zaro wani karamin kit daga locker ya bud'eshi ya zaro zoben diamond wanda yafi wancen kyau da tsad'a, ya saka mata a finger, da murmushi akan fuskarsa yace,
"I love you Angel...".
Saida gabanta ya yanke ya fad'i, ta dubeshi da sauri yace,
"Yeah... Miye na mamaki don na kiraki da Angel, after all you are my favorite cousin...".
Da sauri tace,
"Hakane... Yayi kyau... Amma dai ka bani wancen....".
Gani tayi ya murtuke fuska, sai kuma yayi murmushi saying,
"I feel love...".
Ta ware idanu saying,
"Meyyy?".
Yace, "Nace abun da kikaji... Ni k'anin Abba ne, ay bashi ne, ballantana kiyi mamaki...".
Tace, "Amma ban so ka cire zoben can daga hannuna ba saboda nayi mashi alkawarin zan kula dashi kamar yadda sonshi yake manne a cikin zuciyata...".
Abdurrahman yayi wani shegen murmushi sannan yace,
"Angel... Kadda ki wahalar da kanki wajen bayani, na gani a chat da kukayi, saidai na riga na siya maki wannan zoben...".
Fuskarta dauke da damuwa tace,
"Adeel yana matuk'ar sona fiye da yadda kake tunani, nima kuma ina sonshi, hakan zai iya janyo sabani a tsakaninmu, ka bani zoben kadda kayi sanadin rabuwana da wanda nike matuk'ar so fiye da tunaninka...".
Yace, "Idan ya rabu dake sai kiyi mamu wuff da wani, misali ni, tun da har yanzu a kasuwa nike...".
Ta ware idanu, yace,
"Kadda ki damu... Don't worry Angel awww Abdurrahman Angel... Kika sani ko idan na rabaku zan hadaki ne da wanda kike matuk'ar so fiye tunani...".
Saida gabanta ya yanke ya fad'i ta zaro idanu, a razane tace,
"Who?".
Saida yayi dariya sannan yace,
"Kin fini sanin ko waye... And don't worry Angel, your secret is safe with me... Calm down kadda ki tada hankalinki, na fad'a ne kawai... Uhmm Abdurrahman Angel...".
Ji tayi zufa ta soma keto mata duk da Ac dake a motar, yana driving tana raba idanu, hankalinta a tashe, kadda dai ya gane itace....
Yayi parking a wani katon shopping mall, tayi sama da niqab dake fuskarta, ya zuba mata idanu yana murmushi, tace,
"Yaa Abdurrahman...".
Abdurrahman yayi firgigit saying
"Yeah... Angel...".
Rumana tace, "Meyyy kake tunani har haka?".
Yace, "Ina tunanin Angel dina ne...".
Sai kuma ya zaro kwalin iPhone babbar wacce take hannunta ya mik'a mata saying,
"Here you go, na sauya maki waya...".
Rumana ta amsa tareda sakin murmushi saying,
"Na gode, thanks so much, Allah ya saka da alkhairi, Allah ya jikan Alhaji...".
Yace, "Amin...".
Sai kuma ya zaro waya daga pocket din wandonsa, she thought chat yake, gani tayi ya d'ago yana wani shegen murmushi, saida gabanta ya yanke ya fad'i, bata son yana wannan murmushi, yana tada mata hankali, gani take ya riga ya gane itace, yace,
"Duba ki gani...".
Kamar ba zata amsa ba, sai kuma ta amsa, ta zaro idanu yayinda gabanta ya yanke ya fad'i a sanadin cin karo da tayi da text message da ta rink'a tura mashi a kokarinta na son taimaka mashi ya fahimci inda zai samu wacce zata soshi saboda Allah kuma ta zauna dashi koda bashi ko sisi, bata d'ago ba domin bata son ya fahimci yanayinta, idanunta akan majigin wayar trying her best to sound normal tace,
"Wacece wannan wadda take kaunarka har haka?".
Ji tayi yace,
"Ki cigaba da karantawa zaki gani..".
Ta karanta mi bayan itace da kanta ta rubuta, bata d'ago ba sannan ba tace dashi komai ba, ta mik'a mashi wayar tareda cewa,
"Na karanta, kuma nayi farin ciki da damuwarka ta zama tarihi, ka samu wadda take sonka saboda Allah... Amma mi kake tunani? Nana Firdaus ce ko Halima?".
Ya tsareta idanu saying,
"Ya aka yi kika fidda kanki bayan kema kina daya daga cikin cousin dina en mata dake a garin nan...".


Rumana ta gama tsurewa, ta sadakar wa kanta cewa ya riga da ya ganota, an yanka ta tashi, amma duk da haka ta dake saying,
"Na cire kaina ne saboda nasan bani bace...".
Abdurrahman yayi wani shegen murmushi sannan yace,
"Ni kuma kinga ke na fara sakawa alamar tambaya kuma har yanzu a saman kanki take...".
Rumana ta zaro idanu yayinda gabanta ya yanke ya fad'i shikenan ya gane ita ce, ji take kamar ta d'aura hannu a ka ta fasa ihu, gabanta ne yayi wata mahaukaciyar fad'uwa amma da yake shu'umi ne sai ya basar yayi kamar bai lura ba, yace,
"Idan muka koma gida zan bud'e maki instagram, likee da snap chat kinga sai mu rink'a musayar pictures ni da Abdurrahman Angel... Ki rage razana da yawa haka, ay sai ki saka asarinki ya tonu before it time... Beside you don't have to worry yourself cox your secret is safe with me... Uhmm...".
Tareda amsar wayarsa, ya b'alle murfin motar ya fita tareda zagayawa ya bud'e bangaren da take, saida ta maida niqab dake a fuskarta sannan ta zuro kafafunta tareda fitowa, ya saka hannu ya zare niqabin tareda kashe masu hoto, ya mayar da niqabin a motar saying,
"Hotuna zanyi mamu, kiyi yadda kikaga nayi...".
Ya d'aga wayar sama tareda turo baki, itama ta turo baki ya kashe masu selfie, yayi masu snapping pictures sosai, ya duk'e yana kallonsu, ta matsa kusa dashi tareda lek'awa tana gani kuma sunyi kyau sosai, yace,
"Let go...".
Suka jera suka shige ciki, ma'aikatan wajen suka rink'a kwasar gaisuwa a wajen boss dinsu, saida ya gama gaisawa dasu sannan ya wuce ofishinsa, katon office mai girma komai yaji ban da barkono a idanun tsohuwa 😂 ta zauna akan kujera dake gefe yayinda shi kuma ya zauna akan kujerarsa yana jujjuyawa da ita yana kallonta yana murmushi, manager ne ya shigo suka gaisa, yace,
"Manager kaje da Angel ka had'ata da wani ya rik'e mata trolley tayi shopping, here's my card ku cire kudin idan ta gama, and here's my car key ku saka a ciki...".
Manager yace, "Sure rank'a ya d'ad'e...".
Abdurrahman yace, "Angel ki bishi kuma ki tabbata kinyi shopping da yawa other wise uhmm bazan fad'a maki...".
Manager yayi gaba, Rumana ta mik'e tabi bayanshi, shopping tayi sosai gudun abun da yace zaiyi, beside ita tsoro yake bata yanzu, sai yayi kamar ya gane itace sai kuma ya goce, bayan ta gama manager ya rakata ofishin Abdurrahman ta zauna ta jira ya gama abun da yake sannan ya mik'e suka wuce, ya bud'e mata bangaren mai zaman hakanan ta shiga sannan ya zagaya, manager ya bud'e mashi bangaren direba ya shiga, yayi mata murmushi yana driving a nutse, saidai gani tayi yayi parking a wani katon restaurant, ya fito tareda zagayawa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment