Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tsaye tana jiran shigowarsa palon.

Da qaramar murya yace,

Sabhaul khair ya ammy.

Kai kawai ta daga masa sbd masiffen tashin hankalinda tasamu kanta aciki na fargabar kar ace tunaninta na cikine da rumanah ya tabbata.

Dakinta takoma ta zauna jira ganin yashiga dakin tareda turo qofa.

Zaune take bakin gado tana ganinsa taji idanuwanta sun ciko da hawayen muguwar kewarsa datayi batasan lokacinda ta miqe ta fada jikinsaba ya lumshe ido tareda qara shigarda ita jikinsa.

Jin zafin jikinta yasashi dagota yakalleta cikin wata irin murya yace,

Qafan ne?

Girgiza kai tayi tana kallonsa.

Da gira ya yayi mata tambayar then wat is it.

Zamewa tayi taje bakin gado ta zauna cikin sanyin murya tace,

Ciwon kai.

Zama yayi bakin gadon tareda dago fuskarta yayi kissing bakinta yasake taba jikinta yaji zafin
Baice mata qalaba ya zare rigarsa tareda ajewa ya kwanta kan gadon tareda lumshe fararen idanuwansa

Saidata aje numfashi ahankali kafin ta nufi gadon ta hau tashige jikinsa tareda qanqamesa sukai shiru kowanne najin bugun zuciyar dan uwansa yanaji zafin jikinta na shiga jikinsa ahankali ya saki wata irin boyayyar ajiyar zuciya.

Daga haka baccin dabasuyiba adaren ya daukesu ammy dake zaman jira tashigo dakin tayi saurin juyawa ganin yanda sukai bacci hankali kwance.

Kasa zama tayi ta kasa tsayuwa sbd idan har cikineda rumanah to yazama dole aciresa sbd tsoronta na bata rumanah zata iya haihuwar namiji Wanda hakan shine babbar masifar dazata tono abubuwa ciki harda yanda iyayen rumanah din suka rasu.
#mamuhgee.
[15/07, 02:16] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationšŸ’”_



*25*
Not edited
Zama tayi tareda rafka tagumi cikin zullumi da rashin sanin madafar tunaninta
Abu 'daya tasani shine tana tsananin qaunar rumanah kamar itace ta haife musamman a yanxu datake hango soyayyarta mai tsanani a idanuwan Maheer 'dinta saidai duk wannan qaunar da yardar zata rushe tazama qiyayya da tsana mai tsanani idan sirrin rasuwarsu asma'u da bulama ya bayyana ga rumanah abinda bazatasoba kenan.

Qarfe goma da mintuna goma sha biyu suka farka yatashi zaune tareda tayarda ita zaune yana gyara mata gashinta daya barbaje.

Kallonsa tayi tareda sakin kasalallen murmushi
Ya shafi gefen fuskarta tareda bude baki yace,

Yaya?

Lumshe ido tayi cikin laushin murya tace,

Yayi sauki yanxu banajin ciwon kan.

Lumshe ido yayi tareda jinjina kai kafin yakalli agogo yace,

Ya salam" yana sauka daga kan gadon.

Tare suka shiga toilet din dakinta sukayi wanka Wanda yadaukesu dogon lokaci sbd tsayawa shiririta.

Koda suka fito kan cinyarsa ya zaunar da ita tana goge masa ruwan jikinsa yana kallon gashinta dake 'digo masa ruwa sbd wasan dasukai acikin bathtub yasa dole suyi wankan tsarki.

Riqo hannunta dake goge gashinsa yayi tareda Shafo gashinta har zuwa fuskarta ya zarce cikin towel dinta ya shafo cikinta dake lafe yana kallonta cikin wani irin yanayi da galabaita da zuciyarsa ke ciki.

Daqyar ya bude baki cikin wani irin taushin murya yace,

I have something precious inside you so daga yanxu bazaki sake ganin albinon malaminkiba sbd gudun daukar jajayen ido da qaton baki.

Murmushi zancensa yasa tasaki tareda zare hannunta taci gaba da goge masa gashi batareda tace komaiba.

Sake riqe hannunta yayi yana tsareta da ido yace,

I will miss this smile dakikeyi danki hanawa suhailat mijinta.

Kallonsa tayi gabanta na faduwa sbd jin sunan suhailat yasatajin faduwar gaban ta sunkuyar dakai tareda tashi daga jikinsa ta dauko hand dryer ta jona tafara busar masa da gashinsa mai tsananin laushi.

Shidakansa ya shiryata cikin pink gathered neck top da black straight skirt ta Sanya black hula ta fito ta nufi dakin sa ta dauko masa kayan dazai saka takawo masa yasaka suka fito palon hannunta na cikin nasa tanata 6anbare hannunta amma takasa ahaka yajata har gaban ammy dake sintiri a tsakiyar bedroom dinta tana ganinsu tasaki murmushin qarfin hali tana qarajin tausayinsu dan ko ayanxu datake ganin yanayinsu bama zasu iya rabuwa da junaba saidai duk soyayyarsu qila basuda rabon hada zuria sbd bazata so rumanah ta zamto itace zata fara haifarwa maheer namijiba gwara dai wata kokuma suhailat duk da itama bazataso wani Abu yasametaba saidai so sone amma sonkai yafi.

Cikin kulawa tace,

Rumanah yajikinki?kan yadaina ciwo ko?

Kai ta daga tana sake janye hannunta amma Sam kamar bashine riqeda hannunba.

Abinci sukaci a dining ammy madai hartafi rumanar jin kunyar abinda maheer din kemata kuma ko ajikinsa tamkar bashine yakeyiba.

Daqyar sukaga sungama ammy tarigasu barin gurin tana girgiza kai sbd batasan haka 'danta yake 'dan duniyaba.

Ammy na barin gurin takallesa kamar zatayi kuka yazuba mata ido tareda sakin wani miskilin murmushi kafin ya miqe tsaye ya ranqwafa yayi kissing kanta yace,

Ki kula.

Ya fice yana duba agogon hannunsa sbd lokacin tafiyarsa yayi sosai.

Bayansa tabi da kallo hawayen datake riqewa suka gangaro tasa hannu ahankali tashare tareda miqewa ta nufi dakinta ta zauna bakin gado sai kawai siririn kuka ya kufce mata.

Yini tayi adaki kwance bayan sallah babu abinda ke tayarda ita ko abinci yau ammy daki tasa aka kai mata sbd ta fahimci halinda take ciki na tafiyar maheer 'din.

Da daddare ma kasa bacci tayi harsai kusan asuba ya saceta koda ammy ta leqo taga bacci takeyi bata tadataba sbd tasan balallaine tasamuyin bacci da daddare ba.

Koda gari ya waye sosai guraren qarfe goma ammy tadawo ta tararda ita cikin wani zazzafan zazzabi nan hankalinta yafara tashi musamman yanda jikinta yayi wani mugun zafi banda amai babu abinda takeyi

Ganin abin na girmama yasata sanarda s salma nan aka kirawo Dr faduwa tazo tadubata tareda fara mata pregnancy test dan karta maganin da baikamacetaba awon farko ciki ya tabbata nan ammy taqara shiga damuwa ga farin ciki ga fargabar abinda zai iya zuwa yadawo.

Magani tarubuta tareda Wanda zaita tasamu dan bacci kota huta daga aman.

Kallonta ammy tayi bayan fitar Dr faduwa tasauke ajiyar zuciya tareda mata sannu cikin tsananin kulawa da qaunarta.

Abinci ammyn tasamu taci daqyar kafin tayi sallah tayi wanka ta kwanta wani sabon baccin yayi gaba da ita.


Tunda yatafi bata sake lafiya ba sosai ciwo ya kwantarda ita komai taci baya zama cikinta
Duk inda hankalin ammy yake ya ninka tashi drip kuwa tasha ledoji qarshemadai daina samata ruwan akayi.

Batasan 'daga masa hankali kokuma shiga haqqin suhailat shiyasa bata fada masa saidai duk yanda taso tare alamarin fin qarfinta yayi dan yanxu wata biyu da tafiyarsa ga mamakinta cikin harya fara tasawa gashi har lokacin ko zaman arkiqi bata iyayi koyaushe akwance take.

Gyara zama tayi ta fuskanci Dr faduwa cikin nutsuwa da damuwa tace,

Yanxu wata hudu kenan cikin yake?

Abinda scanning dina yabani kenan"" dr faduwa tafada tana sake kallon takardar scanning din.

Cikin tsananin damuwa sultana takalli Dr fadwa tace,

Inason axubarda cikin tunda yaqi bata lafiya wuyardatake sha tayi mata yawa banason wani Abu yasameta tunda mijinta baisan dashiba.

Kallonta Dr tayi cikin nazarin zancenta sbd tanaga idan anyi hakuri duk wannan wuyar zata wuce duk da itama tana tsananin tausayin rumanah din.

Cikin nutsuwa tace,

Inaga tunda haryakai wata hudu aqara hakuri idan yakai wata bakwai duk wannan wahalar zata rage sosai.

Girgiza kai ammy tayi cikin damuwa tace,

Acire kawai shine abinda nakeso yanxu.

Kallonta Dr tayi cikin nazari kafin ta bude jaka ta fiddo takarda ta rubuta allura tace aje yanxu akawo zatayiwa rumanah din sai zuwa dare idan ciwon mara yataso idan tafara zuba sai akai mata ita asibiti.

Cikin qanqanin lokaci ammy tasa akaje aka kawo allurar nan suka nufi dakin rumanah dake kwance tana baccin datasamu yadan dauketa.

Yawu masu 'dacin damuwa da wasi wasi ammy ta hadiye cikeda tsananin tausayin rumanah dakuma takaici da baqin cikin abinda zatayi

Bude ido rumanah tayi cikin wani irin laushin ciwo suna hada ido da ammy
Ammyn tayi saurin sunkuyar dakanta sbd tasan haqqoqan rumanah bazasu barsuba komai daren dadewa saidai idan har zubar mata da ciki shine abinda zai kare mata ita daga masifar mineelik to ashirye take data ringa zubar mata da ciki idan tasamu.

Cikin tausayawa Dr ta kalli rumanah tace,

Sannu rumanah,
Allura za'ai miki kisamu 'dan qarfin jiki.

Murmushi qarfin hali tasaki daqyar tareda 'dan muskutawa tabada bayanta cikin nutsuwa tasoka mata allurar tayi mata tana mata sannu.

Saurin barin dakin ammy tayi sbd hawayen dake qoqarin ciko idanuwanta
Cikin tsananin sanyin murya takalli Dr faduwa data fito dakin tace,

Awa nawa allurar zatayi kafin cikin ya lalace yafara zuba sbd........

Wani wawan jiri taji yayi mata muguwar diba tana kallon qofar palon saida Dr ta riqota tareda juyawa itama sukai ido biyu dashi tsaye yana kallonsu babu mai iya gane yanayinsa acikinsu shiya mugun tayarda hankalinsu.



Manage wlh ciwon kai ke damuna yau.
#mamuhgee
[16/07, 00:25] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationšŸ’”_



*26*
Haske writers associationšŸ’”



*_Dan Allah daga yanxu yanzu idan kasan labari baya maka dadi zaifi idan zaka daina bi sbd wata maganar batada dadi kuma kowane marubuci idan harya fara rubuta labari to shi yasan saqon dayake son isarwa kuma idan har mai karantawa yayi hakuri ahankali zai riqa fahimatar abinda akeson isarwa dan haka pls mu riqa sanin maganar dazata fito bakinmu,_*
*_Nidai nasan abinda nake rubutawa idan kasan baka iya_* *_magana mai dadiba to zaka iya tsayawa daga nan sbd bazanso kaci gaba dabiba dan abinda zaizo agaba._*



Not edited.
Ammy ya qureda idanuwansa dasuka mugun qara sanyata damuwar abinda tayi muryarta na rawa takira sunansa daqyar.

Ya lumshe idanuwansa yasake kallonta Dr faduwa na ganin haka ta sulale ta fice dan ita ko kallo bata ishesaba.

Gaban ammy yaqaraso ya tsaya cikin wani irin yanayi na tsananin 6acin rai da bata ta6a ganinsa acikiba yace,

Bantaba samun tarba irin wannan ba ko sakin fuska babu bare murmushinki da murnarki.

Da mamaki ta kallesa da sauri zuciyarta na qara tsinkewa dan kuwa abinda take hangowa acikin idanuwansa ta tabbarda yajisu.

Murya cikin sanyi da tsananin damuwa tace,

Maheer nasan kaji komai amma dan Allah inaso ka fahimci manufata tayin hakan dan nikaina ba'ason raina nayi hakan ba wlh zanfi kowa farin cikin ganin rumanah ta haifa maka 'yaya saidai I can't risk her life.......

Oh please ammy karki fara kawo maganar risking life anan sbd babu Wanda ya isa yahanawa bawa shiga qaddararda Allah ya dora masa,
AmmyĀ  kinsan meyasa kuke wahala da masifar mineelik haryansu shine sbd kuna sake qarfafawa abin ne,
Meye alaqar 'yayana da wannan tunanin naki dazaki min haka?
Meyasa zaki rabani da abinda ko hannuna bai shigaba?
Shin ammy ina iliminki da saninki yayi dazakiyi tunanin namiji zata haifa bayan bakida masaniyar hakan......

Cikin 'daga murya da takaicin abunda ke faruwa ayanxun tace,

Kana tunanin ina nuna kamar nasan zata haifi namijine shiyasa nayi hakan?
Amatsayina na uwa nayi hakan sbd sanin matsayin dazata hau idan ta haifi namiji Wanda kasan mezata zama idan harta zauna wannan matsayin musamman da jinininta bai zamto na sarautaba saitafi wainda suka gabata zama baraza da abin fargaba......

Cikin tsananin baqin ciki ya katseta da cewa,

Rumanah har abada bazata ta6a hawa wannan kujerarba koda ta haifi namiji koda hakan na nufin ni nakar6i mulkin zan karba ni nazama masifar......

A tsawace tace,

Ka riga karasa wannan damar ta zauna throne 'din mineelik tun lokacinda kace baka karbi magajin mineelik ba dan haka ko kanaso kabaka ayanxu atarihince 'dankane yanxu yakeda cikakken ikon karbar mulkin mineelik kuma kafin ya girma mahaifiyarsace kawai takeda ikon bawa duk Wanda taga damar riqon qwaryar mulkin 'danta idan kuma taso ta itace dakanta zata.......

Idan angansu kenan a mineelik 'din...yafada zuciyarsa na qarasa daukar zafi.

Itama cikin zafi tace,

Wannan ne baka isaba sbd labarin cikin na isa a kunnen sultan bazata qara ko kwana biyu ba'a mineelik ba dan haka zabi ya rage naka kodai acire wannan cikin kodai rumanah ta rasa rayuwarta amatsayin rumanarta......

Ayau da wanine agabana bake mahaifiyata ba da bazai sake ko minti 'daya da kansa a gangar jikinsaba,
Zuciyarsa tariga tagama 'daukar wuta bazai iya cigaba da maganaba ya wuceta ya nufi dakin rumanah dake kwance lamo tanaji mararta na murda mata ahankali saidai ko wani qwaqwaran motsi bata iyayi saidai jikinta dayayi mummunan sanyi hakanan takejin maraicinta na taso mata.

Qamshinsa taji yashiga hancinta ahankali ta bude idanuwanta dasukai laushi takalli qofa tagansa tsaye cikin yanayin dabata ta6a ganinsa ba ta lumshe ido sbd tasan idanuwanta ne kawai ke ganinsa sbd zuciyarta tasamu sukuni.

Qarasowa yayi baice komaiba ya dauketa cak ya nufi qofa da ita ya fito ammy dake zaune palon ta rafka wani mugun tagumi cikin tsananin damuwa da zullumi
ta miqe tana kallonsa yazo yatsaya gabanta cikin danne halinda yake ciki yace,

Komawa zanyi idan ta sauka zankawo miki ita.

Kafin tayi wata magana ya wuce yabarta da baki bude idanuwanta dasukai jajir suka ciko da qwallan damuwa ganin tun yanxu alamura na neman ca6ewa.

Wani babban private hospital ya nufa da ita tun ahanya yasa akai musu booking flight koda suka isa harta fara fita hayyacinta sbd jinin daya 6alle mata sosai.

Cikin gaggawa aka fara dubata dan tsaida jinin dayake suma doctors din asibitin qwararrine yashiga cikinsu dan baibari kowa yataba masa itaba,
Cikin ikon Allah suka samu nasarar tsaida jinin batareda cikin ya zubeba saidai kwata kwata baza'aso taringa babban motsiba sbd anriga antaba lafiyar cikin dole saiya kwana biyu yasake qarfi.

Adakin datake kwance yashiga toilet ya wanke jikinsa tareda canxa shirt sbd sosai jini ya 6atasa.

Sunsamu ticket din da asuba jirgin zai tashi shiyasa yasake mata wasu injections sbd motsin daza'ai da ita
Yana zaune sofa din dake dakin akai kiran asuba ya tashi yayo alwala yayi sallah yana idarwa babu bata lokaci akai rubuce rubucen daza'ai suka nufi airport cikin ambulance ko mintuna ashirin basuyi da isaba jirginsu ya 'daga.

Da rana tsaka suka isa Georgia direct motar asibitinsa tazo ta daukesu suka nufi asibitin nan aka fara bata sabon treatment likitocin basu zaunaba saida suka sake tabbatarda komai is back to normal.

Baibar asibitin ba saidata farka ta bude idanuwanta dasukai nauyi takallesa tareda lumshe ido sbd ba qwari ajikinta sosai.

Matsowa gabanta yayi yatsaya tareda kallon cikin idonta ya riqo hannunta tareda sakar mata siririn murmushi ahankali ya furta,

Hey yene konjo(my pretty)

Kallonsa tayi fuskarta na bayyanarda farin cikin ganinsa dakuma sunan daya kirata dashi.

Da kansa ya dagata yadauketa yakaita toilet yayi mata wanka yacanza mata kaya patients sabbi ya rasa yanda zaiyi ya daure mata gashinta dole yahaqura yabarshi asake yabata tea tasha yabata magani da sauran injection dinta kafin yayi kissing goshinta yafice.

Koda ya isa gida qarfe tara na dare lokacinda suhailat tagansa bude baki tayi tana kallonsa cikeda mamakin ganin jiya yatafi amma yadawo yau bayan batasaka ran dawowarsa da wuriba.

Rungumesa tayi cikin danne mamakinda tace,

Hey welcome.

Rungumeta yayi tareda sakin ajiyar zuciya da 6oyayyan numfashi sbd shikadai yasan halinda zuciyarsa ke ciki ayanxu sbd tabbas yasan akwai rigima agaba saidai bazai ta6a bari rumanah ta Shiga abinda kakannin kakanninsa suka aikatoba koda hakan na nufin shi yafadawa abinda yayi gudu tun qurciyarsa matuqar hakan shine zai kare rumanah da abinda zata Haifa so be it.

Bedroom dinsa suka nufa ya tube yashiga wanka itakuma ta nufi kicin tacewa Carolina ayi abincinda akasan maheer din naci.

Daga haka takoma dakinsu amah tasanardasu dadynsu sundawo suka fito da tsallen murnarsu.

Sakin fuska da jiki yayi sosai dan gudun shiga haqqin suhailat 'din da yaransa saidai cikin zuciyarsa damuwace mai tarin yawa duk da kasancewar cikin ya tsaya damuwa batabar zuciyarsaba musamman dayasan dole zasu koma mineelik sbd ammynsa takoma 'dakinta badan hakaba bayajin rumanah zata koma mineelik.

Sosai suhailat ta lurada akwai abinda yake ransa na damuwa duk da abune mai wuya ka iya gane yanayinsa.
Batason tana shiga abinda bai shafetaba musamman yanxu dayakeda wata matar kuma 'yar 'dakin ammynsa dan haka shishigi kan abinda babu ruwanta ba nata bane sbd kartajiyo abinda zai sakata damuwa.

Fruits kawai yaci koda suka zauna dining kuma harsuka gama bai yiwa kowa maganaba duk da ko yaransa sunsaba da miskilancin daddyn nasu sbd kosu wani lokacin idan abin ya motsa baya iya yimusu doguwar magana saidai idanuwansa dake ladaftar da mutum.

Da daddare koda yakira wayar Dr olie yasanar masada tasamu bacci tundazu.

Kallonsa suhailat dake kwance jikinsa tayi still taqi tambayarsa meke faruwa bayan taji da hospital yake magana batai la'akari da ko ammynsa ceba dayake yasaba da haka take shiyasa bai tsaya tunanin banxa akan hakanba da haka tai bacci cikin jikinsa ya qurawa kyakkyawar fuskarta ido hakanan yakejin tausayinta sbd ba ita yakeji cikin tsakiyar zuciyarsaba,
Bayajin fitar kowane numfashinsa da ita aciki saidai tanada wani irin girma da qima a idanuwansa ta yanda bazai iya barin ta quntatu akan abinda yake tsananin so ba.

Rufe idanuwansa tareda dakin 6oyayyar ajiyar zuciya.

Qarfe bakwai yafito wanka yakalli suhailat data shigo dakin batareda yakalletaba yana gyara gashinsa yace,

Carolina ta hada breakfast na mutum 'daya a basket and it should be something light.

Kallonsa tayi tana zaunawa gefen gadonsa tace,

Ok amma pls who is the patient?

Batareda yabar abinda yakeyiba yace,

'Yar ammy.

Da mamaki ta kallesa tace,

Bansan waye haka ba.

Then kibarshi idan anyi discharging nata zaki ganta.

Miqewa tayi tazo gabansa ta tsaya tana kallonsa yana saka rigarsa tace,

Ok zanbika muje tare nadubata ko waye tunda hanyar zuwa office dina ne.

Baice komaiba yagama shirinsa suka sauko tana maqale da hannunsa.

Da gudu su amah dake qoqarin zama a dining sukayo gurinsa yasaki fuska cikin kulawa yayi pecking kowannensu yana cewa,

Good morning to sweets angels.

Good morning to you too daddy""suka fada suna kissing kumatunsa both sides.

Dining suka nufa dukkaninsu sukai breakfast
Shidai daqyar ya iyacin toasted bread one slice da black tea yamiqe
Suma dai dayake sun gama suka dauki school bags dinsu suka fito dukkaninsu Carolina tabiyosu da basket 'dinda aka shirya breakfast dinda yace.

Motarsu amah daban driver yafara wucewa kafin yashiga Lamborghini dinsa suhailat tashiga yaja suka fice daga gidan.

Koda suka isa asibiti suna shiga reception yatsaya batareda yajuyo gefentaba yace,

Kije room 36 zanzo idan naga drĀ  Andrew.

Ok tace tareda kissing hannunsa ta wuce da basket din ahannnunta.
Shikuma kai tsaye office dinsa ya nufa.

Tana isa qofar dakin ta tsaya tareda Sauke ajiyar zuciya dukda batasa waye acikiba ta murda qofar tashiga.

Zaune take tsakiyar gadon nurse na gyara mata kanta daya barbaje yana damunta.

Tsayawa tayi tsakiyar dakin qafafunta na rawa gabanta yayi mummunan faduwa ganin rumanah ce,

Ahankali tasauke idonta kan qaramin cikinta daya fito ga wani haske mai firgitarwa dataga tayi.

Fita numfashinta yafarayi dasauri wani irin zufa ya karyo mata amma saitayi saurin kiran sunayen Allah acikin zuciyarta kafin tasauke numfashi mai sanyi tasaki murmushin qarfin hali tareda qarasowa bakin gadon inda rumanah ta tsareta da ido itama numfashinta na fita da sauri amma ganin tasaki fuska yasata qaqalo murmushi tana cewa,
Sannu da zuwa.
#mamuhgee.
[17/07, 01:12] 80k: *_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationšŸ’”_



*27*
Aje basket din hannunta tayi tana sake qaqalo murmushi tace,

Ashe kece babu lafiya baby baifadaminba kawai yafadamin numbern dakin ne,
Sannu ya jiki?

'Daga kai tayi ahankali tana cewa,

Alhmdllh.

Shiru dukkaninsu sukayi babu wacce numfashinta bai fita da sauri sbd ganin 'yar uwarta.

Suhailat cikin jikin rumanah din take satar kallo dan kuwa batasan haka take kishin mijintaba saidataga cikin dan kuwa Allah ne kadai yasan irin ciwo da radadin datakeji axuciyarta saidai tana qoqarin fincikewa sbd batason zubarwa da kanta qima a gurin mijinta da 'yayanta harma da rumanar datake kishiyarta.

Rumanah kuwa jitayi duk atakure take da wanzuwar suhailat din gashi nurse tagama abinda takeyi ta fice.
Hakanan takejin bata iya kallonta sosai sbd ganin take zuciyarta da shaidan zasu hasaso mata maheer atareda suhailat din Wanda hakan na matuqar girgiza zuciyarta.

Cikin kulawa suhailat ta miqe ta bude basket din ta hada mata black honey tea sai pancakes da toasted chicken datai laushi sosai ta zuba matasu a plate tareda aje matasu yanda zata iya ci.

Cikin sanyin murya rumanah tace,

Nagode amma inaso zanshiga toilet....

Wayar suhailat dince tayi ringing ta sauka da sauri sbd mum 'dintace batareda taji mai rumanah din ke fadaba ta fita dan amsa wayar.

Ganin ta fita yasa rumanah sauke qafafunta qasa ahankali ta sauko ta nufi toilet din dake dakin ahankali sbd jiri.

Tana kaiwa tsakiyar dakin wani irin jiri ya dibeta daidai shigowarsa dakin.

Saida tajita jikinsa tayi saurin sakin ajiyar zuciya sbd ta sadaqarda cikinta yagama zubewa idan ta fadi.

Bude idanuwanta data rintse tayi takallesa cikin fargaba sbd ganin kallon dayake mata murya na rawa tace,

Toilet zanshiga.

Yanda ya dauke gira daya yasa tasan menene azuciyarsa tayi qasa dakai cikin tsananin sanyin murya tace,

Yi hakuri bansan zan.....

Just shut up"""yafada yana daukarta gaba 'daya ya bude toilet din suka shige.

Sauketa yayi ahankali kamar kwai
Ta dago takalli fuskarsa taga ba wasa tasaki 6oyayyan murmushi cikin zuciyarta tana cewa,

Ko fushi kyau yake masa.

Brush ya miqa mata ta karba tayi tana kallonsa sbd kallonsa yanxu matuqar nishadi da nutsuwa yake bata tana gamawa ya miqa mata towel tareda jawota jikinsa yazare mata kayan jikinta itadai ido kawai take binsa dashi sbd yau ko ta6insa nutsuwa yake bata.

Da yake shower ce bai shigaba ita kadai tashiga tayi wankan shikuma yana tsaye gaban mirror yana goge inda rigarsa ta baci da ruwan allurar dayaje yiwa wani patient kafin yashigo dakin.

Tana gama wankan ta dauki towel ta daura tareda zare shower cap din kanta ta tsaya gaban madubin da yake dubawa tana fuskantarsa.

Wasu kayan yasanya mata saidai bada bra ba duk saiyaji ransa yabaci da yanda kayan patients din sukai mata kyau amma bai nunaba yasake gyara mata gashinta ya dauketa suka fito tana kallonsa gira 'daya ya dauke yace,

Wannan kallon fa matata tana nan so be carefull bata hadani da komaiba.

Murmushi daya bayyana fararen haqoranta tasaki tareda sake qanqamesa tana fitarda sautin murmushinta ahankali
shima murmushin gefen baki yasaki suna kawowa tsakiyar dakin sukai ido hudu da suhailat dake zaune tayi musu kallo 'daya ta dauke kai tana qoqarin danna kira awayarta.

Saurin saukowa jikinsa rumanah tayi sbd taji nauyin suhailat din sosai koba komai ka girmama mai girmama kansa ta zauna bakin gado tana suuke kanta qasa.

Kallo 'daya yayiwa suhailat yagano halinda take ciki yaji tabasa mugun tausayi sbd baisan lokacinda ta dauka azauneba gashi sun dade aciki gashi qila batasan yana cikiba.

Hannu yakai yakamo hannunta tareda miqar da ita ya matsota gabansa yana kallon cikin idonta datake qoqarin 6oye halinda take ciki cikin kulawa yace,

Are you ok?

Kai ta 'daga masa batareda yakallesaba
Yayi kissing forehead dinta yace,

I will be in my office""yasa kai yafice yabarsu.

Jawo abincin rumanah tayi tafara ci hannunta na rawa sbd rawar da zuciyarta keyi.

Suhailat ma batareda takalli fuskar rumanah din ba tace,

Zantafi office am getting late Allah yasauwaqa.

Tana gama fada ta dauki handbag dinta ta fice hawayen datake riqewa suka gangaro mata ko office dinsa bata biyaba ta wucewarta saidata isa office dinta ta rufe siririn kuka ya balle mata amma dannesa tashigayi sbd bataga dalilin kukanba tunda dama tasan tanada kishiya meye abin jin zafi dan taganta da ciki bayan itama Allah yabata nata 'yayan ba juya yayitaba.

Saidata samu nutsuwa tayi masa text tace ta wuce office and she's very late so shiyasa bata biyo office dinsaba.

Tana ficewa rumanah ta aje breakfast din sbd dama turawa kawai takeyi.

Yana gama karanta text dinta ya aje wayar tareda lumshe fararen oily eyes dinsa.

Yinin ranar dukkaninsu a darare sukayisa sbd kowanne da abinda ya maqalewa zuciyarsa.

Baibar asibitin ba yau sai qarfe goma na dare lokacinda rumanah tayi bacci kenan.

Koda yakoma gida suhailat bata nuna damuwar komaiba a fuskarta itada 'yayanta su maqalqalesa suna masa oyoyo
Yayo wanka bai sauko cin abinciba sbd yaci pizza tareda rumanah a asibiti.
Koda suhailat taji cewar yayi dinner murmushi kawai tayi tace,

Ok bari nacewa Carolina tasaka a fridge.

Kodata dawo dakin yana kwance wayarsa a kunnensa yana magana da antynsa wadda yake biwa tana qara basa haquri akan abinda yafaru shidai kunnuwane kawai nasa baya iya zuba dogon zance.

Kwantawa tayi ajikinsa tareda rungumesa ta rufe ido alamar bacci
Yayi mamaki sbd basu cika kwana daki dayaba koman dare wani lokacin dakinta take komawa ta kwana.
Koda yagama wayar tayi bacci yakalli fuskarta kafin ya lumshe idanuwa fuskar rumanah daya baro tana barci tafado masa yasake rungume suhailat ajikinsa yana kamar rumanah ce ajikin nasa.

Washe gari ma tare sukaje asibitin saidai ko zama batayiba gaisawa kawai sukayi ta wuce gurin aikinta sbd ganin irin kallon da maheer kewa rumanah sbd sai yanxu cikinta yafito dakyau sbd kayan da aka canxa mata sunso kamata saikuma basu kama 'dinba.

Bayan wucewar suhailat nurse 'din dake kula da ita ta fita sbd idan yashigo fita sukeyi.

Kallon 'dan cikinta yayi batareda ya amsa gaisuwartaba ya dauki file dinta yafara dubawa.

Qamshinsa daya cika dakin ta shaqa tana lumshe ido cikeda qaunarsa mai zafi dake cin zuciyarta.

Yana gama dubawa ya kalleta a miskilance yace,

Did you bleed today?

Girgiza masa kai tayi kala kallonsa ya juya yafice baisake cewa komaiba.
Numfashi tasauke a sanyaye ta zame takwanta.

Kwananta biyar a asibitin akayi discharging dinta tunda suka kamo hanyar gida numfashinta ke fita da qarfi
Jin tayi tafison komawa Libya gurin ammy hankalinta zaifi kwanciya acan.

Suhailat ma tunda tasan zasu dawo gida anyi discharging dinta jikinta yake sanyaye.

Carolina tagyarawa rumanah dakinta tun na farko sosai.

Qarfe goma sha

Please Login or Register in order to submit comment