Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


Ta hargitse tarasa abinyi gabaki daya ta birkice shikansa ta hanasa ganin kanta bare yasan meke faruwa babban tashin hankalin daya riskesu shine sanarwar da akayi za'a bawa uwar magajin mineelik kujerarta ta uwar sultan.

Sam ammy ta rasa ina zata saka kanta shikansa baya cikin nutsuwa sbd bazai taba bari ta karbi sunan uwar sultan ba gashi dole zata karba itace zata bawa duk Wanda takeso riqon kwarya.

Yau kwanansu biyar da haihuwar dukkanin yaran suna sashen ammy tun safe.

Tunda sukazo abeel hassan ke kuka sosai anmayardashi gurin hamaifiyarsa saima qara birkicewa da yayi nan hankula suka tashi tuni sultan yasa atara duk masu magani da likitocin mineelik amma sai qara rikicewa yakeyi nan hankalin rumanah itama yayi masifar tashi ta rikice.

Cikin tashin hankali suka dunguma zuwa royalhall inda ake duba yaron kowa hankalinsa atashe yake.

Kallo daya yayiwa rumanah yaji lissafinsa yasake kwancewa kafin yayi wani yunquri sarkin gida yossouf Kaleb yashigo jikinsa na matuqar rawa ya zube gaban jakadiya yayi mata magana qasa qasa hankali tashe jikinsa na wani irin mazari.

Zaro ido Jakadiya tayi cikin sabon tashin hankali jikinta yadauki muguwar rawa kowa hankalinsa nakanta anajiran jin saqon menene
Ta zube gaban sultan tareda sauke kanta jikinta na tsananta rawa cikin muryar tashin hankali da tsananin fargabar rasa rayuwarta tace,

Allah yataimaki sultan ina cikin baqin cikin sanardakai ankama baiwa mamani da dafin baqin maciji tabawa abeel Hussain da jemaal antabbatarda sun rasu saidai ankamata.

Rumanah dake zaune ta miqe a firgice jikinta na rawa saidai ko daga qafa batayiba ta yanke jiki ta fadi agurin.

Cikin tashin hankali yayi kanta kai tsaye yadauketa yabar palon su ammy na mara masa baya hankali tashe musamman sultana da a sashenta suke shaf tashin hankalin abeel hassan yasa suka mantasu acan.

Sultan kuwa numfashi ya sauke cikin wani irin yanayi ya miqe tsaye idanuwansa na canzawa.


Suhailat na zaune tana shan magani daqyar sbd ciwon ciki da jirin datake fama dashi tun safiyar yau din
Jakadiya ta shigo mata.

Murya na rawa tace,

Ina neman afuwar saqon baqin cikin danazo dashi Allah yakarbi ran jemaal........

Bata qarasaba suhailat ta miqe tsaye atake jini ya 6alle mata ta yanke jiki ta fadi.
#mamuhgee

*_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationšŸ’”_



*33*
_A gaggauce_
Cikin tsananin tashin hankali Jakadiya tasa akayiwa Dr ammenen kiran gaggawa koda ta iso itama hankalinta tashe yake da jin abinda yafaru atake suka fara qoqarin tsayar da jinin daqyar yarage zubowar sosai saidai bata farkaba sbd allurar dasukai mata sbd jininta yayi matuqar hawa mai muni idan ta farka awannan halin zata iya samun paralyz.

Sai bayan sunbaro gurinta aka sanarda maheer abinda yasameta lokacin yana qoqarin ganin rumanah ta farfado sbd duk iya abinda zaiyi ta farfado yayi bata farfadoba tashin hankalinda yake ciki yanxu yafi kowane tashin hankali na rayuwarsa,
Rasuwar yaransa gakuma halinda rumanah take ciki yanxu kuma ana fada masa suhailat ma...dafe goshinsa yayi tareda fitarda numfashi mai qarfi da zafi idanuwansa na sake canzawa.

Ammy sbd tashin hankalinda take ciki ko tsayuwa sosai bata iyayi tsaye take gaban gawarwakin yaran a palonta kallo daya tayi musu ta dauke kai hawaye na ciko idanuwanta sbd ganin yanda kalar jikinsu takoma mai duhu sbd dafin daya shiga jini da jijiyoyinsu sosai.

Zaman dirshan Jakadiya tayi tareda dora hannu 'daya akai tana jinjina wannan baqar rana data zo musu koda suke tsananin buqatar haihuwar maza gashi ansamu mazan amma tun ranarda aka fara naqudarsu masifa tafara saukar musu saidai wannan masifar dasuke ciki yanxu mai hadari ce sbd koda misali sunanka yafito cikin wannan zancen mutuwace hukuncinka..

Jikinta na rawa ta miqe ta dauki gawar su biyun ta nufi fada qafafunta na wani irin rawa daqyar ta iya kai kanta gaban sultan ta zube tareda shimfidesu ahankali tana furta,

Tuba nake da kawo mugun gani gaban sultan da muqarabansa.

Kallo daya yayiwa likitan gargajiyansu ya taso yazo gaban yaran ya durqusa yadauki abeel Hussain yadubasa tareda zura hannu cikin bakinsa ya Ciro yakalla ya kalli sultan ahankali ya sunkuyar dakai ya girgiza kai alamar yariga ya rasu.
'Daukar jemaal yayi yaduba shima ya tabbar musu da yarasu.

Atake sultan yakalli kaleeb cikin zallar 6acin rai da nuna ikonsa yace,

Akai mai laifin kurkuku mafi tsanani ahadata maciji mafi hadari har zuwa gobe kafin tafadi Wanda yasata sbd bayin kantabe batada isar dazata iya yiwa ko bawan mineelik kallon banxa bare iya kashe jinin sultan.

Cikin zaquwa kaleeb yace,

Angama sultan...ya fice yana kwatanto irin azabar dazasu ganawa mamani.

Cikin wani irin mummunan yanayi na firgici da tashin hankali ta farka tareda miqewa zaune jikinta na bata irin rawa tafara qoqarin tashi yayi saurin riqeta yana son kallon cikin idonta amma taqi tsayawa gabaki daya bata cikin hayyacinta fixgewa takeyi da qarfi yasake riqeta tareda girgizata da qarfi yakira sunanta.

Tasaki wani irin kuka mai qarfi tareda fixgewa daga jikinsa ta zube qasa tafara kuka sosai tana qanqame jikinta sbd wani irin ciwo da ra'dadi mai zafi takeji cikin ranta kamar zuciyarta bazata iya daukaba.

Sake riqota yayi ya rungume jikinsa da qarfi duk yanda taso qwacewa kasawa tayi tacigaba da fidda kuka mai radadi.

Wani irin ciwo da baqin cikiĀ  takeji na cin zuciyarta numfashinta har sarqewa yakeyi gurin kukan.

Kasa magana yayi sbd radadin da zuciyarsa ke ciki na rashin 'ya'ya biyu lokaci 'daya dakuma ganinta cikin wannan halin.

Ammy kallon Jakadiya tayi idanuwanta na qoqarin boye qwallarta tace,

Ya akayi mamani tashigo nan harta bari aka kamata domin na tabbarda tana sane tabari aka kamata akwai abinda take nufi da hakan Wanda shine tashin hankalina.,
Meyasa bata kashesu a dakunan uwayensuba sai agurina?
Innalillahi, allahumma ajirni fi musibati
Wannan wace irin masifa ce mai wuyar cinyewa.

Cikin sanyin jiki a raunane Jakadiya tace,

Alqawarin Allah ne zai tabbata sbd sbd ayanxu alamu sun fara bayyanar mulkin mace a mineelik Wanda hakan na nufin ba'a zubarda jiniba yanxune za'a zubar dashi.

Girgiza kai ammy tayi da sauri cikin tsananin fargaba da rudu tace,

Rumanah bazata taba zama mai zubarda jinin bayin Allah ba,
Nayi gudun haka kowa yakasa fahimtata,
Na roqi Allah a zuci da fili akan kar rumanah ta haifi namiji idanma ansamesa yazo babu rai amma hakan bata faruba yanxu bansan ta ina kuma wannan masifar ta 6ullo ba.

Duk yanda yaso ganin rumanah tadawo nutsuwarta abin ya gagara saima zuru datayi da ido kukan yadaina fita saidai hawaye kawai ko motsin kirki bata iyayi ta rakube gefe guda ta takure kanta.

Lokacinda aka shigo aka sanarda ita zuwan ammy dubata bata motsaba saima rufe idanuwanta datayi hawayen ciki suka gangaro tunani abubuwa da dama na dawo mata,

"" mafita 'dayace karta haifi namiji idanma ta haifesa mutuwarsa itace mafita""

"" yaya kike tunanin zan fuskanci rumanah ranarda ta San cewar mune sanadin mutuwar iyayenta""

Rintse idanuwanta tayi da qarfi nauyi da zafin zuciyarta na qaruwa saidai batason barin zancen yashigeta a irin yanayin datake ciki yanxu sbd tanason tayiwa ammy fahimta mai kyau bazataso abinda kunnuwanta sukaji mata ba yazama gaskia.

Ammy kasa haquri tayi ta nufi dakin lokacin maheer yaje dubo suhailat.

Har ammy taqaraso gabanta bata motsaba daga inda take takure idanuwanta jajir.

Cikeda tsananin kunya da tausayinta murya na rawa tace,

Rumanah har abada bazan iya cire qaunarki arainaba sbd qaunace Allah yasakamin cikin raina Wanda kisani har abada bazan iya yin abinda nasan zan cutatardake ina fatar zaki riqe hakan aranki...Allah yaji qan abeel Hussain.

Juyawa tayi ta fice jikinta asanyaye sbd tana iya hasaso wasi wasi azuciyar rumanah.

Tana fita rumanar sulale ta kwanta agurin tasaki sabon kuka tana dafe qirjinta dake mata zafi da wata irin tafasa.

Cikin wata irin kaca mai tsananin nauyi da zafi aka na'do mamani da nauyin kacar yasata tafiya ahankali a duqe sbd ko qafarta daqyar take dagawa sbd nauyin kacar datake 'daureda ita.

Aka bude wani tsohon kurkukun dayafi shekara goma ba'a shigesaba aja jefata ciki da qarfi kanta ya bugu da bango take goshinta ya fashe da jini ta fitarda numfashi daqyar sbd azaba gashi batada hannun shafawa taji sbd irin 'daurin da'akayi mata ko numfashi daqyar take fitarwa.

Ta lumshe ido cikin azaba ta bude idon takalli qofar dishi dishi take gani sbd ba qaramar buguwa tayiba gashi anyi mata wani irin duka na rashin imani dan kariya biyu akayi mata a hannu 'daya.

Wani irin kwando aka bude tareda jeho abinda ke ciki aka rufe qofa
Wani irin baqin maciji tagani ya bude kansa yana fitarda huci.

Mummunar faduwa gabanta yayi wasu irin hawayen azaba da tsoro tareda baqin ciki suka gangaro mata jikinta ko qarfin dazaiyi rawa bashidashi sbd ti6is akayi mata.

Tana kallo macijin ya kwantarda kai yayi cikin wani qaton rami dake gurin Wanda shikansa ramin baza'a rasa wani macijin acikiba ko abinda yafisama.

Maganarta da adama ta tuno tana fargabar kar komai yaqi tafiya yanda suka tsara.

""" idan kikai nasarar basu wannan dafin suka sha zasu mutu atake kuma ki tabbatarda ankamaki duk wuya da azaba karki ce nice kice sultana ce Wanda kowa yasan hukuncinta na kisa ne kafin akasheta za'a bani matsayinta na sultana nikuma zanyi amfani da wannan matsayin na hana akasheki kuma daga lokacin namiki alqawarin matsayin Jakadiya kintashi daga baiwa har abada saidai kuma idan kika fadi sunana kisani babu 6ata lokaci dukkaninmu za'a kashemu amma idan kikace itace nizan kubutar dake kinga burinki na shekara da shekaru yacika ga 'yanci da dukiyar kanki dazaki tara""""

Numfashi tasaki a wahalce tana sake qarfafawa zuciyarta dan cika sauran aikin dan kuwa koda ta mutu tasan burinta akan zuriar bulama da asma'u yacika.


Suhailat data farfado ahankali hawaye kebin fuskarta suna sauka kan qirjinta idanuwanta arufe sbd ko hannunta daqyar take iya motsasa.

Qunci ne arayuwarta da zuciyarta,
Rayuwarta ta lalace batada wani sauran farin ciki,
Ta rasa mijinta badan ya rasuba,
Ta rasa rayuwar aure mai farin ciki,
Ta rasa lafiyarta,
Ta rasa mahaifarta gurin haihuwa ga abinda ta haifa ta rasashi mai zaunawama ya rungumeta ya rarrasheta ta rasa
Wace irin rayuwace mai tattareda garari take ciki?

Wani irin kuka mai qaramin sauti tasaki zuciyarta na mata ciwo mai tsanani
Kewar iyayenta da 'yayanta takeji sbd sune kadai sukasan zafinta da damuwarta.

Qarasawa yayi bakin gadon tareda Rungumeta da sauri yana jin tausayinta fiyeda kansa sbd yasan tafi kowa cutatuwa sbd tafi rasawa tunda ba wata haihuwar zata sakeba.

Akaro na farko arayuwarta taji batason kusancinsa agareta sbd nauyi hakan ke qarawa zuciyarta saidai ko motsi sosai bata iyayi bare ta zame jikinta hakan yasa wani sabon kukan qunci zuwar mata ahankali.

Sosai ya lurada batai farin ciki ko jin sanyi da ganinsaba akaro na farko arayuwar aurensu daya hango wani yanayi daban akansa wanda ba sonsa bane atareda ita ya rufe ido cikin wata sabuwar damuwar yanajin tausayin kansama sbd wata jarabawace Allah yake jarabtarsa da ita akan rumanah wadda idan baiyi taka tsantsanba zai tashi da Rabin jiki ranar lahira saidai kuma baisan yaya zaiyiba sbd sonta yazama halitta ajininsa.

Ahankali ya furta,

Allah yaji qan jemaal.

Sakinta yayi ya miqe tareda ficewa batareda ya qara kalma 'daya ba.

A wannan daren mineelik ba kowa yasamu damar kwantawaba bare ya rintsa sbd dukkanin dole da masautar na cikin tasa kalar damuwar.

Rumanah dai duk yanda akayi da ita taci abinci ko motsi taqiyi daga inda take idanuwanta sun bushe sunyi jajir ko gani sosai batayi sbd kumburin idanuwanta.,

Suhailat kuwa har lokacin bata iya kwakwaran motsi sai hawaye da ciwon qirji dayake cinta ita kanta anyi anyi taci abincin amma ko bude ido taqiyi sai hawaye take zubarwa.

A rayuwarsa wannan ne karo na farko dayaji yayiwa sarauta da gidan sarauta wata irin muguwar tsana sbd yasan son mulkine yasa akai hakan,
Ya tabbatarda kisace ta tabbata akan baiwar datayi da wainda suka sakata saidai bayajin zai tsaya ganin hakan gobe zaayi hidimar radin sunansu a goben zasubi jirgin dare su koma dan idan yananan zuciyarsa zata bugane da halinda matansa suke ciki musamman suhailat datake buqatar kulawa sosai.

Ammy da jakadiya kusan a zaune suka kwana ko ruwan arziki babu Wanda ya iya sakawa maqoshinsa sbd tashin hankalin dazai iya faruwa gobe sbd duk Wanda sunansa yashiga koda misali ne cire kansa ya wajabta gashi a sashen ta abin yafaru shine babban tashin hankali da damuwar dasuke ciki musamman dasukasan wacece mamani.

Ayau mineelik acike takeda duk wata masarautar dake zagaye da maqwaftaka da ita tareda wasu sarautun wasu qasashen da dama sbd gabatarda sunan magajinnta dakuma miqawa uwar magajin mineelik kambun saukewa da 'dora sabon sultan.

Wannan matsayin daza'a bata ayau shine abu mafi ha'dari da tashin hankalinda yake ciki ayau
Ammy duk yanda taso daurewa kasawa tayi saida hawayen baqin cikin datake ciki suka gangaro mata tun a daren jiya ta hana su ganta bare ta sanarda ita hadari da kuma illar abinda zata fada.
Saidai alqawarine shi ya daukarwa kansa zai tabbarda ta miqa mulkin nan ga sultan ya dauketa sunkoma adaren yau din.

Lokacinda aka hallara dan qaddamarwa saqo ya isowa sultan uwar magaji batada lafiya bazata iya fitowa.
Kai tsaye aka fara qaddamar da komai aka radawa abeel Hassan sunansa tareda qaddamar da sunan ummu-rumanah acikin littafin tarihin mineelik amatsayin uwar magaji.

Nan take masu rubuta tarihi aka bude paging fara rubuta nata.

Daga ammy har yarima maheer babu Wanda ya halarci taron kuma sarai sultan yagano manufarsu tayin hakan zasu fuskanci hukuncinsa daga baya ayanxu baiwa mamani ce agabansa zai bata wata irin mutuwa mai firgitarwa itada wainda suka sakata ga 'yan baya.

Koina yayi tsit jiran hukuncin sultan akeyi lokacinda mamani ta tabbatarda Jakadiya ce tasakata amatsayin itama sultana ce ta aikota.

Tsita akayiĀ  kowa wuta ta dauke masa musamman sultan da mamakin baiwa mamani yakamasa sbd yafi kowa sanin sultanarsa bazata aikata hakanba,
Tabbas wannan baiwa mai taurin raice saidai ji da ganin hukuncin sultan kawai tajeyi batasan waye sultan ba.

Kallo daya yayiwa kaleeb cikin babbar murya yace,

Aje ajefawa zakuna ita su cinyeta da ranta akawo qashinta asa 'dakin kayan tarihin mineelik...

Da ido adama dake dake gefensa tayiwa sultan aqeel magana ya gyara zamansa tareda kallon sauran sarakunan dake Royal hall din yace,

Idan aka kashe wannan baiwa batareda ta fadi wainda suka sakataba baka kai qarshen matsalar a mineelik ba sbd gobe ko jibi magajin ne da kansa za'a kashe kuma hakan zaisakawa mutane wasi wasin hukuncinka tunda ta fadi wainda suka sakata anshare anyi kamar bata fadaba.

Ido cikin ido yakalli sultan aqeel yace,

Babu Wanda ya isa yayi wasi wasin hukuncina a qarqashin mulkina da ikona ko wanene batareda na ciyar da namansa ga dabbobinaba.

Murmushin mulki sultan aqeel yasaki yace,

Hakane kuma idan kanason hakan yacigaba da faruwa saika nunawa mineelik Kaine sultan kuma Kaine kake yanke hukunci kowane irine akan ko wanene.

Nan take sauran sarakunan suka marawa gaskia baya suka qalubalanci sultan akan adalci idan har sultana ce tasakata to ayi adalci ayanke hukunci daidai yanda yakamata.

Atake mutane suka fara kallon kallo da hayaniyar abinda aka fada nan mamaki ya kama sultan kenan har akwai wainda zasu iya tambayar hukuncinsa su qalubalanci yanayin mulkinsa
Atake yace aje a kama Jakadiya arufe ya 'daga hukuncin zuwa gobe duk me hannu aciki kafin faduwar rana baya duniya.

Lokacinda akaje aka kama Jakadiya aka rufe
Sultana kuwa rufe sashenta akayi tareda aje masu tsaron qofar da doka mai qarfi daga sultan babu Wanda zai shiga gurinta ajira hukuncinsa zuwa gobe.

Lokacinda zancen ya isa kunnen maheer kai tsaye gurin sultan yanufa akai masa iso lokacin anwatse sai gobe a shaida hukuncinda zai iya yankewa.

Kallonsa yarima yayi cikeda takaici da baqin cikin yanda yasan sultana bazata aikata hakan ga yayansa ba amma ya yarda haryana iya tunanin yanke mata hukunci
Kai tsaye yace,

Amatsayina na uban magaji zan kar6i mulkin mineelik har lokacinda zai girma ya karbi da hannunsa.

Wani irin murmushin takaici sultan yasaki batareda yakallesaba yace,

Mulkin mineelik da za6ar mai mulkin na mutum 'dayane yanxu dan haka ka rasa damarka,
Mahaifiyarka kuma koni bazan iya kubutarda itaba idan har bincike ya nuna da hannunta aciki.

Yana fadar haka ya shige tabarsa zaune idanuwansa na kadawa jajir.

Duk inda tashin hankali yake masarautar na ciki dan shi kansa sultan jinjina alamarin yake aransa yana jaddadawa yana kuma fatar bincike yasa kar asamu hannun sultana aciki.

Acikin daren babu kalar azabar daba'a bawa mamaniba tace Jakadiya tasaka ta.

Jakadiya aka hau bawa baqar azaba amma daqyar take iya furta babu saka hannunsu aciki.

Acikin daren saqon neman sulhu da sassaucin hukunci yazo daga masarautar Libya dakuma wasu masarautun duk sai alamarin yasake girmama ya sake cabewa sultan gashi komene adaren ne sbd gobe dolene zai yanke hukunci.

Nuratu datun jiya take kuka da tashin hankalin halinda mamani ta fada koda bincike yazo kanta ba qaramin rikicewa tayiba saidai tafada musu komai na dangane da zancen dasukaji su Jakadiya nayi da sultana itada rumanah akan basuso ta haifi namiji.

Atake aka kaiwa sultan wannan zancen hankalinsa ya matuqar tashi saidai har lokacin yanada wasi wasin zancen ga asirinsu na 6oye daya fara shigowa cikin zancen Wanda tonuwar dolema yayi gaggawar yanke hukunci sbd kar maganar ta bankado atake ya yanke hukuncin kisa ga dukkaninsu ukun gobe.

Acikin daren hankula suka masifar tashi jin anyekewasu sultana hukuncin kisa washe gari.

Duk wata zuriar masarautar tun acikin daren suka fara isowa musamman 'yayan sultana da kuka sunyisa na zuci dana fili hankalinsu amatuqar tashe yake.

Yarima maheer Kansa ya rufe adaki duk yanda yake tunanin masifar ta wuce nan abu 'daya yasani bazai mahaifiyarsa ta fuskanci hukuncin kisar wulaqanciba.

Kwance take lamo idanuwanta jajir ko kukan bata iyayi duk abinda yake faruwa bata saniba sbd ta hana abar kowa shigowa gurinta.

Ahankali taji antsaya akanta batareda tadagoba ta lumshe ido tareda budewa taji muryar suhailat cikin wani irin yanayi tace,

Nazo neman alfarma agurin sbd kece kawai zaki iya tsayarda abinda ke shirin faruwa.

Tashi zaune tayi ahankali batareda takalli suhailat dinba
Itama suhailat sauke kanta tayi sbd batason kallon rumanah dan ganinta ke tuno mata da ba itace zuciyar mijintaba.

Hawayene suka gangaro mata tasaka hannu ahankali tashare taci gaba da cewa,

Nice uwar datai rashin abu biyu lokaci daya kuma zuciyata cike takeda neman adalci,
Ina roqonki amatsayina na uwar data rasa 'da da mahaifarta akan adalci zanso ganin anmin adalci saidai bazanso akashe Wanda bashine mai laifinba sbd mai laifin zai cigaba da aikata 6anna aboye har wadda tafi wannan.

Cikin dasashiyar murya da sanyi tace,

Adalcin nima nake nema amatsiyana na marainiyar da aka raba da iyayenta dakuma uwar da aka rabata da 'danta tun bata gama warkewa daga zafin naqudarsaba.

Asubar fari yashigo dakinta idanuwansa da yanayinsa suka karya mata zuciya ta dauke kai daga kallonsa tareda mayarda kanta kan gwiwoyinta.

Tsayawa yayi agabanta zuciyarsa cikeda baqin cikin kasancewarsa shine zai roqi wani yabasa sarautarda shine ya gada saidai yasan kubutarda ammynsa na nufin ya karbi sarautar ayau yazamo shine zai yanke hukunci sbd yagano sultan sbd 6oye wani sirrinsa yakeson yanke hukuncin da gaggawa ayau.

Kallonta yayi da idanuwansa dasukai jajir yace,

Inason kibani sarautar mineelik ayau.

Kallonsa tayi da sauri da jajayen idanuwanta dake budewa daqyar sbd kumburi.

Juya mata baya yayi yace,

Ki shirya ina jiranki kafin lokacin yanke hukuncin su ammy yayi.

Ficewa yayi tabisa da kallo zuciyarta na harbawa.

Cikin wani irin yanayi na sabon tashin hankali ta 'dauki abeel hassan ta fito palo takalli nuratu dake rakube tun acikin daren tana jiran fitowarta tayi kuka har batada qarfin yin wani.

Kai tsaye tace,

Meke faruwa?

Da sauri nuratu ta tashi ta zube gabanta tana hawaye tace,

Ina neman afuwa akan shaidar dana bayar akan sultana da jakadiya gashi zasu rasa ransa sanadin shaidata saidai wlh ina rantsuwa da rayuwata mamani bayin kantabane sakata akayi saidai wlh bansan wayake sakataba dana fada nan fitardasu sultana dan haka ashirye nake da daukar hukuncinki.

Da wani irin sabon baqin ciki da takaici takalli nuratu saidai takasa cewa komai ta nufi qofa ta fice kai tsaye sashen suhailat ta nufa.

Zaune take a dakinta taqurawa akwatinanta data saka Carolina hadawa ido idanuwanta jajir.

Tsayawa gabanta rumanah tayi tareda miqa mata abeel hassan idanuwanta na cikowa da hawaye tace,

Duk duniya ayanxu kece kawai na yarda dake akan 'dana sai Ammy dan haka ina riqonki daki riqesa har sai lokacinda kikaji zuciyarki ta gamsu da adalcin dazan baki,
Na miki alqawarin duk Wanda yakeda hannu aciki ayau zai fuskanci hukuncinsa.

Ficewa tayi kai tsaye ta nufi sashenta tashiga wanka zuciyarta na wani irin zafi tana fitowa tagansa tsaye cikin 'dakin idanuwansa jajir ya kalleta ta 'dauke kanta tareda isa gaban madubi ta zauna.

Cikin zafi ya jawota gabansa cikin 'daga murya yace,

Me kike nufi da abinda kika fadawa suhailat?

Bata kallesaba tace,

Kubutarda uwata.

Sakinta yayi da sauri tareda kallon cikin idonta yace,

Kinsan abinda kike fada?
Kinsan abinda hakan ke nufi?
Bana buqatar ki shiga komai abu 'daya nace kiyi shine ki bani matsayin danace inaso....

Kallonsa tayi da jajayen idanuwanta cikin rawar murya tace,

Nima bana buqatar ka saka kanka cikin ha'dari dan haka bazan taba baka mulkin mineelik ba koda hakan na nufin rasa rayuwatane....

Riqota yayi da qarfi tareda girgizata yace,

Idan kina sona bazaki taba bari ataba mahaifiyata ba sbd itace rayuwata dan haka dole zaki bani mulki.

Hawayen dasuka cika mata idone suka gangaro mata ahankali tace,

Namaka alqawarin babu abinda zai samu uwar data haifi halitta mafi soyuwa arayuwata kozan rasa raina.

Shiga jikinsa tayi ahankali tareda rungumesa hawaye na tsinke mata.
Rintse ido yayi tareda rungumeta ahankali ya furta,

KECE RAYUWATA UMMU-RUMANAH BULAMA.

Dagowa tayi takallesa hawaye far in ciki na tsiyayo mata saidai bazata iya cewa komaiba.

Ruwan kan table din dake tsakiyar dakin ta dauka tareda kaiwa bakinsa tana tsiyayar hawayen tausayinsa dana kanta.

Ahankali yasha yana kallon cikin idonta.

Ahankali ta furta,

Karka gujeni kome zanzama arayuwa dan allah,
Ko bayan raina kayi kayi alqawarin tunawa dani.

Lumshe ido yayi jikinsa na mutuwa idanuwansa na fara gani dishi dishi a firgice yake kallonta sbd gano wani abune tabashi saidai kafin yayi wani yunquri ya zube kan gadon ta durqusa ta gyara masa kwanciyarsa tareda shafa fuskarsa ta miqe.



Dukkanin wani maison sheda hukuncin sultan na cikin qasar da wajenta sun hallara sultan na fitowa guri yayi tsit ya zauna kan kujerar mulkinsa atake aka fito da mamani da jakadiya dukkaninsu babu mai iya tsayuwa sbd azaba da 'daurin dake jikinsu.

Kukan baqin ciki Jakadiya takeyi sbd irin mutuwar tozarcin dazasuyi tareda sultana.

Mamani na ganin masu jiran umarni sun tsaya akansu da takobuna suna kashe ido sbd laifi da qyallinsu hankalinta yatashi tabude ido daqyar tanason magana kaleeb ya take mata kai.

Ana jiran ana fitoda sultana cikin wani irin ama aka sanarda fitowar uwar magaji.

Atake kowa yayi tsit sultan yayi saurin kallon qofar
Tafito cikin wata irin doguwar ethiopiany royal gown red colour mai tsananin tsawo da adon black stones wuyanta da kanta na kyallin farin zinari kallo 'daya zakayi mata kasan tana cikin baqin ciki.

Cikin wainda ke tareda ita Dan tsaron lafiyarta ta kalli gefen daya jiki na rawa ya fidda bayananta dake rubuce jikin fatar rubutu ya miqawa sarkin na'din sarautar mineelik.

Budewa yayi tareda fara karanto da qarfin muryarsa yanda duka alummar dasuka halarci gurin zasuji.


"" NI UMMU-RUMANAH BULAMA MATAR YARIMA MAHEER UWAR MAGAJIN MINEELIK AYAU KWANA 'DAYA DA NADIN SUNAN MAGAJIN MINEELIK NA SAUKE SULTAN ABDULSHAMS ABDALLAH DAGA MULKIN MINEELIK NA KARBA HAR ZUWA RANARDA 'DANA MAGAJI ABEEL HASSAN ZAI KARBI MULKI DA HANNUNSA.."""

Tsit koina yayi sbd firgici da mamaki
Sultan da adama kusan atare suka miqe tsaye tsabar firgici.

Ammy da ake fitowa da ita kadan ya rage ta yanke jiki ta fadi sbd jiyo sanarwar.

Jiki na rawa sarkin nadi tareda duk sauran sarakuna da wazirai suka miqe ta nufi kujerar mulkin mineelik gabanta da numfashinta na fita da sauri
Sultan dayayi mutuwar tsaye ya zare hular mulkin ya miqawa sarkin gida atake aka dauko kayan rantsarwa aka rantsar da ita atake ta zauna kujerar mineelik aka saka mata hular.

Lumshe jajayen idanuwanta tayi wani irin baqon yanayi mai qarfi na shigarta
Wani irin qarfin zuciya da taurin zuciya taji yana shigarta tsawon lokaci ahaka duk anyi tsit anajiranta.

Ahankali ta bude idanuwanta dasuka bushe nan take tagyara zama takalli inda sultan yake zaune yana kallonta cikin isa shima yanajiran jin nata hukuncin ta juyo takalli indasu mamani suke cikin daga murya tace,

Akawo abinda mamani tafiso aduniya.

Cikin gaggawa aka jawo nuratu aka durqusar tsakiyar gurin kai tsaye tace,

Ku yankata agabanta uwarta idan bata fadi Wanda yasakataba cikin seconds uku.
#mamuhgee.

*_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers associationšŸ’”_



*34*
Not edited.
Arazane sultan,adama,ammy,da baqin sarakunan dasukazo suka kalleta
Babu Wanda ta kalla acikinsu tayiwa kaleeb kallo 'daya idanuwanta na sake bushewa cikin gaggawar cika umarninta kaleeb ya daga shar6ebiyar takobinsa mai cire kai lokaci 'daya ya 'dora a wuyan nuratu dake hawaye ta qurawa rumanah ido.

Numfashin wahala mamani ta fitar cikin tashin hankali ta bude baki zatai magana adama datai mutuwar zaune tayi sairi tashi tsaye jikinta na wata irin tsuma zatai magana rumanah ta 'daga hannu batareda takalleta tace,

Duk Wanda yayi magana batareda hukunci ya gama tabbatuwaba abakin rayuwarsu ko wanene.

A gigice adama tasake kallonta cikin wani sabon tashin hankalin

Please Login or Register in order to submit comment