Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

takoma ta zauna zufa na karyo mata jikinta na wata irin tsuma.

Tayar da ita akayi tana numfashin azaba takalli takobin datake qyalli a wuyan nuratu takuma tabbarda yankata din za'ayi.

Ahankali rumanah ta 'dagawa kaleeb kai alamar yacika aiki.
Atake ya 'daga takobin cikin wahalalliyar murya mamani tace,

Gimbiya adama ce.

Cak kaleeb ya tsaya sbd harya 'dora takobin a wuyan nuratu harma saida ya'dan yanketa.

Arazace sultan yakalli adama data jiqe jagaf da zufa jikinta na tsuma tanason kare kanta gashi ance duk Wanda yayi magana bbakin ransa kuma tasan tsaf rumanah zata iya sbd tasan abinda ka cikin karagar zaifi shigarta kasancewarta mace dan haka zatafi rashin tausayi da imani.

Sarakunan dake gurin duk ita suke kallo cikin mamaki yayanta kuwa kuka suka fashe dashi gashi babu ikon ko qwaqwaran motsi.

Rufe ido rumanah tayi wani irin yanayi na tsuma zuciyarta gawar 'danta da iyayenta tana mata yawo ido da irin tozarcinda ammy ta fuskanta akan hakan
Fuskar maheer ce ta fado mata da irin tashin hankalinda tagani ataredashi tsakanin jiya zuwa yau ta bude idanuwanta dasukai jajir tace,

Ni sarauniya ummu-rumanah bulama na halastawa takobin kaleeb adana jinin adama kisheer ayau agaban mijinta da 'yayanta tareda sauran alumma duk Wanda ko a fuska ya nuna hukuncina baimasaba a shayar dashi dafi daidai irin Wanda adama tashayarda qannen magajin mineelik.,

Baiwa mamani arufeta mai rubuta tarihi yaje tabasa tarihin sarauniya rumanah arubuta atarihin mineelik tana gamawa bazata qara minti biyar aduniyaba a shayar da ita Kofi 'daya na daafin macijin dayafi kowanne kaifin dafi,
Sultana zaarah da jakadiya sunfita da zargin da ake musu.

Sultan abdulshams arufesa a turakarsa babu shiga babu fita aabisaga zarginsa na qoqarin yanke hukunci batareda bincikeba harsai angama bincike akan niyarsa sultana zaarah ce kawai keda damar shiga da fita agurinsa sai yarima maheer.

Arikice sultan yakalleta ransa na mummunan 6aci da baqin ciki ace rana 'daya cikin mintunan dabasu wuce biyarba baiwa wadda bama asalin 'yar qasaba ta saukesa akan mulkin daya gada iyaye da kakanni,
Ta yankewa matarsa kisan wulaqanci agaban dubban jama'ar dasuke shakkar ko kallon inda yake sannan yanxu tace arufesa a turakarsa wannan shine tozarci mafi muni arayuwa...

Yanxu ta karbi mulki idan tagano shine asalin dalilin mutuwar iyayenta akwai masifa sosai sbd yanda sihirin karagar nan ke shigarta nan cikin qanqanin lokaci zata zamewa kowa masifa mai matuqar hadari musamman shi saidai duk masifa duk balai bazai bari yayi mutuwar wulaqanci a hannuntaba koda hakan na nufin hada hannu da balain da aka binne shekaru tun kafinsu.

Kama adama akayi aka fara janta tayi saurin kwacewa ta isa gaban rumanah ta zube tana kukan tashin hankali jikinta na mugun karkarwa saidai takasa magana sbd umarninda rumanar tabayar ko kallonta rumanah batayiba ta kalli su kaleeb atake suka fara yiwa adama jan wulaqanci.

Jikin ammy ne yadauki rawa cikin sabon tashin hankali take kallon rumanah tana girgiza kai sbd matuqar tafara mulkinta ayau da zubarda jinin wani to tabbas zaiyi wuya bata zamewa mutane abin tsorobas.

Qoqarin isa gurin rumanah din tayi aka dakatar da ita ta hanyar tareta tayi saurin kallon rumanah data rufe idonta tanajin wani irin baqon yanayi shigarta.

Cikeda rashin imani da tausayi kaleeb ya daga takobinsa yacire kan adama data mutu tana ihu da fizge fizge.

Tsit gurin yayi sbd tsoro da firgici sbd duk mulkin sultan ba'a taba kashe mutum agaban alumma ba sai yanzu nantake kowa yaji tsoro da fargaba tareda tashin hankali na shigarsa atake kaleeb ya 'daga takobinsa dake 'digar jinin adama sama ta bude idanuwanta ahankali takalli jinin dake diga qasa ahankali tasauke ajiyar zuciya ta miqe tsaye.

Cikin wani sauti da babban sauti sarkin na'di yace,

Dogon zamani MINEELIK ASSULTANA UMMU-RUMANAH UWAR MAGAJI.

Juyawa tayi wasu irin samudawan masu bata tsaro da kuyankinta mata suka mara mata baya tashige.

Tafiya kadan tayi ta tsaya cak sbd abinda takeji ajikinta
Wani irin abu takeji kamar yana tafiya da motsi ajikinta ta dafe qirjinta da takejin yana quna.

Ammy tayi saurin nufota aka sake tareda
Rumanar ta 'daga musu hannu daqyar alamar subarta ammyn tayi saurin qarasowa kafin tayi yunqurin ta6ata sukaga ta yanke jiki ta fadi jini na fita ta hancinta atake hankalinsu yayi masifar tashi ammy na qoqarin 'dagota suka gansa kansu idanuwansa jajir jijiyoyin sun firfito ya durqusa ya dauketa ya nufi sashenta da ita cikin qanqanin lokaci aka zuba wasu irin tsaro tundaga qofar sashenta har zuwa qofar masarautar atake labarin halinda take ciki ya yadu nan mutane suka sake shan jinin jikinsu atake aka rufe duk wata qofar shige da fice dake mineelik aka dauko duk masu bada maganin sarauta na asalin gargajiyarsu nanda nan aka hau dubata suna qoqarin tabbatarda abinda suke tunani.

Cikin wani irin tashin hankali da damuwa yake,
Zafi sosai yakeji acikin xuciyarsu akaro na farko dayaji zuciyarsa na karaya akan abu saidai yasan mutuwace kawai zata rabasa da rumanah dan haka duk abinda zata zama ayanxu ashirye yake daya sadaukar da rayuwarsa akan cetota daga masifar dake tattare da wannan karagar.

Jini ne sosai yake fita ta hancinta ahankali tafara wata irin jijjiga jijiyoyin jikinta suka ringa firfitowa Kore sosai nan take hankalin su negasi(masu maganin gargajiyar qarnin baya na sarauta) ya tashi
Maheer da idanuwansa sukai mugun rikidewa yayi saurin nufarta zai rungumota cikin wani irin sauti negasi yace,

Karka kusanci inda take ko kusa a wannan yanayin hadarine mai matuqar gaske dankuwa dafine yake yawo ajikinta yanxu idan jininta yafi qarfin dafin zataci qarfinsa ta tashi idan kuma dafin karagar yafi qarfin jininta shikenan sai hakuri sbd har abada bazata koma daidaiba zata zama rabi hankali rabi nakashe.

Cikin wani mumman tashin hankali ya dafe goshinsa akaro na farko yaji idanuwansa suna qoqarin tara hawaye ya fito dakin baya gani sosai sbd tashin hankali
Ahankali yaji andafasa yana juyowa yaga suhailat rungume da abeel baisan sanda ya fada jikintaba ta rungumesu gaba daya shida abeel din hawaye na gangaro mata cikeda tausayinsa dana rumanah taso tafiyarta ayau saidai ganinsa Cikin halinda bata taba ganinsaba yasata jin bazata iya tafiya tabarsa a lokacinda yafi buqatarta,tabbas idan tanada wata qaddara arayuwa to soyayyar maheer ce dan haka kamar yanda zai sadaukar da rayuwarsa gurin kulada rumanah duk halinda zata shiga mai kyau ko mara kyau to itama zata zauna ta sadaukar da rayuwarta gurin kula dashi da zame masa garkuwa duk lokacinda zai nemi hakan.

Ammy dake zaune tareda sauran 'yayanta yayun yarima sun biyu da Jakadiya da sauran masu tsaro da jiran tsammanin halinda ake ciki ta rafka tagumi zuciyarta na harbawa da qarfi sbd tasan me hakan ke nufi dan kuwa rumanarsu tariga ta tafi sbd idan har komai yagama shiga jikinta duk abinda yafaru shekara da shekaru tun kafa mineelik zata gani Wanda shine idan kaga masifun dake ciki yakeda wuya baka haukaceba idan ka farka.
ASALIN MINEELIK.......
#mamuhgee

Kuyi manage na fitane so mu kama gobe.

_*TARAYYA*_
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_



*35*
Not edited
*Asalin Labarin mineelik*

Soyayya da cin Amana haÉ—i da Yaudara suka, kafa daular, asalin masifar ya fara ne, daga ranar laraba ga watan maris 1836. Mafarin rigimar daga mutane huÉ—une, jigogin masarautar, Musaman Sultan Jamal wanda shi ya haifar da kome....

Tafiya suke a gajiye ga dare ya fara rabawa, yunwa da kishirwa ya addabesu, dan haka suka yanke hukuncin da zaran sun sami, wani guri a can gaba zasu yada zango kasancewa sun fito daga yanki sham, fatauci duk cikinsu babu wanda yake iya magana sai Jamal, sabida Allah yayoshi mutune magananne, da kuma son raha,
"Kayyasa! Ajani karda ka gaji da tafiyar dan naga kaman rakuminka ke janka ba kai kejanshi ba."

"Wai shin Jamal baka gajiya da magane, haba tun da muka fito kaiÉ—ai ke surutu gaskiya kacika surutu kayi mana hakuri haka dan yunwa muke ji." inji Kojo.

"Shi kenan kojo nayi shiru kuma bazan sake magana ba, amma kusan matuƙar muka ce zamu shiga Ehtophiea a wannan daren akwai damuwa mu yada zango anan gaba."

Shirun da sukayi ya tabbatar da amincewar sauran.

Tafiya sukayi sosai har suka isa dajin kurfa, wanda yake cike da ababen tsoratarwa, É—an tafiya kaÉ—an sukayi É—ayansu amari yaga wani irin Haske mai tsananin kyalli cikin duhu ya ware ido sosai yasake kallawa domin kuwa ya tabbatarda mage yake gani mai shegen hasken nan kamarna zinari cikin zaquwa da fargaba yace.
"Ku dakata naga wani abu, kamar Zinari."
"Amari nima nagani tsoron siffar abin yasani shiru gashi can kamar mage ko?" Inji Jamal,

Linzamin rakumarsu suka ja, suka tsaya Jamal da Amari suka sauka, daga bisa rakumansu, Ajani da Koja suna tsaye suna kallonsu, tafiya sukayi me É—an nisa suna niman Zinarin basu ganshi ba,
Tsaki Ajani yayi wanda ya kasance shine babbansu, cikin fushi yace.
"Dalla kuzo mutafi kusan inda muke ciki wannan dajin kurfa cike yake da al'ajabi da ban tsoro matumar kuka ce zaku bi na gane gane mutuwa zamuyi ku fito muje."
Murmushi Amari yayi cikin nutsuwa yace.
"Na rantse da abin bautana bazan bar dajin ba, Jamal idan zaka bisu ba damuwa amma ni sai naga abinda ya turewa buzu naÉ—i"

Shiru sukayi sunsan Amari da kafiya da kuma taurin rai, matukar yace zai yi abu ba makawa sai ya aikata,

Cikin laluma kojo yace.
"Shikenan zamu tayaku nima! Ai duk cigabanmu ne, Ajani kayi hakuri mu tayasu niman zinariyar."

Tsaki Ajani yayi sannan ya koma inda suka ajiye rakumansu, suka kafa tanti karan dake wajen dajin suka tsinta, suka kunna wuta suna shan É—umi,( bawai dan lokacin sanyi ba'a mutanen da suka kuna wuta su zauna suna hira, musaman fatake matafiy idan suka yada zango.)

Zama sukayi a gurin, sannan suka ciro guzirinsu suka fara ci, bushashiyar gasashiyar fulawa sai bushashen inabi, sai ruwa suna ci suna hira, har dare ya raba sannan kowa ya koma tantinsa.

Kasancewa dajin mugun gurine koda suka shiga sai da suka kafe ilahirin gurin dan kar wani mugun dawa ya iya shigowa ya cutar dasu.

Asalinsu wadanan, Fataken yan garin Ethiopia ne, sun kasance marayu basu da uba basu da Uwa, sai wani marikinsu wanda shima bai jima da mutuwa ba.
Ajani shine babba a cikinsu sai mai binshi Kojo, sai kuma Amari da karamunsu jamal.
Dukda kasancewarsu marayu haka bai hanasu kaunar junansu ba, dan ko ciwo É—aya keyi duk sai sun kwanta kamar marasa lafiya, dukda haka suna da mabanbanta halaya, Ajani baida yawan magana, amna kwai saurin fusata sai amma haka bai sashi ya gaza zama mai hakuri ba,

Sai Kojo, mutune mai matukar fahimta ga daÉ—in zama da kowa kuma duk inda zai zauna zai matukar wuya kaji ance ana rigima dashi, sabida ya iya zama da kowa, sai Amari, masifaffe mara hakuri amma kome zaiyi akan gaskiyarshi yake, yana da matukar taurin kai, dan shi duk abinda yasaka agaba toh sai yaga bayanshi, amma mutune mai me tsage gaskiya.

Sai Autansu Jamal wanda ya kasance mutum ne hakuri da juriya ga barkwace da iya zama da mutane, kuma yana da shiga rai dan duk inda ya zauna sai kasamu ana alfahari dashi, sai dai yana da abun dariya dan idan yazauna kusada kai sai ya cika maka cikinka da barkwace da raha.
Wannan kenan....
Washi gari da safe duk suka tashi, nan suka karya a gurguje suka shiga dajin, niman zinarin nan, har rana takusan faÉ—i basu gani ba, tsurawa dajin ido amari yayi yace.
"Jamal jiya ba'a nan muka ga kyalin zinarin mai sufar mage."

GyaÉ—a mishi kai Jamal yayi cike da bashi kwarin gwiwa, murmushi Ajani yayi sannan yace
"Amari zan tura kojo gari ya sayo mana kayan aiki sai mun tono wannan zinarin na yarda da kai."

Cikin farin ciki Amari ya rungume Ajani yana cewa,

Yene dan uwa.

Gurin tantinsu suka dawo suka ciro kuÉ—i silalar akabawa Kojo, yaje ya sayo kayan aiki.

Tafiya ce ta wuni guda dan haka ya haye rakuminshi ya kutsa cikin gari, bai isa ba sai da duhu ya fara rabawa, sannan ya isa gidansu anan ya kwana washi gari ya shiga kasuwa ya sayi abinda suke bukata wanda, na kayan tono,

Yana gamawa ya aza kayan akan rakuminshi,sannan yabar garin,

Tafiyar kaman dai yanda yazone sai da dare ya fara ya isa gurinsu dan ba iyakar kayan aikin yasaya ba, har da kayan abinci yasaya musu,

Zama sukayi a gurin suka ci abinda ya kawo, sannan suka shiga hira yanda zasu tono rijiyar zinarin.

Suna gurin har dare ya farayi sannan suka shige tantinsu.
****
Washi gari suka je inda suka hango zinarin suka shiga tonoda kwashe kasa, a hankali suka ta aikin tono har dai sukayi nisan zango ga dare yayi dole suka hakura zuwa gobe.

Washi gari ma haka suka cigaba da tonon ba dare ba rana har sai da suka shafe kwanaki goma sha takwas da yini daya babu zinarin babu labarinshi karshe hakura sukayi da tono, duk suka zauna jigum, cike da bakin ciki Amari ya fashe da kuka, wanda ya kashe jikin yan uwanshi, rarrashinsa suka shiga yi, kafin yayi shiru mikewa yayi yace.
"Dole sai na isa ga, Ebo sarkin bokaye dan shine zai iya duba min abinda idanuna ya gani."

Cikin son mara mishi baya suka mike take suka nufi cikin gari, dukda dare ne haka bai hanasu tafiya ba, har suka shiga garin gidansu suka nufa, suka kwana washi gari suka tashi dukkansu suka nufi gidan Ebo.

Sarkin bokayen garin, tun daga bakin kofar gidanshi suka hangoshi kwarjale, irin wanda mahajata ke raɓawa akafaɗarshi hannunshi rike da sandar tsafi, goshinsa yashafa bakin gari, inda yaja jan gari a goshinsa,

"Lalle lallae da zuwan sarakunan karnin farko, barka da zuwanku, a koda yaushe k'addara kamar zare ce mai kaifi, amma shahara da É—aukaka tana biye a bayanta ku shigo ciki."

Jikinsune yayi sanyi, zama sukayi akan fatar zakin dake shimfiÉ—e, a tsakar É—akin, shi kuma ya koma kan kujeranshi.

"Ina jinku."
Yace musu, tunda suka É—auko niyyar zuwa gurinshi, yaji haka ajikinshi sai dai lokacin da ya hangosu yaga tagomashin É—aukaka wanda yake É—auke da duhun na ban mamaki.

Cikin zakuwa Amari ya buÉ—e bakinshi zaice wani abu m, take bokan ya dakatar dashi ya kalli Ajani, ya masa alamun yayi magana.
Cikin nutsuwa ya faÉ—a mishi abinda suka gani.
D'auko wata yar jaka yayi, ya buÉ—e bakinta, ita wannan jakar da fatar jimina akayita, sabida ajiyar abubuwa kananu.

Wasu duwatsune a ciki wanda suke cakuÉ—e da wuri, wasu kalamai bokan yayi sannan ya jijjiga duwatsun ya watsa, a tsorace yakalle su baki É—aya sake É—iba yayi ya watsa, a firgice ya mike yace.
"Shin kungatane?"
Suma atsorace suka kalli juna, sannan suka kalleshi, kaman haÉ—in baki suka ce.
"Wa kake nufi?"

Komawa gurin zamanshi yayi a nutse, yace.
"Sarauniya Mineerlik?"

"Mineerlik kuma? Sarauniya kuma ai mu bamu ganta ba, kawai mage muka gani ita kuma ta zinarice."

Suka faÉ—a mishi haka a tsorace.

"Tabbas ita kuka gani, itace tafito dan sau É—aya take fitowa ashekara, kuma ta tafi bazaku sake ganinta ba sai wata shekara idan da rabon haka kuma ko wace shekara da kalar siffar datake fitowa amma tabbas k'addaranku ce takaiku gurin har kuka ganta."

Shiru sukayi cike da damuwa, suka shiga kallon juna Kojo shi yayi karfin halin tambayar bokan yace
"Wacece ita haka.?"

"A'a É—an saurayi wannan duniyace ta taskar arziki, daula ce ta musaman Sarauniya Mineerlik sunanta sunan kujeranta."

"Toh Ebo taya zamu sake ganinta? Tunda ake kaddaranmu ce ta haÉ—amu da ita domin kuwa wannan zinarin saimun mun mallakesa" Inji Ajani,

Gyara zama yayi cikin yarda da abinda zaice.
"Wato wannan dajin da kuke gani ba daji bane, kamar sauran da dazuzzuka, shi É—in alkarya ce ta aljanu ko nace muku duniyar aljanu ce, shi yasa yake cike da abubuwan al'ajabi, masana tarihi sun tabbatar da cewa, babbar masarautane a gurin me É—auke da babbar fada na sarkin aljanu Penya, shine mamallakin fadar da kuma alummarsu ta aljanu, lokacin da cutan ajali yazowa penya sai ya bar wasiya, koda ya mutum Kalsh shine shine magajinshi, alakacin matar Kalsh Sultana Neelah tana É—auke da tsohon cikin, haihuwa ko yau ko gobe....

Bayan kwana biyu jikin mai martaba penya yayi tsamari, haka duk wasu likitotin gargaji suna fama dashi, tashin hankali yayiwa Kalsh yawa domin a lokacin aka sanar mishi, Sultana Neelah tana, kan gwiwa,

Hankalinshi yayi matukar tashi, ana cikin haka Sarki Penya ya mutu, hankalin Kalsh yayi matukar tashi ga rashin Uba ga matar a wani hali gabi ɗaya sai ya shiga kiɗima, ana hidima kai mahaifinshi amna shi ya koma kofar ɗakin karɓan haihuwa, ya zauna.

Sai da Neelah tashafe kwana biyar sannan ta sami nasaran haihuwar Y'arta mace, mai tsananin kyau wacce tunda ake haihuwa azuri'ar ba'a taɓa samun y'a kamar yarinyar ba, sai dai abin takaici kwanar Sultana Neelah ta mutu sakamakon ciwon cikin haihuwa, gashi a ranar aka bawa Kalsh mulkin garin, ga murna ga bakinciki, fito mishi da Yarinyar jakadiya tayi ta zube a kasa cikin kuka tace.
"Sultan ga yarinyar nan, ta rasa uwarta a daren jiya."
Idanunshi cike da zubda kwalla ya karɓi Yarinyar ya ɗagata ga Alummarshi yace.
"Sultan Kalshe Penya, Nasamu Y'a mace naka mata Suna Mineerlik, haka kuma kujeran mulkina shima sunansa kenan Mineerlik, da fatan ku sanya mata albarka."

Cikin maÉ—aukakkiyar murya alummar aljanu sukace mun ji mun amince da abinda kace munawa Sultana Mineerlik, Barka da zuwa da kuma albarka ya cika rayuwarta."

Juyawa Sultan kalsh yayi rike da jaririyar, zuwa cikin gida ya isa har ɗakin da gawar Sultana Neelah, yana shiga ya zuɓa gwiwarshi cike da zubda kwallah yace.
"Neelah kin É—aukar min alkawari baki cika ba, Ina soyayyar da kika fada min zamu shimfiÉ—a ina kaunar da kika min alkawarin zamu nunawa abin ciknki Neelah ya zaki tafi kibarni da É—awainiyarta, Ina soyayyar da kika min alkawari min, abar kaunata kin tafi kin barni da kewarki da soyayyarki wanda yake tankar gubace a gareni."

Kuka yake cike da damuwa da É—imauta, ruwan kwallar dake zuba daga idanunshi yana sauka akan fuskar mineerlik, a hankali ta buÉ—e idanunta tana kallon mahaifinta, sai ta rufe, sabida É—igar kwalla, jakadiya ce tazo amshi Sultana Mineerlik a hannunshi wacce take motsi da kuka kasa kasa, na alamun yunwa, dan har tasaka hannunta abakinta....
#mamuhgee

*_TARAYYA_*
_wattpad@mamuhgee_
_Haske writers association💡_



*35 to 40*
Not edited.
Kusan kwana uku rumana na halin mutuwa ko rayuwa, maheer ya cira,rai da,sake Samun ta amatsayin abokiyar rayuwa kashi na biyu,
Arazane sultan,adama,ammy,da baqin sarakunan dasukazo suka kalleta
Babu Wanda ta kalla acikinsu tayiwa kaleeb kallo 'daya idanuwanta na sake bushewa cikin gaggawar cika umarninta kaleeb ya daga shar6ebiyar takobinsa mai cire kai lokaci 'daya ya 'dora a wuyan nuratu dake hawaye ta qurawa rumanah ido.

Numfashin wahala mamani ta fitar cikin tashin hankali ta bude baki zatai magana adama datai mutuwar zaune tayi sairi tashi tsaye jikinta na wata irin tsuma zatai magana rumanah ta 'daga hannu batareda takalleta tace,

Duk Wanda yayi magana batareda hukunci ya gama tabbatuwaba abakin rayuwarsu ko wanene.

A gigice adama tasake kallonta cikin wani sabon tashin hankalin takoma ta zauna zufa na karyo mata jikinta na wata irin tsuma.

Tayar da ita akayi tana numfashin azaba takalli takobin datake qyalli a wuyan nuratu takuma tabbarda yankata din za'ayi.

Ahankali rumanah ta 'dagawa kaleeb kai alamar yacika aiki.
Atake ya 'daga takobin cikin wahalalliyar murya mamani tace,

Gimbiya adama ce.

Cak kaleeb ya tsaya sbd harya 'dora takobin a wuyan nuratu harma saida ya'dan yanketa.

Arazace sultan yakalli adama data jiqe jagaf da zufa jikinta na tsuma tanason kare kanta gashi ance duk Wanda yayi magana bbakin ransa kuma tasan tsaf rumanah zata iya sbd tasan abinda ka cikin karagar zaifi shigarta kasancewarta mace dan haka zatafi rashin tausayi da imani.

Sarakunan dake gurin duk ita suke kallo cikin mamaki yayanta kuwa kuka suka fashe dashi gashi babu ikon ko qwaqwaran motsi.

Rufe ido rumanah tayi wani irin yanayi na tsuma zuciyarta gawar 'danta da iyayenta tana mata yawo ido da irin tozarcinda ammy ta fuskanta akan hakan
Fuskar maheer ce ta fado mata da irin tashin hankalinda tagani ataredashi tsakanin jiya zuwa yau ta bude idanuwanta dasukai jajir tace,

Ni sarauniya ummu-rumanah bulama na halastawa takobin kaleeb adana jinin adama kisheer ayau agaban mijinta da 'yayanta tareda sauran alumma duk Wanda ko a fuska ya nuna hukuncina baimasaba a shayar dashi dafi daidai irin Wanda adama tashayarda qannen magajin mineelik.,

Baiwa mamani arufeta mai rubuta tarihi yaje tabasa tarihin sarauniya rumanah arubuta atarihin mineelik tana gamawa bazata qara minti biyar aduniyaba a shayar da ita Kofi 'daya na daafin macijin dayafi kowanne kaifin dafi,
Sultana zaarah da jakadiya sunfita da zargin da ake musu.

Sultan abdulshams arufesa a turakarsa babu shiga babu fita aabisaga zarginsa na qoqarin yanke hukunci batareda bincikeba harsai angama bincike akan niyarsa sultana zaarah ce kawai keda damar shiga da fita agurinsa sai yarima maheer.

Arikice sultan yakalleta ransa na mummunan 6aci da baqin ciki ace rana 'daya cikin mintunan dabasu wuce biyarba baiwa wadda bama asalin 'yar qasaba ta saukesa akan mulkin daya gada iyaye da kakanni,
Ta yankewa matarsa kisan wulaqanci agaban dubban jama'ar dasuke shakkar ko kallon inda yake sannan yanxu tace arufesa a turakarsa wannan shine tozarci mafi muni arayuwa...

Yanxu ta karbi mulki idan tagano shine asalin dalilin mutuwar iyayenta akwai masifa sosai sbd yanda sihirin karagar nan ke shigarta nan cikin qanqanin lokaci zata zamewa kowa masifa mai matuqar hadari musamman shi saidai duk masifa duk balai bazai bari yayi mutuwar wulaqanci a hannuntaba koda hakan na nufin hada hannu da balain da aka binne shekaru tun kafinsu.

Kama adama akayi aka fara janta tayi saurin kwacewa ta isa gaban rumanah ta zube tana kukan tashin hankali jikinta na mugun karkarwa saidai takasa magana sbd umarninda rumanar tabayar ko kallonta rumanah batayiba ta kalli su kaleeb atake suka fara yiwa adama jan wulaqanci.

Jikin ammy ne yadauki rawa cikin sabon tashin hankali take kallon rumanah tana girgiza kai sbd matuqar

Please Login or Register in order to submit comment