Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tayi tare da fad'in Barka da yamma.

Mai martaba Ya amsa da yauwa, yana ga kaman kina cikin damuwa? Domin Fuskanki ya nuna hakan.

Tace inada magana ne akan Yarima.

Da sauri mai martaba yace maiya sami Yarima din??

Tace babu komai magana ne akan auranshi da yake son karawa....

Mai martaba yace ba jiya nace abar wannan maganan ba, sai nan gaba

Tace hakane, amma ina son fad'a maka Yarima yanzu yabar wajena, akan maganan auran nashi, labarin yanda sukai da Yarima ta fad'a mishi harda mafarkin da Yarima yakeyi, sannan tace ina son in baka shawara ,tunda muke da Yarima bamu taba cewa yabar Abu ba, sannan daka baya ya dawo da maganan......

Mai martaba ya dakatar da ita da fad'in, lallai wannan babban magana ne, Yarima yana mana biyayya a matsayin mu na iyaye..... Tunda har na hanashi maganan ya kara taso da ita bai kamata in hanashi ba, domin hanashi zai iya sawa ya bijire mana, domin shi SO daban yake, sannan muma ya kamata mu masa adalci mu amince da duk wata bukatarshi Indai bai sabama Shari'a ba..... Yau na fahimta abunda ya dad'e yana damuwa, lallai iyaye k'alu bale garemu Idan d'anka ko y'arka suna maka biyayya tare dajin duk wata magana taku, Indai yaron ya Kawo muku abu kuka nuna bakwa so, Indai ya dage Toh ku tayashi son Abun tare da mishi fatan alkhairi..... Sau da yawa wasu iyayen suke saka yaransu suke bijire musu Bayan yaran suke da gskya amma iyayen Suki yarda da kudiran yaran, in ba'a sami Mai hakuri ba saiya bijire musu, yaka mata iyaye su dinga Lura da miye yaransu suke so tare da abunda suke bukata.... Kar matsayinku na iyaye yasa ku manta hakkin yaranku akanku...... Haka zalika Kuma yaran Kar soyayya yasa ku bijire ma iyayenku ,domin Kaf duniya babu mai muku son gskya kaman iyayenku....... Akwai wani labari da naji na wani yaro da yake son auran wata yarinya....... Yarinyar kowa yasan bata ji, Ma'ana dai y'ar iska ce yarinyar, lokacin da yaron Ya fad'ama ma iyayenshi sai suka k'i yarda suka ce ya nemi wata, shiko yaron yace Wlh ita yake so, aka buga aka raya, Baban yaron yace sam bai yarda Yaronshi ya auro yarinyar ba domin y'ar iska ce....... Ganin yanda babanshi ya dage, sai yaron Ya daina musu komai dama iyayen ba masu karfi bane, yaron ke musu komai tunda yana aiki,...... Toh Kunga irin matsalolin dake faruwa, a sanda naji wannan labarin Nayi takaici Sosai, ai iyaye iyaye ne, yaka mata mu dinga hakuri dasu, mu muna ganin mune akan dai dai, haka suma suke gani sune akan dai dai, in kayi hakuri kabi umarnin su, kasan kwana nawa za suyi a duniyar?? Koko saika rasa su zaka Fara kuka dayin dana sani?? Wlh baka taba sanin muhimmancin iyaye sai basa raye, sai munyi hakuri da iyayenmu sau da yawa kana ganin abunda yake dai dai kuma kowa yasan dai dai ne amma su sai suce sam, in mutum ya duba Aida basa haka, yanzu harda girma daya kamasu sai yasa suke irin haka, Idan mutum yana girma tunaninshi yana kara canzawa...... Idan har yaro yana tuna haka ya kamata ya dinga hakuri da iyayenshi, sannan abunda kama iyayenka kaima haka naka za suyi maka shairi ko khairan, sannan Indai kai burinka kuntata ma iyaye bazaka taba ganin haske ba a rayuwa..

Mum tace hakane, Allah yasa mu dace

Mai martaba ya amsa da Ameen, tare da fad'in zan tura aje a nema masa auran yarinyar cikin satin nan insha Allah, saiku Fara shiri

Mum tayi y'ar murmushi tare da fad'in Allah ya bada Sa'a zamma Yarima albishir

Dariya Mai martaba yayi tare da fad'in dan nema ba, Ashe tun a mafarki yake ganin yarinyar ikon Allah.

Mum tace Wlh nima nayi mamaki, Allah dai yasa abokiyar zama ce.

Mai martaba yace lallai soyayyarsu had'in Allah ne, duk Wanda yace zai shiga tsakani akwai matsala

Mum tace hakane, tayu rabo ne na kusa tsakani sai yasa ya kasa hakuri, kuma rabo na kisa

Mai martaba yace hakane, Allah ya shige mana gaba.....



Mai martaba yasa an tura gidansu bariki, inda su waziri suka je, kuma babu laifi su waziri Sun yaba da irin gidan tarbiyan da bariki ta fito, domin tunda Yarima ya fad'a mata ranan da za suzo bariki ta hayo wasu mutum biyu Sunan sune y'an uwan mahaifinta, sannan duk ta tsara musu yanda za suyi.

Koda waziri yayi maganan sadaki akan nawa zasu yanke

D'aya daka cikin kawun Bariki na karya yace dubu hamsin ya isa, domin karancin sadaki shine albarkan aure,

Waziri yaji dad'i Sosai domin ya gano gidan mutunci Yarima yake neman aure sannan ba masu kwadayin abun duniya bane, duk da ya gansu talakawa kuma ko yanzu a sauron gidan suke zaune, Ma'ana a zaure.

Nan take Waliyan Yarima suka biya sadaki, dubu hamsin tare da K'ara million d'aya suka ce wannan kaman matsayin kyautatawa ne, tunda iya abunda suka yanke shine na sadakin,

Dakyar iyayen bariki suka amshi kud'in, domin cikin mutanan Yarima sunce gidan sarauta in sun bada Abu dole ake amsa, ba'a miyar musu. Sannan an tsaida rana nan da wata biyu

Nan dai akayi addu'a tare da tashi kowa Ya wuce.....

Cikin Wanda sukazo daka gefen Yarima harda Mai Anguwa, ma'ana sarkin u/kanawa, wanda Kafin su zo shine aka bama damar yin bincike akan gidansu yarinyar da irin tarbiyanta, kuma yace babu wani matsala gidan tarbiya yarinyar take Yadai yi magana Mai Kyau akan gidansu bariki 🤔 ko Mai yasa yayi haka?? Bayan yasan yanda sarauta take?? Sannan hausawa na cewa shidai ramin karya kurarre ne, koma dai miye dalili za muji zamu gani....

Koda su waziri suka koma, sunyi ma Mai martaba bayanin irin gidansu bariki, Sun fad'a mishi gidan mutunci Yarima yake neman aure, sannan suka kara da fad'amai sai dai talakawa ne Sosai ba masu karfi bane, domin yana yin gidansu ya nuna hakan, kuma kaman gidan Haya suke, waziri ya kara da fad'in sai dai abunda ya kara burgeni duk da irin talaucin su , suna da wadatar zuci, basu da kwadayin abun duniya

Mai martaba yaji dad'i Sosai, tare da fad'in ina son Kafin Ayi bikin a nema musu Gida su koma, wannan kyauta ce daka gareni

Waziri yace an gama godiya suke .

Bariki bayan magabatan Yarima sun tafi, ta fito ta sami babanta na Bariki da sauran mutanan, nan suka bata kud'in, sannan ta sallami mutum biyu din akan saita kara nemansu. Tafiya sukayi suna godiya.

Kallon abbanta na Bariki tayi tace gskya aiki yayi kyau

Yace Sosai kuwa, sai naji dama auran nan da iyayenki na gskya kika had'asu, ina tsoran ranan da asiri zai tonu

Bariki tace karka damu, komai a tsari nake tafiyar dashi.

Yace dakyau tare da fad'in ni kam inda mmnki zata yarda Aida munyi aure

Bariki tace dagaske kakeyi?

Yace dagaske nake Wlh

Bariki tace Aikam zan mata magana sannan ni zan biya sadaki, da kayan lefe akwati guda biyu ai zan had'a maka Indai dagaske ne wlh, nima na samu lada

Yace ina godiya Kinga gwara Ayi auran, tunda nida ita Kar tasan Kar ne

Dariya bariki tayi tare da fad'in wannan haka yake.

Yarima Aliyu yana barin asibiti ,direct wajan bariki ya nufa, inda bata ma San da zuwanshi ba, saida ya kirata yace ta fito yana waje, Dan haka ta tashi ta fita ta sameshi a mota

Yarima kallonta yayi cikin jin dad'i tare da fad'in amaryata

Murmushi tayi cikin jin kunya tare da gaidashi

Amsawa yayi tare daja mata hanci, yace am so happy today

Kallonshi tayi tare da fad'in happy for wht?

Yace soon zaki zama tawa ..... Oh na manta kin ma riga kin zama, Ashe an bani ke har an biya sadaki...

Murmushi kawai tayi

Yarima yace yaushe za muje kiga gininki?

Tace a'a basai Naje ba,

Yace toh ni ina son kije ki gani , ya za'ayi kenan??

Tace zan tambayi Umma inta amince sai muje

Murmushi yayi kawai tare da kawar da maganan yace, Mai kike bukata Ayi da bikin mu??

Tace kaman me??

Yace event din da za'ayi

Shuru tayi tana nazari inta yarda Ayi event Kar a wajan event taga Wanda ta sani, Kar su fad'ama Yarima gskya Kafin ita ta fad'amai, kai gskya a'a.. Kallon Yarima tayi wanda shima ita yake kallo tace Yarima inaga Kar Ayi wani bidi'a.....

Kamo hannunta yayi tare da fad'in, a'a ya kamata muyi koda Abu d'aya ne, muyi dinner, inaga zaifi

Tace toh amma fah badan taso ba, ta dai amince ne dan Kar yaga kaman ta'ki yarda da maganansa.....

Kallonta yayi yace tunda an gama maganan event saura na akwati zan baki kud'i Kisai irin kayan da kike so, duk da za'a kawo miki daka gidanmu, wannan wanda zan baki akwai wanda nake bukata ki siya wanda only me zan dinga ganinki dashi, saiki K'ara da irin naki choice din .

Bariki ido ta rufe ciki jin kunyan maganan Yarima, ta rasa mai yasa Idan yayi mata wata maganan take jin kunya Bayan tasan ita bata jin kunyan magana gaban kowa, kodan Yarima badan iska bane sai yasa nake jin kunyan shi? Tabbas hakane domin duk Wanda kuka ga yana maganan banza gaban wani in kuka duba za kuga shiya bada dama Ayi mishi.

Sunyi fira akan in zai dawo zai Kawo Mata kud'i cash ta siya abunda take so sannan ya Mata sallama ya tafi ..... Toh andai ce duk abunda akace an yishi had'e da karya komai daren dad'ewa gskya zata bayyana, zamu gani asiri zai tonu Kafin biki ko sai Bayan biki muje zuwa........










~MARYAM OBAM~

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment