Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wannan lokacine sarki hudes ya sa aka
kwance igiyar data daure jarumi hubairu da
waziri
kuddaru
kafin wani daga cikinsu yace uffan tuni sarki
hudes ya bada umarnin subar
garin
nanfa aka dauke jarumi hubairu, waziri kuddaru
da gimbiya sima sukayi sama
cikin 'yan dakiku kadan aka kule acikin gajimare
al'amarin daya jefa mutanen birnin tehran cikin
rudani da rikitar kwakwalwa
domin wannan shine karo na biyu da mutuwar
sarkinsu lu'umanu mutuwar da basu da
tabbacinta
awannan karo na farko sunga ya mutu kuma y
dawo to shin wannan karon ma zai sake
dawowane
wannan tambayar babu wanda yasan amsarta
aduk fadin garin
shin zasu sake nada sabon sarkine ko kuwa
zasu
jirane zuwa wani lokacin kamar yadda akayi a
wancan karon? WANNAN SHINE ABIN DAYA
FARU ABIRNIN
TEHRAN BAYAN ANYI GAGARUMIN YAKI
TSAKANIN SARKI HUDES DA ALJANI
ZARMUKU
ALJANIN DAYA ZAMA DAYA DAGA CIKIN
ALJANUN DA SUKE SHIGA JIKIN GANGAR
JIKIN
SARKI LU'UMANU SUNA BARNA ADORON
KASA Bayan bakar gizon ya bace bat da
zarmuku da
gangar jikin lu'umanu bai sake baiyana ba say a
tsakiyar fadar nan wacce akewa lakabi da.
BAHAR ZUZ DA BAYYANARSU SAI BAKAN
GIZON
NAN ya rikide ya zama BOKA SHAMHARU
cikin fushi yayi wurgi da aljani zarmuku kamar
yayi wulli da jikakken tsumma
ahankali ya ajiye gangar jikin lu'umanu akan
tebur
adaidai wannan lokacine gaba daya hadimansa
sukayi sujjada agareshi cikin girmamawa
shikuwa zarmuku sai ya kama kuka saboda
takaici musamman idan ya dubi dungulmin
hannunsa mai zubar jini
shamharu ya nuna wata kofar lu'u lu'u da
hannun
sa sai kofar ta bude
sarki lu'umanu ya fito daga cikin ta ya taho
garesu cikin kunar rai da fushi sannan ya dubi
shamharu yace
ya shugabana yana dakyau ka barni na shiga
jikin
gangar jikin nan nawa dakaina naci gaba da
yakar makiayan mu na karar dasu gaba daya
don na fuskanci cewa su zarmuku bazasu iyayin
komai ba.
Mu hadu a part D don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU✍️✍️
PART D ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Cikin alamun damuwa shamharu ya dafa
kafadar
lu'umanu yace
yakai babban wakilina adoron kasa kayi sani
cewa banida kamarka aduk cikin bil'adama
kuma
na sani cewa aikin da zaka iya yi mini babu wani
aljani dazai iya yinsa
amma ka sani cewa ma'abota addinin
musuluncin
nan hatsabibaine matuka
musamman sarki hudes dinnan ina shakkarsa
domin sihirinsa nada matukar karfin da zai iya
nasara akanka,shiyasa bazan bari kayi fito na
fitoba dashi
gwara day muci gaba da amfani da gangar
jikinka
amma ruhinka yaci gaba da zama anan harsai
ragowar aljanun guda dari tara da casa'in da
takwas sun kare
yanzu aljanin dazai shiga gangar jikinka shine
makabu
makabus yafi aljani zarmuku karfi, juriya
da jarumta sau arba'n,tabbas ina ganin zai iya
kawar dasu sarki hudes
nida kai zamuci gaba da aikina na cika
MATSATSUBI
ina mai bakin cikin sanar dakai wani bakin labari
bisa wata babbar masifa datakeson afko mana
tabbas idan her masifar nan ta samemu tamu ta
kare
kuma dukkan shirin my ya wargatse
cikin tsananin damuwa lu'umanu ya sake
rissinawa yace
ya shugabana wace irin masiface ke ahirin afko
mana?
maimakon shamharu ya ce wani abu sai yayi
nuni da hannunsa izuwa wani babban allon tsafi
take hoton sundukin haske ya bayyana sai gashi
dauke da birirrika guda ahida
acikinsa yana mai tsala gudu
shamharu ya ce kaga wadannnan birarrika na
cikin
sundukin nan to ba birarrika bane,sarki azbir ne
tareda su jafar yelisa, mashrila, mazlish da
kuma
aljani gulzum
tun tuni nayi maka bayanin ko suwaye su jafar
da irin bala'in da suka janyo mana
wannan sundukin da kake gani daga can wata
duniyar aka aikoshi
don ya narkar da duniyar su jafar
idan har duniyar su ta narke tamkar ankone
sirrikan tsafinane gaba daya
dani da kai da dukkan hadimaina mutuwa
zamuyi
gaba daya
kodajin wannan batu sai hankalin lu'umanu ya
dugunzuma yace
ya shugabana yanzu menene abinyi?
shamharu yayi ajiyar zuciya yace
abinyi guda daya ne tak Yanzu zan nuna maka
shi ka gani
nantake shamharu ya shafi allon tsafinsa
say sunduki sarki azmul gallar ya bace
wani sabon sundukin ya baiyana wanda ya
kasance ankerashine
da zallan lu'u lu'u kuma yana dauke da wasu
dakarun boka shamharu guda goma sha biyu
acikinsa
sundukin nata tsala gudu acikin sararin
samaniya
tamkar gudun tauraruwa mai wutsiya shamharu
ya ce
kaga wannan sundukin nawane kuma na
turashine don yaje yayi karo
da sundukin azmul gallar su tarwatse gaba daya
asama
shin tabbas idan sukayi karon zasu tarwatse?
lu'umanu ya tambaya
shamharu ya ce haka dai nake kyautata zato
amma banida tabbas, lu'umanu ya ja dogon
numfashi yace ya shugabana kayi
hakuri d yawan tambayoyina kasan na kasance
cikin damuwa
shamharu ya kyalkyale da dariya yace karka
damu ina son bil'adama mai yawan tambaya
domin ni kaina ina kara samun ilimi daga cikin
tambaya
fadi kome kake son fadi zan bka amsa iyakar
sanina
lu'umanu yayi gyaran murya yace
yanzu idan sundukin nan guda biyu suka hadu
suka tarwatse halittun dake cikin sa suma sun
hallaka kenan?
kodajin wannan tambaya sai shamharu ya
bushe
da dariya yace
kwarai kuwa ai indai sukayi karon nan say su
jafar sun hallaka
hakama dakarun dake cikin nawa sundukin
yanzu haka shingin sa'a uku kacal sundukin ya
riski sundukin azmul gallar
don haka say muci gaba da kallon allon tsafin
nan
don muga abinda zai faru idan sundukin biyu
suka hadu
yayin da shamharu yazo nan azancensa sai
sarki
lu'umanu ya sake kidima
yayi shiru yana mai kallon allon tsafi kawai
daga nan kuma sai ya dubi shamharu yace
ya shugabana dazu kace wancan sundukin
dazai
hallaka duniyarmu daga wata duniyar aka
aikoshi
kuma yanzu naji kace sundukin sarki azmul
gallar
kuma awacce duniyar yake
shamharu yayi murmushi yace
hakika kayi tambaya mai amfani kuma mai
mahimmanci,
yakai lu'umanu kayi sani cewa
sarki azmul gallar shine ke mulkin wata duniya
dake sama
wacce akewa lakabi da duniyar iska
yana zaune acikin babban birnin kasar
wanda ake kira da harjulul mulk aduk dunuyoyin
dake sama babu mai girma da fadi kamar
duniyar
iska
kuma halittun cikintama sunfi nako ina karfin
sihiri da hikima
sarki azmul gallar yayi bincike y gano cewa duk
cikin duniyoyin dale sama da kasa babu waji
sarki
mai karfin sihiri kamarsa face ni
don haka na zama babban makiyinsa
babu yadda za'ayi yasan sirrikan tsafina face ya
narkar da duniyar ku
ni kuma babu yadda za'ayi nasan sirrikan
tsafinsa face an kammala rubutun KUNDUN
TSATSUBA na biyu
wanda a halin yanzu su ruziyal suke kan aikinsa
bayan ya sami nasarar narkarda duniyar kune
zai
debi kasarta ya maida ita kankanuwa
sannan ya kera kubar MIFTAHUL ZARBIL da ita
idan yayi wannan kuba zaiyi amfanida ita wajen
kulle nasa KUNDUN TSATSUBAN wanda yanzu
haka yana nan a kulle acikin fadadsa wacce ake
kira da saukatul askur
yakai lu'umanu kayi sani cewa halwar tsafin
dana
shiga kwanakin baya na gano hanyarda zambi
na
zamo matsatsubi da wur wuri
basai nabi waccan hanyarda nakeson biba da
farko
hanyar kuwa itace ta shiga fadar saukatul askur
don sato kundun tsatsuban sarki azmul gallar
shiga wannan fada ba karamin bala'i bane da
tashin hankali agareni.
kayi sani cewa zuwana duniyar iska abune mai
sauki kamar cire silin gashi daga cikin tandun
mai
ammafa bazan iya shiga fadar sa ba face na
kera
wata kubar wacce zata bude kofar shiga fadar
ita kuwa wannan kuba daidaì take da
MIFTAHUL
ZARBIL
irin wacce za'a kulle KUNDUN TSATSUBAN da
ita
idan ina so na kera wannan kuba cikin kankanin
lokaci saina samo abu uku
abu na farko shine narkakken ruwan dutsen da
yafi kowanne dutse girma aduniya
abu na biyu shine dutsen wuta wanda ke cikin
duniyar karshe ta duniyoyin kasa
abu na uku shine rabin ruwan tekun dun8ya kaf
wadannnan abubuwa uku su za'a cakuda adafa
su sannan a sana'anta kubar MIFTAHUL
ZARBIL
wacce zan iya bude kofar fadar saukatul askur
da
ita
don na dauko kundun tsatsuban sarki azmul
gallar
idan har na karanta wannan littafi saina sirrikan
tsafi gud@ dubu sau dubu
wato ninkin na cikin nawa kundun tsatsuban
koda shamharu yazo nan azancensa sai
lu'umanu
yayi ajiyar zuciya yace
ya shugabana ai wahalar wannan aiki
tafi ta mujira agama rubutun kundun tsatsuba
na
biyu
nikam banga ta yadda zaka iya samo
wadannnan
abubuwa uku ba
harka kera kubar da zaka bude fadar saukatul
askur da itaba
idan kuwa kayi hakuri nanda ahekaru ashirin
za'a
iya gama rubutun sabon kundi
cikin tsawa da fushi boka shamharu yace
kai lu'umanu ashe baka da hankali bak@ da
wayo
ai idan na bari akakai wannan lokaci su jafar
zasu iy gama karance kundun tsatsuba
sa'ata kawai itace ace a yanzu su hallaka acikin
sundukin haske na sarki azmul galllar
yanzu dai ka saurara kaga abinda zai farù
garesu
bayan nan zanyi maka bayanin yadda zamu
samo
wadannnan abubuwa uku acikin kwanaki
arba'in
kuma zan sanar dakai yadda zamuyi sihiri mu
tafi
duniyar iska don mu yaki sarki azmul gallar
mu hallakashi tareda jama'arsa sannan mu
shiga
fadarsa mu dauko kundun tsatsuban sa
koda shamharu yazo nan azancemsa
say yayi shiru baikara cewa komaiba
har lu'umanu ya bude baki
zaice wani abu sai yayi masa nuni da yayi shiru
su duka biyun suka kurawa allon tsafin idanu
suna kallon
yadda sundukin shamharu ke keta giza gizai
asararin samaniya
aikuwa sa'a uku na cika saiga sundukin azmul
gallar ya doso kan sundukin shamharu
cikin abinda bai wuce dakika daya ba
sundukan biyu suk@yi karoda juna
take sundukin shamharu ya tarwatse ya
dagargaje asama babu abinda ya rage ajikinsa
face ruburbushin wuta da toka
lokacinda wannan abu ya faru saida fadar
shamharu tayi girgiza zata rushe
faruw@r 'akan keda wuya sai sukaga wata iska
mai karfi ta fasa
sundukin hasken azmul gallar ta debe birarrikan
nan guda shidata bace dasu
take shima wannan sundukin ya bashe ya
dagargaje
koda ganin haka sai shamharu ya shafi allon
tsafinsa hoton ya bace
cikin tsananin bakin ciki shamharu ya takarkare
ya kwarara uban ihu
sannan ya fashe da kuka, al'amarin daya janyo
girgizar kasa afadar tasa kenan
saida rabin sa'a ta shude sannan fadar ta samu
ta tsaya waje guda.
Mu hadu a part E don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏
Najibullahi Muhammad ☝️
#LEGENDs.
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU✍️✍️
PART E ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
marubucin littafin ya ci gaba da cewa...
Cikin fargaba d tsoro sarki lu'umanu ya matso
kusa DA shamharu yace
yashugabana menene ma'anar wannabe Abu daya
faru?
shamharu ya dagakai ya dubi Lu'umanu idanunsa
back DA wuta
din tsananin takaici yace
shikenan anyi biyu babu
bukata batata biyaba
haka ma ta sarki azmul gallar
yakai lu'umnu kayi Sam I cewa wannan iska daka
Gabi wacce ta fasa sundukin sarki azmul gallar ta
zuke su jafaru dake ciki
bakomai bace face iskar kundun tsatsuba
kuma y karanta kansa sannan yabi su jafar inda
suke ya zukosu
suka fada cikinsa dama ka'idarsa kenan
yanzu babu abinda zamuyi face ka biyoni izuwa
cikin dakin halwata
domin muyi wani aiki na tsawon sa'a guda cif
amma kafin hakan zansa aljani makabus ya shiga
jikinka y tafi izuwa birnin tehran
domin yaci vaba da mulki domin yanzu haka
mutanenka sun shiga tararrabi
irin wanda suka shiga awancan karon
saukinta ma mun taho d gangar jikinka bamu
barta acan ba
shamharu ya dubi makabus yace na umarceka
daka shiga cikin jikin nan
kuma idan kaje birnin tehran kayi mulki irin
wanda sarki lu'umanu yakeyi
bayan kwana biyu kayi shiri ka tafi neman
gimbiya sima wacce ke tareda su sarki hudes
duk bala'in da za'ayi ka tabbat ka rabasu da
gimbiya sima inyaso saika gudo da ita izuwa nan
nidakaina zan daura aurenta da lu'umanu
koda gama fadin haka say aljani makabus yace
angma ya shugana
nantake aljani makabus ya rikide yazama haske
ya shiga jikin gangar jikin lu'umanu wacce ke
kwance akan tebur kamar gawa
shigar hasken keda wuya sai gangar jikin ta mike
zumbur
kawai saita rikide ta koma aljani makabus take ya
mike tsaye tsaye ya bude fuka fukansa yayi sama
ya ratsa ta cikin gini kamar yadda danshin ruwa
ke ratsa gini yayi fitar burgu
bayan faruwar hakan say sarki shamharu ya dubi
aljani zarmuku ya daka masa tsawa yace
banza rago
tashi kaje ka cigaba da aikinda kakeyi afadar nan
tunda ka zama nakasasshe bazaka iyayin aiki
awajeba
cikin biyayya da kakkarwar jiki zarmuku yace
angma ya shugabana nan da nan zarmuku ya
shiga wata kofa shi kuwa shamharu saiya kama
hannun lu'umanu ya shiga dashi cikin dakin
halwarsa ta tsafi
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU TSAKANIN
BOKA SHAMHARU DA RUHIN LU'UMANU ACAN
FADARSA DAKE TSUBURIN BAHAR ZUS
Acan fadar sarki dujalu kuwa hankalin kowa
adugunzume yake
shidai sarki dujalu ya tsorata ainun d tsoho
rafkanagu domin ko alanari baitaba jin ance ga
wani mutum daya jefa mage abakinsa ba da ranta
ya taune ya hadiyeta ba
amma yau gashi y gani da idonsa
tabbas zuciyarsa ta fara saka masa cewa duk
yadda akayi rafkanagu ba mutum bane aljanine
abangaren tsoho rafkanagu, ruziyal, da boka
hajarul makarus kuwa hankalin su ya tashi
sakamakon tsoron kada sarki dujalu ya ki karasa
musu wannan labarin na bokanya tazubul luhucul
lokacin da ayyuka suka rikice afadar sai sarki
dujalu yace afitar da tsoho rafakanagu daga cikin
fadar
har antusa keyarsa za'a fita dasu say boka
hajarul makarus ya dubi sarki dujalu yace
yakai wannan sarki mai adalci da cikar mulki shin
kayi imani da tsafi kuwa?
sarki y daga hannu alamar adawo dasu take aka
maido dasu hajarul makarus yace
saboda na fuskanci cewa baka da kariyar tsafi
ajikinka
ka tuna cewa awancan karon an turo damisa
gidanka donta hallaka ka,
yanzu kuma an turo mage gidanka don ta
hallakaka
amma duk ka kasa fahimtar cewa makiyanka ne
ke son ganin bayanka
yanzu take zan nuna maka hujja don ka gamsu
da zancena
ina mai sanar da kai cewa nida abokan tafiyata
matsafane ahiyasa muka gano haka
kafin sarki dujalu yace wani abu tuni hajarul
makarus yayi nuni da hannunsa izuwa g bango
saiga hoton wadansu mutum biyu ya bayyana
sunayin maganar sirri acikin wani daki
daya daga cikinsu sunansa amad wandaya
kasance kanine ga sarki dujalu uwa daya uba
daya
dayan kuwa sunansa madarus yakasance sarkin
yakin birnin
armad ya dubi madarus yace
kai ammafa shegen sarkin nan namu ya cika
taurin rai
ka dubafa ka gani mun tsafance damisar gidansa
donta kasheshi amma ya tsallake
munsake tsafance kyanwar gidansa ya tsallake
kaga inda ya mutu da tuni na zama sarki kai
kuma ka zama wazirina
yanzu menene abinyi?
madarus yace abinyi kawai shine ka tashi mu
koma wajen bokana don ya bamu wata sa'ar
ai ance mai nema yana tareda samu
armad yace kwarai kuwa
nantake suka fice daga cikin dakin gaba daya
asannan ne hajarul makarus ya sake nuna
bangon da hannunsa hoton ya bace
dujalu yayi ajiyar numfashi ya kama yiwa tsoho
rafkanagu godiya bisa taimakonsa da yayi
nan take sarki dujalu ya a tura aka kamo dan
uwansa armad da sarkin yaki makarus aka
bankaresu ya tsiresu da mashi da hannunsa
sannan aka kwashe gawarwakinsu akai waje dasu
bayi sukayisauri suka goge jinin daya zuba agurin
sarki dujalu ya koma kan karagarsa ya zauna
sannan aka kawo sihirtaccen shayi aka baiwa
kowa yasha harda shì kansa
sannan yayi gyaran murya yace
to saiku shirya zanci gaba daga inda na tsaya
acikin labarin hikayar bokanya tazubul luhucul
dujalu ya sakeyin gyaran murya
Bayansu yarima sammaru sun gama begen
gimbiya fauwaz acikin zuciyoyinsu
sakamakon ganinta da sukayì acikin madubin
tsafi
sai boka hulumul bakahur ya dubesu daya bayan
daya yace
yanzu wacce shawara kuka yanke?
shin zakuyi wannan tafiyane akan dawakai ko
kuwa akan aljanu zaku tafi?
gaba dayansu sukayi shiru suna dùban juna aka
rasa wanda zaice uffan
daga can sai gimbiya ashwarya tace haba ya
za'ayi mu zabi wahala alhalìn ga sauki
aikawai ka hadamu da hadimankasu kaimu
nikam na sallama rayuwata don ceton mahaifina,
dadaina koma gida babu maganin cutar nan
gwara na mùtum awajen nemansa
koda ta gama fadin haka saita dubi yarima
lubaiku, yarima larbuz, yarima sammaru, yarima
lauhana, da boka karluz tace
shin acikinku akwai mai shawara daban wadda
batayi daidai da tawaba?
gaba day@nsù suka sakeyin shiru daga bisani
suka ce
muma mundauki zabinki na t@fiýa akan hadimam
hulumul bakahur
koda jin haka sai boka hulumul bakahur ya
kyalkyale da dariý@ yace
yanzun nan kuwa zaku tafi izuwa kogon muddarul
ikisina
batareda bata lokaciba boka hulumul bakahur ya
kira sunayen wadansu aljanu guda shid@ guluz,
amzil, hurus, karmash, karfil da azgar suka
bayyana agabansa, gaba dayan wadannan aljanu
sun kasance manya manya masu siffofin jakin
dawa
saidai sunada fuka fukai guda hudu,
kuma sunada hannaye hur hudu irin na bil'adama
masu dauke da yatsu biyar da cako cakon farata,
komai nasu iri dayane babu wanda yafi wani
girma
kuma jikinsu gaba d@ya alullube yake da farin
gashi tamkar fatar rago kuma ga laushi
boka hulumul bakahur ya dubi aljanun shida yace
yaku manyan hadimaina kuyi sani cewa
ban kiraku nanba saidon ku debi jaruman nan
guda biyar tare da boka karluz ku tafi dasu izuwa
tsakiyar duniyar nan tamu inda bishiyar gwandar
nan take mai tsawon zira'I dari uku
kodajin wannan batu saì guluz, amzil, hurus,
karmash, karfil da azgar suka fashe da kuka gaba
d@yanSù,
cikin matukar damuwa guluz ya dago kai ya dùbi
boka hulumul bakahur yace
ya shugabana kayi sani cewa babu wani aiki da
z@ka umarcemu dayì muki yinsa
ina mai rokonka daka sauya mana wannan aiki d
wani
domin tabbas mumsan bamu isa mu iya kètarè
dazuzzukan nan guda uku b@
masu mugun hatsari face mun zama gawa
kayi sani cewa iyayenmu da kakannin mu sun
hallakane acìkin wadannan dazuzzukan
lokacinda suke bauta ga mahainka,
mai zai hana kayi mana adalci muci gaba da
rayuwa.
Mu hadu a part F din Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART F ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Wannan kalami na aljani guluz ba karamin firgita jaruman shida yayiba
domin sun fara tunani aransu cewa
lallai abinda yasa aljanun firgita b karami bane
yarima sammaru da gimbiya ashwarya ne kadai basu firgitaba
domin sun sallama rayuwarsu bisa wannan tafiya
basa tunanin dawowa araye saidai da yake dan adam baya fitar da rai ga samun rabo
suna masu fatan samun dacewa
boka hulumul bakahur ya dubi aljani guluz ya daka masa tsawa yace
dolene kuyi wannan tafiya walau zaku dawo ko ba zaku dawoba idan kuwa kuka bijere mini dayanku bazai sake shakar numfashiba
cikin rawar jiki su duka sukayì sujjada ga hulumul bakahur suna masu cewa
tuba muke ya shugaban mu
ba tareda bata lokaciba hulumul bakahur ya sa aka kawowa matafiyan guziri mai yawa aka dora akan aljanun guda shida
sannan hulumul bakahur ya dauko wani mulmulallen siririn ice
wanda akan tsininsa akwai kyallin haske
ya mikawa yarima sammaru yace
kaine shugaban wannan tafiya ungo wannan ka rike
idan kukaje gindin wannan doguwar bishiyar gwandar kayi nuni da wannan ice izuwa karkashinta
take kasa zata bude ku shige cikinta harku isa tsakanin duniyar bakwai da duniya
ta takwas inda kogon muddarul ikisina yake
ku sani cewa tun kafin ku shiga cikin karkashin kasa
zakuyi sallama da wadannan hadiman nawa wato guluz don su dawo gareni
idan har sun tsira da rayuwarsu kafin ku isa
hulumul bakahur ya bude tafin hannunsa sai g wani kuttu yace
ungo wannan ka rike shi da kyau bakomai bane
face maganin rauni
duk wanda yaji ciwo acikinku ku zuba masa wannan maganin akan ciwonsa
take jinin zai tsaya
kuma ciwon zai warke sumul komai girmansa da muninsa
wannan ce kadai gudun mawar da zan iya baku ta karshe
ina mai muku sallama tareda fatan samun nasara
tabbas nasararku nasarata ce
ina mai yi muku tuni da cewar koda kun samu nasara ba lallai bane ku dawo gabadayanku ba cikin koshin lafiya
koda boka hulumul bakahur yazo nan azancensa saiya juya ya shige cikin wata kofa ya kulle
jaruman suka tsaya suna kallon junansu
sukuwa aljanun sai sukayì zugum kamar an aiko musu da sakon mutuwa
boka karluz yace
to me muke jira ne aisai kuzo mu tafi
kafin dayansu yace wani abu tuni boka karluz y haye bayan aljani guluz
cikin sauri yarima sammaru ya daka tsalle ya dirga akan aljani amzil
yauhana ya hau kan hurus, yarima lubaiku ya hau kan karmash
yarima larbuz ya hau kan karfil, itakuwa gimbiya ashwarya ta daka tsalle ta haye kan aljani azgar
nan take aljanun suka bude fukafukansu suka tashi dasu sama
suka fice daga fadar ta cikin wata wangamemiyar taga
sannan suka luluka sama sukaci gaba da tsala gudu
duk wanda yaga wadannan aljanu guda shida asararin sama
awannan lokaci dolene su birgeshi su bashi sha'awa
amma inda yasan inda zasu nufa da saiya zubar musu da hawaye su baka tausayi
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU YARIMA SAMMARU BAYAN SUN HADU SU SHIDA AFADAR BOKA HULUMUL BAKAHUR
al'amarin bokanya tazubul luhucul kuwa
lokacinda ta isa birnin hindu tareda hadimanta
bata samu wata matsala domin cikin 'yan dakiku kadan ta sami nasarar sakawa sarki bahacal cutar mutuwar barin jiki
tareda duk makusantansa
batareda bata lokaciba ta wuce birnin farisa
acanne ta gamuda muguwar matsala wadda tasa taji kamar ta fashe da kuka
bakomai bane ya janyo hakanba face ta tararda cewa sarki katimul barhul da yan majalisarsa sun kasance tare waje daya
sunata bautar gunki acikin wani daki na gidan sarautar
daya bayan daya ta rinka tura hadimanta don cika aiki duk saida suka mutu
guda daya ce tayi saura, saida rabin jikinta ya kone wannan hadiman na kiranta da suna izlis
yayinda izilu taga rabin jikinta ya kone saita fashe da kuka ta dubi lazibul luhucul tace
ya shugabata kinga dai abindaya faru ga yan uwana duk sun mutu
saura ni kadai, nima din kuma gashi rabin jikina ya kone,
kiyi sani cewa babu irin dabarun da bamuyiba,
don ganin mun sami sa'a amma abu ya faskara ,
na rantse da darajar tsafinki idan kika sake turani mutuwa zanyi
ina mai rokonki dakije da kanki ki aiwatar da wannan aiki domin yafi karfina
kodajin haka sai jikin tazubul luhucul yayi sanyi
ta kasa cewa komai daga can sai idanunta suka ciko da kwalla
bakomai bane ya haddasa hakanba face takaici da bakinciki
wai ace kamar ita yau ga wani aiki ya gagareta
cikin tsananin fushi tazubul luhucul ta bace ta bayyana akofar dakin da sarki katimul barhul da yan majalisarsa suke ciki suna bautar gunki
kai tsaye tasa hannunta n hagu ta bude kofar ahankali
faruwar hakan keda wuya sai wani irin haske ya fito daga cikin dakin ya bugi hannunta
take hannunta ya soye ya motse kamar an tsoma auduga acikin ruwan zafi
tazubul luhucul ta kwarara ihu mai ban tsoro ta bace bat
daga wajen saitaga ta sake bayyana agaban azlis
koda azlis taga shugabarta da motattsen hannu saita sunkuyar da kanta don biyayya
a sannan ne ta tsuguna kasa ta fashe da kukan bakin ciki
domin tunda ta fara harkokin tsafi bata taba samun bacin ranaba say yau
ba zato sai taji an dafa kafadarta ta baya
cikin razani ta waigo sukayì arba
ba wata bace tsaye akanta ba face kawarta
kuma uwargidanta aljana saubatul azwas itama hannunta na dama ya zama dungulmi
kuma hawaye na zuba a idanunta
tazubul luhucul ta fasheda kuka sannan suka rungume juna itada saubatul azwas
her tazubul luhucul ta bude baki zatace wani abu
sai saubatul azwas tayi mata nuni da tayi shiru
kawai saita dafata suka bace tare suka bar izlis atsaye awajen ba tareda sanin abinda zatayiba
saubatul azwas da tazubul luhucul suka bayyan agaban gidan sarautar sarki katimul barhul nesa kadan
kawai sai saubatul azwas taga wani katon mulmulallen dan buda ya taho daga sama ya fado kan rufin dakin dasu sarki katimul barhul ke ciki
al'amarin daya haddasa girgizar gidan kenan gaba dayansa
tareda wata irin kara mai iya kashe dodon kunne
nan take sarki katimul barhul da yan majalisarsa suka firgice kuma suka watse kowa ya cika wandonssa da iska
sai gashi suna kokawar fita daga dakin bautar
aikuwa duk wanda ya fito sai ya fadi rabin jikinsa ya shanye
dayansu bai kubuta daga masifarba
koda ganin haka sai farin ciki ya lullube tazubul luhucul da saubatul azwas suka rungume juna
suna masu kyalkyala dariyar mugunta her suka bace
agaban izlis suka sake bayyana suna kyalkyala dariyar
bayan sun nutsune tazubul luhucul ta dubi saubatul azwas tace
yake kawata yaya akayi kika rasa hannu guda daya?
koda jin wannan tambaya sai fuskar saubatul azwas ta yi bakin kirin tace
yake kawata kiyi sani cewa inbadon da sauran kwananaba aduniya
da tuni na hallaka abirnin misra, lokacinda naje garin n iske sarki usman da duk mutanensa nayin ibadarsu
awannan lokaci ko kusa da gurin ibadarsu ban isa najeba
koda naga saura dakika dari uku lokaci y kuremini sai nayi
kundun bala n fada gidan sarki usman ai kuwa ina taba kofar gidan sai hannuna ya kone kurmus
bisa dole na bace daga wajen na koma bayan gari
awannan lokaci saura dakika dari lokaci y cika
nanfa na zauna ina takaici da bakin cikin abu biyu wato rashin sa'a da kuma nakasa
kwatsam saiga wani aljani waishi kalmus
kalmus yakasance ma'abocin addinin muslunci ne
amma kuma yana muna furtar musulman duniya
ya kasance mai himma wajen bautar ubangijinsu na musulunci dayin addu'o'i ka'in da na'in dare da rana amma fa bisa samun biyan bukatun duniya
idan her kalmus yaji zai sami kyautar dukiya mai yawa babu irin aikin da bazai iyayiba
koda kalmus ya bayyna agabana saiya rissina ya kwashi gaisuwa yace
yake saubatul azwas inda zaki biyani wani abu daga gareki
dabaje na aiwatar da burinki akan sarki usman da 'yan majalisarsa
koda jin haka sai farin ciki ya kamani nace fadi abinda kakeso indai I na dashi zan baka
kalmus yace inason ki bani makullin taskar dukiyarki naje na debi iyakar iyawata
koda jin haka sai nayi shiru Ina tunani bakomai ne y sani wannan tunani ba face
sanin cewa shekarata dubu bakwai d dari bakwai ina tara wannan dukiya acikin wani kogon dutse mai tsananin tsawo da fadi
babu komai acikinsa face akwatunan lu'u lu'u,zinare, jauhar, murjani, yakutu da zubar daji
wadanda ni kaina bansan adadinsuba, kullum saina kai akwatu dubu cikin wannan kogo
banida burin tsaywa da kai akwatunan sai nan da shekaru guda dubu bakwai da dari bakwai sannan ne nake ganin babu wani mahaluki daya kaini tarin dukiya
kisani cewa na tsafance wannan taska ta dukiyata yadda babu wani mahaluki daya isa ya shiga face ya mallaki wata kuba
mai lakabi da miftahul dinar
ko yaushe wannan kuba tana makale a kuguna kuma adaure kamar guru
bayan nayi dan tunani na tuno da mahimmancin aikin dake gabana saikawai na fiddo kubar
miftahul dinar na baiwa aljani kalmus
ai kuwa yana karba saiya fizgi sihitacciyar hodar nan yaje ya watsawa su sarki usman da yan majalisarsa duk suka kamuda ciwon barin jiki.
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
Mu hadu a part G don Jin cigaban wannan KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART G ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
#LEGends.
https://www.facebook.com/groups/332169966389024/?ref=share
Marubucin littafin ya ci gaba da cewa...
Daga nan sai kalmus ya kama hanya y tafi izuwa taskar dukiya ta
wacce ke can karshen bangon duniya ta arewa
saida kalmus yaje tsakiyar teku yayi kicibus da sarkin barayin aljanu

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

1 Comments On MATSATSUBI BOOK 3
avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Good really enjoy the book waiting for Miftahul Zarbil

Please Login or Register in order to submit comment