Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

dole badon son ransu ba
dama tun akan hanyar sun tabaji igiyoyi na danyar jijiyar bishiya
nantake aka fito da ita kowa ya daura ajikinsa
tamau yadda bazai kwanceba sai da kyar
yarima sammaru ne akan gaba,
sannan ashwarya, sai yauhana da karluz, aljani guluz ne daga karshe
kuma duk suna rike da hannun juna
kai tsaye suka nufi cikin dajin halalul masur yayinda suke kara kusantar radadin zafin wuta
koda suka zo gaban gadar nan waddaa akayi da itatuwan danyen kara
sukaga yadda iska ke majaujawa da ita
saiduk suka razana har dashi kansa jarumi ssammar sai da yaki kamar ya koma da baya
amma daya tuna wahalar da suka sha abaya saiya dake cikin karfin hali
da dakakkiyar zuciya ya kama gadar da hannu guda
sannan ya dora kafarsa akai ya fara tafiya
domin basu da wani zabi face
bi takan gadar. tun da sama da kasa wutace keci ganga ganga
gadarce kadai a tsakiya kuma itama wuta na lasota daga sama da kasa
babu abinda zai baka mamaki face wutar dake ci a sama
domin da zarar mutum ya daga kansa sama
saiyaga babu gajimare ako'ina sai wannan kazababbiyar wuta
cikin sauri sammaru da abokan tafiyar sa suka haye kan gadar suka fara tafiya
ahankali cikin hikima,
don kada kafafunsu su zame
faruwar hakan keda wuya sai iskar nan mai karfi ta kada
al'amarin daya janyo hautsinewar gadar kenan
tamkar tamkar an shilla majajjawa saiga su jarumi ssammaru
asama suna katantanwa cikin tsananin juriya
sammaru ya tattare karfinsa gaba daya yaci gaba da rike gadar
yazamana gaba daya karfin abokan tafiyarsa na jikinsa
idan harya gaji ya saki igiyar gaba dayansu ne zasu subuto su fado
cikin wutar dake kasa kawai sai rigar jikin ashwarya ta kama da wuta
haka kuma kafar aljani guluz ta kama ci da wuta
cikin dimauta ashwarya ta dinga gwada sirrikan tsafinta
da kyar ta samu ta kashe wutar dake cin rigarta
sannan ta kashe wadda ta kama kafar aljani guluz
amma kafin hakan tuni kafar guluz ta kone kurmus
kamar wacce aka tsamo daga cikin tafasahshen ruwa
itakuwa rigar ashwarya ta fatattake ta kone
amma kokadan fatar jikinta bata taba ba
ana cikin wannan haline gajiya ta riski yarima sammaru
baisan sa'adda ya saki gadarba
gaba dayansu suka rikito zasu fado cikin wuta su duka
ba zato ba tsammani sai sukaji an rukosu gaba daya suna reto asaman gadar
kuma hannun sammaru aka ruke
cikin sauri sammaru ya dago kai yayi arba da wanda ya rike hannunsa
ba wani bane face gimbiya fauwaza 'yar sarki usman na birnin misra
tana zaune akan gabjejen farin aljani
mai kwarjini da haiba
cikin jarumta fauwaza ta dagasu sama su duka ta dorasu akan aljanin dake dauke da ita
fuskarta cike da murmushi kawai sai aljanin ya cilla dasu aguje
cikin 'yan dakiku kadan suka fice daga cikin dajin
cikin kankanin lokaci suka bayyana awani daji wanda babu komai acikinsa face wata bishiyar gwanda guda daya kacal
wadda tsawonta yakai zira'i dari uku
WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA SU YARIMA SAMMARU
BAYAN SUN KUSA HALLAKA ACIKIN DAJIN HALALUL MASUR
Al'amarin bokanya tazibul luhucul kuwa da kawarta aljana saubatul azuwas
lokacinda suka bace bat
tareda hadimarta izlis basu sake bayyana ako'ina ba sai
sai acikin kogon tsafin saubatul azuwas suna masu kyalkyala dariyar farinciki
bisa nasarar d suka samu ta sanyawa sarakunan duniya cutar mutuwar rabin jiki
bayyanarsu keda wuya saubatul azuwas taga wani irin jan hayaki
acikin wani kaskon tsafinta
koda ganin haka sai hankalinta ya tashi
ta dubi tazibul luhucul atsorace tace
yake kawata kiyi sani cewa lallai akwai wani mugun abu dake shirin faruwa ga shirinmu
don haka ya zama wajibi mu gaggauta bincike
kafin tazibul luhucul tace wani abu tuni saubatul azuwas tayi nuni da hannunta
izuwa jikin wani farin allon tsafi
dake jikin wani dutsen kogo
saiga hoton su yarima sammaru tareda jaruma fauwaza akan aljani
suna sauka akasa atsakiyar
tafkeken dajin nan mai bishiyar gwanda guda daya
saukarsu keda wuya sai yarima sammaru ya rude ya rikice
saboda kyawun fauwaza da kuma kwarjininta
kawai sai ya kura mata idanu ya kasa motsi
bare yayi magana tamkar gunki
itakuwa gimbiya ashwarya sai kishi ya turnuketa
ta murtuke fuska ta dubi fauwaza tace
yaake wannan 'yar sarki tayaya kikazo inda muke kika ceci rayuwarmu
kuma menene dalilin ki na ceton rayuwarmu?
kiyi sani cewa mu ma'abota tsafine, ke kuma ma'abociyar addinin musulunci ce
lallai babu alaka mai kyau atsakanin mu
sa'adda gimbiya fauwaza ta ji wannan tambaya sai tayi murmushi tace
kafin na baki amsar tambayarki inaso ki amsa min tawa tambayar tukunna
shin kin sannine da har kike kirana da matsayin 'yar sarki?
ashwarya ta bushe da dariya tace kwarai kuwa na sanki
bake bace gimbiya fauwaza 'yar sarki usman na birnin misra
ai tun kafin muzo nan boka hulumul makahur ya nuna mana acikin madubin tsafinsa
sa'adda kike yaki abirnin askandariya
kodajin wannan batu sai fauwaza tayi ajiyar zuciya tace
kwarai kinyi gaskiya kiyi sani cewa bayan naci birnin askandariya da yaki
na wuce izuwa birnin hindu wato kasarku nacisu da yaki
sannan na wuce izuwa birnin kisra, farisa, rum, da birnin sin na ci su da yaki
kuma na kafa tutar musulunci akasashen
yanzu haka duk iyayenku da danginku sun zama musulmai kamata
na iske iyayenku akwance acikin cutar mutuwar rabin jiki
kuma nayi musu alkawari da izinin ubangiji zanzo musu da maganin cutar
yanzu haka mahaifinama na can akwance cikin wannan cutar
kuma an nuna mini amafarki sewer shima bazai warkeba
harsai na shiga cikin kogon muddarul iksina na debo tsumin bokanya tazibul luhucul dake cikin taskar tsafinta
na bashi yasha,
domin makarin common da tayiwa iyayenmu na cikin wannan tsumin magani
yaku wadannan jarumai idan zakuyi imani da ubangiji na zan shiga cikin kogon muddarul iksina na debo muku wannan tsumin magani
acikin sauki ba tareda kunsha wahala ba ko kun hallaka
idan kuma ba zaku bayarda gaskiyaba zan rabu daku kowa tasa ta fishsheshi
sa'adda gimbiya fauwaza tazo nan azancenta saisu sammaru sukayi tsuru tsuru
wannan ya dubi wannan, wancan ya dubi wancan
daga can sai gimbiya ashwarya tace
muna bukatar muyi shawara
kawai saita sauko daga kan aljanin suma suka bita izuwa nasa kadan
daga inda su fauwaza suke don su tattauna,
ashwarya ta dubi sammaru, yauhana karluz da aljani guluz tace
kunji abinda fauwaza ta fada, yanzu shikenan kuna ganin ya kamata mu yarda da ita?
babu mamaki fa yaudarar mu takeson da tayi
yarima sammaru yayi ajiyar numfashi sannan yace
yake ashwarya ina son ki sani cewa su ma'abota addinin musulunci sun kasance kaifi daya
basa karya, kuma suna rike alkawari
hakika na dade inajin labarin su awajen mahaifina
kuma na tsinke da lamarinsu
ya kamata my tsaya muyi tunani fa masu iya magana sunce biri yayi kama da mutum
tabbas har azuciyata na yarda cewa fauwaza taci kasashenmu da yaki
kuma tabbas zata iya shiga cikin kogon muddarul iksina ta debo mana
wannan tsumin magani
idan baku mantaba ai boka hulumul makahur yayi mana bayani akan haka
ko a yanzuma zuwan da tayi t ceci rayuwarmu ai ya ishemu
abin ishara nikam na yarda da ita kuma ashirye nake dana mika wuya agareta
don karbar wannan addini nata mai tsarki
kafin ashwarya tace wani abu tuni sammaru yasa takobinsa ya yanke igiyar da suka daure jikinsu da ita
ya tafi izuwa ga fauwaza
koda ganin haka sai yarima yauhana yabi bayan sammaru
boka karluz kuwa saiya tsaya tareda gimbiya ashwarya
sammaru yazo gaban gimbiya fauwaza yace
yake wannan kyakkyawar 'yar sarki jarumar jarumai
kiyi sani cewa na aminta da duk kalamanki don haka na yarda na karbi
addininki
kodajin wannan batu sai farinciki ya lullube gimbiya fauwaza
alokacin ne yarima yauhana ya karaso agaresu ya dungusa kafarsa guda daya shima ya nuna amincewarsa da karbar musulunci
LEGEND IS YOURS
ALTHOUGT LIKE AND COMMENT THAT IS OURs
MU HADU A PART N DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI βœοΈπŸ™**MATSATSUBI**πŸ’₯πŸ’₯
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART N ❀️❀️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🀴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
BARKANMU DA SAFIYA ABOKAI, MUNA FATAN ALLAH YA SADAMU DA ALKHAIRAN WANNAN RANA YA KUMA KARE MU DAGA DUKKAN SHARRI πŸ™πŸ™πŸ™
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA.....
Gimbiya fauwaza ta biya musu kalmar shahada
suka maimaita
gamayin hakan keda wuya ashwarya da boka
karluz sukazo garesu
da zuwa sai ashwarya ta dubi sammaru
idanunta na zubda hawaye tace
yakai masoyina kayi sani cewa her abada bazan
taba karbar addinin musulunci ba
domin ma'abotansane sanadiyar mutuwar
kakannina
tuni nayi alkawari da zuciyata cewa bani basu
har abada, hakika yau ne ranar rabuwata dakai
amma ka sani cewa har na mutu bazan daina
begenkaba
acikin zuciyata, yanzu zamu shiga cikin kogon
muddarul iksina
nida boka karluz inaso ku saurari fitowarmy da
sa'a bakwai
idan lokacin ya cika kukaga bamu fitoba to
tabbas mun hallaka
sai ku kuma ku shiga, da wannan kalami
nake maka bankwana idan da rabon mu sake
saduwa zamu sadu nan gaba
koda ashwarya ta zo nan a zancenta sai idanun
yarima sammaru suka ciko da kwalla yaji sonta
ya dada mamaye zuciyarsa fiye da koyaushe
harya miko hannu zai riketa saita goce ta finciko
boka karluz
cikin sauri ta fizge icen nan daga jikin sammaru
tayi nuni dashi
izuwa karkashin bishiyar nan ta gwanda
take wani wawakeken rami mai tsananin zurfin
da babu karshe ya bayyana
wata irin iska mai karfi ta fito daga cikinsa
ta zuke ashwarya da boka karluz suka fada ciki
suka bace bat, sannan ramin ya bace bat
tamkar bai taba wanzuwaba
adaidai nan ne aljana saubatul azuwas ta shafi
allon tsafinta hoton ya bace
cikin tsananin bakin ciki ta kurma ihu
sannan ta kama kafadun tazibul luhucul ta
girgiza tana mai rusa kuka
sannan tace
yake kawata tabbas shirinmu yana daf da
wargajewa gaba daya
idan har bamu dauki matakin gaggawaba........
cikin razani tazibul luhucul tace
yanzu wane mataki zamu dauka?
babu abinda zamu iyayi face gagarumin sihiri
mu tafi izuwa kogon muddarul iksina tareda
dukkanin dakarun mu na yaki
mu yaki wadannan makiya namu mu kawar
dasu daga doron kasa
kiyi sani cewa idan aka debo tsumin maganin
nan daga cikin taskar ki
take jikina da naki zai tsatstsage ya ruguje
tamkar rushewar sabon gini karshen mu kenan
kodajin wwanna batu sai hankalin tazibul
luhucul ya dugunzuma ta rude ta kidime
nantake ta kira dukkanin hadimanta wadanda
sukayi saura
ta umarcesu dasuyi shirin yaki
itama saubatul azuwas ta kirawo nata dakarun
cikin kankanin lokaci suka hado muggan
makaman yaki
marasa adadi kala kala harda irin wanda ido bai
taba ganin irinsaba
sukuwa dakarun yakin saida adadinau yakai
dukkaninsu aljanu ne zakwakurai masu
dakakkiyar zuciya
koda tazibul luhucul da saubatul azwas suka
dubi dunbun dakarunsu
sai sukaji zuciyarsu ta karfafa duk shakkar da
sukeyi ta gushe
harma sukeji cewa suna da tabbacin samun
nasara akan makiyansu
domin suna ganin cewa karfin wannan rundunar
tasu
yakai su yaki dubiyar ma gaba dayanta
ba tareda. bata wani lokaciba tazibul luhucul da
saubatul azuwas aukayi wadannan dakarun
yakin guda miliyan daya jagora izuwa tsuburin
muddarul iksina
idan mutum yaga wannan tawaga sa'adda suke
tafiya
saiyayi zaton gaba daya tsuntsayen duniyane
suna gasar tseren gudu
acan makeken dajin nan kuwa mai bishiyar
gwanda guda daya kacal
har yanzu gimbiya fauwaza na tareda yarima
sammaru da yarima yauhana
da kuma farin aljanin nan suna jiran fitowa
ashwarya da boka karluz
daga cikin kogon muddarul iksina
ahalin yanzu sa'a hudu sun shude saura sa'a
uku kacal lokacinda suka debarwa kansu ya
cika
tsawon wannan lokaci hirace ta barke tsakanin
gimbiya fauwaza dasu yarima sammaru
inda ta basu labarin irin gwagwarmayar datasha
afilin daga yayinda ta yaki manyan kasashen
duniya guda biyar
da kuma yarda ta rinka samun taimakon allah
alokacin ne ta basu labarin wannan aljani wanda
ke tareda ita
wanda ake kiransa da suna hadimul addin
wato fassara sunan nasa na nufin
mai yiwa addini hidima
hadimul addin ya kasance matashin aljani dan
kimanin shekara
dari shida da arba'in, tun yana yaro ya taso
acikin addinin musulunci
sa'adda baifi shekara bakwaiba awata kasa ta
aljanu
da ake kira madinatul azwab
kaf acikin wannan gari babu musulmi guda daya
sai hadimul addin
shikansa ya karfi addinin ne a wajen wani
bafatake
da yazo zai ratsa ta cikin garin don cin kasuwa
a sirrance wannan bafatake ya sanar da hadimul
addin musulunci
kuma ya koyar dashi yadda ake bautar allah
yayinda hasken musulunci ya ratsa zuciyar
hadimul addin
ya zamana tsoro da kaunar allah sunyi katutu
aransa
saiya kebe daga cikin aljanu ya shiga cikin wani
kogon dutse
mai zurfin zira'i dubu ya zauna aciki yana bautar
allah
kullum dare da rana bashida wata addu'a face
allah ya
ba bashi karfin dazai iya yakar aljanun kasarsa
shi kadai
domin ya kafa daular musulunci
lokacinda hadimul addin ya shiga wannan kogo
ya zauna yana da shekara bakwai ne kacal
aduniya
bai gusheba yana bautar allah da yin wannan
addu'a harsai daya kai shekara dari shida da
talatin da uku suka cika
awannan rana yaji wani irin karfi mara misali ya
shigeshi
cikin kankanin lokaci
nantake ya fito daga cikin kogon ya wuce kai
tsaye izuwa gidan sarki
koda shigarsa cikin fada aka ganshi buzu buzu
cikin ga shi
babu aski sai aka bushe da dariya ana
tsammanin mahaukacine
hadimul addin yayi tsaye agaban sarki yana kai
kallonsa ido da ido yace
yakai wannan sarki kayi sani cewa nine wane
dan wane
yau shekara ta dari shida da talatin acikin dutse
ina bautar ubangijin musulunci wanda bai
haifaba
ba'a haifeshiba, shine wnda bashi da farko
bashi da karshe
shine sarkin da ba shida kishiya
kuma shine ya halicci sammai da kassai da duk
abinda ke cikisu
yakai wannan sarki ina mai kira agareka daka
daina bautar wanin ubangijin musulunci
ka dawo izuwa tafarkin gaskiya idan kuma kaki
zan yakeka
na kafa tutar musulunci awannan kasar
tun sa'adda hadimul addin ya fara wannan
jawabi nasa fadar gaba daya tayi tsit
ana sauraro da mamaki koda ya gama jawabin
sai zuciyarsa ta kama tafarfasa ya dubi hadimul
addin ya daka masa tsawa
yace
kai yaro karyarka tasha karya ire irenka sunzo
nan da irin wannan furuci kafin kai duk baga
bayansu
barekai daka zamo dan mu lallai yau zan bar
abin misali akanka
na rantse da darajar tsafi waninka bazai. sake
sha'awar kawo wargiba
kamar yadda kayi
nan take sarki ya dubi wasu dakarunsa yace
ku kama wannan yaron ku daureshi tamau
hannu da kafa
sannan ku dinga yankar naman jikinsa sala sala
harsai kunyi gutsun gutsun dashi
kafin sarki ya gama rufe bakinsa tuni dakarun
nan sun afkawa
hadimul addin nanfa wuri ya yamutse
cikin dakika biyar ya karkashesu
dukda cewa adadinsu yakai dubu goma
kuma baiyi amfani da makamiba ko guda daya
da karfin damtse kawai ya rinkayi musu dundu
da barin makauniya
duk makaminda suka buga ajikinsa baya tasiri
tamkar sun sari dutsene,
koda ganin haka sai sarki ya ruga cikin gida
ya sami guri ya labe, nanfa dakarun garin gaba
daya sukayi ta shigowa
cikin fadar sukayiwa hadimul addin kawanya
sama dasu dubu dari tara da casa'in da bakwai
sai da aka kwana dari ba daya ana yaki
tsakanin aljani hadimul addin da wadannan
dakarun
amma shi kadai ya kashesu gaba daya
sannan ya shiga gidan sarautar ya kamo
sarkinsu ya murde masa wuya
daga nan ya tara al'ummar garin gaba daya
ya musuluntar dasu koda suka nemi ya zama
sarkinsu
sai yace bashida bukata, daga wannan rana
hadimul addin yaci gaba da yakar kasashen
kafiran aljanu
kawo iyanzu ya yaki kasashe dubu bakwai da
saba'in da bakwai
yana kan wannan aikine allah ya sadani dashi
na nemi taimakon sa akan ya kawo ni nan don
na taimake ku
kuma na sami damar shiga kogon muddarul
iksina
koda gimbiya fauwaza tazo nan a zancenta sai
mamaki ya kama yarima sammaru
da yarima yauhana suka kara imani da allah
suka tabbatar da cewa babu wani abu dazai
gagari allah
hakadai hira taci gaba da gudana har sa'a
bakwai ta cika su gimbiya ashwarya basu fito ba
daga karkashin bishiyar
yayinda yarima sammaru yaga basu fitoba saiya
kaddara aransa cewa tuni ashwarya sun mutu
don haka sai idanunsa suka ciko da kwalla ya
fara zubar da hawaye
koda gimbiya fauwaza taga halin daya shiga
saita cire farin kyallen data rufe fuskarta dashi
suka dubi juna Ita da sammaru tace
yakai sammaru shin idan ka aureni bazan debe
maka kewar ashwarya ba?
tabbas wannan hawayen dake zuba daga
idanunka domintane.
MU HADU A PART O DON JIN
**MATSATSUBI**πŸ’₯πŸ’₯
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART O ❀️❀️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🀴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
CIGABAN LITTAFIN ✍️✍️✍️
Koda jin wannan batu sai yarima sammaru ya ji
gaba daya bakin cikinsa ya yaye
tunanin ashwarya ya gushe daga zuciyarsa
baisan sa'adda yayi murmushi ba
yana mai cewa
yake sarauniyar kyawawan duniya hakika duk
wanda ya mallakeki
tamkar ya sami maganin takaici da bakin ciki n
zan kasance mai matukar farinciki idan kika
zamo matata
fauwaza tayi murmushi tace idan har muka fito
daga cikin kogon muddarul iksina araye nayi
maka alkawarin kaina
tana gama fadin hakan ne ta umarceshi
da hawowa kan aljani hadimul addin
ba tareda bata lokaciba ta umarci shima
yauhana da ya hawo kan aljanin
fauwaza ta daga hannayenta biyu sama
tana mai rokon allah da sunayensa kywawa
guda dari b daya
ya ubangijin komai da kowa na rokeka dan
isarka da isar mulkinka
ka shigar damu wannan kogon na muddarul
iksina
inda wadannan makiya namu suka boye tsumin
maganin da muke nema
ka bamu nasara akansu har mu fito lafiya
gama rufe bakinta keda wuya
sai kasa ta tsage hanya ta samu
take aljani hadimul addin ya shige dasu ciki
sukayita tafiya akarkashin kasa
kamar na zasu tsaya ba
bisa taimakon allah suka iso tsubirin muddarul
iksina
acikin rabin sa'a alhalin kuwa tafiyar shekara
goma sha biyu ce
ga sadaukin aljani mai matukar jarumta da karfin
gudu
koda isowarsu bakin kogon sai suka ga gawar
gimbiya ashwarya data boka guluz
GASKIYA NI AKAN RA'AYINA BANJI DADIN
MUTUWAR GIMBIYA ASHWARYA BA AMMA
BANSAN NAKA RA'AYIN BA MAI KARATU
Akwance kirajensu afafe alamar aljanu ne suka
kwakule cikinsu
cikin hanzari su sammaru suka kautarda kansu
ga barin kallon gawarwakin
cikin yanayin tausayi d tashin zuciya
nan dai fauwaza da hadimul addin suka cigaba
da karanta addu'o'i
take kofar kogon ta bude da kanta
suka shiga ciki
da shigarsu suka tsinci kansu acikin wata irin
tangamemiyar fada
mai girma da fadi babu komai acikinta face
tarkacen tsafi iri iri fiye sa kala miliyan dubu
a tsakiyar fadar kuwa wata irin katuwar tukunya
ce atsaye cikin iska
itadai wannan tukunya an cikatanr da saiwoyin
itatuwa
guda miliyan dubu daya
kowacce saiwa tana maganin cuta kala daban
tukunyar ta cika fam da saiwoyin
sai fitar da wani irin tururi takeyi
fauwaza taci gaba da karanta addu'o'i har tazo
gaban wannan tukunyar
da zuwa saita fiddo watta babbar battar fata
ta tsoma acikin tukunyar
saida battar ta cika fam da ruwan maganin
sannan ta tsamota ta kulle bakinta ta ratayata
aka fadarta
faruwar hakan keda wuya sai
su bokanya tazibul luhucul suka bayyana acikin
kogon tareda
dakarun yakin su guda miliyan dubu daya
kafinsu fauwaza suyi wani yunkuri anui musu
kawanya babu ta inda zasu ratsa su fita daga
cikin kogon
tazibul luhucul da saubatul azuwas suka karewa
su fauwaza kallo
sannan suka bushe da dariya alokaci guda
kuma suka murtuke fuska
saubatul azwas tayi nuni da dan yatsanta izuwa
ga aljani hadimul addin
tace
kai karamin kwaro maci amanar aljnu kayi sani
cewa
na dade ina shiri akanka inda shirina ya
kammala
kafin kazo nan da tuni ka zama mushe amma
dukda haka rana bata baci ba
yau zan gama dakai domin nasara na garemu
ma'abota tsafi
cikin fushi hadimul addin ya dakawa saubatul
azwas tsawa yace
ke tsohuwar munafukar allah, ba tacciyar wadda
ta dade tana sabo adoron kasa
kiyi sani cewa yaune ranar da dubunki zata cika
dake da wannan
munafukar ta kusa dake da izinin ubangijin
gaskiya sai mun ragargaza ku mun kawar daku
daga doron kasa
saubatul azwas ta sake bushewa da dariya
sannan tace
ai sai angwada akan san na kwarai kuma sai
miya ta kare ake sanin maci tuwo
cikin tsawa saubatul azwas ta dakawa
dakarunta tsawa tana mai basu umarnin su afka
musu
nan take wuri ya hargitse da masifaffen yaki
aljani hadimul addin ya tari dakarun aljanun
gaba daya
shikadai ya zame musu annoba, fauwaza ta tari
saubatul azwas
suka fara karawa, shikuwa yarima sammaru ya
tari tazibul luhucul suka ware gefe daya
inda ta fara kyalkyala dariyar mugunta tace
kai karamin alhaki yaune ranar da zan nuna
maka cewa
ba sani ba sabo, kuma alkawarin dana dauka
abaya
na cewar bazan taba kaba ya kau
tabbas sai na yanke kanka na tafi dashi har
gaban mahaifinka
nanuna masa dan bakin ciki ya kasheshi ya
mutu
tun kafin lokacinsa ya cika
kodajin haka sai shima sammaru ya daka mata
tsawa yace
ke bakar annamimiya munafukar allah kiyi sani
cewa
yanzu da da ba daya bace
ada ina cciki jahilci amma yanzu hasken ilimi n
gaskiya sun baibayeni
baki isa ki sami nasara akainaba
da izinin ubangijin musulunci saina yi miki kisan
gilla domin na huce takaicin wahalar da kika
jefamu aciki nida abokan tafiyata da kuma
iyayenmu
domin jininki ya zama ga rayukan da akayi asara
ki sani cewa saduwarmu da gimbiya fauwaza ba
karamin rahama bace agaremu
domin itace ta cece mu daga hallaka a dajin
halalul masur har muka kawo iyanzu. kafin
sammaru ya gama ruglfe bakinsa tazibul luhucul
ta nuna shi da sandar tsafinta
wani irin haske ya bugeshi yayi sama y bugu da
ginin dutse
ya fado kasa a sume, nanfa tazibul luhucul taci
gaba da dariyar mugunta
awannan lokaci ne yauhana ya lura da abindake
faruwa g sammaru
cikin karaji ya daga takobinsa sama yana mai
kabbara
ya durfafi tazibul luhucul aguje da nufin ya
sareta
koda taga ya taho gareta gadan gadan saita
fara nunashi
da sandar ta ta tsafi bisa mamaki saitaga tsafin
nata yaki yayi tasiri
sakamakon kabbarar da yakeyi,
al'amarin daya firgitata kenan tayi sauri ta bace
acan bangaren fauwaza da saubatul azwas
kuwa addu'a da tsafine suka hadu
da zarar saubatul azwas taga fauwaza zatayi
mata lahani saita bace bat
shikuwa aljani hadimul addin tuni yayi fata fata
da dakarun nan guda miliyan dubu daya ya
kashe kusan rabinsu
duk inda ya kutsa kansa saidai kaga suna yanke
jiki suna faduwa kasa matattu
yana cikin wannan haline ya waigo yaga halinda
gimbiya fauwaza take ciki
kawai saiya kwalawa fauwaza kira yana mai yi
mata tuni data karanta wata addu'a nanda nan
kuwa fauwaza ta fara addu'a afili al'amarin daya
janyo karyewar alkadarin saubatul azuwas da
tazibul luhucul suka kasa bacewa kenan
nanfa fauwaza da yarima yauhana suka kuntata
su da sara da suka ya zamana cewa
babu abinda yake tasiri face tsagwaron karfin
damtse da jarumtaka
dukda cewa tazibul luhucul ta tsufa saidata
nunawa yauhana tsohon kashi
ashe wannan sandar tata ta tsafi takobice
take ta zare ta
ta dagata ta shiga kai masa sara da suka harta
sami nasarar yi masa yanka guda uku
daya aka daya akafarsa daya kuma adamtsen
hannunsa na dama
bashiri ya saki takobinsa ta fadi kasa
adaidai wannan lokacinne yarima sammaru ya
farfado
cikin zafin nama ya mike tsaye yana mai kwalla
kabbara
kawai sai ya suri takobinsa yayi kan tazibul
luhucul
ta hauta da sara da sara da suka cikin sauri da
bajinta
tun tana iya maida martani har ta kasa
ya zamana tana kokarin kare kanta
kawai take
suna cikin hakane sammaru ya shammaceta ya
daka tsalle asama ya fille mata kai
take kan yayi sama jini yayi tsartuwa ginger
jikinta ta fadi kasa riki ca
koda ganin abindaya faru sai saubatul azwas ta
kwarara uban ihu
ta bude fuka fukanta ta nufi kofar fita daga cikin
kogon
cikin sauri gimbiya fauwaza ta karanta wata
addu'a ta tofa mata
koda yawun bakin fauwaza ya dira ajikin
saubatul azwas sai gaba daya jikin nata
ya kama da wuta
nanfa ta dinga kurma ihu mai ban tsoro wanda
ka iya kashe dodon kunne
cikin dakika uku tayi bindiga ta tarwatse
ya zamana sassan jikinta yayi gutsun gutsun
adaidai wannan lokacinne aljani hadimul addin
ya gama da ragowar dakarun
dayansu bai tsira da rayuwarsa ba
koda su sammaru sukaga sun sami nasara sai
farinciki ya lullube su
take sukayi wa allah godiya
sannan aljani hadimul addin ya debesu ya fitar
dasu daga cikin muddarul iksina
dama battar maganin nan tana rataye bisa
kafadar
bisa kafadar gimbiya fauwaza
aikuwa suna fitowa daga cikin kogon sai taskar
ta kama da wuta
gaba daya ta kone kurmus duk abubuwan dake
ciki suka kone kurmus suka zama toka
aljani hadimul addin bai hutaba saidata kai su
sammaru
gidajensu kowa ya baiwa mahaifinsa tsumin
maganin nan
yasha ya warke daga cutar mutuwar rabin jiki
hakama sauran sarakunan guda hudu wato
mahaifin gimbiya ashwarya
da duk 'yan majalisarsu
saida suka sha wannan tsumin suka warke
lokacinda iyayen ashwarya, lubaika, sukaji cewa
'ya'yayensu
sun mutu akokarin nemo wannan mahagani sai
suka fashe da kuka
sukayi ta bakin ciki mara misaltuwa
ita kuwa gimbiya fauwaza saita sake komawa
birnin misra
tareda yarima sammaru ta gabatar dashi awajen
mahaifinta
amatsayin wanda zata aura, ba tareda
gardaamar komaiba sarki usman ya amince
aka daura aurensu, bayan nan ne yarima
sammaru ya dauki matarsa gimbiya fauwaza
ya koma kasarsu inda ta karbi mulki daga
hannun mahaifinsa suka ci gaba
da rayuwar ango da amarya cikin jin dadi da
kwanciyar hankali.
MU HADU A PART P DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI βœοΈπŸ™

**MATSATSUBI**πŸ’₯πŸ’₯
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART Q ❀️❀️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🀴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️ KT
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
TAKUN KARSHE ✍️✍️✍️✍️✍️🀸🀸🀸
Yaku 'yan uwa da Abokai na wannan gida Mai Albarka, masu bibiyar littafin mu na MATSATSUBI. kuyi sani cewa a yau Allah yasa muka kawo karshen wannan littafi na uku, sannan Kuma zamuci gaba da na gabanshi wato MIFTAHUZZARBIL insha Allah a ranar LARABA✍️✍️☝️ muna fatan Kuna nishadantuwa da irin Labaran da muke Dora maku..
Fatan Alheri a gareku ✍️✍️☝️
Najibullahi Muhammad
#LEGENDs of KATSINAπŸ’ͺ
βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“βœ“
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA...
Koda sarki dujalu yazo nan alabarinsa sai boka
hajarul makarus
yayi ajiyar zuciya yace
yakai wannan sarki shin yanzu kayi imani da
addinin musulunci?
hakika wannan labari gaba dayansa yana nuni
ne da nasarar mabiya addinin musulunci
koda jin wannan tambaya sai sarki dujalu ya
bushe
da dariya sannan yace
yakai wannan boka kayi sani cewa abinda ya
hanaka karbar addinin musulunci shine ya
hanani karba
amma ka sani cewa idan akazo da labari ana
fadin hakikanin gaskiyar labari
domin idan na boye gaskiyar wata kila nan gaba
xata fito da kanta
da wannan kalami nake muku bankwana saiku
tafi
domin na sallameku dama iyakar hikayoyin
danayi muku alkawari kenan
cikin murna da godiya tsoho rafkanagu, ruziyal
da hajarul makarus
suka tattara inasu inasu suka fice daga cikin
fadar
daga nan suka cigaba da tafiya da kafafunsu
saida suka isa bayan gari sannan rafkanagu yayi
girgiza yace
yanzu kuma ina muka dosa?
ruziyal yace ai yanzu kuma birnin sin zamuje
don mu samo wadansu muhimman labarai
awajen sarki mazluch
kodajin haka sai boka hajarul makarus yayi tsaki
yace
kawai kace baya zamu koma
ruziyal yace kaga aiba laifina bane abune akan
tsari
kamar yadda na ziyarci kasashe bi da bi
harsaida n rubuta kundub tsatsuba
na farko haka ma yanzu zamubi wannn tsari
kafin wani dga cikinsu ya kara cewa wani abu
tuni
aljani.rafkanagu ya suresu su biyun agadon
bayansa
yayi sama ya nufi birnin sin
WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GA TSOHO
RAFKANAGU BAYAN SUN GAMA JIN HIKAYAR
BOKANYA TAZIBUL LUHUCUL AFADAR SARKI
DUJALU MAI SIHIRTACCEN SHAYI
SHAYINDA IDAN AKASHA SHI BA'AJIN YUNWA
DA KISHIRWA
KUMA BA'AJIN BARCI DA KASALA
Al'amarin boka shamharu kuwa da sarki
lu'umanu kuwa
lokacinda suka shiga cikin dakin halwar tsafi
acan birnin baharzus
sai shamharu ya zauna agaban wadansu
tarkacen tsafi ya zura musu idanu
yana mai nazari da bincike.shikuwa lu'umanu
saiya tsaya abayansa ya kame
kamar

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

1 Comments On MATSATSUBI BOOK 3
avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Good really enjoy the book waiting for Miftahul Zarbil

Please Login or Register in order to submit comment