Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gyara damara
don zamushiga inda kabilar dodanni ta hudu take
babu mamaki gaba dayanmu mukai labari
amma dai jajircewar itace
nasarar mu
ina maiyi mana fatan nasara
da wannan jawabine sammaru ya rufe jawabinsa
nan take ya zare takobinsa ya dagata sama yayi ruri
suma abokan tafiyar tasa sukayi yadda yayi
nan danan ihun nasu ya cika dajin gaba daya
al'amarin daya fargar da ragowar dodannin kenan
suka fara tsallen murna don sun cewa yau ga abincinsu
nan tafe, cikin hanzari jjaruma biyar suka dane
bayan aljanun hudu
da yake aljani amzil da hurus sun mutu
sai yarima sammaru da gimbiya ashwarya
sukahau kan aljani guluz tare
yarima yauhana, larbuz suka hau kan asgar
shikuwa boka karfil shikadai ya haye kan
karmash
akabar aljani karfil shikadai ba kowa akansa
kamar an cilla kibiyoyi haka aljanun suka luluka cikin gajimare
suka nausa cikin daji
tafiyar da sukayì kadance suka riski kabilar dodanni ta hudu
nantake aka garkame da matsiyacin yaki
saida aka shafe kwana guda cur ana
wannan yakin
daya ninka na baya bala'i da tashin hankali
a wannan lokacine aljani karfil da yarima larbuz suka mutu
yarima sammaru ,gimbiya ashwarya, yauhana da boka karluz kuwa saida suka sume
dukda cewa sun gama kashe dodannin gaba daya
sai bayan sa'a daya suka farfado, saboda tsananin jigatar da sukayi
hakama su aljani guluz bayan hankalinsu ya dawo cikin jikinsu sai bayan sa'a hudu
da yake a inda akayi wannan yaki akwai wani kogi
sai dukkanninsu suka shiga cikin
kogin suka sha ruwa kuma sukayi wanka
bayan sun fitone suka zauna suna hutawa
tsawon dan lokaci babu wanda yace kala
,
daga can sai gimbiya ashwarya ta dubi sammaru tace
yakai jagoran tafiya kayi sani cewa
inada wata shawara agaremu wacce nake ganin zata fisshemu
koda jin haka sai sammaru yace
fadi shawarar ki muji, yake jaruma mai kaifin basira
ashwarya tayi murnushi sannan tace
inaganin yana da kyau mu karawa kanmu horon yaki
anan wurin domin na fuskanci kowannenmu nada tasa baiwar daban
kuma inaganin yakamata mu kirkiri wasu
makaman fadan daban
wato ina nufin makamai wadanda zasu taimaka mana
wajen saurin kashe dodannin nan tunda sun kasance masu yawan gaske
koda jin wannan batu sai kowa yayi na'am da shawarar
nanfa aka fara tunanin yadda za'a kirkiri sababbin makaman fada
sai da aka shafe kusan rabin sa'a ana tunani
kowa yayi shiru yana wasa kwakwalwarsa
yarima yauhana ne ya fara magana da cewa
ni ina ganin mu samo dogayen itatuwa mu ferayesu
suyi tsini sannan mu kera manyan baka wadanda za'a dunga harbawa itatuwan ga dodannin suna tsiresu
nasan dai mu bazamu iya tabe bakarba,
ammasu aljani guluz zasu iyayi
koda jin wannan batu sai kowa ya kama tafi
nantake akaje aka samo itatuwa masu yawa aka fiffikesu
kowanne ice guda bazai daukuba awajen
mutum arba'in
saboda tsawonsu da nauyinsu
amma su aljani guluz da dan yatsa daya suke daukar guda goma
bayan an fiffike wadannan itatuwa sai kuma akazo aka kera baka guda uku manya
kowacce guda daya tafi yarima sammaru tsawo da nauyi
sauran biyun kuwa aka baiwa aljani karmash da asgar
nanfa sammaru yayita koya musu yadda ake harba kibiya
har suka kware daga nan kuma saisu sammaru
suka fara jarraba jarumtaka atsakaninsu
ma'ana shida ashwarya
suka yaki juna, kowa na nuna tsagwaron karfi, juriya, dabara da jarumtaka
haka ma yarima yauhana da boka karluz
suma suka ware suka rinka gumurzu
awannan karon dai su aljani guluz 'yan kallo suka zama,
saida suka cika da tsananin mamakin jarumtaka
irin ta gimbiya ashwarya da jarumi sammaru
domin kowannensu yayi abubuwan al'ajabi da za'a jinjina masa
domin kare jini biri jini
sukayi
amma abangaren yauhana kafa daya gareshi saida ya wahalar da boka karluz matuka
shida kansa ya san cewa ruwa ba sa'an kwando bane
domin anfishi karfi, kuruciya da dabarun fada
bayan angama baiwa juna horon fada
sai kuma
aka shirya aka shiga daji na. biyar
don asamu nasara akansu
cikin kankanin lokaci .kowa yagamsu da shirin,
sannan aka zauna aka huta tsawon sa'a hudu
wannan karon yarima sammaru baiyi ruriba
wato shigar sumame sukayi wa dodannin
lokaci guda sukaji ana sakar musu kibiyoyi suna tsiresu
kafin dodannin su ankara fiye da rabin su,
duk wannan aikine na guluz da aljani karmash da azgar
suna cikin wannan barnane kibiyoyin nasu suka kare
nanfa ido ya raina fata suka koma bayansu ssammar
koda ganin haka sai sammaru, ashwarya, yauhana da boka karluz suka zare takubbansu
suka ruga ga dodannin alokaci guda
suna ruri suka hausu da sara da suka
duk inda suka ratsa sai dai kaga dodannin suna zubewa kasa matattu
da yake tun farko an karya lagon wadannan dodannin bisa ganin an kashe fiye da rabinsu
basu sami wani karfin gwiwa ba bare su iya karya
alkadarin jaruman, nanfa su sammaru suka yita ragargazarsu
baji ba gani dukda cewa dodannin sun karaya saida suka kusa hallaka jaruman
domin babu wanda bai samu mugun rauni ba ajikinsa
akwai wani lokaci da wani dodo ya lumawa sammaru farce agefen cikinsa
sammaru yayi ihu ya fadi kasa
dodon ya kaiwa sammaru hari da nnufi ya talitseshi
cikin zafin nama ashwarya ta janye sammaru daga wajen
kafar ta nutse acikin karkashin kasa inda sammaru ya fadi
kafin dodon ya cire kafarsa tuni ashwarya tayi alkafira
asama ta luma masa takobi a tsakiyar kan dodon
dodon ya fadi kasa rikica kamar faduwar giwa
haka aka gama wwanna yaki sammaru baya cikin hayyacinsa bisa wannan suka da dodon yayi masa
wannan karon kuma babu ruwan maganin da boka hulumul bakahur ya basu
tun awancan yakin maganin ya kare
dukkanninsu jaruman haka suka kwanta agalabaice
babu mai iya tabuka komai
gimbiya ashwarya ce kadai mai koshin lafiya
shikuwa sammaru yafi kowa galabaita
don har wani irin aman jini da kakari yake kamar zai mutu
al'amarin daya firgita gimbiya ashwarya kenan
bata san sa'adda ta kama kuka ba dakyar boka karluz
ya bude baki yace da ita ta bude jakarsa ta dauko
wani garin magani ta shashshafA musu
aikuwa hannunta na karkarwa ta bude jakarsa da sauri ta dauko magananin
saida ta fara shafawa sammaru maganin sannan ta shafawa kowa
bayan nan saita koma kusa da sammaru ta zauna
ta dora kansa akan cinyarta tana kallon fuskarsa hawaye na diga akansa
bazato ba tsammani sai taji sammaru ya kawo gwauron numfashi
gami da bude idanunsa
nantake farinciki ya lullubeta bata san sa'adda ta rungumeshi ba
tana kukan murna
sammaru ya mike zaune yana mai kallon fuskarta cikin farinciki
yace ''godiya agareki yake ma'abociyar kyawu da
kwarjini ina fatan nima nayi miki sakayya irin wacce kika yi min ta ceton raina
koda jin wannan batu saì ashwarya tayi murnushi tace
sakayya daya nake bukata daga gareka
kawai ka bani matsuguni acikin gurbin zuciyar ka
ya zamana cewa ni kadaice mai shige da fice da acikinta
kodajin haka sai sammaru yaji wani farinciki ya lullube shi
harma ya kasa motsi da bude baki
dagacan kuma sai yace
yake ma'abociyar kyawu da kwarjini kiyi sani cewa
tun ranar da idanuna suka fara arba dake naji na kamu da tsananin kaunarki
zuciyata da ruhi suka suka aminta dake har ya zamana basa son jin komai akusa dasu face ke
tabbas ina matukar begenki da kaunarki
kamar yadda da keson iyayensa
haarya iya salwantar da rayuwarsa saboda su
koda sammaru yazo nan azancensa
sai gimbiya ashwarya ta sake rungumeshi suka rukunkume juna
kamar ba zasu taba rabuwaba
adaidai wannan llokaci su yarima yauhana da boka karluz suka farfado sosai suka mike zaune
koda sukaga abinda ke faruwa tsananin gimbiya ashwarya da yarima sammaru sai suka cika da murna
aljani guluz da karmash da asgar suka katse shirun dake wajen
ta hanyar yin tafi da shewa bisa murnar samun nasarar wannan yaki.
MU HADU A PART K DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU ✍️✍️
PART K ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
CIGABAN LITTAFIN....
Cikin hanzari sammaru da ashwarya suka saki
juna suna masu jinn kunya.
nanfa suka ruga wajen su yauhana da karluz
suka rungume su
akaci gaba da farin ciki
bayan an nutsune sai yarima sammaru yayi
gyaran murya
ya dubi kowa yace
yace yaku yan uwana ku sani cewa yanzu ne fa
zamu tunkari kabilar dodanni t karshe
wannan kabila tafita sauran bala'i,yawa da karfi
don haka ya zama wajibi agaremu muyi shiri
irin wanda bamuyi kamarsaba abaya
inba hakaba kuma gaba dayan mu babu wanda
zaiyi rai
kodajin wannan batu sai dukkaninsu hankalinsu
ya tashi
aka manta da wahalar da aka sha abaya
aka shiga fargabar abinda za'a dosa agaba
yayinda yarima sammaru ya fuskanci cewa
zuciyar kowa ta karaya
saiya shiga karfafa musu gwiwa da jinjinawa
kowa bisa irin jarumtakar daya nuna abaya
lokacin da yaga sun sami kwarin gwiwa sai ya
kawo shawarar cewa su sake kera sababbin
kwari da baka guda hudu
wato shi ya dauki daya ya rabawa su
ashwarya,yauhanad ,karluz sauran
bayan ya basu yace dasu kada ku harbi ko'ina
ajikin dodannin face kansu
domin anan ne kawai kibiyar mu zata yi tasiri
ajinkinsu
amma kibiyar su aljani guluz zatayi tasiri ako'ina
ajikin dodannin
bayan su sammaru sun tanadi kibiyoyi masu
yawan gaske
sai kuma suka samo jijiyoyin bishiyoyi danyu
murtuka murtuka irin wanda ko mutum yasa
kaifin takobi basa yankuwa
nan take suka yita saka raga dasu
saida suka saka raga mai yawan gaske sannan
sammaru ya rabawa kowa aikinsa
yayinda aka shiga dajin kabilar dodanni ta
karshe
yadda ya tsara aikin kowa shine
aljani karlaz zai tashi sama ya dinga jeho raga
kan dodaninn
aljani guluz da asgar zasu tsaya asama ne suna
harbo kibiya kan dodannin
su kuma su sammaru ta sama zasu ding harbin
dodannin da nasu kibiyoyin
sai an tabbatar cewa kibiyoyin sun kare sannan
za'a far musu da sara
aikuwa kamar yadda aka tsara haka al'amari y
kasance
cikin shammace dodannin nan sukaji an
lullubesu
kuma ana harbinsu da manyan kibiyoyi da
kanana
nanfa suka dinga mutuwa kamar annoba
kiri kiri dodannin nan suka kasa komai
akayita ragargazar su
amma da yake yawansu ya wuce kima sai akaga
kamar karuwa suke
hankalinsu sammaru bai tashiba
saida sukaga saura kadan kibiyoyin nasu su
kare
amma har yanzu basu kashe dodannin ba
lokacinda kibiyoyin suka kare say fada ya sauya
launi
domin ragama ta kare kuma dodannin da raga
ta lullube
basu mutuba suma suka fire karkatse ragar da
kaifin hakoransu
suna fita daga ciki,, al'amarin daya firgita yarima
yauhana da boka karluz kenan
suka juya da baya da nufin guduwa
cikin sauri sammaru ya ruko hannunsu
yace
haba zaratan jarumai ashe kun manta da
tsananin wahalar da kuka sha abaya
shin mutuwa ce bakuwarku?
kokuwa kogin jini ne bakonku? ku tunafa cewa
kunga bala'i
kunga masifa babu tashin hankalin da baku
ganiba
karku bani kunya domin maza basa gudu
don wuya ko halaka
daku mutu ragwaye gwara ku mutu mazaje afilin
daga
mu hada karfi mu daku da ashwarya tabbas
zamu gama da wadannan halittu
kamar yadda muka gama da wadancan
kodajin wannan batu sai yarima yauhana mai
kafa daya da boka karluz mai yankakken kunne
sukaji waji sabon karfi ya shigesu
kafin sammaru da ashwarya suyi yunkuri tuni
sub zare makamansu
sun ruga inda dodannin suke
cikin hanzari sammaru da ashwarya suka kai
musu dauki
koda aka hadu da dodannin nan sai wuri ya
yamutse, kura ta turnuke sararin sama
ihu, ruri da karar karafa ta yawaita
nanfa akayita turnuku ruguntsumi, artabu,
gwagwarmaya da dauki ba dadi
saida aka shafe kwana guda da yini daya ana
wannan azababben yaki
awannan gumurzune boka karluz ya rasa
hannunsa guda na dama
domin wani dodone ya gutsureshi yayi loma
guda dashi
shikuwa yarima yauhana saidaya zamana ko'ina
ajikinsa sarane
na faratan dodannin jini nata zuba daga jikinsa
amma bai fasa ragargazarsuba
wani lokacinma saidai kaga ya taso da karfinsa
yaci gaba da daukar rai
gimbiya ashwarya da yarima sammaru kuwa sun
zama
tamkar shaidanu atsakiyar dodannin duk inda
suka kutsa
saidai kaga dodannin na zubewa akasa
kamar ana sassabe agona
lokacinda gumu yayi gumu sai wani dodo ya
shammaci
ashwarya ya sureta da hannu daya ya dagata
sama da nufin ya rotsata akan wani dutse
kamar walkiya haka yarima sammaru ya daka
daga
can nesa inda yake ya durga agaban dodan
kafin ya makata akan dutsen tuni sammaru ya
soka masa takobi acikin kwayar idonsa guda
bisa dole dodon ya saketa ahankali amma
dukda haka saidata fado kasa
ta sami rauni agoshinta
koda sammaru ya zare takobinsa daga cikin
kafar idon dodon
sai takobin ta fito tareda kwayar idonsa cake a
tsininta
nantake dodon ya fadi kasa matacce
ashwarya ta mike da nufin ta mike tsaye
amma sai wani dodon ya cafi kugunta ya dagata
sama kamar ya dauki 'yar tsana
kawai saiya bude bakinsa da nufin ya cinyeta
nanma sammaru ya sake dako tsalle asama ya
saita bakin dodon da tsinin takobinsa
tuni takobin ta huda shi ta faso bayan keyarsa
ba shiri ya saki ashwarya ta fado tsakiyar
dodannin
nantake suka kai mata wawa da nufin suyi
gutsun gutsun da ita
kawai sai ganin sammaru sukayi akansu yana
bare musu kawuna da kaifin takobinsa
kai atakaice dai saida sammaru ya ceci
ashwarya akalla sau goma sha daya awannan
yaki
amma dukda haka saidata suma sakamakon
yawan raunukan dake jikinta
bayan sun gama karar da dodannin ne gaba
daya su
yarima sammaru, yauhana, boka karluz suka
yanki jiki suka fadi kasa sumammu
aljani karmash kuwa tuni rai yayi halinsa
don dodanni sunyi walima da jikkunansu
aljani guluz ne kadai atsaye afilin yakin
ya tsaya kyam yana shara kuka
saboda ganin irin mutuwar wulakancin da yan
uwansa sukayi
adaidai wannan lokacinne magariba ta doso
amma su sammaru basu farfadoba
saida sanyin asuba ya busa ,aljani guluz ne ya
taimakesu ya bude jakar boka karluz
ya debo magani ya shashshaa musu, sannan
yaje ya nemo ruwa ya basu suka sha
sa'adda ashwarya ta bude idanun taga bata
mutuba
kuma taga masoyinta araye sai farinciki ya
rufeta
ta dubi sammaru tace
godiya agareka mara adadi yakai masoyina
hakika inbadon kaiba da tuni na dade a
kushewa
sammaru ya yunkura da kyar ya gyara zama ya
maida mata damartanin murmushi yace
aikema inbadon keba da ban rayuba na kawo
iyanzu har na ceci rayuwarki
babban farinciki na shine na ganinki araye
yana gama fadin hakan ne sukaji boka karluz ya
fashe da kuka
al'amarin daya dugunzuma hankalinsu kenan
gaba daya
yarima yauhana yaja kafarsa guda ya matso
kusa dashi yace
yakai abokina ina dalilin wannan kuka naka
karluz yace
ka dubi kunnuwana babu su kuma ka dubi
hannuna shima babu
ka sani cewa har abada halittata ta sauya bazan
sake dawowa daidaiba
duk wannan abu ya samenine kawai don
kwadayin neman sirrikan tsafi akogon muddarul
iksina
tabbas yamzu na kasance mai nadama bisa
barin kasata, dangina da harkata don wannan
bukata
wacce banida yakinin samun biyanta
kodajin haka sai yarima yauhana yayi
murmushin yake yace
haba abokina aikai kukan dadi kake
kadubenifa ka gani kiri kiri na zama gurgu mai
kafa daya
dole saida sanda zan iya tafiya
kuma ka tuna cewa badon bukatar kaina na baro
gidaba
saidon na ceci rayuwar mahaifin ,ka tuna cewa
ni dan sarkine mai takama da mulki
amma ga yadda rayuwata ta kasance
lallai na fika madama da bakin ciki
hakadai akaci gaba da hira awannan waje har
yamma tayi dare ya fado
atakaice dai saida su sammaru suka kwana biyu
awannan wuri suna jinyar jikinsu
sannan kowa ya sami kwarin jikinsa
yanzudai tafiya ta rage saura su hudu kacal
lokacinda sukayi shirin barin wannan wuri ne
donshiga daji na biyu wato dajin nan da ake kira
zamutul makatul
yayinda sammaru ya dubi kowa yace
yaku abokan tafiya kuyi sani cewa yanzu zamu
shiga cikin jejin zamutul makatul mai dauke
da mugayen namun dawa, kuma sihirtattu
kamar yadda boka hulumul makahur yayi mana
bayani dolene muyi
amfani amfani da karfin tsafi da kuma karfin
damtse
a wannan daji don haka ke ashwarya dake da
karluz ne zaku
wuce gaba ni kuma ina biye daku in yauhana da
guluz su kasance abayana,
ina yi muku tuni da cewar
wanda duk yasan sirrin daji acikinmu toya dinga
nusar damu
don musami kubuta da wannan bayanine
sammaru ya kammala zancensa
ba tareda bata lokaciba
ashwarya da boka karluz suka wuce gaba
sammaru ya bisu abaya sannan yauhana da
guluz
saida sukayi tafiyar sa'a guda cif sannan suka
iso dajin zamutul makatul
dajin zamutul makatul ya kasance yanada
dogayen bishiyoyi da manyan tsaunika
sannan akwai kwazazzabai
da duhuwoyi masu yawa,
komai jarumtakar mutum idan ya shigo cikin
wannan daji
dolene zuciyarsa ta buga don yasan cewa dole
asamu
muggan dabbobin daji acikinsa da muggan
aljanu
da shigarsu sammaru cikin wannan daji sai
sukaga hanya ta rabu kaso uku
hanya ta farko ta nufi inda wadansu manyan
tsaunika suke guda uku
hanya ta biyu ta nufi inda wadansu dogayen
bishiyoyi suke masu yawa
ba adadi
itakuwa hanya ta uku ta nufi cikin wadansu
kwazazzabai ne
wasu da ruwa acikinsu, wasu kuma babu
da yake gimbiya ashwarya ce akan gaba saita
tsaya cak
sa'adda aka zo wannan mararraba ta daga
hannu alamar atsaya
nantake kuwa kowa ya tsaya ashwarya ta waigo
ta dubi sammaru tace
to ga hanya ta kasu gida uku wacce yakamata
mu bi?
MU HADU A PART L DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU✍️✍️
PART L ❤️❤️
Na: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
MARUBUCIN YACI GABA DA CEWA....
Kowa yayi shiru sai aljani guluz yazo ya karewa hanyoyin kallo
yana nazarinsu, sannan yace
kunga wannan hanya ta farko wacce zata kaimu
wajen manyan tsaunikan can tana da mugun hatsari
domin ba'a rasa muggan dabbobin daji da aljanu acikin tsaunika
domin sukanyi gidajensu aciki
itakuwa wannan hanya ta biyu wacce zata kaimu wajen dogayen bishiyoyi
anan ne manyan tsuntsaye masu hadari suke buya
waccan hanyar kuwa ta uku mai kwazazzabo saidai a samu dabbobin ruwa acikinsu
domin mahadace ta teku
kodajin wannan batu sai yarima sammaru yace aikuwa indai hakane gwara mubi hanya ta uku
domin tafi saukin hatsari
nantake gimbiya ashwarya ta wuce gaba suka nufi wannan hanya mai kwazazzabai da yake hanya mai dauke da duwatsu da kuma ruwa saida sukayi tafiyar sa'a guda cif
sannan suka iso bakin wata korama wacce sai an wuce ta cikinta sannan za'a
hau kan turba
koda zuwansu wannan wuri kawai sai aashwary ta daga hannu kowa
ya tsaya,
nantake tayi 'yan tsubbace tsubbacenta
donta gano abinda ke cikin wannan korama
amma bataga komai ba face kananan kifaye
koda ta gama saita baiwa boka karluz wuri yayi nasa kokarin shima
baiga komai ba, kawai sai ashwarya ta fada cikin koramar sannan kowa yabi bayanta
kash rashin sani yafi dare duhu inda sunsan masifar da zasu riska acikin wannan korama
da basu shigetaba, saida sukazo tsakiyar koramar sannan wata katuwar
maciijiya ta taso sama daga karkashin ruwa
koda maciijiyar ta mikar da. wuyanta sama sai ya tafi kamar zai tabo rana don tsananin tsawo
cciki razani kowa ya zare takobinsa
ashe macijiyar nan jeloline da ita barkatai
masu tsawo da kaifi tamkar zabira
su sammaru suka juya da baya da nufin su fita daga cikin ruwan
kawai sai sukaga jelolin macijiyar sun fito sunyi musu kawanya
babu inda zasu ratsa su wuce
bisa dole suka juya suka tsaya atsakiyar suna kallon
wannan dogon wuya nata
wanda har yanzu tafiya yakeyi bai tsayaba
sa'adda aka shafe sa'a guda sai wuyan nata ya tsaya
yakai makura wato iyakar tsawonsa
ba zato sai wuyan ya lankwaso
kasa wanda shike dauke da katon kan macijiyar
bakin ya wangame gaba daya yana aman bakin dafi
sannan ga wasu irin hakora gaftara gaftara
aciki tamkar an jera hauren giwa guda dari
ahankali bakin ya rinka saukowa kasa
tamkar yadda wuyan yayi sama dazu
ahankali kuma jelolin macijiyar wadanda
sukayi wa sammaru kawanya
suka rinka kumbura, koda faruwar wannan al'amarin sai hankalinsu sammaru ya dugunzuma kowa ya zare takobinsa
yana saran jikin macijiyar saidai kaga tartsatsin wuta yana tashi
yayinda takubban nasu ya sari jikin macijiyar tamkar akan dutse suke sarawa
nanfa dukkaninsu suka firgice suka
saduda cewa ba tsumi ba dabara
tabbas hallakarsu tazo
sammaru ya nutsu yana nazarin jelolin macijiyar da kuma bakinta
wanda ke saukowa kasa ahankali
daga can kololuwar sama
kawai sai yayi ajiyar zuciya ya dubi ashwarya, yauhana, karluz da guluz
yace yaku abokan tafiyata kuyi sani cewa yaufa karyarmu ta kare
domin duk abinsa muke takama dashi bazai kwacemuba a wurin macijiyar nan ba
ku sani cewa idann ta gama kumbura nantake zata mammatse jikin mu ta kakkarya kasusuwan jikinmu
sannan ta lankwamemu da wannan katon bakin nata dake saukowa
shin acikin ku babu mai wata dabara wacce zata fishshemu?
karluz da ashwarya suka dubi juna
kawai sai suka fara jarraba karfin sihirinsu
akan macijiyar
duk abinda sukayi saiya zamo abanza domin yaki ya fara aiki
wannan tasa kowa ya karaya, masu kuka suka fara
masu nadama suka ci gaba dayi
boka karluz yaci gaba da nazarin kumburin macijiyar dakuma
saukowa kanta kasa ya gane cewa
adaidai lokacin dakan
yazo dafda kawunansu zata kumbura,
ta matsesu don haka sai ya cigaba da tunanin mafita azuciyarsa
domin shi tun yana yaro baitaba fitarda rai ga samun nasara ba
bisa duk abinda yasa agabansa
haka dai yaci gaba da tunanin har sa'a guda
saida ya rage saura kamu daya tsakanin kawunansu da bakin macijiyar da kuma gangar jikinta
danasu boka karluz ya tuno da wata dabara
nantake cikin zafin nama boka karluz ya zaro allon tsafinsa ya jefashi
cikin bakin macijiyar
yin hakan keda wuya sai macijiyar ta kama da wuta ta dinga wani ruri
tana faduwa da mikewa acikin ruwan da kyar su sammaru suka samu suka sulale daga jikinta suka haye koramar
gaba daya sannan suka yita shara gudu
saida sukayi gudu tsawon rabin sa'a
sannan suka tsaya suka juya baya
daga nan inda suka tsaya din suna iya hango macijiyar har yanzu ruri take tana faduwa da tashi
al'amarin daya janyo girgizar dajin gaba daya kenan
ahaka dai ta kone kurmus ta daina motsi koda su sammaru suka ga cewa macijiyar ta mutu
sai suka zauna dirsan suna haki
bayan kowa ya nutsune sai sammaru ya dubi kkarlu yace
gaisheka babban boka hakika nayi maka jinjina
da godiya mara adadi hakika yau inba don kaiba da tuni mun zama abincin wannan macijiyar
shin ya akayi ka tuno da wannan dabarar ta jefa allon tsafinka abakinta?
kodajin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa boka karluz
alokaci guda kuma ya fashe da kuka
al'amarin daya tashi hankalin kowa kenan
saida sammaru ya rarrasheshi sannan ya daina kukan
boka karluz yayi gyaran murya ya dubi sammaru yace
yakai gwarzon jarumi kayi sani cewa bantaba tsammanin cewa
idan na jefa allon tsafina abakin macijiyar nan zamu kubuta ba
kasan ance komai jarrabawa ake kuma sa'a naga mai rabo
lallai rabon kubutar mune yasa na jefa allon tsafina abakin macijiyar
kayi sani cewa ba komai ne ya sakani na fashe da kukaba
face sanin cewa daga yau na rasa dukkanin sirrikan tsafina har abada
kuma bazan sake yin wani abuba wanda yadanganci tsafiba har yayi tasiri har abada
saboda na kona allon tsafina da hannuna
kaga shikenan na rusa burina na duniya gaba daya
duk wahalar nan da nasha abaya ta zama abanza
gwarama ace na hallaka tun afarko
koda boka karluz yazo nan azancensa saiya sake fashewa da kuka nanfa tausayinsa ya kama su sammaru
suka ci gaba da rarrashinsa
bayan kamar rabin sa'a sai yarima sammaru ya dubi dukkaninsu yace
yaku abokan tafiya kuyi sani cewa mun gama da dajin zamutul makatul yanzu kuma zamu shiga cikin jeji na gaba wanda akekira da halalil masur
ina mai tunasar daku cewa
shifa wannan daji ne na wata tsafaffiyar wuta
maici sama da kasa, gabas da yamma, kudu, da arewa
atsakanin sama da kasa ne kawai akayi wata gada wacce saidai mubi ta kanta ne zamu wuce
ku sani cewa ita wannan gada anyita ne da zallan itatuwan danyen kara da kuma danyen jijiyar bishiya
akoyaushe wuta tana laso jikin gadar kuma wata irin iska
mai karfi na jijjigata, kuma duk abin dake kan gadar zai iya hallaka
ko kuma ya fado kasa
ko kuma iska ta wullashi cikin wuta
babu abinda zai kwace mu awannan wuri face karfin damtse
hikima da kuma karfin tsafi don haka tun yanzu saimuyi
koda sammaru yazo nan azancensa
sai kowa yayi shiru aka rasa wanda zaice uffan
aka shiga tunani daga can sai gimbiya ashwarya tace
ga tawa shawarar
dafarko dai acikin mu nan babu mutum mai karfi da zafin nama
kamar sammaru don haka shine ya kamata ya fara hawa kan wannan gada
inyaso ni sai na bishi abaya don na taimaka masa da sihirin tsafina
yayinda bukatarsa ta taso
haka kuma dolene mu daddaure jikkunan mu da danyar jijiyar bishiya ya zamana
muna hade da juna yadda karfin iska bazai tarwatsamuba
dukda haka dolene mu ruke hannayen juna
ya zamana cewa wannan na ruke da wannan
aljani guluz ne zai zamo na karshe yarima yauhana kuma ya zamo atsakiya
tunda kafa daya gareshi
ina ganin hakane zamu cije da karfin tsiya
muyi tafiyar kwana guda akan gadar
har mu fita daga dajin halalil masur
sa'adda ashwarya tazo nan azancenta sai kowa ya gamsu da shawararta
kuma aka jinjina mata bisa wannan kaifin basira
data nuna tareda tsagwaron hikima da kaifin basira
gimbiya ashwarya ta sake duban kowa daya bayan daya
tace
tofa ku sani wannan dabarar tawa ba lallai bane ta kubutar damuba
kawai dai nayi hasashene, zamu iya tsira kuma zamu iya hallaka
amma dai mu karfafi zuciyoyin mu akan samun nasara
akan wannan bayani ne akarufe bayani kowa ya mike tsaye aka ci gaba da tafiya
sai da suka kwana uku suna tafiya
sannan suka iso dajin halalil masur
koda sukazo daf da farkon dajin sai sukaji
radadin zafi na busowa
kuma suka hango yadda wuta ke alkafira sama da kasa
saiduk suka firgice suka juya da baya
yarima sammaru da gimbiya ashwarya ne kadai basu juya da baya ba
cikin fushi sammaru ya waiga garesu ya daka musu tsawa yace
LIKE DA COMMENT DINKU SUNE SUKE BAMU KWARIN GWUIWAR CIGABA DA ZABO MUKU LABARAI SANNAN MU ZAUNA MUYI TYPING DINSA HAR MUYI MUKU POST.
MU HADU A PART M DON JIN CIGABAN WANNAN KAYATACCE KUMA KASAITACCEN LABARI ✍️🙏
**MATSATSUBI**💥💥
LITTAFI NA UKU✍️✍️
PART M ❤️❤️
NA: ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI 🤴
POSTING: NAJIBULLAH MUHAMMAD ☝️☝️
TYPING: HABIBULLAH MUHD KABARA ✍️✍️
MARUBUCIN LITTAFIN YACI GABA DA CEWA...
************
Ina zaku koma?
to kusani cewa bala'in dake bayanku ya ninka na gaba sau dubu
domin baku isa ku sake ratsawa ba ta cikin dajin buluzul mahaful da dajin
zamutul makatul araye
ya zama dole kuzo mushiga cikin wannan daji mu ketareshi
don mu isa inda muke hari idan kuwa kuka ki zan yakeku da kaina
na hallaka ku gaba daya
kodajin wannan batu sai yauhana,
karluz da boka guluz suka dawo da baya
cikin sanyin jiki da karayar zuci
bisa

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

1 Comments On MATSATSUBI BOOK 3
avatar
abasu-kala

10 months ago

Reply

Good really enjoy the book waiting for Miftahul Zarbil

Please Login or Register in order to submit comment