Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kai na ya yi yana kallan Innati dake sauke ajiyar zuciya yace " Zan wuce Khadija ki kula da yarinyar don Allah" murya a shaƙe Innati tace "InshaAllahu Baba"

"Toh MashaAllah,Allah ya tayaki riƙo" .

Bayan tafiyarshi ne muka samu damar karyawa. Lura da nayi har zuwa lokacin ran Innati a ƙuntace yake yasa na kawo mata zanchen samun aikina.

Murmushi ta saki cikin jindadi ta ce " MashaAllah auta Allah ya yi mana jagora yasa ki fara aiki nan a sa'a, ina san kiyi aikin nan Auta ko dan na samu sauki wajen dangin Mahaifin ki, saboda suna ganin kaman na barki cikin halin kuncin rayuwa na kuma hana su ɗauke ki tunda suna ganin suna da hakƙi akan ki. Ki kula da tarbiyar da nabaki Auta don Allah". Addu'a ta yimin sosai da fatan farawa a sa'a.

Duk irin murnan da nake na samun wannan aikin, ƙasan zuciya ta cike yake da zullumi da fargabar irin rayuwar da zanyi a ƙarƙashin mutum da ada ban dauƙeshi a bakin komai ba. Sai gashi a yanzu nike ƙarƙashin sa.






MUJE zuwa.




E 5-6.


F͟A͟C͟I͟N͟G͟ T͟H͟E͟ H͟A͟T͟E͟.



Yau ya kama litinin. Tun asuba dana tashi ban koma ba na hau aikace- aikace daya kamata nayi don ko azkar ɗin da nake zamanyi ban samu nayi ba saboda gudun makara. Wajen karfe shida da rabi na gama komai na shiga wanka. Atamfar da Ramlat ta bani na ɗauko. Ɗinkin riga da sket ne ,ba'a yiwa kayan wani ado na azo a gani ba amma ɗinkin ya yiwa atamfar kyau sosai. Shiryawa nayi cikin atamfar da sket din yaɗan kamani saboda nafi Ramlat jiki. A gurguje na fito yafe da mayafin da yasha guga wanda ya shiga da atamfar sosai. Duk da banga kaina cikin mudubiba amma nasan kayan sunyi min kyau ko daga yada Innati tayi ta zuzu tawa.

Wajen ƙarfe bakwai daidai na fito bayan nayiwa Innati sallama tabini da addu'a da kuma fatan alheri. Toh da yake ban kashe kuɗin da Baba Salmanu ya bani ba na adana su saboda kuɗin mota. Allah ya taimake ni kuwa ina fitowa na samu ɗan sahu. Ƙarfe 8 saura minti shida tayimin a bakin ƙofar office din Mrs Eman Lamin.

Kafin kace me har karfe 9 tara ina nan zaune banga alamun zuwanta ba. Har na fara sarewa da zama sai gata ta fito ta private elevator ɗinsu . Sanye take cikin light green din business suit da tayi masifar yi mata kyau. Kanta sanye da ɗan ƙaramin hijab iya wuya. Lokacin da nake da ƙuruci yata ina masifar san fashion. Sai in ɗauki awanni ina karanta magazine na fashion brands na kuma yi order duk wanda naga ya birgeni. Sai gashi babu wani abu da yarage min a yanzu bayan wannan ƙaddarar data same mu.

Wuce ni tayi fuskarta ɗauke da murmushi cikin sauri na miƙe ina gaisheta "Goodmorning, Ma'am!" Tare da bin bayanta. Juyuwa ta yi ta kalle ni tace " Eman,call me Eman" ta shige office ɗin nima na bita. Umarni ta bani dana zauna kan kujerar dake fuskantar ta, ta kuma ce na fito da biro saboda akwai abinda zata gayamin mai muhimmanci na rubuta.

"Kinga office ɗinki?"ta tambayeni, tana gyara kwaliyar fuskarta. Daga Jakarta har zuwa ɗan ƙaramin midubin dake hannunta kana gani kasan sunyi kukan kuɗi. I was supposed to have a future like her. Jikina ne ya yi mugun sanyi. Rayuwa juyi- juyi.

"A'a" nace ina girgiza mata kai.

"Sai fa da na gayawa Haidar ya miki Tour na floor namu idan kin zo fa" ajiyar zuciya ta suke ta miƙe tsaye. " Muje na nuna miki da kaina".


Saida ta gama zaga yawa dani sannan tace "muje kiga office ɗin Mr President " .


Idanuwan mu ne suka sarke cikin na juna bayan mun shiga cikin President office. Yana zaune kan kujerar dake bayan katon tebir dake cikin office ɗin . Sanye yake cikin Black suit amma ya cire ta saman sai farar rigar ciki, botiran rigar kusan rabi duk a buɗe. Hannun rigar ma a nannaɗe suke zuwa gwiwar hannu. Biro ne a bakinshi da takardu baje a gabanshi da alama aiki yake yi. Dan ga gashin kansa nan duk ya sakko gaban goshin sa kaman wanda ya zuba ruwa akan.

Murɗawa naji ciki na ya yi, zuciyata na wani irin bugu nace "na shiga uku what's happening ne?" . Wai duk ya aka yi hakan ta faru?.
Wani irin mugun haɗe fuska ya yi yana kallon mu dan baiyi tunanin tare muke ba.

Bata lura da yanayinsa ba cikin joyful tone ta cemin " wanna shi ne President kuma mamamlakin A&E, Neehal Meet AYAAN LAMIN my twin brother" A ruɗe nake kallanta jin wannan furuci nata. Sai yanzu nake ƙara ganin matsananciyar kaman da sukayi dashi. Murmushi naga ya yi mata da bai kai zuci ba.

"Ayaan don Allah ka ƙarasa yi mata bayanin aikinta, ina da meeting ne da finance department bani da time please "

Cikin yaƙe yace "sure,sis" kai ta ɗaga mishi ta fice a office ɗin. Iskar dake tsakani dashi was so tense da nake jin yanda hannuna ke haɗa uban gumi. Wuce ni yayi shima ya fice daga office ɗin nayi saurin binshi. Office ɗina muka shiga ba tare da ya juyu ba ya faramin bayani

"aikin ki shi ne kiyi filling duk wani important document ki kuma yi arranging dinsu a different categories,
Ki amsa wayar da suke da muhimmanci ,ki yi corresponding duk wani information ga client ɗinmu, ki kuma karbi duk wani visitor da zaizo dan ganin CEO wato Eman kenan"

Tunda ya fara maganan na zuba masa ido ina jin ciwon yanda ko kallan fuskata bayasan yi. Ko da yake banga laifin sa ba.

"Ina tunanin last Secretary data tafi tabar miki duk wani important abu da ya dace, dan haka ki duba da kyau ki amsa calls masu muhimmanci ki mikasu gurin Eman" ƙoƙarin ficewa yake bayan ya gama min bayani. Kasa jurewa nayi cikin sauri nace masa " Me yasa ka ɗauke ni bayan ka ganeni? Ko kayi hakan ne dan rama abunda nayi maka a baya?."

Chak ya tsaya da tafiyar da yake ya juyu yana kallo na. Takowa ya yi har inda nake tsaye. Sai naga na zama wata ƴar ƙarama a gabanshi saboda girma da tsayi da yake dashi yanzu ba kamar da ba da kibar ta boye tsayin sa. Da kakkausar murya ya ce " what did you say?".

Murya na rawa na ɗanja baya nace " me yasa ka ɗauke ni? Is this some kind of twisted revenge?"

Wata irin dariya ya saki yana wani irin groaning cikin zafin rai ya ce " Dont give yourself too much credit, Miss.Neehal, ke ɗin bakiyi worth da zan rama abinda ki ka yimin ba, ni ba selfish mutum bane da zan tsaya bata lokacina gurin rama abinda ki ka yi min. Time ɗina abu ne mai matuƙar muhimmanci bazan yi wasting dinshi akan wanda bai can-cance shi ba." Wani irin abu naji ya daki ƙirjina kaman wadda aka dabawa wuƙa a ƙahon zuci saboda zafin da maganan tashi tayi min.

" Idan ta ni ne baki chan-chanci wannan aikin ba bare har ki taka ƙafarki cikin building ɗin nan, har ki ka samu damar shigowa cikin main office ɗina. Eman ita ce ta baki wannan aikin, it was all on her"

Yana gama faɗin haka ya wuce ni ya fice a office ɗin ya bugomin ƙofar da ƙarfi gaske har saida na firgita . Wani irin guilt da embarrassment suka rufe ni hawaye masu ɗumi suka biyo kuncina.



***

"𝘐𝘥𝘢𝘯 𝘵𝘢 𝘯𝘪 𝘯𝘦 𝘣𝘢𝘬𝘪 𝘤𝘩𝘢𝘯-𝘤𝘩𝘢𝘯𝘤𝘪 𝘸𝘢𝘯𝘯𝘢𝘯 𝘢𝘪𝘬𝘪𝘯 𝘣𝘢 𝘣𝘢𝘳𝘦 𝘩𝘢𝘳 𝘬𝘪 𝘵𝘢𝘬𝘢 ƙ𝘢𝘧𝘢𝘳𝘬𝘪 𝘤𝘪𝘬𝘪𝘯 𝘣𝘶𝘪𝘭𝘥𝘪𝘯𝘨 ɗ𝘪𝘯𝘯𝘢𝘯,𝘩𝘢𝘳 𝘬𝘪 𝘬𝘢 𝘴𝘢𝘮𝘶 𝘥𝘢𝘮𝘢𝘳 𝘴𝘩𝘪𝘨𝘰𝘸𝘢 𝘤𝘪𝘬𝘪𝘯 𝘮𝘢𝘪𝘯 𝘰𝘧𝘧𝘪𝘤𝘦 ɗ𝘪𝘯𝘢. 𝘌𝘮𝘢𝘯 𝘪𝘵𝘢 𝘤𝘦 𝘵𝘢 𝘣𝘢𝘬𝘪 𝘸𝘢𝘯𝘯𝘢𝘯 𝘢𝘪𝘬𝘪𝘯, 𝘪𝘵 𝘸𝘢𝘴 𝘢𝘭𝘭 𝘰𝘯 𝘩𝘦𝘳"



Maganan dake tamin amsa kuwwa cikin kunne kenan harna koma gida. Waɗannan kalamai dake fitowa daga bakinshi sun ƙara sani cikin damuwa matuƙa. Kasa taɓuka komai nayi bayan na koma gidan wajen la'asar. Sallah kawai nayi na samu guri na kwanta ko abinci na kasaci tun wanda naci da safe. Innati batayi tunanin komai ba ta ɗauka ko gajiyar aiki ce kawai tunda yau na fara. Tunda na kwanta nake tunanin farkon haɗuwa ta dashi da rayuwa ta shekaru shida da suka wuce.



6 𝙮𝙚𝙖𝙧𝙨 𝙗𝙖𝙘𝙠. 2017


A yatsine nake kallan sabon driver da Abbu ya kawo min wanda hakan ya zama kaman al'ada duk shekara sai an chanza min sabuwar mota da kuma direba.

Kallanshi nake tundaga kan takarmin ƙafarsa da yake a suɗe har zuwa kayan jikinsa dake a kuɗe. Yana da ƴar ƙiba ba canba dan har wani ɗan tunbi ya ajiye. Duk irin direbobin da Abbu ke kawo min this is the worst a cikin su. Akwai rashin wayewa a tattare dashi. Murmushi yake min ganin yanda na zuba masa ido ina nazarin shi. Wani irin amai naji yana taso min saboda haƙoransa da nagan su jajir dasu babu alamun suna samun ishashshen wanki. For God sake a ina Abbu ya samo min wannan ƙazamin mutumin haka, dan a ƙalla zaiyi sheraka ashirin da tara.

Nayi tunani komawa ciki na samu Abbu, amma nasan komawar tawa zai jamin faɗa ne gurin Innati saboda shigar dake jikina. Kayan makaranta ne riga da sket, sket ɗin ya masifar kamani daga tsakiya kuma ta baya an tsagashi tun daga wajen gwiwar ƙafa har zuwa ƙasa. Rigar jikina ta uniform ɗin itama ƙarama ce sosai da koya na ɗaga hannuna sai cikina ya ɗan fito. Kaina babu ɗankwali ko hula sai gashin kaina dana tufke a tsakiyar kai na saki jelar gadon bayana. ɗan ƙaramin throne ne a kan nawa da aka rubuta "Queen" a jiki. Hatta takarmin ƙafata shima dogone mai tsinin gaske. Sai ƴar jacket ta sweeter dana ɗora kan rigar tawa.

A yatsine na miƙa mishi jakata da nake ganin bai dace da ya riƙe ba. cikin sauri kuwa ya ƙarba ya buɗemin ƙofar bayan motar na shiga. Idan na dawo dole Abbu ya samo min new driver ,wannan idan ina zuwa makaranta dashi ai raina ni zasuyi. I'm the queen of my school, everything should be perfect and that include the driver.

***

Abbu na wato Alhaji Maleek Abdallah attajirin mutum ne dake harkar saida motoci ko ince safarar motoci daga ko wace ƙasa. kuma Alhamdulillah ubangiji ya sa masa albarka cikin kasuwancin nasa dan har campanoni wajen uku yake dasu na motoci. Toh a can saudia yaje umrah suka haɗu da Innati (Khadija zubair) , don ita Innati na balarabiyar saudiya ce shi kuma Abbu na bafulatani.

Ni kaɗaice Allah ya basu shi yasa na taso cikin gata da soyayya da nake ganin babu kamarta a duniya. Babu abinda zan gani yanzu na nuna ina so ba tare da ya mallakamin shi ba, mota kuwa kamn yanda nace duk sheraka ne sai an chanza min sabuwa dal. Wani lokacin Innati har faɗa takeyi akan gatan yana yawa ni macece kuma wannan gatan da yake min zai iya lalatamin rayuwa. Amma Abbu yace shi sam dole ya bawa ƴarsa gata dan duk wani abu da yakeyi saboda ni ne. Idan bai bani abunda nake so ba mene amfanin dukiyar tasa?. Wannan faɗan da yake rufeta dashi a duk lokacin da tayi magana yasa take yin shiru koda kuwa taga abinda bai mata ba.

Zan iya cewa ni mutum ce mai tsananin san tsabta da ganin komai ya tafi yanda ya dace. Sannan ina da faɗa da kuma rashin kunya ta bugawa a jarida dan bana barin kota kwana komai girman mutum idan ya shiga gonata bana raga masa koɗan uban waye shi.


Ninah ita ƙaɗaice kawata dan bada kowa nake hulɗa ba duk irin yanda da yawa suke so suna hulɗa dani saboda gata da kuɗi da kuma kyau da nake dashi. Toh ba kowa ne ya kai level ɗin da zai shiga crew ɗina ba sai ita kaɗai. Ita ɗinma saida ta haɗa kwalitis ɗin tukun. Wato kyau, gayu, gata, sannan kuma ƙudi. Yanda muke jida kai da ɗagawa a school yasa suka bamu nickname da 'Mean girls' .

Bayan wannan kuma duk shekara nike cinye gasar kyau da kuma fice wajen fashion da kuma aces da nake fito dasu a dukkanin results nawa, Ninah kuma tazo a second. Wannan dalilin yasa aka bani crown na 'Queen' dake kaina a koda yaushe. A yanzu muna ss2 ne muna shirin shiga 3, a lokacin ina da shekara 16.



E 7-8



kusan tare ya faka motar data su Ninah. Ban fito ba na zauna ina kallan driver ɗinta daya buɗe mata mota ta fito cikin yauƙi da isa. Ɗan murmushi ne ya kubce min domin kusan komai namu iri daƴa ne.

"Hajiya mun iso " Naji muryar shi a kaina. Juyawa nayi na kalleshi yana tsaye riƙe da murfin motar. Cikin jin haushi nace "Sai ka yi min ihu a kunne?,makauniya ce ni?" Murmushin da yake ne ya kubce masa a sanyaye ya ce "kiyi hakuri Hajiya, naga kaman kina tunani ne"

Mugun tsaki naja na fito daga cikin motar ,fitowa ta ya yi daidai da ƙarasowar Ninah. A yatsine take kallan shi kaman yanda nayi tace " Queen who's this?" Cikin yatsina nima na bata amsa "sabon driver ɗina ne" kallan shi tayi tun daga sama har ƙasa kafin ta saki wata irin dariya data kular dani na zabga mata harara ina gyara Prada jakata dana ƙarba a hannun sa.

Sai da ta yi mai isarta sannan tace cikin dariya " For God sake Queen, kina so a raina mu ne, God forbid Queen he has to go.like look at him his so dirty, gaskiya ki gayawa Dad a kawo wani" . Ban bata amsa ba na juya ina kallan shi, ya matsa can gefe kanshi a ƙasa jikinshi a matuƙar sanyaye. Bansan me yasa ba amma sai naji banji daɗin yanayin da naga ya shiga ba .suarin kawar da tunanin nayi a zuciyata , nace and so what idan baiji daɗin ba? what's wrong with me ne?.

"Ka dawo kaman 4 ka ɗauke ni" Ban jira amsar sa ba na wuce cikin school Nina ta rufamin baya.

"But Queen kin san me?" Kai na girgiza ina kallan Ninah dake kusa dani muna tafiya kaman wasu ƴan fashion.

Cigaba tayi da cewa " Wannan driver ɗin naki is one in billion fa, idan ya samu hutu dajin daɗi baƙaramin Hot guy bane wlh" baki na taɓe domim nikam banga abinda take faɗi ba. Dagani har ita burki mukaci hango Zain current boyfriend ɗina tare da rival ɗina Hanan. Kaman yanda nake nida Ninah itama haka take da maƙarraban ta. Zan iya cewa she's a copycat dake son ganin ta mallaki duk wani abu dana mallaka. Tanaso taga ta wuceni a komai amma ta kasa samun nasara.

Ido na zuba musu zuciyata na zafi. Yanda suke wa juna wani kallo da murmushi ya isa ya tabbatar maka da soyayya mai ƙarfi ta shiga tsakanin su. Zain is the definition of perfect guy da every girl zataso ta mallaka. He's the King na school ɗinmu kaman ni. Kyau, aji, kuɗi babu abunda bashi dashi. Da alama takusa nasara ta wannan fannin. A fusace na wucesu.

Wucewar tawa yasa suka farga ya biyoni cikin sauri yana min magana. Ban kulashi ba har na shige ɗakin da aka yishi musamman dan hutuwa na banko ƙofar. Sai da ya gama magiyarsa har ya gaji yatafi. Muryar Ninah naji tana magana da na buɗe mata.

"Queen, tana can tana dariya fa na samun nasara data farayi, kuma abin haushin har yanzu suna tare walahi"

Da sauri na leka ta window ina kallan su har yanzun kuwa suna zaune cikin garding na school ɗin. Babu wani damuwa a tattare dasu. Batun yau nasan Zain da bin mata ba amma tunda muka fara dating ya daina kula kowa sai ni, dan cewa ya yi na mallaki duk wani abu da yake nema agurin mace amma yau sai gashi da Hanan dan itama ba baya ba wajen kyau.

A fusace nayi jifa da jakata tare da sakin ƴar kara hawaye masu zafi suna bin kunci na. Bansan cewa ina san Zain har haka ba sai yanzu dana ganshi da Hanan. Dafani Ninah tayi tace

"in baki shawara Queen"

kai na ɗaga ina kallanta hawaye na bin fuskata. Janyo ni tayi muka zauna a gadon dake ɗakin hutun tace

" stop showing kina sanshi da yawa, yanda yayi carefree duk da yasan cewa kina sanshi amma hakan baisa ya daina kula mata ba. Ki nuna masa kema zaki iya moving forward ba tare dashi ba, ki sashi shima ya yi feeling jelousy ɗin nan. Wannan driver naki ki gyarashi a matsayin fake boyfriend ɗinki harzuwa lokacin da zaki koyawa Zain hankali sai ki rabu dashi kinga kaman hakan duk cikin aikinsa ne ki bashi kuɗi masu yawa idan kin gama amfani dashi."

Shiru ne ya ratsa tsakanin mu ina tunani anya kuwa idan nayi hakan na kyauta? Wasa da feeling din wani?

"Ki daina wani tunani Queen wannan ne kaɗai option ɗinki da zaki kara jan hankalin Zain kan ki, kinsan babu wani outsider da zaki kawo a school dinnan da Zain bai sanshi ba. Shine kadai option dinki idan yaganki da wani dole zai shiga taitayin sa, kuma shi driver ɗinnan na ɗan lokaci ne ai zakiyi playing ɗinsa sannan ki dauka hakan duk cikin aikin sa ne"

Kai na ɗaga alamun gamsuwa da shawarar ta muka fito kaman babu wani abu da yake damuna. Da ido suka bimu ganin yanda muka wuce su cikin ko in kula. Ta gefen idona na hango Hanan kaman za tayi bindiga saboda baƙin cikin bata ganni yanda taso ba. Murmushi nayi a zuciyata nace yanzu zamu fara buga wasan nida ke.


***


Kaman yanda nace masa kuwa karfe huɗu tayi masa a harabar school ɗin tamu. Tunda na fito daga class nake kallanshi ina tunanin ta inda zan fara plan din nawa. Har yanzu kayan shi na safe ne a jikin shi babu alamun ya yi wanka bare ya chanza kaya. Yatsina fuska nayi na cigaba da kallanshi.

Kafin na karasa gurin nashi na hango Hanan tare da Zain suna ƙoƙarin shiga motar shi. Saurin ɗauke kai nayi kaman ban gansu ba. Inajin yanda idanuwan Zain ke bina da kallo. A zuciya ta na ƙara ƙudurta niya ta na ganin nima na rama abinda ya yi min.

Da murmushi na ƙarasa gurin sabon drive ɗina da bansan sunan shi ba. Mamaki kwance kan fuskarsa yake kallo na dan sai yake ganin kaman idanuwansa ne ke masa gizo. Ban bari ya fuskanci komai ba na miƙa masa jakata tare da bude bayan motar na shiga. Tunda muka dauƙi hanya na kafe shi da ido ina tunanin maganan Ninah. Tabbas idan yaji hutu ba ƙaramin mutum bane kaman yanda tace amma ni yanzu bashi ne a gaba na ba, domin kyan Zain ya rufemin ido da yasa nake ganin duk wani namiji yabi bayansa.

Toh kuda muka koma gida ma banjira ya buɗe min motar ba na fito tare da yi masa murmushi na wuce ciki. Da kallo ya bini cikin matsanancin mamaki. Ɗaki nayi kai tsaye na watsa ruwa da ɗauro alwala. Ban fito ba saida nayi salla sannan na shirya cikin riga da wando, wando mai kamar buje. A falo na samu Innati rike da charbi tana ja. Nufer ta nayi na faɗa jikinta cikin shagwaɓa. Kai ta girgiza tana murmushi tace

"wannan shagwaɓa taki Auta,tashi maza kici abinci yau cimarki ce nasa akayi miki"

Ta ƙwalawa Abu kira da takawo min abincin. Da kanta Innati ta bani abinci ina ta zuba mata shagwaɓa yanda naga dama. Abbu ne ya shigo cikin sauri da alama muhimmin abu ne ya dawo dashi dan bai cika dawowa da wuri ba. Dagani har Innati muka bishi da ido. Guri ya samu ya zauna Innati ta yi saurin miƙewa tana masa sannu da zuwa kafin ta shige kitchen dan samo masa abu mai sanyi. Nima tasowa nayi na zauna kusa dashi ina gaisheshi. Kaina ya dafa ya ce " Auta ya ki ka ga sabon direban naki " Naso in ce masa baiyi min ba amma tunawa da nayi da plan ɗina nai suarin cewa

" bashi da matsala Abbu " kai ya jinjina ya cigaba da cewa

" yaron arziki, yana da hankali da nutsuwa. A can main titi na ganshi yana saida ruwa a danja. Bansan me yasa ba duk yaran dake gurin shi kaɗai ido na yakai kansa kuma naji bazan iya barin shi ba tare da na taimaka masa ba. Dana bibiyi rayuwarsa sai na gane ashe maraya ne bashi da uwa bare uba. Can gidan marayun da yake zaune suka gayamin irin halayan kirkin da yake dasu. Yana ƙoƙarin ganin ya samu na kanshi dan ya taimaka wa duk wani dake gurin. Sunce min babu irin aikin da baiyi ba, ƙwadago, gini ne, wanki,garuwa da sauran su. Ko kaɗan bashi da girman kai akan neman na kansa har sharar kwata ya yi. Wannan dalilin yasa naji yaron ya kara kwanta min a rai naso nayi Adopt nashi, amma shi sai ya nuna ya wuce matsayin da zaije gidan wasu a matsayin ɗa tunda ya doshi shekara ashirin harda tara. Nayi nayi yaƙi amin cewa yace indai taimakon asa nake son yi toh ya yarda na bashi aiki ko wane irine zaiyi."

Innati ce ta fito ɗauke da faranti mai kyan gaske da jug na ruwa da lemo mai sanyi a kai. Gabanshi ta ajiye ta zuba masa sannan ta miƙa masa itama ta samu guri ta zauna kusa dashi. Wani irin kallan so naga Abbu na ya yiwa Innati da ya bata kunya ta sunkuyar da kai katsa. Murmushi nake ina kallansu. Soyayyar Abbu na da Innati na kullum sabuwa take dawowa. A kullum addu'ata nima Allah ya bani miji da zai so ni kaman yanda Abbuna ke san Innati.

Da murmushi a fuskata nace " Abbu mene sunan shi" ajiye ruwan dake hannunsa ya yi yana kallona sosai da mamaki a fuskarsa yace " wai Auta kina nufin bakisan sunan deriban naki ba " Baki na turo ina kunkuni. Yar dariya Abbu ya yi yace " sunan shi AYAAN, bai gayamin sunan baban shi ba tunda yace shi ma bai sansu ba"

AYAAN na ƙara maimaita sunan cikin zuciyata. Ga sunan nashi mai daɗi amma shi kuma Sam bai dace da sunan ba. Karar wayar Abbu ta katse min tunani na. Inaji Abbu ya ɗaga tare da kiran sunan Alhaji Nura. Shi din Aminin Abbu na ne zan iya cewa kusan tun ƙuruciyata suke tare. Duk da irin wannan shekaru da suka yi tare har ila yau zuciyata ta kasa amincewa dashi na kuma rasa dalili. Sau tari idan na ganshi ko naji suna waya da Abbu sai inji na shiga shakku a kansa da kuma wasi-wasi.

Duk yanda naso naji hirar tasu hakan gagara ya yi dan tashi Abbu ya yi ya fice gaba ɗaya daga falon hakan kuma ya ƙara tabbatar min da magana ce mai muhimmanci.


***


Kaman yanda na tsara cikin satin ba ƙaramin sakewa Ayaan fuska nayi ba Ninah na ƙara bani shawara yadda zan kara jan hankalin sa duk sanda muka haɗu. Tun yana mamaki da tsoro har ya saki jiki daniz . Ba ƙaramin janshi jikina nayi ba dan wani lokacin kullum da yamma nake fitowa na same shi a nan ƙofar ɗakin maigadi suna hira na zauna nima muyita hira dashi. Na lura hakan ba karamin daɗi yake masa ba dan har takai idan ban fito ba zaita zirga- zirga a bakin kofar falon mu.

Ni kaina ina mamakin yanda muka shaƙu dashi haka cikin ɗan ƙanƙanin lokaci duk da ni da manufa nake yin komai. Abbu yafi kowa jindaɗin yanda yaga na sakewa Ayaan dan na lura soyayyace daga Allah ya ɗora masa ta san shi.

Toh yau tunda muka ɗauki hanyar makaranta na lura da irin kallan da yake min . Murmushi ne yaso kubcemin ganin haƙata ta cinma ruwa. Littafin dake hannuna na ajiye ina kallansa ta mirror da yake kallona a fakaice.

Nace " Wai menene ka ke ta kallo na haka? Ko kana da magana ne?". Hannu ya cusa cikin sumar kanshi da take a

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment