Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mun kyale ki ki fito da wani amma ba wannan yaron ba dan nayi bincike a kansa ba yaron arziƙi bane saboda haka akwai yaron Alhaji Nura dake can Oxford yana karatu. Mun yanke shawarar zamu haɗaki dashi dan batun yau Nura ke gayamin cewar yana san mu ƙara kulla zumuncin mu ta hanyar haɗaku aure ba. in kinsan wata ai baki san wata ba. Wannan babu fashi ko mutuwa za kiyi sai anyi auren nan. Tashi ki bani guri shasha kawai."
Da matsanancin kuka na tashi nayi ɗaki na.

Toh zan iya cewa bayan tafiyar Ayaan abubuwa sun cigiba da tafiya kaman da. Daga Abbu har Innati babu wanda ya ƙaramin maganan sa dalilin da yasa maganan yaran Alhaji Nura shima na tattara na watsar saboda ban ɗauki abun serious ba. Tsakani da Zain kuwa sai ma abinda yafi na da. Soyayya muke sosai dashi babu wanda bai san hakan ba. Duk ƴan matan da suke kawo masa hara cin ubansu nake har ita Hanan ɗin da taga babu sarki sai Allah ta hakura da nufinta naganin ta kwaceshi dan yanzu wani sabon wulakanci nake na rashin mutumci.

***

Sati biyu yau da barin Ayaan gidanmu a kuma yaune juma'a Abbu ya tashi da wani irin matsanancin ciwon ciki cikin dare Innati ta tasheni mukayi asibiti dashi cikin matsanan cin tashin hankali dan bazai yiwu mu jira family Doc ɗinmu yazo ba. Cikin gaggawa sukayi emergency dashi. Har wajen bakwai na safe basu fito da Abbu ba a wannan lokacin dagani har Innati munyi mugun laushi idanuwa sunyi luhu-luhu saboda kuka tun Innati tana rarrashina har itama ta kama kukan muka haɗu muna tayi nida ita.

A haka su Baba salmanu suka riske mu. Faɗa ya rufe mu dashi danme zamu zauna muna kuka? ciwo ai ba mutuwa bane. Toh zuwansu Baba salmanu da matan su muka ɗan samu sassaucin tashin hankalin da muka shiga. Muna nan a zaune shiru ɗaya daga cikin likitocin ya fito da sauri yana ina familyn Alhaji Maleek. Da azama muka miƙe gaba ɗayan mu mukayi kanshi. Saurin juyawa ya yi yana cewa mu biyo shi. Gaba ɗaya muka bishi kaman zamu kifa saboda sauri. Ɗakin hutun da suka kwantar da Abbu muka shiga yana kwance kaman gawa sun ɗora masa oxygen. Wani irin kuka muka fashe dashi dagani har Innati mukayi kanshi. Rungume Abbu nayi ina matsanan cin kuka ina kiranshi. Hannunshi naji a kaina yana shafawa cikin halin ciwo.

Ɗagowa nayi ina kallanshi fuskata jage-jege da hawaye da majina. oxygen ɗin dake fuskarsa ya sauke yana jan numfashi a wahalce ya fara magana da kyar " ki kula da kan ki Auta. Ina sanki a koda yaushe" Innati ya kalla dake gefe a tsaye ta toshe baki cikin matsanan cin kuka. Murmushi ya yi mata cike da so kafin ya maida hankali kan ragowar mutanen ɗakin yana kallansu ɗaya bayan ɗaya. Baba salmanu ne naga ya matso kusa da Abbu ya kama hannushi hawaye nabin fuskarsa ya fara karanta masa kalman shahada. Da murmushi a fukar Abbu na ya fara maimatawa yana kallo na. Banyi tunanin komai ba na ɗauka addu'a ce suke masa dan samun sauki. Amma sai naji Innati ta ƙara fashewa da wani irin kuka ɗakin gaba ɗaya ya ɗauka da koke- koke.

Gaba ɗaya likitocin sukayi kan Abbu da ya daina motsi amma fuskarsa ɗauke da murmushi. Ina kallo suna ta koƙarin danna masa ƙirji na ɗan wasu lokuta kafin su juyu kanmu suna bada hakuri. Wani irin zama nayi daɓar a ƙasa kaman mutum mutumi. Jina da gani na gaba ɗaya suka ɗauke na daina fuskantar me ake yi.

Har akayi wa Abbu sutura aka kaishi ɗakinshi na gaskiya bansan wake kaina ba . Da ido kawai nake bin mutane bana fuskantar duk wani abu dake wakana. Babu iya bakin ƙoƙarin dasu Baba Salmanu da likitoci basayi a kaina dan ganin na fita daga cikin wannan depression ɗin dana shiga. Saboda irin shi ne idan mutum ya shiga babu irin abunda bazai aikata ba zai ta tunani na suicidal .

Har akayi arba'in ɗin Abbu bata sauya zani ba dan wani lokacin har gizo nake gani yana min yana kirana inzo mu tafi. A zabure zan tashi inyi waje a guje ina kiran Abbu yazo mu tafi. Tun ana ganin abun kaman wasa ya fara wuce tunani dan ko barci banayi . Haka zan kwana na wuni a zaune babu uhm bare uh'um. Toh muna cikin wannan tashin hankalin wani musifar ya ƙara samun mu kusan zan iya cewa shi ne maƙa sudin dawowar hankalina.

Wajen karfe biyu na dare ina zaune kaman koda yaushe Innati a gefe na tana sallah sai matan Baba Salmanu dake barci. Tunda akayi mutuwar suke nan dan Baba salmanu yace baza su tafi su barni cikin wannan halin ba Innati baza ta iya dani ita kaɗai ba dole tana buƙatar taimako. Wata irin ƙara mukaji kaman an fasa bomb. Rabon da naji wani motsi tun ranan mutuwar Abbu sai yanzu da naji wannan ƙarar, ina kallo su Innati suka miƙe tsaye a firgice suna kallon juna cikin tashin hankali . Bakinsu na zubawa ido dake furta innalillahi wa innailaihi raji'un. Bamu farga ba aka bugo ƙofar ɗakin da muke ciki kaman za'a ɓalla. Wasu mutane ne suka shigo jibga-jibga sanye cikin baƙaƙen kaya fuskarsu a rufe. Ga mugayen bindigo da makamai a hannunsu.


Ɗakin suka shigo cikin tsawa suka yi magana da muyi waje. Nidai ina zaune ina binsu da ido Innati tayo kaina dan kamani. Wani cikinsu ya fisgeta suka yi waje da ita. Bansan ya akai ba sai ganina nayi tsaye a tsakiyar falon da suka tutse su Innati dasu Baba salmanu. Babu wanda basu ɗorawa makami a kai ba. Ogan su dake zaune kan kujera na zubawa ido. Ikon Allah kenan. wato duk da cewa ya rufe ido dan ɓadda kama baisa na kasa gane Alhaji Nura ba dake sanye da baƙaken kaya da baƙar face mask.

Fuskantar da ya yi naso na ganeshi ya taso cikin sauri ya fisgoni na zube a ƙasa. Jana ya yi kaman kayan wanki ya mayar ɗaki ina jin kukan su Innati ya ƙarasa tsanan ta Baba salmanu dake kwance a ƙasa sun daureshi ya hau basu haƙuri cikin tashin hankali da suyiwa Allah kar su cutar dani . jefar dani ya yi a tsaƙar ɗakin ya durkusa kusa dani. Fuskar da yasa ya cire yana kallo na sai uban huci yake.

"ke dan ubanki kina cikin halin marasa hankalin ma saida ki ka gane ni. ? Kinga nan " sharɓeɓeyar addar dake hannunsa ya kawo saitin fuskata " ki ka kuskura ki ka sanarwa da wani cewa da sa hannuna cikin fashin nan da akayi sai kinci ubanki. Zansa a gama da Uwarki da ta rage miki a yanzu ba kuma zan bari ta tafi cikin sauki ba. Kinga waɗannan mutanen da ki ka gani kaf ɗinsu zansa su yaga mata rigar mutunci kafin su kashemin ita. Duk wani motsi naki zai kasance a kan ido na ne a yanzu zan barku da ranku ne saboda Mahaifinku dan babu abinda ya yi min kuma hakan bai hanani san dukiyarsa ba da yake shirin mallaka miki ita, saboda haka duk ranan da ki ka kuskura ki ka sanarwa da wani abunda ya faru sai kinyi ban kwana da duk wani naki daya rage miki a duniya. Kinji abinda nace ?"

Bansan cewa kuka nake ba sai danaji danshin ruwa yana ɗiga kan hannuna. Tunda Abbu ya mutu kukan da ake ta so nayi banyi shi ba sai yau. Menene rayuwannan ne gaba ɗaya? Ashe Allah ne ya yi ikon sa da yasa tunda na taso tsawon shekaruna ban taɓa yarda da mutumin nan ba. Ka yarda da mutum ya cuce ka. Wane irin yarda ne Abbu baiyi da mutumin nan ba har ya faɗi ya mutu? Ashe shi da fuska biyu yake zaune dashi. Allah wadan mutane masu hali irin nasa. Kuka ne ya kubce min mai ƙarfin gaske ina dukan ƙirjina saboda wani irin ciwo da naji zuciyata tana min. Muryar Innati na jiyo cikin kuka tana kirana da alama sunji kukan da nake dan haka sukayi tunanin ko wani abun yakemin.

Wuƙar ya kara kaɗan min kan fuskata da bindigar shi ya ce " kinji abunda na gaya miki ko? in har ki ka kuskura ki ka sanar wa wani ƙudurin dana ɗauka na ƙyale ku zan fasa na kuma sa yanzu gaɓa ɗaya su kashe min kowa na gidan nan a barki ke ƙadai zuciyar ki ta buga. Ƴan fashi ne su basu da wani imani umarni kawai zan basu su cika aiki" Kaina nake girgizawa alamun babu wanda zan gayawa. Mugun murmushi ya yi ya miƙe tsaye yana maida fuskarsa.

Kaman yanda ya shigo dani yanzu ma haka ya kwasheni a ƙasa ya yi waje dani. Kusa da Innati ya yi jefa dani na rarrafa jikinta ina kuka kaman raina zai fita ta rungume ni sosai tana kuka mara sauti.

Munaji muna gani suka kwashe komai na gidan tun daga kan takardun gida, motoci, filaye,kamfanoni. Basu barmu da komai ba suka koromu daga gidan ko cokali basu bari mun ɗauka ba.

Koda ƴan sanda ma suka zo kwasarmu sukayi zuwa station . Baba Salmanu yace babu amfanin zuwa tunda ba'asan kosu waye ba, sun godewa Allah da yasa babu wanda suka cutar bayan sun tabbatar da babu abinda ya yimin dan haka muka koma gidan shi a can kubuwa. Anyi iya binciki dan gano waɗannan mutane amma abu yaci tura dan washegari da akaje gidan ma sun garƙameshi da wani irin kwaɗo mai shegen security. Saboda haka ne yan sanda suka ce komawar mu gidan zai iya zama matsala babba tunda suma sun kasa binciko mutanen bare a san daga inda suke ko wanda ya turo su, idan har muka kuma za su iya dawowa a ko wane lokacin dan ganin sun cimma manufar su .Ni kaɗai nasan ko wake da sa hannu a wannan abun amma nayi alwashin babu wanda zaisan hakan indai hakan na nufin kare Innati dasu Baba Salmanu daga mugun nufin Alhaji Nura. Sosai nake taka tsantsan dan sai nake ganin kaman yanda yace ɗin yana bibiyar rayuwata.

Rayuwa tayi mana tsanani babu ranan da zata fito ta faɗi banyi kukan rashin Abbu na ba. Dole mukayi hakuri muka fawwala Allah dan su kansu jami'an tsaron sun fara gajiya da case ɗin anyi bincike iya bincike babu nasara. Tunda wannan abu ya faru sau ɗaya Ninah tazo yimin jaje ban ƙara ganin taba har ila yau. Shima Zain ban kuma ganin saba amma naji Innati tace yazo dubani bayan mutuwar Abbu lokacin bana gane mutane. Nayi mamakin yanda Ninah ta juya min baya a lokacin da nake bukatar ta, gashi babu waya da zan kirata naji dalilin da yasa ta daina nemana saboda ita kanta makarantar dole na barta dan babu halin da zan cigaba da zuwa tafi karfina a yanzu.

Baba Salmanu yana iya kacin bakin ƙoƙarinsa a kanmu duk da shima ba wani ƙarfi ne dashi ba. Dalilin da yasa Innati ta saida sarƙar gwal dinta dake wuyanta tun ranan da Abbu ya kawo mata ita daga dubai. Kuma Allah cikin ikon sa basu ga sarƙar ba ranan da sukayi mana fashi. Karamin gida tasa Baba Salmanu ya samo mana wanda muke ciki yanzu. Yaso hanata tafiya dani Innati tayi ta rokon ya bar mata ni tana gani na ko ta dinga jindadin da ɗebe kewar Abbu. Toh zan iya cewa Baba Salmanu ne ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen ganin na zana Waec da Neco nan makarantar gomnati da ƴaƴansa suke zuwa. Na samu kuma da kyar nayi jami'a yau naje gobe bazan jeba saboda halin rayuwa. Zan iya cewa Alhamdulillah na fito da sakamako mai kyau sai dai aikin ya yi min wahalar samu duk irin faɗi tashin da nake akai saboda rayuwar yanzu ta zama komai sai kana da hanya.
tunda wannan abun ya faru nake jin kunyar ranan da zan haɗu da Ayaan. Na kara yarda rayuwar yanzu ba koma bace. Allah ke bayarwa kuma ke hanawa. Baya kuma barin wani dan wani yaji dadi .Yau ina mutanen dana ɗauka sune mutane duk sun gujeni ko a hanya bamu haɗuwa dasu.


𝐏𝐑𝐄𝐒𝐄𝐍𝐓 𝐃𝐀𝐘(𝐂𝐈𝐆𝐀𝐁𝐀𝐍 𝐋𝐀𝐁𝐀𝐑𝐈)

Next page 👉


Tohhhhhh fa.
Kuzo mu taya Neehal Kuka.
o(╥﹏╥)o



E 13-14



Washegari da safe kasa tashi nayi don na shirya. Gaba ɗaya naji aikin ya fice min a kai. Tunda nayi sallan asuba nake kwance kan dadduma nayi zurfi cikin tunani har gari ya waye ban sani ba. Muryar Innati naji a kaina tana cewa " Auta lafiya ki ke kwance har yanzu karfe bakwai banga alamun kina da niyar zuwa aiki ba?" Idanuwa dake a rufe na buɗe ina kallan Innati dake tsaye a kaina tana kallo na cikin damuwa. Tunani nake ko in gaya mata naga Ayaan da matsayin da Allah ya bashi yanzu?.Amma sai nayi deciding akan hakan .Yunƙurawa nayi na miƙe zauna cikin ɗan yaƙe nace da Innati " Barci ne ya kwashe ni bansan gari ya waye ba"

"toh maza ki tashi ki shirya kar ki makara" .Ban musa ba nayi waje. Tsintsiya na ɗauka da niyar shara Innati tayi saurin katse ni " Auta me za kiyi ne? Ajiye tsintsiyar nan maza kije ki shirya kinsan cewa tafiyar ce ba kaɗan ba ko kina so ne daga fara aikin naki ki fara basu matsalar da zasu kore ki?" Badan naso ba na ajiye tsintsiyar na shige banɗaki. Saboda yanda garin yake yazu lokacin zafi yasa shi kanshi ruwan ɗumi ne dashi. A gurguje na fito na shirya cikin rigata dogowa da bancika sata ba sai in fitace zanyi mai muhimmanci. Doguwar riga ce maroon ƙirar turkey da Abbu na ya kawo min ita daga saudiya. Gashin kaina na tufke kaman gammo nayi roll da mayafin rigar. Kayan suna masifar yimin kyau duk sanda na sasu. Innati ce ta shigo ɗakin rike da kofin shayi da plate ɗin abinci. Ɗumamen towon shinkafa ne da miyar ɗanyan kuɓewa sai tururi yake.

Ajiye wa tayi gabana tana cewa "maza zauna kici abinci kiyi harama ki tafi lokaci yana tafiya "

Da sauri kuwa na zaune na take tuwon nan tunda ta shigo dashi yawuna ya tsinke. Wato Innati na badai iya girki ba. Inta sarrafa maka abinci sai kaji kaman ka haɗa da kwanon ka cinye. A gurguje na gama karyawa na fito ina yiwa Innati salma ta bini da Addu'a. A ƙofar gida mukaci karo da Ramlat tana ƙoƙarin shiga. Naji daɗin ganin ta kuwa dan jiya gajiya bata bari na shiga ba. Da yake sauri nake gaisawa kawai muka yi da niyar mun haɗu da yamma.

Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi ina kallon ƙofar tafkeken ginin dake gabana bayan na sallami ɗan sahun daya kawo ni. Takawa nayi gaba security dake tsoron kofar , yau murmushi ya yi min ya buɗemin ƙofar da kansa da alama ya gane ni. Nima murmushin na mayar masa na shige ina masa godiya. Kai tsaye nayi lifter da zata sada ni da office ɗina bayan na danna button floor ɗinmu. Ƴan mintina kaɗan lifter ta fara aiki sai kuma naji ta tsaya ƙofar ta buɗe. Zare ido nayi ina kallan Ayaan dake tsaye hannunsa rike da wasu files yana dubawa ba. Da alama hankalinsa ya yi nisa akan file ɗin dan bai lura dani ba ya shigo cikin lifter ɗin . Matsawa na ƙarayi can gefe kaman na shige bango ina rokon Allah yasa yanda bai lura dani a ciki ba har ya fita bai kula ba. Duk da tsoro da fargabar da nake bai hanani lumshe ido ba saboda kamshin turaren sa mai shege daɗi da sanyi tamkar wood and rains. Ta kasan ido nake kallansa yana sanye da wata grey coat tayi masifar yi masa Kyau. Gashin kansa a jike da alama bai dade dayin wanka ba. Yawu na haɗiye ina cigaba da kallan sa zuciyata na harbawa da masifar gudu.

Babu zato ya ɗago kansa idanuwan sa suka fada cikin nawa. A take naga ya haɗe fuska wannan calm expression dake fuskarsa ya kau. Rufe file ɗin ya yi ya matsa can gefe kaman wanda yaga wani mugun abu. Jiki na ya ƙara yin sanyi na sunkuyar da kaina katsa hawaye sun cika ido na. Lifter ɗin na tsayawa ya yi saurin ficewa daga ciki na bishi da kallo. A sanyaye nayi magana a fili " Allah gani gare ka" Cikin sauri na fito na rufa masa baya dai-dai Eman ta fito ta cikin private elevator ɗinsu. Da mamaki naga tana kallan Ayaan da alama itama tana tunanin abinda yasa shi bin normal lifter ta staff bai bi tasu ba.

Yau floor ɗin namu a cike yake da ma'aikata da alama aiki ake na musamman. Tsayawa ya yi suna magana da Eman nayi saurin wuce su dan shiga nawa office ɗin. Kasancewa ta dashi yanzu yasa ni cikin wani yanayi jikina gaba ɗaya babu inda baya rawa.

Wani irin mugun harɗewa nayi na kuwa yi muguwar faɗuwa. ƴar ƙara na saki saboda gwiwar hannuna da kafata da suka yi mugun buguwa a ƙasa. Wato badan ciwon da nakeji ba zafin ciwon ya ɗauke min hankali da babu abunda zaisa ban mutu a gurin ba saboda embrassment. Gurin gaba ɗaya ya ɗauki shiru idan kowa yana kaina babu wanda ya yi yunƙurin taimaka min. Muryar Eman ce ta katse shirun ta nufo ni cikin sauri tana "subhanallahi sannu Neehal Allah yasa ba kiji mugun ciwo ba". kamani take ƙoƙarin yi danta miƙar dani tsaye, bansan me yasa ba nake wishing ya taimaka min amma shi sai naga kaman faɗuwar tawa ta yi masa daɗi saboda wani kallon da naga yana min inexplicable emotion kwance kan fuskar sa. Kaman wanda faɗuwar tawa ta bashi wani strange comfort ne. ƙwalla naji sun cika idona kuka yana neman kubce min Allah ya taimake ni na haɗi ye shi.

Kanshi kawai ya girgiza yazo ya wuce mu yabar Eman nata ƙoƙarin kamani dan na miƙe. Ƙoƙarin da naga Eman nata yi ne yasa na daure ciwon da ƙafata take na miƙe tsaye ina mata murmushin ƙarfin hali nace mata na gode. Sannu ta ƙaramin ta juya tana kallan ma'aikan gurin da har yanzu suke tsaye kaman sunga tv. Tsawa ta daka musu "Kallan me ku ke haka? Baku taba ganin mutum ya faɗi bane?" sum-sum kowa ya kama aikin sa . Juyuwa tayi kaina tana ƙaramin sannu kafin ta wuce office ɗinshi. Da ɗingishi na ƙarasa office ɗina. Ina shiga kuwa na fashe da kukan da nake ta rikewa.


***


"Me ki ke cikin office yanzu lokacin lunch break"

murya Emana ta daki kunne. Da suari na juya inda naji muryar tana tsaye jikin ƙofata bata shigo ba. Rufe file ɗin da nake dubawa nayi na miƙe tsaye ina kallanta nace " Ma'am "

"ba nace ki dinga kirana da Eman ba?" Ta tambaya tana min murmushi.

"Yes Eman, dama ina karanta files ne na client kawai dan ƙara gane aikin sosai" Inaji ta sauke ajiyar zuciya ta shigo cikin office ɗin nawa. "Ya hannun naki da ƙafar basa miki ciwo dai ko?" Murmushi na yi sosai naji ina matuƙar santa saboda kulawan da take bani. Amma kuma ina cikin fargabar ranan d zata gane wace ni duk da ban sani ba ko ya gaya mata abunda nayi masa.

Nace "ba wani ciwo bane sosai ƴar buguwa ce kawai"

"Yauwa to saboda bamu aiki lokacin break lunch, wannan dokace ta kamfani, let's go" tace tana yafatoni da hannu. Cikin inda- inda nace

"Amma Ma'am, ina..umm Eman.." kafin in ƙarasa abunda nake son faɗi ta yi saurin ficewa dan kar ma taji. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi nabi bayanta duk da ina jin zafin kafata dake zugi. Office ɗint na shiga. mutum biyu na tarar a zaune ,muna haɗa ido da Ayaan kirjina ya yi mummunan bugawa. Ɗayan da suke tare fuskarsa ɗauke take da murmushi saɓanin Ayaan da yana ganina ya mugun haɗe fuska.

Nuna shi Eman tayi tace "Neehal wannan Haisam sunan sa ƙaramin kanine ne shima dan abinda ya yi Ayaan shi ya yisa aminan juna kenan. Shi ɗin brother ne from different Mother" ta ƙasara maganan cike da tsokana fuskarta ɗauke da katon grinning. Daga Haisam har Ayaan a tare suka yi groaning Ayaan yace "your just older with five minutes , stop bragging about it, is not like kin bani shekara biyar" Gwalo tayi masa yaƙara groaning yana rolling idanuwasa sama. A take naji na zama wata bare cikin su. I wish , i wish..

Haisam ne ya katse min tunanin "Neehal, barka da zuwa A&E naji labarin ki gurin Eman, Nice too meet you" ɗan yake nayi nace masa na gode. Kujerar da yake kai ya tashi ya bani. Kaman bazan zauna ba na zauna a ɗaɗare. Abinci ya ɗauko ya ajiye gabana da murmushi a fuskarsa yace "bismillah." Saida na kalli Eman ta yi min murmushi sannan na fara cin abincin ban yarda na kalli Ayaan dake zaune a gefe na ba.

Inajin Eman da Haisam suna ta zuba musu tamkar dai yanda siblings suke. Sai kayi tunanin da gaske shi ne ƙanin nata. A fakaice na kalli Ayaan dake kallan su kaman baya gurin. Kaman yasan kallansa nake ya juyu ya kalle ni. Haisam ya kalla ya ƙara kallo na kafin ya ɗan sunkuyo inda nake yace

" is like you hit a jackpot, gashi nan rich and handsome kaman yanda ki ke so" ya ƙarasa da mugun smirking .

Hawaye masu zafi suka biyo kuncina nakasa jurewa cikin sauri na tashi zan fice Eman ta ce " ina zaki baki gama cin abincin ba?"

Murya ta na rawa nace mata " zan shiga banɗaki ne " Ɗan kallo na tayi kaman ta fuskanci wani abu.
"Ki tafi da abincin naki kya ƙarasa a office ɗinki" har cikin raina naji daɗin hakan cikin sauri kuwa na ɗauki abincin na fice daga office ɗin ina jin idansu a bayana.


E 15-16.



Da wuri na gama aiki na yau na fara haramar tafiya gida saboda Eman ta bani damar duk sanda na gama zan iya tafiya. Wajen uku da rabi na fito na samu ɗan sahu. Gaba daya ɗan chanjin da yake hannu ba baifi dubu ɗaya ba Allah ya taimake ni ya kawo ni a ɗari huɗu. Gobe bansan yanda zanyi da kuɗin motar dawo ba amma zan tambayi Eman ko zai yiwu ta fara bani Allowance. A tsakar gida na tadda Innati tana jin mutuniyar ta ta wato redio.

"Wash Innati na gaji walahi"

"Har kin dawo da wuri haka Auta?"

Da yar shagwaɓa nace " eh walahi Innati yau na tashi da wuri" takarmin ƙafata na cire ina duba idon ƙafata da ya yi ja'a sosai, sai yanzu nake jin ciwon ƙafar. Cikin sauri Innati ta tashi zaune ta riƙe ƙafar tana cewa " subhanallahi Auta, me ya sami ƙafar ki ne haka?"

"Gurɗuwa nayi Innati" cike da damuwa ta rike ƙafar tana dubuwa "sannu ,ki huta sai muje gurin mai gyara ya duba miki" Da sauri na girgiza mata kai nace " A'a Innati baya min ciwo fa, bugewa ce kawai nayi idan na gasa da ruwan zafi zai daina " Tasanni da mugun tsoro, na tsani abunda zai taɓamin lafiyar jiki.

Kai ta girgiza "Shikenan toh kije kiyi sallah kici abinci bari na dafa ruwan zafin kizo na gasa miki ƙafar" .


***

A shagwaɓe na riƙe hannun Innati dake danna min ƙafa da ruwan zafi hawaye sai gudu suke a fuskata. Tun ɗazu take gasamin ƙafar duk yanda naso na kwace ta hana ,tun inajin zafi har na daina amma fa nasha kuka ba kaɗan ba. Shigowar Ramlat yasa Innati kyale ni ba kuma ƙaramin daɗin ƙafar naji ba. Ɗaki muka shige nida Ramlat bayan sun gaisa. Kallo ɗaya nayi mata na hango damuwa a tattare da ita. Ƙafaɗarta na dafa nace

"Lafiya dai meya faru na ganki cikin damuwa haka?"

Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta juyu tana kallo na. Hawaye naga suna bin kuncin ta. Hankalina ya masifar tashi tuni na manta da tawa damuwar da nake ciki. Hankali a tashe na rumgumeta ina ɗan buga bayanta. Sai da tayi kuka sosai sannan ta janye

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment