Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

jiki tana share hawaye tace

" Ina cikin damuwa mai tsanani Neehal. Yau na haɗu da kaddara ta da ba lallai na ƙara ganin sa ba"

Mamaki ne ya kamani dan na kasa gane inda magananta ta dosa. Saida ta share majina ta cigaba da cewa

" dazu zan tafi gurin aiki naje tsallaka titi mota ta kusa buge ni Allah ya taimake ni na sha da ƙyar, da masifa naje ɓangaren direba ina buga glass dan koma waye ya fito tunda ya yi shirin kaini lahira ban shirya ba. Lokacin da ya fito ƙirjina ya yi mugun bugawa na kasa aiwatar da zagin da nayi niyar yi masa. Wannan Kalman da ake cewa love at first sight ne don na kamu da son wanda bansan shi ba bare in san in da zan ganshi. Har ya gama bani haƙuri ya tafi bana cikin hayyaci na sai ƙarar horn daya firgita ni na farga da ya tafi. "

Hannuna ta riko hawaye nabin fuskarta tace " Zuciyata ciwo take min, inaji a jikina sanshi zai zama ajalina Neehal. Walahi na kamu da mugun san shi gashi bansan inda zan ƙara ganin shi ba, wata kila bazan ƙara ganin shiba har nabar duniyar nan" Da kuka sosai ta ƙarasa maganan nima kukan na fashe dashi saboda mugun tausayi data bani. Toh dama ko wane bawa da irin tashi ƙaddarar,ita kuma ta ta ƙaddarar kenan san wanda baisan da zaman ta a duniyar ba. Rumgume ta nayi sosai mukayi ta kuka babu mai lallashin wani. Da ƙyar muka iya haƙura mukayi shiru saboda kiran sallan magriba da ake. Saida mukayi sallah mukaci abinci sannan ta yiwa Innati salma ta tafi.

Bayan tafiyar ta zama nayi kusa da Innati ina tunanin maganan da mukayi da Ramlat. Ko wane ne ita kuma Allah ya jarrabeta da san shi haka?. Naci alwashin inshaAllahu zan dinga sanya ta cikin addu'a idan shidin Alkhairin ta ne Allah ya hada fuskokinsu shima ya so ta kaman yanda take san shi ,idan kuma ba Alkhairin ta bane ya musanya mata da mafi Alkhairin sa.


***

A hanzarce na shige kamfani saboda yau na kusa makara dan ban fito ba sai karfe takwas saura, yau makara nayi ban tashi da wuri ba itama Innati saboda raba daren da tayi tana nafilfilu bayan tayi sallan asuba barci mai nauyi ya dauƙe ta duk muka makara. Cikin sauri na shige lifter ina ƙoƙarin danna floor din da nake sai gashi ya shigo babu zato . A ɗan firgice naja baya dan banyi zaton ganin shi ba na kuwa tafi gaba ɗaya zan kifa ta baya saboda harɗewa nayi. Bansan ya akayi ba sai jina nayi kwance a kirjinshi ina shakar daddaɗan kamshin turaren sa.

A mugun hankali na buɗe ido ina kallanshi ya zuba min ido fuskarsa babu wani emotion a tattare da ita. Sosai nake karewa kyakkyawar fuskarsa da sajenshi ya kewaye kallo. Yanzu na hango tsantsan kyan da Ninah ke gayamin. Cikin sauri na janye jikina daga nashi murya ta na rawa nace

"Uhm...kayi hakuri don Allah "

"Kin manta yanda ake tafiya ne? " yace cikin fushi . Kai na girgiza masa jikina ya yi sanyi nace " kayi hakuri ciwon ƙafata na fama ban sani ba" saurin kallon ƙafar tawa ya yi ya maza ya ɗauke kai cikin basar wa yace

"Next time ki dinga tafiya da ido a buɗe."

Kaina na sunkuyar bance masa komai ba. Ina mamakin dalilin da yasa yake biyo wannan lifter ɗin ba tasu ba. Duk da irin bakar maganan da ya gayamin samun kaina nayi cikin farin ciki ina hasko yanda ya yi saurin tare ni na faɗa jikinsa bai bari yau na faɗi a ƙasa ba. Ta kasan ido nake kallan sa ya juyamin baya yana danna waya kaman babu kowa a tare dashi. Lifter na buɗewa kuwa ya fice babu ko waiwaye.

Wajen azahar Eman ta shigo office ɗina rike da wasu takardu da alama sauri take cikin sauri tace " ki dubasu do Allah client ne daga US kiyi accessing ɗinsu ki kaiwa Ayaan please " ƙoƙarin ficewa take nayi saurin tare ta ina so na yi mata maganan Allowance ɗina. A gogon hannunta ta kalla tana cewa

" yanzu ina da important meeting idan na dawo zan kira ki sai ki gayamin koma mene ki ke son faɗi idan kuma urgent abu ne za ki iya gayawa Ayaan , after all his the President of this place" ficewa tayi cikin sauri na saki ajiyar zuciya. Bana san abunda zai sa yaji wannan problem ɗin nawa dan bana so ya yi taking pity a kaina. Ficewa nayi nima na nufi nashi office ɗin ƙirjina na bugu. saida na kwankwasa ƙofar kafin na buɗe bayan ya bada iznin shiga. Kaman koda yaushe dai yauma aiki ne baje a gabanshi. Bansan me yasa ba yana san cire botiran gaban rigar sa ko dan yaga hakan is very attractive ne? . Yawu na haɗiye dan ɗagowa ya yi ya zuba bin tsumanmun idansa da suke a lumshe kaman maijin barci.

Muryata na rawa kai gaba ɗaya jikina rawa yake cikin in-ina nace masa " Files ne Eman tace na kawo maka na mutanen US"

"stuttering doesn't sound really professional ,Miss Neehal" kunya ce ta kamani kumatu na ya yi jaa (blushing) na borin kunya.

"Kayi hakuri " nace masa ina ƙoƙarin ficewa a office ɗin idona ya kai kan faffaɗan kirjinshi dake buɗe sai shining ya ke. Tsintar kaina nayi ina waigen shi har ina neman faɗuwa duk da kuwa shi ma bawai ya daina kallo na bane. Ai kuwa nayi mugun karo da ƙofa . chak na tsaya ina kallan ƙofar hannuna kan goshi na dan na kasa wani kwakkwaran motsi. Ji nayi kaman ƙasar gurin ta tsage na shige ciki. Ban kuskura na juya ba bare naga yanayin sa nayi saurin buɗe ƙofar cikin sauri na fice harda ɗan gudu na.

Ƙofar ya zubawa ido bayan fitar ta kafin ya saki wata ƴar dariya yace " Nature doesn't change that easily , kaman miciji ki ke ,yana cikin instincts ɗin ki kai harbi a ko wane lokaci. Dan haka i will not trust you no matter what" ( Toh fa)


***

Toh kaman yanda Eman ta ce zata nemeni. Wajen la'asar ta kirani ta landline nazo office ɗinta. Gaba ɗaya na shirya na fito da niyar tafiya gida tunda na gama aiki na. Banyi tunanin ganin Haisam da Ayaan zaune cikin office ɗin nata ba. Banso hakan ba dan bana san yaji halin da nake ciki. Kujerar data nuna min na zauna ina fusknatar.

"Yauwa Neehal kince kina san magana dani?"

Ayaan na kalla dake danna waya kaman baisan da zama a gurin ba. Muryata na raw nace " Eh dama..dama.. nace ko ...ko zaki fara bani allowance ,ina bukatar kudin ne"

Shiru ne ya ɗan ratsa tsakanin mu har shi dake danna waya ya ɗago yana kallo na. Kai Eman ta jinjina " amma yaushe ki ka fara aikin da ki ke son Allowance?,Neehal, dokarmu bamu bada allowance sai in mutum ya kasance yana da wani kwakkwaran uzuri mai ƙarfi ko munga irin kwazon da mutum ya yi gurin aikin sa. Tabbas kin fara nuna kwazo gurin aiki duk da baki daɗe da farawa ba, amma ina son insan dalilin da yasa ki ke san Allowance tun yanzu."

Kai na sunkuyar ƙasa cikin sanyin murya nace " Ina da uzuri ne mai girma a gabana kuma bayan hakan dole in tanadi kuɗin motar da zan dinga zuwa saboda bani dashi"

"Kar kice na dame ki da tambaya, daga ina ki ke zuwa?,ba cikin abuja ki ke ba"

kai na girgiza na ce mata " Daga suleja nake zuwa" jinjin kai ta ƙara yi cikin mamaki .ta ƙasan ido nake kallan Ayaan daya zuba min ido fuskarsa ɗauke da tarin tambayoyin da ban shirya amsa su a yanzu.

"Amma in baza ki damu ba ko zaki ƙaramin briefing background ɗinki"

"sunana Neehal Maleek, mahaifina ya rasu shekara shida da suka wuce, muna zaune unguwar suleja nida Innati na" kai ta jinjina tana ɗan wasu yan rubuce-rubuce a takarda. Ban kalli Ayaan ba bare nasan yanayin da ya shiga na mutuwar Abbu da yaji amma ina jin yanda idansa gefen fuskata. Drawer ta ta buɗe ta ɗauko wata yar envlope ta miƙo min tana cewa " yana da kyau ki buɗe account saboda halin rayuwa. " Ƙarɓa nayi ina mata godiya nayi saurin miƙewa na fice daga office ɗin.

Kaman yanda na saba inda nake taran ɗan sahu nan na tsaya ina nema amma yau kaman anyi ruwa an ɗauke babu ko ɗaya. Nakai wajen minti talatin a tsaye ina jira har na fara sarewa na fara takawa da kafa. Lafiyar- yar Black Mercidez ce tasha gabana da take da black tint. Ɗan ja nayi baya ina kallan motar da tunanin wanda yake ciki. Glass ɗin motar aka sauke Haisam ya leko da kansa fuskarsa ɗauke da murmushi. Na lura shi mutum ne ma yawon fara.

"Shigo na rage miki hanya," Girma da mutuncinsa da nake gani yasa ban musa ba na shiga cike da kunya. Sai dai zamana ke da wuya hancina ya shaki daddaɗan turaren Ayaan da a yanzu nayi masifar gane shi. Da mugun sauri na juya bayan mator. Yana kwance a bayan motar kaman mai barci idanuwansa a rufe. Shima Haisam kallan Ayaan ɗin ya yi da yaga na firgita da ganinsa . Murmushi ya yi mai ƙayatarwa ya ce "Dont mind him he won't bite" a kunya ce nayi ƙasa da kaina kirjina na bugu. Toh da kwatance mukaje har ƙofar gida Allah yasa layin namu mota na shiga. Duk yanda Haisam ke jana da hira kasa sakin jiki nayi saboda Ayaan dake kwance a bayan motar. Muna zuwa gida kuwa nayi masa godiya na fito cikin sauri na shige gida.


ZANYI MISSING NAKI MOM SANI 🤧😭😭

༺༻
E 17-18.


Ban shiga gida ba na tsaya a soro ina mai da numfashi. Ƙirjina dake harbawa na dafe na rasa dalilin da yasa duk lokacin dana kasance tare dashi nake samun kaina cikin wannan bugun ƙirjin. Leƙawa nayi ta jikin hudur ƙofa naga ko sun tafi, ga mamaki na sai naga motar tana nan har yanzu basu tafi ba. Sun ɗauki tsawon minti biyu a kofar gida kafin naga motar ta yi rebus ta fice daga layin namu. Ni kuma da shegen gulmar tsiya ina nan tsaye ina leƙen su har saida na daina ganin ƙurar motar. Ajiyar zuciya na sauke mai ƙarfi na fito da envelope ɗin da Eman ta bani na buɗe. Ido na zare ina kallan bandir na dubu ɗai-ɗai har guda biyu a ciki.

Fito da ƙudin nayi ina ƙara juya su cikin mamaki. Toh ai ko kuɗin aikin nawa dubu 80 ne duk wata bai kai dubu ɗari ba, a lissafe dubu dari biyu kenan. Ko kuɗin aiki na ta bani ne na wata biyu da yan satittika? Gobe inshaAllahu zan tambaye ta idan naje zan kuma karɓi number ta.

A hanzarce na shiga gida cikin farin ciki dan ba ƙaramin daɗin kuɗin nan naji ba. A guje na faɗa jikin Innati data fito daga banɗaki cikin ɗoki nake nuna mata kuɗin. Itama murnar ta yi bayan ta gama tambaya ta yanda a kai na sami kuɗin. Kwashe duk yanda muka yi na gayamata ,tayi mamaki itama take tunanin da nayi ko kuɗin aikin nawa ne suka bani.


***

Washegari ya kama weekend babu aiki shi yasa nasha barci na da safe bayan nayi sallan asuba dan ban koma ba sai da gari ya waye ina tulawar karatun Qur'ani. Ban tashi ba sai wajen karfe goma na safe shima Innati ce ta tashe ni na karya. Da yamma nayi niyar zuwa kasuwa dan siyo mana duk wani abu da nake ganin ya dace.

Tun daga kan shinkafa, garin tuwo, fulawa, shinkafar tuwo,wake, mai,magi da sauransu babu abinda ban siya ba. Mota guda nayi ya dauko min kaya. Har kayan sawa na siyo mana nida Innati atamfofi ƴan ma daidaita kuɗi da dogayen riguna. Sai ƴan hijabai da mayafai. A takaice dai kudin nan 50 hamsin kawai na dawo da ita, amma nasan dai nayi mana siyaryar da zamu ɗan kwana biyu bamu nemi wani abu ba. Harta kawu Salmanu ban barshi ba sai da na kai masa dubu goma ya karba da kyar danshi mutum ne da sam bai damu da rayuwar duniya ba. Ko sanda Abbu na yake raye sai dai ya yi masa abu a ɓoye dan baya karɓa sai in takama dole ne duk irin yanda Abbu ke ƙoƙari wajen ganin ya wadata dangin shi.

Kawu Salmanu mutum ne shi da sam bai damu da rayuwar duniyar ba gaba ɗayan ta. Yace mai kuɗi ,talaka,muƙami,mulki duk ɗaya suke gurin Allah bai basu wannan matsayin dan wani yafi wani ba face wanda yafi kusanci dashi. Shi yasa yana matuƙar wahala a bashi a bu ya karɓa sai in ta kama masa dole. Babu irin naci da mita da Abbu baya yi akan hakan dole ya haƙura ya kyale shi sai dai in ya yi niyar yi masa abu ya yi a ɓoye ba tare da sanin sa ba.

Nima yanzu saida na sashi gaba da kuka sannan ya karɓa yana min addu'a da fatan samun miji na gari. Kuma inda yake ƙara burgeni duk da rashin ƙarfi da bashi dashi bai hana ya wadata gidansa ba. Baza ka tabajin sunce basu da wani abu ba yana iya ƙoƙarinsa wajen ganin ya sauke wannan nauyi da hakki da Allah ya ɗora masa.


***

A yanzu nayi sati biyu da fara aiki a A&E industrie kuma Alhamdulillah ina jindaɗin aikina dan babu wata matsala da nake fuskanta saboda Eman tana bani kulawa yanda ya kamata, sannan shima Haisam sosai ya ke jana a jiki duk da cewar naki sake masa kaman yanda yake so, saboda duk lokacin da suke tare da Ayaan ya yi min magana toh fa ya dinga jifana da mugun kallo kenan in mun haɗu kuma ya jefa min baƙar magana kaman "Careful dai kar ki yi tunanin shima target ɗinki ne, ya wuce limit ɗinki"

Tun ina zama nayi kuka na koshi har na fara sabawa da ire-ire waɗannan kalamai nasa. Toh yau tunda nazo na fuskanci kaman akwai matsala a kamfanin saboda yanda naga ma'aikata na ta bin bene basu bin lifter . Gurin receptionist na tsaya ina tambayar ta kome ya faru naga suna bin wannan bene da bashi da ƙarshe?. Sai take gayamin wai elevators ɗinne suka samu matsala jiya tayi trapping mutane sai da aka ɗauko masu gyara suka buɗe ta shi ne aka hana bi sai an gyara su tukun.

Ajiyar zuciya na sauke ina mata godiya na wuce hanyar stairs da zan bi. A bakin stairs ɗin na tsaya ina tunanin ta inda zan fara. Mutane sai wuce ni suke daga masu hawa sai wanda za kaga ya sakko a jigace. Toh ni da nake 25floor fa? Allah yasa doguwar riga ce a jikina baka mara nauyi. Babu wani ado a jikinta dan irin ƴan gwanjon nan ce sai flat takarmi dake ƙafata fari mai yatsa.

Jan numfashi nayi na gyara zaman jakata tare da tattare rigata na fara hawa benen da bismillah. Zufa nake haɗawa saboda mugun gajiya da ƙafafuwana sukayi ina ta wuce mutane wasu a zaune kan benen suna hutawa wasu a durƙushe. Gaskiya duk wanda ya yi wannan gurin ba ƙaramin mugun mutum bane wlh.

Tamkar iska naji an wuce ni cikin sauri na dago ina kallan bayan Ayaan dake hayewa benen ko a jikinsa. Toh dama yaushe zaiji wani abu kaman gajiya irin wannan ingarman jiki da Allah ya bashi. Hamdala nayi a bayyane bayan na kawo floor ɗina. Ƙuguna na rike na ɗan ranƙwafa ina mayar da numfashi kaman wadda tayi tseren gudu.

"Miss Neehal "

Naji muryar shi na kusantu inda nake. Cikin sauri na mike tsaye da kyau ina kallan Ayaan dake nufu ni fuskarsa a murtuke. Muryata na rawa na amsa da

"Yes sir"

Gaba na ya tsaya yana cewa " Nabar files a ƙasa gurin receptionist mai muhimmanci, ko zaki karɓo ki kawo wa Eman please ?"

Kallanshi nake kaman wanda ke da kai huɗu, ni kaina bansan nayi masa wannan kallan ba sai ji nayi yace

"Akwai problem ki ke min kallo kaman mara hankali?,ko baza kije bane?" saurin girgiza masa kai nayi na sauke kaina kasa na ce " sorry, amma ...uhm.. amma lifter din ta lalace"

"So? That's a very shitty excuse Miss Neehal. Idan baza kije bane kawai ki fito fili ki faɗa kina wasting time ɗina" da sauri na ce masa "no zanje" ina girgiza kai.
"Good " yace yana min wani irin kallo kafin ya juya ya yi hanyar office ɗinsa.
Yanzu ma saida nayi minti ashirin da biyu kafin na sauko ƙasa. Ƙafata har rawa take ciwon ƙafata ya tashi ina tafe ina hardewa har gaban receptionist din na tambayeta file din tace min babu wasu files a nan. Haka na ƙara komawa nayi jage- jage da zufa numfashi na yana fita da sauri da sauri saboda wahala.

"Baya ...baya.. nan" na ƙarasa maganan breathlessly ina rike gefen cikina da naji ya riƙe ƙafafuwana suna rawa. Haɗa hannuwansa ya yi guri ɗaya yana ƙara gyara zama kan kujerar da yake ya ce " gashi kuma files ne masu matuƙar muhimmanci ko zaki je parking lot ki duba ko na barsu cikin mota" ya miko min muƙullin mota yace ga "key ɗin motar da kinje ki danna za tayi horn" .

Wai anya kuwa yasan me yake faɗa kuwa?da ƙyar na tako na ƙarbi muƙullin daga hannunsa na fice daga office din. A yanzu kam guri na samu na zauna ina haki kafata tana wani irin raɗaɗi kaman nayi kuka. Sai da na ɗauki tsawon minti biyu a zaune ina maida numfashi kafin na mike na cigaba da tafiya. Toh a can parking lot ɗinma babu irin duban da banyi amma banga wasu files ba. Ina cikin duban ne wayata ta hau ƙara cikin fita hayyaci na ciro ta daga cikin jaka ina duba baƙuwar number da ban sani ba. Ɗagawa nayi tare da sallama muryata a shaƙe bata fita sosai saboda gajiya.

Nace "Hello wake magana?"

"Miss Neehal, kizo naga files din"

diff ya kashe wayar ba tare da ya jira nace wani abu ba. Wani irin damke wayar nayi ina ji kaman nayi jifa da ita. Dama yana da number ta ?nasan da gayya yasani wannan wahalar dan kawai ya ganni cikin kunci. Hana kaina kuka nayi na daure ciwon da ƙafata takemin na koma ina ɗan ɗin gishi.


***

Toh kaman yanda Eman ta saba duk lokacin lunch break sai ta kira ni munci abinci tare a office ɗin ta. Yauma dai kaman kullum suna ta musu ita da Haisam kaman masu ganin hanjin cikin su. Nidai ina zaune ina aikin kallansu ina murmushi ko kadan ban bari na damu da Ayaan dake zaune a gefe na ba yana kurban coffee. Babu zato wayan shi ta fara ringing saida ta kusan katsewa sannan ya ciro ta daga aljihun rigar shi. Ta ƙasan ido nake kallan haɗaɗɗiyar Galaxy ultra dake hannunsa wadda sunan Angel ya bayyana jikin screen ɗin wayar.

Tsintar kaina nayi da kasa ɗauke ido daga kan wayar har ya kaita kunne. Wani irin abu naji ya tsarga kaina sunan Angel da naji ya ambata cikin wata irin murya mai sanyin gaske. Bansan me aka ce ba naga ya saki murmushi wanda kana gani kasan an gaya masa magana mai daɗin gaske. Cokalin hannuna na ƙare damƙewa ina juya abincin na kasa cigaba da ci. Haka kawai nake jin wani iri. Saboda yanda yake maganan ƙasa-ƙasa yasa duk yanda na kasa kunne dan naji abinda yake cewa na kasa har ya gama wayar da murmushi a fuskarsa.

Muryar Eman naji tana cewa " Angel ce ta kira?" Kai kawai ya ɗaga mata baice komai. "Ta kusan dawowa ne?" Nan ma kan ya ƙara ɗaga mata baice komai ba. Murmushi naga tayi cie da farin ciki tana kallo na tace "na gaya miki kuwa My little Ayaan is taking? Yana da aure?" Wani irin dum naji kirjina ya bayar kunne na ya yi wani irin ƙara shuuu kaman an buga min guduma. Bata lura da yanayi naba ta cigaba da cewa " Kinsan akwai wata yarinya da brother ɗina ya taɓa so shekara shida da suka wuce. Duk da yace min yarinya ce ƙarama a time ɗin amma tayi amfani da son da yake mata ta sashi cikin gagarin rayuwa, he loves that girl deeply but sai tayi breaking heart nashi ta hanyar amfani da feelings dinshi saboda yana ƙarƙashin ta tana ganin cewa shi ba mutum bane saboda yana a matsayin talaka. I hate that girl with passion duk da ban santa ba amma na tsaneta tsana mai karfi bama ita kaɗai ba duk wasu masu irin halinta na tsane su. But sometimes kuma ina mata godiya saboda ta sanadiyar ta ya haɗu da Angel from the sky ta so shi at his worst duk da ya kasance bashi da komai. Ya guje mata but ta nuna masa san gaskiya kusan ita ce ta yi sanadin wannan rayuwar da ki ka ganshi a ciki ta nemo mu ,mu danginshi da muke neman sa na tsawon shekara 29. A yanda iyayen mu ke bani labari ranan sunan mu aka sace Ayaan . So for ever zamu kasance a depth nata saboda ta bada gudummawa sosai cikin rayuwan sa duk da cewa itama yarinya ce ƙarama. Dan zan iya cewa za kuyi shekara ɗaya da ita idan ma kin girme ta baifi ki bata shekara daya ba ko biyu."

Tunda ta fara magana kaina ke kasa wani irin gumi yana bin gefen fuskata da bayan wuya na. Ko ƙwaƙƙwaran numfashi na ƙasa fitar wa. Murya ta na rawa na ɗauki excuse na fice daga office ɗin bayan na kalli Ayaan da shi ma yake kallo na a yanzu fuskarsa ɗauke da wani expression da baza ka gane me yake jiba. Farin ciki ko baƙin ciki. Ina jin Haisam na cewa Eman "sarkin zuba hirar ta isa haka mana" ni dai nayi saurin ficewa na barsu .




Tohhhhhh inji mai Tallan totowa🤣🤣🤣

Ana wata ga wata inji yan chacha😂😂😂

Me ku ke tunanin Eman za tayi idan ta gane Neehal ce yarinyar da take magana a kai??

Wacece wannnan Angel da aka magana a kai haka.??


TOH INA FATAN MASOYAN LITTAFIN "KAIDIN MACE" ZAKU BANI GOYON BAYA DON MUN KUSA KAWO KARSHEN FREE PAGES INSHAALLAHU.😅




✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟✯



E 19-20



Tunda na koma nawa office ɗin na kasa taɓuka komai. Kalman auren da yake dashi ita tafi tsayamin a rai matuƙa. Ni dama nasan cewa a rashin sani Eman take bani wannan kuluwar duk ranan da ta gane ni kuwa wata ƙila ma korata za tayi. Toh amma me yasa bai gaya mata nice yarinya ba? Ƙofar office dina da aka buga ita ta dauke min hankali daga tunanin da nake na ɗago ina kallan Haisam dake tsaye cikin office ɗin nawa fuskarsa ɗauke da murmushi mai ƙayatar wa. Haisam kyakkaywan mutum ne Black beauty wanda saboda hutu da jindaɗi fatar tasa ta zama kaman irin ta black Americans mai sheki sosai. Dogo ne ba chan ba dan bai kai Ayaan tsayi ba shima kuma yana da ƙirar majiya ƙarfi dan yana da faffaɗan ƙirji. Idanuwan sa manya ne daidai misali. Yana da dogon hanci sai full lips da yake da su jajur dasu kaman yasa musu janbaki.

Kujerar dake fuskanta ta ya ja ya zauna yana cigiba damin murmushi "ki yi hakuri da Eman wani lokacin haka take da ɗan banzan surutu, she doesn't know when to shut up" kallan sa nake cikin rashin fahimta kaman ya sani kuwa ya cigaba da cewa " na san kece Neehal yarinya da ya taɓa so, i know saboda ya gayamin and ranan da ki kazo office dinnan ya ganki ya tabbatar ke ce he drink his ass off ,thank fully Angel bata nan, da tayi scolding nashi" kaina na sunkuyar ƙasa jikina ya yi sanyi.

"But i know yanzu kin chanza, ba yarinyar da yake gayamin bace da, kina da halaye masu kyau

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment