Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mu ya ceton kanmu?"
'Fita daga cikin wannan daki ya tsirarmu wuya daga kurkukun gabadaya, kawaj ka nuna mini
hanyar da za mu bi ta kai mu inda rariyar gidar har take mai fitar da ruwa waje.
Gama fadin hakan ke da wuya sai nsam ya zura kafafunsa cikin tagar sannan ya mikowa Barsad hannunsa ya kana kawai sai ya dago Barsad sama tamkar karamin yaro ya janyo. Barsad ya cafo saman tagar da hannayensa biyu a lokacin da tuni Insam ya fita waje ya duro kasa bisa kafafuwansa. Cikin hanzari shi ma Barsad ya fice ta cikin tagar ya dira waje yana dira ya wuce gaban Insam da gudu ya nufi wani bangare dabam na gidan a kuwa sai shi ma Insam ya rufa masa baya suka rinka falfala wani irin masifaffengudu wanda inda mutum na tsaye a wajen idan suka zo suka gifta shi hucin iskar gudun nasu ne zai yar da shi kasa.
Koda dakaru suka hango Barsad da Insam a guje sun nuti wannan bangare na gidan sai suka biyo su aka kasa tsere.sati to Dakarun da ke can gabansu kuwa Suna hangosu suka zare takubba suka rugo kansu, ya zamana cewa ana nema a sa su Barsad a tsakiyaa yi musu rubdugu. Ko da su Insam suka fahicmi abin da ke shirin faruwa sai suka fara banke dakarun ta gaba ta baya. Wata irin tafiyar yaji suka rinka yi da dakarun tamkar ana Sassabe a gona. Duk da cewa dakarun na dauke da makamai na hannunsu sai ya zama na banza domin bazar da su suka yi ta yi yi tamkar ana karkado busassun ganyayyaki kasa daga kan bishiya.
A daidai wannan lokacin ne suka ji an fara busa wani kaho mai karar tsiya, shi dai wannan kaho in dai ka an busa shi a wannan kurkuku to tabbas babu zaman lafiya kuma alama ce ta cewar akwai fursunan dake kokarin guduwa.
Shugaban dakarun Gadaraz na kwance a cikin dakinsa na barci tare da matarsa Ilaila sai kawai ya ji karar wannan kaho Nan take ya mike zaune zumbur yana mai ture Ilaila daga kan kirjinsa. Hakan ne ya sa itana ta farka daga barcin ta durbe shi cikin alamun damuwa a lokacin da tuni ya sauko daga kan gado ya fara sa kayansa. "Wanemai rabon mutuwar ne kuma yake kokarin guduwa daga gidan nan a wannan daren?"
Gadaraz ya ce Ni ma abin da hake mamaki kenan. Mutum biyu he kacal daga cikin fursunoni za su iya yunkurin guduwa daga gidan nan wato Insam da Barsad kuma suna kulle cikin dakin horo babu yadda za su iya fita bare ma har su yi kokarin gudu. Bari dai na je na ganewa idanuna"
Ilaila na jin haka sai ita ma ta vi wuf ta mike tsaye ta fara sa kayanta ta ce 'Ai kuwa ni ma ina son na ga ko waye wannan mai tsautsayin wanda ya gaji da rayuwar a duniya."
Shi dai Gadaraz ko kallonta bai yi ba sai ya ci gaba da shiri, ya debi dukkanin makamansa na yaki, ya sa a jikinsa sannan ya fice daga cikin dakin.
Nan da nan ita ma Ilaila ta sa tufafinta da takalmanta, ko da ta nufi kofar fita daga dakin sai ta ga layar tsafin mnijin nata a ajiye a kan tebur.
Al'amarin da ya yi matukar ba ta mamaki ke nan. ta tsaya cak tana kallon layar tana tunani da wasu-wasi. Ita dai Ilaila a saninta da Gadaraz dare da rana baya rabo da wannan laya face sai idan zai kwanta barci da daddare sannan yake cireta daga wuyansa ya dora ta a kan wannan tebur kuma da zarar alfijir ya keto yake farkawa daga barci ya dauki abar sa ya mai da ita wuyansa.
Ko sau daya a tsawon shekaru biyu da ta aure shi ba ta taba ganin ya mance da wannan laya ba, sai yau. Lallai akwai ayar tambaya a cikin wannan al'amari. Gama ayyana hakan ke da wuya sai laila ta yi sauri ta fice daga cikin dakin ta janyo kofa. ta rufe da mukulli. Sannan ta falfala da gudu izuwa cikin kurkukun Duk fadin cikin wannan kurkuku Ilaila ce kadai ya mace wacce babu wani fursuna da lya isa ya yi mata ko da kyakkyawan kallo saboda tsananin tsoron mijinta da ake yi.
Ilaila ta kasance kyakkyawar mace ta gaban kwatance amma shekarunta za su kai talatin da biyu Zuwa da uku. Ba komai ne ya sa Gadaraz ya auri llaila ba face kyawunta da kumajarumtakarta domin ta kasance mace mai kamar maza sannan matsalarsu a rayuwa iri daya ce. Gadaraz ya hadu da laila ne a can kurkukun birnin Misira a lokacin da shi ne Shugaban dakaru masu tsaron kurkukun wanda ya kasance na mata ne zalla. A tarihin wannan kurkuku na birnin Misira wanda aka gina shi sama da shekanu dari da doriya baya ba a ta6a samun fursunar da ta sami damar guduwa daga cikinsa ba sai Ilaila kuma sau biyu tana guduwa da kyar da sidin goshi Gadaraz ke iya bin bayanta ya kamota ya dawo da ita, amma sai bayan sun yi mugun artabu ya sha bakar wahala domin sai sun yi wa juna rauni saboda karfin damtsenta na sadaukantakar da Allah ya ba ta. Kawai da karfin sihiri ne ya ke samun lagonta har ya sami nasarar kamata.
Ba wani laifi Ilaila ta yi ba face shiga gidan Sarkin Misira domin ta dauki ansar mutuwar mahaifinta wanda ya kasnace Bafaden Sarkin.
Sia da ta sami nasarar shiga har cikin turakar sarkin amma da yake yana da karfin sihiri ba ta gan shi ba alhalin ga shi kwance a kan gado yana ta faman sharar barcinsa.
Nan fa ta kama dube-dube a cikin turakar ashe wadansu kuyangi dake kwance a kasa masu taya sarki barci ba barci suke ba sun ii motsin shigowarta Har sai da ta tsallakesu ta nausa can cikin turakar sarkin sannan daya daga cikinsu ta mike tsaye cikin sanda ta je, ta dauki wata gudùmar katako ta doka a kan wani Faifan karfe.
Nan take karar faifan ta cika gidan sarautar gabadaya. Nan da nan sai ga dakaru da yawa ta ko'ina suna 6ullowa a guje dauke da makamai.
Kafin Ilaila ta ankara tuni dakaru sama da guda arba'in sun kewayeta a tsakiyar turakar sarkin Karar wannan faifan karfen ce ta tashi sarki Marhat daga barci.
Koda ya mike zaune ya ga bakuwar mace a tsakiyar turakarsa ga dakaru sun kewayeta ta yi shigar yaki sai ya kura mata idanu da kyau ya ga bai santa ba bai taba ganinta ba a birninsa gabadaya.
Har Sun yunkura za su afka mata sai sarki sai Marhat ya daka musu tsawa suka ja da baya, sannan ya sauko daga kan ya gadonsa ya dubeta cikin murmushi, ya ce "Ke yanmata jwace ce ke kuma wane gangancin ne ya kawo ki har cikin turakata domin ki yi min sata'
Ko da jin wannan batu sai llaila ta rmurtuke fuskarta ta dubi Sarki Marhat cikin harara mai Duna tsananin kiyayya ta ce da sata na zo yi ba nan zan shigo bacikin turakarka da can baitul mai zanje inda kake 6oye dinare da lu'u-lu'u zuwa na yi na dau ranka."
Da jin wannan batu sai sarki Marhat ya dubi dakarunsa da dukkanin hadiman dake wajen ya Kyalkyale da dariyar mugunta, sannan ya dubi laila ya ce, "Laifin me na yi miki kike son ki kashe ni?"
Ilaila ta ce "Ka kashe mutum daya jal wanda shi kadai ya rage mini a duniya Barde Amzad. Ni yarsa ce don haka yau dole ne takobina ta sha jininka."
Sarki Marhat na jin wannan batu sai ya sake kura mata idanu da kyau kuma ya bushe da dariya a karo na uku ya ce "Tabbas ni ne na kashe Mahaifin ki ba don komai ba sai saboda shi ne kadai ya san sirrina na dukiyata, da kuma sirrin tsaron rayuwata. Ina tsoron kada wata rana ya ci amanata ya hada baki da wasu a raba ni da rayuwata ko dukiyata.
To fa nima jin wannan batu na jaruma Ilaila da Sarki Marhart yasa na tsaya ina kallon su ni ne dai Abubakar Saleh inkiya Mijin Soja anan zan dakata sai kuma wani lokacin idan mai kowa da mokai ya kaimu wani lokacin dan jin cigabansa wannan kasaitaccen labari.
Sannan ga masu son complete PDF da wasu littattafan zasu iya tuntubata ta wannan Number 08138873799.
GWARZON SADAUKI
Littafi Na Daya (1)
Part C
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Kafin nace komai ina jiyawa yan uwa barka da juma'a da fatan Allah Ya sadamu da alkhairan wannan rana, Amin.
Dama na sami labarin yana da ya guda daya, wacce tun tana da shekaru bakwai ya dauketa daga nan cikin birnin Misra ya kai ta can birnin Askandariya wajen wani gawurtaccen mayaki ana ba ta horo na jarumta. Babu irin neman da ban yi miki ba, ke da mayakin da ya ba ki horo amma ban ganku ba. Akwai wani littafi wanda ke dauke da sirrin inda na boye dukiyata da kuma inda sihirin tsaro na rayuwata yake a hannun mahaifinkil Har na kashe shi ban san inda littafin yake ba. kuma bincike ya tabbatar mini da cewa ke ma baya hannunki sai dai babu mamaki kin san a inda yake. Kina da zabi guda biyu, za6i na farko shi ne ki sanar da ni inda wannan littafi vake zan ba ki dukiyar da har ki mutu ba za ta Kare ba. amma za ki bar mini kasata ko kuma na yanke miki hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.'"
Lokacin da ilaila ta ji wannan batu ha Sarki Marhat sai ta ara fusata ainun ta ce "Kai tsohon azzalumi kuma butulu na san irin bautar da mahaifina ya vi maka kuma duk matsayin da kai kai a yanzu shi ne sanadi domin ya ba ni labarin komai abin da ba zan iya tunowa ba kawai shi ne inda wannan littafi yake na sirrinka saboda ina yarinya karama a lokacin da ya ba ni labarin komai! Ni da kai babu sulhu sai dai kaifin takobi ya shiga tsakaninmu.
Kafin Sark Marbat va budi baki va kara fadin wani abu tuni llaila ta afkawa Dakarun dake kewaye da ita ta hau su da sara da sukacikin wata irin gagarumar jarumtaka da matukar zafin nama.
Kafin Cikar dakiku đari da tamanin ta zubar da su kasa. wasu a mace wasu agalabaice cikinini.
Nan take Sarki Marhat va kama vi mata tafi sannan ya dubeta ya ce "Tabbas kin cika jaruma sia dai mahaifinki ya yi kuskure da bai samo miki sihirin tsafin da za ki iya tunkarata ba.
Ilaila ta daka masa tsawa ta ce "Ni ban yarda da tsafi ba don haka tsafin naka bai isa ya kare ka daga sharrin takobina ba."
Tana gama fadar hakan sai ta nufi Sarki Marbat gadan-gadan tana mai daga takobinta sama da nufin ta sare shi amma sai ya nunata da dan yatsansa guda na hagu.
Take ta kasa ta riketa ta kasa motsawa gabal Nan fa ta yunkura iya karfinta amma ta li ta kasa yin ko taku daya.
Sarki Marhat ya sake daga hannunsa sama sai takobin hannunta ta dawo hannunsa sannan ya dubeta ya bushe da dariya ce "Idan ina son Kashe ki yanzu take zan fille miki kar to amma ba zan kshe ki ba, saboda babu mamaki nan gaba a dallin ki na gano inda littafin sirrina yake.Zan kai ki kurkuku na ajiye ki duk ranar da kika tuno inda mahaifinki ya boye littafina zan sake ki na cika alkawarin da na daukar miki na kyautar dukiya mai yawa, sannan k bar mini kasata."
Yana gama fadin hakan sai ya tafa hannunsa sau biyu nan take wasu dakaru kimanin su arba'in suka bayyana na musamman masu matukar gima da kwarjini suka shigo cikin turakar dauke da sarkoki suka daure hannayen Ilaila da kafafuwanta suka fice da ita.
A cikin wannan dare aka kai Ilaila cikin kurkukun mata na birnin Misira kuma wadannan dakaru guda arba'in na musamman masu matukar girma da kwarjini ne suka sa ta a cikin keken doki doki suka kai ta.
Shi dai wannan kurkuku an gina shi ne a tsakiyar wani daji da ake kira Lanmras kuma a cikin karkashin kasa aka gina shi kafin mutum ya isa kofar farko ta shigarsa sai ya taka matattalaka guda dubu daya da dari uku. Duk abin da dza a yi amfani da shi a cikin kurkukun ana tanadar na kwana talatin ne cif kuma in ban da sadauki Gadaraz da amintattun dakarun tsaro guda arba'in babu wanda yake da ikon shige da fice a Cikin| kurkukun face da izinin Sarki Marhat.
Fursunonin dakc cikin wannan kurkuku guda dubu shida ne da dari uku, dakarun mata masu tsaronsu guda dubu uku nc sai kuma dakaru maza guda dubu biyu. Ba a ganin rana a cikin wannan kurkuku sakamakon yana karkashin kasa amma ko allura ce ta fadi kasa sai an ganta saboda irin manyan fitilun dake cikinsa masu matukar haske.
Abincin da aka bai wa fursunoni a cikin wannan kurkuku mai daraja ne da inganci kuma ba a yanke wa fursuna hukuncin dauri rai da rai.
Mafi yawan fursunonin da ake kawowa suna da amfani ga Sarki Marhat don haka ba so ake a kashe su ba.
Ana kawo su ne domin a yi musu hukuncin wani laifi da suka aikata ko kuma ana so a matsasu su fadi wani kirri da ake so a sani ko kuma ana so a vi amfani da su wajen cimma wata manufa ko nasara a yaki kasuwanci ko| kuma siyasar duniya.
Fursunoni suna samun komai ha ljin dadi duniya cikin wannan kurkuku kuma ba a barin su cutar da junansu. Da zarar an ga sun fara rikici ko fada sai a vi saur a taba $u, dan ma a daki guda suke sai a raba masu makwanci don kada wata ta shammaci abokiyar fadanta ta cutar da ita. Duk wannan bai hana a hukunta fursunonin ba, idan suka aikata laifi ko kuma idan suka karya dokar gidan.
Idan fursuna ta yiwa lyar'uwarta babban rauni za a sata cikin matsattsen daki wanda ko kwanciya ba za ta iya yi ba a cikinsa kuma ba shiga ba ita har tsawon kwana talatin sannan duk lalurar da ta kama ta sai dai ta yi a cikin dakin. Kuma kullum sau daya kacal za a ba ta abincin da ruwa.
Wannan dalili ne ya sa fursunonin suke matukar kiyayewa wajen yin mugun fada saboda sun san irin azabar da za a yi musu.
Idan kuwa fursuna ta kashe yar'uwarta fursuna koda bisa tsautsay1 ne to fa sai ta shafe wata Uku cur a cikin wannan kuntattaccen daki! sannan a fito da ita a kai ta wani daki daban wanda ake kira "ihunka banza."
Shil dai wannan daki ha ihunka banza ba shi da rufin sama. keji nc na Karafa masu kaurin gaske. Babu batun wanka ko wanki kuma a wajen za ki kawar da duk bukatarki!
T'sananin wari, doyi da zarni ma ya ishi mutum. Saboda dauđar jiki da ta tufafi kwarkwata da kudin cizo ya ishi fursuna bala'i.
Abin takaicin ma shi ne sai ka Iske sama da mata arba'in a cikin wannan daki na ihunka banza kuma In dai aka sa fursuna a cikinsa sai ta shafc wata shida cur a cikinsa sannan za afito da ita a yanka mata sabon horon aikin wahala na tsawon shekaru uku cif kullum ba fashi.
Bisa wannan dalili ne fursunonin ba sa yarda su aikata laifin kisan kai musamman saboda duk wadda ta shiga dakin ihunka banza bata fitowa lafiya sai dauka da cuta.
Haka za ka kgansu sun rame Sosai babu kyan gani, wasu ma sai an dade ana jinyarsu ana ba su maganı da kulawa a cikin kurkukun sannan za su warke kuma su ci gaba da karbar horonsu na aikin wahala. Wasu ma idan suka kamu da cutar tana iya zama sanadin ajalinsu.
A ranar da aka kawo jaruma Ilaila cikin wannan kurkuku wanda akalýi wa |lakabi da mugun gida tana daure tamau cikin sarkoki hannu da kafa, sai ta ga an shige da ita cikin wannan gidan kusa aka yi ta tafiya da ital Sai da aka bude kofofi guda goma sha daya sannan aka iso wani babban fili inda dakunan fursunoni yake, a can gefe daya kuma wani rukuni ne daban inda dakunan dakaru maza yake sannan kuma akwai bangaren dakaru mata amma su wadannan dakaru gidaje aka yi musu isassu a wadace babu takura.
Wasuma daga cikin dakarun maza da mata akwai auratayya a tsakaninsu kuma suna rayuwa tare da ya'yansu.
Akwai bangaren kasuwarsu da kuma inda aka koyar da ya'yansu jarumtaka da iya yaki domin idan suka girma su sami aiki irin na yayensu.
Abin da zai bai wa mutum mamaki shi ne yadda sarkin Misira ya dauki wannan kurkuku da muhimmanci matuka ya zamana cewa ana kashe makudan kudade a cikinsa domin hatta albashin da ake biyan dakarun gidan mai tsoka ne kuma idan ka tsufa kana aiki a gidan ba za a sallameka ba, kuma za a ci gaba da biyanka rabin albashinka har izuwa karshen rayuwarka.
Idan ma ka mutu ba ka babban da wanda zai gaji aikinka to za a ci gaba da bai wa iyalinka albashinka.
Abinci da abin sha kuma kyauta ake bai wa dakaru baya daga cikin albashinsu. Hakan ne ya sa dakarun birnin Misira suke matukar kwadayin a kai su aiki cikin kurkukun mugun gida.
Lokacin da aka] iso wa wannan babban fili inda dakunan fursunoni yake sai aka tsaya cak. Kawai sai ilaila ta ga dakarun mata su hudu sun zo sun karbeta daga hannun dakaru maza. Nan take suka kwance sarkokin dake jikinta sannan suka tafi da ita izuwa wata kofa. Masu gadin kofar suka bude aka wuce da ita ciki! Da shigarsu sai ta ga ashe wani rukuni ne na wasu dakunan fursunoni dama da hagu birjik kamar ba su da adadi kuma a cikin ko Wane daki guda fursunoni biyu ne kacal.
Akwai gadaje guda biyu a kowane đaki dauke da shimfidu masu taushi da tudu kuma akwai dan karamin makewayi wanda aka rufe shi da labule. Wajen da ake tsuguno kuwa a cikin makewayin kamar kujera yake kuma bahayar tafiya yake cikin wani dogon bututu wanda ya kai har cikin jwata cibiyar ruwan kogi.
Kafin a wuce farkon dakunan wannan rukuni akwai wani daki uda daya na musamman wanda an vi shi ne domin shugabar dakarun mata. Kujera biyu ne jal da teburi guda a cikin wannan daki.
Nan take aka shigo da ilaila cikin wannan daki inda ta yi arba da wata shirgegiyar mace zaune a kan kujerar ta kura mata idanu tana murmushi.
Akwai tuffa a hannun matar gami da wata yar karamar wuka tana yankan tuffar tana ci kuma ga ruwan inibi a cikin tanmbulan da kofin karfe a kan teburin. Kawai sai aka zaunar da Ilaila bisa kujerar da ke fuskantar shugabar dakarun sannan dakarun da suka kawo Ilaila suka juya suka fice daga cikin dakin, suka bar Ilaila da shugabar su biyu kacal.
Duk da cewa Ilaila jaruma ce ta gaske sai da kwarjinin wannan shugabar dakard ya sa zuciyarta ta dan buga saboda ta kasance mace mai kirar mazal duk jikinta a murde yake cike da kwanji ga jjiyoyi sun tashi sun yi burdin-burdin a jikinta, sannan idanun ta jajaye ne ba kyan gani kuma ko kadan babu annuri kan fuskarta ka ko hararar mutuum ta vi sai hantar cikinsa ta kadu. Shi kansa murmushinta yana kama ne da fushin dodo Ilaila ta dubi wannan mata ta yi murmushi kamar wacceta ga tsohuwar Kawarta Ba tare da huna wata alama ta tsoro ba ko shakka sa Ilaila ta kai hannunta ta dauki wannan kofin karfe da kuma tambulan na ruwan inibi ta siyaya uwan inibin a cikin kofin ta kai bakinta ta sha,
Sai da ta kurba sau uku sannan ta gyara Zama gami da yin gyaran murya ta sake duban matar a karo na biyu ta ce "Kin burge ni fa da ba ki hanani Shan ruwan inibin nan ba. Ba ni.labari, mene ne dokokinku a gidan nan na san dalilin da ya sa aka fara kawo ni wajenki kenan?
Sa'adda mata ta ji wannan tambaya sai ta bushe da dariya mai karfi kai ka ce jaki ne ya ashe da kuka aboda kaurin muryarta. Lokaci guda kuma sai ta tsuke bakinta ta vi shiru ga barin yin yi dariyar sannan ta mike tsaye ta ajiye tuffar da take ci da karamar wukar akan teburin ta ljuyawa Ilaila baya ta ce.
Da kyau yarinya mai wayo, tabbas ke abokiyar tafiya ce. Za mu zauna da ke lafiya muddin za ki kiyaye dokokinmu kuma za ki kasance mai ladabi a garemu "Doka ta farko a gidan nan íta ce,j ba a tsokanar fada amma idan aka tsokaneki za ki iya kare kanki. Doka ta biyu kada ki yi wa yar'uwarki rauni babba kuma ko da tsautsayi ka da ki kashe fursuna domin akwai hukunci mai stananin gaske. Doka ta uku ita ce duk fursunar da ta yi yunkurin guduwa za ta kwana ta yini ne ci ba sha, sannan za ta fuskanci horo mai tsanani na kwana goma sha hudu.
Idan kunne ya ji gangar jiki ta tsira. Ya ke Ilaila ki yi sani cewa sunana Barita, ba ni da tausayi ba ni da imani! Ban yarda da kuskure ba, kuma ba na lamintar raini."
Sa'adda Ilaila ta ji wannan batu sai ta yi đan guntun murmushi sannan ta ajiye kofin da take shan ruwan inibi sannan ta dauki wannan ragowar tuffa wadda Barita ke cil ta kai izuwa kan bakinta domin ta ci, amma sai Barita ta vi wuf ta damki hannun Ilaila ta murda shi baya, ta turata i zuwa jikin bangon dakin, ta manneta da garų.
Ilaila ta kurma ihu sakamakon tsananin zafin da ta ii bisa murdewar hannun nata a lokacin da ta i kamar hannun nata zai cire.
Barita ta kwace tuffar daga cikin hannun Ilaila ta sa a bakinta, ta ci gaba daci ba tare da ta saki hannun nata ba ta ce! "Kin manta ne na gaya miki cewa ba na son raini."
Ko da jin wannan batu sai Ilaila ta wurkila jikinta ta yi wani irin juyi saiga shi ta murde hannun Barita kamar yadda ta yi mata, ita ma ta manneta da garu. Barita ta ii wani irin zafi wanda in ta ce za ta kwace za ta iya samun matsala a hannun nata.
Al'amarin da va vi matukar ba ta mamaki kenan saboda bata taba zaton za a iya samun wata ya mace mai karfin da za ta iya yi mata haka ba. Ilaila na murmushi ta ce, "Ai ba raina ki na yi ba so nake ki gane cewa ni ma fa jan wuya ce.
Kafin Ilaila ta gama rufe bakinta tuni Barita ta turota baya da dukkan Karfinta sun fadi kasa. A daidai wannan lokaci ne wasu dakarun mata su goma suka rugo izuwa cikin dakin da nufin su rufe Ilaila da duka amma sai Barita ta dakatar da su. Barita ta mike tsaye. Sannan ta mikawa Ilaila hannunta, ta kama ta tasheta tsaye.
Barita ta yi murmushi ta ce, Hakika na yarda ke ma jan wuya ce domin ke ce mace ta farko dana taba murdewa hannuna kuma ta kwace a gwagwarmayar da na yi a duniya. Tana gama fadin hakan sal ta dubi wadannan dakarun mata guda goma ta ce "'Ku tafi ku ba mu wuri ina da maganganu da yawa da wannan fursunar.
Ko da jin wannan umarni sai dakarun goma suka Ijuya suka fice daga cikin dakin Barita da Ilaila suka koma kan kujerun biyu suka zauna suna masu fusknatar juna sannan Barita ta dubeta ta ce, "Na san an kawo ni ne nan gidan bisa laifin shiga gidan Sarki har cikin tururakarsa da niyyar kashe shi, wanda ka'ida hukuncin kisa ne a kanki amma sai gashi an kyale ki! Ina fatan kin san dalilin da ya sa ba a kasheki din ba ko?"
To Masu karatu nima fa bansan wannan dalili ba, dan haka zamu rugunduma mu tafi wajen Barita domin da alama ita tasan dalilin daya sa ba a kashe ilaila ba.
Sannan ga masu son complete pdf zasu iya tuntubata ta Numberta har ma da wasu littattafan 08138873799
GWARZON SADAUKI
Littafi Na Daya (1)
Part D
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Cikin mamaki Ilaila ta dubi Barita ta ce, "Kina nufin cewa idan na sauya tunani da

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

4 Comments On GWARZON SADAUKI Book 1
avatar
maimunatu-7

10 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
maimunatu-7

10 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
daiy

10 months ago

Reply

Replying to maimunatu-7

Ki downloading ki karanta ko ki karanta shi anan shafinmu amma ki sani kafin ki iya downloading dole sai kinyi subscribtion na shafinmu wanda mafi karanci shinw 1k Naira

avatar
atiku

9 months ago

Reply

Zansamu complete littafan nan a pfd kuwa

Please Login or Register in order to submit comment