Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shawara zan iya cimma burina?"
Barita ta ce "Kwarai kuwa. Ai kowane mutum yana da buri a rayuwarsa ba ke kadai ba ce kike da shi. Ki tsaya, ki yi nazari da lissafi a kwakwalwarkil Ki đauki misali a kaina. Ni din nan na kasance jaruma ta gaske domin sau tara ina jagorantar yaki a kasar nan ana samun nasara. Na san kowane irin tuggu da makirci alvaki. Idan ina son mulki ko yaki!
dukiya zan ya mallakarSu a rana đaya. Amma mene ne dalilin da ya sa ha zauna a wannan kurkukun na Sarkin Misira na biyana albashin da bai wuce na kasheshi a kankanin lokaci ba? Lallai ruwa baya tsami banza Yau shekarata bakwai ina aiki a nan gidan kuma ba komai nake zaman jiran ba facel ke din nan. "
Sa'adda Ilaila ta ii wannan batu sai mamaki ya kara turnuketa ta dubi Barita cikin alarmun rashin fahimta ta ce, "Ban gáne ni kike jira ba. A kan wane dalili kika shafe shekaru bakwai kina jirana a nan kuma ya ya akal vi kika san cewa zan zo ban din?"
Sa'adda Barita ta j wannan batuı sai ta yi lmurmushi ta ce "'Saurin me kike yi haka? Kada ki damu za ki sami amsar wadannan tambayoyin naki amma ba daga bakina ba sai daga bakin shugaban dakarun gidan nan gabadaya."
Ilaila ta ce, "Wane ne kuma shugaban dakarun gidan han?"
"Sunansa Gadaraz duk wani umarni daga gare shi nake karbalKafin ki san komai sai kin haye wasu jarrabobi guda biyu ko uku da za mu yi miki."
Ilaila ta ce "Wane irin jarabawoyi za ku yi mini kuma a kan wane dalili?
Barita ta murtuke fuska ta ce Ba kodayaushe ba ne ake yin tambayoyin komai yana da lokacinsa. Shiru ma amsa ce.
Yanzu za ki tafi izuwa dakinki, za ki koyi wani darasin a wajen abokiyar zamanki,"
Barita ta gama fadin hakan sai ta tafa hannunta sau biyu nan take wata Badakariya ta shigo wani irin kallo Barita ta yi mata sai kawai ta kama hannun Ilaila ta tasheta tsaye ta ja ta suka fice daga cikin đakin suka nufi Inda jerin dakunan fursunonin| yake.
Ta wannan lokaci gabadayan fursunonin gidan suna dakunansu a kulle. A jikin kofar kowane daki akwai lambarsa. Sai da aka wuce sama da dakuna arba'in sannan aka iso dakin da za a sa Ilaila mai lamba arba'in da daya.
Da isowarsu bakin kofar dakin sai Badakariyar ta dauko wani makulli a cikin aljihunta ta sa a cikin kafar kubar kofar ta murda. Take kofar ta bude sai ta hankada Ilaila ciki sannan ta janyo kofar ta rufe da makullin.
Wata mace ce kwance a kan gado na daya dake cikin dakin ta rufe fuskarta da mayafi Duk da cewa ta ji motsin bude kofar dakin oami da $higowar Ilaila sai dai ko motsi bata yi ba, sai da Ilaila ta zo kanta ta tsaya tana kallonta sannan ta bude baki ba tare da ta bude fuskarta ba ta ce, "'Sannu da zuwa Jaruma Ilaila, ina yi miki barka da zuwa mugun gida. Zauna a kan gefen gadonki mu yi magana."
Ba tare da wata gardama ba kuwa sai laila a ije ta zauna a kan gefen gadon. Zamanta ke da wuya sai matar ta mike zaune daga kwance ta bude fuskarta.
Koda Ilaila ta yi arba da ita sai ta kamu da tsananin mamaki kuma ta firgita ainun, ba ta san sa'adda ta matsa baya ba zuwa can karsher gadon ta dube ta a tsorace ta ce, 'Ke Nazima ashe ba ki mütu?"
Sa'adda da Nazima ta ji wannan tambaya sai ta yi murmushi ta ce, "Ni kaina ban san cewa ban mutu ba sai da na farfado na tsinci kaina a cikin wannan kurkükun. ldan ba ki manta ba a lokacin da aka tura mu dajin Hairul Salas domin ceto ráyuwar Yarima Ansar mú tara ne jarumai mata amma ai mu uku ne muka isa dajin a raye. Ni da ke da kuma wata jaruma wacce duk ta fi mu karfi da iya yaki, wacce ta rufe fuskarta har muka rabu dá ita ba mu ga kamanninta ba. To ba wata ba ce wannan jaruma face Barita shugabar dakarun mata na wannan kurkukuni.
Lokacin da Nazima ta zo nan a zancenta sai ta ga laila ta yi shiru tana kallon kasa tana tunani!
Nazima ta taba kafadarta ta ce "'Wai shin kina tare da ni kuwa?"
Ilaila ta gyada kai talce! Ina tare da ke ki dan ba ni lokaci kadan so nake na tuno da duk abubuwan da suka faru a dajin Hairil Salas tun daga farkon tafīyar tamu har izuwa dawowarmu. Kin san fa yau shekara shida kenan.
Gama fadin hakan ke da wuya sai Ilaila ta rufe idanunta ta cigaba da tunani kamar haka:
Abin ya faru ne a wata safiyar Juma'a a cikin kasuwar birnin ta Misira, A wannan lokaci kasuwar ta cika makil da mutane maza da mata ana ta harkokin kasuwanci, kawai sai aka ga wasu dakarun gidan sarki su hudu sun shigo cikin kaasuwar bisa dawakai dauke da wadansu takardu suna watsawa mutane. Awannan lokaci Ilaila na tsaye a kofar wani shago tana siyen kayan rafi.
Ko da aka watso takardun gabanta sai ta sunkuya ta dauki guda daya ta fara karantawa kamar haka:
Sako daga Sarkin Misira zuwa ga duk wani jarumi wanda ya yarda da kansa, lna mai sanar da ku cewa dan uwana Yarima Ansar ya fada hannun Dakarun Sumame a shekaranjiya da safe lokacin da ya fita Zuwa bayar gari rangadi, nasa dakaruna sun tafi nemansa amma har yau dayansu bai dawo ba. Duk jarumin da iya sami nasarar dawo da dan uwana a rayc cikin koshin lafiya zan ba shi kyautar Dinare cikin rijiya mai tsawon kamu arba'in a matsayin tukuici.
Lokacin da Ilaila ke karanta wannan takarda sauran jama'ar dake kasuwar ma suna ta karantata amma duk wanda ya ii sakon dake cikir wannan takardar sai nan take ya yar da takardar.
Nan fa jama'a suka rinka fadin albarkacin bakinsu wasu su ce ya za a yi a sami wanda zai iya yin aikin wanda ya gagari dakarun sarki! Wasu kuma suka rinka cewa ai abu ne na sa'a.
Duk wanda yake da rabo shi ne zai sami wannan babbar kyauta amma kuma aiki ne mai hadarin gaske wanda daida yake da mutun ya siyar da rayuwarsa. Dalii kuwa Shi ne a duk sa'adda dakarun sumame suka kama mutum a bayan gari suna tafiya da shi ne izuwa cikin dajin Hairil Salas, shi kuwa dajin Hairil Salas dauke yake da rukuni-rukuni na dakarun sumame a kalla sun kai guda bakwai. Kowanne rukuni guda yana da sama dadakaru.dari kuma suna buya ne a cikin duhuwoyi da kan manyan tsaunika.
Yawanci idan suka kama mutum suna maisheshi bawa ne su siyar da shi ga wasu dakarun sumamen daga caan kuma a daukc shị daga nahiva gabadaya a kai shi wata.
Sa'adda jaruma Ilaila ta zo karshen a karatunta kan wannan takarda sai ta it an cd duk ljarumi da yake son ya yi wannan aiki ya isa gidan Sarki gobe da safe domin a hada shi da abokan tafiya kuma a bashi guzuri gami da somin tabin ladan aikin da zai tafi. Koda ganin hakan sai murna ta kama Ilaila saboda ta san cewa ta sami wata dama wacce ta dade tana jira. Nan dai ta kammala siye-siycnta ta tafi gida
Gidan Ilaila yana can karsher gari ne inda babu mutane kuma ita kadai take rayuwa a cikin gidan sai wata magenta guda daya. Da shigar Ilaila cikin gidan sai ta wuce kai tsaye izuwa dakin girki ta ajiye cefanen da ta yi a kasuwa magenta na biye da ita da gudu. Dama ta siyo wani soyayyen kifi don haka sai ta dawo falo ta zauna sannan ta zubawa magen kifin a cikin wani kasko Magen ta kama cin kifin ita kuma Ilaila ta kura mata idanu!
Ilaila ba ta da wani buri wanda ya fi ta sami damar yin arba da Sarkin Misra ta kasance shi ta sami kusancin da za ta iya kasheshi. Bisa wannan dalili ne kadai ta kudiri niyyar shiga wannan aiki na zuwa dajin Hairil Salas ba wai don ladan da za a biya ba kuma ko kadan ba ta yi tunanin irin mugun hadarin da za su fuskanta ba a jwannan gagarumin aiki, ita kadai Ilaila ta yi ta tunani gami da shirye-shiryen yin wannan tafiya har gari ya waye.
Tun kafin alfijir ya keto Ilaila ta mike ta kammala shirinta. Bayan ta yi shigar yaki sai ta rufe fuskarta da bakin mayafi sannan ta fito daga cikin gidan nata. Har magen nan ta biyo ta sai ta koreta ta ruga cikin gonakin dake bayan gidan Ilaila ta janyo kofqrat gidan ta sa makulli a kulle, kawai sai ta kwance dokinta ta hau ta zabure shi izuwa gidan sarauta.
Da isowar Ilaila kofar gidan Sarkiko kallonta ba a yi ba, aka bude mata kofa ta kunna kai ciki ta ci gaba da tafiya bisa dokinta har ta iso babbar harabar gidan inda ta iske abokan tafiyarta mahaya mutum tara a jere. Kawai sai ita ma ta shiga layinsu ta tsaya. Abin da ya bai wa Ilaila mamaki shi ne gabadaya abokan tafiyar tata mata ne zalla su tara babu namiji ko guda daya.
Daya daga cikinsu ta rufe fuskarta da hular karfe ta yaki ba a ganin komai face shatar idanunta hancinta da kuma bakinta.
Lokacin da wadannan dakarun mata takwas suka ga Ilaila ta shigo cikinsu ta tsaya sai gabadayansu suka kura mata idanu amma ban da wacce ta rufe fuskarta da hular karfe.
Adaidai wannan lokaci ne suka ji an busa algaita kuma an buga tambari alamar cewa Sarki ya fito. Ai kuwa sai ga Sarki ya iso gaban wadannan mayakan mata guda tara wasu tsirarun dakaru da fadawa na take masa baya.
Sa'adda ya zama cewa tazarar da ke tsakanin Sarki Marhat da su ba tanwuce taku biyar ba sannan ya tsaya cak ya dube su daya bayan daya da kyau kuma ya dubi wani babban Bafadensa dake tsaye daf da shi ya ce.
"Wace ce waccan jarumar da ta rufe fuskarta da bakin mayafi kuma ya ya aka yi gabadayansu suka kasance mata babu namiji ko guda đaya a cikinsu Bafaden ya ce Ya shugabana waccan jarumar da ta rufe fuskarta da bakin mayafi a can bayan gari take rayuwa ita kadai a cikin gidanta na haya, a iya bincikenmu ba mu gano asalinta kd danginta ba a garin nan kuma ba ta yin mu'amala da kowa amma an ce a garin ta girma kuma tun tana Karama ta taso da jarumtaka.
Sa'adda Sarki Marhat ya ji wannan batu sai ya sake kura wa Ilaila idanu har izuwa tsawon yana dakiku daga can kuma sai ya y murmushi ya dubi Bafaden ya ce babu matsala ma koda tana da wani mugun hufi kanmu tun da ba za ta dawo araye ba. Maza a ba su guzuri da kuma dukiyar da muka yi alkawarin ba su.
Ba tare da bata wani lokaci ba kuwa aka kawo guzuri da dinare mai yawa aka rarrabawa mayakan matan tara sannan Sarki Marhat ya dube ya, Yanzu ha sallameku domin ku tafi ilzuwa dajiN Hairil Salas domin karbo dan'uwana yarima Ansar daga hannun dakarun sumame in dai kuka sami Wannan nasara lallai zan cika alkawarina a garcku na baku dinare cikin ijiya kamu arba'in zurfi da fadi.
Ko da jin wannan batu sai gabadayan mayakan matan guda tara suka zare takubbansu daga cikin kufe sukal daga sama suna masu yin kururuwa, Sannan suka lashi akubban da harsunansu. Wannan alama ce ta cewar ba gudu ba ja da ba sun đauki alkawarin cika wannan aiki.
Nan dai suka mayar da takubban nasu cikin kufc sannan suka kada linzamin dawakansu suka juya da baya suka nufi kofar fita daga cikin gidan sarautar amma sai Sarki Marhat ya ga Ilaila ta juyo tana yi masa wani irin kalld shi kuwa sai ya ba da kallon murmushi na mugunta har sai da suka fice daga cikin gidan sarautar gabadaya, sanan Sarki Marhat ya dubi babban bafadensa ya "Na ga wutar daukar fansa a cikin idanun waccan yarinyar mai bakin mayafi a fuska Duk yadda aka yi akwai wata tsohuwar gaba A tsakanina da ita Ta kowane hali kada a bari ta tsira da rayuwarta."
Babbanl bafade ya fisina ya ce "An gama ya shugabana.
Shi dai Yarima Ansar shi ne kadai dan'uwan Sarki Marhat na jini wanda ya rage a duniya don haka a masarautar gabadaya shi ne kadai zai iya gadar karagar mulki. Bisa wannan dalili ne Sarki Marhat ya dauko hayar wasu dakarun sumame va sa suka sace Yarima Ansar lokacin da ya fita rangadi bayan gari domin a batar da shi gabadaya.
Bayan dakarun sumamen sun dauke Yarima Ansar sun tafi da shi sai suka yi kicibis da wasu bakin dakarun sumamen a cikin daji inda yaki ya barke a tsakaninsu. Take a wajen kowa ya mutu Yarima Ansar ne kadai ya tsira da rayuwarsa ya ruga cikin daji da gudu kuma ya gano cewa dan'uwansa ne Sarki
Marhat ya shirya masa wannan makirci domin a siyar da shi a matsayin bawa a kai shi can wata nahiyar inda ba zai taba dawowa ba sai dai ya gama rayuwarsa a cikin bauta.
Lokacin da labari ya riski Sarki Marhat cewar dakarun sumamen da Suka tafi da yarima Ansar duk sun mutu kuma ba a ga Yarima Ansar din ba sai hankalinsu ya dugunzuma. Bisa wannan dalili ne ya sa gasar Dinare mai yawaa kan wanda ya je ya dawo da shi amma sai ya bayar da umarnin cewa duk wanda ma ya samo shin shi ma a kashe shil don kada ya sanar da mutane sirrin makircin da ya kullawa dan'uwansa Yarima Ansar.
Idan kùma järuman da aka tura nemo Yarima Ansar ba su samo shi ba to a kama su a kai su kurkuku a kulle amman banda wannan jaruma mai hülar karfe.
Al'amarin Jaruma Ilaila kuwa abin da ta ayyana a zuciyarta shine idan har Sun sami nasarar samo Yarima Ansar sun zo da shi gidan sarki to a nan take zata yi amfani da wannan damar ta kashe shi.
Lokacin da mayakan matan guda tara suka fito daga cikin gidan sarautar birni Misira sai suka nausa cikin daji Suka yita tafiya bal yada Zango har tsawon sa'a Shida sannan suka tsaya a bakin wata korama domin su huta kuma su ci abinci.
Tsayuwarsu ke da wuya sai kowa ya sauko daga kan dokinsa suka fara daur3 dawakansu a jikin bishiyoyi, suka karasa bakin koramar suka shiga gefenta ta zuba ruwa a jikinta.
Jarumar dake zaune kusa da Ilaila ce ta dlubeta cikin murmusbi ta ce Sunana Nazima ke kuma fa?"
Ilaila ta maida mata martanin murmushi ta ce "'Sunana Ilaila. Me yasaki shiga wannan gasar mai hadairn gaske?
Nazima ta yi gwauron nunfashi sannan ta ce "Sau tari akan ce dole take sa mutum ya tari abinda ya fi karfinsa. Mu uku ne a gidanmu kuma dukkaninmu mata ne. Iyayenmnu sun mutu tun muna yara sannan nice babba kuma sai naje kasuwa nayi dako sannan nake iya samo mana abin da zamu ci tsawon shekara da shekaru haka muke gudanar da rayuwarmu har yanzų da na kai shekara ashirin da Uku. A gidan haya muke da zama kuma yanzų saurą wata dáya kacal na aurar da Kannena mata amma ga shi ban ajiye ko dinare daya ba. Saboda haka ina ganin takardar da Sarki ya bayyana wannan gasa sai na kudiri da niyyar Shigarta domin na biya bukatata.
Ilaila a yi ajiyar numfashi ta ce, Ni kuwa ban Shiga wannan gasa fomin kudi ba sai domin cika wani tsohon buri dake cikin zuciyata."
Ayi haƙuri jina shiru kwana biyu ina cikin damuwa ne shiyasa I can't post wallahi shiyasa I'm sorry guys
Ga masu son complete pdf zasu iya tuntubata ta Numberta har ma da wasu littattafan 08138873799
GWARZON SADAUKI
Littafi Na Daya (1)
Part E
Marubuci: Abdulaziz Sani M/Gini
Typing: Abubakar Saleh AlQuyraemey
Ko da jiin wannan batu sai Nazima ta dubi Ilaila cikin mamaki ta ce. "Ke kuwa wane irin buri ne haka wanda har zai sa ki sallama rayuwarki dominsa?"
Ilaila ta ce Ya fi dalilin da ya sa kika sallama taki rayuwar domin inganta ta 'yan'uwanki. Kamar yadda Ilaila da Nazima ke yin wannan hira haka sauran abokan tafiyarsu ma suke yin tasu hirar dabam amma ban da wannan jaruma mai hular karfe domin ita tun da aka fara wannan tafiya ma ba ta yi
magana da kowa ba ware kanta ma ta yi da aka isi bakin wannan korama kuwa a haka ta wanke fuskarta ba tare da ta cire hular karfen ba."
Bayan kowa ya gama zuba ruwa a jikinsa sai suka fito daga cikin koramar suka koma gefe daya. Nan take kowannensu ya bude jakar guzurinsa suka dauko abinci suka fara ci.
Ita kuwa mai hular karfe sai ta sake komawa can gefe daya ta jingina da wata bishiya tana hutawa. Ba ta cl komai ba amma sai ta ɗauko battar ruwa ta kwalkwala sau uku sannan ta zuba idonta akan sauran abokan tafiyar amma hankalinta ya fi karkata kan su Ilaila.
Duk irin kallon da take yi mata ashel Ilaila na lura tun a farkon fara tafiyar ma. Hakan ne ya sa Ilaila ta ɖubil Nazima ta ce "Ni fa ban yarda da wancan jarumar mai hular karfe ba. Akwai alamun munafurci a cikin idanunta. Ina ji a jikina cewar an hada baki da ita domin a cutar da mu cikin wannan tafiyar in ba don hakan ba saboda me zata rinka ware kanta daga cikinmu?"
Nazima ta yi ajiyar zuciya sannan ta ce "Ni ma ina jin hakan a jikina don haka ya zama wajibi mu yil taka-tsantsan da ita, to amma fa ita çe shugabar wannan tawaga tamu, na ji hakan ne daga bakin wani badakaren sarki kafin ki zo ki samemu.
Ilaila ta ce "Abin da nake zargi ya tabbata kenan."
"'Mene ne kuma abin da kike zargi?"
Ilaila ta yi murmushi ta ce "Ba sai na fada miki ba ai za ki gani da idanunk domin sannu ba ta hana zuwa."
Haka dai su llaila suka ci gaba da hutawa a wannan wuri har magariba ta tiske su Magariba na yi sai mai hular karfe ta mike tsaye ta fara shiri sannan ta dubi su ilaila ta ce "'Saura tafiyar rabin sa'a mu shiga dajin Hairil Salwas don haka ku tashi ku Shirya yanzun nan za nu ci gaba da wannan tafiya.
Ko da jin wannan batu sai Ilaila ta dubi jarumar ta ce "Ya za ki ce mu tashi mu ci gaba da tafiya a cikin eannan daren alhalin inda za mu shiga ko da rana tsaka ba a ganin mugayen dake buya a cikinsa bare a cikin duhun dare,"
Cikin fushi mai hular karfe ta dakawa Ilaila tsawa ta ce "Ke yanmata ki yi sani cewa jarumi na kwarai baya tsoron dare ko rana. Kowa ya sayi rariya ai ya san za ta yi zubar ruwa. Dukkaninmu nan mun san da irin hadarin dake cikin dajin Hairil Salas amman a hakan muka amince muka siyar da rayuwarmu, Ki sani ni ce shugabarku a cikin wannan tafiya.amma idan kina ganin cewa ban dace da matsayin ba zan baki dama yanzu mu gwada 'yar kashi. Idan kika sami nasarar kai ni kasa a cikin rabin sa'a na yarda zan ba ki jagorancin tafiyar tamu, kuma duk umarnin da kika bayar ni ma shi zan bi, amma idan ni ce na kai ki kas to dole ne ki ci gaba da bin umarnina babu musu ko gardama.
Ko da jin wannan batu sai Nazima ta dubi Ilaila ta kada kai tana mai yi mata nuni da kada ta amince da wannan sharadi.
Ilaila ta dubi sauran abokan tafiyar ta ga suma duk sun nuna mata hakan kawai sai ta yi murmushi ta dubi mai hular karfen ta ce, 'Na amince da wannan sharadi naki.
Nan take mai hular karfe ta cire makaman yakin dake jikinta ta watsar a gefe guda sannan ta gyara tsayuwa ta yafito Ilaila da hannu tana nufin ta taho su gwabza.
Aikuwa sai ita ma Ilaila ta ciro makaman jikinta, ta watsar a kasa ta tsaya tana kallon mai hular karfe!
Suka fara kallon kalo har tsawon dakika arba'in. Kawai sai Ilaila ta ruga da gudu zuwa kan mai hular karfe cikin zafin nama Kafin mail hular karfe ta ankara tuni Ilaila ta sureta ta yi sama da ita zuwa kan kafadarta daniyyar ta bugata da kasa. Amma sai mai hular Karfen ta sa guiwar hannunta ta doki gadon bayan Ilaila.
Ba shiri Ilaila ta direta kasa kuma ta tsuguna kasa bisa guiwarta guda saboda zafin da ta ji a gadon bayan nata.
Cikin hanzari mai hular karfe ta kawowa Ilaila bugu da kafa zuwa kan fuskarta Ilaila ta sa ahannayenta biyu ta kade kafar tata.
Nan fa suka ruguntsume da azababben fada ya zamana cewa suna kaiwa junansu naushi da bugu da hannu da kafa suna karewa. A hakan suka ci gaba da kokarin kai juna kasa, amma sai abu ya gagara sai da suka shafe dakika arba'in da biyar suna kwamarzuwa ya zamana cewa sun hadawa junansu jini da majina amma kuma duk suna iya jure bugun.
Al'amarin da ya daurewa su Nazima kai kenan domin gashi dai a zahiri jaruma mai hular karfe ta fi Ilaila girma kwarjini gami da kirar karfi amma sai ga shi karfinsu na neman zuwa daya.
Su Nazima dai ba su san sa'adda suka fara yi wa Ilaila tafi ba. Ko da ganin haka sai mai hular karfe tanfusata ainun don haka sai ta ja da baya ta sake gyara tsayuwa ta yafuto Ilaila da hannu a karo na biyu.
Da ganin haka sai Ilaila ta ji a jikinta cewar wannan karon fa akwai mugun tanadin da mai hular karfe ta yi mata, idan ta ruga gareta don haka sai ta fara tunanin cewa ya kamata ita ma ta sauya salo.
Maimakon Ilaila ta ruga da gudu izuwa kan mai hular karfe sai ta tunkareta da klan sauri-sauri a maimakon gudu.
Tana isa daf da ita sai ta kai wa kafarta sura Cikin zafin nama mai hular karfe ta janye kafarta, kafin Ilaila ta yi wani yunkuri tuni mai hular karfe ta rungumeta a kan kirjinta, kawai sai ta yi amfani da hannayenta biyu ta matse gadon bayan Ilaila.
Ilaila ta kurma uban ihu sakamakon tsananin zafin da ta ji domin ji ta yi kamar kasusuwan bayanta sun karye don haka ba ta san sa'adda ta saki jikinta ba, gabadaya don haka sai mai hular karfe ta maka ta da kasa.
Ilaila ta bajc tana numfarfashi ta kasa mikewa Mai hular karfe ta sunkuyo da fuskarta daidai kanta Ilaila ta ce.
"Bambancina da ke a bayyana yake daga yanzu babu sauran gardama a tsakanina da ke. Tashi mu ci gab ada tafiya.
Tana gama fadin hakan sai ta mikawa Ilaila hannunta ta kama ta.tashe ta tsaye. Ba tare da bata wani lokaci ba $ai duka su taran suka kunna fitilun itatuwa sannan suka haye kan dawakansu suka ci gaba da tafiya domin isa dajin Hairil Salas.
Sai da suka shafe sa'a daya cif suna tafiya sannan suka iso farkon dajin hairil Salas. Dama mai hular karfe ce a kan gaba don haka sai ta ja linzamin dokinta ta tsaya cak, ta dubi cikin dajin iya hangenta kuma ta.dubi dama da hagun dajin ta yi nazari.
Kawai sai ta sauka daga kan dokinta ta daure shi a jikin bishiya sannan ta zare takobinta kuma ta rike garkuwarta bayan ta yar da fitilar icen dake hannunta kawai sai a kunna kai lzuwa cikin dajin.
Ko da ganin haka sai su ma Su Ilaila suka yi koyi da ita suka bi ta a baya da sauri! Duk da cewa dare ne akwai duhu amma sai ga shi suna ta tafiya tamkar suna ganin duk abin da ke gabansu amma a zahirin gaskiya ba sa ganin komai sai dai suna taka sawayensu a hankali yadda ba alljin motsin kuma suna amfani da kunnuwansu domin jin duk wani motsi a cikin dajin, bisa mamaki sai da Suka shaf kusan dakika daril da saba'in suna tafiya ba su ga komai da kowa ba!
Kwatsam sai suka iso wani katon fili wanda aka share shi sarai ko ciyawa daya babu kuma ba bishiyoyi da dawatsu a wajen Suna isowa.wannan wuri sai kuwa suka ji an kewaye su da fitilolin itatuwa birjik ba adadi! Dakarun sumame ne rike

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

4 Comments On GWARZON SADAUKI Book 1
avatar
maimunatu-7

10 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
maimunatu-7

10 months ago

Reply

Inasan litafin nan pls

avatar
daiy

10 months ago

Reply

Replying to maimunatu-7

Ki downloading ki karanta ko ki karanta shi anan shafinmu amma ki sani kafin ki iya downloading dole sai kinyi subscribtion na shafinmu wanda mafi karanci shinw 1k Naira

avatar
atiku

9 months ago

Reply

Zansamu complete littafan nan a pfd kuwa

Please Login or Register in order to submit comment